[Advertisements⬇️]

FULANIN TASHI CHAPTER 3 - Bankinhausanovels
Thu. Oct 6th, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

FULANIN TASHI CHAPTER 3

 

 

 

Ammar ya isa kano lafiya, ya sauka a gidan wani amininshi Jalaludeen.
Bayan sun ɗan taɓa hira ne suka fita yawo, shima sai da Jalaludeen ya tursasa Ammar kafin ya je saboda kwata-kwata Ammar ba mutum bane mai san yawon jaraba ya fison kaɗaici fiye da shiga cikin mutane.

sai gabda sallar magrib suka dawo da kaya niƙi-niƙi a hannu, wani ɗaki suka jide kayan dukka sannan suka zauna zaman huce gajiya, labari sosai su kayi na makaranta amma sam Ammar be fahimta duk wani motsi da zeyyi sai gabanshi ya faɗi idan ya tuna ya bar ƴar mutane a cikin jeji bata san kowwa ba ga amanar da iyayenshi suka bashi ga ƙaƙubebben aurenshi dake kanta dana sani da nadama amincewa ta saka shi a gaba ta hanashi sukuni.

Ɓangaren Samha kuwa bayan wani lokaci jikinta ya ƙara zafi sosai, har wani huci yake fita mata ga azababben ciwon kai dake damunta bata ko iya miƙewa a haka ta rarrafa zuwa ɗakin Hamma Surajo ta ɗauko man shanu da magunguna sai wani ajiyayyen nono wanda ya daɗe a ajiye daga gani ya yi tsami, amma saboda yunwar dake ƙwaƙularta yasa ta kafa kai ta shanye shi tas ba tare da taji tsamin ba, magani ta ɓalla tasha sannan ta koma ta kwanta a katifar da Ammar yake kwana taja bargonshi ta rufe jikinta dukka tana ta ajiyar zuciya a haka har wani malalacin bacci yaci ribar saceta.

Washe gari da sassafe Ammar ya shirya zuwa airport saboda ƙarfe tara dai-dai jirginsu zai tashi zuwa Abuja, Jalaluddeen ne ya ɗaukeshi a motarshi ya kaishi tare da kayayyakin da ya siya, seda Jalaluddeen ya tsaya har jirgin su Ammar ya tashi sannan shima ya juya zuwa gida cike da kewar Aminin nashi.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Babban gidane mai ɗauke da part kusan guda shida, dukka ginin iri ɗaya ne sannan kowwane da gate ɗinshi sedai ba suda wani tazara sosai, zazzaune suke a babban falon gidan wasu a ƙasa wasu a saman kujera, daka kalli fuskokinsu zaka tabbatar da akwai shaƙuwa sosai a tsakaninsu, Ni’ima ce ta shigo bakinta ɗauke da sallama, dukkansu amsawa su kayi sannan ta bisu ɗaya bayan ɗaya ta gaidasu, Ummi dake zaune hakimce akan kujera fuskarta tasha farin glass irin na likitoci, zare farin glass ɗin tayi sannan tace “Ni’ima amma dake za a je ɗauko Ammar ɗin ko?”, sunkuyar da kai ƙasa Ni’ima tayi sannan tace “A’a Ummi zan fitane zuwa an jima zan dawo kafin nan nasan sun iso”,
“Okay”, kawai Ummi tace tukum ta kalli wata yarinya dake zaune kusa da ita, cike da zolaya tace “Auta amma a gida zaki zauna ki bari mu dawo ko?”, Ummi ta ƙarashe maganar tana murmushi! Buga ƙafa ƙasa Auta tayi tukum tace “Ummi aikuwa da tafiyar nan ba tayi kyau ba, ƙafata ƙafarki, babban Yaya guda ace bazan je ɗaukoshi ba gara ma Anty Ni’ima kar taje ta zauna”, tayi maganar tana kumbura baki.

Harara Ni’ima ta zabga mata tana faɗin “Auta nima ba zanje ba, zamu fita da Momi kafin ku dawo mun rigaku ai”,

“E amma Anty Ni’ima ai sai na rigaki ganin Ya Ammar”, ta faɗa tana murmushi.

NI’ima ba tace da ita komi ba ta tashi ta tafi,

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]