[Advertisements⬇️]

FULANIN TASHI CHAPTER 1 BY RUƘAIYA A UMAR (WAHEEDAT) - Bankinhausanovels
Thu. Oct 6th, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

FULANIN TASHI CHAPTER 1 BY RUƘAIYA A UMAR (WAHEEDAT)

 

Hankali tashi ta shigo gidan kamar an jehota, kai tsaye ɗakinsu ta shiga ta fara dube-dube tana wani kalan kuka, sosai ta firgita da rashin ganin Baffa da Kuka kowwani lungu da saƙo na gidan duk tabi ta duddba amman bata gansu ba, cikin yanayi na ruɗu da tashin hankali ta fita daga gidan ta kama hanyar makarantarsu, da yake tafiyar ba cikin konciyar hankali ta ke yi ba sjiyasa cikin lokaci ƙanƙani ta isa makarantar, Uncle Ammar ta samu zaune ya zabga uban tagumi shi kaɗai ganinta kawai da ya yi daga sama yasa gabanshi wani ya yi wani kalan mummunar faɗuwa ƙirjinshi ya fara dukawa kamar ze fita, duƙar da kanshi ya yi ƙasa ziciyar na harbawa da sauri da sauri, ita ko samu wuri tayi kusa gareshi ta zauna, sunyi zama kamar na binti uku babu wanda yace da wani ƙala cikinsu, daga bisani kuma ta fashe da wani kalan kuka mai tsuma zuciya, Uncle Ammar dake kusa da ita ya tashi ya miƙe zai tafi, hannunshi ta kama da dukka hannayenta ta ƙara fashewa da kuka cikin maganarta da bata fita da kyau tace “Ancle Amar sun tafi sun barni ba ni da kowwa Baffa da Kuka sun tafi”, ta ƙara fashewa da kuka.
Ammar kuwa kallonta ya ke yi kamar yau ya saba ganinta ranshi a matuƙar ɓace ya tun kuɗeta ta faɗi ƙasa zuciyarshi na zafi ya ɗaga kai ya kalleta haɗi da nunata da hannunshi bakinshi har rawa ya keyi wajen faɗin “Wallaahi Samha kika ƙara nuna kinsan ni sai nayi miki wulaƙanci”, ya faɗa yana watsa mata yawon bakinshi, harya fara tafiya sai kuma ya dawo ya ɗauki farar takardar dake kan bencin da ya zauna sannan ya yi tafiyarshi,

da kallo Samha ta bishi kana ta miƙe tsaye ta nufi gidansu, ko da ta isa gidan babu wanda take kira sai Kuka da Baffa tana kuka tana nemansu, samun waje tayi da zauna akan tulin ciyawar dake wajen tasa kanta tsakan kanij gwiwarta tana kuka, miƙewa kuma tayi kamar an zabureta ta fara bin shatin ƙafafunsu Baffa da kuma shanayensu tayi tafiya mai nisan gaske amman bata taddasu ba wannan shiya tabbatar mata dasu Baffa sun tafi kenan, hankalinta ba ƙaramin tashi ya ƙarayi ba gashi ta gaji ga galabaitar da tayi wajen wani kududdufi ta samu ta zauna kanta na wani kalan sara mata, tana nan zaune wasu matasa suka zo wucewa su biyu, Lamiɗo ne ya kalli Giɗaɗo yace “Hai Giɗaɗo ka ga Samha can muje mu sameshi”, da sauri Giɗaɗo ya ɗaga kai ya kalleta sannan ya saki wani murmushi mai kyawon gaske da ya ƙarama fuskarshi kyau sannan ya buga sanda haɗi da cewa “Mu tai”,

Samha kuwa tana hango su Giɗaɗo da Lamiɗo ta miƙe tsaye a zabure ta fara gudu hankalinta a matuƙar tashi, hanyar gida ta kama su Giɗoɗa na biye da ita, kasancersu maza manyan garadai shiyasa suka cin mata lokaci ƙanƙani.

Hannunta Giɗaɗo ya kama haɗi da waska mata wani kalan mari wanda sai da ganinta ya ɗauke gaba ɗaya, a gifice ta ɗago ta ganna masa cizo amman ko gizau beyi ba, marinta Lamiɗo ya yi shima yana dariya, Giɗaɗo ne ya cire mata ɗankwalin dake kanta ya ingizata ta faɗi, bulalar da suke dukan shanu da ita ya ɗaga ya fara dukanta ta ita tana kuka kamar ranta zai fita.

suna tsaka da tafiya Baffa ya dafe ƙirjinshi a daidai lokacin da Kuka ita ma ta dafe nata ƙirjin cikin yanayi na ciwo ta kalli Baffa sannan tace “Baffa Samha anya ba muyi kuskuren barin Samha wajen kaɗo ba? Baffa Samha ƙirjina zafi ya keyi anya babu wani abu da yake faruwa dashi kuwa?”, ta faɗa tana rushewa da kuka haɗi da dafe zuciyarta dan danan wani kalan tari ya sarƙeta, dukka ayarin da suke tafiya suka dakata saboda jin tarin Kuka sukayo kanta gaba ɗaya, amai ta farayi da guda-gudan jini, da sauri Hamma Surajo ya ɗauko magungunanta ya bata sannan ya bata soyayyen man shanu da kettu,
cikin lokaci ƙanƙani tarin ya lafa, kana Hamma Surajo yace ma Baffa ko zasu dakata da tafiyar su ɗan huta saboda Kuka tana wahala gashi tafiyar ƙafa za suyi suje wani garin duk da sunyi nisa sosai dan har sun fita daga mai duguri sun fara shiga yankin nijar, Baffa bai ƙi ta Hamma Surajo ba suka samu waje suka zauna sannan Baffa ya kalli Kuka haɗi da dafa kafaɗarta sannan yace “Kuka ki tsaida hankalinki gu ɗaya babu abinda ke faruwa da Samha kawai kewarta ce ke damunki, sannan kin sani kanki Ammar ba zata cutar da Samha ba, kin manta shine Malaminta da ya yi Alƙawarin kareta da mutuncinta”, ya ƙarashe maganar yana jinjina mata kai.

da sauri Samha ta tashi ta fara gudu kamar zata tashi sama Giɗaɗo da Lamiɗo ma mara bata baya au kayi, ji tayi ta bangaji mutum kamar dutse wanda saboda gigicewar da tayi bata ma san kowaye ba, ƙanƙameshi tayi ta baya ta saki wani kalan kuka mai ban tausayi, cireta ya yi a bayanshi ya juya da ita ta gabanshi ya kalli fuskarta, a matuƙar firgice Ammar y yake kallonta ranshi a ɓace yaja gefe da ita ya zaunar da ita a kusa da dutsen dake wajen sannan ya tinkari su Giɗaɗo, ganinshi kama mayunwacin zaki yasa su Giɗaɗo firgita suka juya a guje binsu ya yi da gudu shima aikuwa yaci sa’ar kamasu ya zare belt ɗin dake kwankwason shi ya fara dukarsu dashi kamar an aikoshi srda ya tabbatar da ya musu lilis ya barsu kwance tukum ya dawo ya ɗauki Samha cak ya yi da ita gida.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Ajiyeta ya yo gefe ya haɗa wuta ya ɗaura ruwa, tukum ya dawo kusa da ita, kallonta ya yi fuska babu alamun wasa sannan yace “Ke Uban me ki kaje yi wajen Giɗaɗo har suka miki wannan dukan”, ya faɗa yana zabga mata harara.
Cike da tsoronshi da ya bayyana ƙarara a fuskarta tace “Uncle Ammar babu abinda nayi musu, na fita biɗarsu Baffa da Kuka ne suka ganni suka kamani da duka”, ta faɗa kwalla na zubowa a idonta,
Ƙara murtuke fuska Ammar ya yi sannan yace “Kinga Samha ke da su Kuka sai a lahira na rantse da Allaah duk ranar da kika ƙara fita ba tare da izinina ba sai na ɓallaki, harta boko kika ƙara zuwa sai na naɗa miki duka banza kawai sha sha sha”,
Kallonshi Samha ta ke yi sosai cikin zuciyarta tana ƙara maimaitawa ita da su Baffa sai a lahira kenan sun tafi kenan sun barta.
Shikenan dama Kuka da Baffa basa sonta hawaye ne ta fara tsatsafowa daga idanunta tana shirin fashewa da kuka Ammar ya daka mata tsawar da sai da ta firgita, nuna ta ya yi da yatsarshi yace “Wallahi kika mim kuka sai na fasa miki baki”, tsit Samha tayi sedai hawayen dake fita daga idonta,
Ɓangaren Ammar kuma ɗaki ya faɗa ya ɗauko first Aid box ɗinshi ya dawo, kujera yaja gefe kusa da ita ya zauna,
“Miƙo ƙafar!”, yace da ita cikin ɗaga murya, ganin fuskarshi babu alamar wasa yasa ta miƙa ƙafar tana kallonshi, harara ya wurga mata tukum ya kama ƙafar ya fara wankewa, a hankali ta fara jin zafi saboda wankin da hydrogyne ne, tun tana daurewa harta fara kuka tana cije baki amman bai kyaleta ba har sai da ya gama mata dressing ɗin tukum ya sake mata ƙafar, zuwa ya yi ya mai da sannan ya juye mata ruwan wanka a botiki ya surka haɗi da kallonta, idonshi ne ya faɗa kan fuskarta yadda tayi dama-dama da majina babu kyan gani, tsaki ya yi cikin zuciyarshi yana faɗin nikam an haɗani da jaraba wallahi, zuwa ya yi ya cafko wuyar rigarta seda ta kusa faɗuwa ya yi sauri ya tare ta, Samha kuwa kallon fuskarshi tayi da sauri ta sunkuyar dakai gani tayi ya koma mata kamar wani dodo.
ɗago idon da zata ƙarayi suka yi 4eyes wanda sai da ƙirjinshi ya bada wani kalan sauti, ranshi a matuƙar ɓace ya ɗago yace mata “ke! dan ubanki ubanwa kike kallo,?” sunkuyar da kanta tayi bakinta na rawa kamar mazari tace “kiyi haƙuri Uncle Ammar bake nike kallo ba”, ta faɗa cikin yanayin maganarsu na fulani,

kama bakinta Ammar ya yi da dukka hannayenshi biyu ya ja sosai tukum ya saƙala hannayenshi ciki wata kalar azaba ce ta ziyarci Samha har bata san sanda ta saki fitsari a tsaye ba, shiko Ammar besan meke wakana ba faɗi kawai yake “shegiya kawai zaki gane kurenki yau sai na mai da wannan shegen bakin naki mai kama da na Aku babba, banziya kawai”, ya ƙarashe maganar yana ingizata ta baya ta faɗa kan ciyawa, kuka Samha ta rushe dashi, ya yinda Ammar ya juya a fusace zai wuce nan ya kula da fitsarin da Samha tayi, riƙe baki kawai ya yi ganin fitsarin har takalmanshi sai da suka taɓa, cikin zuciyarshi kuwa yana hararo irin dukan da zai mata yau.

kallon gefenshi ya yi aikuwa idonshi ya faɗa kan ramdar dake kusa dashi, tuntsirar da ruwan zafin dake cikin bukiti ya yi ya kamfato ruwan randar wanda ya yi sanyi sosai ya an taya ma Samha a jiki, a firgice ta miƙe tsaye jikinta na kaɗawa gashi yanayin garin lokacin sanyi ne, cire belt ɗin dake jikinshi ya yi ya kama dukanta kamar an aiko shi haɗi da marinta sai da ya yi mata lilis sannan ya barta a wajen ya wucewarsa, ita ko Samha ta daku babu abinda ta ke yi sai ajiyar zuciya tana kiran sunan Baffa da Kuka da Hamma surajonta,

Sedai su Baffa suka huta lokacin ciwon Kuka ya lafa, sauke guzurinsu su kayi suka ɗaura ma tumaki, tukum Baffa ya ƙara jera kayan da kyau har aka samu inda Kuka zata zauna tukum suka kaɗa tumakinsu da shanaye suka ci gaba da tafiya,

Sai da yamma liƙis tukum Ammar ya dawo lokacin Samha tayi barci ta farka, wajenta ya yo gadan-gadan kamar zai daketa saboda haushi ta ƙara bashi, lalle yau ya tabbatar da halin fulani da ake faɗi kenan, wato tana nan inda ya barta bata tashi ba, ɗaga hannu ya yi da niyyar marinta kawai idonshi ya sauka kan fuskarta, da kallo ya bita ganin lahanin da ya yi ma ƴar mutane gefen fuskarta ta bakinta ba ƙaramin kumbura su kayi idanuwanta sun rufe rub sai ƙwayar fari-farin da kake hangowa, gaba ɗaya ta fice hankalinta kamar ba Samha da ya sani ba, tsaki ya yi ya juya ya nufi ɗaki, ashana ya ɗauko ya ƙara haɗa wuta ta ruru tukum ya ɗaura tukunyar kasa, ya dawo kusa da ita ya zuba mata ido yana kallonta, suna haɗa ido sai ya duƙar da kanshi ƙasa yana waskewa, tunanin ya makomar rayuwarta ya fara yi wanda tunda ya ɗauki alƙawarin kula da ita wannan tunanin yake masa yawo a kwakwalwa, lalle ya ɗaukarma kansa babban abu wanda kwata-kwata beyi shawara da wani ba kafin ya yanke wannan hukuncin, lalle akwai gagarumar matsala, tunaninshi ne ya tsaya cak! saboda Ni’ima da ta faɗo masa arai, “tabɗijon ya ayyana aranshi saboda yasan halin Ni’ima sarai, ga kuma Anty Shuraima da tafi kowwa matsala ga tafiyar tashi ta ƙaraso zuwa gobe shi ba wani aboki yake dashi ba balle ya nemi shawarshi,

Bayan kamar mintuna goma da ɗaura ruwan ya tashi yaje ya taɓa yaji ya yi zafi rau, juye mata ya yi a bokiti ranshi na ƙara ɓaci ya kai mata banɗaki tukum yazo ya tada ita yana kawar da kanshi gefe, tsandara ihu tayi wanda sai da ya saka hannayenshi ya rufe kunnenshi “Lafiya!?” ya daka mata tsaya, hannunshi ta kama da hannu biyu tana faɗim “Uncle Ammar ƙafata zata karye “,ta faɗa cikin harshen fulani.

Kasancewar Ammar ya yi zama da Hamma Surajo kuma yana fahimtar fillancin babu laifi yasa ya fahimci me take cewa, “zata karye”, ya maimaita aranshi, karde ace ya targaɗa ƴar mutane, sai yanzu ma ya kula da ƙafar harta tasa, zaunar da ita ya yi gefe ya ɗauko ragga (tsumma) da ruwan zafi ya ja yatsar sannan ya gasa mata tana
kuka tana turjewa a haka suka gama sannan yace mata “miƙe kije kiyi wanka”.

kallonshi tayi tace “Uncle Ammar ban iya wanka ba, Kuka ce take min kullum”,

A zabure Ammar ya kalleta idanuwanshi suka firfito waje kamar me shirin shiɗewa yace “me kika ce!”,

ɗaga masa kai tayi sama ta maimaita masa abinda tace, buga ƙafa ƙasa Ammar ya yi kamar zeyi kuka sannan yace “Yanzu ni keki so na miki wankan kenan?”, dan tabbas an haɗashi da aiki babba ba ƙarami ba…….

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]