[Advertisements⬇️]

JENNIFA CHAPTER 20 - Bankinhausanovels
Thu. Oct 6th, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

JENNIFA CHAPTER 20

 

 

 

Yai mmk sosai ya kurawa wayan ido me yaka mata yayi shin xaibar bikin gidansu yaje ?? Ajiyar xuciya yayi jikinsa ya mutu kiran wayan ya kuma yi ga mmkinsa sai yaji switch off ranshi ya baci akira ace ana son ganinka sannna akashe waya ?? Yai tsaki shifa baxai kara karanbanin binckar wacece itaba har sai lokacin datagaji ta aiwatar da mummunan kudirinta da sauri ya koma cikin gida hannun shi rike da damin rafofi na liki

        *****          *****

Liki sosai A.k yake mata guri ya cika da mutane kowa na liki anata xuba kudade a hankali ta xame daga cikin filin rawar ta nufi cikin gida kai tsaye dakinta ta nufa tarushi GAM sannna ta xauna ta rushe da kuka kuka sosai take xuciyarta akuntace meyasa ya khaleel yake mata haka ?? Meyasa rayuwar ta take cikin rashin sa’a ?? Meyasa komai yake xuwan mata adabarbarce ? Kuka tasaka Wanda take matukar so yau ake Sa ranarsa da wata shikenan tayi asarar first love dinta ?? Meyasa shi baya sonta ?? Ta yi shiru ta tunani xuciyar ta ta tuna mata baya sonki xaiyi kissing dinki ?? Murmushin jin dadi ya kufce mata daxu daxu ya shanye miki lip tas hannu tasa tashafa lip dinta ta lumshe ido ta tuno lokacin daya ke kissing dinta tsikar jikinta ta tashi ta ajjiye ajiyar xuciya idonta ya kai kan wayar ta baya sonki xai sai miki waya iri daya da ta budurwarsa ?? Dariya me hade da kuka tayi ta janyo wayar hade da rungumeta akirjinta ta kunna wayan ta bude images din da tai musu ta tsaya kan Wanda sukayi ita da ita yayi masifar Kyau ferpect mach ta fada tana murmushi ina sonka Mr coffee kai kadace da tsarina da kai kawai xan iya rayuwar aure haka taita sambatu xuciyarta kamar madaci kidan data keji ya fara damunta haushi ya cikata sai yamma likis dan har anfara kiran sallah sanna taji hayaniya ta tsaya kidan ma antsaya taji dadi kwankwasa kofa akayi ta tashi ta bude gabanta ya fadi ba walwala afuskarsa ya shigo hade da rufe kofar yana kallonta dagani kasan na tuhuma ne ke bakyajin mgn ko ?? Me nace miki ?? Bana ce ban yadda ki koma ba ?? Shiru tayi kanta akasa tarasa amsar bashi zan dau babban mataki akanki me prince A.k garkuwa yace miki muryarta na rawa tace cewa yayi yana sona runtse ido yayi cikin jin haushi da jimami ke kuma me kikace masa ban bashi amsa ba dariyar me naga kunayi dashi tai shiru bakiji bane ! Am a a ban wllh Mr coffee bakomai what ? Mr me ? Da sauri tasa hannu ta rufe bakinta Sam batasan da sunan da takirashi ba murmushi yayi ganin ta tsorata ki fada masa kina da miji bana son na kuma ganinki da shi adake tace miji ? Nifa ya khaleel ba aimin miji ba matsowa yayi kusa da ita yasa hannu ya dago mata da fuska look dago kai ki kalleni ta dago kai atsorace ni nai miki miji bana son ki kula kowa ta sunkuyar da fuskarta ya dago da fuskar meyasa kike son wahalar da kanki ? Ta kalleshi shima kallonta yake suka kurawa junansu ido batare da sun fargaba muryarshi taji asanyaye Jennifer ya kira sunanta jikinta amace ta amsa da kyar hade da sauke fuskarta dago ta ya kuma yi ya matso gab da ita sunajin iskar numfashin su kin fisan kiyita wahalar da kanki ?? Meyasa baxaki ba xuciyarki abinda take soba ya fada yana kurawa lip dinta ido babu komai axuciyata karya kike akwai kinfison ki barshi aranki sai dai kishigo daki kita rusa kuka da sauri ta kalleshi ki fada plx yafada cikin wani yanayi idonshi akan lebenta ahankali ta xame tai katsa ya bita da kallo dan jikinsa yai matukar sanyi ya juya xai fita tabi kyakyakyawan bayansa da kallo ki tabbata kin fada mishi abinda nace sannan kada ki kuskura ki bashi numb dinki ya fice daga dakin hawaye ya sauko mata tarasa gane inda yasa gaba  ta mike da kyar ta shiga toilet dan tayi wanka

        ******          ******

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Tana fitowa daga wankan ta Sa doguwar rigar less ta shafa mai hade da yin kwalliya sosai duk tasan dare yayi ba kuma inda xata tana cikin shafa janbaki maroon ruby tashigo kina nan anacen anata nemanki ta xaro ido kadan waye yake nemana ?? A.k Garkuwa kin rikitamin bro fa kiyi sauri tai shiru sbd karar kiran wayar ta murmushi tayi special bro gata nan dariya to shikenan kafata kafarta xan kawo maka ita yanxun nan ta katse wayar kinga yadda ya daga min hnkl shi Jennifer Jennifer taso muje gaban Jennifer ya fadi da ta tuno gargadin mr coffee sannan tana matukar jin kunyar ruby baxata iya musu da itaba jikinta sanyaye ta mike tabi bayanta ruko mata hannu tayi sukai bangaren ya khaleel kai tsaye dakin suka shiga ita kam a tsorace ta shiga dakin xaune ta ganshi da farar singlet da yana ganinsu yasaki murmushi special sis ngd sosai dariya tayi nacika alkawari ta juya asha hira lfy ta fice ya harari Jennifer shine kika gudu kika barni ko ?? Kai dan rainin hnkl gata nan dakace baka sonta ba da sauri ta kalleshi dan batasan yana dakinba yana kwance kan 3 siter yana sanye cikin farar sheet da 3 quarter yana danne dannen wayrashi cikin hada rai yace meye haka Prince ? A gaban yarinya kake irin wannan zancen dariya yayi sorry manya Jennifer ya kira sunanta ta amsa ina son naji amsata ta saci kallon ya khaleel idonshi a kanta ya galla mata harara karar shigowar test taji ta duba ya khaleel ne … Ki fada masa kina da miji kin amince min xaki aureni ? Da bara ta fado mata tace ina so kabani lokaci zanyi shawara wani kallo ya khaleel yai mata wane irin tunani malama ki bashi amsa yanxu khaleel plx kabita asannu a tsorace tace kayi hkr ammin miji ta kalli ya khaleel yai mata jinjina da hannu ta saki numfashi wannan ba damuwa bane Jennifer tunda ba ki aure ba zan cigaba da Neman aurenki har sai kinyi aure zan hkr Suka  kalli juna tai murmushi hade da cije lebenta na katsa wato ta rama abinda yake mata kwafa yayi ya mike ya shiga bed room dinshi yana barin wajan taji zaman ya gundireta ta mike wayar ta tafi A.k yasa hannu ya dauka yai dialing numb dinshi kiran ta shigo yaga numb din sannan ya mika mata wayar sukai sallama ta fice daga dakin jagwab ta fada kan gado tana tuna abinda ya faru tsakanin su banko kofa taji anyi gabanta yai mummunan faduwa ganin su zahra cikin tsawa zahra tace ubanwa ye yace kiyiwa Prince A.k mgn ke wacce irin mayyace ? Anty Jidda anya kuwa banza take barin maza shegiya duk inda taje sai ance ana sonta ? Ina fa banza agumi take musu irin Nasu na mugayen yare to wllh ahir dinki Jidda tace kina kallofa da kyar na rabata da ya khaleel irin bakin cikin dana kunsa akan wannan kafurar wai ma waya gayyace ki taronmu ?? Kin wani Sa banxan karamin  material dinki kina rausaya wai ke mai Kyau fadamin suwaye munana ?? Zahra tace warning na karshe dan ubanki ki fita har kar A.k dan yafi karfinki kije kisami dan jagaliya dangin ojuku ki aura ba ki dinka hange hangen wayanda suka fi karfinki ba shasha sha ! Anty Jidda yarinyar nan sai mun mata Jan wuya na fuskanci Yar rainin hnkl ce cikakkiyar Yar iskaba xamuyi maganinki kin kusa barin gidan nan akoma cen acigaba da sai da garau garau sukai mata tass sannan suka fice ta share hawayen fuskarta da ya xubo tai tsaki ke kika damu da wani Prince A.k garkuwa

Basu dade da fita ba ya shigo awahalce ta kalli kofar yau kam taga ta kanta ya tsaya atsaya hannunshi cikin aljihu baxaki huta ba har sai kin fadi abinda ke cikin xuciyarki kada ki kuskura wata alaka ta hadaki dashi kiyi maza ke yanketa ki fada mishi kice mijinki baya bukatar ganinki da kowa ko dole ne yaja dan karamin tsaki ke ! Ta turo baki nifa ba sunana ke ba yai shiru yana kallonta ni kuma dashi nai niyyar kiranki mai yasa baxaki fadi maganar Da barinta xai iya janyo miki ciwo shikenan tunda kin xabi ki barta tai ta wahalar dake ya fice tabi kyakykyawan bayanshi da kallo tana mmkin maganganunsa a hnkl ta furta ina sonka mr coffee amma baxaka tafajin Kalmar nan abakina ba koda kuwa xata xame min illa araina kuka ya kufce mata ranar kam batai barci ba tunane tunane ta kwana yi

    *****           *****

Washe gari ya haisam ya wuce office ya dauko wasu muhimman takaddu da ya manta su acen yana shiga ya gansu su uku biyu maza ita kadai mace ya kallesu ta waiwayo tana xabga masa shu’umin murmushi kana mmk ? Ta fada tana kallonsa meye abin mmk dan na ganki anan bayan nasan xaki iya aikat fiye da haka me ya kawo ki office dina ? Ko kin gama aiwatar da aikin daya kawoki gidanmu ? Wai shin Jennifer ke wacece ? Murmushin ta Kuma  yi nima shina ke so nasani ya wurga mata kallo wannan kuma ke kika sani dan bazan yadda da salon rainin hnklinki ba plx haisam ta katseshi wacece Jennifer ? Mikewa yayi yana kallonta dan gani yake ta gama raina masa hnkl wacece ke ? Ni kike tambaya matsayinki ? Ni bani bace Jennifer ta kalli mazan nan biyu Mara Sa Kyan gani suka fita so nake nasan wacece ita sunana hindatu …..

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]