[Advertisements⬇️]

FULANIN TASHI CHAPTER 5 - Bankinhausanovels
Wed. Nov 30th, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Buɗe gidan Mallam liman ya yi, ya shiga saboda sallamar da yake tayi babu wanda ya amsa yasn indai akwai mutane a ciki to dole zasu amsa,
Mallam Liman har ya yi tafiya mao ɗan tazara a cikin gidan sai kuma ya ysaya jim kaɗan, wani tunani ne ya ɗarsu a zuciyarshi, murmushi ya yi tukum ya juya ya tafi.

Samha jiki ya yi zafi sosai dan har ta sanƙare a ƙasa saboda sanyin da yake kaɗata ga kuma yanayin garin na damina, gashi ta kumbura sosai zanen belt ɗin Ammar duk ya fito ruɗu-ruɗu a jikinta saboda Samha ba baya ba wajen haske,

*ABUJA*

Bayan Ammar ya ƙara hutawa ya yi baccin gajiya harya tashi Ni’imatullah ba ta dawo ba, saukowa ƙasa ya yi ya fita daga part ɗinsu gaba ɗaya zuwa na Ummi,
Zaune ya taddata tayi jugum kamar me nazarin wani abu, Sallaama ya yi ta amsa sannan ya shiga ciki ya zauna kusa da ita ya kwantar da kafaɗarsa a tata, a duk lokacin da Ammar yake da damuwa ya kanyi hakane dan ya samu sassauci musanman yadda ya mai da Ummi kamar mahaifiyarsa dan ko Ammi bema abinda ya kema Ummi.
Ummi kuwa tasan halin mutumin nata shiyasa ta zame jikinta haɗi da kallonsa, “Son”, Ummi ta kira sunansa, ido ya ɗago ya zuba mata ba tare da yace da ota komi ba, amma daga ganin fuskarshi zaka tabbatar da irin dmuwar da yake ciki.
Ummi ta ci gaba da cewa “Lafiya kuea? na ga kamar baka cikin nutsuwarka”.
“Ummi babu abinda ke damuna sai zancen Ni’imatullah! ki duba tun sanda ta fita tun kafin na iso amman har yanzu ba ta dawo ba, sannan na kira wayarta bansan iyaka ba ba’a ɗauka ba, anya babu abinda Ni’imatullah ke ɓoye min Ummi, ko kuwa akwai abinda kuke ɓoye min gaba ɗaya?”,

tunda Ammar ya fara magana Ummi take kallonshi, tasan tabbas duk abinda Ammar ya faɗa hakane, sedai kuma ba tada amsar tambayoyinsa saboda bata san inda Ni’imatullah da Hajiya Uwa suke zuwa ba, kullum zata ce zasu fira amma sai sukai dare basu daeo ba.
murya can ƙasa Ummi tace “Kwanyar da hankalinka Ammar angon Ni’imatullah duk inda su kaje ai zasu daeo ko? kuma kasan yadda Ni’imatullah ke sonka ba zata yi abinda zai dameka ba, kawai ka jira lokacin dawowarta ya yi ai ba gudu tayi ba”, Ummi ta ƙarashe maganar tana kallon fuskar Ammar haɗi da murmushi, Ammar kuwa shiru ya yi bece da ita komi ba ya miƙe tsam ya haye gadon dake falon ya ja dogon lulluɓi.

*KALTINGO*

zaune Mallam Liman yake yana jan casbi, sai Iya dake kusa dashi tana tankaɗen garin tuwo, Mallam Liman ne ya kira sunan iya ta amsa sannan ya ci gaba da cewa”Iya nidai gaba ɗaya hankalina be kwanta da wannan lamarin ba, yau kwana biyu kenan banga Ammar ba, sannannbanga Samha ba, Anya lafiya kuwa”, ya yi maganar yana jinjina kai alamar jimami.

Miƙewa tsaye Iyat tayi tana faɗin “Mallam kace ba kaga Samha da Ammar ba sannan ka tambaya anya lafiya, ba kaje gidan ja duba su bane ba?”, ta ƙarashe maganar tana shiga ɗaki ta ɗauko mayafi tayi gaba abinda dam ta tabbatar da babu lafiya!
Mallam Liman ma biyota ya yi a baya, yana faɗin “Iya naje gidan ɗazu nayi sallamar duniyar nan ba’a amsa ba, shiyasa na koma da baya kinsan sha’anin mata da miji bansan halin da zan shiga na tsincesu a ciki ba”, yana maganar suna tafiya da Iya, wacce ko saurararshu ba tayi ba jinshi kawai ta keyi amma gaba ɗaya hankalinta yana ga Samha.

ko da suka kawo gidansu Samha iya bata tsaya sallama ba faɗawa gidan tayi tana kiran sunan amsa amma ba’a ansa ba, kai tsaye ta shige ɗakin, duhu ne ya mamaye ɗakin gaba ɗaya baka ganin wani hasken kirki, da yake iya tasan kanɗaki saboda ba yau ta fara shiga ba, ba kuma jiya ba sai kawai ta sanya kai ta shiga ta buɗe windo, dandanan haske ya mamaye ko ina, dudubuwa Iya ta fara yi ina zata ga Samha saboda tasan Samha da shiritar tsiya yanzu haka ta ganta ta shige wani wajen saboda kar ta mata faɗan me yesa bata zuwa kwana biyu, ko ina ta leƙa bata ganta ba, hankalin Iya ba ƙaramin tashi ya ƙara yi ba, a hanyar fitowa ne taci karo da abu kamar mutum, kallon ƙasa tayi idonta ya yi arba da Samha dake kwance cikin gudawa da amai, salato Iya ta fara yi tana buga hannu haɗi da kiran Mallam Liman, a ruɗe ya shigo ɗakin kamar me shirin tashi sama, kafin Iya ta nuna masa Samha sai idonshi ya faɗa akanta, a zabure Mallam Liman ya ja da baya haɗi da kiran sunan Samha, duƙaea Iya tayi ta kama hannunta dukka biyu tana girgizawa, shiru tayi babu amsa sai ma wani irin nauyi da hamnayen nata su kayi, idanuwanta a kafe, bakinta sai kumfa yake fita, dosai Iya taji tsoron halin da Samha take ciki, magana ta fara yi tana kuka dosai kamar ranta zai fita, shi kuma Mallam Liman yana bata haƙuri da bata baki, Iya bata tsaya saurarenshi ba, ta fita da sauri a gurguje ta ɗibo ruwa ta watsa ma Samha, bata ko motsa ba balle asaran farkawarta, Iya na kuka ta ƙara komawa ta ɗibo ruwan ta watsa mata nan ma ko gizau ba tayi ba, MallamnLiman kuwa ya kasa komi hawaye ne kta tsatsafowa daga idonshi jikinsji ya yi sanyi da lamarin Iya ce kaɗai me ƙarfin hali,

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

ruwan randae gaba ɗaya Iya ta ɗebo ta watsa ma Samha amma bata canza zani ba, sosai Iya ta ruɗe ta fara magana cikin kuka tana faɗin “Mallam ka ga abinda nike jiye maka da shiga irin lamarin nan ko? yanxu mr gari ya waya ya kashe musu yarinya ya gudu ya barmu sab….. maganar Iya ce ta tsaya cak saboda ta kasa ƙarashewa kuka ya sarƙeta, zaman dirshem tayi a ƙasa tana rizgar kuka da tuna irin Amanar da Ammar ya ɗauka a gaban jama’a sannan ta sanya hannunshi a takarda ta kuma rantsuwar da ya yi akan Samha, wannan wata kalar cin amanace, yanzu idan hanya ta biyo da iyayen Samha suka dawo me zasu ce musu, wannan ranar wata kalar rana za’a kirata a wannan garin.
Abinda be taɓa faruwa ba ya faru a ta dalilinka Mallam, shima Mallam Liman yana kuka kamar wani ƙaramin yaro yana faɗin be taɓa tunanin Ammar ze tozartasu har haka ba, in auren ne beso a katse shi mana ya yi tafiyarsu, amma seda ya yi ma yarinyar mutane duka ya na ƙasa musu ita sannan ya tafi ya barta cikin wannan halin,
Iya da Mallam Liman sun ɗauki kusan awa guda akan Samha amma bata farfaɗo ba, cikin kuka Mallam Liman ya miƙe haɗi da umartar Iya sanya gyalenta su kama Samha su fitar da ita daga gidan zuwa gidanshi a mata sutura acan.
Babu musu Iya ta miƙe ita ma tana kuka ta sanya gyale suka kama Samha suka fitar da ita daga gidan, basu damu da yanayin da take ciki na guduwar da tayi ba, gidan Mallam Liman suka nufa da ita saboda acan ne za a mata sutura a kaita makwancinta.

Murhu Iya ta haɗa ta ɗaura ruwa sannan ta fita maƙota ta sanar musu da rasuwar Samha, kafin kace kwabo mutane sun taro a gidan Iya kowwa na faɗin albarkacin bakinshi.
Liman kuwa masallaci yaje ya tada Sallah bayan an gama ne yake sanar musu da rasuwar Samha karda kowwa ya wuce su tsaya ayi mata Sallah a kaita gidanta na gaskiya,
Cikin gida kuwa an juye ruwan wanka Iya ta tsarkake ma Samha jiki ta wanke gudawan da tayi tas sannan ta fara mata wanka kamar yadda addininmu ya faɗakar, an ɗauko likafani za’a sanya mata kenan Iya ta ƙura ido a ƙirjinta ganin kamar yana bugawa kaɗan-kaɗan, zani ta ɗauko ta lulliɓeta, sannan ta leƙa waje inda mutane suke sunyi cirko-cirko, wasu ba dan Allaah suka zo ba, sai dan su bama idanunsu abinci.
Da ƙyar Iya ta gano Mallam Liman ciki dandazon mutane, faɗa masa abinda ta gani tayi aikuwa a zabure Mallam Liman ya fito cikin Mutane ya ratsa matan dake cikin gidan ya wuce ɗaki, ƙura ma Samha ido ya yi, aikiwa ya tabbatar da abinda Iya ke faɗa masa gaskiya ne, kai tsaye ya fito waje ya sanar da jama’a kowwa ya kama kanshi Samha ba mutuwa tayi ba doguwar suma tayi sannan ya koma cikin gida ya umarci Iya da ta shiryata, babu musu Iya ta shirya Samha, shi kuma Mallam ya fita zuwa titi dan ya samu ya ɗauko abin hawan da zai kaisu asibity, babu jimawa sai ga Mallam Liman ya dawo da mota, fito da Samha akayi aka sanyata a mota sannan Iya ta shiga Mallam Liman ya shiga suka ɗauke hanya zuwa cikin garin gombe.

*KANO STATE*

Jalaluddeen na zaune ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya yana shan coffee, takardu ne birjik akan tebur yana dubawa saboda gobe zeyyi sammako zuwa Aminu kano dan yana da marasa lafiyar da zai gani daga ƙarfe bakwai na safe zuwa bakwai na dare.

Tunowa da takardar da ya ajiye a ɗakinshi ya yi wanda ya kwana biyu be leƙa ba yasa ya miƙe ya shiga ɗakin, kasancewar be cika san haske sosai ba, shiyasa ko da yaushe yake kashe glob ɗin ɗakinshi yawanci yafi barin na falo.
Kunna glob ɗin ya yi ya shiga ya fara duba takardun saboda suna da matuƙar mahinmanci tartare dashi, yana tsaka da duba takardun ne yafi karo da wata farar takarda a gefe, kamar bazai ɗauka ba dan harya gota ta saboda yasan ba xata wuce ta wani patient ɗin bace, ɗauka ya yi ya fito da ita daga cikin ambilo ɗin ya buɗeta gaba ɗaya, zare glas ɗin dake fuskarshi ya yi ya zauna gefen gado saboda farkon abinda ya fara gani ajikin takardar shine, *TAKARDAR YARJEJENIYA*

cike da mamaki yace “yarjejeniya da ni ko dawa”, zuciya mai saƙe-saƙe ce tace dashi ka mai da hankali dai ka karanta saboda ba kada amsar tamvbayarka sai a cikin takardar, bin shawarar zuciyarshi ya yi ya fara karanta takardar kamar haka.

_TAKARDAR YARJEJENIYAR AURE TSAKANIN AMMAR TANIM BATURE DA RUƘAIYA BUKARI ARƊO_

_Ni Bukari Arɗo na aura ma ƴata Ruƙaiya Bukari Arɗo aure tare da kamili kuma natsatsen mutum Ammar Tanin Bature akan sadaki mafi sassauci naira dubi biyar_

_duk da na kasance bafulatanin mutum ba muda matsogoni guda, shiyasa na yanke shawarar aura ma Ruƙaiya Bukari Arɗo aure da Ammar Tanim Bature, banyi gaban kaina ba, seda na tsaida shedu guda ukku, liman da hakimin kaltingo sai makwafcina Mallam Harisu tare da amincewar shi Ammar ɗin_

_dole ta sani barin Ruƙaiya (Samha) wajen Ammar saboda ina son ƴata tayi karatu mai nisan gaske, kuma ina saka ran dawowata nigeriya lokaci ƙanƙani_

 

ko da Jalaluddeen yazo nan a karanta takardar zufa ta wanke jikinshi tsaf, cike da mamaki yake kallon takardar sannan ya juya bayan takardar ya ci gaba da karanta ɗayan fejin.

_Ni Ammar Tanim Bature, na amshi auren Ruƙaiya Bukari Arɗo, nayi rantsuwa da Allaah zan kula da ita zan cika burin iyayenta, nayi Alƙawarin bata kariya sannan zan kasancr mata miji na gari_

a ƙasan takardar kuma sai saka hannun mutum biyar suka ya biyo baya kowwane da lambar wayarshi Mallam Liman, Ammar, Baffa, Mallam Haris.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]