[Advertisements⬇️]

JENNIFA CHAPTER 22 - Bankinhausanovels
Wed. Nov 30th, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Da kuka matar tacigaba da mgn plx ki sauke bindigar jikin hindu asnyaye ta sauke bindigar Ku yan’uwan sulthana ne Ku shigo ciki tayi gaba tana xubar da kwalla suka bita abaya dukkansu jikinsu amatukar sanyaye falon baki tai musu masauki ta kawo musu kayan motsa baki dukkansu babu Wanda yai marmarin taba kayan xuciyoyinsu sun kwadaitu da son jin y akai aka haihu aragaya sulthana tana zaune idonta yayi jajir ta hada kai da gwiwa sam bata San inda kanta yake ba sbd tsabar rudun daya ruda mata kwakwalwa matar ta fito hannunta dauke da jaka karama har yanxu kuka take ta xauna afalon kusa da sulthana sannunku da xuwa bayin Allah sunana hjy Aisha sulthana ba yata bace na tsince ta a abuja lokacin danaje xiyarara ganin yan’uwan mamana a shekara ta 1996 a watan December na dauko ta muka dawo nan da xama wannan shine kayan da na tsince ta dasu akwai photuna guda biyu da nata Dana wasu yanbiyu nasan tabbas kune sannan da wanann awarwaron ta dauko musu da kuma wannan barimar har da takaddun haihuwanta Wanda aranar ya tabbatar min da kwananta arba’in a duniya nayi kuka sosai akan wannan rashin imanin da aka akaitawa wannan jinjira wani mahaukacin kuka sulthana ta saki su Kansu jenny da hindu kuka su ka Sa cikin matukar karfin hali hindu tace wannan wacce irin uwace me watsar da yayanta ? Wani kallo na raxana hjy tai musu ban gane ba yanda ta watsar da sulthana hk ta watsar damu wani salati hjy ta saki cike da mmk da mugun ta ujjibi wannan ya tabbatar min da mahaifiyar mu Yar 9ja ce yaxama dole mu binciko ta a duk inda take hakane yayana hjy ta fada ubangiji Allah yasa adace amma zanso naji dalilin da xaisa ta watsar da Ku Jennifer tace abin mmkin shine shekara 1 da watsar damu ta kuma watsar da sulthana ita kanwarmu ce wannan abu dole ya daure kai haisam cikin matukar tausaya yace wllh ni kaina narasa warware wannan lamari abu sai kace wani lbrin film ko novel ? Cikin jin haushi sulthana tace bana jin ko a novel antaba wannan daurin gwarman haka suka cigaba da tattaunawa xuciyoyinsu tunkushe da kunci

    *******     *********

Kwanansu takwas suka dawo 9ja abinda yake daurewa kowa kai yanda basa iya xama waje daya da junansu sai sunyi fada suna sauka gidan hindu take g.r.a sulthana ta kalli hindu wannan gidan nawaye ?? Jennifer tace gidan Hindu ne tsaki sulthana tayi kinga bake na tmvy ba hade da galla mata harara akufule tace kuma na baki amsa ki dau mataki hindu tace gidana ne ya mutsa fuska sulthana tayi dama sai ke din bangane sai ni din ba mai kika mai dani ?? Sai ma amfada Yar daba Yar zaman kanta karuwa taja tsaki wani wawan duka hindu ta kaiwa sulthana ni ce karuwa ? Ta rufeta da duka da sauri jenny ta tunkude daga jikin sulthana wannan wacce irin masiface jenny ta fada kubarmu da masifa daya mana haba sulthana meyasa baki da kunya ? Tsaki sulthanan taja yayan karuwa har kunya garesu ? Sororo sukayi cike da mmkin mgrnta ta mike tana haki sbd dukan da hindu tai mata kwakwalwar kifi gareku idan Maman mu ba karuwa bace to wacece ?hawaye ya xubo mata wacce macece zata dunka watsar da yayanta haka barkatai ? Kuka Jennifer tasa tabbas hakane akwai sulke cikin nadi muddin na ganta sai tamin bayanin da xaisa har ta dinka wullar damu abola hindu tace wllh wllh duk da tana uwarmu wahalar Dana sha da gararin danayi sai na hukunta ta sulthana ta amshe da naku duk mai saukine duk randa muka hade shaketa zanyi kowa ya huta dukkanmu babu Wanda bashi da tabo ke tanuna Jennifer kafura ke kuma Yar daba ni kuma futsarriya ta dalilin futsara ta har sai da aka taba harbin hajiya ta Allah ne yasa tana da sauran rayuwa kai da ji kasan ba uwar arxikice ta haifemu ba haisam ne yai karfin halin katsesu kuyi hkr ba kowacce mgn ake fdawa iyaye ba duk min rashin adalcinsu akn yayansu kaga Malan sulthana ta katseshi sbd kai naka iyayen basu wullar da kai ba ? Toma ina ruwanka ? Nifa natsani shishshigi da tusa kai aruwata kaida wayancen banxayen sakarkarun ta nuna yaran hindu meye amfaninku akn rayuwarmu tsawa haisam ya kwatsa mata fuskarshi a tmke ki shiga hnklinki a tsorace ta kalleshi Allah ya baka hkr ke hindu ki sallami wayancen garadan dan banga amfaninsu ba bazan sallamesu ba idan ke bakiga amfaninsu ba ni na gani tare ki ka ganmu amana ce me karfi atsakaninmu banza Yar fashi kawai kar Allah yasa ki sallamesu…. Wanka mata mari Jennifer tayi tafashe da kuka Allah ya isa banza kafura da gani ubanki katon arnene dan wllh ban yadda ubanmu daya ba hindu tace da kin barni da ita na koya mata hnkl fitsarriya mara tarbiyya cikin jin haushi jenny tace akwai Mara tarbiyya irinki hindu taiwa jenny wani kallo kura ce xatace da kare maye ke bakiga mummunan tabon jikinki ba na kafurci cikin kuluwa sulthana tacewa hindu dallancen Yar safarar koken Yar fashi da makami duk kinfimu mummunan tabo makisiya kawai ya isa sulthana jenny ta kwatsa mata tsawa mufa ba Sa anninki bane tsaki tayi shekara daya da wata biyar har wani girman arxikine ? Xaki bude baki yayyyyayaya ke babba ta kuma yin tsaki jenny ta rike kirjinta na tsaneku wllh sulthana tace nafiki jin tsanarku hindu tace inajin kamar na kasheku na huta inna kalleku wani bakin ciki nakeji na musamman nima haka sulthana ta fada jenny tace ina jin kirjina kamar ya tsage sbd kiyayyrku haisam yace innalillahi wannan wacce masiface ? Ya mike zan tafi gida dare nayi gobe zan dawo mu tattauna wannan gagarumar matsalar ya fice yana jin wani abu aransa

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

      *******      *********

Daren ranar basuyi bacci ba hk suka dinka fada da rigima da doke doke karfe uku na dare suna rigima da kyar yaran hindu suka tsawatar musu da bindiga suna xauna a falo 4 na dare da wani abun kowacce tayi tagumi su kadai suka San me sukeji daya daga cikin yaran hindu yace madan a matsalarku fa tana bukatar masani da sauri ta kalleshi boy one wanne irin masani ? Akwai wani malami dana Sani in xaku yadda gobe tun da safe muje dan gaskiya wannan lamari naku yana bukatar irinsu da sauri kowacce ta amince dan abin ya ishesu sosai

    ****************

Tun da safe suka tafi ko breakfast basu yiwa ba abinda ya basu mmk mutumin yana cikin tsakiyar dukar daji suna xuwa boy one xaiyi jawabin abinda ya kawosu ya dakatar dashi cikin jimami yace al’amarinsu yafi karfina gaba dayansu suka raxana abinda zan iya fada akanku shine zargin da kukewa iyayenku ha haka bane kun fito cikin wata xuri’a me dunbin tarihi da kuma wata gagarumar baiwa yanxu haka suna cike da sonku da nemanku al’amarinku abune me matukar hadari kunyi kuskure wajan haduwarku waje 1 tabbas da kuncigaba da xama xaku iya kashe junanku sbd karfin sihirin dake tare daku bayan an rabaku da iyayenku ba a barku ba sai da aka biku da wannan asirin me matukar wahalar karyuwa bazan iya karya wannan asirin ba sbd akwai amana atsaka nina da bokan da yai wannan aiki abu daya zan muku shine na baku maganin da xai rage muku kiyayyr juna da jin haushin kanku da kukeyi wani kullun magani ya Ciro ya watsa acikin garwashin wutar da ke gabansu nan da nan hayaki ya turnike

wajan suna shaka suka fara tari da atishawa me karfin gaske ya miko musu wani ruwa yace su xuba a kofar gidansu inda suke xaune sannan suka tashi jikinsu duka asanyaye a hanya ma sai da aukayi fadan amma bai kai xafin na jiya ba suna xuwa suka xuba maganin a kofar gida wani hayaki ya tashi me ban mmk suka shiga gida suna mmkin abun a falo suka tadda haisam yana xaman jiransu da sauri sulthana tai wajanshi sannu da xuwa ya haisam ta fada tana juya ido da kyar ya amsa da yawwa wani abin mmk ne ya faru wajan wani boka mukaje sai alokacn ya kalleta da mmk boka ? Ya maimaita ta kwashe lbr ta fada masa ya mike tsaye meye hakan ? Ku mata meya ke damunku ne meyasa in kuka shiga masifa xuciyarku take bushewa kun manta Allah mai ikone akan komai ? Baxaiyiyu ba kai boy one kaje ka wanke inda kuka xuba maganin nan oga sorry ammafa wajan ya bushe dan hayaki ne ya tsahi kamar ba a xuba komai ba oh ya rabbi ! Ya dafe kai wllh sai kun tubarwa Allah wannan bai dace ba ya sabawa shari’ah sulthana ce tamarairaice kayi hkr ya haisam tsaki yayi bai kalli inda takeba kuje ku fara istigfari ya fice ranshi abace Jennifer ta mike jikinta asanyaye nima kunga tafiyata wani kallo sulthana tai mata xuwa ina tai tsaki inda kika aikeni tai ciki ta dauko akwatinta ta fice daga gidan ko sallama batai musu ba

**********     **********

Ta sauka dai dai kofar gidan tafiya mai adaidaita kudinshi a xaune ta ganshi kan bencin gate man tunda tashi go yake mata wani irin kallo hannunshi rike da ruwan cway yana sha tadan durkusa aladabce tace barka da hutawa ya khaleel baice komai ba sai tabe baki da yayi murmushi tayi aranta hade da mugun jin dadin ta lumshe idonta tana jan akwatinta nayi missin dinka mr coffee ganinka Dana yi yanxu yasa naji farin ciki sosai suwaiba ce ta rugo da gudu suka rungume juna barka da xuwa Jennifer munyi kewarki har daki takai mata Jakarta ina yan gidan ta tamby suwaiba Yar gidan yayan Momy ce ta haihu sukaje ganin baby yaushe ta haihu ? Daxu suna cikin hira taji karan wayanta dariya tayi hade da nunawa suwaiba screen din wayar suwaiba ta xaro ido muryarshi asanyaye yace mata ki. Kawomin coffee yanxun nan ta kashe sukayi dariya sannan ta mike suka jeru xuwa kitchen suna hira daga dawowata da coffee zan fara da gaggawa ta hada masa ta kai masa yana danne dannen wayarshi ta sunkuya ta ajjiye xata fita yace xonan ta saki numfashi taxauna ina kikje ? Kuma da ixininwa ? Edo naje da ixnin mamana OK tashi kije ta mike kinga ! Yqce mata kina da abinda xakice ? Eh ta amsa masa dago kai yayi yana murmushi ina jinki muryarta na rawa tace inaso zan musulunta wullar da wayr hannunshi yayi da sauri ya karaso kusa da ita xaki musulunta kai ta daga masa yayi dariya ta jin dadi ya ruko hannunta duka biyu hade da runtse ido kana gani kasan najin dadi turo kofar akayi Jidda ce ganinsu a haka datayi yasanya ta kwalla ehu  hakanne ya janyo hnklim su Momy da suka dawo tare da sauri sukai wajan abinda suka gani ya basu mmk khaleel rike da hannun Jennifer fuskarshi cike da walwala Jennifer taja hannunta tana kokarin kufcewa ya finciko hannun sbd mutuwar da jikinta yayi yasa ta fada jikinshi gaba dayansu suka xaro ido cike da mmk Jidda ta rushe da kukan bakin ciki.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]