[Advertisements⬇️]

FULANIN TASHI CHAPTER 6 - Bankinhausanovels
Tue. Nov 29th, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Jalaluddeen ganin komi yake tamkar a mafarki, amma taya akayi wannan auren kuma ya ya akayi Ammar yazo kano be sanar masa, kenan akwai abinda Ammar ya ɓoye masa shiya ko da yazo be wani saki jiki kamar yadda ya keyi ba, ina ita Ruƙaiyah take, tabbas akwai wani babban lamari da yake tunkarar Ammar, zufa Jalaluddeen ya sharce ya ɗauki takardar ya mata jan ɓoyo dan ya tabbatar da Ammaar ya manta da takardar nan ne amma da bazai barta ba, jiki ba ƙwari haka Jalaluddeen ya dawo falo ya zabga uban tagumi yana tunanin Alƙawaran da Ammar ya ɗauka gefe ɗaya kuma ga Ni’imatullah.

ƙarfe huɗu da kwata Ammar ya farka daga barci, lokacin kuma Ni’imatullah ta dawo, buɗe idon da zeyyi da fuskarta ya fara cin karo ta ƙura masa ido tana masa kallon kurilla.
kamar a mafarki Ammar ya ga Ni’imatullah aikuwa ya zabura ya miƙe tsaye haɗi da kallonta, “Honey”, ya kira sunanta cikin sarƙewar murya,
Lumshe ido Ni’imatullah tayi tace “Na’am my soul”, yadda ta furta my soul shi ya hanama Ammar amsawa dan cikin wani kalan salo mai matuƙar birgewa ta faɗi sunan, Ammar ya buɗe baki zeyyi magana kenan Ni’imatulla ta dakatar dashi da hannayenta ta hanyar faɗin “My Soul kaje kayi sallaah tukum kalli agogi ka gani ƙarfe huɗu da kwata ta faɗa tana wani farrr da ido wanda seda tsogar jikinshi ta tashi, wata kalar gajiyace ta saukar masa har ya kasa iya cewa komi sedai kawai ya miƙe ya shige toilet ɗin Ummi ya ɗauro alwalla ya fito.

da ya fito bega Ni’imatullah ba ya tada sallah amma hankalinshi na gareta gaba ɗaya beda wata nutsuwa, yana idarwa dai-dai lokacin Ni’imatullah ta haɗa masa tray ɗin abinci da ta girka masa na tarba, anan kan sallayar tace ya zauna da yake irin manyan sallayar nan ne, babu musu ya koma ya zauna dan har yana ƙoƙarin tashi.

Zuba abincin tayi a plate, shinkafa ce da miya daga ganinta da ido kasan ta haɗu bama sai ka kaiga baki ba, tsayawa haɗuwarta ɓata lokaci ne, matsowa tayi kusa dashi kamar zata shige jikinshi ta fara bashi a baki yana ci, shima yana bata dukka dai suna ci suna hirar soyayya a haka har ta cika masa ciki dam da abinci wanda rabonsa da yaci kalar abincin harya manta tissue ta ɗauka ta goge masa baki tukum ta jashi zuwa babban falo,
Gaba ɗaya ahalin gidan manya da yara suna zaune suna hira dan biki aka haɗa sosai na tarbar Ammar, zama ya yi cikinsu suka ci gaba da hirarsu cike da so da ƙauna, dukka mutanen gidan kowwa mamakin Ni’imatullah yake saboda rabonta da ta zauna ayi hira da ira har an manta, se gabda sallah magrib suka watse bisa umarnin Alhaji Salihu bature kakansu kenan, maza suka nufi masallaci ya yinda matan suka yi sallarsu a gida.

*GENERAL HOSPITAL GOMBE STATE*

Tunda su Mallam Liman suka shiga cikin asibityn da Samha likitoci suke kanta amma an kasa shawu matsalarta, duk firowar da likita zeyyi sai ya tsaya ya yi ma Mallam da Iya faɗa akan lamarin Samha, yanzu ma fitowarsa ta huɗu kenan, hankie ya ɗauka ya share goshin shi da zufa ke tsatsafowa sannan ya dubi Mallam da Iya dake zaune abin duniya ya haɗu ya musu yawa, da yake ba musulmi bane shiyasa yake musu wulaƙancin da yaga dama “Ke ki biyoni office”, yace da ita Iya yana wurga mata harara ya yi gaba abinshi,
Miƙewa Iya da Mallam su kayi suka bishi a baya har zuwa Office ɗinshi, jan kujera ya yi ya zauna tukum ya nuna musu kujera yana faɗin “seku zauna”, zama Mallam da Iya suka yi ba suce komi ba suka tsaya jiranshi.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

glass ya ɗauko ya sanya a idonshi tukum ya ɗauko wata farar takarda ya yi ƴan rubuce-rubuce sannan ya kallesu yace “Gaskiya maganar da zan faɗa muku kun tafka babban kuskure, taya zaku bar yarinya da ciwo a jikinta har zuwa wannan lokaci baku kawota asibity ba? sannan wani kalan marar imani ne ya daketa har haka,” ya faɗa yana kallon fuskokinsu sannan ya ci gaba da cewa.
“Munyi iya ƙoƙarinmu dan ganin numfashinta ya dai-daita amman mun kasa, maganar da zan faɗa muku itace dole zamu rubuta muku takarda zuwa asibity *MALLAM AMINU KANO* dan su bata kulawa ta musanman, gobe da sassafe akwai likita na musanman da zai duba marasa lafiya idan kun isa da wuri zaku iya ganinsa idan kuma kun tsaya sanya to maganar gaskiya ba zaku gansa ba sai nan da sati biyu”, ya idashe maganar yana zaro ambilon a cikin loka.

Tunda Dr. Samuel ya fara magana Mallam da Iya suke kallonshi har zuwa lokacin da ya idashe aya, ajiyar zuciya Iya ta sauke sannan ta miƙa hannu ta karɓi takardar ba tare da jira Mallam ba ta fice a office ɗin.
Mallam ne ya kalli Dr. haɗi da faɗin “ayi mana total ɗin kuɗin da aka kashe mu biya sannan ayi mana wata Alfarma dan Allaah da Mamarta da ita zasu kwana a cikin asibity ni kuma zan koma gida da daren inje in harhaɗo kayan da za’a buƙata”,

“Ba kida hankali ne”, Dr. Samuel yace ma Mallam tukum ya ci gaba da cewa “Ki ɗauka ƴarki ku tafi bamu buƙatarku a nan, tunda ba biyani kuɗin gobe za kuyi ba”,

“A’a Dr zamu biyaka”, Mallam Lima ya faɗa hawaye na gangaro masa jin sunan da Dr. Samuel ya kirashi da shi.

shiru Dr. Samuel ya yi, sannan yace “Kinga koda zaki biyani to wallahi yarinya naki ba zata kwana anan ba, wajen ajiye gaea za a kaita, tunda ita da gawa ba suda maraba kingane ko?”

cike da mamaki Mallam Liman ya ɗago yana kallon Dr. sannan yace a wajen ajiye gawa kace fa?”,

“yes abinda na faɗa kenan in kuma kina da ja to shikenan gani gaki”,

Roƙon Dr. Mallam ya dungayi akan ya yi haƙuri yabar Samha ta kwana a cikin asibity amma fafur yaƙi yace dole sedai ta kwana a wajen gawarwaki, Mallam Liman yana kuka kamar ƙaramin yaro ya fita daga office ɗin nashi ya tafi inda Iya take zaune, sanar mata ya yi da abinda likitan yace, hankalin Iya in ya yi dubu ya tashi, ta shiga matsanancin ruɗu akan lamarin ba ta cema Mallam komi ba ta kama hanya ta nufi office ɗin Dr. Mubakar wanda shima ya yi faɗa sosai ba kamar Dr. Samuel ba,
Zaune ta same shi ya yi jugum yana nazarin wani abu,
Sallam ta masa ya amsa idonshi akanta, nuna mata wajen zama ya yi ta zauna tukum ya ɗauko kofi ya tsiyaya mata ruwa mai sanyi ya bata, karɓa Iya tayi ta kafa kai ta shanye tas tukum ta ajiye masa kofin kana ta fara roƙonshi akan su yima musu haƙuri dan Allaah zuwa gobe zasu wuce da Samha kano gashi ba suda ƴan uwa cikin garin Gombe, kuma ance likitan idan yaxo Aminu kano be dawowa sai bayan sati biyu.

Cike da mamaki Dr. Mubarak yake kallon Iya har takai aya sannan ya kalleta yace “Amma Mama wa yace ba zai muku alfarmar kwana ɗaya ba kacal a asibityn nan?”, ya faɗa yana zare siririn gilashin dake fuskarshi,

Share hawaye Iya tayi tukum tace “Dr. abokin aikin kane yace sedai akaita wajen da ake ajiye gawarwaki”,

Cike da mamaki Dr. Mubarak ya miƙe tsaye yana tunanin da wani Dr. kenan suka duba Samha bayan Dr. Samuel, lalle ko inhar Dt. Samuel ne tabbas zai aika amman bari yaje ya same shi.

ganin ya miƙe yasa Iya itama ta miƙe gabanta na faɗuwa tana jiran taji amsar da zai bata.

“Zauna Mama ina zuwa bari in sameshi “, yace da ita tukum ya fita.

Zama Iya tayi shi kuma Dr. Mubarak yaje ya sami Dr. Samuel da maganar, nan ya fara kame-kame yana ƙaryata maganar Iya, dakatar dashi Dr. Mubarak ya yi sannan ya yi masa kashedi tukum ya bar offfice ɗin ranshi babu daɗi, a hanyarshi ta komawa Office ne ya haɗu da Mallam saboda office ɗinsu akwai ɗan tazara dashi, Mallam na ganinsa ya miƙe tsaye ya bi bayanshi ba tare da Dr. Mubarak yace dashi komi ba,

Bayan Dr. Mubarak ya shiga office ɗin nashi ya zauna sai ga Mallam ya shigo.

Wajen zama ya nuna masa, ya zauna tukum ya ɗago ya kalli Iya da take ta faman kuka saboda tausayin halin da Samha take ciki………..

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]