[Advertisements⬇️]

KHAIREEYAH CHAPTER 7 - Bankinhausanovels
Thu. Oct 6th, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

KHAIREEYAH CHAPTER 7

 

Su kamalu sun tsure, fitsari neh kawai basuyi a wando ba, sai zufa suke duk AC da yake tashiwa a motar, dan su a rayuwar su suna tsoron sojoji balle sunga sunyi cracking bindigan su, d’aya daga cikin boys na Kamalu yace

“Wayyo Allah nashiga uku, wayyo Mamata idan sun kashe mu sun kashe banza fa Kamalu”

Kamalu kam kasa cewa komai yayi duk jikin sa yana 6ari, ba abun da suke ambato wa sai “wayyo”

Khairiyya ma tayi mugun tsorata, zuciyan ta sai tafasa yakeyi, sai “Inna lillahi wa Inna ilayhir Raji’un” take nanatawa idan sun har6e tama da sunan Allah a bakin ta

 

D’aya daga cikin sojan neh ya tambaye broh na Chris yace

“O’boy what happen, who are they”

Yayan Chris yace

“Sun ma Chris duka” a irin hausan shi da baiyi kwari ba, wasu sojojin tsoki sukaja wasu kuma sun nufa wajen Khairiyya

Tsawa suka daka musu

“Oya come out before we shoot you”

Jikin ta yana rawa ta fito a motar ta su Kamalu ma suka fito, duk kallon ta sukeyi d’ayan yace

“Ba ke bace d’azu kika shiga”

Tace “Yes Sir”

Yayan Chris yace “All of you go on your kneels now”

Duk suka zube kasa, Khairiyya ce tayi karfin hali tace

“Bakusan mei yafaru ba kawai zaku d’aura mana laifi, ni gaskia ba wani kneel down da zanyi, kun san ni wacece?” ba karamin karfin hali tayi ba tafad’a, sai jinjina wa kanta take

Brother na Chris yace

“I don’t care who the hell are you just go on your kneels”

Wasu sojoji suna basa hakuri akan ita mace ce wasu suna zigasa ai ta raina su neh, su Kamalu har sun fara shan duka, wata bak’ar mota ceh had’adde da hilox biyu d’aya a gaba d’aya a baya ya dunno kai zuwa gate d’in, gaba d’aya suka tsaya ba matsowa suka sara wa motoci ukun

Sojan gaban cikin jeep ya fito ya bud’e bayan, wani saurayi neh mei jini ajiki wanda bazai haura shekaru talatin da biyar ba, baza kira sa dogo ba amma shi ba gajera ba madai daici mai faffad’ar kirji da gani yaci gym, kalan sa irin chocolate colour mai kyau, yana da ido daidai da hanci wanda ya dace da fuskar sa, ga bakin shi karami sai saje wanda ya kwanta luff a kyakkyawan fuskar shi, fuska a murtuke ya fito a motar yana kallon Khairiyya da sojojin yace

“What’s happening here”

Duk sun rud’e suka ce

“Nothing Sir”

Ya juya wajen Khairiyya yana kallon ta yace

“What are you doing here”

Kallon sa Itama take, a jikin uniform nasa taga an rubuta *Captain Suraj a.a*, muryan ta yana rawa dan tayi matukar tsorata dashi tace

“Sir One of them try to rape me, a garin kare kaina shineh yaji ciwo and kuma shineh zasu mini duka nima”

 

“What! Ya juya yana kallon su” duk hankalin su ya tashi, ya kara juyawa yana kallon ta, ita kuwa sai zare zaren ido takeyi, yana ganin ta yasan sharri take musu dan shi yana iya ganeh gaskiar mutum da wuri

Yace “you can go now”

Ta juya wajen su Kamalu wanda suka d’an sha bugu tace tashi mu tashi

Ta 6angaren captain Suraj kuma mamaki yakeyi, wannan wace irin yarinya ce karama batajin magana tasa kanta acikin masifa bata tsoron abunda yan iska sojoji zasu mata yace

“Zamu raka ki gida”

Ya juya wajen sauran sojojin yace

“Idan nadawo zakuyi explaining abun da kuke so ku mata, stupid”

Aka bud’e masa mota ya shiga, su Khairiya ma suka shiga motar su, bayan ta suke bi, dan su Kamalu sunyi hanyan su daban, ita Khairiyya zuciyan ta na tsinkewa wai meisa dole sai ya biyo ni neh koh bai yadda da ni baneh, haka dai har suka karaso anguwar su wanda yake Circular Road, daidai tazo gate ta tsayar da motar, ta fita aciki shima Captain Suraj aka bud’e masa kofa yafita

Ya samei ta a inda take tsaye yace

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

“Ke daughter’n Alh Ibrahim Muhammad fu’ad mai naira neh”

Tace “Eh”

“Be carefull next time dan bakisan da irin mutanen da zaki had’u ba, dan daga ganin ki nasan ke kika ta6o su”

Khairiyya tace

“Nifa ban ta6o suba su suka fara” tana tura baki, hakan da tayi ba karamin kyau ya mata ba, kallon ta kawai yakeyi baya kifta ido, azuciyar shi cewa yake

“Yaa salaam Allah mai iko, irin wannan halittar”

Haka ta karashe maganar yana kallon ta, ita kuwa da ta lura haka ta buga masa hannu tace

“Hea you Suraj, what are thinking”

Yadawo hankalin sa yace

“Nothing, zan na zuwa dubaki In Shaa Allah duk time da nake maiduguri, do take care of yourself please”

Tana murmushi a fili amma can cikin zuciyan ta cewa take mtsw Mallam yi sauri ka tafi dallah na tsana shishshigi, tace

“Ohk I will, bye”

Ya juya zai tafi Itama zata shiga motar ta yace

“emm please can I have your digits”

Tace”sure why not”

Ya mika mata wayar sa ta saka numban ta, a take yayi dialing yashiga, yace save my number please

“Don’t worry I will, thanks” ta shiga motarta ta danna horn da karfi aka bud’e mata gate, shiko yana so ya tambaye sunan ta amma yakasa

Tana shiga gida ta fad’a parlour ta zauna akan kujera tace

“Wayyo Allah what a Day! munyi catching Fun sosai wow” sai dariya take idan ta tuna da Corper Chris da Kamalu yadda suka tsure da sukaga sojoji sunyi cracking bindiga, darawa take kamar wata zararriya, can bayan tagaji tafara ihun kiran masu aikin ta dan da tashigo bata gansu ba, atake duk su ukun suka fito, Khairiyya tace

“Wai bakuji na shigo baneh baza kuzo ku mini sannu da zuwa ba, tukunna ma uban mei kukeyi a ciki”

Duk sun tsorata dan kallon film sukeyi aciki wanda ya d’auke hankalin su basu san lokacin da tadawo ba, Haule neh tayi karfin halin cewa

“Hajiya kiyi hakuri kallo mukeyi bamuji ba”

Kallo ta watsa musu kan tace

“Ya muku kyau toh, Dije mei kika dafa”

“Hajiya pepper fish da soyayyan doya”

“Bana so bazan ciba, had’a mini hamburger da pickles kafin nayi wanka nafito”

“Toh Hajiya angama” cewar Dije

Khairiyya ta juya wajen Indo tace

“Ki gyara mini d’aki nah na upstairs zan koma can yau so kikai mini duk abun da is important can d’akin nagaji da kwana a kasa”

“Toh Hajiya” cewar Indo

Ta kara juyawa wajen Haule tace “had’a mini ruwan wanka yanxu” itama Haule ta fice

 

Saurayi neh fari sol wanda bazai haura talatin ba koh ishirin da tara,  kwance akan katuwar gado, idon sa arufe wanda yasa na kare masa kallo sosai, yana da dogayen eyelashes da gira kamar wanda aka zana bak’i sosai, ga hancin sa dogo kamar pencil sai bakin sa karami pink kamar wanda ya saka jan baki, ga sajen fuskar sa baki shima wanda ya dace da kalar sa,gashin kansa bak’i da d’an tsayi, fuskan nan wani waje yayi jaa zur haka ma jikin sa, da ganin alama duka aka masa

Bud’e d’akin akayi, wata mata wanda baxata haura shekaru hamsin ba tashigo, ko ba fad’a ba ansan jinin sace dan kamanni da suke, sai dai duk da haka tafisa haske, ta zauna kusa da shi tace

“Haba Zilyadeen, mei yayi zafi haka, tun ranar da abun yafaru baka magana baka cin abinci, meisa baka da hakuri neh just forgive en forget”

Bud’e idonsa yayi wanda ni Nana I was shock, idonsa manya manya fari kal dashi, Yace

“Mummy bazan ta6a forgetting  ba not to talk of forgive, taci mini mutunci ta ciwa Inna mutunci, ba yarinyan Fu’ad mai naira baneh, ai baza ta 6oya ba, zan koya mata hankali mummy, mummy sai ta…. ”

Bai karasa maganar ba tasaka yatsan ta a lips nashi, tace

“Shhhhh Zil, idan har ni na haife ka toh Forgive en forget, idan kana kauna ta ka yafe mata ta kacire wannan abun a zuciyar ka”

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]