KHAIREEYAH CHAPTER 12

Khairiyya ta kasa believing abun da kunnen ta yaji, sauka tayi a motar taje daf kusa dashi tace

“I beg your pardon”

Sabir ya kara cewa

“Yes is true, bazan miki karya ba, I mean what I said, I can kill for you, I can die for you”

Murmushi Khairiyya tayi sosai tace

“Mei yayi zafi haka, oya give me your digits nayi dialing yanxu”

Atake ya bata tayi dialling sai gashi yashiga, Sabir yace

“Toh mss hot wani suna zanyi saving”

Khairiyya tana murmushi wanda ya kara fidda asalin kyaun ta tace

“Khairiyya or Kim”

Sabir yace “kina son Kim Kardashian neh haka”

“No ni asalima bata burge ni, KIM shortcut na suna nah kenan, full name nawa Khairiyya Ibrahim Muhammad”

Sabir yace “Ohhh dats nyc mss hot, zanyi saving da Kimhot”

Khairiyya tace “ohhh so swt of you, kasan nayi lattin school sai munyi waya bye” ta shiga motanta ta fisga sai school, parking slot tayi parking motar ta, a lokacin karfe tara da rabi, makaran tan shuru dan ko wani student suna ajin su, tafiyan ta take ahankali kamar wacce take tsoron taka kasa, d’aga kai da zatayi sukayi ido hud’u da Corper Chris, Murmushi take masa amma shiko ya d’aure fuska sai ra6e ra6e yake dan kunya, Khairiyya tace

“Good Morning Corper Chris, 2days ban ganka ba, I so much miss you”

Shiko ko kulata baiyi ba yawuce abun sa, dariya ta fashe  tace ohhh my goodness I just can’t forget that day it was so much fun

An tashi a makaranta Khairiyya taja motar ta, gudu take sosai akan kwalta, bata ankara ba kawai taji ta buge wata mota C400, tace

“Ohhh ma God, mtseww yanxu dole na sauka na basa hakuri kenan, lemme pick wayata incase yace na biyasa na masa transfer a account nashi”

Shiko wanda ta buge tsai da motar yayi kawai koh sauka baiyi a motar ba

Khairiyya tsoki taja tace

“Mtsew yanxu bazai sauka acikin motar baneh ya wani zauna salon nazo na basa hakuri kenan ai nima motar tawa taji ciwo”

Knocking mirrow motan tayi, takalmin soja na fara hangowa, wa zan gani ni Nana, Captain Suraj neh cikin uniform nasa wanda yake mugun masa kyau, bakin ta mutuwa yayi data gansa, kasa furta komai tayi, shiko Suraj wayan sa ya d’auka yayi dialling number’n da Khairiyya ta basa lokacin, sai kawai wayan ta fara ringing a hannun ta,Suraj yace

“Saura na kiraki anjima kice wrong number”

Shiga motar sa yayi ya fisga ya barta a wajen tsaye ta kasa furta uffan

Sai kusan bayan minti uku ta fusga iska, tace

“Yaa Allah ka mini tsari da soldiers”

Shiga motar ta itama tayi sai gida, tana shiga gida tayi wanka tayi sallah taje dining dan cin lunch, bud’e food flask tayi taga pounded yam en eghusi soup, tsoki taja tace

“Dije ta raina mini sense wlhy, sau nawa zan gaya mata banson cin heavy food, batasan ina maintaining figure na baneh mtsew” kwala wa Dije kira tayi sai gatanan ta fito

“Wai ni Dije banyi warning naki akan heavy food ba, koma ace zakiyi sai kinayi after every month”

“Ai hajiya last time danayi pounding yam ai yakai wata biyu ba d’aya ba”

Khairiyya tace “Toh ni bana ra’ayin ci, dafa mini Indomie yanxun nan”

Dije tace toh Hajiya, azuciyan ta cewa take ai koh Hafeez na book d’in MUNAY (Burin hafeez) bazai nuna miki cin indomie ba, bayan minti biyar sai ga Dije ta ajiya mata indomie a gaba wanda yasha kayan had’i, Khairiyya tace

“Yawwa koh kefa Dije amma kullum ana fad’a muku abu d’aya”

Bayan ta gama ci ta wuce d’akinta ta kwanta, amma sai mei, tunanin sojan nan neh fal a ranta,sai tunanin Cap Suraj take, wai shin ya kirata a waya yace mata mei, mtseww banson takura da shishigi a rayuwa ta wlhy”

Wayan taneh ya fara ringing, duba kan screen tayi taga Sabir, dogon tsoki taja tayi rejecting call d’in, wani number neh ya kara kiranta, mtseww nasan sabir neh  yakira da wani layi daban, d’aga wa tayi tace

“Haba Sabir daga baka number ta har ka fara damuna”

Can 6angaren wanda ya kira yace

“Cap Suraj not Sabir”

Baki ta bud’e, dakyar ta iyi furta

“Umm yaa Suraj emm ina kwana”

Murmushi yayi wanda taje sautin yace

“Ina yini dai, just wanna tell you expect me at night around 8”

Khairiyya tace “Suraj malami na yana zuwa bayan isha’i, saidai kazo immediately bayan Magrib”

 

Shuru yayi kan yace Toh shikenan zaki ganni bayan Magrib In Shaa Allah, bye” ya katse wayan

Wayan tabi da kallo, mei zaizo yamini mtsww

Ana idar da sallah Magrib Khairiyya tayi wanka ta saka sleeping dress, ta dau Qur’anin ta tana muraja’a, batafi minti goma da farawa ba taji wayan ta na ringing, dubawa tayi taga Suraj, d’auka wa tayi kan tayi magana yace

“Ina bakin gate”

“Toh” kawai shineh abun da tace ta zura wani dogon hijab har kasa tasaka, Haule takira tace akwai mutum a bakin gate a bud’e masa gate, kuma ki ajjeye mana kujeru biyu, kiyi serving nashi

Haule tana murmushi tace Toh hajiya kice munyi babban bako mana

Tsoki Khairiyya taja tace

“Please don’t think otherwise, karkiyi zaton koh saurayi nah neh, kawai gaisawa zamuyi, kina da clueless mind wlhy just go kifara aikin dana saka ki”

Haule tace toh Hajiya, bayan kamar minti biyar saiga Haule ta dawo tace

“Hajiya angama, bakon ki na jiran ki”

Toh nagode Haule, ta fitar da designers perfume nata ta fesa ta fita, zaune ta samei shi har ya bud’e ruwan da aka kawo masa

Zama tayi a d’ayan kujeran ta gaishe shi, fuska a sake ya amsa, shuru neh ya biyo bayan gaisuwan na kusan minti goma

” Khairiyya koh”Suraj yace da ita

She was surprise tace”How do u know”

Murmushi yayi yace kin manta aiki na neh, tace ohhh haka

Haka duk sukayi shuru kowa da abun da yake sakawa a ransa, Khairiyya sai cewa take a zuciyar ta

“Oh Emm Gee, he’s so damn boring, ba hira ba komai sai kallo nah mtsew na tsana mutum haka wlhy”

Shikuma Suraj cewa yake a zuciyar shi “Allah yayi halitta, koman ta mei kyau neh”

Khairiyya kasa hakuri tayi tace

“Ammm Yaa Suraj you are so boring, so sorry i dnt mean to be harsh but gaskian kenan” tana tura baki

Shiko kallon ta yakeyi kamar kar ta daina magana cox muryan tama soo swt, Khairiyya still taji shuru tace

“U Wanna catch some fun tomorrow, I mean if u re less busy we can hang out together, I can sense that u re living a boring life”

Kallon ta yake da mamaki, taya tasan yana living boring life, yace

“Ohhh wow that’s nice of you, Allah kaimu”

Ta amsa da Ameen, ya mata sallama yatafi itama ta shiga gida, tana idar da sallan Isha’i malamin ta yazo ya mata karatu, bayan ya tafi tayi wanka tabi lafiyan gado, wayan ta neh yafara ringing, duba screen tayi taga Sabir dan tayi saving number’n shi, d’auka wa tayi, shi yafara magana yace

“Haba mss hot, ya zaki mini haka neh”

Khairiyya tace “So sorry dude kasan yayana baya bari nayi soyayya sai da yardan shi, tun d’axu ina convincing nashi dakyar ya yarda amma da sharadin sai kun had’u dashi, yana so yaganka, Sabir yace

“Kar kiji komai mss hot ba matsala ai”

Khairiyya tace “Dude kace you can kill and die for me koh”

Sabir yace Sosai ma mss hot, I can kill en die for you, I can do anything for you trust me

Khairiyya tana murmushin mugunta tace

“Wow thanks dude, you are such a durlin, bye zanyi bacci miss you”

Sabir dad’i yaji da tace masa miss you da durlinyace

“Ohk mss hot sleep tight and sweet dreams of me”

Khairiyya tace sure durlin I will, ta katse wayan tace Oh ma God, m gonna catch some fun tomorrow 24/26

About Ismail

Check Also

BAKAR INUWA CHAPTER 23

Ganin taƙi cin komai Anne ta kira sunanta. Ta ɗago domin amsawa taci karo da …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *