[Advertisements⬇️]

FULANIN TASHI CHAPTER 4 - Bankinhausanovels
Thu. Oct 6th, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

FULANIN TASHI CHAPTER 4

 

shiri sosai su kayi na zuwa taro Ammar wanda saura kaɗan jirginsu ya isa Abuja, babbar mota suka hau gaba ɗayansu, Abu a gaban mota Ammi da Ummi da Amra a bayan mota.

sun isa airport lafiya suka samu gefe suka faka kafin jirginsu Ammar ya iso, sunanan zaune har lokacin ƙarfe goma da rabi, wanda shi dai-dai lokacin da jirgin zai sauka, fitowa gaba ɗaya su kayi saboda sanarwar da suka ji, babu jimawa mutane suka, cincirundun mutane ne sosai wanda seda su Ammi suka ji taoro kamar wani abun ya faru, kowwa ka gani a wajen fuskarshi ƙunshi da fara’a wasu sunzo taron ƴan uwansu wasu abokai,mutane ne suka fara fitowa daga cikin jirgin kowwane kowwane cike da aji, daga ganinsu ka ga yaran manyan mutane ƙusoshi a gomati, Amra ce ta kalli Ammi sannan tace.

“Ammi wai na ga har yanzu banga Ya Ammar ya fito bane”,

murmushi Ammi tayi wanda ya ƙarama fuskarta kyau sosai, zungurar Amra tayi tace.

“ok ɗaga idonki ki gani”, atare ni da Amra muka ɗaga ido, kafin inyi wata-wata Amra ta zabura da sauri ta nufi Ammar dake saukowa kamar ansa shi dole,

Sanye yake da farin yadi mai laushin gaske, daga ciki kana iya hango farar vest ɗinshi,fuskarshi sanye da wani farin glass mai kyau da sheƙi, sajen fuskarshi ya kwanta ya yi luf dashi farine mai faɗin ƙirji beda wani tsawo can amma Allah ya hore masa kyau dai-dai gwargwado, *AMMAR TANIM BATURE* kenan.

Gaba ɗaya ƴam matan dake wajen suka juya suna kallon wannan tsadaddan yaron mai ji da aji da wayewa, sosai ya tafi da mutane musanman ƴam matan dake wajen rabida kwatansu sun juya suna kallonshi.
Shi ko Ammar ganin ahalinshi yasa ya dinga murmushi yayin saukowa jirgin, hakan da ya yi ba ƙaramin ƙara masa kyau ya yi ba, wurga ido Ammar ya keyi yana tunanin ta ina zai ga Ni’imatullah ta ina zata ɓullo, ganin bai da amsar tambayar ne yasa ya kawar da tunanin aranshi.

Yana ƙarashe saukowa da gudu Amra ta isa gareshi ta rungumeshi sosai tana dariya, shima dariyar ya keyi sosai yana faɗin “Auta wai nikam yaushe zaki dena wannan rawar kan naki”, kumburar fuska Amra tayi tace shikenan broda ka dawo ba muda saƙat to sai randa na girma, ta faɗa tana jan hannunshi saboda ta kula da ƴam matan da suka shagala suna kallonshi wasu harda ɗaukarsu hoto.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Suna ƙarasowa wajensu Ammi, ya saki hannun Amra ya rumgume Ammi da Abu, sai Ummi da ya kalla ya keta zuba murmushi, cike da ɗoki da son kasancewa da ita saboda ita ce ta reneshi ya saki Ammi yaje ya rumgume Ummi haɗi da sakin wata nannauyar ajiyar zuciya,
ɗagoshi Ummi tayi haɗi da kallon fuskarshi, wani kalan fari ta ga ya ƙara mata kyau, ajiyar zuciya itama Ummi ta sauke sannan ta ƙara juya dashi ta gabanta yadda zasu fuskanci juna da kyau, “Son!” Ummi ta kira sunanshi kamar za tayi kuka.
Girgiza mata kai ya yi alamar tayi shiru kana ya amsa da “Na’am Ummi”, yana murmushi, Ummi ta buɗe baki zata ƙara magana Ammi ta dakatar da ita ta hanyar faɗin “Ummi ku shiga mota mu tafi wannan maganar taku bazata ƙare ba idan har kuka fara ta”. kyakyawan murmushi ne ya bayyana a fuskar Ummi ba tace komi ba taja hannun Ammar zuwa wajensu Daddy, hannayenshi Daddy ya kama ya rausayar da kai yana faɗin “A lalle ka manta dani wato Ummi ka sani kawai kenan?” da sauri Ammar ya haɗa hannyenshi dukka biyu yana faɗin “Tuba nike ranka shi daɗe”, sosai Ammar ya bama su Daddy dariya, wato sunan da yake kiran Daddy dashi kenam kasancewarshi Soja, da yake Ammar hannun Daddy ya tashi kuma a barrack sau da dama yana jin matan sojoji dasu sojojin kansu suna kiransa da ranka shi daɗe, shiyasa shima yake kiranshi da ranka shi daɗe.

Daddy ne yaja kunnen Ammar yana faɗin “An yafe maka ranka shi daɗe”, nan ma dariya su kayi gaba ɗaya Ammar ya ƙara cewa “ranka shi daɗe Daddyn ranka shi daɗe”, dukkansu suka ƙara yin dariya cike da farin ciki suka ɗunguma zuwa mota.

Daddy be ke tuƙa motar sai Abu a gaba, Ammi, Amra, Ammar da Ummi a gidan baya, Ammar ya bi ya takwaikwaye Ummi kamar yaron goye yana ta zuba mata shagwaɓa ita ma tana biyeshi.
Sun ɗanyi nisa da tafiya Ammar ya kai bakinshi setin Ummi ya mata raɗa “Hajiya Ummi wai ina sukrukar taki”, rankwashi Ummi ta gina masa wanda seda ya dasa ƙara sannan tace “wai Ammar yaushe za kayi kunya ne? to tace za ta fita ne ba zata samu zuwa ba”.

“Uhm”, shine abinda Ammar ya faɗa cike da mamaki.

suna tafiya suna fira cike da so da ƙaunar junansu suka isa gida, bayan sun huta Ammar ya yi wanka ya sauko ƙasa nan suka wuce dining cin abinci, anan ma ɗin seda suka daɗe suna hira sannan Ammar ya miƙe ya shige ɗakinshi, mamakine fal aranshi yana tunanin ina Ni’imatullaah ta shiga ne be gantaba, bayan yadawo da ɗaukin ganinta.

Ɓangaren Samha kuwa abin ba’a cewa komi dan ciwo ya cita sosai yanzu kuwa har bata iya miƙewa, amai sosai tayi tare da gudawa tayi dama-dama da jikinta bata ma san inda kanta yake ba, komi ya kwance mata kwance take warwas a ƙasa kamar wata gawa, duk wanda ya ga halin da Samha take ciki a wannan lokacin dole ya tausaya mata.

Mallam liman ya fito daga masallaci bayan an idar da Sallar Azahar, waiwagawa ya yi bega Ammar ba, cike da mamaki ya tambayi Sanda ina Ammar yake lafiya kuwa yau be ganshi ba kwata-kwata.
Amsar da Sanda ya baima Mallam Liman ce tayi matuƙar bashi mamaki, hanyar gidan Baffa ya nufa yana tafiya na saƙe-saƙe aranshi, da kuma mamakin yaushe Ammar ɗin ya tafi be sanar masa ba, sannan ina Samha take, sune suka haɗu suka masa katutu a wuya ahaka har ya isa gidan.
Sallam Mallam Liman ya yi har sau uku babu wanda ya amsa.7/8

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]