[Advertisements⬇️]

JENNIFA CHAPTER 21 - Bankinhausanovels
Thu. Oct 6th, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

JENNIFA CHAPTER 21

 

 

 

Wani irin kallo yai mata me kike son cemin kwantar da kai tayi nafada mk bani bace Jennifer wacece ita ?? Yayi shiru hade da kallonta inajinki yafada yana gyra xama

Sunana hindatu ban San kaina ba ban kuma San wacece ni ba nataso a hannun marikina gawurtaccen dan fashi dan damfara dan safarar kayan maye yanxu haka yana hannun hukuma atsare kafin aka mashi yasha fadamin ba shi ya haifeni ba duk lokacin Dana girma xai bani wani lbr me ban mmk akaina kwatsam ranar damukaje fashi a shopping mall na ganka har ka kirani da wani suna daya ban mmk dalilin dayasa na hana akashe ka dan abinda na da de ina nema kenan in San kaina shiyasa naita bin diddiginka har na gano inda kake

Shiru yayi yana kallonta dan shi Sam  bai yadda ba ita bace bace wayar shi ya ciro ya kira mahboob bata dade tana ring ba ya daga yace dan Allah mahboob hadani da Jennifer zan sata wani aiki gata ma muna tare a kitchen ya mika mata waya atsorace ta amsa ya rasa mai zaice da yaji muryarta tabbas itace ya kalli hindatu datake gabanshi ya kuma saurari muryar Jennifer da kyar ya saita kanshi yace ta dafa masa indomie yana nan tafe ya kashe wayar ya kalli Hindu tai murmushi kadan yasaki numfashi ikon Allah Allah mai halitta kin San wani abu ? Kai ta girgixa dai dai da maganar Ku iri dayace ba banbanci yanxu ya kikeso ayi ? Ina so duk yadda xa ai yanxu ka kirata taxo nan office dinka muga juna kamata yayi kitashi muje gidanmu kai ta girgixa masa koda zanje gidanku to ba yanxu ba kai tsaye numb din Jennifer ya kira ta daga atsorace yace taxo xata rakashi kasuwa akai kayan matan da yake son siya amma a office xata sameshi yanxu yanxu danjuma ya kawota ganin cewa a gaggauce yace yaxo yasa ta fito da sauri ta fada wa danjuma ya dauketa suka taho

     ******        *******

Basa bata lokaci ba suka iso yace danjuma ya juya ita kuma ya shigo da ita a tsorace take dan gani take kamar wata muguntar ya shirya mata ta ga mace axaune amma bata ga fuskar ta ba sai da taje gab da ita ta saci kallonta karaf suka hada ido a kidime suka mike lokaci daya suka mike hade da kurawa junansu ido Jennifer ta nuna ta da yatsa wacece ke ? Hawaye ya xubowa Hindu tace wa haisam kayi namijin kokari Dole ka kasa tantanceni da wannan halittar Alhamdllh lallai wahalata taxi karshe ki karemin kallo ni Yar uwarki ce rungumeta tayi ita dai Jennifer mmk da ta ujjubi ya hanata mgn ta xauna jikinta na karkarwa Hindu tace dole ki kasa mgn tashi muje ki nuna min iyayenmu abakinsu xamuji komai haisam ya mike gsky kam.dan al’amarin naku akwi son jin dalili gaba dayansu suka mike itakam Jennifer binsu kawai take har suka shiga mota dake haisam yasan hanya kai tsaye ya hau titi Hindu ta kalli Jennifer kinki mgn ta kawo wani gwauron numfashi sannan tace mmk ne ya kamani ban taba tunanin haka ba sai ga shi na ganki wllh babu wani abu daya banbantani dake axahiri sai dai ko abadini nayi mmkin wannan ikon Allah ni kaina banyi tunanin tsananin kamarmu dake takai haka ba dai dai da murya fa ko ba’a fada ba ai ansan mu yan uwan juna ne haisam ya tsaya dai dai kofar gidansu Jennifer kai tsaye cikin gidan suka shige a daki suka tadda Maman David ita da papa da David da yake kwance akan cinyarta da gudu Jennifer ta karasa hade da fadawa jikin Maman David da oyoyo my jenny su haisam suka karaso shida Hindu araxane Maman David take kallon Hindu murmushi tayi hindun ta shigo Jennifer ya nunawa mama Hindu mama dama mu biyu kika Haifa ? Ya akayi baki taba fadamin ba fata rai tayi ke kadai na Haifa wannan ban Santa ba sam papane ya kalli Hindu da mmk yace wannan wanne irin kama ne ? Mikewa mama tayi me kuka xo yi ?, tacewa haisam kuna son sawa yata wani irin tunanine ? Dama sam hnklina bai kwanta da yin aiki a gidanku ba Ku tashi Ku fita ni yata ita kadai na Haifa bansanki ba ke ta nuna Hindu hawaye ya saukowa Hindu ko baki fada ba ni nasan ba ke bace uwarmu hannu tasa cikin riga ta xaro karamar bindiga ta nuna kan David ko ki fadamin gsky kona kashe ramammen dan nan naki kuka mama tasa plx karki harbeshi haisam ya mike Hindu kibi ahnkl kada ki harbeshi idan har bata fadi gsky ba kashe shi zanyi inkashe wancen mijin nata me kwala kwalan ido jin an ambaci papa yasa yace ko baki harbemu ba dole gsky tai halinta kuka Jennifer tasa kina da hnkl dan sunce ba iyayenki bane shine xaki kashesu ? Yimin shiru ! Hindu ta kwatsa mata tsawa ba iyayenki bane papa ya mike ina zaka hindu ta fada tana Nunashi da pistol din hannunta ya daga hannu sama zan dauko muku wata shedane yana ina ? Ta tmby shi yanuna wani tsohon akwatunshi haisam ya tashi da Kansa ya dauko papa ya bude jikinshi na rawa ganin anbude akwatin yasa mama rushewa da kuka wata leda ya dauko acikin akwatin ya xaxxageta kayan jarirai na sanyi da wani karamin dankunne da awrwaro na gwal suka fado sai envelope ya ciro wani karamin pix tabbas Jennifer Yar uwarki ce dan gashi nan a pix din da muka tsince ta ya mika mata pix din ta kalla hawaye ya sauko mata duk wayan nan kayan ina da irinsu ya akayi ka tsince ta ??,

Yana rubuce ranar talata a shekara ta 1995 watan July anan garin KANO a unguwar janbulo da safe muka tadda an ajjiye ta agefen bola dai dai kofar gidanmu nacen jikinta dauke da wannan kayan kunnanta da wqnnan barimar hannunta sanye da wannna awarwaron sai wanna envelope din aciki ansaka wannan pix din da kuma takaddanta na haihuwa wannan ranar ta nuna watan ta daya da kwana goma cif rushewa da kuka sukayi dukansu hindu da Jennifer ita hindu tana kukan bakin cikin wannan ramari cikin kuka tace rana daya aka wullar damu hannu tasa a aljihu ta ciro barima irin ta Jennifer da awarwaron sak iri daya sauran kayan suna cikin mota itakam Jennifer kukan tarasa gane kanshi babban bakin cikinta bata San wace rayuwa xata faraba da mmk papa yace kina nufin kema wullar da ke akayi ? Kai ta daga masa tabbas ina so kubani yar uwa ta muje mu binciki asalin iyayenmu papa mungode da taimako Jennifer ta tsaya da kukan ngd iyayena har gobe Ku iyayene kuna raina amma kuyi hkrin rashina na wani lokaci lokaci daya naji ina son ganin aslin iyayena dole zanbita baxan iya xama da wannna daukin ba takarsa da kuka mama kukan takeyi nabaki goyon baya jenny Allah yabaku Sa ‘a hindu ta mike haisam ya mike xuciyarshi cike da tausayinsu Jennifer fa ma mikewa tayi tana kuka mama xan dawo nan da kwana 2 tafice da sauri tana kuka suka shiga mota gaba dayansu

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

       ******      *******

Haisam ya ce ina xamu hawaye na sauka a idon hindu tace gidana dayake cikin hotoro g.r.a ya ce ita kuma Jennifer fa ? Shine ban San ya xamuyi ba muje cen din ma yanke shawarar yadda xa ai basu bata lokaci ba suka iso kai tsaye falo suka xauna dukkansu jikinsu asnyaye Jennifer tace ta ina xamu fara Neman iyayenmu haisam yace wai Hindu wacece wannan matar dana ganki da ita a saudiyya? Tai masa wani irin kallo saudiyya ??ta maimaita yes ya fada yana kallonta ko bake bace sulthaana ? Araxane ta mike cike da jin dadi bani bace Alhamdulillah bani bace shikenan wahalar mu ta yanke iyenmu nacen duk yadda akayi matar nan itace mahaifiyar mu ikon Allah haisam ya fada tabbas kuwa dan akwai sulthana ban da yanxu kince min ba ke bace baxan taba yadda ba dan yanda kuke tsananin kama da Jennifer haka take da Ku itama Jennifer dadi taji ya kamata yanxu ya xa ayi muje saudiyyan ni in kun yadda ma gobe muje kai haisam ya girgixa mata baxaiyiyu gobe ba nan da 1 week dai haisam plx hindu ta fada xuciyata tana cike da kwadayin son ganin iyayena ki kwantar da hnklinki dolene sai munyiwa Jennifer biza cikin satin nan dai ajiyar xuciya Jennifer tayi haisam ya kalleta yanxu wqcce shawara kuka yanke ?? Tame ? Suka tmby shi Jennifer mana  anan zan barki a a ya haisam tare xamu koma gida dan bana son kowa yasan wannan zancen har sai mungama iyayenmu plx ka rufa min asiri murmushi yayi bakomai gobe gobe zansa a fara miki shirye shiryen tafiya ya mike yana kallon Hindu kefa kutafi Ku barni anan dan bani da wata matsala suka wuce a cikin mota Jennifer ta dake ya haisam ina son tmbyrka ? Wai shin ya akayi haka ta faru ya kwashe komai ya fada mata ta fashe da kuka yana rarrashinta har suka so gida

   *******************

Suna shiga sukaci karo dashi yana kokarin shiga mota yai mmkin ganinsu tare nan da nan fuskrashi ta canxa  gabanta ya fadi asanyaye ta fito daga mota yana harararta cikin gida ta shige tana jin tsoron abinda xai biyo baya awahalce ta xauna agefen gado hade da dafa kanta daya ke juyawa anya ma kuwa itace ? Jin kanta take kamar ba itaba wai mama da papa ba su suka haifeta ba jin abin take kamar amafarki ta fito daga daki xata gyara falon kasa a xaxxune tagansu dukansu dake har yanxu gidan acike yake da bakin da basu tafiba yawwa ummana taji muryar Jidda kinga mahukaciyar yarinyar da muke mgnr ta daxu ta nuna Jennifer gaba dayansu suka xuba mata ido wacce aka kira mama tace aw wannan ce ? Ai nazaji Yar wani kusa ce agarin nan yanda naga tana daukan knta jiya tana lika daloli ashe Yar su ujuku ce Yar gidan Malan shehu ke ! Jaraba kike kowa ? Gaba daya falon suka Sa dariya banda Momy da ruby zahra tace Jennifer OK koma wa kike xonan atsorace ta je kusa da ita hannu tasa da damki kunnanta meye matsayinki a wannan gidan tana xubda hawaye tace Yar aiki kinga wannan ta nuna zahra da Jidda daki taba minsu kwara ki tabani aknsu babu abinda baxan iyaba bani da Kyau in aka shiga gonta tun jiya aka kawomin kararki babu ke ba Ibrahim bare kuma Prince A.k Garkuwa sbd ba sa’anninki bane sun girmi ajikinki banda ma jaraba irinta namiji mai xaiyi da kaxanta? Dan Allah tashi tasakar mata kunne maxa akawomin hypo da kleen na wanke hannuna na taba kaznta fice kiba mutane waje sum sum ta wuce tana xubar da kwalla daki tana shiga daki ta fada gado hade da rushewa da kuka karar wayarta taji ta daga ba tare da ta duba suna ba muryar Momy taji kiyi hkr Jennifer bani da yadda zanyi sbd ianwar dadynsu zahra ceki kwantar da hnklinki komai zai wuce ba komai Momy ngd ta rarrsheta sosai sannan ta kashe waya

Da gamma tana xaune a daki ya shigo kamar ko yaushe fuskarshi ba walwala ya tsaya atsaye ina kikaje keda haisam ? Tayi shiru dan batai tsammanin tmbyr ba ke ! Bakayaji jine ? Cikin in ina a a a am mun munje kasuwa ne daga yau na hana ya fada cikin fada yai shiru sannan yace asanyaye kada na kara ganin kin fita da kowa kuma bana son nasake ganinki da mahboob ban yadda dakawacen Ku ba sannan daga yau karna kara ganinki da karamin gyale kina jina ?,kai ta daga masa kiyi mgn ina ji kuma zan kiyaye yayi Kyau yace sannan ya fice hawaye ya balle mata tana ganin abu iri iri

“**********************

Cikin sati daya haisam ya gama musu komai na tafiya taiwa Momy karyar xataje Edo state suka taho saudiyya

      Saudiyya

Da yamma suka sauka Jennifer haushin hindu kawai takeji sbd tasa antaho da yaranta maza su biyu Mara Sa kyan gani ga gefe guda na xuciyar ta haushin hindun takeji batasan dalili ba haisam yai musu jagora dan suwa masaukinsu a hanya danja ta tsayadda su yana waiwayo fuskarsa yaganta acikin mota tana waya fuskarta cike da nishadi Hamdala dayayi da Saudi suka tmbyeshi yace ga wacce muke nema nan agabanmu baxasu iya ganinta ba dole suka hakura haisam yace drivensu yabi bayar mortar da ake janta basu Dade ba suka so wani tamfatse tsan gida mai gadi ya bude ta shiga suma suka bita ta fito daga mota tana yiwa motarsu kallon raini fitowa sukayi suna mmkin kamarsu da juna tana ganinsu ta kura musu ido ta kare musu kallo irin kallon sama da kasa sannan ta ya mutsa fuska suwaye Ku ta tambayesu araine ?

Dai dai lokacin da wata babbar mace ta karaso tana fadin oyoyo sulthana ganinsu yasa tai turus ta bata rai suwaye Ku a dake hindu tace mu yan uwan sulthana ne dan ko ba a fada ba ido ya tantance kuje kunemi inda yan uwan Ku suke yata itaka dai na Haifa tsaki hindu tayi nga alamar xaki raina mana hnkl mu kuma baxa mu jure ba xaro bindiga tayi ta nuna matar da ita ko ki fada mana gsky ko na daukeki da wannan  sulthana ce ta shagaban matar dalla gafara malama ance ba sanku ba dolene ?,daga ka wai munyi kama ? Sai dai Ku harbeni tsawa hindu tai mata tsab zan harbeki dan naga baki da kunya fitsararriya matsa sulthana kada su cutar min dake cikin kuka matar take mgn tabbas sulthana ba yata bace tsintar ta nayi tafashe da kuka 39/40

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]