[Advertisements⬇️]

FULANIN TASHI CHAPTER 2 BY RUƘAIYA A UMAR (WAHEEDAT) - Bankinhausanovels
Thu. Oct 6th, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

FULANIN TASHI CHAPTER 2 BY RUƘAIYA A UMAR (WAHEEDAT)

 

 

 

Bakinta har yana rawa wajen faɗin “Aa zanyi da kaina”, nannauyar ajiyar zuciya ya sauke cikin zuciyarshi yana faɗin gaskiya akwai aiki gaba,

Ruwan ya ɗauka ya kai mata bayi sannan ya dawo yace “in kinga dama ki tashi kije kiyi in kuma baki ga dama ba ki zauna har sarkin zama yazo ya sameki”, ya faɗa yana shigewa ɗakin,
Ɗan tsayawa Samha tayi jim kaɗan saboda ita bata masan ya zata fara yima kanta wanka ba, ganin tsayuwar ba zata mata bane yasa ta cangala ƙafa ta wuce bayi wanka tayi jiƙa-jiƙa wanda ake kira da saka tsami dan ba tayi amfani da sabulu ba ta fito ƙafar nan duk dauɗa ga fasonta duk ta fama dan dama Kuka ce ke ƙoƙarin gyara mata ƙafar, ɗaki ta faɗa ta shafa mai da huda tukum ta ɗauki kayan fulani kalar blue ta saka sai a sannan ta fara jin wani kalan sanyi na shigarta,
bargon da suke lulluɓa ita da Kuka ta ɗauka ta lulluɓe gaba ɗaya jikinta, ba jimawa barci ɓarawo ya saceta,

Ɓangaren Ammar kuwa bayan ya tabbata ta gama wankan ta wuce ɗaki sannan shima ya fito ya surka ruwan ya kai bayi, wanka yayi ya ɗauro alwala sannan ya fito, sallaya ya shimfiɗa ya yi sallaah beko tsaya shafa mai ba shima yabi lafiyar gado saboda ba ƙaramin gajiya ya yi ba ga ɓacin rai da ɗacin da zuciyarsa ke masa duk suka haɗu suka masa yawa a maƙoshi.

Yana nan kwance ya yi shiru ya lula duniyar tunani kiran Ni’ima ya shigo wayarshi, ƙin ɗaukar wayar ya yi seda ta kira sau kusan huɗu sannan ya buga tsaki ya ɗauka wayar danshi tsakani ga Allaah yanzu haushin kowwa ya keji.

lumtse idonshi ya yi zuciyarshi fes saboda yadda yaji Ni’ima ta kira sunanshi da “My soul”, har cikin jinin cikinshi seda yaji sunan kamar bashi ba,
“Na’am ranki shi daɗe barka da war haka”, Ammar ya faɗa idonshi a lumshe dan ba ƙaramin sagewa jikinshi ya yi ba, tsakani har ga Allaah bazai iya kwatanta irin son da yake ma Ni’umatullah ba, muryarta ce ta dawo dashi daga ɗan hutun da ya tafi na ƙanƙanin lokaci “My soul naji kayi shiru ne”, Ni’ima ta faɗa tana ƙara lafewa jikin Momi,

“No Ni’ima ki bari zuwa an jima zan kiraki”, yana gama faɗar haka ƙit ya kashe wayar,
Ni’ima kuwa kallon Mominta tayi tana murmushi haɗi da rufe fuskarta da hannayenta tukum tace “Momi yace zai kirani zuwa an jima, wallaahi na ƙosa naga Ammar gaba ɗaya kewarsa ta dameni”,

“Eye”, cewar Momi tana dariya,

Ɓangaren Ammar kuwa koma wa yayi kan gadon bonon ya konta yana tunanin mafita kafin zuwa gobe da safe, yana nan kwance bacci yaci nasarar ɗaukarshi,

*Waiwaye*

*BORORO* wasu fulani ne da ake ma laƙabi da fulanin tashi,Fulani ne da ke yawo daga guri zuwa wani gurin. Basu da takamaiman gurin zama guda ɗaya. Kullum a tafe suke suna ƙoƙarin samawa dabbobinsu na kiwo guri mafi yalwar abinci. Suna kiwata shanu, awaki, tumaki, kaji, zabi da sauransu
Mahaifin Samha wato Baffa sun kasance suna zama na tsawon shekara ɗaya a waje, in suka zo lokacin tafiyarsu nayi zasu tartara komatsansu su ƙara gaba, Baffa ɗan asalin senegal ne yawon kiwo ya kawoshi nigeria a nan ne ya haɗu da Kuka Mahaifiyar Samha har suka daidaita, bayan bincike da akayi aka gano mahaifin Samha (Baffa) mutum ne mai karamci da nutsuwa uwa uba ilimin Addini, bayan aurensu da sati biyu Baffa ya tartaro tare da Kuka suka dawo gombe da zama, anan suka yado zango a kaltingo, mahaifiyar Samha sana’ar seda Nono ta keyi jama’ar gari da kansu sukan shigo cikin rugar Arɗo su saya, bayan shekara ɗaya da aurensu Allaah ya azurtasu da samun ƙaruwar ɗa na miji, bayan Kuka tayi arba’in taje gida daga can Baffa ya ɗauketa zuwa senegal nan ma taga danginshi, shekararsu ɗaya a senagal suka ƙara tartarowa zuwa najeriya, Bayan haihuwar Hamma Surajo sai da Kuka tayi shekara bakwai sannan taƙara haihuwar ɗiya mace, taci sunan Mahaifiyar Baffa Ruƙaiyah amman sun ɓoye sunanta ana kiranta Samha, tunda aka haifi Samha Baffa da Kuka da Hamma Surajo suka ɗauki son duniya suka ɗaura ma Samha komi Hamma Surajo ya samu Samha haka Baffa da Kuka,

Bayan Samha ta kai shekaru shida suka fara fita kiwo da Hamma Surajo, sannan Baffa ya saka su makarantar Allo data zamani, Samha nada matuƙar wayau da mai da hankali ga karatu duk abinda ta sanya a gaba shi ta keyi, wannan dalilins yasa ba ruwanta da kowwa ta mai da hankalinta ga karatun ta musanman karatun boko, Samha na Aji uku a ƙaramar makaranta Uncle Ammar yazo bautar ƙasa a garin kaltingo, kasancewar karkane wajen babu wadataccen gurin zama ga yanayin wajen sai a hankali shiyasa ya fara kwana a cikin makaranta ya ware wani aji wanda ba’a karatu ya mai dashi masaukinshi.
Wata rana anyi ruwan sama irin mai iskar nan duk ya jiƙa Ammar da kayansa gashi babu wurin zuwa, anan ne Allaah ya haɗashi da Baffa lokacin ya gama kiwo yana dawo wa, ko da Baffa ya nemi Ammar yazo gidansa ya zauna da ƙyar da suɗin goshi ya yarda, da farko ba ruwansa da kowwa dan ko abincinsu baya ci a cewarshi ƙyamarsu ya keyi daga baya kuwa sai ya gyare ya zama ɗan gari komi ci yake sosai, har suka ƙulla abota da Hamma Surajo, tafiya tayi tafiya lokacin tafiyarsu Baffa yazo, ga karatun Samha kuma Baffa ya daɗe yana tunanin akan shawarar da zai yanke daga baya kawai ya yanke shawarar gara ya barma Ammar Samha, tayi karatu a wajensa mai nisan gaske wanda da shine zata ceci kanta, Baffa ya samu Ammar da maganar, Ammar kuma ya amince itama Kuka ta amince haka Hamma Surajo, ranar da su Kuka zasu tafi aka ɗaura ma Ammar Aure da Samha ba tare da ya yi shawara da kowwa ba, Baffa ne wakilin Samha sai liman wakilin Ammar, bayan an gama ɗaurin auren Baffa ya tartara kan iyalanshi da shanayenshi suka lula lokacin ita kuma Samha ta tafi rafi ɗibo ma Kuka ruwa, wannan shine.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

*Dawowa labari*

cikin dare zazzaɓi ya rufe Samha mai zafin gaske, bakinta ne yaketa karkarwa jikinta na rawa kamar mazari ga kanta da yake ciwo kamar zai rabe gida biyu, ga tsoro ga duhun da gari ya yi, ya yinda Ammar shima ƙarfe biyu dai-dai ya farka, damuwa da tunanin yadda zai yi da Samha sun haɗu sun masa yawa aka, ga ƙaƙubabben aurenta dake kansa, “Mtsw”, ya ja tsaki zuciyarsa na masa babu daɗi tabbas akwai rigima gagaruma idan Ni’imatullah ta san da wannan auren, abu mafi girma ma iyayenshi amman ba komi yasan yadda zai yi da Abu tunda shine matsalar, ganin zancen zuci bazai masa bane yasa ya miƙa ya fito waje ya ɗaura alwalla sannan ya koma ɗaki dan gabatar da sallar nafila, ƙidar da sallaar keda wuya ya fara jiwo nishin Samha ƙasa-ƙasa, kasa kunne ya yi dan ya tabbatar da ta ina yake jiwo nishin nan, wani dogon tsaki yaja saboda ya tabbatar da Samha ce ke wannan nishin, banza da lamarinta ya yi, ya ci gaba da addu’a bai tashi daga kan sallayar ba seda ya jiwo kiran sallaah, miƙewa ya yi da casbi a hannunshi ya fita gidan gaba ɗaya ya tafi masallaci.

Samha kuwa saboda bige-bigen da ta keyi har ta faɗo ƙasa sai uban sambatu ta keyi kamar zautatta, kiran sunan Baffa da Kuka ta keyi murya ƙasa-ƙasa, can kuma ta fara kiran sunan Hamma Surajo tana neman temako, faɗi take ” Ayya Allaah sarki wayyo ni Allaah Uncle Ammar kizo ki ceceni, kada in mutu ban ƙara ganin Kuka da Baffa ba, Hamma Surajo ina kake kazo ka bani ketto jikina zafi”, tun tana iya sambatu har tayi shiru ta fara shiɗewa idanuwanta suka fara sama tana miƙewa kamar me shirin barin duniyar gaba ɗaya,
(Samhaty Habibty how market nasan ba kida dauriyar ciwo)😉😜

sai da gari ya yi haske lokacin har rana ta fara fitowa sannan Ammar ya dawo gida lokacin Samha ta galabaita sosai, ɗakin Hamma Surajo inda yake kwana ya shiga yayi shirinshi tsaf ya fito kamar wani bature ya rataya jakarshi ya fito waje, tsayawa ya yi jugum a barandar gidan yana tunani, zuciya mai saƙe-saƙe wata zuciyar tace dashi ya tafi wata kuma ta kwaɓeshi, ya kai a ƙalla 30mins yana tunanin ya zeyi, cikin rashin ƙwarin gwiwa ya nufi ɗakin Kuka, Sallama ya yi, yaji shiru babu wanda ya amsa jugum yayi a tsaye a wajen yana tunanin ina Samha ta tafi, yana tsaka da tunanin ya fara jiyo numfashin Samha ƙasa-ƙasa, kasa kunne ya yi danya tabbatar da me yake ji, tabbas numfashin nata ne, jiki a saɓule ya ajiye jakar dake rataye a kafaɗarshi ya shiga cikin ɗakin,

Cin karo ya yi da abu a ƙasa kamar mutum, tsayawa ya yi cak ya ɗauko wayarshi a cikin ajihunshi ya kunna dandanan haske ya bayyana a ko ina, kallon abinda ya ci tuntuɓe dashi ya yi, ja da baya ya yi sosai cike da tsoro yake kallonta,
Samha ce kwance cikin amai mai yawan gaske, numfashi ta keyi ƙasa-ƙasa wanda iyakarshi maƙogoronta, ba ƙaramin firgita ya yi da yanayinta ba ganin sauran numfashin nata yana ƙoƙarin barin jikinta gaba ɗaya, cikin ruɗu da tashin hankali ya tsoguna ƙasa ya tallabota gaba ɗaya a ƙirjinshi yana kallonta, gaba ɗaya tunaninshi ya tsaya cak ganin numfashin nata ma ya idashe tafiya.

A ruɗe ya sunkuceta gaba ɗaya ya fito da ita waje, a saman ciyawa ya ajiyeta ya miƙe kamar mazari ya isa wajen randa ya buɗe ya ɗauki cofin dake ajiye a saman randar ya ɗibi ruwa wanda ya yi sanyin gaske kamar an sanya shi a fridge, cikin sauri-sauri yazo ya watsa ma Samha ruwan amman bata ko motsa ba, miƙewa ya yi ya ƙara ɗibo ruwan, wannan karan a kwarya ya ɗibo ya watsa mata.
Firgigit ta farka jikinta na wani kalan rawa kamar ana kaɗata, haƙoranta na ƙara sosai idonta na zubda wasu zafafan hawaye, dafe kanta tayi da hannayenta dukka haɗi da kwalla ƙara mai ƙarfin gaske “Kuka”, ta kira sunanta,

“ke!”, Ammar ya daka mata tsawa sannan ya ci gaba da cewa “ki nutsu nace ko, wallahi kika ƙara yin motsi sai na ɓallaki”, ya ƙarashe maganar yana miƙewa jakarshi ya ɗauko ya ɓalla magani ya bata paracetamol da amozin dan ya rantse ya kuma rantsewa ko mutuwa za tayi sedai ta mutu amman shi tafiyarshi zeyyi,

Yana bata maganin ya miƙe haɗi da rataya jakarshi babu imani a tartare dashi ya fice.

Samha na kallonshi ya tafi bakinta ya kasa furta komi, tana ta ƙoƙarin dakatar dashi da ido amman ya kasa fahimta, hawaye ne keta shatata daga idonta cike da tausayin kanta da kanta taja jikinta da rarrafe ta shige ɗaki, a ƙasan siminti tayi ma kanta makwanci dan ta tabbatar yanzu ba tada wani ƴanci ko gata shikenan ta ta taƙare, gara ta fara rayuwar rashin gata tun yanzu,
Wani ɓangare na zuciyarta kuma tana jin zafi da ƙonar tafiyarsu Baffa, duk da ita yarinya ce sosai amma tasan zafin rashin iyaye kusa gaskiya su Baffa basu mata adalci ba.

Ammar kuwa babu tausayi a zuciyarshi yaje tasha ya haye mota ya yi kano washe gari jirginsu zai tashi zuwa Abuja.

_*FULANIN TASHI_*

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]