KHAIREEYAH CHAPTER 11

Wata doguwar habbaya bak’i ta saka da touches blue a saman, tayi rolling da vail nashi, yau powder da lipgloose da mascara ta shafa batayi heavy makeup ba, ta saka takalmi high heel black yana da touches blue da Jaka black, ta d’auka  key mota

Hanya kicin direct tabi tashiga, ta kalla Dije tana wanke wanke, tace

“Dije ku shirya dake dasu haule na kaiku shopping”

Dije ta washe hakora tace Toh hajiya, ta wanke hannun ta tace hajia bara na musu magana, d’aga kai Khairiyya tayi tace

“Toh Wlhy na baku minti biyu idan baku fito ba zanyi tafiya ta” ta juya tabar kicin d’in

Fita tayi harabar gidan wajen parking space, wata bakar 4matic mota tashiga, wow motar ta kar6e ta ba karya, kafin ta rufe kofa har su Dije sun fito, suma suka shiga motar, gaishe ta sukayi tayi kamar bataji ba,Khairiya  tace

“Kar ko wacce tayi siyayyen sama da dubu talatin, toh nidai na fad’a muku”

Duk suka had’a baki sukace

“In Shaa Allah hajia”

 

Babbar Mall suka shiga, ko waccen su sai duba abin siya take, Khairiyya kuwa tana wajen agogo da bangles, tana cikin dubawa taje an tab’a ta tabaya, ba tare da ta juya ba tace

“Toh menene kuma, kar ko wacce acikin ku nace tayi siyayyan sama da dubu talatin, idan kudin ya haura toh bazan iya biya ba” ta cigaba da duba bangles d’in, aka kara tab’a ta tabaya, juyawa tayi a fusace tace

“Wai wani irin iskanci neh ha..,” bata karasa cewa haka ba tayi ido hud’u da wani yaro fari wanda akalla bazai wuce 22yrs ba, yana da matsanancin tsawo,da kananan ido, sai baki karami amma bak’i kirin, yana murmushi yace

“Oppps sorry baby, I really just can’t stop maslf but you are Hot”

Harara ta watsa mishi tace “I know ama Hot so please can u excuse me”

Yaron yace “Haba baby wannan ai ba class naki baneh, by d way sunana Sabir, ina karanta Info Tech a Malaysia yanxu haka hutu nazo”

Khairiyya tace “Sorry dude but ban tambaye ka ba, so why kake fad’a mini, I have nothing to do with that and please karka saka mini ciwon kai kabar nan”

“Baby I got Cash, zan iya baki ko nawa en I can buy any damn thing for u” cewar Sabir

Khairiyya tace “toh Mallam I ain’t interested, koh ce maka akayi banda kud’i, Wlhy saidai na baka badai kai ka bani ba, stupid jerk”

Bangaje shi tayi ta wuce, ta same Indo tace maza suzo siyayyan ya isa haka, basu gama ba dole suka bar mall d’in, Sabir bai hakura ba har wajen motar ta yaje yace

“Haba baby sonki dagaske nake koh number wayan ki kibani please”

Khairiyya bata kara cewa komai ba ta fisga motar ta tabar wajen

 

A yau su Khairiyya zasu koma makaranta dan hutun jamb da aka basu yakare, Haule ce tashiga d’akin Khairiyya dan ta da ita a barci, kwance take akan tile na d’akin akasa, ta dunkule da alama tana jin sanyi dan ga sanyi AC har biyu, ga iskan fan ga kuma sanyin tiles, tana sharan baccin ta ga kwalaben syrup har uku a kasa, Haule sai bubbuga ta take tana cewa

“Hajiya ki tashi yanxu fa karfe bakwai da rabi zakiyi latti” Khairiyya kam sai baccin ta takeyi, haka Haule ta cigaba da bubbuga ta har sanda ta tashi, da muryan bacci tace

“Wai ni Haule kee wace irin mutum ce ina bacci zakizo kina tadani ehh, ai wannan rashin hankali neh”

“Hajia kiyi hakuri naga zakiyi lattin makaran ta neh shiyasa na tashe ki” cewar Haule

Khairiyya ta harare ta tace

“Toh ina ruwan ki da makaranta na, nifa shishshigi neh bana so”

Hajiya kiyi hakuri cewar Haule, Khairiyya tana kumbure kumbure ta tashi ta shiga toilet, bayan minti uku sai gata ta fito, a gurguje tayi shirinta ta d’auka motar ta 4matic baka tafita dashi, tana kan titi taji ana mata horn da karfi, ta duba ta mirrow motar ta taga wata Benz blue tana binta, birik taja ta tsayar da motar, wanda ke cikin motar ya sauka a motar, ba kowa baneh illa Sabir, wanda suka had’u a mall, tana ganin shi ta madubin motarta taja wani dogon tsoki

Zuwa wajen motar yayi yace

“Baby gashi Allah ya kara had’amu, please number ki nakeso da address naki please”

Khairiyya ba karamin haushi ya bata ba tace

“Idan na baka uban mei zakayi dashi”

“Haba Baby zan na kiranki ina jin swt voice naki mana, the 1st tym I saw you I fall in love with you, love at 1st sight kenan please just give me your digits”

Dogon tsoki Khairiyya taja tace

“Toh bazan bayar ba, ana dole, kaga ka matsa mini a hanya koh na buge ka, idan na buge ka na buge banza kasan nayi lattin school koh”

Sabir gaban motar yaje yace

“Sai dai ki buge ni, I love you, I so much love you, to the end of infinity, I can kill for you, I can die for you, idan kin buge ni na mutu ba matsala sabida ina kaunar ki, ina mutuwar sonki

About Ismail

Check Also

BAKAR INUWA CHAPTER 23

Ganin taƙi cin komai Anne ta kira sunanta. Ta ɗago domin amsawa taci karo da …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *