[Advertisements⬇️]

FAMILY DOCTOR COMPLETE HAUSA NOVEL - Bankinhausanovels
Thu. Oct 6th, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

FAMILY DOCTOR COMPLETE HAUSA NOVEL

 

 

[5/21, 3:27 PM] Oummu Ɗahirah: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTORS*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER’S ASSO📖*
”’®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓”’

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

_Thanks be May God bless everyone, peace and blessings be upon our leader Prophet Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam, may God bless you and grant me the ability to write this book, may God grant me the ability to write what will benefit the nation ameen._

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA’S FAMILY.*_

*LITTAFAN MARUBUCIYAR*
_NAFEESAT._
_BARRISTER IBRAHIM KHALIL._
_LABARIN DEEBIZAH._
_MALAMA LADI._
_JARUMAI_
_LUBABATU (ƴar ƙwallon ƙafa)._

.

*EPISODE One*

Doctor ” Al’ameen Abubakar Khabeer Cindo ” and his wife ” Prof. Nafeesa (Baby) Isma’il Audu, ” as you know in the story of * NAFEESAT * They live in Kaduna, and they still live in the city, owned by their five children.

*1_ DOCTOR NOOR (LAWAL AL’AMEEN ~YARON UMMEE NAFEESA~)* Wanda a yanzu ake kiran sa Big Dady, matar sa ɗaya *Hajiya Asiya (Hajiya) ƴa ga Muhsina,* yaran su uku, Doctor Usman, sai Doctor Zainab ~yanzu haka tayi aure,~ sai kuma Yusra.

*2_ HAJIYA RABI’ATU AL’AMEEN (IKRAM) ~WANDA A YANZU TANA AURE A GARIN KATSINA~* tana zaune da iyalan ta acan.

*3_ DOCTOR ABUBAKAR AL’AMEEN ~WANDA YANZU AKE KIRAN SA DA ABBA~* matar sa ɗaya Doctor Fatima (Hajja Fatu) ~ƴa ga Abokin Doc. Al’ameen wato Haidar da ƙanwar sa Ihsan,~ yaran su Biyu, Doctor Al’ameen (Baffa), sai ƙanwar sa Shakira.

*4_ DOCTOR AL’AMEEN AL’AMEEN (ABBU)* Matan sa biyu, ~Bilkisu (Umma) ƴa ga Baseera,~ yaran ta uku Doctor Zulaiha ~tayi aure,~ sai Fadila da autan su Fadil. Sai matar sa ta biyu *A’ISHA (AUNTY AMARYA)* yarinyan ta ɗaya ”’NAFEESAT”’ suna kiran ta da Ɗahira.

*5_ HAJIYA LAILA AL’AMEEN* yanzu haka tana aure a Kano, ta auri babban Yaron *WALID.* Suna zaune da iyalan su can.

Waɗannan familyn yanzu haka suna zaune ne a gida ɗaya kowa da part ɗin shi, sai dai akwai Babban parlour’n da ya haɗa su, yanzu haka Doc. Al’ameen Wanda a yanzu suke kiran sa da *KAKA* ya kai shekaru 89years. Tuni ya ajiye aikin sa sakamakon yana fama da ciwon ƙafa wanda a halin yanzu yana zaune ne a wheel chair, matar sa Prof. Nafeesa (Baby) Shekaru uku kenan da Allah ya amshi abin sa.

Za kuyi mamaki idan nace muku duk ka familyn Doc. Al’ameen gaba ɗayan su *DOCTORS* ne, wannan shine burin sa kuma Allah ya cika masa.

Babban asibitin da ya gina ya ƙara haɓɓaka shi wanda a halin yanzu Five Block ne, kuma sosai asibitin me suna *(AL’AMEEN FAMILY HOSPITAL)* tayi fice a ƙasar Nigeria, gaba ɗaya familyn suna aiki ne a Hospital ɗin.

Yanzu haka a halin yanzu an shirya yin babban Walima don taya Doc. Ɗahira(Nafeesa) Al’ameen Al’ameen, Doc. Shakira Abubakar Al’ameen, Doc. Yusra Noor Al’ameen, da Doc. Fadila Al’ameen Al’ameen. Murnan kammala karatun su na likitanci, wanda za su soma aiki ne a ranan da a kayi musu waliman tare da sabbin ma’aikata da za’a ɗiba a ranan.

*KU BIYO NI DON JIN LABARIN WAƊANNAN FAMILYN*

Zaune suke su Huɗu a Babban katafaren parlour’n gidan da ya’amsa sunan sa a haɗuwa da ƙayatarwa, da shigowan ka parlour’n Babban Hoton Prof. Nafeesa (Baby) zaka soma cin karo dashi, wanda tayi sa ne lokacin da ta zama Professor, tana sanye da baƙar abaya me tsananin kyawu da burgewa, wanda duk da kasancewar ta baƙa ba ƙaramin kyau yayi mata ba, sai tayane kanta da Milk Colour ɗin Veil, kyakykyawar fuskarta yalwace take da murmushin da ya ƙara fito da tsantsan kyawun ta tare da Dimpul ɗin ta, a tsaye take ta riƙe ƙugu da hannu biyu tare da ɗan ɗage kanta, da alamun sanda akayi hoton bata san ma za’a yi sa ba. kusa da hoton kuma wani tanƙamemen hoton ne da a cikin sa Al’ameen ne tare da ita Babyn, suna zaune manne da juna sun saka ankon shadda me ruwan powder, gefe da gefen su kuma Noor ne tare da Ikram jingine da jikin su, duk kan su dariya suke yi time ɗin da aka ɗauki hoton, sai gefe kuma sauran hotunan ƴan gidan ne kowa da iyalan sa, sannan sai aka ɗau guda ɗaya wanda su kayi gaba ɗaya familyn, shi wannan ba’a daɗe da yin sa ba, don gab da rasuwan Prof. Baby akayi sa, gaba ɗaya idan ka kalle su sosai suke kamanceceniya da juna, sai dai banbancin launi da ya raba su.

Doc. Al’ameen wato KAKA tare da yaran sa maza su uku zaune cikin parlour’n suna tattauna yanda za su gudanar da Waliman yaran su kamar yanda suka saba a duk sanda yaran gidan suka gama karatun su na likitanci.

“Kai takwara yaushe matarka zasu dawo ne? Kasan jibi ne walima, ya kamata su dawo don itama Matata (yana nufin Ɗahira kenan) ta sami damar shiryawa yanda Ya kamata”. Kaka dake zaune saman wheel chair yake wannan maganan

ABBU yace, “insha Allahu Dady zasu dawo zan sake tuntuɓan su inji, sabida mahaifin A’isha (matar sa Aunty Amarya) jikin ta yayi tsanani ne shiyasaka suka jin kirta”.

Kaka yace, “to shikenan Allah ya dawo da su lafiya”.

Gaba ɗaya suka amsa da “ameeen”.

Sannan ya kalli Big Dady yace, “Kai kuma da yaushe ne Usman yace “zai dawo?”

Big Dady yace, “Allah ya taimaki Dadyna! na yi masa magana amma yace “in ba ka haƙuri ba zai samu daman zuwa ba sabida aiki sun yi masa yawa”.

Cikin nuna alamun fushi Kaka yace, “wai yaushe Usman yabzama me taurin kai ne? Ko don yana tunanin na ba shi dama ya zauna acan yayi aiki shine yake son ɓata min rai? To, ka gaggauta kiran sa ka faɗa masa umarni nake ba sa; dole ne ya zo wannan taron Waliman da za’a yi, ko me yake yi ya’ajiye sa ya halarci taron nan”.

Gaba ɗayan su su kace “Allah ya huci zuciyar ka Baba”.

“Insha Allahu zan sanar masa Dady kuma zai zo”. Cewar Big Dady kenan

Gyaɗa kansa Kaka yayi kana yace, “za ku iya tafiya na sallame ku, Allah yayi muku Albarka”.

Gaba ɗayan su suka amsa da “ameen” kana suka tashi suka fice.

Shi kuma Kaka janyo Remote yayi ya sauya tasha zuwa African t.v yana sauraron wa’azi

Da sallama Fadil ya shigo parlour’n, wanda ya kasance shine ƙaramin gidan don shekarun sa baza su wuce 14yrs ba. zama yayi kan kujeran da ke kusa da na Kaka ya saka hannu ya ja gemun Kakan da ya kasance fari fat, yana dariya yace, “Kakus kana hutawa ne?”

Kaka bige hannun sa yayi yana faɗin, “Ƙaniyar ka Fadil, kai ma ka koyi jan min gemun ne yanda Matata take min?”

Dariya ya tuntsire da shi yace, “to ai hakan ya fi dace wa da kai Kakus, don me baza ka aske gemun ba ka bar abu sai faman lilo yake yi, wlh watarana kana barci zan silalo in cire maka kowa ya huta”.

Dariya shima Kakan yayi yace, “lallai ka raina ni da yawa amma ina da me maganin ka, ka jira ya dawo zan faɗa masa duk abinda kake min”.

Zumbur Fadil ya miƙe yana waro ido waje yace, “afwan Kakus kaima ka san ba mu haka da kai, wlh yau ne kawai nace bari in ɗana Amma baran sake ba, Kar kasanar masa don Allah kaji Kaka na”. Yaƙarike maganar nasa yana me marairaice fuska kamar zai yi kuka

“Shaƙiyin yaro ashe kana da tsoro har haka?”

Waro idanu Fadil ɗin ya sake yi yace, “iyyee Kaka taya bazan ji tsoro ba bayan kana son ka haɗa ni da Zakin gidan mu? Ni dai ka ga tafiya na don tunda ka’ambato shi bazan iya zama anan ba”. Yana ƙarisa maganar ya ruga aguje yabi hanyar part ɗin su

Da dariya Kaka yabraka shi, kana ya girgiza kan sa aran sa yana cewa, “lallai Usman ka koya ma yaran gidan nan tsoron ka, ba ka a cikin gidan ma shekara da shekaru amma har yanzu tsoron ka be bar cikin ran su ba”.

Ci gaba da kallon sa yayi, sai can kuma ya ɗago kansa yana kallon hoton matar sa Baby, Wanda take ita kaɗai ɗin, murmushi da hawaye ne a haɗe suka taho mishi tunawa da rayuwan su, kullum ranan duniya sai ya zub da hawaye a kan ta, coz Ko wacce rana sai ya kalli hoton ta sama da ashirin, kuma aduk sanda zai kalla ko yayi kuka ko yayi dariya sabida abinda zai tuna na game da rayuwan su a wannan lokacin, gaba ɗaya ɗakin sa idan ka shiga hotunan ta ne birjik, da sanda take tashen ta da sanda ta tsufa, har ta bakin gadon sa inda yake saka kansa akwai hoton ta da ya’ajiye a wajen, mutuwan ta ya bala’in girgiza sa wanda yayi kamar bazai rayu ba, sai daƙyar ya dawo hayyacin sa bayan dogon jinyan da yayi, har yanzu har gobe soyayyar ta tana nan daram a zuciyar sa, domin kamar ƙaddara ne da Allah ya saka masa na tsananin ƙaunarta, kullum fatan sa ace ga ranan da zai bi ta, shima ya koma ga mahaliccin sa kamar yanda ta tafi ta bar sa..

Dafa kafaɗun sa da akayi shi ya dawo dashi hayyacin sa, Yusra ce tsaye kansa tana kallon sa, idan da sabo yaci ace sun saba da ganin Kakan nasu cikin wannan halin, kuma sun san da cewa ba komi yake saka sa a halin nan ba illa tuna Kakar su.

“Kaka har yanzu dai ka ƙi ka dena tuna wannan tsohuwar matar taka, har yaushe ne zaka cire ta arai ne kayi rayuwan ka cikin kwanciyar hankali? Mu nan mun ishe ka rayuwa ba sai ka tuna ta ba, me ake yi da tsohon Zuma bayan ga sabbin zuma? Don Allah ka dena ɓata time ɗin ka a kan ta”.

Hannu ya saka ya share hawayen yana murmushi yace, “Yusra kenan baza ki taɓa gane wa ba, amma kowa ya san da cewa tsohon zuma shi ne wanda ke magani, sannan ba’a iya manta shi ko wani hali mutum ya shiga, Ni Matata ta fiye min ku duk kan ku, idan da za’a bani zaɓi daku da ita in zaɓa, ita zan zaɓa in bar ku”.

Taɓe baki Yusra tayi tace, “to don baka zaɓe mu ba sai me Kaka? Our parents will vote for us because they love us.”

Kaka yace, “to naji ban ce kiyi min rashin kunya ba, said me to my room”.

“Da can Ni na ɗauko ka?”

Hararan ta yayi yace, “I have noticed that Yusra is jealous of my wife, but you will die. I will never love you. She is the only one who betrays me. kuma wlh idan baki gungura Ni kin mayar dani ɗaki na ba da Yayan ki zan haɗa ki, ke ce farko wacce zan kai ƙara wajen sa”.

Turo baki tayi ciki-ciki tace, “ka daɗe baka kai ɗin ba, in yaso sai ya kashe Ni kar ya bar Ni da rai”.

“What are you saying?” Kaka said looking at her

“Me kuwa kaji na ce?” Tafaɗa tana huro hanci kafin ta soma tura sa

Murmushi Kaka yayi yace, “na san maganin ku dani kuke zan cen”.

Tana gungura sa cikin ɗakin sa ta fito tayi nasu part ɗin cike da haushin Kakan.
[5/21, 3:28 PM] Oummu Ɗahirah: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTORS*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER’S ASSO📖*
”’®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓”’

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

_Godiya ta tabbata ga Allah me kowa me komi, tsira da aminci su tabbata ga shugaban mu Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallam, Allah Nagode maka da kabani daman rubuta wannan littafin, 🙏🏼ya Allah kabani ikon rubuta abinda zai amfani al.umma ameen._

.

*EPISODE Two*

Da shigan Yusra parlourn su ta sami Hajiya zaune tana kallo, ƙarisawa tayi ta zauna kusa da ita tana ci gaba da cunno baki gaba

Da ido Hajiya taraka ta dashi kana tace, “Ke dawa? zaki shigo min parlour Babu sallama?”

Yusra kallon Hajiya tayi har a lokacin fuska a turɓune tace, “it’s Kaka and I, wai cewa yayi zai haɗa ni da Ya Usman idan ya dawo”.

Tsaki Hajiya taja tana hararan ta tace, “ai maganin ku kenan tunda baku da kunya, idan ya haɗa ku dashi sai ku dawo hankalin ku”.

Yusra kamar za tayi kuka tace, “to Hajiya ba kakan mu bane menene in mun yi wasa dashi?”

“It’s up to you. Get up and go to Zainab’s house. I’ve been waiting for you for a long time. tun ɗazu ta kira Ni a waya kuma na neme ki sama da ƙasa ban ganki ba, sai ki kwana acan in yaso gobe kun taho tare”.

Miƙe wa Yusra tayi ta nufi hanyan ɗakin ta, har ta kusa shiga Hajiyan ta kira ta, dakata wa tayi ta juyo tana kallon ta bayan da ta’amsa

“Ki shiga ɗaki na ki ɗauko Flower kwata biyar ki tafi dashi, nima sai kuyi min nawa don bani da lokaci aiyukan za suyi min yawa, cincin ɗin na kwata biyu kaɗai za kuyi min”.

“To”. Yusra tace hakan tana wuce wa ɗakin Hajiyan.

_*****_

“Calm down, what can I tell you? Shakira, kin san Buri na shi ne In ga ranan da za’a ce mun fi kowa a wannan familyn, I want to see the future of the *AL’AMEEN FAMILY HOSPITAL* back under us. wannan dalilin ne yasaka na saka wa Baffa sunan Kakan ku, kuma dalilin ne yasaka na matsa wa Abban ku yabar Ni na koma makaranta na zama Likita, I know that one day my dream will come true. ”

Shakira looked at her mother and said, “Hajja, how do you think this hospital will be ours alone? Kar ki manta fa Familyn mu babba ne kuma kowa yana da gado idan har Kaka akace ya mutu, sannan taya kike tunanin sunan Ya Baffa zai taimaka mana don samun Asibitin nan?”

Hajja Fatu smiled and said, “Hmm, I know what I am thinking. Please keep your eyes peeled. Insha’Allah sai mahaifin ku ya gaji asibitin nan, sai mun fi kowa fice a cikin asibitin nan, sannan sunan Baffa da na saka don ina so ne nan gaba koda bayan ran Kaka ya zamana shi ke juya Hospital ɗin, ma’ana kowa yayi tunanin sunan ɗana ne sannan a manta da kakan ku, Ni a ganina hakan zai yi sauƙin zama namu”.

Shiru Shakira tayi tana kallon ta sai kuma ta kwashe da dariya

Hajja Fatu dake faman kallon ta baki hangame tace, “Ke ban son iskanci! Why are you laughing like that?”

Wlh Hajja you laughed at me, wai taya ma kike tunanin Jika zai mallaki Hospital ɗin Kaka idan har don kin saka sunan sa? Bayan kin san da cewa ABBU ma sunan Kakan yaci, to ki faɗa min da ɗa da jika wanne mutane za su yi tunanin Hospital nashi ne?”

“Hmm ai fata nake yi sannan cewa nayi ina so kowa ya ɗauka cewa Al’ameen ɗina ne aka saka, kin ga Ni da Abban ku da ke da Baffa duk muna aiki a cikin asibitin, don haka nake so nan gaba asibitin ya zamto na mu, ke dai kawai ki mayar da hankalin ki da zaran akace kun soma aiki, duk abinda baki fahimta ba kizo waje na ki sanar dani kinji?”

Gyaɗa kanta Shakira tayi tana kallon uwar nata

“Now call me Baffa and we will talk to him.”

“Ok”.

Tashi Shakira tayi ta nufi corridor’n da zai sada ta da ɗakin Yayan nata.

*****
The next morning gidan Doctor Al’ameen sosai ya cika da mutane ƴan uwa, Hajiya Ikram da Hajiya LAILA har sun iso da iyalan su, haka ma su Aunty Zainab da Aunty Zulaiha, nan da nan gidan ya rincaɓe da hayaniya sai shirye-shiryen abubuwan da za’a yi suke yi.

…….. ……. ……. ……. ….

Baƙar Mota ce ta sanyo kai cikin ƙaton gidan da ya tsaru iya tsaruwa, kai da gani kasan mamallakin gidan ba ƙaramin hamshaƙin me kuɗi bane, sosai gidan yake da girma da yalwa Two upstairs ne, idan ka shiga haraban gidan yana da yalwa sosai wanda aƙalla zai cinye motoci kusan ashirin, sai kuma Part ɗin masu aiki da akayi daban, da akwai Garden a ta bayan gidan tare da abubuwan more rayuwa, the home of Doctor Al’ameen and his family.

Motar na packing wata mata da a ƙalla baza ta wuce 45years ba ta fito, sai kuma wata matashiyar budurwa da shekarun ta ba zai fi 25years ba itama ta fito, tana sanye ne da wani Abaya green colour Wanda a gefe da gefen rigan an sanya ratsin blue, sai kwalliyan Flower da akayi da stone masu matuƙar ƙyalƙyali daga sama har ƙasa, tayi Rolling kanta da ɗankwalin Abayan da ya kasance Blue, sai ta saka wani ɗan siririn farin glass Wanda ya ƙara fito da zallan kyawun ta da kwarjinin ta; tare da fito da manyan idanuwan ta da ƙwayan idanun suka kasance sky Green, kallo ɗaya idan kayi mata zaka san da cewa ba ƙaramar mugun haɗuwa tayi ba, fara ce sosai tana da kyawun fuska tare da ƙira me kyau, sai dai ta kasance siririya ce sosai kuma matsakaiciya, kana kallon ta kasan cewa za tayi yanga ne da yawa, don ko maganar ta da tafiyan ta idan tayi zaka san cewa Nature ɗinta ne hakan

Matar kallon drever’n da ya fito cikin motan tayi tace, “Ali where are you doing now?”

“I will go to the hospital because Alhaji said, ‘If I drop you off, he will sent me.'”Ali said respectfully.

Gyaɗa kanta tayi kana tace, “ok go, idan ka dawo I’ll sent you later”.

“To Hajiya”.

Daga haka juyawa tayi ta nufi cikin gidan, Matashiyar yarinyan itama tabi bayan ta. koda suka shiga ciki Direct Part ɗin su suka nufa, lokacin da suka shiga cikin ɗan madaidaicin parlour’n su da sallama a bakin su

Fadila ce zaune tana kallo ta’amsa musu

“Welcome Aunty” Fadilan saying

“Yauwa Fadila, ke kaɗai ce zaune?” Aunty Amarya tace hakan cike da fara’a tana kallon ta

Fadila ta bata amsa da “Eh su Umma na General parlour”.

“Ok mu ma ai bamu shiga cikin gidan ba nan muka taho, bari in shiga ɗaki in yaso sai in shiga can mu gaisa”.

“Toh aunty”.

Wuce wa ɗakin ta Aunty Amarya tayi

ita dama tuni Ɗahira ta wuce tasu ɗakin wanda ya kasance tasu tare da Fadila, tana shiga ta’ajiye Jakan dake hannun ta ta zauna gefen gadon ta, zare ɗankwalin da tayi Rolling a kanta tayi ta’ajiye tana bin gadon ta kwanta, kanta na kallon sama yayin da ta ƙure Cilling ɗin ɗakin da kallo, ta ɗan jima ahaka kafin ta sauke ajiyan zuciya tana lumshe kyawawan idanuwan ta, sai kuma ta buɗe ta tashi zaune tana zare Glass ɗin idanun ta ta miƙe ta nufi gaban Looking glass ta buɗe Locker ta’adana, darect Sif ɗin kayan ta tanufa ta ciro wasu riga da wando na Pakistan Milk and Red colour ta zube su saman gado, kayan jikin ta ta soma cire wa kafin ta ɗaura towel ajikin ta tashige toilet, wanka tayi ta ɗauro alwala ta fito, sai da ta shafa Lotions ajikin ta kafin ta saka kayan ta ɗaura Hijab tayi sallan asar da ta wuce su tun a hanya, bayan ta gama ne ta nufi wajen Looking glass ta zauna tana kallon kanta a madubi, tagumi ta zuba still tana ci gaba da kallon kanta

Fadila ce ta shigo ɗakin idanunta ya sauka akanta, sai ta taɓe baki tana ƙarisawa wajen ta tace, “Are you all right?”

Sai a lokacin Ɗahira ta ɗago kanta tana kallon ta, sai kuma takau da kan tare da faɗin “me kika gani?”

Fadila batace komi ba ta juya ta tafi, dama wayan ta tazo ɗauka, tana ɗauka ta fice a ɗakin, wannan shi ne halin su su duk ka biyun basu cika kula juna ba duk da duk kan su suna da ƙyaliya, But kasancewar Iyayen su suna kishi shiyasaka su ma suke taya su a junan su, ga dai shi ɗaki ɗaya suke kwana amma sai su wuni su hantse ba wacce zata kula ƴar uwanta, ba me shiga harkar ɗaya sai sun ga dama, ita dama Ɗahira ƴar ba ruwanta ne, bata cika shiga shirgin da ba nata ba, bata da son hayaniya amma tana da fara’a da kirki, komi tana yin abinta ne cikin class, sai dai alokaci ɗaya baza ka taɓa fahimtar halin ta ba sai ka zauna da ita, Fadila ma haka sai dai wani lokacin tana da yawan wulaƙanci a ɗabi’a, domin miskilancin ta yayi yawa don in bata ga dama ba ko kai uban waye baza ta kula ka ba sai taga dama.

Ɗahira cire tagumin tayi ta soma shafe Baby face ɗin ta da kayan makeup, ita gwanar son gayu ne duk sanda zaka ganta bata rabo da kwalliya, Light makeup tayi wanda ya ɗau fuskarta sosai ya ƙara fito da zallan kyawunta, ba maganar wasa ba Ɗahira tana ɗaya daga cikin kyawawan gidan, duk a cikin ƴan matan gidan zan iya cewa tafi su kyau duk da suna matuƙar kama, sai dai ita yanayinta da komi nata ya banbanta da nasu

Buɗe Lockern tayi ta ciro Glass ɗin ta tasanya Wanda ya zame mata ɗabi’a ko yaushe idan zaka ganta tana tare dashi, sai ta miƙe ta nufi gaban gadon ta taɗau wayan ta ƙirar IPhone 11+, takalmin ta kawai ta sanya ta fito batare da ta yafa komi ajikin ta ba baya ga ɗankwali da ta sanya ta rufe tulin gashinta, tana fitowa parlor ta hangi Fadila zaune har yanzu, sai dai wannan lokacin wayan ta take dubawa, ɗakin Mahaifiyar ta tawuce, tana shiga babu kowa hakan yasa ta fito ta doshi cikin gidan, sai da ta wuce wani dogon corridor kafin ta buɗe wani ƙofa ta shige, ahankali ta soma taka Step tana sauko wa sai gata cikin wani kyakkyawan parlour ƙarami, sai tabi ta wani ƙofan ta fito babban parlor’n gidan da ya kasance cike da mutane kowa sai harkan gaban sa yake yi, tana isa ta gaishe dasu sannan ta wuce wajen ƴan matan dake can gefe zaune, zama tayi gefen Shakira da Salma (ƴa ga Hajiya LAILA),

Shakira CE ta soma cewa, “Now I ask Aunty Amarya where are you? She told me kina Sashin ku ai”.

Ɗahira She smiled and said, “na tsaya wanka ne”.

Fiddausi da ta kasance ƙanwar Salma tace, “to ya Naga hannayen ki rabbana suna dukan cinya, ina tsaraban tamu?”.

Kallon ta Ɗahira tayi tace, “What are you eating na baka na zuba? Let me rest for a while, sai ki zo ki taya ni kwance jakan”.

Gaba ɗaya wajen su kayi dariya ban da Yusra dake faman latsa wayan ta ko ɗago kai bata yi ba

Shakira tace, “kin ji ƙyale wannan yarinyan bata da hankali, ke da akaje Duba marar lafiya kike zancen tsaraba?”

Ɗage gira Fiddausi tayi tace, “to kuma akace idan anje baza’a yi tsaraba ba? Nasan da cewa waɗannan tsofaffin baza su barta haka ba sai sun haɗo ta da abin lasawa”.

Shamsiyya (ƴa ga Hajiya Ikram) tace, “ƙwarai kuwa Fido sai dai idan mu baza’a bamu ba, don naga tunda ta shigo Shakira take ƙifƙifta mata idanu”.

Salati Shakira ta saki tana rufe bakin ta tare da zaro idanu, sai suka saki dariya suna shewa, wasu suce “eh su ma sun gani” wasu kuma suce “kai Shamsiyya banda ƙarya”.

Dogon tsaki Yusra taja ta miƙe ta wuce abin ta, yayinda duk kan su suka bi ta da idanu kana Salma tace, “Oh, that juju girl, what’s wrong with her?”

Dawo da idanun ta Ɗahira tayi gare su tana murmusawa tace, “Ni kun ga tafiya na bari inje in miƙa gaisuwata ga Kaka tunda naga ban ganshi anan ba”.

Tafa hannu Fiddausi tayi tace, “ai Kaka yau sai dai yayi haƙuri mun hana sa fitowa, cewa yayi bazai iya da surutun mu ba ya shige ciki ya kwanta”.

Tashi Ɗahira tayi tana faɗin “ai gwara haka kar ku ƙara masa damuwa”.

Daga haka ta wuce batare da ta kula su da sukayi mata caaa ba.
[5/21, 3:29 PM] Oummu Ɗahirah: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTORS*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER’S ASSO📖*
”’®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓”’

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA’S FAMILY*_

*NATSUWA A SALLAH*
_Sallah babbar matsala ce. Ganawa ce tsakanin Bawa da mahaliccin sa, Ubangiji maɗaukakin sarki. Saboda haka ana buƙatar cikakkiyar natsuwa, a tattara hankali wuri ɗaya domin wannan ganawa ta musamman._
_A cikin ayoyi biyun farko na suratul Mu’uminun ana faɗa mana cewa:_
_”Lalle ne, muminai sun sami babban rabo, wanɗanda suke a cikin sallar su masu tawali’u ne.”_
_Watau, Muminai wanɗanda idan sun tsaya yin Sallah sai gaɓoɓin su da zukatan su su natsu, babu wani abu mai shagaltar da su daga ambaton zatin Allah maɗaukakin sarki, to, irin su suke rabban ta. Natsuwa cikin sallah da ƙasƙan da kai ga Allah su ne alamun imani na gaskiya da Tauhidi tsantsa, don kuwa ko yaushe bawa yayi kusa da Ubangijin sa sai ya haɗa jin tsoron sa, musamman ma dai a sallah inda yake ganawa da shi, yake tunawa da girman sa._

.

*EPISODE Three*

A hankali ta sanya hannun ta ta soma jan gemun sa

Hakan yasaka ya buɗe idanuwan sa ya sauke a kan ta, murmushi yayi yana kallon ta yace, “Ni dama nasan babu wanda zai min haka sai ke, When did you come back?”

Murmusawa tayi tana janye hannun ta tace, “yanzu babu daɗewa”.

Tashi zaune yayi yana faɗin “To ya me jikin da fatan ya samu sauƙi?”

Sai da ta dawo kusa dashi kana tace, “Alhmadulillah Kakus suna gaishe ku kowa da kowa”.

“Mun gode muna amsawa”.

“My Kakus miss you so much”.

Murmushi Kaka yayi yana ɗaura hannun sa a kan ta yace, “nima haka Matata, You have left me alone I miss you, kin bar ni da waɗannan yaran mara su kunya masu ido a tsakar ka ko hiran basu taya ni”.

Dariyan ta me kyau ta saki tana jingina kanta jikin Kakan tace, “Kakana kenan! don’t worry, I’ll be back. hira har sai ka gaji daji, akwai labarin ma da na samo maka”.

“Well I hear you tell me”.

Ƙofar da aka turo ne ya sanya Ɗahira rufe bakin ta without saying a word. Big Dady ne tare da Abbu suka shigo da sallama, amsa musu su kayi yayinda Ɗahira ta tashi da sauri ta nufi Mahaifin nata ta rungume shi tana faɗin

“Abbu na”.

Murmushi yayi yana shafo kanta yace, “to ya kin dawo ko zaki fara?”

Dariya tayi tace, “I’m really missing you, Abbu.”

Sai kuma ta sake shi, Then she hugging Big Daddy and said, “Daddy, I’m the only one.”

Shafo kanta yayi shima yana smiled and said, “my daughter when did you come back?”

“Now Dady”.

“To ya me jikin yaji sauƙi dai ko?”

Gyaɗa masa kai tayi tana faɗin “Alhmadulillah”.

Big Dady yace, “madalla haka ake so”.

Sannan ya juya yana kallon Kaka yace, “Dad, we’re here to talk about new products da za’a shigo dasu.”

Kaka yace, “to shikenan”.

Abbu da ya samu wuri ya zauna yace, “Mamana bamu wuri za muyi magana”.

Big Dady yace, “a’a barta kawai ta zauna”.

Murmushi Ɗahira tayi tana kallon Big Dad tace, “bari dai inje in dawo Dady, because I have some things to do”.

“Well shikenan Daughter”.

Daga nan fita tayi ta rufo musu ƙofa, She did not go back to the General Parlor. Sai tabi ta wani Corridor da zai sada ta da Part ɗin su, tana cikin tafiya ta hangi Baffa ya taho shima ɗin, yayi shigan nan nasa na ɗamewa irin shigan wizaye, kansa babu hula sai kwantaccen gashin kansa da ya sha askin zamani, sosai yayi masa kyau ya sake fito da kyawun sa ainun, hannun sa Sigari ne yake sha, shima yana hango ta ya matse Sigarin a hannun sa ya kashe kana ya tura shi cikin aljihu

Murmushi ya saki lokacin da ya’iso wajen ta yana faɗin “Oyoyo My Lovely sister”. Ya nufe ta da ninyan Hugging ɗin ta

Tayi saurin ja da baya tana murmusawa tace, “Oyoyo My Lovely Brother”.

Sai ya ɓata fuska and looked at her and said, “Why don’t you let me hug you?”

Still tana murmusawa tace, “ka san ba na so fa”.

Ɗage kafaɗa yayi yana cewa, “ok to ya Hanya? kin dawo ko ki neme Ni, kinsan nayi missing ɗin ki sosai”.

Ɗan huro hanci tayi tana kallon sa, sai kuma ta ɓata fuska tace, “Ya Baffa kamar warin Sigari nake ji?”

Waro idanu yayi yace, “Really?”

Sai ta harare sa tana cewa, “Where is our promise?”

He smiled and touched his forehead and said, “Sorry Sis ban saɓa miki ba ai”.

“I don’t agree, ga shi kana bani haƙuri”.

“Da gaske my Sister na Dena sha, sai dai idan hancin ki ya juyo miki wani warin daban”.

Kallon sa kawai take yi, sai kuma tace, “ok I Believe You”.

He smiled and said, “so where are you now?”

“I’ll go back to our Part”.

“Mu je ki taya ni hira mana”.

Girgiza kanta tayi tace, “No grave until tomorrow, now I have something to do.”

Baffa haɗe hannayen sa yayi yana kallon ta yace, “Please Mana my sis”.

Ɗahira ɗan kawar da kanta tayi

ya sake cewa, “Please kinji?”

“Ok Muje”.

Murmushi ya sakar mata yace, “yauwa ko ke fa”.

Itama murmushin tayi tabi bayan sa suka jera suka nufi cikin gidan.

Suna shiga cikin ɗakin sa tabi ɗakin da kallo tana yamutsa fuska, sai kuma ta kalle sa tace, “Wai Ya Baffa kwana nawa ɗakin nan be ga shara ba?”

Shafo kansa yayi yana kallon ta shima yace, “wlh kin san ban da lokaci kuma ga shi ke kinje anguwa, and na saka Shakira ita kuma kin san halin ta ba wani iyawa tayi ba”

Gyaɗa kanta tayi kana tace, “ok bari in gyara maka yanzu ko”.

“Ok my sis let me help you”.

Zuwa tayi ta soma kakkaɓe gadon yana tayata suna hira, bayan sun gama suka share ɗakin tare da wanke Toilet ɗin ɗakin, ita tayi Moping shi kuma ya koma kan sofa ya zauna yana latsa wayan sa

Bayan ta gama ta dawo kan hannun kujeran ta zauna tana kallon sa tace, “Yaya na gama maka bari in wuce sashin mu kar Mama taji ni shiru”.

Ok my sister, Thank you so much, that’s why I love you so much coz you are so kind”.

She smiled and said, “Yayana kenan! I love you more than anyone else in this house. Kaima kana da kirki.”

Tashi tayi tana nufan saman drower ta ɗau wayan ta tadawo tana kallon sa da shima ya kafe ta da nashi idanun, murmushi tayi masa tace, “Na tafi Yaya”.

Miƙewa yayi ya rako ta har bakin ƙofa kana ya koma ciki yana zama saman kujera tare da aza kansa ya kwantar kan hannun yana lumshe idanun sa, murmushi kawai yake saki yana tuna ɗan kyakykyawar fuskarta, sosai yake matuƙar son ƙanwar tasa, kuma so na aure, burin sa kawai a rayuwa yaga ranan da zai mallaki Ɗahira a matsayin matar sa domin tayi masa tako ina, sai dai har yanzu ya kasa samun ƙwarin gwiwar tunkaran ta yace mata yana son ta

Ɗahira tana da wani irin kwarjini da zai yi wuya namiji ya tunkare ta da zancen so, shiyasaka tun tasowan ta bata taɓa yin saurayi ba duk da tana da farin jini sosai na mutane, a lokacin da suka je ABU Zaria karatun su na Degree yawancin Friends ɗin ta maza ne, kuma duk acikin su babu wanda ba so yake kawo sa wajenta ba but basu iya gaya mata.

Shima haka Baffa ya daɗe yana ƙaunar ta yana dakon son ta Amma har yanzu be iya sanar da ita ba, kuma duk abinda tace “yayi ko ya bari” yana bari, shi ɗin ma’abocin shan Sigari ne don wani lokacin har Alcohol yake korawa, amma babu wanda ya sani a gidan sai ita kaɗai kasancewar tana yawan zuwa ɗakin sa koda ba ya nan, wani lokacin sai tazo ta kwanta tayi barcin ta, yawan kusancin su dashi ne ya saka tasan wannan sirrin nasa, kuma tun sanda tace ya dena sha ya dena, sai dai har yanzu Sigari ne be dena gaba ɗaya ba, amma idan har zata gani zai yi ƙoƙarin ɓoyewa.

*WASHE GARI*

Ranan ne ya kasance ranan Walima, kowa idan ka gani agidan cikin farin ciki yake, sosai gidan ya sake cika sai hada-hada ake yi, har mutanen Maiduguri tushen su kenan duk sun hallaro, duk girman gidan nan sai da aka cika sa da mutane

Ƙarfe 02:00pm. Aka soma tafiya *AL’AMEEN FAMILY HOSPITAL* kasancewar acan ne za’ayi taron, haka motoci manya-manya suke ta jidan mutane suna kai su.

 

 

 

_Kar ku manta da_
*Share*
*Comments*
*Vote*
*Like.*
[5/21, 3:30 PM] Oummu Ɗahirah: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTORS*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER’S ASSO📖*
”’®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓”’

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA’S FAMILY*_

*NATSUWA A SALLAH*
_Manzon Allah mai tsira da aminci, ya ce, “sallah ba kome ba ce illa miƙa wuya da tawali’u…” Kuma ya ƙara da cewa, “Bawa bai samun ladan sallar sa sai gwargwadon abinda ya hankalta daga sallar.” Watau, gwargwadon natsuwar mutum cikin sallah gwargwadon darajar da yake samu gun Allah. Don haka ne ma ma’aikin Allah ya ce, “Allah ba ya juya wa Bawa baya yana cikin sallah matuƙar bai waiwaya ba; idan ya waiwaya kuwa, sai Allah ya bijire masa.”_
_Babu abin da yake kawo waiwayo cikin sallah kuwa sai gafalar Bawa da muƙamin Ubangijin sa, watau ya zama tamkar wanda ya tsaya yana ganawa da Ubangijin sa alhali zuciyar sa tana shagale da wani abin dabam. A kan wannan matsala ne Allah yake ce wa Manzon sa, da al’ummar sa ma, a cikin suratul A’ARAF aya ta 205:_
_”Kada ka kasance daga gafalallu.”_
_In muka lura sai mu ga cewa ta ya ya kuwa gafalalle zai iya tunawa da muƙamin Ubangijin sa yana cikin wannan hali na rashin kula har wani abin tsoro ya auku? Bugu da ƙari, daman can ga shi Allah ya yi umarni a cikin suratul Ɗ.H., aya ta 14 da cewa:_
_”Kuma ka tsayar da Sallah domin tuna Ni”._
_In mutum ya Yi haka, ana fata ya rabban ta._
_Allah yasa mu dace._

.

*EPISODE four*

Babban haraban asibitin cike yake da mutane bila adadin, mutane ne kamar tsaki kama daga yara manya masu kuɗi da manyan likitoci duk an gayyace su, har ta da gwamna Malam Nasiru El Rufa’i sai da aka gayyace shi wajen, komi ana yinsa ne akan tsari gunun sha’awa

Ɗahira, Shakira, Yusra da Fadila can na hango su wajen zaman su daban, sosai su kayi kyau cikin shigan su na material fari ƙal da akayi masa ɗige-ɗigen Coffee colour, ɗinkin doguwan riga akayi musu fitted, sai suka yane kan su da Goldeen Veil tare da sanya Hill shoes shima Golden, sosai su kayi matuƙar kyau kamar ka sace su ka gudu sai faman haskawa suke yi kamar taurari

Nan akayi ta gabatar da komi cikin girma da arziƙi, daga ƙarshe aka gabatar dasu a matsiyin waɗanda ake taya murna tare da sauran sabbin ma’aikata da za’a ɗiba.

Wata kyakykyawar Farar mota ce ta shigo haraban asibitin, a hankali motar take tafiya har zuwa inda sauran motocin suke fake, tsawon mintuna 5 kafin aka buɗe motan ya zuro kyawawan ƙafafun sa kana ya fito a hankali yana rufe motan, kyakykyawar saurayi ne da aƙalla bazai wuce 32yrs ba, fari ne tarrr kamar kalatsa shi jini ya fito don har wani ɗaukan idanu yake yi, yana sanye da Milk ɗin riga me gajeren hannu da ya matse sa sosai, sai Blue Jeans tare da sanya Combat a ƙafafun sa shima blue, yana da yalwan gashin kai kwantacce baƙi siɗik tare da ɗan siririn sajen sa, Kallo ɗaya idan kayi wa Guy ɗin zaka tabbatar da ya haɗu ne tako ina, *USMAN NOOR AL’AMEEN* kenan, *(The Younger Doctor)* yaro kyakykyawa me Izza da Son nuna shi wani ne, ma’aboci Son gayu da son hutu

A hankali ya taka ya soma tafiya cike da taƙama ya nufi inda su Big Dady suke.

Har aka gama taron sannan kowa ya soma tafiya gida, sai yamma duk yawancin ƴan uwa suka soma watsewa sai gidan ya rage daga ƴaƴan Kaka sai jikokin shi suka rage waɗanda basu tafi ba, su ma ɗin a gobe duk za su watse su tafi

Washe gari ƙarfe 05:00pm. Na Yamma gaba ɗaya a halin gidan sun hallara a babban parlour bisa umarnin Kaka

Ɗahira ce tafito daga Part ɗin su don ita bata riga ta tafi ba, tana sanye da doguwar rigan atamfa kalan ja da ratsin Milk da ruwan ƙwai, rigan iyakan ta ƙwaurin ƙafafuwan ta kuma sosai tayi mata kyau ta sake fito da tsantsan kyawunta da kwarjinin ta, sai tayi Rolling da ɗan ƙaramin Veil da iyakan sa kafaɗun ta, Slippers ne a ƙafanta tana tafiya tana latsa waya, hira take yi da freinds ɗinta na Facebook sai faman doka murmushi take yi, gab da ta iso ƙofan da zata sada ta da General parlour taji tayi karo da mutum wanda hakan yasaka wayan ta ya zame ya faɗi ƙasa, a hankali ta ɗago kanta tana kallon sa

haka zalika shima ɗin dai-dai da sanda ya sauke nashi idanun cikin ƙwayan idanuwanta da yafi tsana cikin rayuwan sa

kallon sa kawai take yi babu ko ƙyafta idon

While shi kuma ya ɗaure fuska tamau yaja jikin sa ya wuce, gab da zai buɗe ƙofa ya tsinkayi zazzaƙan muryan ta tana cewa

“Ba ka ganin kayar min da waya ne?”

Cak ya tsaya yana juyowa ya kalle ta da tsananin mamaki da ya nuna a face ɗin sa, ita kuwa a lokacin kallon wayan nata da ya fashe take yi cike da tsananin baƙin ciki sannan ta ɗago kyawawan idanun ta tana kallon sa itama fuskarta a ɗaure

A hankali ya tako ya’iso gaban ta still yana ci gaba da kallon ta, duk da ya daɗe be ganta ba kuma tayi masa girma ainun but be yi tunanin cewa ta kai matsayin da har za tayi masa irin wannan maganar ba, shiru yayi yana ƙare mata kallo yayinda itama ɗin shi take kallo batare da ko alaman tsoro ya nuna a fuskarta ba, abinda ya ƙara ba shi matuƙar mamaki kenan, domin yasan ada babu wanda tafi tsoro sama dashi, idan har zata gan shi ko za taji sunan sa tsoro ne da fargaba suke kawo mata cafka, ko kaɗan bata haɗa hanya dashi bare magana ya haɗa su, duk inda akwai shi to ta haramta wa kanta wurin har sanda zai bar wajen

Kuma hakan ya samo asali ne tun sanda ta tashi da wayon ta take matuƙar tsoron sa, ba don komi ba sai tsananin azaban da yake gana mata da tsanar da yake nuna mata afili ko a ɓoye, shi kuwa tun sanda aka haife ta ya haɗa idanu da ita shikenan yaji ya matuƙar tsanar ta, ba don komi ba sai don ƙwayar idanun ta da ya kalla, sabida idan har zai kalle ta sai yaji faɗuwar gaba me tsanani tare da tsoro wanda hakan ne ya saka mishi muguwan tsanar ta cikin ran sa, sosai cikin ƙwayar idanun ta da suka kasance sky green suke bashi tsoro da fargaba, hakan yasa tun tana ƙarama ko ɗaukan ta ba ya yi, da zaran ya ganta duka ne abinda ke haɗa shi da ita, har zuwa kuwa girman ta da ta gane shi ɗin mugu ne, koda laifi sukayi ƴan gidan gaba ɗaya, to ita yake kamawa ya fanshe kaf dukan da zai yi musu akan ta, ko agaban waye babu wanda zai iya hana sa, kuma koda an hana sa sai ya san yanda yayi ya haɗu da ita ya gana mata azaba, Ɗahira ta tashi cikin tsoron sa matuƙa wanda ya haddasa mata tsanar sa fiye da wanda yake mata, kwata-kwata bata ƙaunar sa bata ƙaunar ganin sa koda jin sunan sa ne, ta saka wa kanta shi ɗin maƙiyin ta ne wanda babu wadda tafi tsana a duniya sama dashi

Wajen shekara 9-10years kenan babu shi a ƙasan, yana can ƙasar Turkey yana aiki acan, tun sanda ya tafi karatu ya zauna can sai dai yazo gaishe su, Ɗahira ta dena jin tsoron sa ne don kawai daɗewan da tayi ba ta ganin shi, and sai kuma girma da yazo mata, yanzu baza ta taɓa juran abinda yayi mata a baya ba, domin ita tana ganin ta wuce matsayin da zata zauna wani banza wanda ba iyayen ta ba ya duke ta bare har taji tsoron sa.

Sauke kansa yayi kan wayan yana kallo, sai kuma ya mayar da idanun sa kanta yana sake ɗaure fuska ya ɗaga ƙafan sa ɗaya ya ɗaura saman wayan ya soma murje ta da ƙaton takalmin sa da ya kasance tamkar irin na sojoji, babu abinda ake ji sai sautin ƙaran fashewan wayan

Ita kuwa Ɗahira sauke idanun ta kan ƙafan sa tayi tana kallon wayan yayinda taji hawaye sun ciko mata idanu sabida tsananin baƙin ciki da yazo mata iya wuya, still ɗago kanta tayi tana kallon sa cike da zallan tsana da ya nuna a cikin ƙwayan idanun nata

shi kuma hawayen da ya gani a idanun nata shi ya saka shi jin wani farin ciki tare da sanyi a ransa, magana ce a bakin sa yake son faɗa mata amma girman kai da Izza sun hana sa buɗe bakin, illa juyawa da yayi ya nufi ƙofa ya buɗe ya shige

Ƙaran rufe ƙofan ne ya saka ta ƙyafta idanun ta wanda hakan ne yasa hawayen ta daman zubowa suka sauka kan kuncin ta, ahankali ta sake mayar da idanun ta kan wayanta da ya gama murƙushe ta duk screan ɗin ya farfashe babu kyan gani, wasu zafafan hawayen ne suka soma sintiri a face ɗin ta, tayi saurin saka hannu ta soma sharewa domin baza ta bama kanta daman nuna raunin ta kan shi ba, dole ne ta nuna masa yanzu ba irin da bane, dole ta nuna masa ba ta tsoron sa, kuma duk abinda yayi mata BASHI ne ya ɗauka dole sai ya biya, don haka ɗaukan wayan tayi ta nufi ciki itama da sauri.

_To fa nan ake yinta, bari muga me zai faru?_

_kar ku manta ku suburbuɗo min Comments ta hakan ne zai bani daman ƙara muku yawan Page._

Plz
*Share and Vote.*
[5/21, 3:30 PM] Oummu Ɗahirah: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTORS*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER’S ASSO📖*
”’®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓”’

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA’S FAMILY*_

.

*EPISODE Five*

Da shigan ta darect wajen Kaka ta nufa, ta sami waje kan hannun kujeran dake kusa da Wheel chair ɗin sa ta zauna tana sauke kai ƙasa

“Matata lafiya wa ya taɓa min ke?”

Abinda ya saka yayi mata tambayar ya santa idan har tazo wuri dole sai ta tsokane shi, ƙa’ida ne sai taja masa gemu kafin ta nemi wurin zama

Ɗago kanta tayi tana kallon sa sai kuma ta soma wurwurga idanun ta tana kallon mutanen wurin da duk suka nutsu suna kallon ta, a kan Usman dake zaune kusa da Abbun ta ta sauke idanu, yayin da shi kuwa wayan sa yake latsawa ko sanin Allah yayi ruwanta be yi ba

“Tell me my wife. I can’t calm down idan ban san abin da ke damun ki ba?”

Dawo da idanun ta kan Kaka tayi cike da marairaice fuska tace, “Kaka Ya Usman ne ya fasa min waya, kuma ya saka ƙafa ya tattaka shi da gangar”.

Kaka salati yayi yana kallon wayan dake hannun ta kana ya mayar da idanun sa kan Usman da har yanzu yaƙi ya ɗago kansa duk da yana jin abinda ake yi, shi har a lakocin mamakin yarinyan yake yi ainun, “yaushe har ta samu ƙwarin gwiwar da har zata kawo ƙarar sa? Lallai yarinyan nan dole ya koya mata hankali”.

“Fodio, why did you break my wife’s phone?”

Shiru yayi batare da ya ɗago kan sa ba, kuma be dena latsa wayan ba

“Kai ba magana ake maka ba? Are you crazy? Uban meyasa ka fasa mata waya? Ka dawo kenan zaka soma takura mata ko?” Big Dady yayi maganar a zafafe yana kallon sa

Sai a lokacin ne Usman ya ɗago kai fuskar nan a ɗaure yana kallon su, sai dai be iya cewa komi ba

Abba yace, “miƙo wayan mu gani uwata”.

Miƙa masa wayan tayi, ya’amsa yana juyawa sai ya ɗago yana kallon ta yace, “Agarin ya yafasa miki wayan?”

“Mun yi karo ne shine ya faɗi, da nayi masa magana shi ne ya dawo ya tattaka min da takalmin sa”.

“It’s your fault, why did you talk to him then? Stop following her shit please”. Abbu yayi maganar yana amsan wayan daga hannun Abba and put it aside

Big Dady said, “why doesn’t she talk and break her phone?”

Sai kuma ya mayar da kallon sa ga Usman ɗin yace, “Make sure you buy her her phone and pay for it, idan ba haka ba zan mummunan saɓa maka kana jina ko?”

Gyaɗa kan sa kawai Usman yayi yana kallon Ɗahira da kanta ke ƙasa, kawai tunani yake yi a ransa abinda zai yi mata idan har ta shigo hannun sa

Kaka ne yace, “ya isa haka Lawal (Noor), karka ɗau abinda zafi haka mana, yanzu mu mayar da hankali kan abinda ya tara mu. Alhmadulillah and Allah show us this time to see my grandchildren finish their studies and become doctors now, don haka na tara ku in sanar muku da Albishir da na tanadar muku”.

Murmushi yayi yana kallon su ɗaya bayan ɗaya kana yaci gaba da cewa, “Zuwa nan da Sunday motocin ku da na siya muku za su iso sai kowa ya zaɓi wanda yake so, wannan shi ne kyauta na a gare ku, sannan ina jan hankalin ku ku mayar da hankali wajen aikin ku, abinda ya kai ku shi za kuyi ba na son wasa,
May God help you all. May God bless you.”

Duk ka parlour’n suka amsa da ameen ban da Usman da har yanzu latsa wayan sa yake yi, nan ɗaya bayan ɗaya suka yi ta mishi godiya kana ya kalli Usman yace

“Kai kuma Fodio, the opportunity I have given you is enough. dole ne ka dawo Nigeria kaci gaba da aiki a asibitin mu, domin baza mu zira idanu ace kana can kana ma Nasara aiki suna ƙaruwa mu nan ka bar mu haka ba”.

Usman da ya ɗago kansa yana kallon Kaka, a karo na farko yace, “wai Kaka meyasaka kake son takura min ne? I don’t want to work here. I want to..”

Be dire maganar ba Big Dady ya daka masa tsawa, hakan yasaka shi yin shiru yana kawar da kai still fuskan sa ba walwala

“Umarni ake baka ba shawara ba ka ajiye aiki ka dawo nan kaci gaba, karka sake mu ƙara ja’inja da kai”. Big Dady ya faɗi maganar da kakkausar murya

Murmushi Kaka yayi yace, “ka bar shi nace Lawal; ba na son kana nuna masa zafi, ai ba cewa yayi bazai dawo ba, abi shi a sannu, kowa zai iya tafiya. idan kuma da me magana ko ƙorafi akan wani abu sai yayi magana”.

Kafin Kaka ya rufe baki Usman yayi saurin tashi ya fice, haka sauran ma su kayi ta tatashi suna ficewa ya rage daga Kaka sai su Big Dady

*****

Hajja Fatu ce ta shigo parlour’n Hajiya da sallama

Hajiya wacce ke zaune a parlour ta’amsa mata sallaman sannan tayi mata maraba

Zama Hajja Fatu tayi tana kallon Hajiya da murmushi a face ɗin ta tace, “Oh ashe haka abu ya faru? Na zo miki jajen abinda Ɗahira tayi wa Usman ne, gaskiya bata kyauta ba”.

Hajiya tace, “Haka ne. amma shima da laifin sa ai, da be taka mata wayan ba baza ta kawo ƙarar sa ba”.

Ɗan taɓe baki Hajja Fatu tayi tace, “eh Haka ne kamar yanda ki kace, amma abinda tayi ai be kamata ba, wannan ai kamar tana so ta haɗa Ɗa da uba ne, ko ba kya ganin yanda Mahaifin sa ya nuna fushi dashi? Kuma da ba haka yake nuna masa ba, don Ni kai na shaida ce wajen ƙaunar da yake masa, amma a kan ta ya rufe idanu ya suburbuɗa masa faɗa a gaban ƙannin sa, wannan abun ba yi bane, idan ma uwarta take zugo ta ai zamu gani”.

Shiru Hajiya tayi tana sauraron maganganun Hajja Fatu, kuma da alamun sosai zancen yake shigan ta duba da yanda fuskarta ta sauya, domin abinda aka yi wa ɗan nata dama be mata daɗi ba, amma kuma maganganun Hajja ya sake saka ta taji haushi matuƙa

Ita kuwa Hajja Fatu ganin haka ya saka ta sakin wani shu’umin murmushi tana cewa, “Ai sai haƙuri amma dai na san yarinyan nan yanzu hure mata kunne ake yi, ada ai ba ta yin haka duk kuwa da cewa yana dukan ta, amma yanzu tunda ana son haɗa sa da ubansa ai an koya mata yanda zata riƙa kawo ƙarar sa, kin ga hakan zai sa Mahaifin sa ya riƙa fushi dashi”.

Hajiya kallon Hajja Fatu tayi don da alamun kalaman nata sun gama ratsa ta sosai tace, “nima naga alamun haka Hajja, sai dai ko ma wa ya koya mata da duk abinda suke nufi da ɗana sai dai ya koma kan su, babu wanda ya’isa ya shiga tsakanin ɗana da mahaifin sa, dole ne ma in ja masa kunne babu ruwan sa da ita tun wuri ya fita harkan ta, ba na son abinda zai saka mu sami saɓani, domin akan ɗana babu abinda bazan iyaba, kowa ya san da cewa ina matuƙar ƙaunar sa; don zan iya yin komi akan sa”.

Ajiyan zuciya Hajja Fatu ta saki tana kallon Hajiyan da alamun nuna damuwa a fuskarta tace, “gaskiya ne Hajiya, gwara dai ayi wa tufkan hanci tun kafin magana tasha banban, Allah ya kyauta gaba to, Ni bari in tashi na tafi”.

“To shikenan Nagode sai nima na leƙo”. Cewar Hajiya da murmushi a fuskarta

Tashi Hajja tayi ta nufi ƙofa ta fice tare da barin Hajiya cikin tunani. Tana fita ta saki wani shu’umin murmushi fuskarta cike da farin ciki, dama abinda take so kenan kuma tana ganin da alamu tarkon ta ya fara kamawa, taku ɗaya zuwa biyu tayi ta tsaya tana juyowa ta kalli ƙofar parlour’n Hajiya, a fili ta furta

“Now the game has started. If I am Hajja Fatu, I will open the heart of everyone in the house. I will make everyone hate you, A’ishah. tare da ƴarkin da kika ƙwallafa rai a kan ta, zan maye gurbin zuciyar kowa da ƙauna ta a ran shi, zaki san kin shigo cikin Familyn da ba na ki ba, mu zuba dani dake..”

“Hajja ke da wace ce zaku zuba? Me tayi miki?”

Da sauri Hajja ta juyo tana kallon ta, wani irin bugawa zuciyar ta tayi, nan da nan tsoro da fargaba ya ɗarsu a cikin zuciyarta har bata san sanda ta fiddo idanu waje ba suna kallon kallo..

.

_Hhhh to Fans shin wa kuke tunanin wacce Hajja ta gani haka har ta sorata ainun?_

_karku manta da Comments, domin comments ɗin ku shi ke saka na ƙara yawan post._
[5/21, 3:31 PM] Oummu Ɗahirah: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTORS*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER’S ASSO📖*
”’®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓”’

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA’S FAMILY*_

*TUNATARWA*
”’Manzon Allah mai tsira da aminci, ya yi mana bayani a kan sallah da abin da Bawa yake iya samu. Cewa ya yi, “Yana yiwuwa mutum ya kawo sallah ga baki ɗayan ta amma a ba shi lada wadda ba ta wuce sudusin ta ko ushurin ta ba.” Abin da yasa haka kuwa shi ne rashin nutsuwa cikin sallah.
Allah yasa mu dace.”’

.

*EPISODE Six*

Murmushi Hajja Fatu ta ƙirƙiro cikin tsananin ruɗewa da son ɓoye halin da take ciki tace, “am..uhmm babu, auhm Ni da wata ƙawata ce da taci amana ta”. Taƙarishe maganar tana sake sakin murmushi

Ɗahira kuwa kallon ta kawai take yi, domin kuwa duk abinda ta faɗa ta riga taji, sai dai tayi tsananin mamaki da al’ajabin abinda Hajja Fatu take faɗa akan Mahaifiyar ta da ita kanta. ita ma ɗin nuna mata tayi kamar bata ji maganar nata ba illa sakin murmushi da tayi tace, “But Hajja, why don’t you forgive her? I don’t see the point in keeping a person in mind.”

Wani irin ajiyan zuciya Hajja Fatu ta saki jin cewa ta yarda da abinda ta faɗa mata, hakan na nufin bata ji maganar da tayi ba kenan, murmushi ta sake ƙirƙirowa tace, “ƴata baza ki gane zafin cin amana ba, amma tunda kin ce in yafe ai Ni me iya yafe mata ne, nima sai yanzu na gane hakan be da wani amfani muyi ta sa’insa akan abinda be kai ya kawo ba”.

Sai kuma ta sauya akalan maganar da tambayarta “ina zaki je kika yo nan?”

Ɗahira said, “I will reply to Mamana’s message,”

Gyaɗa kanta Hajja Fatu tayi tace, “ok”.

Sannan ta juya ta tafi batare da ta sake furta komi ba

Ɗahira kuwa bin bayan ta tayi da kallo har sanda ta ƙule wa ganin ta, maganganun Hajjan ne suka dawo mata

“What does that mean?” Tafaɗa aranta tana sake zurfafa a tunani

Tabbas ta san akwai abinda Hajja ke shiryawa akan Mahaifiyar ta, sai dai kuma duk yanda za’a yi baza ta taɓa bari taci nasara ba, tun farko dama tasan Hajja Fatu ba ta ƙaunar Mahaifiyar ta, Kasancewar ita A’isha wato Aunty Amarya Asalin ta ƴar Soba ce a ƙaramar hukuman Zaria, karatu ya kawo ta Kaduna tana zaune wajen auntyn ta, to anan ne Mijinta Al’ameen ya ganta har ya’aure ta, tun sanda aka kawo ta gidan Hajja Fatu ta nuna ba ta ƙaunarta kuma take son nuna ita ɗin bare ce acikin su, sabida alokacin ƙanwarta dama ta daɗe tana ƙaunar Al’ameen wato Abbu, to hakan ya saka ta ɗau alwashin sai ta fid da Aunty Amarya a cikin gidan ko ta halin ƙaƙa, don a cewarta tunda ƙanwarta bata same shi ba duk a dalilinta, to, itama sai ta rasa shi

Numfashi Ɗahira ta sauke tana ɗauke kanta daga kallon Hanyan da Hajja Fatu tabi, ko kaɗan baza ta so ta faɗa wa Mahaifiyarta wannan maganar ba, domin ta san hankalin ta zai tashi matuƙa, sai dai zata dage da taya ta da addu’a duk wani wanda ke binta da sharri ya koma masa

takawa tayi ta shige Parlour’n Hajiya da sallama

Hajiya da har yanzu take zaune tana tunanin maganar Hajja Fatu, ta ɗago kanta tana bin Ɗahira da kallo, fuska babu walwala ta’amsa mata sallaman

Ita kuwa Ɗahira ƙarisowa tayi ta zauna a kujera tana kallon Hajiya tace, “Hajiya sannu da hutawa”.

“Yauwa”. Hajiya ta’amsa ataƙaice tana sake tamke fuska

Sosai Ɗahira tayi mamakin halin da Hajiya ta nuna mata, domin ta san ta mace ce me fara’a, kuma suna ɗasawa da ita ainun, tayi mamaki da ganin sauyawar fuskarta amma kuma sai ta dangana hakan da ko wani abun ne ke damunta, don ko kaɗan bata yi tunanin abinda ya faru ɗazu ba

“Hajiya dama Mama ce tace inzo in amsar mata saƙo”.

Miƙe wa Hajiya tayi batare da ta tanka mata ba ta shige ɗaki, sai gata ta fito da leda ta miƙa mata

Amsa Ɗahira tayi cike da girmamawa ta tashi ta fice

Ita kuwa Hajiya rakata tayi da harara tana jan tsaki

Ɗahira da har ta fice sai da tajiyo sautin tsakin, hakan yasaka taja ta tsaya tana kallon ƙofar, nan take kuwa abinda ya faru ɗazu ya dawo mata kwanya “kenan Hajiya tana fushi da ita ne saboda abinda ya faru ɗazu?” Ta tambayi zuciyarta cike da mamaki, taɓe bakin ta kawai tayi tajuya tayi tafiyar ta, Part ɗin Hajja Fatu ta shige, babu kowa a parlour sai ta nufi ɗakin Shakira kanta tsaye, tana isa ta tura ƙofar ta shiga da sallama a bakin ta

Shakira dake zaune gaban mirror tana gyara kayan kwalliyan ta ta ɗago da kanta tana kallon ta, sai kuma ta saki murmushi tana cewa, “ƴan mata adon gari me aka kawo min ne?”

Ƙarisawa kusa da ita Ɗahira tayi tana jingina da bango tace, “a’a Ni babu abinda na kawo miki, amsa dai nazo yi, kin san yanzu wayata ta samu matsala shiyasa zaki haɗo min kan Littafaina in tafi dasu”.

Dariya Shakira tayi tace, “kai wlh Ƴanmata yau kin bala’in burge Ni, ashe zaki iya kai ƙaran Ya Usman? Shin wai ina tsoron da kike mishi ya tafi?”

Taɓe baki Ɗahira tayi kana tace, “ai dama ɗan hakin da ka raina wataran shi ke tsole maka ido, kema da kanki kin faɗa da ba yanzu ba, Ɗahiran Da; da na yanzu sun sha banban”.

Miƙe wa Shakira tayi tana sakin murmushi tace, “gaskiya ne ƴan mata, don yanzu ba lokacin Da damuke yara bane, yanzu mu ɗin DOCTORS ne manyan yara, kinga kuwa baza mu iya ɗaukan raini ba, wlh kin burge Ni amma Ni kam ba na tunanin zan iya fa”.

“Dama ai ke matsoraciya ce, Ni dai ɗauko min in tafi Mama jira na take yi”.

Drower Shakira ta buɗe ta soma kwaso mata Books ɗin tana cewa, “hmm baza ki gane bane, Ya Usman ya wuce gaban kwatance, wlh ko wacce mace idan har zata haɗu dashi sai dai ta kalle shi da idon soyayya amma ba faɗa ba, kwarjinin sa da kyawun sa tare da isa da izzar sa su kansu sun ishe ka, ina matuƙar shakkan Ya Usman kuma ba na son abinda zai haɗa ni dashi da har zai saka mu saka ƙafan wando ɗaya dashi, but ke kam nasan kashin ki ya bushe wlh don ba ƙyale ki zai yi ba, ya lafiyan Kura ma bare ace tayi hauka, uhmm ke dai kawai ki guji ranan haɗuwan ku”.

Ɗahira takowa tayi tazo gaban ta ta soma kwashe Littafan tana zubawa a leda, batare da tabi ta maganarta ba tace, “Ni kin ga tafiya na ba ni da lokacin ku daga ke har shi ɗin”.

Tajuya tayi ƙofa zata fice, dai-dai lokacin da Yusra ta turo ƙofan ta shigo suka kalli juna suka ɗauke kai sannan ko wacce ta wuce

ƙarisowa Yusra tayi kusa da Shakira dake zaune bakin gado; itama ta zauna gefen ta tana cewa, “wai ya maganar mu na zuwa shopping yaushe za mu je?”

Shakira tace, “ki bari a kawo mana Mota mana, kin ga sai muje aciki ko ya kika ce? Don Ni wlh bazan fita a tsohuwar mota ba, gwara muje muna tsole idanun Gayu”

Dariya Yusra tayi tana cewa, “shegiya inda ba’a ce za’a ba mu ba fa? ya za kiyi dole ki fita a ciki”.

“Uhm baza ki gane bane amma dai gwara mu bari sai ranan Sunday ɗin muje, kin san har gidan su Marcy za muje ranan wlh”.

Hannu Yusra ta bata suka kashe tana cewa, “gaskiya ne Tawan ai wlh yanzu ma kika tuna min da ita, ahh ai dole ne ma muje, kai wlh har kin sani na ƙosa ranan tazo, uhmm Allah ya kai mu har na hango irin wulaƙancin da zanyi”.

Sai suka kwashe da dariya suna sake tafawa

Shakira tace, “kin san yanzu muka gama hiran ki da mutumiyar taki?”

“Wace kenan?” Yusra ta tambaye ta cike da rashin fahimta

“Wace kika sani ban da Ɗahira, Ni na rasa meyasaka ba ta ƙaunar ki duk sanda zamu zauna sai tayi maganar ki, abun mamakin ma yanda tayi ta zagin Ya Usman anan wajen, uhmm duk wai akan waya”.

Ɗaure fuska Yusra tayi tace, “wlh yarinyan nan akwai ranan da zan cire mutunci mu goge raini, ni fa na gaji da kawo miñ ƙarar ta da kike yi a kaina tana zagi na, wlh zan je inji dalilin da ya saka take zagi na”. Tana ƙarike maganar ta miƙe da ninyar tafiya

Shakira tayi saurin riƙe ta tana cewa, “ke kuma meye haka? Yau ta soma zagin ki da zaki damu? Wlh idan baki iya kama ɓarawo ba sai ya kama ki, yanzu idan kika je sai kice mata mene? ki bari duk ranan da kika kama ta tana maganar naki sai ki ɗau mataki amma ba yanzu ba, kuma menene na damuwa tunda gani ina faɗa miki komi?”.

Yusra dake tsaye har yanzu kallon Shakira take yi har ta dire aya kana ta ɗaura da nata, “But wlh today I have to tell Hajiya everything, dama ina ɓoye mata ne ban son hankalin ta ya tashi”. Daga haka ta juya ta fice fuuu kamar ana tura ta

Tana fita Shakira ta saki murmushi tana cewa, “Dama haka nake so gwara kije ki faɗa ma Hajiyar ki don ta ƙara ƙullatan ta, shegiya Ni wlh ba ƙaunar Ɗahiran nan nake yi ba, da wani idanu sai kace na fataken dare, kai ko a turawan ma bana tunanin akwai masu irin wannan idanun..”

Ƙaran buɗe ƙofarta shi ya katse mata maganar ta, tayi saurin juyawa tana kallon me shigowa, ganin Mahaifiyar ta ne ya saka ta sauke ajiyan zuciya har da dafe ƙirji

ƙarisowa wajen ta Hajja Fatu tayi tana kallon ta tace, “What happened to Yusra leaving here in a rage?”

Dariya Shakira ta kwashe dashi tana cewa, “me kuwa zai faru in ba zugo ta da nayi ita da Ɗahira ba, ai yau sosai na fusata ta don har maganar Ya Usman nayi mata, yanzun ma Mahaifiyar ta za taje ta sanar ma wa”.

Sai kuma ta kuma kwashe wa da dariya tana cewa, “wlh da ma maganar ya koma kunnen Ya Usman inga yanda zai yi ƙulun kubura da ita”.

Hajja Fatu itama dariyan tayi tace, “yauwa ɗiyar albarka ai gwara da kika zugo ta ɗin, idan ta sanar wa mahaifiyar ta na san yanzu gaba ta soma ita da A’isha, hmmm mu zuba yanzu ma aka soma”.

Wannan shine halayyan Shakira da Mahaifiyar ta, ko ince ƙudurun su akan Ɗahira da Maman ta

Yusra da Ɗahira basu shiri tun farko; sakamakon zigin da Shakira take yi a tsakanin su batare da sun sani ba, ita Yusra akwai zafin kai da saurin fushi, tun farko dama ba wani shiri suke yi da Ɗahira ba, hakan yasaka Shakira ta samu dama take ƙara wa abun wuta, duk idan suka zauna tare da Yusra sai ta ce mata, “Ɗahira ta zage ta, ko tayi gulmanta”, hakan yasaka Yusra ko magana ta dena ma Ɗahira kullum kallon ta da abun take yi, ita kuma Ɗahira dama ba me son shiga harkan da babu ruwan ta bane bare kuma idan ana mata wulaƙanci, don haka itama ɗin sai ta fita harkan ta a cewar ta “duk ranan da ta sauko ta dena ɗaga mata kai sai su ci gaba da mutunci” kuma dama Ɗahira tana ganin itace Babba babu yanda za’a yi ta zauna tana bin ƙanwar ta don kawai tana son su shirya tunda ta san bata yi mata komi ba, duk da su huɗun ba wani tazara ne a tsakanin su ba duk sa’annin juna ne, sai dai Ɗahira aka fara haifa yanzu haka shekarun ta 25years and Two Month, sai Shakira me shekaru 25years cif-cif, sai kuma Yusra me 24years and 8month, maraban su da Fadila kwana goma ne

Gaba ɗaya ahalin gidan halayyan su ɗaya ne na jijji da kai da nuna taƙama, sai dai na wasu ya fi na wasu ne musamman ma Usman da ya fi kowa a gidan, kuma hakan a jinin su yake.

.

_Hmm now the game has started because there is a lot cakwakiya in this family, just go ahead and follow me and suburbuɗo me a comment to get more Post.
[5/21, 3:31 PM] Oummu Ɗahirah: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTORS*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER’S ASSO📖*
”’®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓”’

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA’S FAMILY*_

.

*EPISODE Seven*

Sallama tayi ta turo ƙofar ta shigo, Aunty Amarya dake zaune gefen gado ta’amsa mata tana kallon ta

ƙarisowa tayi ta zauna kusa da ita tare da miƙa mata ledan tana cewa, “Ga shi Mama”.

Bata amsa ba tace da ita, “Where have you been waiting for me?”

Ɗahira tace, “na je wajen Shakira amsan Littafaina ne”.

Gyaɗa kai kawai tayi tana ɗaukan ɗan kitt ɗin dake gaban ta ta miƙa mata tace, “ga shi Abbun ki ya ce in baki kyautar sa ne”.

Saurin miƙa hannu Ɗahira tayi ta’amsa tana buɗe wa, murmushi ta saki ganin danƙareriyar sarƙan gwal kana ta kalli Maman nata tace, “ina Abbu ɗin?”

“Ya fita, Ni kuma ki riƙe wannan ledan da kika amso sai ki ɗinka”.

Dariyan farin ciki Ɗahira ta saki kana tayi mata godiya tare da nuna murnan ta a fili, buɗe ledan tayi ta soma duba wa, atamfofi ne guda biyu masu kyan gaske sai kuma Material guda ɗaya

“Mama Nagode sosai Allah ya saka da alheri”.

Murmushi Aunty Amarya tayi tana kallon tilon ƴartan cike da so da ƙauna tace, “ki dena godiya tunda ya zama dole ne mu yi miki”.

Daga nan miƙe wa Ɗahira tayi zata fita, Aunty Amarya ta kira ta ta dawo, sake zama tayi inda ta tashi tana kallon Mamar nata

Ita kuwa cikin sauya fuska tace, “Meyasaka kika kai ƙarar Usman don ya fasa miki waya?”

Shiru Ɗahira tayi tana sunkuyar da kai ƙasa

” I don’t want to hear it again, do I?”

Gyaɗa kanta tayi

“Tashi ki je Allah miki albarka”.

Sai da ta’amsa da “ameen”. Before leaving

Tana fita ɗakin su ta shiga

Fadila na kan gadon ta tana latsa waya sai faman doka murmushi take yi, idan za’a rantse ma bata san da shigowan ta ba

ita kuwa Direct wajen gadon ta ta nufa ta’ajiye kayan hannun ta, fiddo kayan tayi tana gani, har ta gama dubawan ta’adana sannan ta dawo ta zauna ta ciro Books ɗin ta zube su saman gadon

dai-dai lokacin ne Fadila ta ɗago kai ta kalle ta, nan idanunta suka faɗa kan NOVELS ɗin dake zube kan gado, da sauri ta’ajiye wayan ta tataso ta nufo wajen ta tana zama kan gadon;, ta saka hannu ta ɗauki ɗaya daga cikin litattafan, cikin farin ciki ta ɗago tana kallon Ɗahira tace, “Hey Sis Where did you get this book?”

Ɗahira da take riƙe da ɗaya daga cikin litattafan me suna *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* tana dubawa ta bata amsa, “It’s mine”.

“Wayyo Allah wlh na daɗe ina neman Littafin *RAUDHAN* nan amma ban samu ba, Please ki ara min in karan ta, sosai nake son Littafan *JIKAR LAWAL GOMA* amma na rasa inda zan samu, ko da naje kasuwa nayi yawo but Allah be sa na samu ba”.

Ajiye Littafin hannun ta tayi tana kallon ta tace, “Ni kam samun littafan ta ba ya min wuya, idan kina so sai ki bari adawo min da wayata in saka ki group ɗinta”.

Murmushi Fadila tayi tace, “Thanks Sis, kai wlh har naji daɗi! na ƙosa naga ƙarshen abinda zai faru tsakanin *RAUDHA* da Captain Rayyan”.

Miƙe wa Ɗahira tayi ta shige Toilet ta bar Fadila nan zaune har ta soma karanta NOVELS ɗin.

.

_If you need my Book so contact me on this Number 07065334256._

.

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

Tun sanda ya fito General parlour ya nufi part ɗin su, cikin ɗakin sa ya shiga ya rufo ƙofan, Direct gaban Royal Bed ɗin sa ya nufa ya zauna a bakin gadon, har a lokacin be saki fuskar sa ba sai dai baza ka iya gane a halin da yake ciki ba, ya jima ahaka yayi shiru yana tunani sannan daga baya ya miƙe ya soma haɗa kayan sa cikin trolly, bayan ya gama Toilet ya shiga be jima ba ya fito ya bar ɗakin, yana fito wa parlour ya tarda Hajiya zaune tana kallo, a hankali ya taka ya’iso wajen ta ya sami waje kan sofa ya zauna

Hajiya kallon sa tayi tace, “Dama kana ciki?”

Gyaɗa mata kai kawai yayi yana mayar da idanun sa kan t.v

kallon sa Hajiya take yi tana karantan yanayin sa, duk da ta san halin ɗan nata ba kasafai kake gane alƙibilan sa ba, kiran sunan sa tayi

hakan ya saka ya juyo yana kallon ta sai dai be amsa mata ba

“Ina son ka fita harkan yarinyan nan ba na son ko kaɗan wani abu ya sake haɗa ku, yanzu ba kamar Da bane”.

Usman kallon ta yake yi a rashin fahimta, don be fahimci abinda take magana akai ba, sai dai kuma bazai iya buɗe baki ya tambaye ta ba

itama Hajiya ganin yayi shiru be ce komi ba; sai taci gaba da kallon ta don ta san ba amsa mata zai yi ba

sai da yaja lokaci a zaune a wajen be yi abinda ya kawo sa ba kafin daga bisani daƙyar ya buɗe baki yace,”I’m leaving”.

Kallon sa tayi batare da ta gane me yake nufi ba

hakan ya saka ya kawar da kai yana ɗan motsa bakin sa

“Ina zaka je?” Ta tambaye sa don ita bata gane inda za shi ba

In a calm and proud voice he said, “Turkey”.

Hajiya tace, “kamar ya zaka koma kai da kace sai kayi kwana biyu?”

Shiru yayi

“Are you talking quietly?”

“I have a job there.”

Shiru tayi tana kallon sa, shi kuwa ya kau da kai don be san ma su haɗa idanu

“Shikenan amma ka bari sai gobe sai ka tafi, yau dai ka haƙura”.

Be ce komi ba ya miƙe ya nufi ɗakin sa, yayinda ita kuma taraka sa da kallo tana mamakin irin halin sa

Shi kuwa yana shiga keey ɗin mota ya ɗauka ya fito ya zo ya wuce Hajiya still tana bin sa da kallo

parcking space ya nufa ya ɗau motar sa ya bar gidan.

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

*WASHE GARI*

Wajen ƙarfe 05:30pm. Na yamma Ɗahira na zaune saman gadon ta tana karatun Novel *(JARUMAI na Jikar Lawal Goma).*

Fadil ne ya shigo ɗakin kamar an hankaɗo shi ko sallama, wajen ta ya nufa yana dariya yace, “Aunty, are you still here?”

Kallon sa kawai take yi batare da ta furta komi ba

sai ya sake sakin dariya yana cewa, “Yaya Usman ne ya bani saƙo in baki shi ne naje ɗakin Kaka neman ki ashe kina nan kina faman karatun Novel, Wai me kuke karantawa aciki ne?” Yaƙarike maganar yana kai hannun sa kan littafin

Buge hannun sa tayi tana hararan sa tace, “kai ba na son iskanci; Yi abun da ya kawo ka ka ware”.

Miƙa mata Leda yayi tare da wayan ta da aka farfasa yace, “ga kwaraɓaɓɓiyan wayan ki inji Kaka”.

Bata ce komi ba ta’amsa tana ajiye wa taci gaba da karatun ta

shi kuma Fadil tsayawa yayi yaƙi tafiya yana kallon ta

Ɗago kyawawan idanuwan ta tayi ta maida kansa, “What’s stopping me?”

“Aunty Ɗahira ki bani wannan wayan mana tunda kin ga kin samu wata”.

“What are you talking about now?” Ɗahira ta tambaye sa still tana kallon sa

Ɗan turo baki yayi yace, “ai gaskiya na faɗa ba kwaraɓaɓɓiyan ba ce?”

Hannu tasa da ninyan riƙo sa yayi saurin matsawa ya nufi ƙofa yana mata dariya

“Idan na kama ka Fadil..” Sai tayi shiru tana ƙwafa sannan taci gaba da karatun ta

Fadil yace, “to inzo in amsa Aunty?”

Bata kula sa ba Amma kuma sosai ya’ishe ta; don ita ba ta son hayaniya da yawan surutu, shi kuma Fadil ya san ba ta so shiyasaka yaƙi tafiya sai magana yake mata yana son ya ƙule ta, ko kuma taji haushi ta ba shi wayan ya tafi, sai da ya gaji don kan shi sannan ya fice batare da ta sake kula sa ba

Yana fita ta’ajiye Littafin don tunda ya fara surutun sa ta dena fahimtar Book ɗin, ledan ta buɗe ta ciro wayan dake cikin kwali, sai da ta gama jujjuya ta ahaka kafin ta taɓe baki tana buɗe wayan, the same irin wayan ta ne, Simcard ɗin ta ta cire ta saka a ciki sannan ta kunna tare da gyara zaman ta tana murmushi ta soma latsa wayan.

.

Plz kuyi
*Vote and shared*
[5/21, 3:32 PM] Oummu Ɗahirah: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTORS*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER’S ASSO📖*
”’®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓”’

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA’S FAMILY*_

_Wannan shafin naku ne My Fans kuji daɗin ku, Allah yabar ƙauna._

.

*EPISODE Eight*

*MONDAY*

Ɗahira ce tsaye gaban mirror ta buɗe locker ta ɗau ɗan siririn glass ɗin ta tasanya a idanuwan ta sannan ta juya ta ɗau jakan ta ta fice, Direct ɗakin Maman ta ta nufa, tana shiga ita kuma tana fitowa daga Toilet

Kallon ta tayi tace, “Ke har yanzu ashe baki tafi ba?”

Ɗahira tace, “Eh Mama ban gama shiryawa bane yanzu zan tafi”.

Aunty Amarya tace, “to ki kula sosai abinda ya kai ki shi za kiyi, Allah ya tsare”.

Murmushi Ɗahira tayi tace, “Ameen Mama na tafi bye”.

Ta juya ta fice, a parlour ta tarar da Umma tana zaune

“Umma sai mun dawo”.

Umma kallon ta tayi sannan tace, “to adawo lafiya”.

Amsa mata kawai tayi ta fice cikin sauri, parcking space ta nufa ta buɗe motan ta da ta kasance ash colour ta shige tabar gidan

Mintuna 15 ya ɗauke ta kafin takai Babban Hospital ɗin wato *AL’AMEEN FAMILY HOSPITAL* tana shiga tayi parcking motan sannan ta ɗau jakan ta tare da rigan aikin ta tafito, rufe motan tayi kafin ta juya ta doshi cikin Asibitin cikin tafiyan ta na yanga, Lifter ta hau yakai ta hawa na uku kasancewar anan ne Office ɗin ta yake, ko wani Doctors akwai sunan sa agaban office ɗin sa, itama haka an saka Dr. Ɗahira Al’ameen Al’ameen, sai da ta kalli sunan nata tasaki kyakykyawar murmushin ta kafin ta buɗe tashiga ciki, ahankali ta taka har ta’isa kan kujera ta zauna tana ajiye jakan ta tare da rigan aikin ta, files ɗin da ta gani azube akan table ta soma buɗe wa tana dubawa, sai kuma ta miƙe tsaye da nufin fita taji anyi nocking

“Yes come in”. Tafaɗa tana kallon ƙofan

Baffa ne ya shigo hannun sa riƙe da wasu files, murmushi suka sakarwa juna kafin ya’iso ciki ya zauna, itama ɗin komawa tayi ta zauna tana cewa

“yayana Barka da safiya”.

“Yauwa my sweet sister, hope dai kina enjoyed aikin?”

Murmushi tasaki cike da farin ciki tace, “Yes sai dai ban fara ba zuwana kenan”.

Shima murmushin yasaki cike da ƙaunarta a ran sa yace, “Ok ga wasu files ɗin; su ne waɗanda zaki duba anjima da ƙarfe 10:00am, waɗannan kuma na gaban ki na petiens ɗin ki ne Big Dady ya kawo miki, idan kin shirya sai muje in nuna miki Rooms ɗin da suke”.

Ɗahira kallon sa tayi har alokacin da murmushi a face ɗin ta tace, “Tom muje”.

Miƙewa yayi itama ta miƙe tana ɗaukan farar rigan aikin ta tasaka, sosai rigan yayi mata matuƙar kyau fiye da tunanin me karatu, eyeglasess ɗin ta tagyara tana me bin bayan sa

bayan sun fito atare suka jera suna tafiya suna hira sai zuba murmushi duk kan su suke yi.

 

⚫⚫⚫

Buɗe ƙofan tayi ta shigo bayan da Shakira ta bata umarnin shigowa, ahankali ta ƙariso ciki tana karairaya cike da son burgewa ta samu waje ta zauna tana kallon Shakira da itama ta zuba mata idanu tana kallon ta, murmushi ne kwance a face ɗin ta tace

“Suna na Dr. Ayush Abdulkarim, Ni ce office ɗina ke kusa da naki kuma nima ɗin ina cikin wanda Hospital ɗin nan suka ɗauke ni aiki ranan Waliman ku, am.. shine nace bari na shigo mu gaisa”.

Sai alokacin Shakira tasaki fuskarta tace, “ok Ni kuma Dr. Shakira Abubakar Al’ameen”.

Murmushi Ayush tayi tace, “idan babu damuwa zan so mu zama Friends coz tun alokacin Walima naga kin burge ni”.

“Why not”. Shakira tafaɗa tana ɗage kafaɗa

“Thank you, bari inje zan sake dawowa idan na gama aiki”.

Murmushi Shakira tayi mata tace, “ok babu damuwa”.

Tashi Ayush tayi ta fice tana me rufo mata ƙofar, murmushi ta saki tana cije leɓe afili ta furta

“Da sannu Burina zai cika, da sannu mafarki na zai zama gaske, tabbas sai na cika burin zuciyata”.

Juyawa tayi ta shige office ɗin ta dake kusa da na Shakira.

 

⚫⚫⚫

Ɗahira bayan ta gama duba petiens ɗin ta ne ta juyo ta nufi office ɗin ta, ta zo karya kwana kenan su kayi karo da wata matashiyar budurwa har files ɗin hannunta suka zube, cikin sauri atare suka ce

“Sorry”.

Sai kuma su kayi murmushi sannan Ɗahira tariga ta cewa

“Kiyi haƙuri fa”.

Budurwan me suna Safna tace, “no babu komi”.

Sannan ta duƙa ta soma kwaso ma Ɗahira files ɗin, itama duƙawa tayi ta taya ta har suka gama kafin ta’amsa na hannun ta ta wuce

Bayan ta Safna tabi da kallo har ta ƙule sannan ta saki ajiyan zuciya tana murmusawa a ranta tace, “Tana da sauƙin kai ba kamar wancan bugaggiyar da mu kayi karo da ita ba”.

Juyawa tayi taci gaba da tafiyan ta har ta’iso wajen lifter ta buɗe zata shiga, ji tayi an bangaje ta an shige, tana ɗago kai taga Yusra, a ran ta tana mamakin halinta, yanzu suka gama karo da ita ta balbale ta da tsiya but gashi yanzu ta buge ta bata ce mata tayi haƙuri ba. ɗauke kai kawai Safna tayi ta shige ciki tare da danna Number liftern ta rufe.

Yusra ta soma sauka kasancewar office ɗin ta a hawa na biyu yake sannan ita kuma Safna ta sake latsa number yakai ta ƙasa, wasu files taje ta’amso a reception sannan ta sake hawa ya maida ita block 4 inda anan ne office ɗin ta yake, tana ɗaya daga cikin waɗanda aka ɗauka sabbi.

 

⚫⚫⚫

Ƙarfe 01:00pm. Ta gama duba marasa lafiyan ta, miƙewa tayi ta shiga Toilet ɗin cikin office ɗinta ta ɗauro alwala ta fito, sallaya ta shimfiɗa ta gabatar da Sallah sannan ta miƙe ta ɗau duk abinda take buƙata ta zuba cikin jaka ta fito ta rufe office ɗin, lifter ta hau ya kaita upstairs na 5 inda anan ne office ɗin mahaifin ta yake, Direct office ɗin ta nufa tayi nocking aka bata iznin shiga, tura ƙofan tayi ta shige da sallama a laɓɓanta

Abbu ganin ƴar shi da yafi ƙauna cikin ƴaƴan shi a office ɗin sa yayi matuƙar saka shi farin ciki, cike da fara’a ya’amsa mata yana cewa, “Mama na”.

Ɗahira da itama take faman doka murmushin ta ƙariso ta zauna tana cewa, “Abbu Barka da aiki”.

“Yauwa Mama na ya naki aikin?”

“Alhmadulillah Abbu”.

Abbu yace, “masha Allah haka ake so, har kin tashi kenan?”

“Eh Abbu, nazo ganin ka ne sai mu wuce tare”.

Murmushi yayi yace, “Mamana kenan ai ban tashi ba, ina ga yanzu sai zuwa 04:00pm.”.

Gyara zaman ta tayi tace, “to Abbu bari in jira ka sai mu tafi tare”.

“A’a tashi kije gida ki huta Mamana ba na son ki zauna nan, kin ma ci abinci?”

“A’a Abbu”.

Coolarn dake kan desk ɗinsa ya turo mata yace, “ɗauka ki ci”.

Duk da ba ta jin yunwa bata yi masa musu ba ta ɗauka ta soma ci, kaɗan taci ta tsame hannun ta ta shiga Toilet ɗinsa ta wanko hannu ta dawo

Lokacin ne Abbu ya ɗago kai daga rubutun da yake yi yace, “Kin ƙoshi kenan?”.

Gyaɗa masa kai tayi sai kuma tace, “Abbu ko ma ban ƙoshi ba idan na koma gidan zan sake ci ai”.

“To shikenan Allah ya miki albarka ki kula kinji”.

“To Abbu byee”.

Ta ɗaga masa hannu sannan ta fice tana murmusa wa, tana fita haraban asibitin ta shige motan ta taja tayi gida, bayan tayi parcking ta fito ta nufi Part ɗin su, sai da ta soma shiga ɗakin Mamanta ta sanar mata dawowar ta sannan ta nufi ɗakin su, wanka ta soma yi ta shirya cikin wata koriyar atamfa ɗinkin Buba ta ɗaura ɗankwalin shi, eyeglasses ɗin ta tasanya ta fito ta nufi kichen, abinci ta ɗiba ɗan kaɗan ta fito parlour ta zauna tana ci, lokacin ne itama Fadila ta dawo

Ɗahira amsa mata sallaman ta kawai tayi taci gaba da cin abincin ta idanuwan ta na kan t.v, bayan ta gama ta tashi tamayar da plate ɗin kana ta wuce ɗakin Mamanta, tana tura ƙofan da sallama Aunty Amarya ta ɗago kanta daga karatun Hisnul Muslim da take yi, ta kalle ta tana amsa mata sallaman

“Mama bari inje wajen Kaka”.

Gyaɗa mata kai kawai Maman tayi ta maida hankalin ta kan littafin ta, ita kuma Ɗahira ta fice.
[5/23, 3:55 PM] Oummu Ɗahirah: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTORS*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER’S ASSO📖*
”’®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓”’

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA’S FAMILY*_

*NASIHA*
_Sallar natsatstsu ba ta samuwa sai an kare sallar daga duk wani abu mai shagaltar wa, a kuma yi ta cikin lokatai waɗanda ba su hana yin Sallah da zuciya ɗaya kuma ba su zama shamaki tsakanin zuciyar sa daga kome ban da tunanin Allah, sai Allah ya haskaka masa zuciyar sa, ya sami basira ya ji daɗin saduwa da Ubangiji. Daga nan sai ka ga Bawa kullum yana mayar da hankali sosai ga wanda yake ganawa da shi. Wannan ma ya fi ƙarfi cikin sujada domin kuwa Bawa ya fi kusa da mahaliccin sa lokacin da yake cikin wannan hali. Don more wa shi wannan muƙami an ji Manzon Allah yana cewa, “Bawa ya fi kusanta ga Ubangiji. Saboda haka ya yawaita addu’a.”_

.

*EPISODE Nine*

. Cikin siririyan muryan ta tayi sallama tana shiga ciki

Kaka dake zaune saman Wheel chair ɗin sa yana karatun jarida ya ɗago yana kallon ta, sannan ya’amsa mata sallaman yana cewa, “Maraba lale da matata abar ƙaunata, yau ga matata ta zo gare Ni”.

Murmushi me burgewa Ɗahira ta saki tana takowa wajen sa ta zauna a gefen gadon sa tana cewa, “Kakus kenan baka rabo da tsokana ta, sai kace ka daɗe rabon da ka ganni”.

Smile yayi yace, “Matata kenan ke baki san yanda nake ji dake bane, yau gaba ɗaya ba na jin daɗin rasa ki kusa dani, Allah da ba don kar in so kaina da yawa ba, da sai ince ki zauna a gida abinki ba sai kinyi aiki ba, tunda gani Mijin ki Ina son ki kusa dani”.

Dariya sosai Ɗahira tayi kana tace, “Kaka kenan hmm Mijin kwali ko, don dai a kan ka dai bazan iya ajiye aiki na inzo in tare a wajen ka ba”.

Zaro idanu yayi yace, “au kina nufin ban kai matsayin da zan iya auren ki bane na zama na ƙarfen?”.

Sai kuma ya girgiza kansa yana dariya yace, “to bari kiji Ni ɗin Ni ne dai Mijin ki da zaki yi alfahari dashi nan gaba don babu wanda zai so ki fiye da yanda nake ƙaunar ki, har da wanda kike son min gori akan sa”.

In ban da dariya babu abinda Ɗahira take tiƙawa, sosai Kaka yake ba ta dariya idan suna zancen nan, kuma sai ya fuske tamkar da gaske ne maganar tasa

“Hmm ci gaba da min dariya, ban da abinki ma ni fa taimakon ki zan yi, kin san Real Matata tafi ki komi baza ki haɗa kanki da ita ba”.

Wannan karon murmushi tayi tace, “Kakus nawa Ni kaɗai, kaima ban da abun ka me zan yi da tsoho irin ka, idan har matarka ta fi ni komi ai nima Mijina ya fi ka komi, kuma idan kace ƙarya zan kawo maka shi ka ganshi”.

Cike da jin daɗi Kakan yace, “yauwa Jabun Matata ki kawo min shi dama na daɗe ina burin ganin sa, kin ga sai a gwada aga wanda yafi kyau cikin mu, ke kaɗai ce dama ban san saurayin ki ba, amma kin ga su rasa kunya ɓeran tanka duk sun kawo min su na gani”.

Numfashi Ɗahira taja tana kallon sa don ita bata san ma me zata ce mishi ba, ita da bata taɓa yin saurayi ba taya zata kawo masa wanda zata aura?

“You are silent my wife? I love to see who you will marry more than the other children. Burina kenan inga Mijin ki inga wanda zai iya riƙe min ƴar ƙwai na da amana”. Kaka ya ƙarike maganar tasa yana kallon ta da alamun dagaske yake yi

Hannu ta saka ta dafa Wheel chair ɗin sa tana kallon sa, cikin murmushi tace, “to karka damu Kaka, idan ma tsoro kake ji karka mutu baka ga aure na ba ka kwantar da hankalin ka, zan roƙa maka Allah ya barka da ranka har zuwa ranan da zaka ga aure na, me kake ci na baka na zuba Tsoho na?”

Kaka dariya yayi yana jan hancin ta yace, “ja’ira kin ganki”.

dariya tayi itama tana kai hannun ta kan hancin nata

“To ki nuna min shi ko a hoto ne mana”.

Zaro idanu tayi tace, “kaiii Kaka is so expensive, wannan dalilin ya saka na hana sa yin hoto kar ma wata ta mallaki hoton a rashin sani, don shi ɗin yafi ƙarfin ko wace mace idan ba Ni ba, but idan kana son in ɓurɓusa maka wani abu daga cikin labarin sa nima sai ka bani labari me daɗi ta yanda zanji daɗin baka labarin shi”.

“To shikenan yanzu bari in Baki labarin Matata abar alfahari na”.

Murmusawa Ɗahira tayi ta gyara zaman ta da kyau har da buga tagumi tace, “to ina ji bani nasha”.

Sai da yayi dariya kafin yace, “to tashi ki buɗe drowern can ki ɗauko min jakan ciki, ga ɗan mukullin acikin locker”.

Yayi mata nuni da Lockern dressing mirror

Ɗahira da har ta tashi tsaye tanufi wajen ta buɗe ta ɗauko keeys ta kawo masa, shi ya cire mata na drowern ta’amsa taje ta buɗe ta ɗauko masa jakan ta dawo

Zuge jakan yayi hotuna ne da yawa aciki, ya zaro ɗaya daga ciki ya nuna mata

“You see this”.

Amsa tayi tana kallo, shi ne tare da Baby a manne da juna, ga duk kan alamu anyi hoton ne lokacin da ake party, murmusawa tayi tana shafa hoton ta ɗago kai tana kallon sa tace, “Wow Kaka gaskiya kun yi kyau sanda kuke Matasa”.

Murmushi yayi yace, “ke ma kin faɗa ai, mun yi hoton nan ne lokacin da ake Dinnern bikin mu, hmm bazan taɓa manta wannan lokacin ba, Matata har yanzu na kasa manta ta har yanzu kuma ƙaunar ta na nan daram cikin raina batare da ko ɗigo ya fita ba duk da kuwa ba ta a raye, kin san kowa da irin ƙaddaran da Allah yake jarabtan bawan sa dashi, to Ni soyayyarta shine ƙaddara ta, na so ta matuƙa fiye da tunanin mutum, haka zalika taso Ni fiye da tunanin me tunani, Allah Sarki Baby”.

Sai ya saki murmushi yana komar da hawayen idon sa

“I will never forget her in my life. har yanzu zanen halin ta na nan daram cikin raina”.

Murmushi kawai Ɗahira take yi tana kallon Kakan nata, sai da ya dasa aya a maganar nasa sannan tace, “Grandpa tell me about the day you first met her”.

Sai ko Kaka ya saki dariya me sauti, ga duk kan alamu ya tuna wani abu ne, cikin murmusawa yake cewa, , “This is the day I will never forget in my life, ranan da na haɗu da Babyna matata abar ƙauna ta, lokacin da naje Hospital ɗin da nake aiki, a bakin Hospital ɗin na kusa bige ta da motata, hakan ya saka ta tsorata har ta faɗi taji ciwo a hannu sannan kuma nayi mata asaran shinkafan da take siyarwa”.

Ƙwalalo idanu Ɗahira tayi tace, “Kaakaa Talla?”

Dariya yayi yace, “eh Talla, ai talla naga take yi lokacin da muka fara haɗuwa, Hmm my Baby taga rayuwa duk da kasancewar ta ƴar gata don mahaifin ta me kuɗin gaske ne..”

“To amma Kaka ya akayi ta koma yin talla?” Ɗahira ta katse sa da tambayan nan

“Ƙaddara, ko ince canjin rayuwa”.

“To Kaka ya kuka ƙare da ita kuma wani kalma ta soma shiga tsakanin ku? And kuma lokacin ne ka soma sonta?” ta sake tambayan sa cike da zumuɗi da son jin labarin

Murmushi Kaka yayi yana lumshe idanun sa, sai ya buɗe a kanta yace, “kalman da ta soma fitowa a baki na shine haƙuri na bata, sannan ne ta ɗago ta kalle ni, tabbas kallon farko da nayi mata na kamu da matsananciyar ƙaunar ta, kuma sai na nemi alfarman tabi ni inyi mata dressing hannun, da farko bata da ninyan bi na but mutanen da suka taru wajen ne suka saka ta taje, kalman da na soma ji a bakin ta har ta tafi sunan ta kaɗai ta faɗa min”.

“Kaka kasan me?”

Girgiza mata kai yayi yana kallon ta

Murmushi tayi da ya bayyana ƙananun haƙoran ta tace, “abinda yake bani mamaki da burgewa yanda ka auri Mata har uku masu suna ɗaya, ko a Film da littafai ban taɓa ganin hakan ba, kuma har kayi rayuwa dasu alokaci ɗaya”.

Shima murmushin yayi yace, “Allah kenan shi ya ƙaddara hakan, gashi ke kuma kin zo a ta huɗu”.

She laughed and said, “Show me the other pictures, ka ga har yanzu bansan sauran matan naka ba ko a hoto ka ƙi ka nuna mana, wancan ƴar uwan taka da tayi aure a ƙauye kawai nasan zan iya tunawa, tunda nasan ta muna yara kafin ta rasu”.

Jakan ya buɗe ya kuma zaro wani hoton ya miƙa mata

Hoton ta’amsa tana kallon matashiyar da aƙalla zata kai shekara 19 zuwa 20, fara ce sol kyakykyawar bafulatana, da sauri Ɗahira ta ɗago kai tana kallon Kaka tace, “Laa Kaka wlh wannan sak Big Dady, ba su da maraba kamar tayi kaki ta ajiye”.

Murmushi yayi yace, “Matata ta farko kenan *UMMEE NAFEESA,* Mace ƴar aljanna me tsananin haƙuri, dattako da sanin ya kamata, bazan iya fasalta miki kyawawan halayyan ta ba, wannan hoton anyi sa ne gab da zata rasu, Ni na ɗauke ta a waya shine na ba da aka wanko min, Allah Sarki ta rasu da ƙuruciyarta, ta rasu lokacin da nake matuƙar buƙatar ta, ta rasu sanda ta gama naƙudan Noor (Big Dady) batare da ta ganshi ba ta koma ga Allah. Allah ya jiƙan ki da rahma Ummeeta”. Kaka ya ƙarike maganar tasa yana share hawaye

Itama Ɗahira har sai da tayi nata hawayen sabida tausayi sannan tace, “ameen Kaka, may Allah have mercy on them all”.

Amsan hoton yayi ya maida a jaka, yana shirin rufewa Ɗahira ta saka hannu ta zaro wasu hotunan biyu tana cewa, “Kaka ka bari mana ka gama min bayani, wannan kuma yaron me tsananin kama da kai wanene?”

Ta nuna masa hoton ɗan ƙaramin yaro dake wasa da kayan wasan da aka zube masa da yawa a gaban sa

“Yarona na farko kenan sunan sa Arif, Sunan Kakana yaci Khabeer, amma tun yana ƙarami ya rasu”.

Ɗahira tace, “laa Kaka ashe ban da Big Dady dama kayi wani yaron? Wacece maman shi?”

Hoton hannun ta ya nuna mata

“Ga Maman shi nan cikin hoton nan”.

Shafa hoton Ɗahira tayi da hannun ta tana murmushi, hoton KAKA ne da Ƙannin sa biyu Baseera da Ihsan sai kuma Nafeesa mahaifiyar Arif”.

“Kaka kuna tsananin kama sosai duk kan ku kowa ya gan ku ya san ƴan uwan juna ne”.

Murmushi kaɗai yayi ya miƙa hannu ya’amsa hoton sannan yace, “kawo in mayar zanyi sallah”.

“So what about the story Kaka?”

“Ki bari duk sanda na sami lokaci zan tara ku gaba ɗaya in baku cikakken labarin aurena dasu”.

“Yauwa Kakus ɗin mu, Allah yakai mu to”.

Bayan ya zuba hotunan ya bata jakan ta mayar, ita ta tura sa har Toilet ta zuba masa ruwa yayi alwala sannan ta tafi part ɗin su bayan ta bar sa nan cikin ɗaki yana Sallah.

Tana zuwa Parlour’n su da Fadil taci karo yayi ɗai-ɗai yana kallo

“Yauwa Aunty Ɗahira kin bar wayan ki ana ta kira”.

Bata ce komi ba ta wuce cikin ɗakin nasu, ƙarar zuban ruwa tajiyo a Toilet ta san Fadila ce, zama tayi ta ɗau wayan tana duba missed calls ɗin da akayi mata, Baffa ne ya kira ta, itama kiran sa tayi but be ɗauka ba, sai ta’ajiye wayan ta ɗau Novel ɗin da take karantawa *JARUMAI* ta gyara zamanta ta soma karanta wa kafin Fadila ta fito daga Toilet tayi alwala.
[5/23, 3:56 PM] Oummu Ɗahirah: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTORS*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER’S ASSO📖*
”’®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓”’

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA’S FAMILY*_

.

*EPISODE Ten*

 

*WASHE GARI*

BAFFA ne jingine jikin motar sa yana duba waya, yana sanye cikin ƙananan kaya kamar yanda ya saba waɗanda suka matse sa sosai, kansa da askin zamani da yayi masa kyau sosai, sai faman shaining yake yi alamun ya sha mayuka masu tsada

Shakira CE tafito cikin shirin ta, tana tafiya ɗai-ɗai kamar baza ta taka ƙasa ba, har ta wuce ta hangi Yayan nata tsaye wajen motan sa, sai ta juyo tana kallon sa taɗan ɗaga murya tace, “Yaya inzo mu tafi tare ne?”

Lokacin ne Baffa ya ɗago kansa yana kallon ta, sai da ta samu harara kafin yace, “Where is your car and I will take you?”

“Here’s Yaya, wlh I don’t feel good about my body that’s why I don’t like driving”.

Gajeren tsaki ya ja yana ɗauke kai a kanta yace, “babu inda zan kai ki ki nemi drever”.

Har ta buɗe baki da ninyan yin masa magiya sai taga yana kallon hanyan ƙofar shiga gidan yana sakin murmushi, itama juya kai tayi ta kalli wajen

Ɗahira ce ta fito sanye da Jan abaya me kwalliyan Flower’s da stones a jiki, tayi Rolling da ɗankwalin Rigan, face ɗin ta sanye da ɗan siririn farin glasses 👓ɗin ta wanda ya ƙara wa Sky Green ɗin cikin idanuwan ta kyawu, tunda ta fito itama take murmushi tana taho wa cikin tafiyar ta na yanga tamkar zata karye

Tana isowa suka sakarwa juna murmushi me bayyana haƙora, sannan ya buɗe mata motan ta shiga, shima zagaya wa yayi ya shige yaja ya nufi Gate

Shakira dake tsaye kamar an dasa ta ta saki baki tana kallon motar har ta fice

“Cab ɗijam.. Kar dai ace hasashe na ya zama gaske? Uhmm idan ko haka ne tabbas akwai matsala, babu yanda za ayi na bar Yayana yaso wannan me kama da mujiyan.. ina sam”.

Ƙwafa tayi tana nufan motan ta ta shige taja ta fice a gidan, ko a cikin motan tunanin yanda ta gansu yau ɗin ya tsaya mata arai, duk da ta san cewa babu wanda ya kai Ɗahira da Baffa shaƙuwa a gidan, amma kuma abinda take gani cikin idanun yayan ta yasa yau ta ɗaura zargi akan su.

Har tazo ta wuce motan su Baffa a hanya tana kallon motan ta mirror tana jan tsaki, tana kitstsima abubuwa aranta da yawa.

Su kuwa a cikin motan hira Baffa yake ta mata cike da tsananin ƙaunar ta, ji yake yi ba ya son ko kaɗan tafiyan da suke yi ya ƙare sabida shauƙin da yake ji, shiyasaka yake tafiya a hankali kamar bazai yi ba

Ɗahira kallon sa tayi tana dariyan labarin da yake bata tace, “Yaya don Allah ka bari haka kar cikina ya fashe”.

Dariya shima yayi yana kallon ta cike da so yace, “ai Ni nafi son in gan ki kina Farin ciki ne shiyasa nake baki labarin, don haka Ni bazan Dena ba, bari ma in baki wani”.

Murmushi tayi me ƙayatarwa cikin ɗauke kai akan sa tace, “to Yaya kabar ni haka dai zuwa anjima sai ka bani”.

“Well, my dear Sister, it’s over no matter what you want me to do.”

Still Murmushi tayi idanun ta akan titi, sau da dama tana mamakin yanda Baffa yake nuna mata kulawa fiye da tunanin ta, kuma yake yin duk abinda take so yake barin duk abinda ba ta so, tasan cewa yayan nata me ƙaunar ta ne tun tana ƙarama don ba ya son ɓacin ranta.

Yana yin parcking a haraban asibitin ya fito ya zo ya buɗe mata yana nuna mata hanya da hannu, cike da murmushi a face ɗin sa yace, “Yauwa Gimbiya fito an kawo”.

Sunan da ya kira ta dashi ya saka tayi dariya tana kallon sa cike da farin ciki, zuro ƙafafun ta waje tayi ta fito, sannan ya rufe suka jera sukayi ciki.

 

⚫⚫⚫

“I told you to come in at 08:00am o’clock. Me ya tsayar da ke?” Doc. Said yayi maganar yana juyawa cikin kujeran sa

Fari tayi da idanun ta sannan tace, “kai ma ban da abun ka ya Docta; kasan ba a raba mu da ɗan shafe-shafe na kwalliya, kuma ka ga 08:00am yayi wuri da yawa”.

Murmushi ya saki yana sakar mata wani shu’umin kallo

“Uhmm Sulaima kenan! That’s why I love you more sabida wannan kwalliyan naki, ko kaɗan baki wasa da jikin ki wajen kin ga kin fito kin burge kowa, wasu kuwa ko a jikin su be dame su ba”. Yaƙarishe maganar da taɓe bakin sa

Dariya tayi tana sake lanƙwashe murya tace, “Ya Dacta kenan! Ni fa nasan da wacce kake yi, kuma kasan zan iya zuwa in faɗa mata”.

Waro ido yayi yana dariya yace, “rufa min asiri don Allah karki haɗa ni da ita kin san halin ta, but yaushe Ni zaki bani dama ne wai? Na gaji da wannan kwane-kwanen da kike min”.

Sulaima tace, “Ya Dacta Ni fa gaskiya ba na tunanin zan iya harka da kai, ko ka manta kai Mijin Yayata ce? Haba dai ka sauya tunani mana Ni gaskiya bazan iya ba”. Taƙarike maganar a shagwaɓe

Lumshe idanu yayi yana sake kallon ta cike da tsananin sha’awar ta, sai da ya ɗago daga jikin kujeran ya ɗaura hannayen sa kan Deks ɗin sa sannan yace, “Sulaima kin san ni; na sanki, why kike son haramta min kan ki? karki manta fa ba wai na ce miki auren ki zan yi ba bare ki kawo wani zancen Ƴar uwan ki, Ni dai don Allah ki bani dama mu more rayuwan mu tare kin san bazan iya haƙura dake ba, kinga matsayin ki daban matsayin ƴar uwanki daban a waje na”.

Murmushi tayi tana girgiza kanta cike da yauƙi tace, “ya Dacta let’s change our talk, muyi abinda ya kawo ni ka ga ina da inda zan je”.

Doc. Said yace, “to shikenan tunda kin fi son haka, amma ki sani ba wai na bar maganar bane kenan, yanzu ya aka yi kika bar ciki ya shiga jikin ki?”

“Hmm tsautsayi mana, wlh nayi mamaki da naje Hospital aka gwada Ni wai ciki ne dani, kuma duk wani matakan tsaron da na saba yi nayi but abun kamar almara”.

Ɗage kafaɗa yayi yace, “any way muje ki hau gadon in duba ki mu gani, don Nima Ina da aiki yanzu a gaba na”.

Tashi tayi tana cire gyalen jikin ta ta nufi wajen gadon, shima ya tashi ya bi bayan ta.

⚫⚫⚫

Zuwan ta Office ta tarar da patients ɗin ta suna jiran ta, yau bata zo akan lokaci ba hakan yasaka har suka rigata zuwa tunda ƙarfe 10:00am zata soma duba su, yanzu gashi har goma saura

Tana shiga ta saka rigan aikin ta sannan ta zauna taba su umarnin shigowa ɗaya bayan ɗaya tana duba su, tayi wajen awanni biyu tana faman duba su sannan ta gama ta tashi ta shiga Toilet tayi uzurin ta ta fito, wasu files ta ɗauka ta fita ta nufi rooms ɗin patients ɗin ta masu jinya

Tana shiga da gadon farko ta fara, taƙarisa da fara’an ta tana gaishe da matar dake jinyar wata burduwan yarinya, bayan sun gaisa cikin faram-faram sannan Ɗahira tace, “Mama har yanzu bata farka bane?”

Mama tace, “ta farka jiya da daddare, kuma Dacta ɗin da kika ce zata zo ta duba ta ita ta duba ta, ga ma takardan da tace, “in baki”. Ta miƙo mata takardan

Ita kuma ta’amsa tana dubawa, sai da ta gama dubawa sannan ta kalli Maman tace, “Mama to ya jikin nata tana samun sauƙi ko?”

“Ai alhmadulillah Dacta ba kamar jiya da safe ba, ta samu sauƙi sosai”.

Gyaɗa kai Ɗahira tayi tana rubutu cikin wani file, sai da ta gama ta matso kusa da yarinyan ta soma duba ta sannan ta ɗago tana kallon Maman tace, “Mama insha Allahu komi zai zo da sauƙi, idan ta farka sai ta soma amfani da ruwa me ɗumi ana mata tsarki, daga yau sai a soma mata amfani dashi ko yaushe insha Allahu komi zai zama normal”.

“To Dacta mun gode ƙwarai Allah ya saka da alheri”.

Murmushi Ɗahira tayi tace, “ameen Mama Babu komi ai, Allah Ubangiji ya bata lafiya”.

Mama ta’amsa da “ameen” tana sake mata godiya

Daga nan Ɗahira gadon gaba ta wuce, itama Yarinya ce budurwa, wata shirgegiyar mata take jinyar ta, sai dai yarinyan bata kai wancan shekaru ba don baza ta fi 13yrs ba

Bayan sun gaisa da matar ta tambaye ta jikin yarinyan

Matar cike da sanyin murya kamar za tayi kuka tace, “Doctor babu sauƙi wlh yarinyan nan tana shan wahala sosai, tun jiya farkawar ta biyu, kuma duk idan ta farka a firgice take tashi tai ta ihu tana surutai”.

Ɗahira da take bin yarinyan da kallo cike da tsananin tausayin ta ta juyo tana kallon Matar tace, “Mama ki kwantar da hankalin ki insha Allahu zan yi iya bakin ƙoƙari na wajen na ga ta samu lafiya, Allah zai saka mata duk wanda yayi mata wannan abun”.

Share hawayen ta matar tayi tace, “ameen Dactor na gode ƙwarai”.

Daga nan Ɗahira duba yarinyan ta soma yi, ta jima tana duba ta kafin ta saka mata ruwa tayi mata allura ta cikin ruwan sannan tayi mata sallama ta wuce

Sauran gadon ta nufa ta duba su su ma, sannan taje wasu Rooms ɗin, sai da ta gama ta koma Office ɗin ta.

Tana shiga taga Baffa zaune yana kallon ta yana sakar mata murmushi

Itama murmushin tayi masa ta shigo ta nufi wajen zaman ta ta zauna, cikin muryan ta na yanga take cewa, “Yaya na yaushe ka shigo?”

“I Come in right now, what’s your job?”

“Alhmadulillah. How’s yours?”

Murmushi yayi yana shafa suman kansa yace, “uhmm sai godiyar Allah my Sister amma babu daɗi”.

Dariya Ɗahira tayi tana kallon sa tace, “kai kenan Yaya, kai da ka jima tsawon shekaru kana aiki kake faɗan haka ina ga Ni da jiya na soma? wlh Yaya da wahala sosai aikin nan duk na gaji”. Taƙarike maganar ta tana lanƙwashewa ajikin kujeran

Baffa dariya yayi yace, “oh my dear sister ke dai kawai ki ce ke raguwa ce, amma daga fara aiki kice kin soma gajiya?”.

Murmusawa kawai tayi tana ɗan lumshe idanuwan nata don tasan halin yayan nata tsokana yake ji, ita kuma ta gaji ko maganar ma daƙyar take amsa masa

Baffa da ya tsare ta da idanun sa yana sakin murmushi me ƙara masa kyau yace, “sis Naga da alamun kin gaji tashi muje muci abinci”.

Shiru tayi tana ɗan tunani

Hakan ya saka Baffa yace, “Do you have a job?”

Girgiza masa kanta tayi tana miƙewa ta zare rigan aikin tace, “No let’s go”.

Tashi yayi shima cike da jindaɗi suka fito suka jera har wajen lifter, shiga suka yi yakai su downstairs, mota suka shiga suka bar cikin asibitin, babu nisa da Resturant ɗin da suka je.

.

_More Comments more post_🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️
[5/23, 8:43 PM] Oummu Ɗahirah: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTORS*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER’S ASSO📖*
”’®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓”’

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA’S FAMILY*_

.

*EPISODE Eleven*

Bayan sun shiga sun zauna ne Baffa ya tambaye ta abinda take so?

and she answered, “Everything she wants to eat”.

And he ordered Jallof Rice da ferfesun Kayan ciki with some drinks

and they started eating.

Ɗahira ta kalle sa tana murmusawa tace, “How do you get used to coming to your GirlFriend’s restaurant like this?”

Sosai Baffa yayi dariya yana kallon ta yace, “Why did you say that?”

“Uhmm only”.

Murmushi yayi a wannan karon yace, “ke dai ki faɗa abinda ke zuciyar ki”.

Maƙe kafaɗa tayi cike da yauƙin muryan ta tace, “Yaya Ni dai nasan kana min rowan ta ne shiyasa ma baka taɓa nuna min ita ba ko da a hoto ne, but nasan dai kuna fita irin wajen shaƙatawan nan”.

Baffa kallon ta kawai yake yi cike da burgewa, ji yake yi aran sa tamkar yace, “ke ce macen da na taɓa so a *RAYUWATA,* sai kuma ya girgiza kansa still yana murmushi yace, “My sister kenan, idan har zaki yarda wlh ban taɓa yin budurwa ba”.

Ƙwalalo idanu tayi tace, “kai Yaya dagaske kake yi ko wasa? How can it be said that Handsome Guy and you have no girlfriend? Ko dai yaya kana ɓoye min ne ba ka son na sani?”.

Cikin ido yake kallon ta cike da wani irin salo

Hakan yasaka ta ɗauke kanta tana ci gaba da cin abincin ta cike da yanga da ya zamar mata jiki, komi nata hakan take yin sa

Huro iskan bakin sa yayi be ɗauke ido a kanta ba yace, “Da gaske ƙanwata ban taɓa budurwa ba wlh, akwai wacce nake matuƙar ƙauna sai dai har yanzu na kasa sanar mata”.

Ɗago kai tayi tana kallon sa da mamaki kafin tace, “why?”

“Saboda kwarjinin ta..”

Dariyan ta ya saka shi yin shiru yana sake ƙure ta da idanun sa, sosai take dariya shi kuma yana bin ta da kallo cike da tsananin ƙaunar ta da burge shi da take yi

Sai da tayi son ranta sannan tace, “Yaya har akwai macen da zaka kasa sanar mata ƙaunar ka gare ta sabida kwarjini? Shin me tafi ka dashi ne? Kyau ko nasaba ko kuwa kuɗi? Ni na tabbata Yayana duk kwarjinin ta baza ta kai ka ba, kai dai kawai kace kana jin tsoron ta; abun kuma da ban san ka dashi ba”.

Baffa yace, “baza ki gane bane Sister, duk abinda kika lissafo tana dasu, sai dai kamar yanda nace miki kwarjinin ta da cikan kamalan ta ya zarce duk tunanin namiji ya iya tunkarar ta da soyayya, a kullum idan nayi yunƙurin zuwa gare ta da soyayyata sai inga girman ta da kwarjinin ta bazai bari na sanar mata ba, yanda nake ji a gaban ta da bugawar zuciya da zaran nayi yunƙurin sanar mata sai in kasa, sau ba adadi nayi hakan amma na gaza”.

Kallon Yayan nata kawai take yi cike da tausayin sa har yayi shiru, sannan ta ɗaura da cewa, “How can I help you find her love? Why don’t you let me know who I am; and I promise to tell her, sannan kuma zan taya ka yaƙi har sai ta amince da kai, Yaya ban ga macen da zata ƙi son ka ba komin kyan ta komi kwarjinin ta kuwa, sai dai idan har baka faɗa mata ba, Yaya ka cire tsoro ko fargaba ka sanar mata don Allah”.

Murmushi yayi yace, “na gode ƙanwata, haƙiƙa nasan kina son farin ciki na, sai dai bazan iya faɗa miki ko ita ɗin wace ce ba, but I promise I will try to tell her.”

Murmushi tayi kawai ba tare da tayi tunanin matsa masa akan sanin meyasaka be son sanar mata ba? Ita a komi nata tana ma mutum uzuri maybe yana da dalilin hakan ne

“To yaya na gane, but hurry up and tell her because soon Kaka will start talking about your marriage, kuma ka ga idan baka sanar mata ba za’ayi babu kai haka zakai ta zama a Gwauron ka”.

Baffa laughed and said, “Well shikenan my sister, but ni nafi son nayi aure lokacin da kema za kiyi”.

Zaro idanu tayi tace, “Yaya baka shirya auren ba kenan? Because I don’t have a real boyfriend.”

“Hmm you’re just saying, duk da ban taɓa ganin kin kawo kowa gida ba amma fa ina da tabbacin kina da masoyi don kuwa irin ki ba su rasa masoya”.

Shiru kawai tayi a wannan karon tana murmusawa, sai kuma ta duƙar da kanta tana ci gaba da juya spoon ɗin hannun ta cikin abincin

“Talk to us My dear, when will you show me my son-in-law?”

Ɗago kai tayi tana kallon sa tace, “Yaya Ni bani da gwani har yanzu, amma dai ka taya ni da addu’a”.

Sanyi yaji cikin ransa, cike da nuna tausayawan sa a fuska yace, “My dear Sister, I promise to help you. I pray to God to bless a good husband who loves you so much, kuma Allah yasa nan kusa za kiyi aure baza kiyi nesa damu ba”.

Dariya tayi cike da farin ciki tace, “kamar ka sani Yayana ko kaɗan ba na Son auren nesa sabida ba na Son nayi nesa da ku, sannan ba na son na dena aiki a hospital ɗin mu, Burina yana da nasaba da aiki cikin Hospital ɗin mu, ka ga kuwa ba na so na zama kamar Aunty Zulaiha da tabar aiki lokaci ƙanƙani, tayi nisa babu daman ci gaban ta a nan, nima ina so ayi alfahari dani cikin Family na; ya kasance ina ba da tawa gudunmawa wajen haɓɓaka shi”.

Filled with her love Baffa said, “God fulfill your dream My dear sister”.

“Ameen my brother, we should hurry back because my waking time is near, and I want to check on my patients.”

“To sarkin aiki ba kya gajiya?”

Murmushi tayi kawai tana ɗaukan Holandia tana sha, bayan ta gama ta’ajiye tana kallon sa tace,”Come on, I’m full.”

Ɓa ta fuska yayi yana kallon abincin gaban ta yace, “Baki ci da yawa ba ai?”

Marairaice fuskar ta tayi tace, “Yaya na ƙoshi ne”.

“Ok to tashi muje nima na ƙoshi tunda kin ƙoshi”.

Sai da ya biya kuɗin sannan suka fito suka shige cikin motan yaja suka nufi Hospital ɗin

Suna shiga haraban Hospital ɗin suka fito ya rufe motan suka jera suka nufin cikin asibitin

A reception Ɗahira ta hango aunty Zainab, tayi saurin zuwa wajen ta tana cewa, “Aunty Zainab”.

Juyo wa Aunty Zainab tayi tana kallon ta sai ta faɗaɗa fara’an ta tana faɗin “a’a! my sister. I have been asking Fadila Ni kam ban ganki ba tunda kuka fara aiki”.

Dariya Ɗahira tayi tana cewa, “wlh kuwa Aunty nayi ninyan zuwa har Office ɗin ki, to, aiki yayi yawa I don’t have time.”

Aunty Zainab kallon Baffa da ya ƙariso wajen su ya tsaya yana kallon su tayi tace, “oh ka ga masoya! ina kuma kuka je?”

Ɗahira kallon Baffa tayi suka haɗa idanu, sai ta saki dariya tana mayar da idanun ta kan Aunty Zainab tace, “aunty kenan abinci fa muka je ci da Yaya”.

Smiling, Aunty Zainab said, “Hmm Na ga alam ai”.

Baffa dake faman shafa kansa yace, “kin ji ABU da wata magana don mun fita da ƙanwata za kiyi mana fassara daban?”.

Ɗan waro ido tayi tace, “wai laifi ne don nace masoya kaji min yara?”

Yanda tayi maganar yasa su dariya gaba ɗaya

Still Ɗahira na dariyan tace, “Where’s Jinior?”

“Shigo wa ta kenan itama Fadila ta shigo shi ne ta’amshe shi”.

Baffa kallon Ɗahira yayi yace, “mu je kin ji My sister Kar mu biye mata”.

Hararan sa Aunty Zainab tayi tace, “to babu inda zata je.. kaje kai”.

Shima hararan ta yayi yana cewa, “ke fa kina son raina ni fa, wai ba tare kika gan mu ba?”

“Eh tare na gan ku amma aiken ta zanyi”.

Kafin yayi magana Ɗahira tayi saurin cewa, “Yaya ka je zan zo har Office ɗin ka”.

Gyaɗa mata kai kawai yayi jin wayan sa na ringing, zaro wayan yayi cikin aljihu yana yin gaba abin sa bayan ya ɗaga mata hannu alamun ya tafi

“Hmm Ni dai ina mamakin wannan shaƙuwa na ku, anya.. anya..”?

Ƙwalalo idanun ta Ɗahira tayi tana kallon ta tace, “kai Aunty babu daman Yaya ya nuna wa ƙanwar sa kula wa sai da wani abun? Ni fa na ce miki abinci muka je ci”.

“To ai nima ba fitar da kuka yi bane nake magana, mu je kawai”. Aunty Zainab ɗin taƙarike maganar ta tana yin gaba

Ɗahira tabi bayan ta suna sauya hiran su

Office ɗin Aunty Zainab ɗin suka shiga, bayan sun zauna ta ɗauko mata wasu files ta miƙa mata

“Ga shi don Allah Ɗahira, ki kai wa Dr. Said don ba na son ya sake damu na”.

Amsar files ɗin Ɗahira tayi tana kallon ta tace, “Aunty who is Dr. Said?”

“Aff baki san shi ba ashe, yana nan office ɗin sa na kallon nan wajen ta hannun dama”.

“Ok sai na sake zuwa kenan Aunty?” Tafaɗa tana miƙewa tsaye

Murmushi Aunty Zainab tayi tace, “Tom My Sister, ki gaishe dasu Kakus me ran ƙarfe”.

Dariya tayi tace, “insha Allah zai ji”.

Daga haka ta fice bayan sun sake sallama.

Tana fita kamar yanda Aunty Zainab tace mata hakan tayi ta nufi hannun daman ta, tana zuwa ta soma dudduba sunayen Offices ɗin, nan kuwa taci karo da sunan sa a saman nashi Office ɗin, Nocking ta soma yi

Dr. Said dake zaune yana ma wata budurwa bayani yayi saurin ɗago kansa cike da fargaba, kallon Budurwan yayi yace, “Yi maza ki kwashe magungunan nan ki saka a jaka”.

Babu musu kuwa ta kwashe ta zuba a jakan ta

Shi kuma ya gyara zaman sa yana rufe Files ɗin dake gaban sa tare da kifa wa sannan ya ba da umarnin shigowa

Turo ƙofan Ɗahira tayi da sallama ta shigo

Idanun sa ƙyar a kan ta ya’amsa mata sallaman yana kallon ta, duk da be santa ba amma ya ga tana masa kama da Familyn Dr. Al’ameen

Ita kuwa ƙariso wa wajen Table ɗin sa tayi ta miƙa masa files ɗin tace, “ga shi Aunty Zainab ta ce in kawo maka”.

Sai a lokacin ya ɗan saki fuskar sa yana bin ta da wani irin kallo, cike da murmushi a face ɗin sa ya miƙa hannu ya’amsa yace, “Ok thanks”.

Juya wa kawai tayi ta fice ba tare da ta kalli ko budurwan dake zaune ba

Har ta fice yana kallon ta cike da tsananin burge sa da tayi, sosai Ɗahira ta ɗauke masa hankali da kyawun ta da cikan halittan ta, musamman ma da take siririyan mace, domin yana ƙaunar irin su. sai faman doka murmushi yake yi ya kasa ɗauke kai daga ƙofan da ta fice

Sai da budurwan nan ta buga table kafin ya dawo hayyacin sa

Ɗan shafa kan sa yayi yana kallon ta kafin yace, “kin tabbatar cikin nan be wuce 5 Months ba?”

Kallon sa tayi a yatsine kafin tace, “Dr. Na rigada na faɗa maka wata 4 ne”.

“Ok bari in zo”.

Miƙe wa yayi ya nufi wani dogon sip ya buɗe, ya soma bincika kayan aikin da zai yi mata amfani wajen cire mata cikin.

Wannan shi ne halayyan Dr. Said, yana cire wa ƴan mata ciki ba tare da sanin kowa a cikin a sibitin ba, domin doka ne idan har aka kama ka kana irin wannan cin amanar za’a kore ka, asibitin kwata-kwata basu yarda da aikata wannan zunubin ba.

⚫⚫⚫

Ɗahira sai da ta koma Office ɗin ta tayi sallah kafin taje ta ƙara duba patients ɗin ta, tana dawowa ta haɗa komi nata da abinda zata buƙata ta fito ta rufe office ɗin

Office ɗin Baffa dake hawa na biyu ta nufa, dai-dai zata shige cikin office ɗin Yusra ta fito nata office ɗin dake kallon na Baffa, kallon juna kawai su kayi suka ɗauke kai, Yusra har da wani sake tamke fuska ta wuce abin ta tana jan tsaki

Ɗahira juya kanta tayi tana kallon ta cike da mamakin ta, har yanzu ta rasa meyasaka Yusra take nuna mata tsana

Bata gama tunanin ta ba Baffa ya buɗe ƙofan yana kallon ta

Murmushi ta ƙirƙiro tana kallon sa tace, “Yayana na gama”.

“Ok Muje Nima tafiya zan yi na gama na yau kuma”.

Sai da ya rufe ƙofan kafin suka tafi.
[5/23, 11:10 PM] Oummu Ɗahirah: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTORS*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER’S ASSO📖*
“`®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓“`

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA’S FAMILY*_

_Ga masu min magana akan littafin JARUMAI kuyi haƙuri don Allah an samu matsala ne shiyasa na dakata amma insha Allahu zan ci gaba very soon._

.

*EPISODE Twelve*

Fitowar ta kenan daga wanka taji wayan ta tayi ƙaran shigowar Text, kallo ɗaya tayi wa wayan ta ɗauke kai ta nufi gaban dressing mirror, zama tayi kan stool tana tsane gashin kanta, bayan ta gama sai ta ɗau handrayer ta soma busar da dogon baƙin gashin nata me tsananin santsi, sabida santsin sa ne ma ba ta yin kitso sai dai ta riƙa gyarawa

Ajiye handrayern tayi bayan ta gama ta soma shafa Lotions ajikin ta, tana gamawa tayi Light makeup a baby face ɗin ta, sai ta miƙe ta ciro kayan ta tasaka

Doguwar riga ce robber kalan ruwan hanta, babu kwalliya a rigan ko ɗaya sai dai wuyan V yake dashi wanda aka saka masa bakin less white colour, haka ma dogon hannun a ƙarshen an saka masa bakin less, Hula ta saka fari wanda ya kasance na rigan ne, tayi kyau sosai kasancewar ta kyakykyawar

Wayan ta kawai ta ɗauka ta fito Parlour.

Fadila na zaune tana cin abinci at the same time tana latsa wayan ta

She Sit on the One sitter next to Fadila on the Two sitter

Ɗan kallon ta kawai tayi sai ta ɗauke kanta ta mayar kan plasma t.v dake aiki babu me kallo, shiru tayi na ɗan wani lokaci sai kuma ta ɗago wayan ta ta soma latsawa

Da text ɗin da ya shigo wayan ta ɗazu ta fara cin karo, har zata wuce kuma sai ta ga kamar da number akayi mata Text ɗin wanda ada azaton ta MTN ne su kayi mata

Buɗe wa tayi da mamaki take kallon text ɗin, har sake murza idanuwan ta tayi tana sake ƙura manyan idanun nata, jikin ta na rawa ta soma karanta wa:

_”Aslm alaikum ya ke kyakykyawa abar so ga kowa, za kiyi mamakin ganin wannan text ɗin nawa aduk lokacin da ya riske ki, amma ba abun mamaki bane domin an ce me son ɗan tsuntsu shi ke bin sa da ji fa, Ɗahira na daɗe da ƙaunar ki cikin zuciya ta, sai dai har yanzu na kasa fitowa fili na sanar miki, ba don komai ba sai don ban san ya zaki amshe Ni a matsayin Masoyi ba, but know that I love you and I will continue to love you until my breath goes out, I Love You .. I love You with all my heart.”_

_MASOYIN KI✍️_

Ta maimaita text ɗin ya fi sau biyar, gaba ɗaya ta ruɗe domin abin da bata taɓa gani bane a gare ta, tunda take babu wanda ya taɓa nuna yana son ta kuma babu wanda ya taɓa tura mata text da sunan masoyin ta, hakan ne ya saka ta shiga wannan ruɗun tare da bugawar zuciya me tsanani

Zumbur ta miƙe ta nufi ɗakin su

Fadila tabi bayan ta da kallo cike da mamakin sauyawan ta lokaci ɗaya, amma sai dai bata ce komi ba ta maida hankalin ta kan wayan ta.

Tana shiga ta nufi kan gadon ta ta zauna, sake ɗago wayan nata tayi ta sake karan ta text ɗin

“Anya wanda ya turo text ɗin nan ba mistake yayi ba?” Tafaɗa cikin sanyin murya tana bin wayan nata da kallo

Ƙure Numban tayi da idanu ko za ta san me irin shi but ko kaɗan bata taɓa ganin ma irin Numban ba, domin kuwa sabon Numban da MTN suka fito dashi ne me 091

Har ta latsa da ninyan kira taji ko wane ne sai kuma ta yanke da sauri don bata san me zata ce ɗin ba ko da an ɗauka, zuciyarta ta bata shawaran kar ta sake ta kira wataƙil mistake ne aka yi, kuma be kamata ta kira ɗin ba, da haka ta’ajiye wayan ta kwanta tana tsira wa waje ɗaya idanu cike da tunani

Da sauri kuma ta tashi zaune tana faɗin, “amma kuma ya kira suna na ai, Of course I am. This text is for me, but who is it?”

Duk yanda taso yin tunanin gano wanda zai iya mata amma ta kasa, koma wa tayi ta kwanta tana ajiyan zuciya.

 

⚫⚫⚫

Yana kwance saman kujeran sa yana faman latsa wayan sa yana murmushi

Wayan ce ta soma ringing hakan ya saka ya dakata da abinda yake yi yana kallon baƙuwar Numban da aka kira sa, shiru yayi na ɗan wani lokaci kafin yayi peacking call ɗin ya saka a kunne

Daga can ɓangaren muryan mace ce ta doki dodon kunnen sa

“Aslm alaikum”.

“Wa’alaikis salam”. Slowly he gets up and sits up

She smiled and said, “Do you know who Dr. Al’ameen Abubakar Al’ameen is?”

Baffa da yayi tsimi yana sauraron muryan ta sai be ce komi ba

Hakan ya bata damar ci gaba da faɗin, “My name is Dr. Ayush Abdulkarim and I work at your Family Hospital.” Sai kuma tayi shiru tana tunanin abinda zata ce

Baffa yace, “to Allah yasa dai lafiya? But I don’t know you.”

She smiled and said, “Yes, you will never know me because I have just started working at the hospital, but idan har ka bani dama zan iya bayyana maka kai na domin mu san juna, tunda ina son alaƙar mu tayi nisa ne, that’s why.” so I asked for your number and I called you “.

Shiru yayi cike da mamakin ta

“To me zai sa ta so ƙulla alaƙa dashi?..”

Be gama guntun tunanin sa ba ta katse sa da faɗin, “I’ll meet you tomorrow insha Allah, I’ll come to your office. Byee Take care.” Bata jira me zai ce ba ta kashe wayan

Shi kuma ya ciro wayan yana kallo, ya jima a haka yana tunani kafin ya’ajiye wayan ya miƙe ya shige toilet don ɗauro alwala.

 

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

Dariya suka kwashe dashi har da tafa wa

“Wow gaskiya kin yi ƙoƙari Ayush, amma kina ganin zaki iya jawo hankalin shi gare ki har ya manta da wancan shashashan?”

Murmushi me ma’anoni da dama Ayush ta saki tana kallon Shakira tace, “ke dai ki zuba idanu ki gani, da zaran mun haɗu ma zan sanar masa ina ƙaunar sa don ma ya sani tun yanzu”.

Dariya Shakira tayi tace, “Thanks.. sai kuma mu jira muga shirin namu zai yi aiki ko kuwa..”

“Idan ma bazai yi ba sai mu sauya salo”. Ayush tafaɗa itama tana dariyan

Jinjina kanta Shakira tayi cike da jindaɗi sannan tace, “Is it tomorrow when we meet?”

“Yeah insha Allah”. Cewar Ayush tana ɗaukan jakan ta sannan ta buɗe murfin motan

Daga nan sallama su kayi ta fito cikin motan, ita kuma Shakira taja tabar ƙofar gidan su Ayush ɗin

Tana nan tsaye tana ɗaga mata hannu har ta ɓace ma ganin ta, murmushi ta saki tana faɗin, “Uhmm Dama ta biyu kenan, yanzu komi zai soma min daɗi, tabbas Buri na zai yi saurin cika, da wannan shirin naki Ni kuma zan cika tawa Burin”.

Dariya tayi ta shige gidan su

Babban gida ne me sasa biyu, na farkon shi ne na mahaifin ta, inda akwai ɗakuna Huɗu da kichen a bakin ƙofan gidan; sai kuma bayi dake can ƙuryan sasan wanda aka rufe sa da fale-fale

Ƴaƴan Baban su su goma ne maza da mata kuma itace ta Biyar, sannan duk mahaifiyar su ɗaya.

Ɗayan sasan kuma Ƙanin Baban su ne ke zaune da matar sa, yaran sa shida shima maza da mata.

Ba wani kuɗi suke dashi ba amma suna da rufin asiri dai-dai gwargwado, mahaifin su yana ɗauke musu duk wani nauyi da ya rataya akan sa

A cikin ƴaƴan sa mata Ayush ce kaɗai tayi karatu me zurfi har matakin Doctoring, Wanda hakan shi ne burin ta, don tasan shine hanya ta farko da zata iya bi wajen cin ma babban burin ta, wato auren me kuɗi

Tun tana yarinya ta taso tana jin labarin Familyn Dr. Al’ameen Abubakar Khabeer Cindo, kuma sosai take jin labarin Hospital ɗin sa da ya shahara a faɗin Nigeria, wanda idan har za’a yi kwatance, to, da shi ake yi. Wannan dalilin ne ya saka ta ɗaukar ma kanta alƙawarin sai tayi aiki a cikin asibitin sabida ta nuna wa ƙawayen ta da ƴan uwanta tafi su

Zuwan ta asibitin da yanda taga tsaruwan Hospital ɗin tare da Familyn gaba ɗaya sai tayi sha’awar kasancewar ta cikin FAMILYN, burin ta a yanzu shi ne ko ta halin ƙaƙa ta shiga gidan itama ta zama ɗaya daga cikin familyn da su kayi Suna a faɗin Nageria; kuma suke ji da kuɗi da Izza

Binciken Farko da tayi shi ne sanin mutanen gidan, duk da bata samu labari sosai ga jama’an gidan ba amma ta gano Maza biyu ne kaɗai a cikin gidan kuma duk basu yi aure ba, ɗayan yana Aiki a ƙasar Turkey, ɗayan kuma yana aiki a Hospital ɗin su

Sai ta yanke shawaran fara shiga jikin ƴan gidan don samun damar kusanci gare su, abun kuma sai yazo mata da sauƙi office ɗin ta na kusa dana Ƙanwar Baffa ne wato Shakira, don haka ta nemi ƙawance da ita lokaci ɗaya kuma Shakira ta’amince.

A yau ɗin kuma sai ga Shakira ta zo mata da wani aiki akan jan hankalin Baffa ya faɗa tarkon ta duk a sabida a raba shi da Ɗahira, ba tare da Shakiran ta san da cewa Ayush ɗin dama tana neman hanyan da zata shiga jikin ɗaya daga cikin samarin gidan bane; don ta samu ta aure sa.

 

.

 

_plz kuyi *Vote* da Comments._
[5/24, 1:37 PM] Oummu Ɗahirah: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTORS*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER’S ASSO📖*
“`®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓“`

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA’S FAMILY*_

 

*EPISODE Thirteen*

Ahankali ta buɗe kyawawan idanun ta tana sake lumshewa cike da kasala, hannu biyu ta sanya ta riƙe kanta dake faman sara mata a hankali, tayi wajen mintuna biyar kafin ta soma yunƙurin tashi zaune tana jingina bayan ta da jikin gadon, sake lumshe idanun ta tayi tana soka hannu ƙasan pilon ta tazaro wayan ta ta kunna, sai da tasan ya gama kunnuwa kafin ta buɗe idanun ta tana kallon screan ɗin wayan, agogo ta duba taga ƙarfe 07:45am.

Ajiye wayan tayi tana sakin hamma kafin ta zuro ƙafafuwan ta ƙasa tana shirin sauka taji ƙarar shigowan text message, wayan ta ɗauka ta duba taga Numban jiya ne da aka yi mata Text dashi, da sauri ta buɗe jikin ta na rawa ta soma karanta wa

 

_ “Aslm alaikum Good morning Sweetie, I hope you are well? Take care of yourself God bless you then work” _

_MASOYIN KI✍️_

 

Jujjuya maganar take yi cikin ranta cike da tunani kala-kala, sosai take mamakin wannan mutumin da yake iƙirarin shi ɗin masoyin ta ne

“Ko dai ya San ni ne? But who is he? Why bazai fito fili ya nuna min kan sa ba?” Tafaɗa maganar a fili

Ajiye wayan tayi tana ninyan tashi sai kuma ta dawo ta zauna tana ɗaukan wayan tayi dialling Numban, Amma kuma a kashe yake

Shiru tayi tana riƙe da wayan a hannu, ta daɗe tana nan zaune tana faman tunani tare da son gano wanda ke mata wannan text ɗin, ganin zata ɓata lokacin ta tamiƙe ta shige Toilet, wanke bakin ta tayi ta fito ta ɗau ɗan ƙaramin Hijabin ta tasaka a saman kayan barcin ta masu taushi ta fice

Gaba ɗayan su suna zaune a dainning suna breakfast, Abbu ne kaɗai ya miƙe tsaye yana goge bakin sa da tissue alamun ya gama nashi breakfast ɗin

“Abbu Good morning”. Tafaɗi hakan lokacin da ta’iso wajen tana kallon sa da murmushi

Shima murmushin yayi yana kallon ta ya’amsa mata cike da kulawa, sannan ya tambayi “Ya ya ta tashi?”

Ta’amsa mishi tana zama kan kujera kafin ta gaishe da Mahaifiyar ta da Umma

Abbu said, “Fadil, get up and let me drop you off.”

“To Abbu”. Cewar Fadil ɗin yana miƙewa ya nufi ɗakin Umma don ɗauko School Bag ɗin sa

Duk a dawo lafiya sukai ma Abbu ɗin kafin ya fice, Fadil shima ya fito ya bi bayan sa da sauri

Fadila ta soma tashi a cikin su ta nufi saman sofa ta zauna, daga baya kuma Umma da Aunty Amarya su ma suka tashi aka bar Ɗahira ita kaɗai tana karyawa

Bayan ta gama itama miƙewa tayi ta shiga ɗakin su, tana shiga ta cire kayan ta tashiga wanka, bata jima ba ta fito tana ɗaure da Showel a jikin ta

Ƙarisawa tayi ta ɗau wayan ta dake faman ruri, sai da ta zauna kan stool dake gaban mirror kafin ta’amsa call ɗin

“Aslm alaikum Yayana na kaina”.

Sautin murmushin sa ne ya doki kunnen ta kafin yace, “Wa’alaikis salam My dear Sister, kin tashi lafiya?”

“Lafiya lau yaya, kaifa ya kake?”

“Alhmadulillah My dear, har kin fito?”

Girgiza kanta tayi kamar yana ganin ta kafin tace, “a’a Yaya yanzu dai zan shirya in fito”.

Baffa yace, “ok Ni na rigada na fita tun 07:00am. Ina da Theater, but my sister ki je ɗaki na ki ɗauko min takardu dana manta ban ɗauka ba, suna nan akan drower na ajiye su”.

“To Yaya amma ka kulle ɗakin ne?”

“Eh na kulle kiyi amfani da keey ɗin wajen ki”.

Ɗahira tace, “to Yaya”.

“Allah ya kawo min ke lafiya ki kula da tuƙi kin ji?”

Murmushi ta saki cike da jindaɗi kafin tace, “insha Allah Yaya bye”.

Daga nan katse wayan yayi ita kuma ta’ajiye wayan ta soma shafe-shafen ta.

 

 

 

⚫⚫⚫

Yana sauke wayan a kunnen sa ya’ajiye saman table yaci gaba da aikin sa cikin Computer

Nocking yaji ana masa, be ɗago kai ba ya ba da umarnin shigo wa

Buɗe ƙofan tayi ta shigo da siririn sallama me haɗe da kisisina

Hakan ya saka ya ɗago kansa yana sauke idanun sa a kanta, sannan ne ya’amsa mata yana ci gaba da kallon ta

Murmushi tayi wanda ta san yana narkar da duk namijin da ya gani, cikin takun ta da son burge sa ta’iso wajen tana kallon sa still tana murmusawa tace, “Dr. Al’ameen Abubakar Al’ameen”.

Baffa da ya sauke kansa ƙasa yaci gaba da aikin sa, jin ta kira sunan sa sai ya sake ɗago kansa yana kallon ta

Bata bari yayi magana ba tariga sa da cewa, “Can I sit down?”

Be ce mata komi ba illa nuna mata kujera da yayi da hannu

Zama tayi tana kallon sa cike da wani irin salo tace, “nasan baka gane Ni ba ko? I am Dr. Ayush Abdulkarim and I called you yesterday”.

Sai a lokacin Baffa ya ɗan saki fuskar sa kafin yace, “Allah Sarki ai ban gane ki ba, amma fa bakin ki ya riƙe suna na da yawa”.

Ayush cike da yanga tace, “ai ba baki na bane ya riƙe sunan ka ba, sunan ka ne ya zauna a baki na, daɗin sunan ka ke sakawa ba na gajiya da faɗin sunan ko da kuwa na so bari”.

Murmushi kawai yayi yana kallon ta

Ita kuma sai ta gyara zaman ta da kyau tana sake kafe sa da idanu tare da son burge sa tace, “kayi haƙuri da kiran da nayi maka jiya amma zuciyata ce ta kasa haƙuri da son ƙulla alaƙa da kai, idan har baza ka damu ba zan so mu zama friends duk da kuwa nasan nayi maka katsalandan cikin rayuwa, amma gaskiya bazan ɓoye maka ba ka burge Ni ne sosai shiyasa nake son wata alaƙa me ƙarfi ta shiga tsakanin mu”.

Numfashi Baffa ya sauke yana kawar da kansa kafin yace, “naji bayanan ki A’isha duk da kuwa Ni ɗin ba na abota da mata, sai dai bazan iya watsa miki ƙasa a idanu ba musamman yanda kika yabe Ni kuma kike son ƙulla alaƙa dani, babu damuwa”. Yaƙarike maganar yana kallon ta

Murmushi tayi tace, “gaskiya kana da sauƙin kai ba kamar yanda nayi zato ba, naji daɗi da ka amshe Ni hannu bibbiyu Allah yasa hakan shi yafi alkhairi”.

Baffa smiled and said, “ameen no worries”.

Ayush miƙe wa tayi tana kallon sa tace, “Let me go and see you next time, friend?”

 

“Ok Thanks friend”. Yayi maganar cikin kwaikwayon muryan ta

Sai suka yi dariya gaba ɗaya cike da nishaɗi

Ɗaga masa hannu tayi tana murmushi kafin ta juya ta nufi ƙofa ta buɗe

Dai-dai lokacin itama Ɗahira ta saka hannu za tayi Nocking

Ganin an buɗe ƙofan shiyasa ta janye hannun ta tana kallon Ayush da itama ta kafe ta da nata idanun tana ci gaba da murmushin ta

Kallon kallo sukai wa juna na ɗan sakonni kafin Ɗahira ta janye jikin ta a hanya don Ayush ɗin ta wuce

Fito wa Ayush tayi still tana kallon Ɗahira da ita kuma ta cire nata idanun akan ta tana gyara zaman Eyeglasess ɗin ta, sai kuma ta sake kallon ta har yanzu Ayush ɗin itama kallon ta take yi, hakan yasa Ɗahira ɗan sakar mata murmushi cikin sanyin muryan ta me daɗi tace

“Sannu ko”.

“Yauwa sannu”. Cewar Ayush itama tana faɗaɗa murmushin ta

Ɗahira bata sake cewa komi ba ta buɗe ƙofar ta shige tabar Ayush nan tsaye tana bin ta da kallo kamar t.v

Tana shiga ta sauke idanun ta kan Baffa da shima har yanzu yana murmushi be ci gaba da aikin ba

Yana ganin ta ya sake faɗaɗa murmushin sa yace, “welcome my dear Sister”.

Murmusawa tayi kafin ta soma takowa ta’iso wajen; ta zauna a kan kujeran da Ayush ta tashi

“Dear Brother Welcome to work”. Sai kuma ta’ajiye takardun hannun ta a saman table ɗin tana faɗin “ga shi Yaya”.

Ɗauka yayi yana dubawa cike da jindaɗi ya sake kallon ta yace, “yauwa my dear wlh Sam na manta, kuma Abba ne yace na taho masa dasu ashe na barsu a gida, yanzu bari inje in Kai masa”.

Ya miƙe tsaye riƙe da takardun a hannu

Itama miƙewan tayi tana gyara zaman jakar ta a kafaɗa tace, “nima bari in wuce sai anjima”.

Za gayowa yayi suka jera suka nufi bakin ƙofan, shi ya buɗe ƙofan ya matsa mata ta wuce sannan shima yafita.

 

 

⚫⚫⚫

Kallon sa Hajja Fatu tayi cikin ƙasa-ƙasa da murya tace, “Dr. Zubairu idan har ka yi min aikin nan tabbas Ni da kai yanzu muka ƙulla, duk abinda kake so zan taimaka maka da shi, da kuma yarda na zaka ci gaba da shigo da kayan ka ba tare da ka sami wata matsala ba, Ni dai kawai fata na ka shiga jikin su sosai ta yanda zaka gano min duk wani sirri na cikin asibitin nan, kai Ni ban cire maka Mijina ba har shi ina so ka shiga jikin sa, idan har…”

Maganar nata ne ya maƙale sakamakon turo ƙofan da aka yi, idanuwan ta kamar za su faɗo ƙasa haka take bin ƙofan da kallo, ganin wacce ta shigo ɗin ne ya saka ta daka mata tsawa cikin fusata tace, “Are you going to come into my office without my permission?”

Cikin rawan murya Safna da ta ƙame a bakin ƙofan tace, “don Allah Dr. Kiyi haƙuri wlh nayi Nocking naji shiru shi ne na shigo”.

Harara ta balla mata tace, “uban Nocking kika yi, kin yi Nocking ɗin ne zamu kasa ji? Shashashan yarinya kawai”.

Safna saukar da kanta ƙasa tayi duk jikin ta rawa yake yi

Dogon tsaki Hajja Fatu tayi tace, “uban me ya kawo ki to?”.

Da sauri Safna said, “These are the files that Dr. Abubakar told me to bring to you, in the Female ward to check on the Patiens brought in, and then one needs an emergency theatre”.

Tsakin Hajja ta kuma ja kafin ta sake balla mata harara tace, “dalla bani ki ɓace anan”.

Kamar dama jira take yi ta’iso da saurin ta tazuba files ɗin gaban ta ta juya ta fice da mugun sauri, tana fita ta sauke ajiyan zuciya cike da tsoro, sai da ta sake juya kanta ta kalli ƙofan kafin ta sake sauke wani ajiyan zuciyan, cikin ranta take cewa, “waii! wannan matar shegiyar mata ce wlh duk ta tsorata Ni da wannan uban tsawar nata, ko ma uban meye suke tattaunawa da ba ta so inji? Munafuka kawai”.

Sai ta sake kallon ƙofan sannan kuma ta juya tayi gaba da sauri, Office ɗinta babu nisa da wajen tayi saurin shige wa.

 

 

Fadila da ta fito cikin office ɗin ta kusa dana Safnan; tana sanye da labcoat ɗin ta a jiki ta nufi office ɗin Hajja Fatu

Hajja Fatu wacce taci gaba da yin ma Dr. Zubairu bayani ta sake jin anyi Nocking, cak ta tsai da maganar ta tana kallon ƙofan

while shima Dr. Zubairun yabi sahun ta

Siririn tsaki taja tana ba da umarnin shigowa

Fadila opened the door and walked in

Ganin Fadila ce hankalin Hajja Fatu ya ɗan kwanta har da ƙirƙirar murmushi tana yafa ma fuskarta

Cikin miskilancin ta Fadila tace, “Hajja Drugs ɗin nan zaki bani”.

Hajja bata ce komi ba ta buɗe drowan table ɗin ta ta ɗauko keeys ta miƙa mata tana faɗin, “Take” look at the Sif there and pick it up.”

Amsa kawai Fadila tayi ta nufi wajen sif ɗin ta saka keey ɗin ta buɗe ta ciro wanda zata ɗauka ta rufe ta dawo mata da keeys ɗin, tana amsa ta juya ta fice

Ita kuma Hajja ajiyan zuciya ta sauke tana sake mayar da hankalin ta kan Dr. Zubairu da shima yake kallon ta

“Dr na rigada na gane duk abinda kike nufi, kar ki damu zan miki duk abin da kika ce, kin san dama ban da matsala da Dr. Noor tunda Aboki na ne, to sauran ma ba wahala bane tunda muna mutunci dasu, sai dai kuma gaskiya kafin nasan komi zan ja lokaci da yawa, sai dai mu riƙa bin komi a sannu a hankali”.

Washe baki Hajja tayi tace, “Na san da haka Doctor, Ni dai fata na Buri na ya cika, Miji na ko kaɗan ba ya kyauta min matsalan nan duk daga wurin sa yake, idan da ya saka Ni cikin su ai da ba haka ba, amma koda yake..”

Sai kuma tayi shiru tana jan numfashi, cike da takaici tace, “Dr zuwa gobe insha Allahu zan san yanda za’ayi kayan ka su shiga ciki, baka da matsala da wannan”.

Dariya yayi yace, “Na san haka Dr. Shiyasa tun farko na zaɓe ki, Allah dai ya cika mana burin mu gaba ɗaya”.

“Ameen Doctor”. Hajja Fatu tafaɗa tana murmusawa

Tashi yayi yace, “Let it be tomorrow,”

“Ok”. tace dashi tana miƙe wa

Sallama suka sake yi kafin ya fice

Ita kuma Files ɗin da Safna ta kawo mata ta ɗauka a ran ta tana ƙorafin mijin nata, sam bata so kawo mata aikin nan da yayi ba tunda lokacin tashin ta yayi, tsaki taja ta ɗau abinda zata ɗauka ta fice.
[5/25, 7:48 AM] Oummu Ɗahirah: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTORS*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER’S ASSO📖*
“`®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓“`

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA’S FAMILY*_

 

*EPISODE Fourteen*

Sai da ta gama rubutun da take yi kafin ta ɗago kanta tana kallon matar dake zaune gaban table ɗinta ta cikin farin Glasses ɗin ta, murmushi ta sakar mata tana miƙa mata Peppern tace, “ga shi sai kije ki siyo magungunan ciki, za su rubuta miki yanda zaki riƙa sha”.

Matar amsan Peppern tayi sannan tayi mata godiya tana miƙe wa ta fita

Wasu files guda biyu ta janyo ta buɗe na saman tana dubawa

Wayan ta dake ajiye saman Deks ɗin ta yayi ƙaran shigowar Text har sau biyu

Janye idanun ta akan file ɗin da take dubawa tayi ta mayar kan wayan nata, sai kuma ta saka hannu ta ɗauka ta soma buɗe saƙon, mutumin dai da ya soma tura mata text ne daga jiya zuwa yau, saƙon farko an rubuta

 

_”Aslm laikum I hope you have a good day my beauty? How works?” _

 

Ɗayan kuma da ta buɗe an rubuta

 

_”Abu ɗaya da bazai taɓa ƙare wa ba shi ne soyayyar mu da ke, sabida ke kaɗai ce a cikin zuciya ta, ina fata zaki amshe Ni hannu bibbiyu domin in fito fili in bayyana miki tsantsan ƙaunar da nake miki, wlh soyayya ta a gare ki gaskiya ce, ina ƙaunar ki fiye da yanda zan faɗa miki”._

_MASOYIN KI…✍️_

 

 

Ɗahira tayi tsawon mintuna goma bata sake wani motsi ba, zuciyar ta ta gaza ɗaukan waɗannan abubuwan dake faruwa da ita, tunani barkatai sun zo sun yi mata diran mikiya sun hana ta saƙat

Daga ƙarshe kiran layin tayi amma a kashe, ajiye wayan tayi ta miƙe tana gyara zaman Labcoat ɗin ta kafin ta ɗau wayan ta saka cikin aljihun Labcoat ɗin, ta kwashe files ɗin a hannu ta nufi ƙofa, fita tayi ta nufi ɗakunan da Patients ɗin ta suke ta soma bi tana duba su

Bayan ta gama ta dawo Office ɗin ta, cire Labcoat ɗin tayi ta rataye a Hanger kafin ta nufi cikin Toilet ta ɗauro alwala ta fito ta gabatar da sallan azahar

Bayan ta idar ta tattara komi nata ta fito ta rufe Office ɗin, ta hau lifter ya kai ta downstairs

Inda motan ta yake fake ta nufa cikin tafiyan ta kamar baza ta taka ƙasa ba, wayan ta na maƙale a kunnen ta suna waya da Baffa

Mota ta gani a bayan nata ta yanda babu yadda za’ayi ta wuce sai an ɗauke, kallon motan tayi, ta gane me shi, sai ta tsaya kawai tana waige-waige tana ci gaba da wayan ta, wajen mintuna 5 kafin su gama call ɗin ta nufi jikin motan ta tatsaya tana kallon hanya, ga rana sosai yana gasa ta

Tsaki taja tana buɗe motan ta shiga tabar ƙafafun ta a waje, shiru tayi tana jingina bayan ta a kujeran, idan zata ce ranta be ɓaci ba ƙarya tayi, tabbas Yusra ta soma shigan mata hanci da ƙudundune, me zai saka ta’ajiye mota a bayan nata tunda tasan koda yaushe zata iya fice wa? kuma ba wai babu sauran wajen parcking bane tsaban iskanci ne da neman magana

Kusan mintuna 20 da zaman ta, har ta gaji ta fito da ninyan zuwa har Office ɗin ta tayi mata magana, sai ta hango ta ta taho tana shirin buɗe motarta ta shige

Kallon ta kawai Ɗahira take yi kuma sarai tasan ta ganta, amma dayike ita ɗin ƴar wulaƙanci ne ta ɗauke kanta tana tamke fuska ta shige taja motar a guje tabar cikin asibitin

Numfashi Ɗahira ta sauke kafin itama ta shige cikin nata motan, tana ji a ranta idan har ta sake mata haka tabbas zata fuskanci fushin ta, ko kaɗan ba ta juran wulaƙanci shiyasa ba ta shiga harkan da ba nata ba

Motan taja itama ta fice cikin Hospital ɗin.

 

 

⚫⚫⚫

 

*ONE MONTH*

A cikin wannan watan abubuwa da dama sun faru.

Ɗahira ta dage sosai wajen aikin ta ko kaɗan ba ta wasa dashi, ta saka abun a ranta don haka sosai ta jajirce wajen taimaka wa Hospital ɗin nasu

A yanzu ta dena komawa gida har zuwa dare take kaiwa, aiki take yi tuƙuru wajen taimakon mara su lafiya

Da farko mahaifin ta yayi mata magana akan ta dena cika ma kanta aiki, tunda dama ita dutyn safe take yi zuwa rana

A cikin su huɗun ita da Shakira da Yusra dutyn safe suke yi, ita kuma Fadila na rana zuwa dare, sannan kuma akwai masu yin dare zuwa safe

Fadila fannin zuciya ne aikin ta, don haka bata cika samun patients ba a farko that’s why take komawa gida idan bata da aiki, in ta zo ta duba patients ɗin ta sai ta koma gida

Koda Abbu yayi ma Ɗahira magana a kan ta dena cika ma kanta aiki, sai tace masa “ai zata iya,” sannan tana yi ne don taimakon jama’a tunda babu abun da zata yi a gida gwara ta zauna ta taimaka

Hakan yayi musu daɗi sosai, musamman ma Kaka dasu Big dady, kullum saka mata albarka suke yi, sun tabbatar ita ɗin jajirtacciya ce aikin kawai ta saka a gaba

Yanzu ko kaɗan bata da lokacin da suke fita da Baffa sai dai jefi-jefi zai zo ya ɗauke ta su je restaurant su ci abinci

Baffa yanzu sosai suka shaƙu da Ayush don ko yaushe suna tare, a waya ne ko a gida, wasu idan suka gansu suna tunanin ko soyayya suke yi, sai dai shi kawai ya ɗauke ta a friend ne ko kaɗan ba ta ransa, Ɗahira ce har yanzu yake gani a matsayin Masoyiya

Itama ɗin Ɗahiran tana yawan ganin su da Ayush ɗin, sai dai bata taɓa mashi maganar ta ba

Yanzu masoyin ta na Ɓoye sosai kullum sai ya turo mata text ɗin nan, safe, rana da dare, idan ma be turo ba har ba ta jin daɗi, sosai yanzu take jin sa cikin ranta, kuma kullum sai tayi yunƙurin kiran layin amma a kashe, but bata taɓa tunanin itama ta tura masa text ba

Burin ta a yanzu tasan masoyin nata, sabida a yanzu zuciyar ta ta yarda dashi; soyayyar sa ne tsantsa a cikin ran ta.

 

 

 

*___________________________*

 

Yau ta kasance Sunday, kuma yau ne taron Familyn su kasancewar duk ƙarshen wata suna taruwa a General parlour aci abinci tare, masu matsaloli su faɗa a magance musu

Breakfast ne kawai kowa ke yi a part ɗin sa, Lunch kuma da dinner sai su haɗu aci tare, haka za su zauna ayi ta hira tunda babu me zuwa aiki a ranan

Wani lokacin ma har su Aunty Zainab suna zuwa, Aunty Zulaiha CE kawai bata cika zuwa ɗin ba sabida tana nesa sosai, amma idan ta sami lokaci tana ziyartan taron

Gaba ɗaya matan gidan suke haɗuwa ayi girki kala-kala da soye-soye, a babban kichen ɗin gidan suke haɗuwa tare da masu aiki su taya su

Yau ma hakan ta kasance duk sun haɗu suna ta girke-girke

Sauran yaran gidan kuma duk suna General parlour suna ta hiran su

Su Big Dady kuma suna ƙaramin parlour’n dake kusa da General parlour, anan suka zauna suna hira da nishaɗi

A cikin yaran in ka cire Fadila dake part ɗin su babu wanda ba shi ciki, ita dama bata cika son zuwa hiran ba, iyakan da an gama abinci zata zo taci ta tafi abun ta

Kaka shima na ɗakin sa yana karatun Jarida be fito ba, be son su ishe sa da surutu that’s why ya zauna cikin ɗakin sa

Ɗahira na zaune gefen Baffa suna hira suna kallo cikin waya sai dariya suke yi

Gefe can kuma Yusra da Shakira ne su ma suka buɗe tasu shaftan, Fadil ya zauna tsakiyan su sai zuba musu surutu yake yi, su kuma idan ya’ishe su wannan ta mangare shi ta nan, wancan ta mangaro shi ta nan, kuma yaƙi tashi a wajen shi a dole sai dasu zai yi hira

Yau dai su Aunty Zainab babu wacce tazo cikin su.

 

 

………. ………. ………. ………

Babu jima wa aka soma shigo wa da abincin ana jera wa a dainning table ɗin cikin parlour’n dake can gefe, babba ne me cin a ƙalla mutane ashirin

Bayan an gama an hallara a lokacin ne itama Fadila ta shigo ta zauna cikin su, kowa ya zuba abinda yake so

Ɗahira kuwa tana can cikin Parlour tare da Kaka dake zaune kan Wheel chair ɗin sa, dama haka take yi idan har ba ya son zuwa kan dainning ita take zama kusa dashi tana taya sa hira, idan ta ɗibo masa abinci sai su zauna tana taya sa hira suna ci har su gama

Yau dai shima Baffa ɗauko nashi abincin yayi ya dawo kusa dasu yana ci yana saka musu baki

Haka Familyn suka kasance yau cike da nishaɗi

Bayan kowa yaci ya sha aka dawo parlour aka zauna, nan su Big Dady sukai ta tambayan matsalolin mutane, daga nan kuma Kaka ya soma yabon Ɗahira da ƙoƙarin ta kan aiki, haka su ma su Big Dady sai yaba mata suke yi suna saka mata albarka

Abbu da Aunty Amarya hakan ya saka su farin ciki matuƙa

Hajja Fatu kuwa baƙin ciki kamar ya karta, haka ma Shakira sai dai ko kaɗan basu nuna a fuska ba

Hajiya kam babu ruwan ta duk da itama ba wai yabon yayi mata daɗi bane, Umma ma dai na ciki na ciki

Fuskar Yusra kamar zai fashe saboda baƙin cikin yanda iyayen nasu suke yabon Ɗahira, ko kaɗan ta kasa ɓoye abin da ke zuciyar ta, sai cika take yi tana batse wa babu wanda ya kula da ita

Anan Big Dady yake faɗa musu Usman zai dawo gaba ɗaya gobe, iyayen sun yi farin ciki amma ban da yaran don sun san halin sa ba ya da mutunci bare ɗaukar raini, yanzu zai zo duk ya takura musu

Daga nan aka ci gaba da hira, masu abun yi sun tashi sauran kuma sun zauna

Fadila ce farkon tashi ta koma part ɗin su.

 

*__________________________*

Ɗahira ce ta shigo cikin ɗakin nasu

Fadila dake waya tabi ta da kallo, sai kuma tayi dariya tana faɗin, “ga ta nan yanzu ta shigo ai”.

Cire wayan tayi a kunne tana kallon Ɗahiran da ta nufi wajen gadon ta tace, “Ga shi za ku gaisa da Yaya K.b”.

Murmushi Ɗahira tayi ta’iso wajen ta’amshi wayan tana kangawa a kunne kafin ta zauna gefen gadon Fadilan

“Yaya na”. Tafaɗa tana dariya

Shima daga can dariyan yayi yana faɗin, “ƴan mata kin ɓuya da yawa fa”.

“Haba ko dai ka ɓuya? Kaji min wannan mutumin”.

Dariya yayi sosai yana faɗin, “Allah Ni ina nan ke ce dai kika ɓuya”.

“Ai dama kai ba ka son laifin ka,
so how are you, how everyone?”

“Alhmadulillah. how about you?”

Ɗahira murmushi tayi tace, “lafiya sumul kamar yanda kuke, ina Shamsiyya?”

“Ai kam yanzu ta tashi anan ta gama min daɗin baki”. K.b yafaɗa yana murmushi

“Hmm kai dai ka faɗa gaskiya ko dai kai ne ka gama mata daɗin bakin? Ai nasan hali”.

K.B said, ” Let me call her and u ask her,”

“A’a Ni bance ba, ka barta nariga dai nasan Shamsiyya baza tayi maka haka ba, ya Ɗan kinibibi ina fatan yana lafiya? Duk da nasan kai dashi baku da zumunci, wai ace anyi Waliman mu amma kuka ƙi zuwa”.

K.b dariya yayi yace, “sorry Madam wlh kin san Ni aiki ne yayi min yawa, idan ma wani zai ƙi zuwa ai Ni bazan ƙi ba tunda har da my dear, amma insha Allahu kwanan nan zan zo Garin ma”.

Taɓe baki Ɗahira tayi tana kallon Fadila da ta shiga Toilet tace, “Mu dai muna zuba idanu; and Kar ka manta da saƙo na don Allah idan zaka zo”.

“Ok insha Allah, ga fa Mutumin naki nan ya shigo in ba shi wayan ne sai ki faɗa masa sunan da kika kira sa dashi?”

Rufe baki Ɗahira tayi cikin waro idanu tace, “don Allah rufa min asiri kar ka haɗa ni dashi”.

K.b me zai yi in ba dariya ba

Ita kuwa Ɗahira wayan ta miƙa ma Fadila da ta dawo ta zauna kan gadon tana faɗin

“Riƙe wayan ki naga Yaya K.B yana son yaja min salalan tsiya”.

Fadila amsar wayan tayi tana maida wa a kunne, sai kuma tayi dariya tana faɗin, “ai har ta fice ma a ɗakin”.

Dariya ta sake yi tana gyara zaman ta, daga nan hiran su suka ci gaba da yi.

 

Kabir K.B shi ne ɗa na uku wajen Hajiya IKRAM, ɗiyar ta na farko Sunan ta Nafisa, suna kiran ta Aunty Mimi, tayi aure har da yara, sai Isma’il, suna ce masa Dady, sannan K.B ɗin, sai kuma Jalil sannan Shamsiyya, sai ƙannin Shamsiyyan guda uku

K.b ke son Fadila har kowa ya rigada ya san da zancen, yanzu kawai lokaci ake jira sanda Kaka zai ce su fito da mazajen aure ayi musu.
[5/25, 6:44 PM] Oummu Ɗahirah: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTORS*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER’S ASSO📖*
“`®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓“`

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA’S FAMILY*_

_Wannan shafin naku ne masoyana, kuji daɗin ku._❤️

 

*EPISODE Fifteen*

Fitan Ɗahira ɗakin sai ta wuce ɗakin Maman ta kai tsaye, babu ita ciki tana can General parlour

Kan gadon ta tanufa ta soma kwashe mata kayan wankin ta dake ajiye an ninke, kwashewa tayi ta kai mata sif ta dawo ta soma gyara ɗakin, ba wani datti yayi ba amma haka ta sake gyarawa har da wanke mata Toilet, ta dawo Kan kujera ta zauna ta soma duba wayan ta, message ɗin da Masoyin ta ya turo mata yanzu babu jimawa ta buɗe

 

_”Kyakykyawa ta Barka da hantsi da fatan kina lafiya? Ya Weekend Ina fata kina enjoying?”_

 

Murmushi ta saki, a karo na farko yau tayi tunanin tura masa amsa, sai ta soma typing cikin ƙware wa

_”Alhmadulillah ina fata kaima haka? Please I want to know who?”

Sai tayi sending ɗin shi, tana nan zaune tana jiran ko za’a dawo mata da amsa but babu, sai ta gyara kwanciyar ta tasoma chatting da friends ɗin ta waɗanda sukai school tare

Can kuma sai saƙo ya shigo, da sauri ta buɗe tana murmushi duk farin ciki ya cika ta

 

_”Hmm kyakykyawa ta Kar ki damu da sannu zaki san ko Ni wane ne, Ni dai fata na in samu soyyayyar ki, don Allah ki so ni ko da kaɗan da yanda nake miki”._

 

Wani irin farin ciki ne yake mamaye da Ɗahira, sai dai bata mayar mishi da amsa ba tunda bata san me zata ce ɗin ba, sai taci gaba da chatting ɗin ta cike da nishaɗi.

 

 

⚫⚫⚫

Buɗo ƙofan Hajiya tayi ta shiga parlour’n da sallama

Yusra dake kwance cikin 3 Sitter tana kallo ta’amsa mata

Zuwa tayi ta zauna tana faɗin, “Yusra, get me some water.”

Tashi Yusran tayi ta nufi Fridge tana faɗin, “Hajiya wai don Allah da gaske gobe Yaya zai dawo?”

Hajiya bata amsa mata ba har sanda ta kawo mata ruwan, ta’amsa tasha sannan ta’ajiye sauran kan Centre table tana maida hankalin ta kan t.v

Turo baki Yusra tayi ta zauna gefen ta tana cewa, “Hajiya I am talking to you.”

Sai Hajiya ta kalle ta tana hararan ta tace, “dan ƙaniyar ki Dadyn naki ƙarya zai miki? Ina ce a gaban ki ya faɗa?”

Sake bunso baki gaba tayi tace, “to Ni Hajiya gaskiya bazan zauna ba zan koma gidan Aunty Zainab da zama, don wlh bazan zauna anan kullum ina cikin takura ba”.

Hajiya tace, “to Ni ban aike ki ba, idan kin tambayi Dadyn ki ya yarda sai ki fi ruwa gudu ma”.

“Don Allah Hajiya kiyi masa magana mana wlh bazai yarda ba in Ni ce”.

Hajiya bata sake mata magana ba

Ita kuma sai magiya take mata har da ƴar ƙwallan ta

Ko kaɗan ba ta farin ciki da dawowar Yayan nata, tunda sai tafi kowa takura kasancewar Part ɗin su ɗaya, ko kaɗan idan yana nan ba ya ƙaunar kayi ƙwaƙƙwaran motsi a gidan, yanzu sai ya zama laifi a wajen sa

Daga ƙarshe ma Hajiya tashi tayi ta nufi cikin ɗakin ta tabar Yusra nan tana kumbura fuska kamar Flower, ba don ranta ya so ba itama ta tashi ta fice a part ɗin ma gaba ɗaya, duk zuciyarta babu daɗi.

 

 

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

 

*TOMORROW MORNING*

Monday tushen aiki ko Bature na tsoron Monday

Gaba ɗaya ahalin gidan sun tafi aikin su, sai su Umma da aka bari su uku a gidan sai kuma masu aiki, sannan Kaka dake Part ɗin sa

Hajiya itama tunda ta tashi ta soma soye-soyen ta wanda zata tarbi Babban ɗanta dashi, yau gaba ɗaya farin ciki ya cika ta Allah-Allah take yi anjima yayi ta ga dawowar sa, dama sun yi waya jirgin ƙarfe 02:00pm. Yace mata zai biyo; don haka komi take yin sa a tsanake, ita da kanta ta shiga ɗakin sa ta gyara masa tayi masa duk abin da ya dace, bayan ta saka airfreshna sannan ta ƙara masa da turaren tsinke ta rufo ɗakin ta koma kichen taci gaba da harkokin ta.

 

 

⚫⚫⚫

Ɗahira tunda ta fara duba Patiens ɗin ta take jin kanta na sara mata, amma dayake ita ɗin jajirtacciya ce bata bi takai ba taci gaba da harkokin ta

Bayan ta gama ta nufi
Ward ta duba sauran mara su lafiyan ta sannan ta dawo Office ɗin ta

Tana son yau ta koma gida kamar lokacin tashin ta but ko kaɗan ba ta ƙaunar taje ta haɗu da maƙiyin ta (sunan da ta saka masa kenan)

Tunda Baffa ya shigo ɗazu ya sanar mata da lokacin da zai je ɗauko sa a airport take ta jin ta babu daɗi, sosai kan nata yake ƙara ciwon

Agogon dake ɗaure a tsintsiyan hannun ta takalla taga ƙarfe 01:20pm. Ne yanzu

Tsaki taja ta tashi ta nufi drower ta ciri magani tasha da ruwan Robber dake ajiye saman table ɗin ta, Labcoat ɗin ta tacire ta rataye akan Hanger sannan ta cire Eyeglasess ɗin ta ta’ajiye saman table ɗin ta nufi Toilet

Alwala ta ɗauro ta fito ta tada sallah, har ta’idar tana zaune nan tana lazimi, barci ne ya soma fisgarta don haka ta tashi ta ninke sallayan ta’ajiye ta nufi gaban table ɗin ta taɗau Glasses ɗin tamayar a idanun ta

Hanyan ƙofa ta nufa don zuwa Office ɗin Abbu ta kwanta acan, amma me ta tuna sai ta dawo tana jan tsaki

Ta san idan taje can zai tilasta mata ta koma gida ne, kuma a yau dai ba ta buƙatar ganin ta a gida, shiyasa ta dawo ta zauna kan kujeran ta ta ɗaura kanta a Deks ta rufe idanun ta, dayike barcin ne sosai yake cin ta don haka babu daɗewa ya ɗauke ta.

Koda ta farka babu ciwon kan a yanzu, sallan Asar tayi sannan ta saka Labcoat ɗin ta, tana shirin fita ne Beeper ɗin ta ya soma ruri, don haka ta fita da sauri tayi hanyan emargency ward.

 

 

 

⚫⚫⚫

At home, everyone was celebrating Usman’s return

Gaba ɗaya matan gidan suna part ɗin Hajiya sun je taya sa murnan dawowa

Sai da kowa ya watse sannan Shakira da Yusra da take Part ɗin su Shakiran yanzu suka nufi sashen Hajiyan don su gaishe sa

Yana zaune a dainning yana cin abincin da Hajiya ta girka masa da kanta

Yayi wanka har ya sauya shigan sa cikin ƙananan kaya kamar yanda ya saba

Koda suka shiga gaishe sa suka yi, ya’amsa musu cikin Izza da taƙama

Basu sake cewa komi ba suka miƙe suka fice don ba shi wuri, Part ɗin su Shakiran suka koma suka dasa hira.

 

Shi kuma bayan ya gama ɗakin sa ya koma, kwanciya yayi kan Three sitter ya lumshe idanun sa, shi ba barci yake yi ba kawai kwanciyar yayi, sai da aka kira sallan la’asar kafin ya tashi yayi alwala ya fita

A waje suka haɗu da Baffa suka jera har masallacin dake nesa kaɗan da gidan su

Bayan sun dawo a haraban gidan suka haɗu da Abba da Abbu da dawowar su kenan daga aiki

Gaishe su yayi cikin girmamawa, su kuma sai tambayan shi hanya suke yi cike da fara’a, haka ya’amsa musu sannan ya wuce ya nufi babban Parlour

Fadil na zaune a kan kujera yana kallo shi kaɗai ya shigo

Da sauri Fadil ɗin ya gaishe shi

Da kai ya’amsa masa ya nufi hanyan da zai sada shi da ɗakin Kaka

Da idanu Fadil ya bi shi dashi, sai da ya shige sannan ya taɓe baki a ransa yana mitan “miskilin banza! kai da Fadila wlh ban san wanda yafi mugun hali ba”.

Sai kuma ya kwaɓe fuska yaci gaba da kallon sa.

 

 

Tura ƙofan yayi ya shiga yana motsa bakin sa

Kaka dake zaune kan Wheel chair ɗin sa kamar ko yaushe yana karatun Jarida ya ɗago yana kallon sa, sai kuma ya yalwata fuskar sa da fara’a yace, “Maraba da Jikalle na”.

Takowa yayi ya zauna saman kujeran ɗakin yana kallon Kaka, kaɗan ya saki fuskar sa yace,
“Old man are you still alive?”

Sai Kaka ya saki dariya me sauti yace, “ja’iri ka ƙosa na mutu ko? To ina nan babu inda zan je sai na ga auren ka”.

Kyakykyawar murmushin sa yayi yana shafa gashin kansa yace, “uhmm Kaka kace da sauran ka kenan tunda Ni dai ba yanzu ba”.

“Koma dai me zaka ce sai naga auren ka tukun zan bar duniyar nan, dama tunda nayi muku maganar kai da takwara babu wanda ya haɓɓa sa, kun fi so dai a haɗa da ƙannin ku ko?”.

Usman taɓe baki yayi sai dai be ce komi ba

Kakan changed the conversation and asked, “Ya hanya?” Shi kuma ya’amsa masa a taƙaice

Kaka sai zuba masa hira yake yi, shi kuma daga ya’amsa da Eh sai A’a, daga ƙarshe wayan sa ya ciro yana latsawa yana sauraron Kakan, a haka yaja dogon lokaci a ɗakin kafin ya miƙe yayi masa sallama ya fice.
[5/26, 9:37 AM] Oummu Ɗahirah: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTORS*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER’S ASSO📖*
”’®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓”’

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA’S FAMILY*_

 

*EPISODE Sixteen*

Sai ƙarfe 05:45pm. Ɗahira ta koma Office ɗin ta, Jakarta ta ɗauka da abinda zata buƙata ta fito ta rufe Office ɗin ta nufi Lifter

Tana sauka ta fita ta nufi inda motan ta yake ta buɗe ta shiga, rufewa tayi ta’ajiye jakar ta kan Kujeran me zaman banza sannan tayi ma motan keey, sai dai yaƙi tashi, ta daɗe tana gwadawa amma yaƙi ya tashi, guntun tsaki taja tana dafe goshin ta, lumshe idanuwan ta tayi na kusan minti 2 kafin ta buɗe ta sake gwadawa amma ina har yanzu be tashi ba, fitowa tayi tana ɗan waige-waige, sai kuma ta nufi gaban motan ta buɗe Garage ɗin ta soma tattaɓa wa, duk ta duba ko da akwai matsala ne amma ita a fahimtan ta bata ga komi ba

Tana nan tsaye a wajen tana ɗan sake duba wa taji sallama, sai ta ɗago kyawawan idanuwan ta wanda ƙwayan ciki suke ƙyalli sakamakon Hasken fitillun haraban wajen, amsa mishi tayi tana kau da kanta ganin kallon da yake mata tamkar zai haɗiye ta

“Are you all right? I’ve seen you here before. Are you still gone? What’s going on?”

Ɗahira kamar baza tayi magana ba, sai kuma ta ga hakan be dace ba tunda taimakon ta zai yi, bata ɗago ba ta bashi amsa, “Wlh nima ban sani ba, kawai ta ƙi tashi ne”.

Dr. Sa’id yace, “ok bari in duba miki mu gani ko?”

Babu musu ta matsa mishi yazo ya soma duba mata, shima ya daɗe yana taɓe-taɓen sa kafin yace mata, “wake up the car”.

Shiga tayi tayi ma motar keey amma har yanzu ya ƙi tashi

“Ina ga dai motar ki sai ta ga bakanike coz myb wani matsalan ne babba wanda baza mu iya gane wa ba”. Yayi maganar bayan ya rufe mata garejin

“To Nagode”. Tace dashi tana ciro jakarta kafin ta rufe motan da keey

“In ba damuwa muje in rage miki hanya mana”.

Ta tsinkayi muryan sa da har ta juya baya zata tafi

Jimmm tayi tana tunani domin ita mutumin ko kaɗan be mata ba, coz ta kula kallon tsiya ne dashi tun ganin sa na farko

Murmushi yayi yana takowa wajen ta yace, “don’t worry. Ni ba siyar da kanki zanyi ba, ai kin san a nan nake aiki balle kice Ni ɗin baƙo ne, so ni ba baƙo bane babu wanda be San ni ba, My name is Dr. Sa’id Khan”.

Kallon sa ta ɗan yi sai kuma tayi guntun murmushi tace, “ba damuwa mu je”.

“Yauwa ko ke fa”. Yafaɗa yana yin gaba wajen motar sa

Shi ya buɗe mata murfin motan da zumman ta shiga

Sai kawai ta ga abun yayi mata wani iri domin ita idan har ba Baffa ba basu taɓa hakan da wani ba, hakan ko kaɗan be burge ta ba, amma babu yanda zata yi ta shige ta zauna ya rufe mata

Shiga shima yayi yaja motar suka bar asibitin

A cikin motan ma babu wanda yayi magana cikin su, sai da suka ɗan yi tafiya kafin ya soma jan ta da Surutu duk a kan aikin nasu

Ko kaɗan ba ta jindaɗin surutun nasa

Shi kansa ya gane ba ta ƙaunar hiran sa; yanda take amsa masa maganar kamar baza tayi ba, don haka yaja bakin sa yayi shiru yana mamakin yarinyan, shi tunda ya ganta yaji ta burge sa matuƙa kuma yana son ƙulla alaƙa da ita, sai dai ya ga alamun hakan ba me yiwuwa bane duba da yanda take ɗin, da alamun tana da girman kai kuma zata yi wuyan sha’ani, a yanda ya fahimce ta kenan

Har suka kai ƙofar gidan su kafin ya tsai da motan

Kallon sa Ɗahira tayi cikin siririyan muryanta me kamar tana yanga tace,”Thank you, Dr.”

He smiled and looked at her and said, “It’s all right.”

Buɗe motan tayi ta fito

Dai-dai lokacin su Baffa da Usman suka ƙariso wajen sun dawo sallan magriba

Gaba ɗaya kallon ta suke yi, yayinda Usman ya ɗauke kansa time ɗin da ta juyo zata sauke idanun ta a kansu, cikin gidan ya wuce batare da yayi wa Baffa magana ba

Shi kuma Baffan sai ya nufo ta fuskarsa duk babu walwala yana bin motan Dr. Sa’id da kallo da har ya ja ya tafi

Itama ganin ya taho ɗin ne yasa ta tsaya tana masa murmushi

Yana ƙari so wa idanun sa a kanta yace, “wannan kuma wane ne? ina Motar taki?”

Sai da ta kalli hanyar da Dr. Sa’id yabi kafin ta dawo da ganin ta kanshi tace, “Yaya Motata taƙi tashi ne wlh ban san kuma me ya faru ba, shi ne yace in zo ya rage min hanya”.

Gaba ɗaya zuciyar Baffa ba ta mishi daɗi, tsananin kishi ne yake nuƙurƙusan sa a ransa, daƙyar ya”iya saisaita kansa ya sake jeho mata tambaya

“Aina Motar taki ta tsaya da har kuka haɗu dashi?”.

“A cikin Hospital ɗin ne fa, kuma shima Dr. Ne cikin asibitin shiyasa ma na yarda na hau, but da farko ban yi ninyan hawa ba”.

Murmushi Baffa ya kirƙiro yace, “let’s go then”.

Babu musu tayi gaba yana bin ta a baya duk da ita bata fahimci musabbabin tambayan nasa ba, amma ta san cewa shi ɗin Yayanta ne yana da right ɗin tambayar ta

Sai da suka shiga ciki kafin suka jera cikin gidan, Part ɗin su Ɗahira suka wuce

Suna shiga da sallama, Aunty Amarya dake zaune ita da Fadil suka amsa musu

“Aaah maraba da Mijina”. Aunty Amarya tafaɗa tana yalwata fuskarta da fara’a

Baffa na faman shafa kansa yana murmushi ya ƙariso ya zauna a kan kujeran kafin ya gaishe ta

Ta’amsa masa cike da fara’a tana tambayar sa aiki

Itama Ɗahira sannu da gida tayi mata ta wuce ɗakin su ba tare da ta zauna ba

Su kuma suka ci gaba da hira suna kallo

Daga baya itama Umma ta fito aka ci gaba da hiran da ita

Baffa duk ya ƙosa Ɗahira ta fito amma tunda ta shiga bata sake fitowa ba, shi kuma ya zauna ne don ita amma tunda ta fito ta zuba abinci ta sake shige wa ɗaki, aiki take yi a ciki shiyasaka ta zauna nan ɗin tunda ba ta son hayaniya

Sai da aka kira sallan isha’i kafin Baffa ya miƙe tare da Fadil suka fito

Anan suka ci karo da Fadila itama dawowar ta kenan, gaishe da Baffa tayi

Ya’amsa yana faɗin, “Sarkin miskilanci sai yanzu aka dawo?”

Murmushi tayi tace, “Yaya kana son dai tsokana ta ko?”

Murmusawa yayi shima yana cewa, “ai gaskiya ne, kwana biyu ma gaba ɗaya kamar ba kya nan a gidan, rabon da in ganki na jima sai jiya a wajen meeting”.

Fadil dake tsaye yana sauraron su yace, “ai Yaya wlh duk wanda ya auri Aunty Fadila ya bani, shiyasa ma zan ba ma Yaya K.B shawara tun wuri ya sauya ta don baza tayi daɗin zama ba idan ya aure ta, yana ji yana gani zata mayar da waya abokin rayuwanta ta ƙyale shi yay ta surutun sa..”

Kawo masa duka tayi dole yayi shiru yana matsawa gefe da sauri

“Wlh zan ɓalla ka a nan wajen; Ni sa’ar wasan ka ne Fadil?” Tafaɗa tana hararan sa cike da haushi

Baffa dariya yayi yace, “mai da wuƙan don Allah wasa yake miki”.

Ƙwafa kawai tayi ta juya ta buɗe ƙofan Part ɗin nasu ta shige, tana jin Baffa yana faɗin

“Babu sallama kuma zaki tafi?”

Amma bata jiyo ta kalle sa ba bare ta tanka masa

Su ma wuce wa suka yi suka tafi, Baffa na shan dariyan Fadil da yaci gaba da maganar Fadilan.

 

 

⚫⚫⚫

*08:45pm.*

Suna zaune su huɗu a kan dainning suna cin abinci, babu me magana cikin su sai ƙaran cokula da Plate da ake ji

Kansa na ƙasa yana cakalan abincin kamar bazai ci ba, rabi kuma hankalin sa naga wayan sa yana kallon wani abu da aka tura masa, har kowa ya miƙe suka bar sa nan zaune be ma san sun tashi ɗin ba

Parlour suka koma sukai zaman su, Big Dady da Hajiya suna taɓa hira while Yusra kuma ta mayar da hankalin ta kacokan kan Film ɗin da ake yi a Bollywood, Film ɗin زوجة زوجي searese

A hankali ya miƙe ya taho cikin parlour’n yana shirin wuce wa ɗakin sa

Dady ya tsayar dashi yana faɗin, “Fodio come here we’ll talk”.

Juyowa yayi ba tare da yace komi ba ya taho ya zauna kan One sitter dake Facing ɗin nasu Dady

Ɗan gyaran murya yayi yana kallon sa kafin yace, “gobe ne zaka soma zuwa Hospital ɗin ko ya?”

Cikin ƙasa da murya kamar wanda yake tsoron yin maganan yace “No .. until Monday”.

Jinjina kai Dady yayi kafin yace, “to har yanzu baka shirya aure bane? Tunda ga shi yanzu ka dawo gida Ya kamata ace kun ajiye mata kai da Baffa amma shiru har yanzu baka ce komi ba, kuma idan ban manta ba naji Baba yayi muku magana akan maganar auren ku”.

Shiru Usman yayi be ce komi ba, sai ma sad da kansa ƙasa da yayi

Su kuma sun zubo masa ido daga shi har Hajiya suna sauraron abinda zai ce

Yusra dake kallo ma hankalin ta na wajen

Girgiza kansa Dady yayi don yasan halin ɗan nasa, don babu wanda be saba da miskilancin sa ba

“Ya kamata dai kusan kun girma tun kafin mu ce zamu nuna fushin mu a kan ku ku fito da mata, don baza mu zira muku idanu kuyi yanda kuke so ba, ka tashi kaje Allah yayi muku albarka”. Dady ya sake faɗan hakan

Miƙewa yayi yana ɗan motsa bakin sa kafin ya nufi hanyan ɗakin sa

Su kuma suka rakasa da kallo har sanda ya gifta ta gaban su ya wuce

Ajiyan zuciya Dady ya saki yana miƙewa ya kalli Hajiya yace, “Let me in. I have a job.”

Be jira amsar ta ba ya sake maida kallon sa kan Yusra yana cewa, “Auta ke baza ki je ki kwanta ba sai kin makara ko?”

Kallon sa tayi tana murmushi tace, “Dady zan kwanta yanzu za’a gama wannan sai inje in kwanta”.

Gyaɗa kansa yayi kafin yayi gaba yana shigewa ɗaki

Itama Hajiyan bin bayan sa tayi suka bar Yusra ita kaɗai a parlour’n.
[5/27, 8:43 AM] Oummu Ɗahirah: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTORS*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER’S ASSO📖*
”’®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓”’

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA’S FAMILY*_

 

 

*EPISODE Seventeen*

*MONDAY*

*12:30pm.*

Ya gama shirin sa na zuwa Office, yana sanye cikin wandon jeans blue, sai baƙar riga me gajeren hannu da ya sake fito da hasken skin ɗin sa sosai ya kuma ƙara masa kyau ainun, kwantaccen baƙin gashin sa sai shaining yake yi zuwa siririn sajen sa, babu abinda yake tashi ajikin sa sai sassanyan ƙamshi me tsananin daɗi ga duk wanda ya shiga hancin sa

Wrest watch yake ɗaura wa a tsintsiyan hannun sa me haske sosai da yalwan gashi, fuskarsa babu alamun fara’a ko kaɗan, har ya gama sakawa kafin ya zauna gefen gado ya soma saka Combat ɗin sa da ya kasance Blue Colour da igiyan sa suka kasance baƙi, bayan ya gama saka wa sai ya miƙe ya ɗau briafcase ɗin sa ya fito cikin ɗakin yana rufe wa

Babu kowa cikin parlour’n, sai ya nufi ɗakin Hajiya yayi Nocking yana jiran izni

Hajiya dake zaune kan gado wanda fitowar ta kenan daga Toilet ta ba da iznin shigo wa

Tura ƙofan yayi yana motsa bakin sa idanun sa a kan ta

Kamar yanda itama ta zuba masa idanu tana kallon sa

Takowa yayi a hankali har zuwa gaban ta kafin ya zauna gefen gadon, shiru yayi yana murza hannun jakan dake riƙe cikin fararen tafin hannun sa

Tsawon mintuna biyu Hajiya tana jiran taji yayi magana amma sai taga be da alaman yi, hakan yasa tace, “har ka shirya my son?”

Gyaɗa mata kai yayi yana kallon ta

She smiled and said, “God bless you and good luck.”

“Ameen”. Yafaɗa a hankali wanda a laɓɓan sa ta fahimci abinda yace

Miƙe wa yayi ya taka ya fice cikin ɗakin yana duba agogon hannun sa.

Yana fita wajen motan sa ya buɗe ya shiga ya zauna sannan ya rufe, tada motan yayi yaja ya nufi bakin Gate

Tun daga nesa da me gadi ya hango zuwan sa ya miƙe da sauri ya buɗe masa Gate ɗin, yana fita ya ƙara Speed, cikin mintuna ƙalilan ya’isa haraban Hospital ɗin

Ɓude ƙofan yayi ya ziro ƙafafun sa a hankali sannan ya fito ya rufe, ya juya ya soma tafiya cikin taƙama da izza wanda zaka san a jinin sa ne.

 

 

Shakira da Ayush dake tsaye jikin motan Shakiran, Ayush tana faɗa mata yanda suka yi da Baffa sai idanun ta ya faɗa kan Usman dake doso cikin asibitin, baki buɗe take bin shi da kallo

Hakan yasa itama Shakira ta mayar da hankalin ta inda Ayush ɗin take kallo, nan ta hangi Usman har ya shige

Ajiyan zuciyan da Ayush ta saki me ƙarfi ya saka Shakira take kallon ta cike da mamakin ta

“Lafiyan ki kuwa?” Ta tsinkayi muryan Shakiran da ta sake dawo da ita hayyacin ta

“Hmm ba lafiya ba, wane ne wannan Handsome Guy ɗin da naga kamar yana kama da Familyn ku?” Ayush tayi maganar tana tsare Shakira da idanu

Taɓe baki ita kuma tayi tace, “Yaya Usman ne”.

“Kaiii amma wlh ya haɗu, Ni zan iya ce miki ban taɓa ganin mutumin da ya tafi da imani na a second ɗaya ba irin wannan, kai wlh ban taɓa ganin wanda komi nashi ya dace dashi ba sai wannan guy ɗin, Kai Amma wlh ban taɓa..”

“Ke dallah ya isa mana, meye haka kike zuba min hauka? ko dai hankalin ki ya gushe ne?” Shakira ta katse ta tana kallon ta cike da takaici

“Wlh baza ki gane bane, amma wlh yayi Ni dai ya gama dani”.

Shakira tace, “to shikenan yanzu kenan baki yi da Yaya na sai wannan ko? Ko kin manta alƙawarin da ki kai min?”.

Murmushin yaƙe Ayush ta saki tace, “laa I don’t mean that. I’m just saying my opinion on this, but I’m not saying I’m better than Baffa, I like Baff..” Sai kuma tayi shiru ganin zata saki layi

Shakira da hankalin ta ma ba ya ga Ayush ɗin, tana kallon Fadila da tazo wuce su tayi saurin kwaɗa mata kira

Fadila dake tafiya waya a kunnen ta tajuya ta kallo su, sai kuma ta soma takowa wajen su har a lokacin tana ci gaba da wayan ta, sai da tazo dai-dai gun su sannan ta kashe wayan tana ɗago kai ta kalle su

Shakira murmushi tayi tace, “manyan gari wai ke idan ba an neme ki bane ba kya neman mu ko?”

Guntun murmushi kawai Fadila ta saki ba tare da tace komi ba illa gyara zaman jakan ta da take yi

“Yanzu muka gama magana da mutumiyar ki a kan ki ma”. Shakira ta sake faɗan hakan still tana Murmushi

Kallon ta Fadila tayi da rashin fahimta kafin tace, “who?”

Shakira tace, “Ɗahira, ai ita nake nufi, kullum kuma idan na ganta sai na ce ta gaishe min da ke, Allah yasa tana faɗa miki don nasan halin ta ba wai son ki take yi ba?”

Numfashi Fadila taja sannan tayi murmushi tace, “haka ne.. to Ni zan tafi kin ga nayi late yau ban shigo da wuri ba”. Sai kuma ta ɗan ɗago wayan ta tana duba time kafin ta juya ta tafi ba tare da ta sake furta komi ba

Daga Ayush da tun zuwan Fadilan take kallon ta har Shakira bin bayan ta da kallo suka yi har ta ɓace ma ganin su

Tsaki ne ya biyo bayan shirun nasu

Ayush ta kalle ta da mamaki tace, “mene ne ƙawata?”

Sai da Shakira tayi ƙwafa kafin ta buɗe motan tace, “Allah Fadila tana baƙanta min rai idan nayi mata maganar Ɗahira take nuna halin ko in kula wanda Ni ba hakan nake so ba”.

Dariya Ayush tayi duk da bata fahimci me take nufi ba, ta nufi ɗayan side ɗin ta buɗe ta shiga, itama Shakiran shiga tayi ta rufe ƙofan tare da jan motan suka bar haraban Hospital ɗin.

 

 

 

⚫⚫⚫

Kai tsaye hawa na uku ya wuce inda a nan ne office ɗin sa yake, Office ɗin na kallon na Ɗahira ne

Buɗe wa yayi ya shiga ya rufe, kallon ko ina yake yi da idanu fuskar sa babu fara’a, ko kaɗan ba ya farin ciki da kasancewar sa a nan ɗin, jin sa kawai yake yi cikin takura kuma hakan ne ya ƙara ɓata masa rai sosai

Duk da office ɗin yana da girma, ga shi ya haɗu tako ina amma shi be burge shi ba ko kaɗan tunda ko kwatan nashi na ƙasan Turkey be yi ba

A hankali ya soma takawa ya nufi kan kujeran ya zauna yana kwantar da kansa jikin kujeran, ya lumshe idanun sa yana jujjuya wa cikin kujeran, numfashi kawai yake sauke wa ba tare da ya motsa ba tsawon lokaci, sai da wayan sa ta soma ringing ne sannan ya buɗe idanun sa yana ɗago kai yabi wayan da kallo a inda ya’ajiye saman table, ganin sunan Dady na yawo a screan ɗin wayan hakan yasa shi sanya hannu ya ɗauka ya kanga a kunne bayan yayi peacking call ɗin, shiru yayi yana sauraron sa kafin ya buɗe baki a hankali yace, “Eh na zo”.

Kallon files ɗin gaban sa yayi, sannan ya yamutsa fuska yace, “ok”.

Sai ya cire wayan a kunnen sa yana ajiye wa, ya sake maida kansa jikin kujeran ya rufe idanun sa

Bayan mintuna biyar ya jiyo Nocking, iznin shigowa ya bayar ba tare da ya motsa ba

Ɗaya daga cikin staff’s ɗin asibitin ne ta shigo, ta gaishe sa but ko amsa ta be yi ba, kamar ma be san da wanzuwar ta ba

“Dr Noor told me to bring this to you.”

Hannu ya nuna mata alamun ta ajiye a table

Don haka babu musu tayi yanda yace mata sannan ta juya ta fice

A ƙalla ya ɗau tsawon mintuna goma kafin ya buɗe idanun sa ya ɗago kai yana kallon files ɗin gaban sa, numfashi yaja me ƙarfi sannan kuma ya ɗaura kansa saman table ya sake rufe idanun sa be da alaman yin abinda ya kawo sa.

 

 

 

⚫⚫⚫

Hannun yarinyan ta riƙe tana kallon ta cike da tsantsan tausayi, wai yarinya ƙarama kamar wannan ace an yi mata Fyaɗe, kee duniya ina zaki damu ne? Mene mutane suke nema a kan ƙaramar yarinyan da bata fi shekara biyar ba?

Numfashi taja tana sanya hannun ta kan yarinyan ta soma shafa mata gashi, ko kaɗan yarinyan ba ta motsi, ba ma zaka san tana da numfashi ba sai idan ka ƙura mata idanu sosai zaka ga tana fitar dashi ɗai-ɗai ta cikin Oxgyen ɗin da aka sanya mata

Ta jima tana kallon yarinyan wanda a baɗini tunani ta lula a kan abinda ke faruwa a ƙasar mu, wanda Fyaɗe ya zama ruwan dare a wannan zamanin

Hannun ta tajanye ta miƙe daga kan gadon ta fito waje

Matar dake zaune bakin ƙofan a ƙasa tana kuka ta ɗago kai da sauri tana kallon Ɗahira, sai kuma ta miƙe cikin rawan baki tace, “Likita..”

Kuka ne yaci ƙarfin ta dole tayi shiru

Ƙwallan da ya cika mata idanu na tsaban tausayin matar da ƴarta ta share sannan ta dubi matar a tsanake tace, “Calm down, she will be relieved by God’s will, but follow ME and we will talk”.

Kallon ta Matar tayi alamun kamar bata fahimta ba

Hakan yasa Ɗahira ta sake maimaita mata da Hausa, “ki kwantar da hankalin ki zata samu sauƙi da yardan Allah, amma ki biyo NI ofiice muyi magana”.

Gyaɗa kanta tayi tana saka gefen zanin ta ta share hawayen ta da suka haɗe da majina, sannan tabi bayan Ɗahira da har ta soma tafiya

Office ɗin ta suka zarce, sai da suka zauna sannan Ɗahira ta kalle ta tace, “zan so ki bani bayani a kan abinda ya faru, sam abun be min daɗi ba kuma tabbas dole ne hukuma ta ɗau mata fansa”.

Numfashi taja kafin taci gaba, “Mun rigada mun cire spain ɗin waɗanda sukai mata wannan aika-aikan, kuma insha Allahu idan result ya fito zamu miƙa case ɗin ga hukuma domin abi mata haƙƙin ta”.

Cikin kuka Matar ta soma magana da faɗin, “Likita mun rigada mun bar su da Allah, sam baza mu iya Shari’a dasu ba domin kuwa waɗanda suka aikata mata hakan sun fi ƙarfin mu nesa ba kusa ba, Ni fata na Allah ya tashi kafaɗun ƴar mu domin kuwa ban san me zance wa Mahaifin ta ba idan ya dawo ya tarda abinda ya faru..” Sai ta fashe da kuka tana ɗaura hannun ta ɗaya saman fuskarta

Kallon ta kawai Ɗahira take yi na tsawon lokaci kafin tace, “kar ki damu dole ne mu miƙa wannan case ɗin ga hukuma, domin a yanzu zancen da nake miki Human right sun shiga zancen nan, kuma ya kamata ki kira mijin naki duk inda yake yazo ya ga abinda ya faru hakan shi ne maslaha, sannan ina so muyi magana dashi”. Taƙarike maganar tana janyo Pepper gaban ta taɗau Bairo ta soma rubutu

Matar bata ce komi ba sai kukan ta da take yi

Miƙa mata Peppern da ta gama rubutu tayi, “Ki je ki siyo wannan alluran ina buƙatar su yanzu”.

Hannu ta saka ta’amsa tana jan majina, “Na gode Likita Allah ya saka da alheri”.

Murmushi kawai Ɗahira tayi mata bata ce komi ba, tana bin ta da kallo har ta fice sannan ta kau da kanta tana sauke ajiyan zuciya, hannu biyu ta saka ta tallabo haɓan ta bayan ta ɗaura gwiwowin hannun saman table, sosai take cikin damuwa akan abin da ke faruwa da yaran mutane

“Wai shin mene ne matsalan hakan? Meke jawo yawan Fyaɗe a wannan lokacin? Sannan mene ne mafita?”

Nocking ɗin da aka yi yasaka ta dawowa hayyacin ta, numfashi taja tana kallon Baffa da ya turo ƙofan ya shigo.
[5/28, 9:55 AM] Oummu Ɗahirah: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTORS*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER’S ASSO📖*
”’®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓”’

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA’S FAMILY*_

 

*EPISODE Eighteen*

“Yayana baka tafi ba?”

Murmushi yayi ya tako ya zauna yana cewa, “yanzu na tashi nace bari inzo inga ƙanwa ta”.

“Allah Sarki Yayana, ina to budurwan taka ko ta tafi ne?” Tayi maganar tana dariya

Shima dariyan yayi yace, “kai sis yaushe nace miki budurwa ta ce?”

Ɗage kafaɗa tayi tana taɓe baki tace, “Ni naga alama ne ai”.

“Serious ba budurwa ta bace freindship ne kawai a tsakanin mu”.

“Anya Yaya ban yarda ba?”

Langaɓe kansa yayi yace, “shikenan tunda baza ki yarda ba?”

Ɗahira dariya tayi tace, “na yarda to, yaushe ne kuma zaka haɗa ni da budurwan ka ko sai ka kawo ta gida ne zamu ganta?”.

“Very soon lokaci nake jira ai”.

Ɓata fuska tayi tana shirin magana aka yi Nocking

“Yess come in”. Tafaɗa idanun ta a kan ƙofan

Matar da ta fita ɗazu ne ta dawo

“Sis bari in tafi sai mun haɗu a gida”. Baffa yafaɗa yana miƙe wa

“Ok Byeee Yaya”.

Sannan ta kalli matar tace zauna

Zama tayi kamar yanda ta buƙata sannan ta miƙa mata alluran da ta siyo

Amsa Ɗahira tayi ta duba kafin ta kalli matar tace, “Shin Mijin naki ya zo?”

Girgiza kanta tayi sannan tace, “yana Zaria ne a yanzu haka, sai dai kuma na faɗa masa yace min yana kan hanyan dawo wa”.

Gyaɗa kanta tayi kafin tace, “to ki je ki kula da ita, Dr. Rahab zata riƙa zuwa ta duba ta, idan ya ƙariso sai ku taho tare ina son ganin ku”.

Jinjina kanta matar tayi sannan ta miƙe tayi hanyar ƙofa ta fice

 

Waya ta ɗauka tayi kira sannan ta kara a kunne

“Ki zo ina son ganin ki”. Abun da tafaɗa kenan kafin ta’ajiye wayan taci gaba da duba files ɗin gaban ta

Babu jima wa wata Nurse ta shigo bayan tayi Nocking an ba ta izni

“Gani Doctor” Nurse ɗin tace hakan bayan ta tsaya a gaban table ɗin Ɗahiran

Lokacin ne ta ɗago kai ta kalle ta, sannan taɗau alluran ta miƙo mata tace, “Yauwa Sister ga shi ki je ɗakin da yarinyan nan da aka kawo jiya take kwance kiyi mata alluran nan, Please yanzu zaki yi mata Dr. Rahab bata kusa ne Ni kuma ban yi sallah ba lokaci ya ƙure, ki kula da ita zuwa sanda zata dawo sabida ako yaushe zata iya farka wa kinji?”

Murmusawa Nurse ɗin tayi sannan tasaka hannu ta’amsa alluran a lokaci ɗaya take faɗin “insha Allahu doctor”. Sannan ta juya ta fice

Ita kuma Ɗahira miƙe wa tayi ta cire Labcoat ɗin ta; ta rataye a Hanger, sannan ta zare Eyeglasess ɗin ta tare da agogon hannun ta ta’ajiye ta nufi cikin Toilet ɗauro alwala.

 

 

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

 

Sai da suka gama kitumurmuran su na abin da suke ƙulla wa a kan Baffa da Ɗahira kafin Shakiran ta sauke ta a bakin gidan su sannan taja motan ta tatafi

Ayush bata shiga gidan ba sai ta nufi cikin anguwan, gidan ƙawarta Rumanatu

Rumanatu ƙawa ce wajen Ayush tun na yarinta, da gidan su Ayush ɗin da gidan su Rumanatu gida ɗaya yaraba su, sun taso makaranta tare komi nasu tare har zuwa matakin da suka kai NCE, inda daga nan ne Rumanatu ta dakata da karatun nata, yanzu haka shekara biyu kenan da auren ta, ta taɓa haihuwa ɗan nata na da wata bakwai ya rasu

Gidan ba wani babba bane gidan Rumanatun but gida ne na masu hali tunda mijin ta yana da ƙumban Susa, shima a anguwan yake da zama da iyayen sa

Ƙofar gidan ta ƙwanƙwasa tunda a rufe yake daga ciki, babu jima wa aka zo aka buɗe mata

Rumanatun ce da kanta, ganin Ayush a gaban gidan ta sai ta kwantsama ihu tana rungume ta tare da faɗin, “Ayushhhh”.

Dariya Ayush tayi itama tana rungume ta ɗin, kafin suka saki juna suka shige ta rufo ƙofan, cikin gidan suka shiga suka yaɗa zango a parlour

“Waiii wata sabon gani ai nayi fushi wlh”. Cewar Rumanatu tana ajiye mata farantin silver da ta ciko da drinks

Dariya Ayush tayi bata ce komi ba ta ɗauki Robbern Coke tana buɗe wa

Rumanatun ta sake cewa, “tunda kin zama big girl me amsar Albashi duk wata ai dole ki guje mu”.

Still dariyan Ayush ta sake yi kafin tace, “wlh kema kin san ba haka bane, tsakani da Allah idan zaki faɗa gaskiya kema kin san bazan taɓa juya miki baya ba, ai ke kin fi ƙarfin haka a waje na”.

Kanta ta ɗaga tana taɓe baki tace, “da dai ban san daɗin bakin ki bane, kar fa ki raina min hankali”.

Kwashe wa da dariya Ayush tayi har da ɗan buga ƙafafun ta

Rumanatu ta harare ta tana faɗin, “ke dai kika sani”.

Ɗan langaɓe kai tayi cikin muryan tausayi tace, “na rantse da Allah ki yarda dani My Ruman, wlh aiki ne ya ɓoye Ni but kiyi haƙuri ban sake wa”.

“To ya na iya, yanzu wuni kika zo min ko kuwa?” Rumanatu tace hakan tana tsare ta da idanuwan ta

Sai da ta yatsina fuska kafin tace, “daga wajen aiki nayo nan fa, wlh damuwa ce dani nake neman me bani shawara”.

“Shegiya ashe ba don Ni kika zo ba matsalan ki takawo ki? ke wlh baki da mutunci Ayush”. Tafaɗa tana dariya

“Ke dai bani shawara kawai ki ajiye wannan a gefe, babban matsala ce dani wlh”.

“To ina jin ki fesa min naji”.

Sai da ta sauke numfashi kafin tace, “wlh wani Guy ne nake faɗa miki na kamu da mahaukacin ƙaunar sa, don bazan iya ce miki son da nake masa me hankali bane, yau rana ɗaya na gansa amma wlh baki ga yanda na kasa samun nutsuwar zuciya ba”.

Dariya Rumanatu ta sheƙe dashi har da tafa hannayen ta, “Wayyo Allah ki ce yau kin samu wanda ya susutar dake? tirƙashi zamu sha biki kenan”.

“Ke ba nan matsalan take ba, bari dai in warware miki komi don ki fahimce ni da kyau”. Ayush taƙarishe maganar tana muskuta zaman ta

Tiryan-tiryan tafaɗa mata komi har shirin su da Shakira

Sai da ta gama Rumanatu tace, “lallai kin taro match baki da ƴan wasa, amma kinga Ni shawaran da zan baki tunda har kin samu Baffa ta hanya me sauƙi haka, ga shi har kun zama friend soyayya ce kawai ta rage wanda hakan ba wani matsala bane a wurin ki na sani, to me zai hana ki ƙyale shi wannan Guy ɗin da kika gani, kinga fa kince min Familyn su ɗaya, kar ki je kiyi saki na dafe”.

Izuwa yanzu fuskar Ayush ya sauya da matsanancin damuwa, cikin sanyin murya tace, “wlh nima haka na gani Ruman, sai dai kuma matsalan yanda zuciyata ta kamu da ƙaunar Usman na haƙiƙa fiye da Baffa, wlh a yanda nake ji a yanzu dai zan iya rasa komi nawa don in mallake sa, Usman ba irin mazajen nan da mata zasu gansa su ƙyale bane, wlh kinji na rantse miki ya wuce gaban kwatance, amma baza ki gane hakan ba sai idan kinyi ido biyu dashi zaki gane irin su ne mazan nan da samun su babban nasara ne a duniyar mu, kin san me? Wlh kyau dai Usman bazai nuna wa Baffa ba, fari ne kaɗai zan iya cewa Usman ya ɗara Baffa domin babu maraban su, amma kuma wayewan su tasha bamban matuƙa, duk da Baffa shima wayayyen saurayi ne wanda duk macen da ta same sa ta gama Sa’a, sai dai abinda yafi jan hankali na akan Usman kasancewar sa yayi rayuwan out side, that’s why dole su bambanta nesa ba kusa ba, uhmmm baza ki gane ba amma wlh zuciyata ta kamu, domin ko wacce zuciya da abun da tafi ƙauna, Ni shi nake so ba wanin sa ba”. Ayush taƙarishe maganar da dafe setting ƙirjin ta

Jinjina kanta Rumanatu tayi tana kallon Ƙawar nata cike da tausayi, domin ba kaɗan ba ta bata tausayi don sosai ta hango iya gaskiyar ta a idanun ta, so babban cuta ne ga duk wanda ya kamu da ita dole ya zama abar tausayawa

“Gaskiya kina cikin wani hali Ayush dole in tausaya miki, domin kuwa nima na shiga wannan halin kafin in auri Musbahu, amma Ni abinda nake ganin ya dace kiyi yanzu, ta yanda kika bi da Baffan ta nan zaki bi da Usman ɗin..”

Tun kafin ta gama kai aya a zancen ta Ayush ta katse ta da faɗin, “Ruman yanda nake faɗa miki Usman ya bambanta da Baffa nesa ba kusa ba, a halayyan su daban ne sosai, a yanda Shakira ta faɗa min ta ce mugun me zafin kai ne, yana da tsananin miskilanci fiye da tunanin mutum, be da harka ko kaɗan, wlh Ni kaina da na ganshi na yarda da hakan don banga alamun zai iya saurarona ta wannan hanyan ba”. Sai kuma ta girgiza kanta taci gaba da faɗin, “Inaa! kwarjinin sa ma bazai bar Ni inje ba”.

Numfashi Rumanatu ta saki tana kallon Ayush ɗin, “To yanzu ya kike so ayi?”.

“I don’t know Ruman, shawaran ki nake nema”.

“Ok Ni dai shawarana a nan kawai kibi sa a social media, idan har ya kula ki sai ki faɗa masa abinda ke zuciyar ki, kar ki tsaya tamkar na wannan ki ce zaki ƙi sanar masa, duk da haka ki bani time sai mu san abun yi ko? Ai shawara bazai gagara ba za mu samu mafita”.

Murmushi Ayush tayi tace, “Yauwa my Ruman shiyasa nake son ki, I know zaki iya wlh, yanzu ki bani Numban ki so that mu riƙa communicate, wancan Numban taki idan na kira ba ta shiga”.

“Wlh kuwa, wayan faɗi tayi shiyasa ai”. Rumanatu taƙarishe maganar nata tana amsar wayan Ayush ɗin ta soma ƙoƙarin saka mata Numban

Daga nan hira suka soma yi don Ayush tace mata “ba yanzu zata wuce ba,” don haka Rumanatun ta miƙe domin ta girka mata wani abun, tare suka shiga kichen ɗin tana taya ta.

 

 

 

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

 

Ƙarfe 06:01pm. Ɗahira ta gama komi nata ta haɗa kan files ɗin dake gaban ta, sannan ta ɗau jakan ta tare da files ɗin ta fito cikin Office ɗin nata, rufewa tayi tana juyowa shima Usman ya fito daga office ɗin sa riƙe da kai yana yamutsa fuska

Idanun su ne suka haɗe waje ɗaya yayinda gaban ko wannen su yayi mummunan faɗuwa, musamman ma na Usman wanda ya kasa jurewa har sai da ya runtse idanun sa zuciyar sa na masa wani irin ƙunci

Ya tsani wannan yanayin a koda yaushe da yake rinskan sa, that’s why ya tsani ganin Ɗahira sabida duk idan idanun sa zasu shiga nata to tabbas sai ya rasa nutsuwar sa tare da bugawar zuciya

Buɗe idanun sa yayi tare da sake tamke fuska yana kallon bayan ta da har ta buɗe Office ɗin kusa da ita ta shige

Dogon tsaki yaja ya janyo ƙofan sa yayi gaba cikin tafiyan sa na taƙama.

 

Office ɗin Dr. Rahab abokiyar aikin ta tashiga, files ɗin dake hannun ta takai mata ta fito ta nufi hanyan da zai sada ta da Lifter

Usman na ciki yana ƙoƙarin danna numbobi ta’iso wajen, idanun su ne suka sake haɗe wa waje ɗaya, yayinda suka bi junan su da wani irin kallo me cike da tsantsan tsana

Duk da yanayin da yake ji da ganin wannan idanuwan nata masu matuƙar faɗar masa da gaba but yaƙi ya ɗauke nasa idanun a kan ta, illa aika mata da saƙon tsanar da yake yi

Har sai da ƙofan ta kusa rufe wa kafin Ɗahira ta janye idanun ta taci gaba da tafiya ta nufi Steps, ta gummaci ta ɓata time ɗin ta wajen sauka ta bene da ta haɗa hanya da mutumin da zuciyarta tafi tsana a rayuwan ta

Ko kaɗan ba ta ƙaunar haɗuwa dashi a rayuwan ta, musamman yanzu da ta ganshi ya fito a Office ɗin dake kallon nata wanda ta tabbatar da cewa nasa ne, wani irin baƙin cikin hakan taji a ran ta

Tsaki ta dinga jerawa har ta sauka ƙasa ta fita daga cikin Hospital ɗin ta nufi parcking lot, motan ta tashiga taja tabar asibitin gaba ɗaya.
[5/28, 9:39 PM] Oummu Ɗahirah: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTORS*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER’S ASSO📖*
“`®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓“`

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA’S FAMILY*_

 

*EPISODE Nineteen*

Horn tayi a bakin tanƙamemen Gate ɗin gidan su

Babu ɓata lokaci me gadi ya buɗe mata

Ta kutsa hancin motan cikin gidan, yayinda ta nufi parcking space Direct ta faka motar, jakar ta; ta ɗauka da wayan ta tafito ta rufe ƙofan motan tare da saka mata keey, mayafin ta tagyara kana ta nufi cikin gidan cikin tafiyan ta na tsantsan yanga wanda ya zame mata jiki

Usman dake cikin motan sa yana amsa Call yabi ta da kallo time ɗin da tazo ta gifta shi, kallon ta kawai yake yi har ta ɓace wa ganin sa kafin ya ɗauke kansa, a ransa kuwa yana jan tsaki cike da jin haushin kallon ta da yayi, shi mamaki ma take bashi ta yanda take irin wannan tafiyan tamkar baza ta taka ƙasa ba, kai da gani kasan tana ji da tashen ƙuruciya da tsantsan yanga, wanda shi a ganin sa iya Shege ne, be san cewa Nature ɗin ta bane hakan, ya riga ya zama jinin jikin ta, har a maganar ta da komi nata cikin yanga take yin sa tare da sanyin jiki sosai, shiyasa komi nata daban ne, she has a very classy class.

Wayan sa ya janye daga kunnen sa ya fito cikin motan ya rufe, jin ana kiran sallah sai ya nufi bakin famfo na can wajen masu gadi yayi alwala ya fice a gidan zuwa masallaci.

 

 

 

⚫⚫⚫

Ɗahira na shiga cikin parlour’n su da sallama a bakin ta, babu kowa cikin parlour’n don haka Direct cikin ɗakin su ta nufa

Tana shiga bata zauna ba ta shige Toilet bayan ta ajiye jakar ta da wayan ta, alwala ta ɗauro ta fito

Time ɗin ne itama Fadila ta shigo cikin ɗakin don itama dawowar ta kenan, itama jakar ta ta’ajiye ta nufi Toilet ta ɗauro alwala, tazo ta shimfiɗa sallaya kusa da na Ɗahira ta tada sallah.

 

Ɗahira ta soma idar wa, don haka ta miƙe ta fice cikin ɗakin, ɗakin Maman ta tanufa

Tana zaune a kan sallaya tana azkar, sallaman da Ɗahiran tayi ta amsa mata tana bin ta da kallo

A kan sofa ta zauna tana kallon Maman nata har ta ida azkar ɗin

Sannu da gida Ɗahira tayi mata

Ta amsa mata tana tambayan ta “har kun dawo?”

“Eh Mama”.

“So Masha Allah, what is your job? Is there no problem?”

She smiled Ɗahira and said, “It’s all right, Mama.”

Gyaɗa kanta ta ɗan yi kafin tace, “Then go to the kitchen and get some food, and if you leave it later, then.”

Gyara kwanciyar ta Ɗahira tayi saman dogon kujeran tana ɗaura hannun ta saman kanta tace, “I’ll eat later.”

 

Aunty Amarya bata sake cewa komi ba taci gaba da addu’o’in ta, har sanda ta gama ta tashi ta fice cikin ɗakin.

 

Ita kuwa Ɗahira tana nan kwance tana tunane-tunane cikin ranta, kuma duk tunanin nata akan Masoyin ta ya ƙare, zuciyar ta na ƙwaɗaita mata son ganin shi matuƙa, tana son sanin ko wane ne but ya ƙi amince wa su haɗu, Allah ya gani tana ƙaunar sa itama, zata so su haɗu ko dan ya nuna mata soyayyar da yake mata a zahiri ba a cikin waya ba, har yanzu ba su taɓa yin waya ba, ko ta kira ba ya shiga, amma kuma idan ta tura text babu daɗe wa yake turo mata reply.

Numfashi taja tana juya kwanciyar nata fuskarta ƙunshe da murmushi.

Aunty Amarya da ta shigo tana kallon ta, kaɗa kai kawai tayi bata ce mata komi ba, sai da ta daidaita kanta a sallaya sannan ta sake duban ta tace, “To idan kin gama murmushin da saƙar zucin; ki tashi ki je kiyi sallah, Abbun ku ya dawo ma yana neman ki”.

Murmushi kawai Ɗahira tayi tana kallon Maman nata da har ta soma sallan ta tamkar ba ita ce tayi maganar ba, tashi tayi tana sosa kanta cike da kunya da ya kama ta jin abinda tafaɗa mata, ta fice a ɗakin.

 

Bayan kowa ya idar da sallan sa fitowa suka yi suka hallara a kan dainning, cike da nishaɗi suke gudanar da dinnern su, kai da gani kasan suna farin ciki, musamman yanda Abbu ke ta jan su da hira yana tsokanar su don shi dama al’adan sa ne tsokanar ƴaƴan sa, yana da son yara kuma ba ya da ɗaurewar fuska ga iyalan sa.

 

A haka har suka gama cin abincin suka dawo Parlour suka yi zaman hira, in ka ɗauke Fadila da tuni ta shige ɗaki abun ta, don ita bata cika zaman hiran ba ne sai ta ga dama, kuma ko ta zauna baza ta ce uffan ba, wayan ta ko t.v su ne kaɗai abokan hiran ta, wani lokacin kuma idan an sako ta takan saka musu baki ko tayi murmushi, babu me damuwa da halin nata tunda ba baƙon abu bane a gidan nasu, ba ita kaɗai ba gaba ɗayan su hakan a jinin su yake, sai dai nata abun ya girmama ne, to zan iya cewa halin su ɗaya da Usman domin miskilancin ya girmama.

 

 

 

 

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

 

*Ƙarfe 11:30pm.*

Lokacin ne Hajja Fatu ta tura ƙofan ɗakin mijin ta tashiga da sallama

Be ɗago kai daga aikin da yake yi cikin Laptop ba ya amsa mata

Taho wa tayi ta samu wuri gefen gadon kamar yanda shima yake zaune, ta zauna tana kallon Laptop ɗin, duk da kuwa ba ta ganin abinda yake yi a ciki amma hakan be sa ta ɗauke kanta ba, illa ma ƙoƙarin leƙa wa da take son yi

Shi kuma jin tayi shiru sai ya ɗan ɗago kansa kaɗan ya kalle ta, ganin tana leƙa masa Laptop sai yace, “lafiya dai Hajjaju, what do you want to see?”

Ɗan ja da baya tayi cikin basarwa duk da kuwa taji kunyan kama ta da yayi, sai lanƙwaye murya da tayi tace, “to Abban Baffa laifi ne don na leƙa naga me kake yi? Don’t forget that I am also a doctor.”

 

“Eh ke doctor CE sai aka yi ya ya? Ko an ce miki wannan aikin Hospital ne?” Yayi maganar yana yatsina fuska

“Uhmm Abban Baffa why are you like this to me? Mene ne dalilin ka na son ɓoye min sirrin ku? Kar ka manta fa Ni matar ka ce kuma uwar ƴaƴan ka, sannan a duk matan gidan nan Ni kaɗai ce wacce tayi ilmi me zurfi har kuma take ci da gumin ta, idan baku saka Ni a al’amuran ku na taimaka muku ba; to wa zaku saka? Wlh ba na jin daɗin abinda kake min kwata-kwata, na kula ko kaɗan kana ɗauka ta wata aba ce daban saɓanin yanda ni na ɗauke ka”. Hajja Fatu taƙarishe maganar nata cikin tsantsan damuwa da ya nuna a muryan ta, tabbatan dai abinda mijin nata yake mata ba ya mata daɗi

Murmushi Abba ya saki cike da mamakin matar tasa, shi be ga abinda yake mata ba da koda yaushe idan taga yana aiki sai tayi ƙorafi, musamman idan ya nuna mata aikin be shafe ta ba duk lokacin da ta buƙaci taya sa, to shi me zai saka ya bata bayan wannan sirrin Business ɗin su ne da ƴan uwan sa, don tana aiki a Hospital ɗin ai ba yana nufin tasan sirrin su bane, da me tafi sauran matan gidan ne?…

“Abban Baffa, I am talking and you are listening because you have made Me nothing.” Maganar ta takatse masa tunanin sa

Still murmushin yayi yace, “kin fiye rigima ke kam Hajjaju, kin ga na nemi taimakon ki ne? Meyasaka baza ki ji da naki aikin ba? Ko da ma abinda ya shafi aikin asibiti ne ai ba ɓangaren mu ɗaya ba bare ki taya ni, ki je abun ki na gode”.

A fusace Hajja Fatu take kallon sa, cikin takaici da halin mijin nata da har yanzu ya ƙi ya gane tace, “haka kace ko Alhaji? Well shikenan God help”.

 

Da gama maganar; ta miƙe ta nufi ƙofa don ficewa, duk da har aranta ta nuna masa fushin ta ne don ta san halin sa zai iya dawowa da ita, daga nan ma ya faɗa mata abinda yake yi, ita kuma ta samu damar shiga jikin sa har tasan sirrin komi nasu

Amma kuma ga mamakin ta har ta buɗe ƙofan be ce mata komi ba, ɗan juyo wa tayi ta kalle sa sai taga aikin sa ma yaci gaba dayi tamkar ma be san da ita wajen ba, hakan ya ƙara tunzura ta; ta fice tana bugo ƙofan cike da tsantsan takaici

Murmushi Abba yayi yana bin ƙofan da kallo, kana ya girgiza kansa yana maida kansa yaci gaba da abinda ke gaban sa.

Fitowan Hajja Fatu itama Shakira ta fito a ɗakin ta, kallon Mahaifiyar nata tayi cike da nazarin ta kafin kuma tace, “Lafiya Hajja me ya faru ne?”

Huro hanci tayi tana ɗaga idanun ta ta sauke kan Shakiran dake tsaye tana jiran amsar nata tace, “It’s me and your father. Let’s talk about it tomorrow. I’m not feeling well. What are you doing here?” Ta sauya maganar da tambayan ta

Shakira tace, “I just came out to drink water, har na fara barci ishin ruwa ya tado ni”.

Bata ce mata komi ba ta nufi ɗakin ta tabuɗe ta shige

Da kallo Shakira tabi ta dashi, har sai da ta shige kafin ta janye idanun ta tanufi bakin Fridge, buɗe wa tayi ta ciro goran ruwa tasha sosai, sannan ta mayar ta rufe ta koma ɗakin ta.

 

 

 

.

 

 

_plz I don’t get a lot of comments, if you don’t like it please tell me in Dena, don ba nan kaɗai nake yi ba, can da suka fi buƙata sai in riƙa musu su kaɗai, ta comments ɗin ku kawai zan san kuna so aci gaba._

_kar ku manta Vote and share._
[5/29, 7:11 AM] Oummu Ɗahirah: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR’S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL._

*بسم الله الرحمن الرحيم*


𝐅𝐄𝐄𝐍𝐀𝐇 𝐖𝐑𝐈𝐓𝐄𝐑’𝐒 𝐀𝐒𝐒𝐎📖*
®Ɗ𝚊𝚢𝚊 𝚝𝚊𝚖𝚔𝚊𝚛 𝚍𝚊 𝙳𝚞𝚋𝚞💪✓

𝗝𝗜𝗞𝗔𝗥 𝗟𝗔𝗪𝗔𝗟𝗜 𝗖𝗘✍️

𝗪𝗮𝘁𝘁𝗽𝗮𝗱: 𝗨𝗺𝗺𝘂𝗗𝗮𝗵𝗶𝗿𝗮𝗵👈

\𝗙.𝗪.𝗔📚/

𝗦𝗔𝗗𝗔𝗨𝗞𝗔𝗥𝗪𝗔
𝑁𝑎 𝑠𝑎𝑑𝑎𝑢𝑘𝑎𝑟 𝑔𝑎 𝐹𝑎𝑚𝑖𝑙𝑦 𝑛𝑎 𝑔𝑎𝑏𝑎 ɗ𝑎𝑦𝑎. 𝗚𝗢𝗠𝗔’𝗦 𝗙𝗔𝗠𝗜𝗟𝗬.

 

*EPISODE Twenty*

Da sannu rayuwa taci gaba da gudana, zuwa wannan lokacin Familyn Dr. Al’ameen suna ta shirye-shiryen zuwa Kano ne Bikin Salma (Ƴar Hajiya Laila), yanzu haka saura wata ɗaya

Kaka da kansa ya ba da odan kaya ya raba musu, wai wanda zasu ci biki dashi, matan kaɗai, daga iyaye har ƴan matan, har da su Aunty Zainab da Aunty Zulaiha sai da ya saka aka aika musu dashi, kala bibbiyu ne atamfa da Swiss less, kuɗin su kuwa zai kai dubu ɗari ko wanne, daga gani kasan kayan masu uban tsada ne, sun yi murna matuƙa, nan da nan kowa yakai ɗinki inda zai iya kai wa

Kafin ranan bikin kuwa tuni an amso musu, ranan Alhamis ƴan matan suka shirya tafiya, matan gidan kuma sai gobe juma’a za su taho, su kuma su Big Dady ranan ɗaurin auren asabar za su je, gaba ɗaya har dasu Usman, sannan kuma su dawo a ranan.

 

Tun 11:00am. Suka gama shirin su, ko wacce da jakan ta a hannu, har haraban gidan iyayen su mata suka rako su

Drever ya amsa jakunan nasu ya saka a bayan mota

Yusra ce ta shiga gaba, su kuma su uku a baya, drever’n yaja motan suka ɗau hanya cike da ɗoki

To dama ba wai sun saba zuwa sosai bane, kasancewar Boarding school suka yi a A.B.U Zaria, shiyasa ba su da lokacin kansu bare su riƙa ziyarce-ziyarcen ƴan uwa, kuma suna gamawa suka soma aiki, wannan dalilin ne yasa sun daɗe rabon da su je Kano, gwara-gwara ma Katsina, hutun ƙarshe da suka samu kafin su gama school a can suka yi, sai kuma suka ƙarisa sauran a Maiduguri, Kano ne dai sun shafe kusan shekaru biyar rabon da su je.

Zuwa ƙarfe 02:00pm. Tayi musu a Kano, Direct family house ɗin *General Isah Basheer Isah (Walid)* suka nufa, wanda a yanzu ake kiran sa da Granny

Gate aka wangale musu drever yaja motan zuwa ciki, be tsaya ba sai a ɓangaren su Salma, kasancewar gidan babba ne me Part-part, da ƴaƴan sa guda hudu maza da jikokin sa waɗanda suka yi aure su wajen uku duk a cikin gidan suke da zama, kuma kowa da na shi Part ɗin, sai na Granny ɗin da matar sa da suke ce mata INNA Haja.

Tun kafin ma su fito daga motan su Salma suka fito tarban su, dayake sun san da zuwan su, ƴan mata ne kusan su goma kuma duk jikokin Granny ne, a ciki har da ƴaƴan yaran sa mata da sukai aure a wani wajen

Sai kuma Shamsiyya da itama tazo tun jiya

Nan da nan suka karaɗe ɓangaren da murna da ihun ganin juna, daga baya kuma suka ɗunguma zuwa ciki

Hajiya Laila na zaune a parlour’n ta tana jiran isowar su, ganin su yasa ta washe bakin ta kafin ta fara musu maraba

Gaba ɗaya wajen ta suka isa suna gaishe ta cike da tsananin farin ciki a fuskokin su

Bayan sun gama gaishe-gaishen ne ta tashi taba su waje, nan kuwa suka ƙara ɓarke wa da Surutu ana hiran yaushe gamo, Sarkin surutu Firdausi tuni ta soma zuba ko haɗiye miyau ba tayi, tana ɗire aya take ɗaukan wani

Yau har da Fadila ba’a bar ta a baya ba, domin tayi zaman ta cikin ƴan uwa ana ta hiran da ita

Sai daga baya ne ma da Hajiya Lailan ta fito, take musu tsiya “ko abinci basu ci ba sun zauna suna ta zuba zance”

Salma ita da su Shamsiyya suka tashi suka haɗo musu abincin, duk sun baje a parlour’n suna ci suna ci gaba da hiran su cike da nishaɗi.

Ƴaƴan Hajiya Lailan ne guda biyu maza, Bashir (Abba) da kuma Yaseer suka shigo cikin parlour’n, yanzu haka ko wannen su da iyalan sa, shi Abban ne babban jikan gidan

Gaishe su suka yi cikin girmamawa, su ma suka amsa cike da fara’a da nuna farin cikin su na ganin su, har da tambayan su Baffa da Usman tare da sauran ƴan gida, duk suka amsa musu da “lafiya lau sun ce a gaishe su,” daga nan suka wuce ɗakin Mahaifiyar su suka bar su nan suna ci gaba da hiran su

Ɗahira ce ta kalli Fardausi da ta cika su da Surutu, don ita ce ma ƙarfin hiran, cikin tsokana take ce mata, “Ni wlh da an haɗa ku gaba ɗaya Dady ya aurar daku, ko gidan ma sun huta da surutun ki, yarinya ko haɗiye yawu ba ta yi”.

Dariya gaba ɗaya aka kwashe dashi

Ita kuma Firdausin gyara zaman ta tayi har da karkace ɗankwalin kanta tana faɗin, “me kuke ci na baka na zuba? Ai wlh marriage is time and I’m here to do, amma wlh bazan yarda a haɗa Ni da Salma ba, dole sai na zauna nima na taɓa ƴan matanci na Ni kaɗai, haka kawai ai bazai yiwu ba”.

Hararan ta Salma tayi tace, “dalla yi mana shiru, Ni wlh ban san ma meyasa Dady ya ƙi tilasta miki fiddo da mijin ba, uwar ma me zaki sauna yi musu bayan ba kya cas ba kya as”.

Itama dai Firdausin hararan nata tayi tace, “eh naji dai, baza ai mana auren tare ba ƴar baƙin ciki, wlh nima yanda kika fara aiki kafin kiyi aure, nima bazan yi ba sai na soma aiki na”.

Tsaki kawai Salma taja tana sake kwaɗa mata harara

Firdausin ramawa ta kuma yi, har da murguɗa baki

Dama sun saba kasancewar saƙo da saƙo suke, bare kuma dama Salma tana jin haushi an ce ta fito da miji a haɗa da na sauran yayyin su biyu maza da za ayi musu aure, ita kuma Firdausi da sauran ƴan matan ba’a ce musu ba, hakan yasa take jin haushi tunda ba’a haɗa su gaba ɗaya ba

Su dai sauran sai dariya suke musu, basu tashi ba sai da aka kira sallan la’asar, sai ma lokacin ne su Ɗahiran suka tuna basu yi azahar ba, ganin ƴan uwa da hira ya shagaltar dasu

Ɗakin su Salma suka wuce, wasu daga cikin su kuma suka koma nasu Part ɗin, sallan suka gabatar kafin Ɗahira ta miƙe tana kallon Firdausi dake zaune kan sallaya, tana latsa wayan ta da aka kira time ɗin tana sallah

“Fido tashi ki raka Ni mukai gaisuwa wajen Granny da ƴar tsohuwar matar sa, tun kafin ma ya aiko”.

Ɗago kai Firdausi tayi tana dariya tace, “wlh nima dai naga haƙurin sa da be aiko a kira ki ba”.

“Ko dai be san ta zo bane?” Cewar Haneefa dake zaune itama kan dadduman

“He knows, tunda Ni naje na shafa masa labari har ɗakin sa yau za su zo”.

Ɗahira ta murmusa tana faɗin, “Let’s go. Please, I’m too tired to see him, because I’m missing him.”

Salma tace, “oh wa yaga Ɗahira matar tsofaffi, Ni na kula ma tsofaffin nan duk sun fi son ki, Anya ba da ɗaya za ayi ba between Kaka and Granny?”

Dariya suka kwashe dashi sauran cike da shaƙiyanci.

Fadila da Shakira ma duk tashi suka yi suka bi bayan su Ɗahira don su gaida Granny ɗin, a Parlour suka tarar da Yusra dake zaune ita da Hajiya Laila, nan suka yi mata bayanin “za su je gaishe da Granny ne daga nan su je sauran ɓangaren su gaishe su,” har da Yusran suka tarkata suka tafi.

Part ɗin Granny suka soma zuwa, lokacin Inna Haja na sallah a ɗakin ta

Koda suka leƙa suka ga tana sallah ne sai suka nufi ɗakin Granny, yana zaune kuwa yana duba ƙur’ani, shima idar da sallan sa kenan, dayake ba ya iya fita sabida ciwon ƙafa da yake fama dashi, duk da ba’a Wheel chair yake zaune ba, kuma yana iya tafiya amma ba me nisa ba

General Isah Basheer Isah (Walid) kenan, tsoho me ran ƙarfe, kai da gani kasan an zuba ƙaƙƙarfan jarumi sanda yake matashi, har yanzu kuma idan ka kalle sa zaka ga zubin jarumtar sa, don daga gani kasan da sauran ƙarfin sa sosai, sai dai kawai tsufa ne da yayi, ga furfura da duk ya cika masa kai, kasancewar sa ba me barin gemu ba shiyasa babu komi a wajen sai ƙananun gashi farare kaɗan-kaɗan.

Shigowar su yasaka ya ajiye ƙur’anin yana ɗago kansa tare da cire medical Glass ɗin sa, fuskar sa yalwace da murmushi yake amsa gaisuwar da suke masa tare da bin su ɗaya bayan ɗaya yana kallo

Cikin tsokana Firdausi tace, “wai kuwa ka gane su Granny? Ko sai na maka bayani tunda naga idanun naka sun tsufa da yawa?”

Dariya yayi kafin yace, “ke kam baki da kirki Nana Firdausi, yo idan har bazan gane su ba kema ai bazan iya gane ki ba”.

Gaba ɗaya fashe wa da dariya suka yi, ban da Firdausi da ta kwaɓe fuska tana ma Granny shagwaɓa.

Nan ya soma tsokanar su Ɗahira bayan ya tambaye su mutanen gida, suka zauna suka biye masa suna ta kwasan dariya

Itama Inna Haja da ta idar da sallan, ɗakin ta shigo ta zauna ana yi da ita.

Sai da suka daɗe a nan shashin kafin suka wuce sauran sasukan, suka gaishe da su, a Part ɗin Baba ƙarami suka shantake sukai ta kwasan hiran su.

Washe gari da safe sai ga Hajiya Ikram ta bugo sammako, ita da ƙannin Shamsiyya, sai Babban ƴar ta wacce take aure a Katsinan Aunty Mimi da nata yaran sun taho tare

Zuwa wajen sha ɗaya su Aunty Zulaiha da Aunty Zainab su ma suka zo, gida sai sake cika yake yi kowa ya hallara.

Da yamma sai ga su Aunty Amarya, Hajiya da Umma sun taho, ban da Hajja Fatu, ita zata biyo su Big Dady ne washe gari ranan auren, idan kuma za su koma su Big Dadyn sai su Hajiya su bi su, ita kuma Hajja Fatu za su dawo ranan Lahadi tare da su Ɗahira.

Tunda safe su Ɗahiran ma suka tafi yawon su, babu inda ba su zagaya ba, ba su nan ba su can, ko zama ba sa yi, sai da dare ne ma da suka dawo daga yawon na su suka ga su Hajiya sun zo.

The following day aka ɗaura auren Amarya Salma, sannan aka wuce gidajen Sauran amaren yayyin su aka ɗaura na su

Biki yayi biki, mutane tamkar tsaki, haka suke ta ɓulɓulo wa, su Yusra ma ko ganin ƙeyan su ba ka yi, ana can ana ta shan biki.

Da dare tare da su aka kai amarya gidan ta, sai dai a cikin su babu wacce ta kwana sai Yusra tunda za’a kwanar ma Amarya, tare da sauran dangi da aka bar mata.

 

Zuwa washe gari da yamma suka yi haraman tafiya, ƙarfe 06:30pm. Suka shigo Kaduna.

 

 

 

*WASHE GARI*

Monday tushen aiki, tunda Ɗahira ta shiga Office ɗin ta yau bata huta ba, sosai take da Patients waɗanda zata duba, shiyasa tunda ta shiga ta duƙufe take faman aiki, gaba ɗaya ta gama gajiya ga shi taƙi huta wa kanta.

 

Ƙarfe 05:30pm ta tashi, ta fito daga Office ɗin ta tarufe da keey tayi hanyan Lifter, dayake ta gaji sosai shiyasa tafiyan nata ma sai ya sauya salo, dama gata akwai yanga bare kuma yau me lasisi ne, buɗe Liftern tayi ta shige, tana shirin rufe wa sai ga Usman cikin saurin shima ya shigo, be ma kula da ita ba sai da ya shigo ɗin idanun su suka faɗa na juna, da sauri ko wannen su ya janye nashi suna haɗe rai alokaci ɗaya

Ƙofan fita Ɗahira tayi zata fice, don baza ta iya haɗa hanya dashi ba, sai dai kafin takai ga ficewar sai ji tayi ya jawo ta kiiiiiii.. ta dawo baya, ya jefar da ita wanda tuni ta je ta haɗe da jikin Liftern, saboda azaba ta ƙwalla ƙara tana dafe ƙeyan ta da sauri

Ko a jikin sa sai ma danna number da yayi ya rufe ƙofan, sannan ya tsayar da Liftern cak, yana juyowa gare ta fuska a haɗe..

 

[5/30, 8:44 AM] Oummu Ɗahirah: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR’S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL._

*بسم الله الرحمن الرحيم*


𝐅𝐄𝐄𝐍𝐀𝐇 𝐖𝐑𝐈𝐓𝐄𝐑’𝐒 𝐀𝐒𝐒𝐎📖*
®Ɗ𝚊𝚢𝚊 𝚝𝚊𝚖𝚔𝚊𝚛 𝚍𝚊 𝙳𝚞𝚋𝚞💪✓

𝗝𝗜𝗞𝗔𝗥 𝗟𝗔𝗪𝗔𝗟𝗜 𝗖𝗘✍️

𝗪𝗮𝘁𝘁𝗽𝗮𝗱: 𝗨𝗺𝗺𝘂𝗗𝗮𝗵𝗶𝗿𝗮𝗵👈

\𝗙.𝗪.𝗔📚/

𝗦𝗔𝗗𝗔𝗨𝗞𝗔𝗥𝗪𝗔
𝑁𝑎 𝑠𝑎𝑑𝑎𝑢𝑘𝑎𝑟 𝑔𝑎 𝐹𝑎𝑚𝑖𝑙𝑦 𝑛𝑎 𝑔𝑎𝑏𝑎 ɗ𝑎𝑦𝑎. 𝗚𝗢𝗠𝗔’𝗦 𝗙𝗔𝗠𝗜𝗟𝗬.

 

*EPISODE Twenty One*

Wani kallon tsana yake aika mata dashi, sai dai ya kasa magana duk da kuwa so yake yi ya faɗi wani abun

Ɗahira a hankali ta ɗago kanta her eyes filled with tears, and she looked at him, yanda ya haɗe rai yasaka ta kasa faɗa masa magana, illa haɗiye yawu da tayi tana aika masa da kallo me cike da tsana gami da haushin sa

Sake haɗe rai yayi, cikin izza irin ta shi yace, “har ke kin isa ki kai ƙara ta wajen iyayena ko? Kina jin kin girma kin zama macen da zaki iya ja da Usman Noor Al’ameen?”

Ɗauke kanta tayi a kansa tana sake dafe ƙeyan ta

Tsawa ya daka mata da faɗin, “Am I not talking? Uban wa ya baki ƙwarin gwiwan da zaki kai ƙara na wajen iyaye na?”

Sosai Ɗahira ta tsorata da yanda ya daka mata tsawa, nan da nan jikin ta ya soma rawa ta ƙanƙame jikin ta tana hawaye

Matsowa kusa da ita yayi yana saka hannu ya jawo kanta ta yanda za su haɗa idanu, sosai ya matse mata kan, wanda ya sa ta dinga zubar da hawaye tare da rufe idanun ta gam

“This is the first and last time you would do such a thing to me again, domin Ni ba abokin wasan ki bane, idan ba haka ba uhmmm”.

Sai ya ci je leɓen sa na ƙasa yana sakin kanta, ya juya ya danna Numban Liftern yaci gaba da tafiya, yana kai su downstairs ya buɗe ya fice.

 

Ɗahira dake durƙushe a ƙasa tana ta shashsheƙan kuka, ko motsin kirki ta kasa yi sabida baƙin ciki da ƙuncin da ya cika ta, ji take yi tamkar ana tsaga magudanan jinin ta ana ƙara rura wutan tsanar da take yi masa

“Shin ta ya ma zata iya bari wani ƙaton banza ya zauna yana mata irin cin mutuncin nan? Kamar ta? Me ta tare masa ne?”

Ta jima a haka kafin ta share hawayen ta tare da gyarawa eyeglasess ɗin ta zaman sa, ta miƙe ta buɗe Liftern ta fice, a hankali ta taka har gaban motan ta tabuɗe ta shige, ja tayi tabar Hospital ɗin.

Tuƙin take yi amma hawaye na kwaranya a kyakkyawar face ɗin ta, maganganun Usman ne ke dawo mata kwanya, a haka har ta kai gida tayi parcking motan, sai dai ta kasa fitowa sai ma sake fashe wa da tayi da sabon kuka, sosai ranta ke suya da abinda yayi mata, ta rasa meyasa tarasa ƙwarin gwiwan da zata iya mayar masa da martani, alhanin tayi wa kanta alƙawarin baza ta sake barin sa yaci mata mutunci ba, ko kaɗan baza ta iya jure wa ba, shiyasa abinda yayi mata yanzu yayi mugun ɓata mata rai

Kifa kanta tayi saman sitiyarin motan tana rufe idanun ta ruf, tunanin abinda zata yi masa ta huce take yi, but ta kasa, don haka ta ɗago kanta ta share fuskarta tare da gyarawa ta fito daga motan, rufewa tayi ta wuce Part ɗin su.

 

A ranan sukuku ta wuni ta kasa taɓuka komi, duk idan ta saki jikin ta sai ta tuna abinda ya faru ɗazu, sai kuma gaba ɗaya ta rasa fara’an ta

Aunty Amarya da ta kula da yanayin ƴarta, tayi mata magana, but Ɗahira ce mata tayi, “babu komi”. Dole ta ƙyale ta don ta san halin ta akwai zurfin ciki wani lokacin.

 

Washe gari tana tashi daga barci ta kunna wayan ta, ta soma cin karo da saƙon masoyin ta, yawanci duk complain yake mata a kan rashin reply ɗin ta, kasancewar tunda ta dawo daga aiki ta kashe wayan bata sake kunna wa ba

Murmushi kaɗai tayi ta ajiye wayan ta shige Toilet, sai da tayi wanka kafin ta dawo ta mayar masa da reply ɗin, sannan ta shirya cikin doguwar riga abaya fara me kwalliyan stone da ratsin ja, ta yane kanta da gyalen sannan ta fito

Ɗakin Aunty Amarya ta shiga, tayi mata sallama zata tafi, har ta kai bakin ƙofa ta kira ta tana tambayan ta “taci abinci?”

Dayake Ɗahira ba me yawan yin ƙarya bace don bata saba ba, sai tace mata “a’a but zata ci idan taje can”.

Hararan ta Aunty Amarya tayi tace, “yi maza je kici abinci kar in saɓa miki”

Dole ba don ta so ba ta’amsa mata da “to”. Sannan ta fice

Kan dainning ta wuce ta zauna ta soma haɗa tea, shi ne kaɗai abinda zata iya saka wa a bakin ta don ba daɗin jikin ta take ji ba, ga kanta dake ta faman sara mata sakamakon kukan da tasha jiya.

 

Fadila ne ta fito itama ta zauna akan dainning ɗin ta hau haɗa abun karin ta, sai da ta gama sannan ta kalli inda Ɗahira take a karo na biyu tun zuwan ta wajen, tun jiya ta kula da yanayin ta kamar tana cikin damuwa, sai dai kuma miskilanci ya hana ta tambayan ta, yanzun ma ganin Ɗahiran ta tafi tunani ta kasa shan tea ɗin ne ta kalle ta tace, “Sister, are you all right? What’s wrong with you?”

Ɗago idanuwan ta tayi ta kalli Fadilan kafin ta kau da kai tana sauke numfashi a hankali, ɗaukan tea Cup ɗin tayi tana bata amsa da faɗin, “nothing, I am thinking something”.

 

Fadila bata sake magana ba duk da kuwa bata gamsu ko kaɗan da amsar ta ba, sai ma ci gaba da tayi da yin breakfast ɗin ta.

Miƙe wa Ɗahira tayi tare da ɗaukan jakanta tayi hanyan fice wa, a Steps ta haɗu da Baffa zai yo Part ɗin su, sai ya tsaya yana kallon ta, yayinda itama ɗin ta tsira masa idanu, kafin kuma ta ɗauke nata ganin yanda yake mata kallon ƙurilla, ɗan dai-dai ta fuskarta tayi tana sakin murmushi tace, “Good morning my brother”.

Be amsa ta ba illa jeho mata tambaya da yayi, “What is wrong with you, my dear? What happened to your swollen eyes?”

 

Har a time ɗin murmushin fuskarta be gushe ba tace, “Yaya babu komi.. it’s just that I’m not feeling well”

“Shi ne kika yi kuka?” Ya sake jeho mata tambayar

Shiru tayi tana sauke kanta ƙasa

Sake matsowa kusa da ita yayi yana bin ta da kallo, sosai suka yi kusanci da juna, hakan yasa har suna jin hucin junan su

Da sauri ta ɗago kanta ta zuba masa manyan idanuwan ta, sai tayi saurin ja da baya gaban ta na matsanancin faɗuwa da ganin wasu abubuwa cikin idanun sa, wanda ta kasa fassara su illa saka ta a matsanancin faɗuwar gaba da suka yi, saurin runtse idon ta tayi saboda yanda ƙirjin ta ke sake bugawa sosai, ƙarar sahun takalman da taji yasa ta buɗe ido a lokaci ɗaya

Gaba ɗayan su daga ita har Baffa suka bi Usman da kallo, wanda yake dumfaro wajen su shima idon sa a kansu fuska a turɓune

Ɗahira ɗauke kai tayi daga kallon sa, tana mayar da idanun ta gefe

Lokacin har Usman ɗin ya iso wajen suna gaisa wa da Baffa, iyakan gaisuwa ya haɗa su ya wuce ya nufi hanyar Part ɗin Kaka

Idanu Baffa ya aza kan Ɗahira yace, “meyasa kike son min ƙarya ƙanwata? Kin san duk halin da kika shiga dole ne na gane? Sabida kin kasance mace me fara’a, wanda ba komi ne yake ɓata mata rai ba, kin kasance me juriya me ɓoye baƙin cikin ki ga maƙiya, why kike son nuna gazawan ki?”

Itama idanun ta da suka cika taf da hawaye ta mayar kansa

Ganin ƙwalla cikin idanun ta sai hankalin Baffa yayi mugun tashi, nan da nan ya rikice da tambayar ta yana saka hannu ya riƙo mata hannayen ta

Bata yi yunƙurin hana sa ba, illa lumshe idanu da tayi tana matse bakin ta, buɗe idon tayi cikin rawan baki tace, “How can you tell you what is wrong with me? What have I done? How can Yaya Usman hate me? Meyasa yake son muzguna ma rayuwa ta? Shin na taɓa yin masa laifi ne a rashin sani?” Taƙarishe maganar cike da ɗacin zuciya hawayen na silalo mata daga kuncin ta

Sake damƙe hannayen ta yayi cikin nasa, cike da sanyin murya yace, “Ƙanwata ki dena saka damuwa a kan abinda Usman yake miki, babu abinda kika yi masa, kawai Allah ne be haɗa jinin ku ba, amma insha Allahu wata-rana sai yayi alfahri dake a rayuwan sa, tabbas watarana komi zai wuce my dear, ki saka wannan a ranki zaki ce na faɗa miki, duk inda akwai jini dole ne akwai ƙauna, ke ɗin ƴar uwan sa ce, dole zai so ki kuma zai yi nadamar hakan, Plz ƙanwa ta wannan ya dena ɗaga miki hankali, I’m not happy to see you in this situation. wlh ina ji kamar zan mutu duk sanda na ganki a damuwa, ko kaɗan ba na jin daɗi”.

Murmushi ta saki hawayen ta na sake silalo wa, cikin farin ciki tace, “haƙiƙa shiyasa nake sake alfahari da kai yaya, wlh billahi kai kaɗai ka ishe Ni a matsayin Yaya, ina son ka yayana ina matuƙar son ka fiye da yanda kake so na! insha Allahu kuma bazan sake damuwa da ko wani abu da ya nuna min ba, domin kai kaɗai ka ishe ni”.

Murmushi sosai Baffa yake yi sakamakon jin zantukan ta, tsaban farin cikin jin kalman so a wajen ta, be san sanda ya janyo ta ya rungume ta ba; duk da kuwa ba yau ya soma jin hakan a wajen ta ba

Sosai Ɗahira ta zaro ido da ganin abinda be taɓa faruwa da ita ba, tayi saurin jan jikin ta tana matsawa da sauri

Sai shima a nan ne ya gane abinda ya aikata, yayi saurin saka hannu yana sosa kai cike da murmushi a face ɗin sa yace, “I’m so sorry Ƙanwata, wlh na manta ne”.

Murmushi tayi kawai tana kallon sa, sai kuma ta gyaɗa masa kai

Hakan sai yasa yaji daɗi sosai, don be yi tunani hakan daga gare ta ba, a kullum faɗa masa take yi ba ta ƙaunar irin wannan rayuwan, duk da shi a wajen sa ya saba sosai ga friends ɗin sa da yayi school tare da su, irin wannan rayuwan wayewan shi ne Baffa ya taso dashi, babu ruwan sa don ya rungume mace, amma tun sanda Ɗahira ta soma taka masa birki shima ya rage yi, duk wani halayen sa mara su kyau da yasan za su ɓata mata rai, ya dena su, duk sabida farin cikin ta, shiyasa a kullum sake ji yake yi ƙaunar ta na ƙara wanzuwa a cikin ƙalbin sa, idan har ya same ta a matsayin matar sa kuwa; to, tabbas ya gama dace a rayuwan sa, ita ɗin haske ne cikin rayuwan sa, zai so ya kasance da ita har abada a duniyar sa..

“Yaya mu je kar muyi late”. Tayi maganar tana kallon Wrest watch ɗin dake ɗaure a hannun ta

Murmushi yayi kafin yace, “tom dear”.

A tare suka fita daga gidan.

 

 

 

 

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

 

Washe gari aka wayi gari Kaka be da lafiya, zazzafan zazzaɓi ya tashi dashi, sosai hankalin iyalan gidan ya tashi, nan da nan aka ɗunguma aka yi asibiti dashi

Su Ɗahira suna can labari ya riske su, ai nan ko wannen su ya kiɗime, domin ba ƙaramin ƙaunar Kaka suke yi ba, ko kaɗan ba sa son abinda zai taɓa sa, duk da kuwa ya tsufa amma suna matuƙar ƙaunar sa; ba sa son su rasa sa, ga shi be cika ciwo ba shiyasa hankalin su ya tashi da ganin yanda jikin sa yayi mugun zafi.

Gaba ɗaya iyalan gidan sun hallara a bakin ƙofar ɗakin da aka shiga da Kaka, kowa hankalin sa a matuƙar tashe, da yawan su sun kasa zama sai zagaye suke yi, irin su Ɗahira kuwa sun kasa jure wa sai sharan hawaye suke yi.

 

Su Abbu na ciki su ne masu duba shi, su kansu hankalin su ya gaza kwanciya, sabida halin da suka ga Kaka ya shiga, sun kasa shawo matsalar sai faman zufa suke yi.
[5/31, 12:56 PM] Oummu Ɗahirah: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR’S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL._

*بسم الله الرحمن الرحيم*


𝐅𝐄𝐄𝐍𝐀𝐇 𝐖𝐑𝐈𝐓𝐄𝐑’𝐒 𝐀𝐒𝐒𝐎📖*
®Ɗ𝚊𝚢𝚊 𝚝𝚊𝚖𝚔𝚊𝚛 𝚍𝚊 𝙳𝚞𝚋𝚞💪✓

𝗝𝗜𝗞𝗔𝗥 𝗟𝗔𝗪𝗔𝗟𝗜 𝗖𝗘✍️

𝗪𝗮𝘁𝘁𝗽𝗮𝗱: 𝗨𝗺𝗺𝘂𝗗𝗮𝗵𝗶𝗿𝗮𝗵👈

\𝗙.𝗪.𝗔📚/

𝗦𝗔𝗗𝗔𝗨𝗞𝗔𝗥𝗪𝗔
𝑁𝑎 𝑠𝑎𝑑𝑎𝑢𝑘𝑎𝑟 𝑔𝑎 𝐹𝑎𝑚𝑖𝑙𝑦 𝑛𝑎 𝑔𝑎𝑏𝑎 ɗ𝑎𝑦𝑎. 𝗚𝗢𝗠𝗔’𝗦 𝗙𝗔𝗠𝗜𝗟𝗬.

*NASIHA*
_Sallah tana maganin duk cututtukan da suke samun zuciya. Ita ce haske mai kawar da duhu da zunubai. Abu Huraira ya ce, “Na ji Manzon Allah yana cewa:_
_”Ku duba nan; idan ɗaya daga cikin ku yana da rafi a bakin ƙofar sa kuma yana wanka cikin sa sau biyar kullum, shin wata ƙazanta tasa za ta yi saura?” Sai suka ce, “Ba wata ƙazantar sa da za tayi saura”. Sai ya ce, “Wannan kamar salloli biyar ɗin nan ne waɗanda da su ne Allah yake wanke zunuban mu”._
_A sallah ne ake ganin tahƙiƙanin daidaituwa da adalci. Lokacin da Ladan ya yi kira da cewa: “ku yi gaggawa zuwa Sallah, ku yi gaggawa zuwa ga falala. Duk waɗanda sallar ta rataya a kansu, masu arziƙi da faƙirai, manya da yara, sarakuna da talakawa – dukan su za su taru a sahu guda ba wani bambanci tsakanin su, dukan su bayin Allah ne. Za su taru a bisa aƙida guda a ɗakin Allah, suna tuna Allah kaɗai, suna tawali’u gare shi._

 

*EPISODE Twenty Two*

Wajen awanni biyu da shigar da Kaka, kafin su Abbu su fito, sai dai basu ba ma kowa damar ganin sa ba, sabida a time ɗin sun yi masa alluran barci; yana cikin barci, domin ba sa son ayi hayaniya da zai ja har ya farka daga wannan barcin.

 

Gaba ɗaya iyalan gidan sun kasa kataɓus a ranan, ko jirgawa sun kasa yi a baƙin ƙofar, sai da su Big Dady suka yi musu magana ne, akan “su tafi gida,” sannan ne su Hajiya suka koma gida, yayinda su Ɗahira kuma suka koma bakin aikin su, but jefi-jefi suna kewayo wa ko Kaka ya farka.

 

Har dare be farka ba, haka ilayan Doctor Al’ameen suka kwana a cikin wani hali a wannan ranan, sai washe gari aka samu ya farka, sai dai sosai suka shiga farin ciki a ranan, sabida Kaka ya samu sauƙi tamkar ba shi ba, babu wanda yayi tunanin zai tashi da lafiya haka, sai ga shi har magana yana iya yi, kuma yana iya yin sallan sa, domin tunda ya tashi ya buƙaci a kai sa yayi alwala, sai da ya gabatar da sallolin da ake bin sa, sannan ya samu yaci abinci daƙyar, aka ba shi magani ya sake komawa barci, sakamakon alluran da aka sake mishi, sabida ana son ya sake samun hutu sosai.

 

A ranan haka mutane sukai ta zuwa duba sa, gaskiya Kaka na mutane ne, ba ga talakawan ba; ba ga attajiran ba, manyan mutane kama daga ko wani gari duk ana ta zuwa gaishe shi, har mutanen Maiduguri dangin su duk sun zo wasu daga ciki duba sa, su Hajiya Ikram, Hajiya Laila tun a ranan suka shigo Kaduna.

Kwanan sa biyar a asibitin yana samun kulawa daga ƴaƴan sa da jikokin sa, ya samu sauƙi sosai, sai dai sun hana a mayar dashi gida dole sai ya ƙara samun sauƙi

Shi da kansa ya matsa musu dole suka sallame sa ya koma gida, a ranan sun ga mutanen anguwa, suna ta ɓulɓulowa gaishe da Kaka, da waɗanda suka je asibiti, da waɗanda ma basu je ba duk sun biyo sa gida.

Bayan kwana uku da sallamo sa ne, wanda ta kama ranan Lahadi, ya saka aka tattaro masa iyalan gidan

Bayan kowa ya hallara ya soma musu jawabi akan abinda ya sa ya tara su, ba komi bane illa maganar aure

“Fodio da takwara na da ku zan so ma, har yanzu shiru ban ji kun kawo min maganar wacce kuke so ba?” Yayi maganar idanun sa a kan su

Shiru suka yi ko wannen su, don basu yi zaton akan hakan ya tara su ba. Sai da Abba yayi musu magana kafin Baffa ya buɗi baki yace, “Kaka Ni dai har yanzu bamu gama daidaitawa da wacce nake so ba, but I will bring it to you in a short time, Calm down baza ka mutu ba insha Allahu sai ka ga auren mu”.

Sosai maganar Baffa ya ba wa waɗansu dariya, sabida yanda yayi maganar cikin barkwanci

Abba kuma daƙuwa yayi masa yace, “ka ga naka Baba na, ba maganar wasa ne ya tara mu anan ba kaji ko?”

Duƙar da kai Baffa yayi yana sosa ƙeya yana murmushi

Haka zalika ma Kaka murmushin yayi yace, “to takwara na Allah ya kawo ta lafiya, sai dai a wannan gaɓar lokaci zan ba ku, sabida ina so nan da wata ɗaya kacal ayi auren ku mu huta, ba wai ku kaɗai ba, ina nufin har ƴan matan, gaba ɗayan ku zaku fid do da miji ayi muku aure”.

Sosai maganar Kaka ya razana Ɗahira dake kusa dashi, dasauri ta ɗago kai ta zuba masa manyan idanuwan ta, kamar an tsikare ta kuma tace, “Kaka, do you mean us?”

 

Kallon ta yayi yana murmushi yace, “Yes, my wife, I hope all of you will be married in just one month, domin tabbas na san ba zan jima ba a duniyar nan, wannan ciwon ya ɗaga min hankali, shiyasa na yanke shawaran gaba ɗayan ku; ku fitar da mazajen aure sai a haɗa dana yayyin ku, zuwa nan da sati ɗaya na ba ku ko wacce sai ta turo wanda zata aura, kun ji ko?”

Gaba ɗaya amsa mishi suka yi, ban da Ɗahira da tunanin ta ma ya bar duniyar

Sai kuma Usman da tun sanda Kaka ya soma zancen, ya ɗaure fuskar sa tamau, ko ɗago kai ya ƙi yayi, bare kuma yasa baki.

Daga haka Kaka ya sallami kowa taron ya tashi

Ai kamar jira Ɗahira take yi tuni ta bar parlour’n, sabida ruɗewa har so tayi ta bangaji Usman da yazo ficewa shima, Allah ya tsare hakan be faru ba ta dawo hayyacin ta

Wani banzan kallo ya watsa mata yayi hanyar Part ɗin su hannayen sa biyu cikin aljihu.

Ɗahira bata bi ta kansa ba, tunda ba ta shi take yi ba, yanzu hankalin ta duk a tashe yake, burin ta kawai ta ƙebe tayi tunani, “shin ita wa take dashi ne da zata kawo a matsayin miji? Wannan tunanin shi ne yayi matuƙar wargaza mata duk wani walwalan ta da nutsuwar ta.

Tana shiga Part ɗin su, ta shige ɗakin su ta yaɗa zango a kan gadon ta, buga tagumi kawai tayi ta hau tunanin mafita, bata ankara ba sai ga hawaye

“Innallillahi wa’inna ilaihi raji’un! What is going to happen to me? By the time I get married no one has ever said he loves me, so who will I choose as my husband?” Tayi maganar a cikin zuciya tana me share hawayen da bayan hannun ta

Sai kuma ta saka hannu ta ɗauki wayan ta ta hau lalubo Numban Masoyin ta na ɓoye, wanda tayi serving Numban sa da My LOVE. Shiru tayi tana tunanin me zata yi, sai kuma ta soma kiran Numban, sai dai a kashe yake, wani yawu me ɗaci ta haɗiye cike da baƙin cikin da taji ya tokare mata maƙoshi, bata taɓa jin haushi irin na yau ba a duk sanda tayi yunƙurin kiran sa, amma wayan a kashe. wannan maganar me muhimmanci ne shiyasa ba ta so suyi sa a text message, tafi son ta Kira sa suna jin muryan juna, sannan ta faɗa masa abinda take so ta sanar masa.

Sai dai babu yanda ta iya haka ta tura masa text message kamar haka:

 

_”Now everything is over between us. If you really want me, then I need you to explain yourself to me at this time. I don’t want you to talk to me again unless you do what I need you to do.”_

Abinda ta rubuta kenan ta tura masa, sai ta kwanta tana lumshe idanun ta, tare da zaman jiran reply ɗin sa.

Bata fi mintuna goma da tura saƙon ba, sai ga reply ɗin sa ya shigo

Da sauri ta tashi zaune ta janyo wayan tana duba wa, sosai tayi farin ciki da amsar da ya bata, murmushi kawai take saki tana karanta wa

_”I am also waiting for this day to be beautiful, insha Allahu zuwa gobe zan bayyana miki kaina, just choose me when I come to you.”_

 

Take tayi mishi sending ɗin time ɗin da zai zo, ƙarfe 03:00pm. Tana tura masa ta kwanta tana zuba murmushi, tunanin kawai yanda haɗuwar na su zai kaya take yi, take ta lumshe idanuwan ta tana sake dulmiya a kogin tunanin masoyin nata.

 

 

⚫⚫⚫⚫⚫

Baffa dake tsaye kan benen Part ɗin su, yana tura mata text ɗin ya saki murmushi me fid da haƙora, ya sani dole ne wannan ranan zata zo, amma yanzu ya rigada ya gama shirya mata, ya shirya yanda zai fito fili ya bayyana ƙaunar sa ga masoyiyar sa, domin samun mallakan ta a matsayin matar sa, wanda ya daɗe yana tsimayen zuwan ranan

Wani kyakykyawar murmushi ya sake saki cike da farin ciki a ransa, shafa suman kansa yayi kafin ya soma taka wa ya wuce Part ɗin su, shiga yayi da sallama a bakin sa

Hajja Fatu dake zaune tana jiran dama shigowar sa ne, shiyasa ta zauna a parlour’n zaman jiran sa. Amsa mishi sallaman tayi tana murmusawa tace, “yauwa Baffa na, taho ka bani labarin surukar ta wa”.

Dariya ya saki yana isowa wajen ya zauna tare da faɗin, “kai Hajja wai dama jira na kike yi?”

“Iyi wlh, ai tunda kafaɗa na kasa zaune na kasa tsaye ina so inji wacce me sa’ar ce ta same ka?”

“Uhmmm Hajja kenan! Ko dai Ni ne me Sa’ar dana same ta, ke kanki Hajja sai kin yaba da zaɓi na, because you will never have a Daughter-in-law like her, I know you will be very happy if you know who she is”.

 

Cike da farin ciki Hajja tace, “yauwa ɗan albarka, wlh idan ka samo wacce tayi dai-dai da ra’ayina, you must finish everything for me, domin da ita ne zan riƙa ɗagawa a gidan nan, sannan zan fi kowa fariya”.

Baffa dai murmushi kaɗai yake zuba wa, yana kallon Mahaifiyar ta shi

“Ina jin ka yarinyan ƴar gidan wane ne?”

“Hajja ba wata bace sai Ɗahira wacce kika sani na gidan nan”.

 

 

 

 

 

_To fa nan ake yin ta. Ya kuke ganin za’a kaya?_

_Hajja zata amince da zaɓin Baffa?_

_ko kuwa Ɗahira zata amince da Baffa a matsayin Mijin ta?_

_me zai faru?_

_ta Comments ɗin ku kaɗai zan tabbatar da cewa kuna so in ci gaba, idan kuma ba kwa so falillahil hamdu, dama hutu nake son tafiya, sai mun haɗu a next week._
[6/2, 12:50 PM] Oummu Ɗahirah: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR’S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL._

*بسم الله الرحمن الرحيم*


𝐅𝐄𝐄𝐍𝐀𝐇 𝐖𝐑𝐈𝐓𝐄𝐑’𝐒 𝐀𝐒𝐒𝐎📖*
®Ɗ𝚊𝚢𝚊 𝚝𝚊𝚖𝚔𝚊𝚛 𝚍𝚊 𝙳𝚞𝚋𝚞💪✓

𝗝𝗜𝗞𝗔𝗥 𝗟𝗔𝗪𝗔𝗟𝗜 𝗖𝗘✍️

𝗪𝗮𝘁𝘁𝗽𝗮𝗱: 𝗨𝗺𝗺𝘂𝗗𝗮𝗵𝗶𝗿𝗮𝗵👈

\𝗙.𝗪.𝗔📚/

𝗦𝗔𝗗𝗔𝗨𝗞𝗔𝗥𝗪𝗔
𝑁𝑎 𝑠𝑎𝑑𝑎𝑢𝑘𝑎𝑟 𝑔𝑎 𝐹𝑎𝑚𝑖𝑙𝑦 𝑛𝑎 𝑔𝑎𝑏𝑎 ɗ𝑎𝑦𝑎. 𝗚𝗢𝗠𝗔’𝗦 𝗙𝗔𝗠𝗜𝗟𝗬.

 

 

*EPISODE Twenty Three*

Zumbur Hajja ta miƙe sabida jin bazatan maganar ɗan nata, cikin tsantsan takaici tace, “kana kuwa cikin hayyacin ka Al’ameen? Ɗahira?.. Ɗahiran ce kake nufin zata zamo suruka ta?”

Shima Baffa miƙe wa yayi a wani irin yanayi, domin dai tabbas ya san akwai matsala tunda yaji Mahaifiyar sa ta kira sa da sunan sa na ainihi, cike da alhini yace, “Hajja to mene ne laifi idan na so Ɗahira? Na ga ai ita ƙanwa ta ce ko?..”

Be rufe baki ba Hajja tace, “kai da Allah ja can mara hankali mara tunani, wanda be san inda yake masa ciwo ba, ka rasa wacce zaka so sai Ɗahira? To ban amince ba, idan har Ni na haife ka, to, babu ta yanda za’a yi ka auri wannan yarinyan”.

Sosai hankalin Baffa ya tashi da jin zantukan mahaifiyar na sa, cikin matuƙar damuwa yace da ita, “Hajja wai me Ɗahiran tayi miki ne da kike son jifan ta da baƙin fenti? Mene ne aibun ta shi nake son sani?”

A fusace take kallon sa tace, “aibun ta kake son sani ko? To na tsane ta ne ba na ƙaunar ta, ba na son ta zamo suruka ta, idan ko ka bari hakan ta faru, na rantse da Allah sai na tsine maka albarka”.

“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un! innalillahi wa’inna ilaihi raji’un!!”. Abinda kawai Baffa yake faɗa kenan yana bin ta da kallo

Ita kuwa zama tayi tana huci kamar zakanya, sai kuma ta sake kallon sa tace, “umarni nake ba ka, idan har ka bari wani ma yasan da zancen kana son ta a gidan nan, to har abada bani ba kai, tun wuri kaje ka nemo wata ka aura, ko kuma Ni in zaɓa maka zaɓi na”.

Baffa shiru yayi har yanzu idanun sa a kanta, sai dai a wannan lokacin komi ya tsaya masa cak daga duniyar tasa, be san sanda hawaye suka soma sintiri a fuskar sa ba, sai jin ɗumin su yayi saman kuncin sa.

 

A dai-dai lokacin ne Shakira ta shigo part ɗin, kallon Yayan nata tayi dake hawaye, kafin ta mayar da idanun ta kan Hajja dake faman karkaɗa ƙafafu fuskarta a matuƙar ɗaure, nan da nan hankalin ta ya tashi ta ƙariso da sauri tana tambayan “me ke faruwa?”

Lumshe ido kawai Baffa yayi, sai ya buɗe ya ja ƙafafuwan sa ya nufi hanyar ɗakin sa, yana shiga ya faɗa kan gadon sa ya soma tsiyayar da hawaye, sosai yake kukan zuci, zuciyar sa na tafarfasa, babu abinda ke dawo masa a kwanya sai maganganun Hajja, “shin taya ma hakan zai faru? Taya zai iya cire ƙaunar Ɗahira da ya jima yana dakon sa? Ina sam bazai yiwu ba, idan kuwa hakan ta faru, ya tabbata mutuwa zai yi”.

 

 

**** **** *****

Hajja duk abinda ke faruwa ta sanar wa Shakira

“Ai dama na sani, ba tun yau ba dole ne akwai soyayya a tsakanin su, I already understand Hajja.”

Hajja said, “Then why didn’t you tell me in the first place, sai da abu yayi nisa? Yanzu da ace ban tambaye sa ba haka zai je ya faɗa ma mutanen gida ga wacce yake so, kinga kuwa babu ta yanda za’a yi in hana faruwan hakan, na tabbata wlh sai anyi auren nan, tunda dama iyayen ku babu abinda suke ƙauna sama da su ga anyi haɗin zumunci a gidan nan, ina sam wlh ba dai da ɗana ba, dama Yusra ko Fadila yace yana so sai in bar sa, amma ya rasa wacce zai jajibo min sai ƴar A’ishah, maƙiyiya ta” .

Shakira tace, “Nima kai na Hajja na so raba su tun farko, ina wannan ƙawar tawa da muka taɓa zuwa da ita gidan nan Ayush?”

Hajja gyaɗa kanta tayi tace,”yes I understand her, wacce kuke sintiri a asibiti tare lokacin ciwon Kaka”.

“Eh ita, wlh she really loves Baffa Hajja, kawai ki haɗa sa da ita tunda shima Yayan ya saba da ita”.

Ɓata fuska Hajja tayi tace, “sam ɗana bazai auri ƴar talakawa ba, da ace dai suna da hali ne, amma tunda basu dashi ban amince da ita ba, Ni yanzu na tsara wacce zai aura, idan be samo wata ba, zan haɗa sa da Sa’adatu ne, yanzu ma ɗauko min wayata in Kira Mahaifiyar ta muyi magana, gwara ta dawo nan ko ya ganta ya so ta”.

Tashi Shakira tayi don ɗauko mata wayan, duk da a ranta bata ji daɗin haɗin ba, amma ko ba komi Yayan ta bazai auri Ɗahira ba.

 

Sa’adatu yarinya ce wajen ƙanwar Hajja Fatu, Hajiya Amina wacce tayi aure a Legos. Dama tun farko Sa’adatu ta jima tana ƙaunar Baffa, sai dai shi ya ƙi amince wa da ita sabida bata yi masa ba, wayewar ta yayi yawa, akwai ta da rawan kai.

 

 

 

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

 

*WASHE GARI*

A ranan Ɗahira ta tashi ne cikin walwala da farin ciki, burin ta kawai anjima yayi ta sanya masoyin nata a idanu, koda ta gama shiryawa cikin Abaya baƙa me kwalliyan stones, sai ta yafa gyalen shi ta saka flet shoes, sallama tayi wa Aunty Amarya ta fito ta shiga cikin motan ta

Koda ta isa asibiti Direct office ɗin Baffa ta wuce, sai dai babu shi, domin Office ɗin ma a rufe yake, tayi mamaki sosai amma bata tsawwala ba, sai ta wuce Office ɗin ta.

 

 

⚫⚫⚫

Ɗan adai-daita sahu ne ya sauke Ayush a bakin Hospital ɗin, kuɗin sa ta biya sa sannan ta shigo cikin asibitin

A dai-dai lokacin ne Shakira ta shigo itama da motan ta, parking tayi ta fito tana gyara zaman mayafin ta

Hango ta da Ayush tayi ne yasa ta nufo ta tana washe baki, tana ƙarisowa suka soma gaisawa kafin suka jero suka nufi cikin asibitin, Office ɗin Shakira suka wuce kai tsaye.

 

Sai da suka zauna kafin Shakira tace, “I called your phone yesterday but it turned off. What happened to her?”

“Wlh kuwa babu caji ne, kuma ban samu na kai an saka min ba sai daga baya, yanzu ma na amshe ta wajen me shago”.

“Okay, I want to talk to you. kin san jiya Tsoho me ran ƙarfe ya taso da babban zance?”

Ido Ayush ta tsira mata tana gyara zaman ta tace, “I wonder what happened?”

Sai da ta sauke ajiyan zuciya kafin tace, “uhmmm! Jiya gaba ɗayan mu yace mu fitar da miji, su Ya Baffa kuma su fitar da mata, we will be married in a month”. ta ƙare maganar da murmushi

Waro ido Ayush tayi, sai dai bata iya magana ba

Sai Shakira taci gaba da faɗin,
“But do you know what? There is a problem, because Hajja tayi wa Ya Baffa mata”.

Still shiru Ayush tayi tana kallon Shakira

“Lafiyan ki ƙalau kuwa Ayush? I’m talking you are silent”.

“To ai maganar taki ne tazo min a bazata. Now you mean I will not marry Dr. Baffa?”

Taɓe baki Shakira tayi tana janyo wasu files gaban ta tace, “to ban dai sani ba, amma idan har kin yi ƙoƙari kin saka ya Baffa ya so ki a ɗan ƙanƙanin time ɗin nan, to tabbas zaki iya auren sa, domin Hajja ta ba shi zaɓi, duk wacce ya kawo zata aura masa, sai dai ban da Ɗahira, kin ga kuwa burina ya cika, dama ita ce ba na so”.

A ran Ayush tsaki taja tana cewa, “aikin banza ta jiƙa shi tasha mana, Ni yanzu ba tashi nake ba, matsala ta na ga gwani na”. A fili kuwa sai tace, “ƙawata yanzu shi kuma Dr. Usman kin san wacce yake so ne?”

Kallon ta Shakira tayi, kamar tana tunani sai kuma tace, “taya zan sani? Ai sai nan da sati ɗaya idan Kaka ya buƙaci ganin mu”.

“Haka ne! To bari inje, yanzu ina da aiki da yawa”.

 

“Ok”.

 

Da fitan Ayush ta shige Office ɗin ta, jikin ta na rawa ta soma sintiri a Office ɗin, ko kaɗan ta kasa yin tunanin da zai kai ta ga mafita, duk wata hanya da zata bi domin magana da Usman abun ya faskara, ta jima tana bibiyan sa a facebook amma har yanzu bata samu yayi mata reply ba, kusan kullum sai ta tura masa saƙon soyayya amma a banza

Tsaki ta ja tana zama akan kujeran ta, wayan ta ta sake ɗauka ta shiga facebook ta hau yin masa text, ga dai shi yana online amma bata samu reply ba. Ayush kamar tayi kuka ta ajiye wayan tana buga tagumi

Jin ƙaran shigowar text, tayi tunanin shi ne tayi saurin ɗaukan wayan, sai dai wata best friend ɗin ta ne tayi mata magana, dogon tsaki taja kafin ta yi mata reply, charting suka soma yi, anan take faɗa mata halin da take ci, kasancewar ita ƙawarta Safra ta tambaye ta “kwana biyu ina ta shige?” Shi ne ta soma bata labari aiki ne ya riƙe ta, har suka gangaro kan matsalan ta

Nan Safra tayi mata alƙawarin taimaka mata, ta yanda zata samu Usman a hannu, nan ta sanar mata nan da kwana biyu zata shigo Kadunan, kasancewar ita tana Zaria ne tana karatu

To a nan ne dai hankalin Ayush ya kwanta, duk da bata san Safra sosai ba, kasancewar a Facebook suka haɗu, amma ta yaba da wayewar ta, tasan zata iya taimakon ta, tunda tafi ta sanin kan duniyar.

 

 

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

 

Ƙarfe 01:30pm. Yau Ɗahira ta tashi daga aiki, tana komawa gida ta shiga ɗakin mahaifiyar ta

Aunty Amarya looked at her in surprise and said, “ah a yau kuma da wuri kika dawo?”

Murmushi Ɗahira tayi tace, “yes Mama”.

“Are you all right?”

Still Murmushi Ɗahiran tayi tace, “akwai baƙon da zan yi ne anjima Mama, shi ne na dawo tun yanzu”.

Aunty Amarya smiled and said, “Masha Allah! May Allah bring him peace”.

“Ameen Mama”. Ɗahira ta amsa mata, sannan ta fice tayi ɗakin su

Kwanciya tayi don ta huta, zuwa anjima sai ta tashi ta shirya.

Bata fi mintuna goma da kwanciyar ba, Fadil ya shigo ya sanar mata Aunty Amarya na kiran ta

Koda taje kiran, Aunty Amarya kallon ta tayi tace, “in ce dai kin shirya abinda zaki tarbi baƙon naki?”

“A’a Mama”.

“To haka ake yi ne? Ki je ki shirya masa wani abun, koda yake ki buɗe Fridge ɗina zaki ga markaɗaɗɗen kayan miya dana saka, anjima zan yi amfani dashi, sai ke kiyi amfani dashi ɗin kiyi masa miya zai fi”.

“To Mama”. Ɗahira ta amsa mata tana yin wajen Fridge ɗin

Da kallo Aunty Amarya tabi ta dashi har ta fice, sai ta saki murmushi kawai, a ranta tana ma ɗiyarta fatan dacewa da Miji na gari.

Ɗahira da fitar ta kichen ta nufa takai kayan miyan ta ajiye, sannan sai ta koma kan dainning taci abinci, tana gamawa ta koma kichen ta soma haɗa abincin baƙon ta, shinkafa da miya tayi masa, sannan ta haɗa Juice Kala biyu, sai tayi masa farfesun kifi, kasancewar shi suke dashi, dayake Abbu yafi son kifi shiyasa ba sa rabo dashi a koda yaushe, za su iya rasa Nama na kwanaki a gidan amma ban da kifi.

 

Time ɗin da ta gama komi ƙarfe 02:40pm. Tayi, da sauri-sauri ta zuba a cikin coolars masu kyau, sannan ta wuce ɗaki tayi wanka, tana fitowa ta shirya cikin riga da skert na atamfa me ruwan silver, sai ratsin fari kaɗan-kaɗan, sai tayi make-up tayi ɗaurin ɗankwali me kyau da ya ƙara fito da kyawun ta

Zama tayi gefen gado tana kallon agogon ɗakin, har ƙarfe uku tayi ta wuce ma, wayan ta ta ɗauka tana kallo ko zata ga message ɗin sa, but babu, dole tayi zaman jiran sa.
[6/3, 8:41 AM] Oummu Ɗahirah: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR’S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL._

*بسم الله الرحمن الرحيم*


𝐅𝐄𝐄𝐍𝐀𝐇 𝐖𝐑𝐈𝐓𝐄𝐑’𝐒 𝐀𝐒𝐒𝐎📖*
®Ɗ𝚊𝚢𝚊 𝚝𝚊𝚖𝚔𝚊𝚛 𝚍𝚊 𝙳𝚞𝚋𝚞💪✓

𝗝𝗜𝗞𝗔𝗥 𝗟𝗔𝗪𝗔𝗟𝗜 𝗖𝗘✍️

𝗪𝗮𝘁𝘁𝗽𝗮𝗱: 𝗨𝗺𝗺𝘂𝗗𝗮𝗵𝗶𝗿𝗮𝗵👈

\𝗙.𝗪.𝗔📚/

𝗦𝗔𝗗𝗔𝗨𝗞𝗔𝗥𝗪𝗔
𝑁𝑎 𝑠𝑎𝑑𝑎𝑢𝑘𝑎𝑟 𝑔𝑎 𝐹𝑎𝑚𝑖𝑙𝑦 𝑛𝑎 𝑔𝑎𝑏𝑎 ɗ𝑎𝑦𝑎. 𝗚𝗢𝗠𝗔’𝗦 𝗙𝗔𝗠𝗜𝗟𝗬.

 

*EPISODE Twenty Four*

Har ƙarfe 04:30pm. Ɗahira tana zaune jiran masoyin ta, amma babu shi, kuma babu text ɗin sa, ta ɗauki wayan ta tana ajiye wa yafi sau a ƙirga, daga ƙarshe ta tura masa message, but babu reply, dole ta haƙura ta tashi tayi sallan Asar, sannan taci gaba da zaman jiran sa, ji kawai take yi tamkar ta ɓarke da kuka, amma haka ta daure, a ranta tana ba shi uzuri; Maybe wani abu ne ya hana sa zuwa

Har aka kira magriba Ɗahira na zaune bakin gadon ta, ta zuba tagumi tana ta tunani. Tashi tayi ta gabatar da sallan tukun ta koma ta zauna.

Aunty Amarya aiko Fadil tayi yazo ya kira ta, koda taje sai Aunty Amarya ta tambaye ta “ko bazai zo bane?”

“I don’t know either. Mama, I still keep quiet, and at three o’clock we made it come.”

Ajiyan zuciya Aunty Amarya ta saki, tana kallon Ɗiyarta ta da damuwa ya nuna a fuskarta kafin tace, “to kiyi masa uzuri,
maybe there is something stopping him from coming, Allah yasa dai lafiya”.

 

“Ameen”. Ɗahira ta amsa tana ficewa

Ɗaki ta koma ta kwanta tana lumshe idanun ta, jin ƙarar shigowar text, da sauri ta tashi zaune tana ɗaukan wayan ta, nan da nan murmushi ya suɓuce mata ganin Masoyin ta ne, buɗe wa tayi jikin ta na rawa ta soma karanta wa

 

_”Ban san da bakin da zan baki haƙuri ba Ɗahira, tabbas nasan zaki fahimce ni sabida ke me yiwa kowa uzuri ne, kuma na san kina da kirki da sanin Ya kamata. yau na so in bayyana a gaban ki, in nuna miki tsantsan ƙaunar da nake miki, sai dai kuma abu mafi girma ya shigo rayuwar mu, bazan ɓoye miki sirri na ba Ɗahira, na zaɓi faɗa miki ne kar ki ga laifi na, wanda na san zaki fahimce ni kiyi min uzuri. Mahaifiya ta ta haramta min zuwa gare ki, domin ta ce “idan har na aure ki bata yafe min ba,” ta rigada ta zaɓa min matar da zan aura, don Allah! Kiyi haƙuri domin ba’a son Raina zan bar ki ba, sai don bin umarnin mahaifiya ta, amma ki sani ina matuƙar ƙaunar ki, har in koma ga mahalicci na bazan taɓa dena son ki ba.”_

_A.A.A. Masoyin ki._✍️

 

Lumshe idanuwan ta tayi, hawayen dake tsiyaya akan kuncin ta tun soma karanta text ɗin; suka ci gaba da kwaranya, wani irin ƙunci ne ya tokare mata maƙogwaro, wanda daƙyar take iya haɗiye yawu

Dauriya dai me dauriya sai da ta gwada yin shi, amma ta gaza, dole ta zube kan gadon ta hau rusa kuka, kuka take yi sosai zuciyarta na mata zafi tamkar zai faso ƙirjin ta

Taya ma zata iya jure wannan halin da take ciki, meyasa zai mata haka? Meyasa zai tafi ya bar ta a lokacin da take buƙatar sa cikin rayuwan ta? Ya tafi ba tare da ta gansa ba, ya tafi ba tare da tasan sunan sa ba, dama ashe ba son ta yake yi ba? Meyasa to ya koya mata ƙaunar sa?…

Fadila ce ta shigo ɗakin, ganin Ɗahira a wannan halin, sai tayi saurin ƙarisowa wajen ta hankalin ta a tashe, ta hau tambayan ta “lafiya?”

Cikin kuka Ɗahira ta bata amsa,
“He is gone ..! Wlh I really love him, ban taɓa son wani ba sai shi, meyasa zai tafi ya bar Ni?..” ta kasa ƙarisa wa illa kukan da taci gaba da yi, hawaye na ambaliya a kyakykyawar fuskar ta

Sosai Fadila ta tausaya mata, riƙo ta tayi tana faɗin, “ki nutsu Ɗahira, tell me what happened, shin wane ne shi wanda ya tafi ya bar ki?”

Ɗago idanun ta da suka kaɗa suka yi jazur tayi ta aza akan Fadila, cikin raunin murya take faɗin, “wanda muka yi alƙawarin aure dashi, ya ce min Mahaifiyar sa ta haramta masa aure na, me zai saka yayi min haka? Me zai sa in ba aure na zai yi ba ya zo ya koya min son sa? Meyasa tun farko ya zo wuri na?” Taƙarishe maganar cikin kuka

Da mamaki take kallon ta, sabida ta san babu wanda ke zuwa wajen ta, tunda take bata taɓa ganin Ɗahira ta kawo baƙonta gidan nan ba, “shin aina shi kuma wannan suke haɗuwa?” Tayi ma kanta tambayar, sai dai babu me bata amsa, dole ta kawar da zantukan daga ranta ta soma rarrashin ta. Ta daɗe tana rarrashin ta, amma Ɗahira ta kasa yin shiru, dole ta haƙura ta bar ta, ta miƙe tabar ɗakin.

Kuka sosai Ɗahira tayi, kukan da ke fitowa daga zuciyar ta. Tunda take bata taɓa yin soyayya ba, koda da rana ɗaya bata taɓa son wani ba, amma kuma ta rigada ta kamu da ƙaunar wannan bawan Allan da bata san ko shi waye ba, bata san sunan sa ba, ko kaɗan baza ta iya juran rasa shi ba, soyayyan gaskiya take mishi, taya lokaci ɗaya zai tafi ya bar ta a lokacin da take matuƙar buƙatar sa? Wannan amsoshin su suke yawo a zuciyar ta, wanda ya ƙara haddasa mata cinkushewar baƙin ciki a ranta

Allah ya gani ita baƙuwa ce a soyyayya, ko kaɗan baza ta iya juran wannan yanayin ba.

Har Fadila ta sake dawowa ɗakin Ɗahira na kwance tana kuka

“Wai don Allah Ɗahira baza ki dena wannan kukan da kike yi ba? Taya kuka zai miki maganin matsalan ki? Ke fa ba ƙaramar yarinya ba ce”. Cewar Fadilan tana kallon ta daga bakin gadon ta da ta tsaya

Ɗahira bata ce komi ba, illa miƙe wa da tayi ta shiga Toilet, alwala tayi ta fito ta soma gabatar da sallan isha’i da aka daɗe da yi, har ta idar tana zaune a wajen ta kasa tashi, sai ma haɗa kanta da gwiwowin ta da tayi; tayi shiru tana tsiyayar da hawaye

Fadila dake kwance tana faman latsa waya, ta kalle ta tace, “I forgot I didn’t tell you, Aunty Amarya is calling you”.

Shiru Ɗahira tayi mata

Ita kuma bata sake bi ta kanta ba, taci gaba da charting ɗin ta ita da K.B, tana yi tana sakin murmushi.

Sai da kusan mintuna goma suka shuɗe sannan Ɗahira ta tashi ta fice, babu kowa a Parlour, kai tsaye ta wuce ɗakin Maman ta. Sai da tayi sallama aka ba ta iznin shiga sannan ta shige

Aunty Amarya na zaune akan sallaya, shi kuma Abbu na gefen gado zaune yana waya, da alamun wayan me muhimmanci ne shiyasa gaba ɗaya attention ɗin sa ya ba wa wanda suke wayan ne

Durƙusa wa gaban Aunty Amarya tayi, cikin dashashshiyar muryan ta na wanda tasha kuka tace mata “ga ta”.

“Ya naga kamar kin yi kuka? What’s wrong with you?” Aunty Amarya asked her this question keeping an eyes on her

Sake sunkuyar da kanta ƙasa tayi, in a weak voice and said, “nothing”.

 

Shiru Aunty Amarya tayi na ɗan wani lokaci, sai kuma tace, “je ki kici abinci, kar ki kwanta da yunwa kin ji ko?”

Gyaɗa mata kai tayi tana miƙe wa ta fice

Aunty Amarya tabi ta da kallo cike da tausayin ɗiyar ta ta, tabbas ta san akwai ɗinbim damuwa a tattare da ita, kuma ta gane kuka tayi, amma kuma ba ta son ta dame ta da tambaya a wannan lokacin ne har sai ta samu sauƙin damuwar nata..

“Har kin sallami Maman nawa ne?”

Maganar Abbu ya katse mata tunanin ta, sai ta juyo tana kallon sa, ta ce, “eh, na ga ai kana waya ne, kuma bata ci abinci ba shi ne nace ta je taci. Ko in Kira ta ne?”.

“No. Let her eat her food.”

Koma wa Aunty Amarya tayi ta zauna, don har ta rigada ta yunƙura zata tashi.

 

 

 

⚫⚫⚫

Ɗahira na fita bata ci abincin ba ta koma ɗaki, domin baza ta iya saka komi a bakin ta ba, ko da taci kuwa, baza ta ji daɗin sa ba.

Tana shiga ta haye kan gadon ta ta kwanta, sai dai ta daɗe kafin ta samu barci ya ɗauke ta, gaba ɗaya tunani ya hana ta sukuni, sai daƙyar ta samu tayi barci.

 

Washe gari da zazzaɓi ta tashi, dole ta sake komawa ta kwanta bayan ta yi sallan asuba, har gari ya waye bata farka daga barcin da ya ɗauke ta ba.

 

Kowa ya hallara wajen Breakfast amma ban da ita

Aunty Amarya tambayan Fadila tayi “where is she?”

Sai ta faɗa mata, “she was sleeping, she didn’t wake up”.

 

Har ta ce “taje ta taso ta sabida kar tayi lattin zuwa wajen aiki”

Amma Abbu ya ce, “su bar ta”.

Har suka gama Breakfast ɗin, shi da Fadil suka fice, Umma ta shige ɗakin ta, yayinda Fadila kuma ta koma cikin Parlour ta zauna abun ta tana aikin latsa waya

Aunty Amarya har ta koma ɗaki, sai kuma ta kasa jure wa, don tasan Ɗahira sarai, tunda ta kwanta ba lafiya ba, bare yanda take son Aikin ta, haka kawai yau ranan aiki ba zata ƙi fitowa ba in babu Dalili

Ɗakin ta wuce kanta tsaye don ta duba ta. Tana shiga ta hange ta saman gado ta rufe kanta da blanket, da sauri ta ƙarisa wajen gadon ta saka hannu ta yaye saman kanta, fuskar ta take kallo tana kiran sunan ta

A hankali Ɗahira ta buɗe idanuwan ta da suka yi ja, ta aza su kan Maman ta

“Baki da lafiya ne, me ke damun ki?” Ta jero mata tambayar a yanayin damuwa

Cikin matuƙar sanyin murya da ciwo yake cin ta tace, “zazzaɓi ne ya rufe Ni Mama”.

Cike da tausaya wa take mata sannu, kana tace mata, “ta tashi tayi wanka, inyaso sai ta sha magani bayan taci abinci”.

Babu yanda ta iya haka ta miƙe, da taimakon Aunty Amarya har ta ƙarisa Toilet

Ita kuma Aunty Amarya ta fice haɗo mata Breakfast don ta kawo mata har nan cikin ɗakin. Bayan ta haɗo mata ta kawo mata ta zauna zaman jiran ta.

Kamar shuɗewar mintuna sha biyar Ɗahira ta fito a Toilet, ɗaure take da towel me tsawo iya ƙasan gwiwan ta, sai ta saka wani da ya rufe mata kanta zuwa kafaɗun ta

Tana fitowa Aunty Amarya tace, “yi maza ki shirya ki zo ki karya ki sha magani, kina likita amma kina wasa da shan magani, wataƙil ma tun jiya da kika yi kukan naki zazzaɓin ya kama ki amma kin zauna baki sha magani ba”.

Kallon ta Ɗahira tayi da sauri, sai kuma ta kawar da kanta cike da sanyin jiki ta kariso gaban Sip ɗin kayan su, buɗe wa tayi ta ciro doguwar rigan atamfa. Sai da tagama shirya wa kafin ta iso gaban aunty Amarya dake bakin gadon ta, a ƙasa ta zauna ta tanƙwashe ƙafa ta soma shan tea ɗin da ta haɗa mata, tana yi tana haɗa wa da bread kamar yanda Aunty Amarya ta umarce ta, sai dai tana cin ɗaya biyu taji kamar zata yi amai, ta kalli Aunty Amarya ta marairaice fuska kamar zata yi kuka tace, “zan yi amai bazan iya ci ba”.

“To shanye tea ɗin ki sha maganin”.

Ajiye bread ɗin tayi da ƙwan, ta sha tea ɗin, har sai da takusa shanye wa kafin ta amshi maganin ta kora da sauran

“Ina jin ki, Why are you crying? What’s wrong with you?”

 

Sunkuyar da kanta Ɗahira tayi don bata san me zata ce mata ba

“Ina magana kin yi shiru, meyasa zaki zauna ki saka damuwa a ranki har kiyi irin wannan kukan da ya haddasa miki ciwo? Bayan kin san halin kanki abu kaɗan ne yake haddasa miki ciwo idan kin saka damuwa?”.

Matso hawaye Ɗahira tayi, har yanzu ta kasa yin magana tunda bata san yanda za’a yi ta faɗa ma Mahaifiyar nata matsalan ta ba

“Ko sabida ya ƙi zuwa ne kike kuka?”

Ɗaga mata kai tayi, kafin ta cire kunya ta sanar mata komi

Ajiyan zuciya Aunty Amarya ta sauke, cike da tausayin ɗiyar ta tace, “ki yi haƙuri haka Allah ya so dama ba shi ne wanda zaki aura ba, Allah ya musanya miki da wanda ya fi shi, amma ki dena saka damuwa a ranki kinji? ki fauwala wa Allah komi, ai Kakan ba cewa yayi zai zaɓa muku wani ba idan baku kawo wanda zaku aura ba, don haka ki dena saka maganar auren nan na damun ki”.

Gyaɗa mata kai tayi

Sai da ta sake tausan ta kafin ta fice ta bar ta

Sosai maganar Maman ta ya sanya ta jin sanyi a ranta, dama ita yanzu damuwar ta yanda kowa zai kai zaɓin sa, amma ita ban da ita.

A haka ta saki jikin ta a ranan taci gaba da walwalan ta, sai dai bata je aiki ba ta bar wa gobe.
[6/3, 5:48 PM] Oummu Ɗahirah: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR’S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL._

*بسم الله الرحمن الرحيم*


𝐅𝐄𝐄𝐍𝐀𝐇 𝐖𝐑𝐈𝐓𝐄𝐑’𝐒 𝐀𝐒𝐒𝐎📖*
®Ɗ𝚊𝚢𝚊 𝚝𝚊𝚖𝚔𝚊𝚛 𝚍𝚊 𝙳𝚞𝚋𝚞💪✓

𝗝𝗜𝗞𝗔𝗥 𝗟𝗔𝗪𝗔𝗟𝗜 𝗖𝗘✍️

𝗪𝗮𝘁𝘁𝗽𝗮𝗱: 𝗨𝗺𝗺𝘂𝗗𝗮𝗵𝗶𝗿𝗮𝗵👈

\𝗙.𝗪.𝗔📚/

𝗦𝗔𝗗𝗔𝗨𝗞𝗔𝗥𝗪𝗔
𝑁𝑎 𝑠𝑎𝑑𝑎𝑢𝑘𝑎𝑟 𝑔𝑎 𝐹𝑎𝑚𝑖𝑙𝑦 𝑛𝑎 𝑔𝑎𝑏𝑎 ɗ𝑎𝑦𝑎. 𝗚𝗢𝗠𝗔’𝗦 𝗙𝗔𝗠𝗜𝗟𝗬.

 

*EPISODE Twenty-Five*

Kamar yanda Hajja Fatu tace zata kira Hajiya Amina su yi magana, hakan kuwa tayi, sun gama ƙulle-ƙullen su a waya, kafin suka yi sallama akan zata turo Sa’adatu gobe-goben nan kamar yanda ta buƙata, yanzu ɗin ma don ba ta kusa ne da sun yi waya.

Washe gari zuwa yamma sai ga Sa’adatu ta dira garin Kaduna

Hajja Fatu zuwa tayi har ɗakin Baffa ta tasa shi gaba akan “lallai-lallai sai ya je ya ɗauko Sa’adatu a airport”.

Ba da son ransa ba haka ya tashi ya saka riga a saman Singlet ɗin dake jikin sa, ya fito ya wuce ya shiga motar sa ya bar gidan, a cikin mota in banda tsaki da yake saki babu abinda yake yi, kaso mafi rinjaye na zuciyar sa yana ga Ɗahira, ya rasa meyasa zuciyar sa ta kasa nutsuwa da halin da ya saka ta, yana ji a jikin sa tabbas tana wani hali a sanadiyar Text ɗin da ya tura mata, amma ya zai yi? Bazai iya zuwa ya same ta ba, bazai iya jure ganin damuwa a kyakykyawar fuskar ta ba, ya gummaci ƙaurace mata har sanda komi zai dai-daita. Lumshe idanuwan sa yayi yana buɗe wa sai ga hawaye sun zubo masa a kunci, hannu ya saka ya share yana jan numfashi cike da takaicin Mahaifiyar sa, zuciyar sa sosai take mishi ƙunci fiye da tunanin mutum, yana ji a ransa bazai iya jure wa ba, bazai iya auren kowa ba face Ɗahira, dole ya sake yi wa mahaifiyar shi magana, ko zata iya tallafa wa rayuwar sa, Allah ya gani ba ya ƙaunar yarinyan nan da za’a liƙa masa, sannan kuma bazai iya zuwa ya tunkari wata ɗiya mace da sunan so ba, bare har ya iya auren ta, ita dai Ɗahiran da Hajja ba ta so ita zuciyar sa ke so..

 

Be fasa tunanin sa ba har sanda ya dangana ga airport ɗin, tunda ya faka motan ya hange ta, sabida kasancewar ta doguwar mace, idan har ta tsaya cikin mutane nan da nan ake iya gane ta, ga ta fara kuma tana ƙara wa dana kanti

Ya ɓata lokaci cikin motan kafin yaja numfashi ya buɗe ya fito, yana hangen ta sai faman waige-waige take yi tana duba agogon dake ɗaure a tsintsiyan hannun ta. Lumshe idanu yayi ya sake buɗe wa a kanta, kamar bazai taka ya isa wajen ta ba, sai kuma ya daure cike da baƙin ciki ya nufe ta, fuskar sa babu ko alamun walwala

Sai da ya dangana ga inda take tsaye, sannan ne ta hange sa, ai nan ta saki murmushin da ya bayyana haƙoran ta, wanda da gani kasan tana cikin tsantsan farin ciki, kiran sunan sa tayi tun kafin ya ƙariso

Sai ya kau da kai yana sake ciccin magani, ya tsaya cak a wajen

Ɗaukar jakar ta tayi ta nufo sa tana sake washe baki, tana iso wa wajen sa ta soma gaishe sa cike da fara’a, amma yanda ya amsa mata ne sai walwalan ta ya ragu

“But yaya lafiya dai ko?” Tayi masa tambayar tana kallon sa

Be ce mata komi ba ya juya ya nufi motar sa

Sai ta tsaya kawai tana kallon sa baki sake, duk da ta san ba ya son ta amma ai suna mutunci sosai ba kamar yanda ya nuna mata haka ba, “so what’s wrong with him?” Tayi wa kanta tambayar har yanzu tana tsaye a inda take. Sai da taji horn ɗin motan sa kafin ta ankara, taja akwatin ta ta nufi motan, buɗe bayan tayi ta saka akwatin kafin ta shiga gaban motan ya ja suka bar wajen.

 

A cikin motan ma babu abinda yace mata, duk da kuwa ta sake tambayar sa abinda ke damun sa, amma yayi mata banza, har suka kai gidan ya sauke ta yaja motar sa ya bar gidan

Tsaye tayi a wajen tana bin motar har ya ɓace wa ganin ta, sai kuma jiki a sanyaye taja Trolly ɗin ta tayi cikin gidan, duk wanda ta gani a hanya gaishe sa take yi har ta isa Part ɗin Hajja Fatu

Sosai Hajja Fatu tayi murna da ganin ta, nan tayi ta nan-nan da ita har ta cika mata gaban ta da kayan ciye-ciye

Ruwa kawai ta ɗauka tasha, sannan ta kalli Hajja Fatu tace, “Hajja where is Shakira I didn’t hear her movements?”.

“Ai kuwa Shakira tana wajen Yusra, amma yanzu zaki ga ta zo tunda ta san an tafi ɗauko ki”.

Gyaɗa kai Sa’adatu tayi, kafin ta sake cewa, “Hajja is something happened to Yaya Baffa? na ga tunda muka zo be ce min komi ba ne?”

Murmushin yaƙe Hajja tayi tace, “bar shi nan yanda kika ganshi, shi ya san me ke damun shi”.

Langaɓe fuska tayi tace, “eyya Hajja taya zan bar shi bazan damu ba? kinga fa shi ɗin Yayana ne, wlh baki ga tunda muka biyo hanya duk na gama damuwa da halin da na ganshi, ko dai Ni ce ba ya son gani?”.

Hajja tace, “Taya Zaki ce haka? Ina ruwan shi dake da zai ce ba ya son ganin ki? Kin San tunda nayi masa maganar bazai auri yarinyan da ya zaɓa bane, shi ne ya dena min magana, ko abinci ma ba ya ci a nan, ya dena walwala gaba ɗaya, Ni kuwa bazan yarda ya aure ta ba bayan ga ki kina son shi, muddin idan be kawo wacce yake so ba, to ke ce matar sa da yardan Allah kamar yanda muka tsara”.

Washe baki Sa’adatu tayi, cike da farin ciki tace, “Allah ya amsa bakin ki Hajja ta. Amma to wace ce wacce ya ke so ɗin?”.

“Kar ki damu ba sai kin san ta ba, don ba na son ma maganar tariƙa tsawo azo kuma a samu matsala, maganar ta faɗa kunnen wani”.

“Haka ne Hajja, amma ai Yakamata ki sanar dani tun wuri, don wlh har na ji tsanar ta a raina, kinga kuwa gwara in santa in San yanda zan yi zama da ita koda watarana na ganta”.

Taɓe baki Hajja Fatu tayi tace, “ai kin ma santa tunda ba wata ƴar nesa bace, Ɗahira ce ta nan gidan”.

“What ..! But wlh Hajja I hate this girl so much, God forbid that you forbid her, Allah yasa gwara da kika hana, don wlh wannan yarinyan idan ta aure sa babu ke babu ɗanki, domin irin su ne masu raba uwa da ɗan ta, sai dai ki riƙa hangen sa daga nesa”.

“Ai nima shi na gani, ya rasa wacce zai aura sai ita, ba ga shi ba muna gani a wajen uwar ta, yanda take juya Al’ameen, Bilkisu kuwa ta zama abun kallo kamar ba ita ce matar sa ta farko ba, sai abinda tace za’a yi, ke wlh in gaya miki duk iyayen nasu maza sun fi ƙaunar ta, idan har wani abu zai fito daga hannun su to ita suke ba ma wa, ko Kaka shima idan zai yi shawara da matan gidan ita yake kira, komi yace A’isha, uhmmm wlh abun yana baƙanta mini Rai, shiyasa na matuƙar tsanar ta sabida gaba ɗaya Kaka ya rage nuna min kula wa kamar baya, burina kawai ta bar gidan nan tunda Innar ku Safiyya bata aure sa ba, to nima bazan samu kwanciyar hankali ba har sai na kora ta ta bar gidan nan. Mu dai bar maganar nan ki ci abinci tukunna”.

“Ok Hajja”. Sa’adatu tafaɗa tana saka hannu ta buɗe coolarn

Daga nan sauya hiran suka yi, inda Hajja take tambayan ta mutanen gida da basu gaisa ba.

 

 

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

Gaba ɗaya a kwanaki biyun nan da suka wuce Ɗahira ta sauya, ba komi ya sauya ta ba illa kewar masoyin ta, a kullum ranan duniya zata ɗau wayan ta sau babu adadi don ganin ko zata ga message ɗin sa, sai dai kuma har ranan ta wuce baza ta ga ko me kama da Numban sa ba, ta kasa haƙura har kiran Numban tayi, amma kuma a kashe ne kamar ko yaushe, duk ta rasa nutsuwar ta ta saka wa kanta tunani, kullum bata da aiki sai tunanin sa, idan ta je Office ma zama take yi tayi ta faman tuna sa, har mafarkin sa tana yi wai ga shi sun haɗu, tabbas sosai take son bawan Allan nan da ya guje ta, ta kasa cire sa a ranta ta saba da rashin sa, ga shi ya tafi ya bar ta koda sunan sa ne bata sani ba, illa kawai A.A.A. da ya rubuto mata a ƙarshen text message ɗin da yayi mata na ban kwana, kuma duk iya tunanin ta na ganin ta gano ma’anar A.A.A ɗin ta kasa, haka zata zauna ta saka wannan sunan ta saka wancan sunan don ganin ta ba shi suna, amma ko wanne ta saka sai ta ga be dace ba.

Ga shi tana son tayi magana da Baffa, koda zai ba ta shawara ne, amma kuma ta kasa ganin sa shima, shi kaɗai ne wanda zata iya faɗa masa damuwar ta amma kuma duk idan taje office ɗin sa ba ta ganin sa, dole yau bayan ta shirya zata wuce aiki, sai ta fara wuce wa Part ɗin su ta duba sa, wataƙil akwai abinda ke damun sa ne ba ta ganin sa a Hospital, Tabbas tana ji a jikin ta ba ya zuwa ne, idan da yana zuwa dole zai neme ta.

A time ɗin su Hajja Fatu duk sun tafi aiki, illa Sa’adatu dake zaune ita kaɗai a Part ɗin, tana Parlour ne tana Breakfast tana latsa wayan ta, sai ta jiyo sallaman Ɗahira da ta shigo parlour’n, ɗago kai tayi tana kallon ta, sai ta ɓata fuska tana kau da kanta

Ita kuwa Ɗahira fara’a ta saka a fuskar ta tana cewa, “ah ah yau Sa’ada ce a gidan na mu? Saukar yaushe ba mu da labari?”

Sa’adatu bata ɗago kai ba, sai tsaki da taja tana kai loman abinci

Hakan sai ya sanyayar wa da Ɗahira jiki, bata sake cewa komi ba tayi hanyar ɗakin Baffa

“So, Ma’am, where are you going?”

 

Juyo wa Ɗahira tayi tana kallon ta, hakan yasa suka haɗa ido

Sai Sa’adatu ta banka mata harara tace, “dama kin bar wahalar da kanki a kan Ya Baffa, domin kuwa shi ɗin nawa ne Ni kaɗai, ba’a yi macen da ta isa ta ƙwace min shi ba, don haka idan ma zaki nemi mijin ki a can wani wajen ki nema, domin dai Baffa nawa ne, nima kuma tashi ce”.

Baki sake Ɗahira take bin ta da kallo, a haƙiƙanin gaskiya Sa’adatu ba wai haushi ta ba ta ba, illa dariya da maganar nata ya bata, wanda har sai da ta murmusa, a ganin ta in ba hauka ba, Taya ma zata ce ta zo wajen Baffa ne domin neman soyayyar sa, bacin ta san da cewa shi ɗin yayan ta ne, ko kaɗan bata taɓa kallon Baffa a matsayin wanda zata iya aure ba, ba wai don wani abu ba, a’a, sai dai tana mishi kallon wanda suka fito ciki ɗaya, duk yanda mutane suke fassara su bata taɓa koda kallon abun hakan ba, “to meyasa su suke wannan tunanin?” Ta tambayi kanta idanuwan ta akan Sa’adatu tamkar da ita take yi, sai dai yanda tayi maganar a hankali babu wanda zai iya ji bare ya bata amsa. Ajiyan zuciya ta sauke sannan ta juya taci gaba da tafiya zuwa ɗakin nasa, don a ganin ta ɓata lokaci ne ta zauna tana biye wa Sa’adatu, tasan ciwon kanta, duk da a girme dai baza ta girmi Sa’adatu ba, amma kuma za su yo sa’anni da juna.

 

Tana zuwa ƙofar ɗakin ta cinma a rufe yake, bata yi ƙoƙarin buɗe wa ba duk da kuwa tana tare da keey ɗin ɗakin shi a cikin nata, tunda tasan shi dai ta zo nema ba wani abun ba, shiyasa ta juya ta wuce tabar Part ɗin baki ɗaya, ko kallon inda Sa’adatu take zaune ma bata yi ba. Motan ta ta hau ta wuce Hospital, tana isa ta fara zuwa Office ɗin Baffa, amma kuma babu shi sai dai Office ɗin a buɗe yake, kai tsaye lefter ta hau ta koma Office ɗin ta, ta soma duba Patients ɗin ta, tunda a time ɗin har sun soma zuwa.
[6/4, 11:48 AM] Oummu Ɗahirah: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR’S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL._

*بسم الله الرحمن الرحيم*


𝐅𝐄𝐄𝐍𝐀𝐇 𝐖𝐑𝐈𝐓𝐄𝐑’𝐒 𝐀𝐒𝐒𝐎📖*
®Ɗ𝚊𝚢𝚊 𝚝𝚊𝚖𝚔𝚊𝚛 𝚍𝚊 𝙳𝚞𝚋𝚞💪✓

𝗝𝗜𝗞𝗔𝗥 𝗟𝗔𝗪𝗔𝗟𝗜 𝗖𝗘✍️

𝗪𝗮𝘁𝘁𝗽𝗮𝗱: 𝗨𝗺𝗺𝘂𝗗𝗮𝗵𝗶𝗿𝗮𝗵👈

\𝗙.𝗪.𝗔📚/

𝗦𝗔𝗗𝗔𝗨𝗞𝗔𝗥𝗪𝗔
𝑁𝑎 𝑠𝑎𝑑𝑎𝑢𝑘𝑎𝑟 𝑔𝑎 𝐹𝑎𝑚𝑖𝑙𝑦 𝑛𝑎 𝑔𝑎𝑏𝑎 ɗ𝑎𝑦𝑎. 𝗚𝗢𝗠𝗔’𝗦 𝗙𝗔𝗠𝗜𝗟𝗬.

*HIKIMAR FARILTA SALLAH*
“`An farilta sallah domin a cikin ta akwai godiya ga Mani’imcin sarki jalla Ta’ala, wanda yake shi ne macancancin godiya da yabo, kuma shi ne kaɗai muka keɓe shi da ruku’u da sujada. Ba wani mahaluki da ya dace da wannan. Idan wata masifa ta sami mutum yakan yi maza ya fake da Allah ta yin Sallah, kamar dai yadda Allah yayi umurni a cikin suratul Baƙara, aya ta 45 da cewa:
“Kuma ku nemi taimako da yin haƙuri, da Sallah”.
Ganawar da bawa yake yi da Ubangijin sa a cikin Sallah ita ce bauta wadda take ƙarfafa zumunta tsakanin bawan da Ubangijin nasa. Ubangiji kuma yana yi wa bawan baiwar darajar samun kusanta da shi. Hikima ce kammalalliya da aka farilta sallah, don kuwa ta yin Sallah ne ake kankare wa bawa zunubai, muddin dai ya yi sallah yadda ake so.
An ruwaito cewa annabawan da suka wuce, ko wannen su yana da Sallah da yake ibada da ita. Sallolin suna da lokatai biyar; asuba, azahar, la’asar, lokacin faɗuwar rana da na isha’i. Ashe za mu lura cewa Allah ya tara wa Annabi da al’umma tasa sallolin dukan annabawan da suka gabata.
Allah ya sa mu dace.“`

 

*EPISODE Twenty Six*

*SUNDAY*
Gaba ɗaya sun taru a General Parlour kamar yanda al’adan gidan yake, sai da suka gama raha da nishaɗin su, sannan Kaka ya soma magana da cewa, “Kai Fadil ki rawo Fodio tunda ya ƙi zuwa”.

“To Kaka”. Fadil ya amsa mishi da sauri yana tashi ya fita

Babu jima wa sai ga Fadil ya dawo, ya isar da saƙon zuwan Usman

Kamar mintuna biyar da shigowar sa ne, Usman ya shigo yana ciccin magani, fuskar nan ko alamun fara’a babu, babu wanda yayi masa magana sai Big Dady dake faman hararan sa, sai dai shi ɗin be ma san yana yi ba, tunda be kalli kowa ba, ya samu wuri ya zauna gefen Baffa, sannan ya gaishe su yana latsa wayan sa

Kowa ya amsa, banda Big Dady da hakan ya ƙular da shi, a fusace ya ce, “kai Usman wannan wani irin ɗabi’ar banza ce? Ina ce gaishe mu kake yi amma kanka a waya?”

Sai a lokacin Usman ya ɗago kansa, sai dai be ce komi ba, illa jikin sa da yayi sanyi ya zame hannayen sa daga wayan ya bar sa a saman cinyan sa

Zai sake magana Big Dady, sai Kaka ya tare shi da faɗin, “bar wannan maganar Noor, mu Yi abunda ya tara mu, kasan halin wannan yaron meyasa kake son ɗaukan zafi da shi ne?”

“Baba wlh abun Usman sake gaba yake yi ba baya ba, kamar shi har sai an zauna ana faɗa mishi dai-dai da wanda ba dai-dai ba? Nan ya bar mu muna zaman jiran sa tsawon lokaci, duk sabida shi aka ƙi cewa komi, amma kuma ya zo yana wani sabga daban bayan yasan da cewa magana me muhimmanci ne ya tara mu”.

“Well enough to stop talking, ban san ka da wannan halin ba Noor Kar ka soma ka ji ko?” Kaka ya sake faɗa idanun sa kan Big Dady

Gyaɗa kansa yayi, kana yace, “to Baba Allah ya huci zuciyar ka”.

Murmushi Kaka yayi, yayinda su Abba da Abbu suka amsa da “Ameen, sai haƙuri ai”.

Kaka ya ce, “to ina jin ku, ya muka kwana a maganar yaran nan ne? tunda yau dama na ce zamu sake zama akan maganar”.

Abba ne ya ce, “ai Baba duk na tambaye su kuma na ce su turo mun su, kuma sun zo mun yi musu tambayoyi da Yaya (Yana nufin Big Dady) sannan na bincika duk na gano inda yaran suke, har na saka ayi min bincike a kansu. Uwata kuma da Usman har yanzu ba su ce komi ba akan maganar, shi kuma Baffa ɗazu Mahaifiyar tashi take faɗa min Sa’adatu ta wurin ƙanwar ta Hajiya Amina yake so”.

Kaka yace, “to Masha Allah Baba na”. Sai ya mayar da kallon sa ga Ɗahira da ke gefen sa ya ce, “Matata har yanzu abokin takaran nawa be shirya bane da baki gabatar da shi wajen Iyayen naki ba?”

Shiru Ɗahira tayi kanta a ƙasa

Sai da Big Dady yace, “Daughter you’re talking, are you okay? No problem?”

Bata ɗago kai ba tace, “Daddy, I don’t have anyone to introduce me to.”

“Baki da wanda zaki gabatar kuma?” Cewar Big Dady da Abba da suka haɗa maganar a tare

Sai kuma Big Dady ya ƙara da faɗin, “ko dai kin tsaya ruwan ido my Daughter? Amma maganar babu wanda zaki gabatar ai be taso ba”.

Jikin ta a sanyaye tace ,”Daddy wlh da gaske nake yi, wanda muke soyyayya da shi ya ce “ya fasa aure na, sabida Mahaifiyar sa ta zaɓa mishi wacce zai aura”.

Daga Aunty Amarya har Abbu da su Big Dady sai da jikin su yayi sanyi, haka zalika Kaka da yayi zugum yana kallon ta ya kasa furta komi

“Yanzu Uwata babu kuma wanda zaki iya gabatar wa ne?” Cewar Abba da yayi maganar a sanyaye

Gyaɗa kanta tayi, don haka kawai taji hawaye ya cika mata ido, a ganin ta abun da kunya a tara su a gaban jama’an gidan ace ta kawo zaɓin ta, amma kuma bata da shi, babu wanda zata iya nuna wa a matsayin gwanin ta, kamar ta ƙatuwar budurwa da ita, a ƙalla yanzu kaɗan ya rage ta cika 26 cif-cif…

Muryan Kaka ya katse mata tunanin ta, sai ta saka hannu tana share hawayen da ya zubo mata tana ci gaba da sauraron shi

Tambayan Usman yayi kamar yanda yayi mata

Usman ɗago kai yayi yana kallon kakan, fuska babu walwala a daƙile ya ce, “Babu”.

“Meye kuma Babu?” Abba ya tambaye sa

“I mean har yanzu babu wacce nake so”.

Shiru gaba ɗaya parlour’n ya ɗauka, ana jiran aji wani yayi magana a kan hakan, amma babu wanda ya iya cewa komi, har Kaka kuwa, kowa juya maganar nasa yake yi a mizanin hankalin sa

Kaka kallon Abbu yayi ya ce, “Takwara kun yi maganar da Yayar taku?” (Hajiya Ikram, Yana nufin akan Khabeer da ke son Fadila)

“Eh Baba, Yaya yayi maganar da ita”.

Big Dady yace, “mun yi maganar, har mun tattauna da mijin ta, babu matsala tunda su ma a shirye suke, za’a haɗa gaba ɗaya dana Isma’il da Shamsiyya”. (Sauran yaran Hajiya Ikram, su uku kenan zata aurar itama, har da K.B)

Gyaɗa kansa Kaka yayi yace, “Masha Allah gaskiya nayi farin ciki matuƙa, Allah ya sanya albarka gaba ɗaya”.

“Ameen ameen”. Suka amsa gaba ɗaya

“Yanzu duk abinda kuka ga ya dace sai ayi, kun san dai idan za’a saka ranan nace muku kar ya wuce wata ɗaya? Sai ayi komi a tsanake zuwa watanni biyu, na ƙara lokaci, a lokacin idan Fodio da Matata sun kawo nasu sai a haɗa baki ɗaya, don baza ayi babu su ba. Kai kuma Fodio kayi ƙoƙarin samo mata tun kafin Ni in zaɓa maka kana ji ko?” Kaka yayi maganar ta sigan barkwanci

Be ce komi ba kamar yanda kuwa babu wanda yayi tunanin zai ce.

Daga nan dai aka bar zancen aka kama wani, inda waɗanda suke da abun yi suka bar wajen.

Ɗahira bata wani tada hankalin ta ba akan maganar, ta bar wa Allah zaɓi, a ganin ta idan ta saka damuwa kanta zata cuta, tunda dama bata iya saka damuwa a ranta ba, da zaran ta saka, to shikenan ta dinga ciwo kenan, duk idan ka ga tana ciwo to tabbas da akwai abinda ke damun ta ne, ba ta iya jure wa damuwa ko kaɗan a ranta, bata da dauriyan hakan, domin zuciyar ta ba ta iya ɗauka, shiyasa ba ta shiga sabgar kowa idan har be shafe ta ba, sabida ta san matsalar kanta.

Aunty Amarya har ɗaki ta kira ta, tayi mata nasiha akan hakan

Amma sai Ɗahira ta nuna mata babu komi, har da fara’an ta

Hakan ya kwantar wa da Aunty Amarya hankali matuƙa, ko babu komi taji daɗi a yanzu, tunda ta san dole ɗiyar ta zata shiga wani hali na rashin masoyi, tabbas rashin Masoyi abu ne me ciwo ga duk macen da ta isa aure amma babu ma nemi, sai dai Allah ya zaɓa mana mafi alkhairi.

 

 

 

⚫⚫⚫

Fannin Usman ma, da dare Daddy ya Kira sa ya titsiye sa akan maganar, a cewar sa “ai wannan shirmen banza ne, shirmen hofi. Ta ya zai ce be da wacce yake so duk girman sa, shekara kusan 33 yana musu wasa da hankali”. Tsiya-tsiya sosai Big Dady yayi masa, kuma ya ba shi umarnin “lallai-lallai ya kawo mata zuwa nan da lokacin da Kaka ya ce, idan ba haka ba, zai ɗau mummunan mataki a kansa”

Hajiya na zaune tana jin su, sai dai bata ce komi ba, tunda itama ai tana ƙaunar ganin ɗan nata yayi aure, shi ne babban ɗa a gidan, amma har yanzu be yi aure ba, duk da a ganin ta ai ba wani shekaru ne masu yawa da shi ba, amma ta yanda za’a ganshi da girma, ƙannin sa su ƙara ganin girman sa, ai sai idan yana da mata, itama zata so ta ga jikokin ta ta wajen shi, ai abun kunya ne ma ace yanzu Yusra zata yi aure shi be yi ba, sannan ga ɗaya ƙanwar sa can a ɗakin miji har da ɗan ta, shi ƙaton banza ya zauna.

Shi kuwa Usman ko a jikin sa, tunda a ganin sa dai babu wanda ya isa yayi masa auren dole, don haka be tashi yin aure ba yanzu sai sanda yayi niyya, duk a cikin mata har yanzu be ga wacce tayi dai-dai da ra’ayin sa ba, yana da burin ra’ayin auren mace zaɓin shi da koda yaushe zuciyar sa take raya masa, kuma har yanzu be dace da kalan ta ba, don haka sai sanda ya same ta sannan ne zai yi aure, mata yanzu ba sa gaban sa, shiyasa ya ɗauki maganar Kaka ba ta da wata muhimmanci, bare shi rayuwan boko ya saka wa kansa, har yanzu gani yake yi be kai matakin da har zai iya ajiye mata ba, ɗawainiya ya hau kansa tun da ƙuruciyar sa ya tsufa da wuri.

 

 

 

⚫⚫⚫

Baffa kuwa sosai ya shiga damuwa a wannan ranan, har kuka sai da ya sha ya ƙoshi, ya kuma gode wa Allah, ga shi yana ji yana gani zai bar zaɓin shi babu yanda ya iya, yana kallon wacce yake ƙauna bata da wanda zata iya gabatar wa face shi, amma kuma Mahaifiyar shi tayi masa iyaka da ita.

Ya tuna sanda ya je har ɗakin ta yana kuka ya sake mata maganar “ta amince ya auri Ɗahira, in yaso duk wacce take so ya aura, shi wlh zai aure ta, koda kuwa mata huɗu zata haɗa masa, idan har da Ɗahira to ya amince”.

Amma sai buɗan bakin Hajja tace, “kai Al’ameen ka ji Ni da kyau, Ni Ɗahiran ce ba na so ka aura, bazan taɓa haɗa tsatso da A’ishah ba, domin kuwa na tsane ta a raina, ban taɓa faɗa maka hakan ba, amma yanzu sabida maganar nan ka saka ina bayyana maka sirrin dake raina, to wlh idan har ka kuma sake tayar da maganar nan ma, ban yafe maka ba”.

Kuka sosai Baffa ya fashe da shi, be iya furta komi ba sabida tsaban tashin hankali, wai yau Mahaifiyar sa ce take furta masa kalmar nan duk a sabida wani dalili nata mara tushe, ko a mafarki be taɓa tunanin akwai abinda zai iya bayyana wa mahaifiyar sa yana so ba, ta kasa mishi, sabida ya san tana ƙaunar sa, duk abinda yake so to itama tana so, hakan be taɓa faruwa ba, shiyasa yake ganin abun tamkar almara. ranan ya sha kuka kamar babu gobe, har zazzaɓi ya kwana da shi a ranan. Allah ya ɗaura masa ƙaunar Ɗahira kamar ransa, amma ga shi a lokaci ɗaya ya rasa ta, abinda be taɓa tunani ba ko da a mafarki, ya rigada ya saka wa ransa ita ɗin tashi ce, tunda be taɓa tunanin akwai wata matsalar da zai shiga tsakani ba, ko da ma akwai, to, sai dai a wajen Ɗahira, ita ma kuma be taɓa tunanin zata iya cewa ba ta son sa ba, tunda ya san girman son da take mishi, ya san Ɗahira a kansa zata iya yin komi sabida farin cikin sa, shaƙuwar su ya wuce misali, babu ɓoye-ɓoye a tsakanin su.
[6/5, 7:39 PM] Oummu Ɗahirah: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR’S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL._

*بسم الله الرحمن الرحيم*


𝐅𝐄𝐄𝐍𝐀𝐇 𝐖𝐑𝐈𝐓𝐄𝐑’𝐒 𝐀𝐒𝐒𝐎📖*
®Ɗ𝚊𝚢𝚊 𝚝𝚊𝚖𝚔𝚊𝚛 𝚍𝚊 𝙳𝚞𝚋𝚞💪✓

𝗝𝗜𝗞𝗔𝗥 𝗟𝗔𝗪𝗔𝗟𝗜 𝗖𝗘✍️

𝗪𝗮𝘁𝘁𝗽𝗮𝗱: 𝗨𝗺𝗺𝘂𝗗𝗮𝗵𝗶𝗿𝗮𝗵👈

\𝗙.𝗪.𝗔📚/

𝗦𝗔𝗗𝗔𝗨𝗞𝗔𝗥𝗪𝗔
𝑁𝑎 𝑠𝑎𝑑𝑎𝑢𝑘𝑎𝑟 𝑔𝑎 𝐹𝑎𝑚𝑖𝑙𝑦 𝑛𝑎 𝑔𝑎𝑏𝑎 ɗ𝑎𝑦𝑎. 𝗚𝗢𝗠𝗔’𝗦 𝗙𝗔𝗠𝗜𝗟𝗬.

 

*EPISODE Twenty Seven*

“Dakata da Allah Ayush! Wani taimako kike so in miki ban da wanda nayi miki? Kin tambaye Ni Numban sa na baki wannan kuma ya rage naki, in yaso ki je ki same shi da soyayyar ki, in kuma kin kasa Wannan kuma damuwar ki ne, amma kar ki ƙara zuwa min da banzan maganar nan taki akan Ni ce zan sanar mishi, ina ruwana a ciki?” Shakira take maganar cikin fusata

Ayush dake zaune a gaban table ɗin ta, idanun ta sun cika da ƙwalla, hannu ta saka ta share tana kallon ta tace, “fine naji, sabida na gama miki amfani shiyasa kike son watsa min ƙasa a ido, don kawai na nemi taimakon ki akan nawa soyayyar? Babu damuwa”. Ta ƙarishe maganar tana miƙe wa zata bar Office ɗin

Da tsaki Shakira ta raka ta, bata ce komi ba ta mayar da hankalin ta kan wayan ta, sai yanzu ma take dana sanin amince wa tayi ƙawance da local irin wannan, don da farko a tunanin ta ƴar masu kuɗi ne irin su, shiyasa tayi saurin amince mata, amma yanzu gaba ɗaya dana-sanin yin ƙawance take yi da ita, ta bar ta ne kawai saboda tana mata aiki a kan Baffa da Ɗahira, amma kuma yanzu tunda komi ya ƙare a tsakanin su baza ta iya juran raini wajen ta ba…

Tsakin ta kuma ja cike da takaici.

 

 

 

⚫⚫⚫

Ayush kuma na fita ta tsaya bakin ƙofar ta gama share hawayen ta, a fili ta furta, “wlh wlh sai kin yi nadamar sani na a duniya Shakira, yanda ban yi farin ciki ba kema baza ki taɓa yi ba, idan har kin ga kin samu kwanciyar hankali wajen mijin da zaki aura, to, tabbas nima na samu abinda nake so ne, amma mu zuba dani dake, ba a Shana a zauna lafiya”.
Tana gama faɗar hakan tayi hanyar Lefter don zuwa office ɗin Usman, so take yi yau ayi ta ta ƙare, baza ta iya barin soyayyar sa a zuciyarta ba, tana shan wahala ko da yaushe be ma san tana yi ba, dole yau zata bayyana mishi soyayyar ta, ko da zata samu sukunin zuciya, ga shi duk shawaran da Rumanatu take ba ta be yin tasiri, ita kuma Safra da tace zata taimake ta har yanzu bata sake jin ta ba, ko a waya ma Numban ta ya dena shiga, wannan dalilin ne yasa ta nemi taimakon Shakira, Amma kuma ta watsa mata ƙasa a ido, ita a ganin ta Shakira tana da hanyar da zata taimake ta domin mallakar Usman, shiyasa kai tsaye ta je da ƙoƙon baran ta..

Sanda ta isa bakin Office ɗin, tsaya wa tayi tana gyara zaman Labcoat ɗin ta, sai da ta gyara fuskar ta sannan tayi Nocking, sai dai babu answer, haka ta sake yin wani, sai da ta ɓata time a wajen kafin ya ba ta iznin shigo wa, buɗe ƙofan tayi ta shiga

Yana zaune ne kansa a saman table, ga duk kan alamu barci ne ya so ɗaukar sa sai yaji Nocking ɗin ta, amma kuma duk da haka be ɗago ba yana jiran yaji abinda ke tafe da ko ma wane ne

Ɗan numfashi taja kana cikin ƙarfin hali tace, “Doctor wajen ka na zo, can I sit?”

Sai a time ɗin ya ɗago kansa ya bi ta da kallo, ganin ta da Labcoat ya tabbatar masa da itama ma’aikaciya ce a Hospital ɗin, sai dai be iya ce mata komi ba illa sake haɗe rai da yayi yana kau da kansa daga kallon ta, tare da gyara zaman sa yana jingina bayan sa kan kujeran, har da ɗaga kansa sama yayi ya sake mayar da idanun sa ya rufe ruf

Ayush dai na tsaye tana kallon sa, sosai take jinjina halin miskilanci irin na bawan Allan nan, tabbas idan har ji da kai ne da taƙama, gami da izza, idan har ka zo wajen sa to ka gama samu, ko kai uban waye ne sai ya nuna maka wannan halin nasa, abun a jinin sa yake, sai dai in ka zage sa amma dole ne sai ka kwashi haushi a zaman ka da shi

Sai da ta ɗan ja wasu sakwanni tana tsaye ko zata ji yayi mata iznin zama kamar yanda ta buƙata, amma be ce komi ba, kuma ga duk kan alamu ba shi da ninyan cewa ɗin, don haka ta ja ƙafafun ta ta nemi wuri ta zauna jiki a sanyaye, shiru tayi don bata san ta ina zata fara ba, a tunanin ta abinda ta ɗauka ɗin sauƙi ne da shi, amma kuma sai da ta bayyana gaban sa ta gane hakan ba me yiwuwa bane ta sauƙi a gare ta, tabbas kwarjinin sa da tsantsan cika idanun sa bazai bar ta ta samu sukuni har ta faɗi abinda take so ba. haka ta shafe tsawon mintoci tana zaune ta kasa yanda za’a yi ta sanar masa da abinda ke ranta.

 

Shi kuma Usman tuni ma ya manta da wanzuwar ta wajen, domin ba kaɗan ba barci ne yake son kwasar sa, sabida jiya be samu yayi ishashshen barci sosai ba, kuma yau ɗin kafin ya zo Office ya wuce wani wuri, daga can ma ya wuto nan, shiyasa barcin yake son ya ci ƙarfin sa a yanzu.

 

Daure wa sosai Ayush tayi, ta ara wa kanta jarumta ta soma magana da faɗin, “dama I have come to tall you that..” sai tayi shiru ta kasa ƙarisawa

Tun soma maganar nata ya buɗe idanun sa da suka soma sauya kala, sai dai be motsa daga yanda yake ba, har yanzu fuskar sa na kallon sama ne, yana jiran yaji abinda ya kawo ta, domin dai zai iya cewa be ma taɓa sanin ta ba a nan Hospital ɗin, shiyasa zuwan nata wajen sa yake ba shi mamaki, duk da kuwa ba yau ya saba ganin hakan ba, amma kuma ita ɗin ya dangana hakan da zuwan ta a kan aiki ne..

Sauya maganar nata tayi da faɗin, “my name is Ayush Abdulkarim, wacce take tura maka saƙo a facebook, kuma kwanaki biyu kenan da soma maka magana ta WhatsApp”. Sai ta sake yin shiru

Sai a time ɗin ya ɗago kansa sosai yana sauke rikitattun idanun sa a kanta, sosai ya haɗe rai a wannan karon fiye da tunanin me tunani, wanda har sai da ya sa Ayush ta sunkuyar da kanta da sauri sabida ba ƙaramin tsorata tayi da kallon nan da yake mata ba, tabbas tuni ya gane ta da bayanin da tayi masa, sabida yanda take damun sa a facebook; kullum sai ya ga saƙon ta, that’s why tana faɗar sunan nata ya gane.

Be ce komi ba, kamar yanda itama ta kasa yin magana, tsawon lokaci kafin taji muryan sa ya daki dodon kunnen ta

“Get out”. Ya bata umarni cikin natsatstsiyar muryan sa

Nan da nan sai ga hawaye sharr sun soma kwaranya a fuskar ta, tana kallon sa tace, “don Allah ka taimake Ni kamar yanda Allah ya taimake ka, wlh wlh zan iya rasa raina idan har ban same ka ba, Ina son ka, ina matuƙar ƙaunar ka, don Allah..”

Tsawan da ya daka mata ne, yasa tayi shiru babu shiri

“Out”. Ya faɗa tamkar ana masa dole cikin murya me amo, domin maganar nan da ta saka shi har kanshi ya soma sara wa, dama ga shi yana buƙatar hutu da barci

Miƙe wa tayi idanun ta na tsiyayar da hawaye ta bar Office ɗin.

 

Lumshe idanun sa yayi yana sake jingina bayan sa da kujeran, ya rasa meyasa yanzu mata suka ɓaci, shin ina suka bar kunyan su ta ɗiya mace har suke iya zuwa su sami namiji su faɗa mishi suna son sa? Sosai yake mamakin yanda duniya ta sauya, ko zai mutu ne ai bazai iya auren mace irin wannan local ɗin ba, in ba raini ba kamar yarinyan nan ta zo har gaban sa tana faɗa masa tana son sa, tsaban takaici ma tsaki yaja ya miƙe ya ɗauki keeys ɗin motan sa ya bar Office ɗin.

 

 

 

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

*WEDNESDAY*

Cikin sauri take tafiya kasancewar tayi late, har ga shi 10:03am. Ta yi, wajen motan ta ta ƙarisa ta saka keey tana shirin buɗe wa, sai ta hangi Baffa shima ya fito daga bayan gidan

 

Tafiya yake yi yana waya kansa a ƙasa yana tsola ƙafafuwan sa tamkar yana ƙwallo

Mayar da ƙofan tayi ta rufe ta taka ta nufi inda yake, be ganta ba har sai da taƙariso wajen, inda daddaɗan turaren ta ya doki hancin sa, da sauri ya juyo suka haɗa ido

Murmushi ta sakar masa, don ganin sa ba ƙaramin faranta ranta ya yi ba, tun zaman da suka yi last two weeks wajen meeting bata sake ganin sa ba. bata yi magana ba ganin yana waya

Sai dai shi gaba ɗaya tunda suka haɗa ido ya rasa sukunin sa, wayan kawai yake yi amma hankalin sa ba ya tare da shi, duk da kuwa ya kawar da idanun sa daga kanta. Ɓata lokaci yayi yana wayan yaƙi ya yanke, sai kamo wani zancen yake yi kasancewar da abokin sa yake wayan.

 

Ita kuma tana tsaye ta harɗe hannayen ta a ƙirjin ta tana kallon sa, shiru tayi kawai idanun ta a kansa, sosai take ganin sauyi a tattare da Baffa, gaba ɗaya yanzu ta ga kamar ya sauya mata, kwata-kwata ba ya son ganin ta, idan ba haka ba tasan babu yanda za’a yi a kwana a hantse be nemi ganin ta ba, koda kuwa ta waya ne, amma yanzu tsawon satikai kusan uku kenan ana shirin wata ba ya neman ta, tana ganin kamar akwai wani abinda ke damun sa, yanda gaba ɗaya ya sauya har wani rama yayi…

“Keee!”

Tsawan da aka daka mata ne ya sanya ta dawo hankalin ta cikin matuƙar tsoro

Ba ita kaɗai ba, har ta Baffa da ya juya baya a yanzu ɗin yana ci gaba da wayan sa, sai da ya tsorata da tsawan da aka yi

Sa’adatu ce tsaye ƙiƙam gaban Ɗahira, ta kame ƙugun ta da hannayen ta biyu tana faman huci tamkar zaki, ba komi ya fusata ta haka ba illa fitowar da tayi tana shirin fita, sai ta hangi Ɗahira gaban Baffa ta ƙure sa da idanu ko ƙyafta wa ba ta yi, ga shi kuma har ta iso wajen tana mata magana amma bata ji ta ba, hakan ya sa ta daka mata tsawan nan

Bata bari kowa yayi magana a cikin su ba tace, “uban meye kika tsaya kina kallon sa tamkar zaki cinye sa? Ko dai wani makircin zaki ƙulla iyeee? Ki faɗa idan ba muna-furci da makircin da ke ran ki ba; meye ya kawo ki bayan shi kina kallon sa be ma san kina yi..”

“Kee Sa’ada are you crazy? Kin san da wa kike magana kuwa?” Cewar Baffa a matuƙar fusace da ɗaga murya

Kallon sa Sa’adatu tayi, sai ta zaro masa ido tace, “hankali na ƙalau kuwa Yaya, so nake in San meye alaƙan ka da wannan yarinyan? Ina ce Hajja ta raba ku meye kuma ya sake haɗa ku? Ok har yanzu kana son…”

Mari ya yarfa mata, wanda har sai da yasa ta soma ganin taurari, ba ita kaɗai ba har Ɗahirah dake kusa da ita, bata san sanda hannun sa ya gilma ta gefenta ba, hakan yasa ta tsorata taja baya da sauri tana shirin faɗi

Saurin taro ta Baffa yayi, hakan yasa ta faɗo kansa tamkar ya rungume ta.

A wannan lokacin shi kuma Usman ya fito gida, babu inda idanun sa ya sauka sai a kansu, tsaya wa yayi kawai yana kallon su cike da mamaki. Janye idanun sa yayi daga kallon su yana jan tsaki a fili, a zuciyar sa kuwa cewa yake, “dama daga gani idan wannan sheɗaniyar yarinyan bata ja hankalin maza sun faɗa tarkon ta ba ai ƙarya ne, waye ya san ma ranan da kuka soma hakan”. Motan sa ya ƙarisa ya shiga ya ja ya bar gidan.

 

 

A can kuwa wajen su, Baffa ya kasa cire Ɗahira a jikin sa, while itama ta kasa motsa wa, domin sosai ta tsora ta, sai da ta gama dai-dai ta nutsuwar ta kafin tayi yunƙurin janye jikin ta.

Sa’adatu da tayi mutuwar tsaye na daga tsantsan mamakin marin da Baffa yayi mata, ga kuma takaicin ganin su haɗe da juna, shi ne yasa ta kasa koda ƙwaƙƙwaran motsi, illa bin su da kallo da take yi.

Ɗahira na janye jikin ta ta juya ta wuce ba tare da ta furta komi ba

Baffa be iya dakatar da ita ba, duk da kuwa yana son tsayar da ita ɗin, har ta shige mota yana bin ta da kallo, sahun gudun Sa’adatu da kukan ta kawai ya ji, ya juya yana kallon ta wanda har ta kai ƙofa ta shige cikin gidan. Ajiyan zuciya ya sauke yana bin wayan sa dake ƙasa da kallo, be ma san sanda ya wuntsilar da ita ba garin taro Ɗahira. Lumshe idanun sa yayi a hankali ya furta, “Ina son ki Ɗahira! Ina matuƙar ƙaunar ki! Kuma ba zan taɓa dena ƙaunar ki ba har na koma ga mahalicci na”.

 

 

 

⚫⚫⚫

Ɗahira motan ta kawai take ja tana tunani, ko kaɗan ta kasa gane takamaiman abinda ke damun ta

Tsaki kawai ta ja ganin tana son damun kanta da tunanin banza, ƙara Speed ɗin motan tayi tana kallon agogon hannun ta

Dai-dai ta isa kusa da Hospital ɗin, tana shirin shan kwana ta shiga, bata kula sosai ba, Ashe wata mota babba na ɗan gote ta dumfaro. shi kuma can ɗaya side ɗin me machine ya dumfaro da gudu yana shirin gilma motan, sai motan tayi ciki da shi, Wanda machine ɗin da me machine ɗin tuni sun yi hanyar su daban, inda machine ɗin ta zo kan motan Ɗahira da har ta kusa tura kan hancin motan ta cikin Hospital ɗin, sai ji kake yi motar nata tayi ƙuuuuuuu.. saboda wani wawan burki da taja kasancewar buguwan da machine ɗin tayi a kan motan ta, yayi matuƙar tsorata ta har ta rasa nutsuwar ta gaba ɗaya taja burki a take tana salati

Can kuwa wajen babban motan nan tuni tayi ciki da wasu motan da suka dumfaro ta, nan da nan motoci da mashina suka harhaɗe aka haɗa babban hatsari, jini ya soma ambaliya a titin, machine ɗin nan na saman motan Ɗahira, inda wata motan kuma ta bugi motan nata tuni tayi ratsa-ratsa.

Kankace me mutane sun soma zuwa ceton rai, nan da nan wajen ya hargitse da hayaniya. Allah yasa kusa da asibiti ne, nan akai ta zaro mutane ana nufan asibiti da su.
[6/6, 9:23 AM] Oummu Ɗahirah: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR’S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL._

*بسم الله الرحمن الرحيم*


𝐅𝐄𝐄𝐍𝐀𝐇 𝐖𝐑𝐈𝐓𝐄𝐑’𝐒 𝐀𝐒𝐒𝐎📖*
®Ɗ𝚊𝚢𝚊 𝚝𝚊𝚖𝚔𝚊𝚛 𝚍𝚊 𝙳𝚞𝚋𝚞💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

\𝗙.𝗪.𝗔📚/

*SADAUKARWA*
𝑁𝑎 𝑠𝑎𝑑𝑎𝑢𝑘𝑎𝑟 𝑔𝑎 𝐹𝑎𝑚𝑖𝑙𝑦 𝑛𝑎 𝑔𝑎𝑏𝑎 ɗ𝑎𝑦𝑎. 𝗚𝗢𝗠𝗔’𝗦 𝗙𝗔𝗠𝗜𝗟𝗬.

_Wannan shafin naku ne Masoyana, kar ku ce ban gaishe ku ba😅, to ku shaƙata da wannan na ku ne kyauta, ina ƙaunar ku nima, har da waɗanda suka ɓoye kansu, Ni *JIKAR LAWALI* ina matuƙar jin daɗin nuna soyayyar ku gare Ni, idan baku Fans to babu Ni ce._

 

 

*EPISODE Twenty Eight*

Su Abbu na cikin Office ɗin Big Dady, inda suke meeting a kan shigo da magani da za’a yi musu, da sauran abubuwan da asibitin yake buƙata. A lokacin ne labarin mummunan hatsarin da ya afku a wajen Hospital ya iso gare su, ai tuni sun fito don zuwa su ba da agajin gaggawa

Sai da suka sauka downstairs ne, labari ya riske su da Ɗahira hatsarin ya ritsa. Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un tashin hankalin da suka shiga baki ma bazai iya bayyana shi ba, kankace me sun ruɗe gaba ɗaya kowan su sai sharce gumi yake yi, musamman da suka ga yanda ake shiga da masu hatsarin rai a hannun Allah. Nan su ma suka bi ayari fannin emergency rooms

Su Baffa da Fadila basu fito gida ba ma, labari ya kai musu, tunda shi Baffa dama be yi ninyan shiga ba yau, sai yamma, amma tuni sun ruɗe da su Aunty Amarya sun taho asibitin, sai dai an kasa sanar wa Kaka tunda ba’a san halin da take ciki ba yanzu.

Lokacin da suka iso asibitin, a reception suka tarar da su Aunty Zainab da Yusra da Shakira, tunda su ba fannin su bane, su Big Dady kuma na ciki.

Haka DOCTORS da staff’s suke ta sintiri suna ba da taimakon gaggawa

Baffa wuce su yayi ya bar su nan, shima ya nufi emergency rooms ɗin, duka tagumi suka yi har Hajja Fatu, domin itama taƙi shiga tunda itama ba fannin ta bane. Aunty Amarya ne kaɗai a wajen take share hawaye, sai Fadila da tayi zugum tana tunanin ƴar uwan ta a ranta, har bata san sanda ƙwalla ya zubo mata ba, babu abinda take tuna wa sai fitowar ta gida yanzu da abinda ya faru, dayake ta side ɗin windown ɗakin su suka tsaya, shiyasa tana kallon draman da suka yi da su Sa’adatu daga saman bene. haka Allah ke lamarin sa, da mutuwa ne sai a aiko musu a ce ta mutu.

 

Allah ya taƙaita, Ɗahira bata wani ji rauni sosai ba, sai dai suman da tayi ne har yanzu bata farka ba, ta samu buguwa a kanta har da ciwo, sai kuma gwiwar ƙafafuwan ta da suka ƙuƙƙurje. Alhmadulillah gaba ɗaya ahalin sun samu kwanciyar hankali musamman da suka shiga suka duba ta, time ɗin tana barci tunda an yi mata alluran barci, ba’a haɗa ta da kowa ba a ɗakin da take, sauran suna can rooms ɗin, sun daɗe wajen ta, inda suka je ɗaki-ɗaki suka duba sauran mara su lafiyan.

Sai da ta farka kafin su Aunty Amarya suka bar asibitin, tare da masu aiki suka koma tunda sun kawo musu abinci.

 

Ɗahira tana samun kulawa sosai wajen su Abbu, barin ma kar ace Doc. Sa’id, domin kasancewar fannin sa ne, shi yayi ruwa yayi tsaki yana kula da ita, abu kaɗan ya matso kusa da ita yana tambayan ta abinda ke damun ta, sai hakan ya faranta ran iyalan gidan, musamman su Abba, don a tunanin su akwai wani abu a tsakanin su, tunda itama Ɗahira sosai ta saki jikin ta dashi, ta yanda ma ta nuna sanayya a gare sa.

 

Hakan ko kaɗan be ma Baffa daɗi ba, shiyasa be wani zauna ba ya bar wajen, domin bazai iya zama yana kallon wani banza yana hira da ita ba, da kuma bata kula wa sosai.

Usman kam koda ya san abinda ke faruwa, ko leƙowa be yi ba, yana Office ɗin sa, sai da Big Dady ya kira sa yayi masa faɗa, sannan ne ya zo ya duba ta, kuma komi be ce mata ba, kamar yadda itama bata ko kalli inda yake ba. Haka ya juya yabar ɗakin yana taɓe baki.

Babu wanda ya sanar wa Kaka, har sanda su Abbu suka dawo gida, sannan ne suka sanar masa cikin nutsuwa, amma duk da haka sosai ya ɗaga hankalin sa, cewa yayi “dole sai an kai sa ya duba ta”. Ga shi lokacin dare ne. Dole haka suka fito gaba ɗayan su, Big Dady Abba da Abbu suka nufi asibitin.

 

Umma ce da ɗaya daga cikin ƴan aikin su za su kwana da ita, bisa umarnin Abbu. time ɗin ma tayi barci sanda suka zo

Sai a nan hankalin Kaka ya samu sukuni tunda ya ganta a kyakykyawar yanayi. Sun jima kafin suka baro asibitin.

 

Washe gari da safe ma ya saka aka sake kawo shi

Lokacin Ɗahira na zaune tana shan tea da aka haɗa mata suka shigo, taji daɗin ganin su, nan tabi su ɗaya bayan ɗaya tana gaishe su

Kowan su na amsa mata cike da kula wa, tare da tambayan ta ya jiki?

Murmushi tayi tace, “it’s so easy”.

Big Daddy yace, “Are You sure my daughter babu abinda ke damun ki?”

Gyaɗa kanta tayi tana sake tabbatar masa da cewa, “Yes my Dady”.

Murmushin farin ciki gaba ɗaya suka yi

Kaka yace, “ai gaba ɗaya kin ɗaga min hankali Matata, a jiya kasa barci nayi, ban ma karya ba na taho duba ki, ashe ke ga shi har kin samu saka abinci a cikin ki, kin bar Mijin ki cikin tashin hankali”.

Ɗahira murmushi ta sakar masa, tana langaɓe kai tace, “eyya Miji na, ban sani bane ai, ka ga da ban ci komi ba nima kamar kai, na tausaya maka matuƙa tsoho na”.

Dariya gaba ɗaya suka yi har Kaka da ke faɗin, “Ja’ira”.

Itama dariyan tayi cike da farin ciki. Haka suka ci gaba da hira na ɗan wani lokaci, inda su Big Dady suka tafi Offices ɗin su suka bar Kaka a nan, don ya ce, “ba yanzu zai koma ba”.

Doc. Said ne ya shigo da sallama a bakin sa

Suka amsa mishi suna kallon sa, musamman ma Kaka

Shi kuma murmushi yayi ya iso wajen yana durƙasa wa har ƙasa ya gaishe da Kaka

Kaka ya amsa cike da fara’a da jin daɗin girmama sa da yayi

Ɗahira bata bari ya sake magana ba, ta gaishe shi itama

Amsa wa yayi yana kallon ta yana murmushi, sannan ya tambaye ta “ya jikin nata?”

“Alhmadulillah”. Ta amsa mishi da shi

Zama yayi gefen kujeran da ke kusa da gadon ta yana kallon ta, kafin kuma ya ce, “Yakamata a wanke miki ciwon idan kin gama ko?”

Ajiye Cup ɗin hannun ta tayi tana cewa, “ok Doctor I’m done ai”.

Miƙe wa yayi ya soma haɗa magunguna

Ita kuma suna hira da Kaka, inda yake tambayan ta “wane ne wannan?”

Dariya tayi tace, “Kaka Doctor ne shima ai”.

Gyaɗa kansa yayi yana bin Doctor Said da kallo

A haka dai har Doc. Sa’id ya gama abinda zai mata, sannan ya zauna ana hira da shi

Sosai a nan Kaka ya sake fahimtar akwai wani abu a tsakanin su, inda lokaci ɗaya ya ji farin ciki a ransa, shiyasa ya sake jan Doc. Sa’id a jikin sa, ko ba komi nan da lokaci kaɗan zai ga auren Jikar tasa, ko kaɗan ba ya son ƴan uwan ta su yi aure su bar ta, sosai hatsarin nan ya sake ɗaga masa hankali.

Ana haka su Aunty Amarya suka zo

Ɗahira taji daɗin ganin su sosai, nan ta sake sakin jiki ana ta hira gaba ɗaya, ga shi sosai take farin cikin yanda ake ba ta kula wa, musamman su Big Dady, da zaran mintuna ƙalilan ya wuce za su taho duba ta.

Sai yamma duk suka tafi har Kaka.

Kwanan ta biyar a asibitin tana samun kulawa, kafin aka sallame ta, ta koma gida tana ci gaba da jinya. A haka har ta samu sauƙi sosai, inda ta nemi ta koma bakin aikin ta, amma sai Abbu ya hana ta tunda har yanzu ɗingishi take yi.

Sai da aka shafe kusan sati Uku kafin ta warware, sannan ta koma bakin aikin ta, zuwa yanzu sosai Ɗahira da Doc. Sa’id suke mutunci, koda aka sallame ta a Hospital be taɓa zuwa gidan su ba, amma kuma suna waya sosai, hakan yasa suka saba, har ita Ɗahira tana tunanin son ta yake yi, sabida yanda yake ba ta kula wa ainun, shiyasa ma ta sake sakin jiki sosai da shi, sai dai har yanzu kalman da take so taji a bakin sa ya ƙi ya sanar mata, ko kaɗan ba ta ƙaunar a sake zaman meeting ba tare da tana da tsayayye ba, sai dai babu yanda zata yi tunda be ce yana son ta ba har yanzu, sai ma daga baya ta gane yana da mata har da ƴaƴa biyu, amma hakan be ɗaga mata hankali ba, a ganin ta idan yana son ta zata iya auren sa, tunda duk wani ɗabi’u na kirki shi yake nuna mata, sai dai lokaci na ta ja babu wannan kalman a bakin Doc. Sa’id, ga shi har yanzu saura sati biyu auren ƴan gidan.

Kamar yanda suka saba meeting ranan Lahadi, haka wannan Lahadin aka tara su, Ɗahira aka soma tambaya, amma tace musu “bata da wanda take so” maganar ya girgiza su

Kaka yace, “kina nufin wannan Doctorn har yanzu be yi miki ba?”

Kallon Kaka tayi tace, “Kaka ai ba soyayya muke yi da shi ba, it’s just Friendship”.

“Uwata dama ai ta hakan ne soyayya take ƙulluwa, ke dai kawai ki sanar mana idan da akwai wani abu a tsakanin ku, kar ki zauna ki ce zaki ja mishi aji kinji ko?”

Gyaɗa kanta tayi kafin kuma tace, “amma Abba wlh be taɓa cewa yana so na ba, kuma ma yana da iyalan sa”.

Shiru suka yi duk kan su, kafin kuma Kaka ya sake Tambayan Usman da cewa, “to kai kuma Fodio aina taka take?”

“Nima Kaka har yanzu ban samu wacce nake so ba”.

“Kana nufin har yanzu maganar da muka yi maka baka ɗauke ta da muhimmanci ba?” Big Dady ya faɗa yana kallon sa

Shiru Usman yayi kansa a ƙasa

Nan Dady ya dinga faɗa kamar zai ari baki, kuma ya ce “dole sai yayi aure da ƴan uwan sa, idan be samo matan ba shi yana da hanyar da zai samo masa”

Kaka ne ya tsayar da shi da faɗin, “ƙyale shi Noor, duk hakan be ta so ba, yanzu dai aci gaba da hidiman biki kar a fasa, su kuma Allah ya kawo musu na gari, lokacin su ne be yi ba babu yanda zamu yi da su”.

Daga haka ba’a sake yin wata maganar ba, aka sallami kowa.

Inda daga ranan gadan-gadan aka ci gaba da hidimomin biki, ko wanne fanni suna nasu, tunda kowa a cikin su zai aurar, illa Aunty Amarya ce kaɗai da babu ita, amma kuma komi da ita ake yi ana Fadila, duk ita take shirin komi, sai ƴan uwan Umman dake nasu, duk da suna yaɓa mata maganganu amma ko bi ta kansa ba ta yi, abinda yafi ɗaga mata hankali yanda gidan duk ya cika da mutane, babu hiran da suke yi sai na Ɗahira, wai “har yanzu bata da mashinshini, tayi kwantai, maza ma tsoron zuwa wajen ta suke yi, bare su furta mata suna son ta.” Kowa ba ya lura ba ita kaɗai bace a gidan da baza ayi auren ta ba, har da Usman, shi da yake ma babban su amma yaƙi auren, amma ita kaɗai ake gani

Sanda Ɗahira ta soma jin ƙananun maganganun nan bata wani damu ba, sai dai yanda ƴan uwa suke taran ta da maganar, har wasu suna mata Shaƙiyanci suna yaɓa mata magana, sai abin ya soma damun ta, amma babu yanda zata yi haka take barin abun a ranta, duk da ita bata cika iya ɓoye damuwa a ranta ba, ko ya ya ne idan har tana da damuwa sai ka gane..

 

Gida fa ya sake cika maƙil inda har an soma events, duk da ba kowa bane ke wajen, wasu sun tafi can Katsina, Hajiya Laila ma can ta tafi, sai su Firdausi da sauran ƴaƴan ta masu aure da suka zo nan, Aunty Zainab ma da ita da Aunty Amarya, ana gobe suka wuce can a bisa umarnin Kaka, tunda ba za’a bar Hajiya Ikram ita kaɗai tana biki babu ƴan uwa ba, kowa ya zo nan ya shantake, wasu ma zuwa gobe ranan bikin za su wuce idan za’a kai Fadila can, sai su kwana biyu wasu kuma su yi kwana ɗaya.

Tun ana kwana biyu Sa’adatu ta koma Legos, sai ranan bikin za a kawo ta.

 

 

 

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

Dafa ta Fadila tayi, hakan yasa tayi firgigit tana kallon ta

“What are you thinking sister, I’m talking to you are you quiet?”

Murmushin yaƙe Ɗahira tayi, sai ta gyaɗa kanta tana son mayar da hawayen dake cikin idanun ta tace, “nothing”.

Cike da tausayin ta Fadila tace, “don Allah ki dena saka damuwa a kan maganganun su Inna, ko ma su waye ne zasu yi miki gori don Allah ki dena saka damuwa kinji, ke baki ga yanda kika faɗa bane? Ana bikin mu amma gaba ɗaya kin tsame kanki a cikin mu”.

Shiru Ɗahira tayi, don bata san me zata ce mata ba

Sai itama Fadilan tayi shiru, sai dai bata tashi a wajen ba. Tsawon lokaci suna a haka kafin Fadilan ta kalle ta tace, “Sister, there is something I want to tell you, akwai maganar da naji wajen Hajja da Shakira, shiyasa naga dacewan in faɗa miki”.

 

 

 

 

 

_What do you think Fadila will tell her? 🤔_

_mu je zuwa yanzu aka soma._
[6/7, 10:41 AM] Oummu Ɗahirah: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR’S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER’S ASSO*📖
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

\𝗙.𝗪.𝗔📚/

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA’S FAMILY*_

 

*EPISODE 29 & 30*

Idanu Ɗahira ta zuba mata tana jiran taji me zata faɗa

Fadila tace, “na lura a gidan nan Hajja ba ta ƙaunar ki, kuma ba ita kaɗai ba har ta da Shakira, domin tasha sanar dani abu game dake domin ta haɗa mu faɗa, ban taɓa biye mata ba, sabida narigada nasan abinda ke cikin ranta. A kwanaki biyu da suka wuce na ji su suna zancen ki, maganar rashin samun tsayayye ne da baki dashi, suna faɗin hakan yayi musu daɗi, har suna cewa Allah yasa ma ki dauwama a haka baza ki taɓa aure ba, sannan Hajja take cewa koda ma kin samu, ita tayi alƙawari baza ta taɓa barin ki ki zauna da mijin ki lafiya ba, duk yanda za’a yi sai tayi don raba ki da Mijin, sai ta mayar dake ƙaramar bazawara idan kin yi aure, idan kuma baki yi ba, zata bi duk hanyan da taga zata iya wajen hana ki aure”.

Tun soma maganar nata Ɗahira take tsiyayar hawaye, sosai zuciyar ta ke suya da zancen nan, “wai dama tsanar da Hajja take mata har ya kai haka ne?”

Bata san cewa a fili tayi tambayar ba, sai jin muryan Fadila tayi tana cewa, “yafi haka ma, baza ki san haka ba sai nan gaba kaɗan idan kin san wani sirrin. Sister Ni abinda nake roƙon ki dashi har na sanar miki da zancen nan, saboda ki san maƙiyan ki ne, ki san yanda zaki zauna da su, sannan ki san hanyar da zaki ɓullo wa al’amarin, ki riƙe addu’a domin baki san ta ina za su biyo miki ba, don Allah ina sake roƙon ki, duk wanda zaki aura Sister, ki kasance me mishi biyayya, ki zauna da mijin ki lafiya ko don ki ba ma Maƙiya kunya, Ni ƙanwar ki ce, but I beg you by God, ki tuna magana ta ko bayan ba na nan”.

Sosai a wannan lokacin Ɗahira take hawaye, har da shashsheƙan kuka

Itama Fadila tuni nata hawayen sun zubo, cikin rawan murya tace, “”I miss you Sister, please .. please ki nemi kariyan Allah domin ki guje wa afkuwar wani abu, ba na son wani abu ya same ki ta silan maƙiya..”

“Keee Fadila meye haka? Me kuke yi haka? Kukan meye?” Ƙanwar Umma da suke kiran ta Inna Sailuba take faɗar hakan, shigowar da tayi

A tare suka bi ta da kallo, sai dai babu wanda ya tanka mata, illa ƙoƙarin share hawayen da suke yi

Tsaki taja tana bin su da kallo itama tace, “tashi dalla kin zauna ta saka ki gaba tana kukan muna-furci, idan ba ta son rabuwa dake ne itama tayi auren mana, in ba hassada kuma take miki ba. Ki tashi nace ga Naja’atu can ta dawo ku je gidan me lallin”.

Kamar yanda basu ce mata komi ba ɗazu ɗin, haka yanzu ma babu wanda ya tanka mata, sai dai Fadila ta miƙe tsaye ta wuce zuwa waje. Itama Inna Sailuba ɗin sai bin bayan ta tayi tana sababi har da kumfan baki, “wai Fadila ta raina ta, tana faɗa mata gaskiya amma Ɗahira ta fi ta a wajen ta”. Duk da kuwa tasan cewa halin Fadilan ce ƙyaliya da Miskilanci. Kankace me sauran jama’an da ke zaune a Parlour sun amshe zancen, nan suka soma aibata Ɗahira da ita da uwar ta tunda sun san ba ta nan, suna me zagin su da yin musu gori akan Ɗahiran.

Lumshe idanu Ɗahira tayi tana me sake jin zafi sosai a ranta, sosai take kukan zuci babu me rarrashin ta. Ganin baƙin cikin su zai iya kashe ta, sabida ita bata saba jure irin waɗannan ƙananun maganganun ba, sosai suke damun ta a zuciya, sai damuwar kuma ya haifar mata da ciwo, shiyasa ta tashi tafito ta nufi cikin gidan, kasancewar yamma ta soma shiyasa babu wasu mutane sosai a waje, ta inda tasan ma baza ta same su ɗin ba ta nan tabi ta wuce sashin Hajja

Akwai mutane sosai a parlour’n suna zazzaune suna aiki, kasancewar parlour’n akwai duhun magriba har ta wuce ɗakin Baffa babu wanda ya kula da ita, bare ma a shaida ta, bare kuma gidan biki kowa sha’anin gaban sa yake yi.

Keey ta saka ta buɗe ƙofan bayan ta taɓa taji a rufe yake, ta tura ta shiga sannan ta mayar ta rufe, Direct Kan gadon sa ta nufa ta faɗa ta soma rusa kuka, kawai so take yi ta fitar da duk wani ƙuncin da ke damun ta, domin kuwa muddin bata fitar ba, dole ne tayi ciwo. Sosai tayi kukan babu me rarrashin ta, sai da ta gama ta miƙe zaune ta buga tagumi tana me ci gaba da tunanin zuci

“Ita bata ga makusa a jikin ta ba, duk inda mace me ji da class, me ji da kyawu da tsafta, gami da ilmi ta kai, to meyasa har yanzu ta rasa masoya? Meyasaka har yanzu ta rasa wanda zai ce mata zai aure ta? Ta san tana da farin jinin jama’a, kama daga mazan har matan, babu wanda ba ta harka da su, amma kuma babu wanda ya taɓa buɗe baki yace mata ya zo gare ta ne don soyayya, wanda kuma zai kai su ga aure, sai dai su zo a matsayin tana burge su, tunda tana burge su why baza su sanar mata suna ƙaunar ta ba? Ko kuma dama tana da makusa ne wanda be dace ta samu mijin aure ba?”

Runtse idanuwan ta tayi hawaye na sake silalo mata, cikin muryan ta da ya dishe sosai sabida kukan da tasha tace, “Allah gani gare ka, kai kace a roƙe ka zaka amsa, har yanzu bazan gajiya ba, kuma na san cewa kana ji na. Allah ka zaɓa min abinda yafi alkhairi a rayuwa ta, idan har auren nan ne alkhairi a gare Ni, ya Allah ka zaɓa min miji na gari, idan kuma babu alkhairi a tare da Ni, ya Allah zan rayu ina me gode maka, saboda haka ka tsara min rayuwa ta. Zaɓin ka kaɗai nake nema ya Allah, a duk sanda kaso ikon ka a kaina, a lokacin Ni kuma zan amsa ina me godiya a gare ka ya Allah, Allah na tuba ka yafe min”. Ta ƙare maganar tana sakin wani sabon kukan

Ta jima tana yi kafin ta tsakaita tana me miƙe wa, sai hannun ta ya bigi drowan gadon wani abu ya faɗo, kasancewar ɗakin da duhu sai ta saka hannu zata laluba, hakan yasa ta kama wayan da tayar hannun ta na latsa wa a rashin sani, take a nan hasken ta ta kawo

Ƴar ƙaramar waya ce Nokia, wayan tabi da kallo, kamar ta ajiye sai kuma zuciyar ta ta bata umarnin latsa wa, take a nan ta danna ta ta cire ta a keey, nan ya bayyana wajen Text message, kasancewar daga wajen ne ba’a fita ba ta shiga keey

Rawa jikin ta ya soma saboda ganin text ɗin da ake turo mata, take ta koma ta zauna tana ci gaba da karanta wa, tabbas gaba ɗaya text ɗin da ake turo mata ne anan

“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un… Kar dai ace Ya Baffa shi ne Masoyin ta na ɓoye?” Tayi maganar a fili tana ɗaura hannun ta ɗaya dake rawa a baki

“Ya Allah…” Ta sake faɗa tana kai idanun ta dake tsiyayar da hawaye kan wayan, ci gaba da karanta text ɗin tayi, sai kuma ta koma ta shiga ta duba Numban, take a nan taga Numban nata ne

Lumshe idanu tayi tana jin wani irin raɗaɗi a ranta, babu abinda ya faɗo mata a rai sai text ɗin sa na ƙarshe

“Hajja..!” Ta furta a laɓɓan ta tana me buɗe idanun ta

“Why Hajja? Me nayi miki? Dama ke ce kika hana Ni aure a wannan gaɓar? Ke kika raba ni da Masoyi na na haƙiƙa? Me nayi miki da zafi haka?”.

Miyau ta haɗiye sabida jin wuyan ta ya cinƙushe da tuƙuƙin baƙin ciki, cikin kuka tace, “Ya Baffa meyasa ka kasa bayyana min kanka a matsayin wanda kake so na? Meyasaka ka zaɓi ɓoye min kan ka? Ashe dama da kai ne nake soyayya ban sani ba? Tabbas da baka ɓoye min kan ka ba, da duk haka be faru ba, ga shi Hajja taci galaban raba mu. Meyasa?..” ta kasa ƙarisa maganar dole tayi shiru

Tun soma maganar nata Baffa ya buɗe ƙofan ya shigo, yana tsaye bakin ƙofan yana jin komi, cikin tsananin ƙaunar ta tare da zallan tausayin ta yace, “Ƙaddara ce Ɗahira”.

Saurin ɗago idanuwan ta tayi tana bin sa da kallo, duk da kuwa bata ganin sa sosai, amma hakan be sa ta kawar da idanun ta a gare sa ba

Yaci gaba da faɗin, “Nima sai daga baya na gane nayi wauta, tabbas da na bayyana soyayyar ki a fili, da duk hakan be faru ba, da mutanen gida sun goya mana baya, da Hajja bata ci galaba a kan mu ba. sai dai yanzu kuma babu yanda zan yi, sabida Hajja tarigada tayi min iya ka da hakan, idan har na bari wani yaji, tsinuwar ta shi ne zai ta bibiya ta, ban san ya zan yi ba Ɗahira, amma wlh ina tsananin ƙaunar ki, ke nake so a zuciya ta, kuma har na mutu bazan taɓa dena son ki ba”.

Da gudu ta tashi tana toshe bakin ta, ta zo ta wuce sa ta bar ɗakin

Shima be hana ta ba, ko motsi ma be yi ba, illa runtse idanun sa da yayi hawaye na zubo masa kan kuncin sa.

 

⚫⚫⚫

Direct ɗakin Maman ta tawuce, ta shiga ta kulle kan ta ta hau rusa kuka babu ji babu gani, kukan da ke taɓa mata zuciya, yake ƙara mata raɗaɗin da ke cinkushe a zuciyar ta. Sosai tayi kukan wanda har ya haifar mata da ciwon kai me tsanani

Ita da kanta ta rarrashi kanta tayi shiru, sai dai duk yanda taso ta danne abun da take ji a ranta, ta kuma jure baƙin cikin dake zuciyar ta, ta kasa, gaba ɗaya rauni ne a zuciyar ta, waye zai rarrashe ta? Waye zai kwantar mata da hankali har taji sanyi a ranta? Ya faɗa mata tayi haƙuri haka ƙaddaran ta take?

Lumshe idanuwan ta tayi, hawayen dake maƙale a cikin idanun ta suka zubo saman kuncin ta, ta saka hannu ta share tana me miƙe wa zaune, kanta ta riƙe tana jan majina

“Allah Sarki Mamana, da ace kina nan ke ce zaki share min hawaye na. Meyasa ne Ni kuwa bani da Sa’a a rayuwa ta? Menene aibu na? Shin me na tare wa Hajja da ta tsane Ni har haka? Ya Allah.. ka saka min juriya domin in tsallake wannan jarabawar taka”.

Miƙe wa tayi ta wuce Toilet ta ɗauro alwala ta fito, sallan magriba da isha’i ta gabatar, sannan tayi shafa’i da wutri, ta jima tana kwararo addu’a tana hawaye kafin ta shafa ta miƙe

Ta san Abbun ta ba anan zai kwana ba, sabida jama’a masu biki, kuma dama Aunty Amarya ce ke dashi, shiyasa ta kwanta a ɗakin tunda tasan ba ma zai zo Part ɗin ba.

Daƙyar a ranan barci ɓarawo ya ɗauki Ɗahira.

 

 

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

 

Ranan Saturday 25 March 2021. Aka shaida ɗaurin auren *AL’AMEEN ABUBAKAR AL’AMEEN* tare da Amaryan sa *SA’ADATU ABDULLAHI*

*SHAKIRA ABUBAKAR AL’AMEEN* da Angon ta *SAHABI MAHMUD*

Sai *YUSRA NOOR AL’AMEEN* tare da Angon ta *SULAIMAN HABIB*

*FADILA AL’AMEEN AL’AMEEN* da Angon ta *KHABEER ALH. MUNIR.*

Ɗaurin auren da ya tara dubban jama’a ta ko ina, sai dai mu ce Masha Allah.

Zuwa huɗu ko wacce aka kai ta ɗakin ta bisa umarnin su Big Dady, Fadila aka wuce da ita Katsina da sauran jama’a. Yusra kuma da Shakira duk a nan Kaduna za su zauna, gidan Yusra ma ya fi kusa da gidan su, kuma duk ka su biyun za su ci gaba da aiki a Hospital ɗin su, sabida sai da aka yi yarjejeniya da mazajen nasu kuma sun amince.

Inda Baffa zai zauna kusa da gida ne, gini ne da aka yi musu shi da Usman a gefen gidan su, ga Gate ɗin gidan su ga nasu, sai dai kuma ta ciki a kwai ƙofan da aka yi wanda zai riƙa kai su cikin gidan su, ba sai sun yi wahalan fito wa ta Gate ba, wannan duk tsarin Kaka ne, shi ya siya filin kusa da gida, sabida yafi so iyalan sa su zauna waje ɗaya, har filin Fadil da yake ƙarami akwai shi an ajiye masa, idan ya tashi aure sai ya zauna a nan ɗin

Part ɗin Baffa dana Usman suna kallon juna ne, komi iri ɗaya aka yi musu, ɗakuna uku ko wanne da Toilet a ciki, sai babban Parlour da kichen a ciki da kuma wani Toilet, sannan idan ka fito waje ko wanne yana da faranda a ƙofan ɗakin, komi dai masha Allah, domin ba kaɗan ba an kashe kuɗi a ginin nan, su Big Dady duk suka yi musu komi babu ko ƙwandalan su, kayan ciki kuma suka bar musu su yi da kan su

To Part ɗin Baffa dai ya tsaru sosai, domin zance kuɗi yayi kuka a nan, iyayen Sa’adatu sun kashe mata kuɗi sosai, don ganin sun fito da ɗiyar su, itama zuwa dare aka kawo ta, can babban gidan aka fara kai ta, sai da aka kai ta wajen Kaka yasa mata albarka, sannan su Big Dady suka haɗa su da Baffa suka yi musu nasiha sosai. Daga nan kuma suka wuce wajen Hajja, inda itama tayi wa Baffa faɗa da nasiha sosai, akan “ya riƙe ta da amana, kar taji kar ta gani wajen ya muzguna mata, domin ita ɗin ƴar uwan sa ce, idan kuma aka ce ta kawo ƙarar sa, to wlh sai ta ɓata masa rai”.

Shi dai be ce komi ba, har ta ƙarashe faɗan ta ta sallame su, suka nufo gidan su.

Sai mu ce Allah ya ba da zaman lafiya Amare.

 

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

Ɗahira dai taci bikin nan ne ba a daɗin rai ba, domin kuwa fama take yi da matsanancin zazzaɓi me zafi, kowa be san halin da take ciki ba, ko Kaka da take zuwan mishi hira, ƙin zuwa tayi bare ya san me ke faruwa da ita, shima be neme ta ba tunda ya san sha’anin biki ne

Fadila ita ke matsa mata tasha magani, domin sosai take bata tausayi, ita duk a ganin ta tana damuwa ne saboda rashin auren ta, bata san cewa Ɗahira ta kasa jure rabuwan da suka yi ne da Baffa ba, har yanzu abun na cin mata rai, shiyasa dole ciwo ya kamata.

A haka Aunty Amarya ta dawo ta tarar da ita babu lafiya, hankalin ta yayi matuƙar tashi, duba da yanda ta dawo ta ganta gaba ɗaya ta rame a ɗan kwana biyu kacal da ba ta nan, babu wanda ya duba lafiyan ta, har kuka sai da Aunty Amarya tayi, nan ta kira Abbun su take sanar mishi

Shima hankalin sa ya tashi sosai, tare da ɓacin rai da ya nuna a kan Umma, tunda ai ita ce take zaune da su, amma ta kasa kula da ita, ga shi gida ya hargitse da ƴan biki, shi kansa ba kwana a Part ɗin yake yi ba, kuma ko da yana son ganin yaran sa, yawan jama’a bazai bar sa ganin su ba, shi duk a tunanin sa da ita ake bikin

Dole aka ɗaura mata drip, sabida sosai take jin jiki, duk hankalin su Kaka ya tashi matuƙa, irin su Hajja Fatu kuwa murna fal ciki, domin duk a ganin su baƙin cikin rashin auren ta ne ya saka mata damuwa

Su ma su Kaka abinda suke tunani kenan, shiyasa tayi matuƙar ba su tausayi, a ranan Kaka ya zauna da ƴaƴan sa meeting, inda suka yanke shawaran kawai za su haɗa auren Ɗahira da Usman, tunda dai baza su zuba musu idanu suna kallon su sun ƙi aure ba, sai dai babu wanda ya tayar da zancen, sun bari sai nan da kwana biyu, lokacin an gama huta wa da bikin nan da suka yi.

Itama Ɗahiran sosai take samun lafiya, tunda ana kula da ita sosai

Baffa dai sau biyu yana zuwa gaishe ta, yanda Ɗahiran ta nuna masa ne, yasa shi jin daɗi, domin ko kaɗan bata sauya masa daga yanda suke da ba, gaba ɗaya ta nuna masa tamkar wani abu be faru tsakanin su ba, duk da a zuciyarta tana jin ƙaunar sa. Hakan sai ya mishi daɗi sosai, shima sai ya saki jikin sa yana jan ta da hiran da suka saba

A ranan na ukun ne da zai zo, suka taho da Sa’adatu don ta duba ta, amma daƙyar ta taho, don sai da suka yi faɗa da Baffa ɗin, da cewa tayi, “ba ta zuwa” amma da ya nuna mata ɓacin ran sa, dole ta biyo sa

Suna zuwa tayi mata ya jiki ta miƙe zata tafi, sai ta ga Baffa ma gyara zaman sa yake yi be da ninyan tafiya, ta kalle sa tace, “a’a ya haka kuma? Kai da za mu tafi kuma kake shirin zama?”

Kallon ta yayi, sai ya harare ta, sabida akwai Aunty Amarya a wajen, dayake suna zaune a Parlour ne har Ɗahiran. Kawar da kansa yayi ya soma jan Ɗahira da hira

Sai ta ja dogon tsaki tana faɗin, “Da kai fa nake yi ka zauna ina magana?”

A fusace Baffa ya kalle ta yace, “Ni sa’an wasan ki ne wai Sa’adatu? Ni ne zaki tasa a gaba sai ka ce ɗan ki?”

Murguɗa baki tayi ta hau jijjiga jiki, sai dai bata iya cewa komi ba sabida ganin yanda ya taso mata a fusace

Aunty Amarya ce tace dashi, “ya isa haka Miji na, tashi ka tafi tunda baka san me take buƙata ba, ka je kaji ka dawo anjima”.

“But wlh Aunty Amarya this girl…”

“ya isa tashi ka je kaji?” Ta katse sa da faɗan haka cikin lallami

Miƙe wa yayi yana kallon Ɗahira da ta kawar da kanta yace, “Sweet sister I’m leaving, I will be back soon, we have something to talk about, Allah ya ƙara lafiya kinji?”

Gyaɗa masa kai tayi, a wannan karon tana kallon sa tayi masa murmushi tace, “to Yaya na, na gode”.

Fuuuu Sa’adatu ta wuce ta bar parlour’n

Shima bin bayan ta yayi bayan ya sake yin ma Aunty Amarya sallama

Aunty Amarya ci gaba tayi da ɓare lemon dake hannun ta, a ranta sosai take mamakin abinda yasa Sa’adatu take kishi da Ɗahira, domin tuni ta gane abinda ke zuciyar ta, sai dai kuma bata san cewa da Baffa Ɗahiran tayi soyayya ba

Ɗahira kuwa gyara wa tayi ta kwanta kan two sittern da take kai, tana lumshe idanu tare da faɗa wa duniyar tunani, ita ko kaɗan abubuwan da Sa’adatu take yi ba ya damun ta, amma duk idan ta tuna da yanzu ita ce a makwafin Sa’adatu ɗakin Baffa, abun na mata zafi sosai a zuciya, har ta zubar da hawaye.

 

⚫⚫⚫⚫

Kai tsaye gidan su suka nufa, Sa’adatu tariga shi isa, inda ta zauna a kan ɗaya daga cikin kujerun parlour’n ta tana faman karkaɗa ƙafa, sosai ta cika tayi maƙil tsaban kishi, ita ko kaɗan yanzu ba ta ƙaunar Baffa ya raɓi Ɗahira, gani take yi hakan zai saka mutanen gida su san me ke faruwa tsakanin su, kuma ta san ako yaushe za’a iya kawo mata ita a matsayin kishiya, tunda ita ɗin ƴar uwan sa ce, baza su yi la’akari da daɗewan auren ba ko rashin sa.

Shigowar Baffa ne ya dawo da ita daga guntun tunanin da ta afka

Kallon ta yayi kamar yanda take kallon sa yace, “ke wai Sa’adatu wani irin baƙin kishi ne kike son ki shigo min da shi gida na? Wato rashin hankalin naki ya kai har ki shiga tsakani na da ƙanwa ta? A kan me zaki riƙa min haka? Ke fa baki isa ki hana Ni abinda nayi ninya ba, kuma idan Allah yace Ɗahira mata ta ce, wlh daga ke har wacce take ɗaure miki gindin baku isa ku hana ba”.

Sai kawai yaga ta fashe masa da kuka, cikin kukan take cewa, “wlh tallahi kamar a kunnen Hajja, wato kana nufin Ni da ita ba mu isa mu hana ka kula wancan yarinyan ba ko? Kenan Hajja bata da mutunci a wajen ka? Da kake cewa kar na shiga tsakanin ka da Ƙanwar ka; ai ba Ni ce na raba ku ba, wlh na gaji da abinda kake min, tunda ba ka gani na da mutunci ƙarar ka zan kai”. Tana ƙare zancen nata ta tashi fuuuu ta fice tana ci gaba da kukan ta

Direct cikin gidan ta nufa, inda ta wuce Part ɗin Hajja don Kai ƙaran sa.

Ta bar sa nan tsaye da sakakken baki, sosai ransa ya ɓaci da abinda ta faɗa, “kenan shi be da ikon da zai mata faɗa, sai ta ɗibi ƙafafu ta kai shi ƙara wajen Mahaifiyar sa? Anya zai iya wannan auren kuwa?”

 

 

 

 

 

_to ba mu dai sani ba baffa. 🤷_

💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR’S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER’S ASSO*📖
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

\𝗙.𝗪.𝗔📚/

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA’S FAMILY*_

*TARIHIN FARILTA SALLAH*
”’An farilta sallolin nan biyar ne gabanin ƙaura, watau hijira, da shekara ɗaya da rabi. Sallah ce kaɗai ibadar da aka farilta ta a sama a daren Isra’e, kamar dai yadda aka ruwaito a hadisin nan na Anas. Da farko an umurce shi da Sallah guda hamsin ne; da sannu aka dinga rage su har suka zama biyar a bisa roƙon da shi Manzon ya yi wa Ubangijin sa. Da suka zama biyar, sai Allah ya ce masa su biyar ɗin nan, dai-dai suke da hamsin.
Malamai da yawa sun yi bayanin yadda sallar ma’aikin Allah, mai tsira da aminci, take gabanin Isra’en.
Wasu malaman sun ce, “Gabanin Isra’e, babu wata sallah wadda aka farilta sai sallar dare (Ƙiyamul lail) wadda aka umurci ma’aiki da yin ta ba da iyakataccen lokaci ko adadi ba, kamar yadda yake a suratul Muzzammil, ayoyi huɗu na farko:
“Ya wanda ya lulluɓe! Ka tsayu domin yin Sallah a cikin dare (duka) face kaɗan, rabin sa, ko ka rage abu kaɗan daga gare shi, ko ka ƙara kansa…
Ma’aikin Allah ya kasance yana yin sallar a kashi biyu cikin uku na dare ko a rabin sa ko kuma sulusin sa. Musulmi suka dinga yi tare da shi kamar shekara guda har suka gaji; daga nan sai Allah ya shafe ta don jin ƙan su.
An ruwaito cewa sallar da Musulmi suke yi gabanin tafiyar dare suna yin ta ne kafin faɗuwar rana da kafin ketowarta kamar yadda yake a sallah littafin Almanhalil Azb. Gabanin ƙaurar Annabi zuwa Madina raka’o’in sallah bibbiyu ne, bayan ƙaura ne suka zama hurhuɗu, illa magriba da ta kasance raka’a uku, ita kuma sallar subahi ta tsaya a kan biyu saboda dogon karatun da ake yi cikin ta. Buhari da Ahmad sun ruwaito daga Nana A’ishah cewa, “an farilta sallah raka’a bibbiyu, bayan ƙaura ne aka mai da ita raka’a hurhuɗu, amma an bar sallar tafiya a kan raka’a ne bibbiyu, sai sallar magriba ita ko da ma raka’a uku-uku ce.”
Allah ya sa mu dace.”’

.

*EPISODE Thirty One*

Tunda Sa’adatu ta shiga parlour’n Hajja, ta tarar da ita zaune, sai ta ƙara volume ɗin kukan ta tana nufan kujera kusa da ita ta zauna

Kankace me Hankalin Hajja ya tashi, nan ta soma tambayan ta ba’asin kukan nata

Sa’adatu ta sanar mata da abinda ke faruwa, daga zuwa gaishe da Ɗahira Da Baffa ya matsa mata tayi, har maganganun da ya faɗa yanzu

“Lallai kam Baffa yana son Wasa Dani a gidan nan, amma bari miƙo min waya ta in Kira sa”.

Tashi Sa’adatu tayi ta miƙo mata wayan daga kan Centre table, ta ba ta

Kiran sa tayi ta ba shi umarnin zuwa yanzu

Be daɗe ba kuwa sai ga shi ya shigo parlour’n da sallama

Tsaban tsiya ya ci ran Hajja, ko sallaman ma basu amsa ba, ta hau masa faɗa, ta inda take shiga ba ta nan take fita ba

Ganin abun yayi yawa, sai ya ce, “Hajja wai me tace miki ne da kike min irin wannan faɗan?”

“Uwar ka tace min, nace uwar ka tace min, wallahi tallahi Baffa ka fita ido na in rufe, idan ba haka ba zan mummunan saɓa maka a gidan nan, tunda kake baka taɓa gaya min magana ba, amma a kan wancan shegiyar yarinyan naga alamu kana so ka bijire min, to wlh kar in sake ganin ka raɓe ta, idan ba haka sai na..”

“Hayaniyar mene ne haka nake ji wai?” Cewar Abba da ya fito daga daƙi daga shi sai Singlet da dogon wando, da alamu dai barci yake yi Hajja ta tashe shi da hayaniyar ta

Daga Baffa har Sa’adatu duƙar da kansu suka yi, sun kasa cewa komi, sai Hajja ne da ta cika maƙil da fushi tana shirin magana

Ya katse ta da faɗin, “ya isa, ku tashi ku tafi gidan ku”.

Tashi suka yi daga Baffan har Sa’adatu suka fice

Sannan ya juyo kan Hajjan yace, “wai ke Fatima me kike so ki zama ne? Me Baba na yayi miki da kike son hana sa kwanciyar hankali shi da matar sa? Duk abinda kike faɗa ina ji, wlh idan har baki fasa shiga sha’anin auren su ba, to watarana zaki ji kunya, kuma da kike son raba sa da ƴar uwan sa, kar in ji kar in gani, domin zan mummunan saɓa miki kema, wannan ai rashin hankali ne, tukuna ma me Uwata tayi miki ba kya ƙaunar ta?”

Shiru Hajja tayi don bata san me zata ce ba, shaf ta manta da yana ciki da tun farko bata ɗaga muryan ta yaji ta ba

Ƙwafa yayi kafin yace, “ki ci gaba kar ki fasa”. Ya juya ya shige ɗaki

Sosai ran Hajja ya ƙara ɓaci, a ranta ta ɗau alƙawarin muddin tana numfashi sai ruwan sha ya gagari A’isha da ɗiyar ta.

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

Ranan Monday Ɗahira ta koma bakin aikin ta, saboda sosai jikin ta yayi sauƙi

Shima Baffa ranan ya koma, tunda sati biyu kenan da auren su

Nan hankalin Sa’adatu ya tashi matuƙa, domin gani take yi, Baffa ya koma bakin aiki ne duk sabida ya ga Ɗahira ta koma aikin ta, kuma tasan a can dole su riƙa haɗuwa, wannan abun duk ya dame ta, taje ta sanar wa Hajja

Hajja tace, “ta bar su, zata saka musu idanu, kuma zata yi wa Baffa gargaɗi sosai” domin ita kanta Hajja yanzu ba ta ƙaunar alaƙar Baffa da Ɗahira, hanya mafi sauƙi take son samu don raba su, sam ba ta ƙaunar su ci gaba da yanda suke kamar da, tunda yanzu a ganin ta yayi aure, hakan zai cuta wa Sa’adatu.

Baiwar Allah Ɗahira, ko kaɗan ma bata san wainar da suke toya wa ba, babu ruwan ta, abinda ta saka a gaba shi take yi, a ranan ma da ta dawo aiki ta shirya zuwa gidan su Shakira, tunda ko sau ɗaya bata je ba, da biki bata da lafiya, kuma Aunty Amarya ne ma ta matsa mata taje ɗin, kar ace tana baƙin ciki ne mutanen gida su yi wani fassara daban, shiyasa yau da wuri ta tashi a aiki, zuwa ƙarfe ɗaya da rabi ta dawo

Wanka kawai tayi ta shirya cikin farin Less me ɗige-ɗigen baƙi, riga da skert aka yi mata, wanda yayi mata cif a jikin ta, ya kuma ƙara haska mata white skin ɗin ta, sai ta yafa baƙin gyale bayan tayi ɗaurin ɗan kwalin ta normal, sai dai fuskar nan ya sha make-up, sabida Ɗahira ba baya ba wajen son gayu, musamman na kwalliya, takalmi me tudu tayi amfani da shi fari, ta ɗau HangBag ɗin ta ta rataya ta fito

Umma ce kaɗai zaune a parlour’n

Tace mata, “Umma zan je gidan su Shakira ne”.

Sai Umma ta wangale baki tace, “ahh to Masha Allah, yau kenan zaki leƙa su? To ki gaishe su”.

Murmushi Ɗahira tayi tace, “insha Allah Umma za su ji”. Tana gama faɗar haka ta shige ɗakin Maman ta

Taɓe baki Umma tayi tana kawar da kanta daga kallon bayan Ɗahiran, a ranta tace, “gulma ajali! ba ma asan me zaki je yi ba, Allah dai ya tsare min ɗiya ta ba a nan kusa take ba bare ace za’a je mata”. Sai kuma ta miƙe ta nufi cikin gidan inda zata je kai wa Hajja rahoto.

Ɗahira na shiga tace ma Aunty Amarya “ta shirya zata tafi”.

Shi ne take tambayan ta “baza ta ci abinci bane?”

Tace mata “sai ta je can, zata ci a gidan su”.

Daga haka Allah ya kiyaye hanya Aunty Amarya tayi mata, ta bata saƙon gaisuwa, sannan ta fito. Motar ta ta hau ta bar gidan.

Gidan Yusra ta soma zuwa, tunda babu nisa da su, babu ƙarya gidan ta ya haɗu matuƙa, babba ne sosai tunda mijin ta yana da kuɗi sosai, Costume ne shi, ya taɓa aure kuma sun rabu da matar tuni, har ɗiya yana da ita, sai dai tana wajen Mahaifiyar sa ne

Horn tayi, me gadi ya leƙo, sai da ya zo wajen ta tayi masa bayanin kanta, kafin ya buɗe mata ta shiga ciki, tana yin parcking ta fito tayi cikin gidan

Tun daga haraban gidan komi ya burge Ɗahira, da ace ita baƙauyiya ce, ko ba su da shi a gidan su, da har zilalan yawu sai tayi lokacin da ta shiga parlour’n Yusra, sai dai kasancewar ta wayayyiya kuma masu shi, shiyasa sama-sama tayi ma komi kallo, a ranta kuma sosai komi ya bata sha’awa, tana ganin Yusra ta more da komi, domin tayi Sa’an muhalli.

Fitowar wata babbar mace da kaya haɗin gambiza a jikin ta, ya tabbatar wa da Ɗahira ƴar aiki ce, a ranta tace, “su Yusra uwar son jiki! Har an soma ajiye ƴar aiki”.

Matar iso wa wajen ta tayi, ta zuƙuna har ƙasa ta soma gaishe ta

Saurin yalwata fuskar ta da fara’a Ɗahira tayi, tace da ita, “don Allah Mama ki tashi, Ni Yakamata in gaishe ki ai ba ke ba”.

Murmushi matar tayi tace, “ai babu damuwa ɗiyar albarka, idan na gaishe ki ma girman ki ne, don daga gani ke ƴar uwan matar gidan ce, kinga kuwa be kamata naƙi gaishe ki ba”.

Itama Ɗahiran murmushi tayi tace, “amma ai kin girme Ni Mama, don Allah kar ki sake zuƙuna min kinji? Ki ɗauke Ni tamkar ɗiyar ki”.

“To babu damuwa, insha Allahu. bari in Kira miki Hajiyan”. Matar tafaɗa da fara’a, a ranta sosai taji ƙaunar Ɗahira sabida mutunta ta da tayi, har tana jin da ita ce Uwar gidan nata.

Har tayi nisa kuma ta juyo ta tambayi Ɗahiran “wa zata ce mata ta zo?”

Ɗahira ta sanar mata da sunan ta

Ita kuma ta juya ta shiga ciki.

Kamar shuɗewar mintuna biyar sai ga ta ta dawo, tace mata “ga ta nan zuwa”

“To Mama na gode”. Ɗahira tafaɗa tana murmushi

Itama murmushin tayi tace, “babu damuwa ɗiyar albarka”.

Daga nan juya wa tayi taje ta kawo mata Drinks kamar yanda ta saba tarban baƙi idan sun zo, sai dai na Ɗahira har da abinci ta sawo mata, tunda tana ganin ita ɗin ƴar uwanta ce, be kamata ta tarbe ta da Drinks kaɗai ba, kuma abincin na Mijin ne tayi masa cus-cus, tunda shi ya fi so kuma yace ayi masa. To ta ga bata rigada ta sauke sauran abincin ba, shiyasa ta ɗibo mata nashi.

Matan tana barin wajen, sai ga Sulaiman ɗin ya fito, da fara’an sa ya zauna suka gaisa da Ɗahira, har yana tsokanar ta da “sai yau za su ga idon ta, gaba ɗaya ita tayi wuyan gani, dole sai an cike Form me tsada ake iya ganin ta, da biki ma ko ganin ta be yi ba”

Ɗahira na murmushi tace dashi, “Allah Sarki Yaya Sulaiman, wlh ciwo nayi shiyasa kwata-kwata ban fita waje ba, kayi haƙuri”.

“Eyya Sorry! But ban ji labari ba ko kaɗan wlh, domin dai Yusra bata sanar min ba, ai da mun shiga mun gaishe ki, Allah ya ƙara lafiya, yasa kaffaran zunubai ne”.

“Amin Amin Yaya Sulaiman, na gode sosai”.

Murmushi yayi yace, “ki dena godiya Auntyn mu, mun rigada mun zama ɗaya Yanzu”.

Murmushi kaɗai tayi ita dai

Yace, “sai fa kin yi haƙuri da wannan ƙanwar taki, tana shirya wa ne amma yanzu zata fito”.

“A’a babu komi wlh”.

“To bari in ɗan fita waje, zan haɗu da Maƙoci na ne, idan ta fito ki ce mata yanzu zan dawo”.

Amsa mishi tayi cikin murmushin da ya zame mata jiki

Shi kuma ya tashi ya fice a Parlour’n

Ajiyan zuciya Ɗahira ta sauke, tana ɗauke kai daga hanyar da yabi, sai kuma ta kalli Centre table ɗin da me aiki ta shirya mata abinci da drinks, hannu ta sanya ta ɗauki Robbern fanta, ta buɗe ta tsiyaya a glass cup ta soma sha. Abu kamar wasa har tsawon mintuna 15 suka shuɗe babu Yusra babu dalilin ta, don haka ta zuba cus-cus ɗin ta soma ci, kasancewar sosai take jin yunwa

Tana cikin ci ne, sai Yusra ta fito cikin takun ta ɗai-ɗai tana faman taunan cwhingum

Da kallo Ɗahira tabi ta dashi tana mamakin ganin ta da Shimi da dogon wando, babu alamun dai shirya wa ne ya tsayar da ita, koda yake da ta tuna ba shiri suke yi ba, tasan komi zata iya mata, don haka ta tsayar da cin abincin da take yi tana kallon ta fuskar ta cike da fara’a, ganin yanda tayi mugun sauya mata, tamkar dai ba satin su biyu ne da aure ba, tabbas aure ni’ima ce, Allah yasa mu dace.

Yusra dai tunda ta ƙariso wajen taga abincin da Ɗahira ke ci, sai ta sake ɗaure fuskar ta tamau fiye da yanda ta ɗaure, tana faman fiffizge kai tana taunan cwhengum ɗin ta har da su ƙas-ƙas-ƙas

Ɗahira ita ta soma mata magana, tare da gaishe ta cikin fara’a

Sai da ta zauna ta gama yamutsa fuskar ta kafin tace, “Lafiya. Dama ke ce?”

Murmushi Ɗahira tayi tace, “eh”.

“Yayi to”. Tafaɗa tana sake taɓe baki

Shiru ne ya biyo bayan maganar ta, don ita kanta Ɗahira bata san me zata ce ba, domin kawai yanda ta amshe ta ɗin, sai jikin ta duk yayi sanyi, tamkar ma ta ƙaro wulaƙanci ne, ga shi sai mata kallon banza take yi kamar dai ta ga kashi..

Numfashi taja sabida maganar Yusran da ya dawo da ita hayyacin ta

“Wai Husband ne yasa a kawo miki abincin nan?”

Shiru Ɗahira tayi tana kallon ta, don bata san me zata ce mata ba, tunda bata gane ma manufar ta ba

Guntun tsaki Yusran taja tana ɗaga murya ta soma kiran matar nan, “Marka.. Marka”.

“Na’am yallaɓiya, gani”. Cewar matar da ta fito da gudun ta

“Wa ya baki damar zuba mata abincin Husband?”

Shiru matar tayi tana zazzare ido, ta kalli Ɗahira ta kalli Yusran

Sai da ta daka mata tsawa da faɗin, “ba dake nake yi ba?”

“Kiyi haƙuri Ranki ya daɗe! Gani nayi ƴar uwan ki ce, shiyasa na zuba mata tunda yanzu na ɗaura sanwa, kuma zata…”

“Dalla rufe min baki”. Ta katse ta da faɗar haka

Jiki a sanyaye matar tayi shiru tana sad da kanta ƙasa, zuciyar ta cike fal da mamakin uwar ɗakin nata

“Wlh duk sanda kika sake ɗaukar abincin Miji na kika ba ma wata, a mean ba ita ba ko waye ma, wlh ranki sai ya ɓaci! baza ki sake zamar min a gida ba, ba na haɗa Miji na da ko wani tarkace kina ji ko?” Tayi maganar cikin isa da gadara

“Eh naji ranki ya daɗe! amma wai da naga ita ɗin…”

“Shut up I say”.

Gum Matar tayi jikin ta na rawa, sabida sosai tsawar ta ya shige ta

“Ki kwashe ki mayar min dashi kichen, idan kin girka wancan sai ki zubo mata”.

“To”. Matar ta amsa da sauri tana nufan Centre table ɗin, ta ɗauki Plate ɗin kacokan ta wuce kichen, zuciyar ta gaba ɗaya babu daɗi, sosai taji tausayin Ɗahira har tana sake waigo wa ta kalle ta da zata shiga kichen ɗin

Ɗahira na zaune dai tana kallon ikon Allah, har a ranta sosai da sosai abinda Yusra tayi mata ya bata mamaki da tsoro, “shin wani irin tsana ce take mata da har zata yi mummunan wulaƙanta ta haka? Tana a matsayin ƴar uwan ta?”. Sosai ta danne ɓacin ranta da komi, cikin juriya ta ƙirƙiro murmushi kafin tace, “Allah ya huci zuciyar ki! wlh nima bansan abincin Mijin ki bane, da ban ci ba”. Sai ta miƙe kafin taci gaba da faɗin, “Ni zan tafi, su Umma da Mama suna gaishe ki”. Ta ƙare maganar da yin gaba ta nufi ƙofar fita

Taɓe baki Yusra tayi tana faman kaɗa ƙafa, a fili ta furta, “dama ba gayyar ki nake yi ba”.

Ɗahira na fita ta saka hannu ta share hawayen da suka zubo mata a fuska, ta saki wani irin numfashi tana jan majina, lumshe idanu tayi tana haɗiyar wani abu da ya tsaya mata a maƙoshi

“Lafiya Ɗahira? Why are you crying?” Cewar Sulaiman dake tsaye gaban ta ba tare da ta san da zuwan shi ba.
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR’S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER’S ASSO*📖
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

\𝗙.𝗪.𝗔📚/

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA’S FAMILY*_

*HADHISI*
_An karbo dga Aisha Allah ya ƙara yarda agareta tace ” Manzon Allah s.a.w ya aureta tana da shekara shidda,kuma yatare da ita tana da shekara Tara,kuma Allah ya karbi ransa tana er shekara sha takwas. Muslim ya ruwaito_

.

*EPISODE Thirty Two*

Ɗago kanta tayi tana kallon sa, sai tayi saurin ƙirƙirar murmushi tace, “No, I’m not crying, abu ne ya faɗa min a ido shiyasa”.

Duk da be yarda ba, sai yace, “Eyya sorry! Amma dai ba tafiya zaki yi ba?”

“I’m going Yaya Sulaiman, har da gidan Shakira zan je, and Mama says” I’ll be back soon “.

“To babu damuwa, ki gaida mutanen gidan don Allah”.

“Insha Allah, they will”.

Hannu yasa cikin aljihu ya fito da kuɗi yana faɗin, “amma shi ne Yusran bata zo ta taka miki ba?”

Bata ce mishi komi ba, tunda bata san me zata ce mishi ba

Sai ya miƙa mata kuɗin har 20k Yana faɗin, “ga shi babu yawa kiyi haƙuri”.

Girgiza kanta tayi tace, “a’a wlh bazan amsa ba, ka bar shi Yaya Sulaiman”. Tana faɗan hakan ta wuce sa ta bar wurin

Da kallo ya bi ta da shi har ta kai wajen motan ta, kafin yaja numfashi yana mayar da kuɗin cikin aljihun sa, ƙofan ya buɗe ya shiga ciki da sallama

Yusra dake zaune har yanzu a inda take, tana faman karkaɗa ƙafafu tana latsa waya, ɗago wa tayi tana amsa sallaman nasa idanun ta a kansa

Shi kuwa a kan Centre table ɗin ya sauke idanun sa, zuciyar sa sosai take ɗarsa masa tabbas Yusra ce tayi wa Ɗahira wani abun, domin ya san cewa Yusra ba ta shiri da ita, tunda sau nawa take faɗar magana a kanta, kuma sannan ba ta son ko kaɗan yayi maganar ta a waje, idan yayi kuma ta dinga kushe ta kenan

Kallon ta yayi yace, “meyasaka Ɗahira ta tafi tun yanzu?”

Taɓe baki tayi tace, “can ta matse mata nima ban sani ba”.

Waro ido yayi kanta yana sake gasgata abinda ke ransa, sai kuma ya juya yana kwaɗa wa me aikin nasu kira. Tana fitowa ya tambaye ta “ina abincin nan da na ga Ɗahira tana ci? Yanzun nan daga fitan ta har kin kawar da Plate ɗin?”

Jiki na rawa matar tace, “wlh ranka ya daɗe! Uwar ɗaki na ce ta sanya Ni na ɗauka na mayar tunda abincin ka ne”.

“Kina nufin tana zaune a nan ta saka ki kika ɗauke?”

Jiki a sanyaye ta duƙar da kanta ƙasa saboda uwar hararan da Yusra ta banka mata, ta amsa mishi da “eh. Amma a gafarce Ni yallaɓoi, ba laifi na ba..”

“Je ki abun ki Baaba”.

Da sauri ta wuce ta koma kichen

Sai ya mayar da idanun sa kan Yusra dake ci gaba da karkaɗa ƙafafun ta, tamkar ma bata damu da abinda yake tambaya a kai ba, yace da ita, “Yusra wai Ni shin in tambaye ki? Ɗahira ba ƴar uwan ki bace?”

Ɗago kai tayi tana kallon sa, sai ta turo baki ta soma magana

Ya katse ta da faɗin, “amsa nake so”.

“Ƴar uwata ce mana”.

“Ok ƴar uwan taki ce ta zo gidan nan, kika wulaƙanta ta ko? Shin kin san kuwa abinda kike yi? Da kuka fa ta bar gidan nan”.

Shiru tayi masa

Cike da ɓacin rai yace, “yayi miki kyau! ki ci gaba da abinda kike yi, Ni babu abinda ya shafe Ni, amma ki sani ranan da zaki yi nadama na nan zuwa”. Yana gama faɗar maganan nasa yayi cikin ɗaki da sauri

Tsaki taja kafin ta miƙe tabi bayan sa.

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

Murza sitiyarin ɗin motan take yi zuciyarta na ƙuna, sosai take jin ƙunci da abinda Yusra tayi mata, numfashi kawai take sauke wa duk socond baƙin ciki na ƙara wanzuwa a zuciyar ta, nan da nan kanta ya soma mata ciwo sabida damuwa da tuno abinda tayi mata ya haifar mata, sosai take dana-sanin rashin amayar mata da ƙuncin da ta saka mata, sabida ta san ita zai cuta, amma kuma ta ga ita ta kawo kanta shiyasa be kamata ta biye mata har wani saɓani ya shiga tsakanin su ba, but she promised she would never see her again in her home.

Ta so koma wa gida, sai kuma ta ga be dace taƙi zuwa gidan Shakira ba, can ta wuce duk da bata san gidan ba, sabida kwatancen akwai wahala sosai in dai ba ka taɓa zuwa bane, dole ta kira Baffa ya sake mata kwatancen gidan kafin ta gane

Itama gidan nata babu laifi tunda ita kaɗai ce, amma kuma na Yusra yafi girma da haɗuwa, mijin ta Sahabi aiki yake yi a Companin wutar lantarki.

Sanda ta shiga gidan da sallama, Shakira na zaune a Parlour tana cin abinci tana kallo, ganin ta yasa ta tashi da fara’an ta ta rungume ta

Murmushi Ɗahira tayi, cikin sanyin murya tace, “ƴar uwa nayi missing ɗin ki sosai da sosai”.

Dariya Shakira tayi tace, “ai wlh baki kai Ni ba sister, tun sanda Hajja ta kira Ni tace kina nan zuwa na zauna a nan zaman jiran ki, meyasa ma kika fara zuwa wajen wancan mara mutuncin? Tunda kin san ba shiri kuke yi ba, Allah yasa dai ta amshe ki hannu bibbiyu bata miki wulaƙacin da ta saba ba, ba Ni nasha don Allah ya kuka kwashe?”. Ta ƙare maganar har da gyara zaman ta tana zuba wa Ɗahira idanu

Shiru Ɗahira tayi, nan maganar da Fadila ta faɗa mata ya faɗo mata, hakan yasa ta saki murmushin yaƙe tace, “ke dai Shakira, daga zuwa baza ki bari na huta ba sai ki soma min gulman wata?”.

Hannun ta ta watsa saman cinyoyin ta tana faɗin, “ai wlh ke dai bari Sister, na damu dake ne wlh, domin nasan halin Yusra yanda ta tsane ki, ruwan gidan ta ma baza ta bari ki sha ba”.

“Uhm to babu abinda ya faru tsakanin mu, ta amshe Ni hannu bibbiyu, har abinci na ci”.

Ƙure ta da ido Shakiran tayi, sai ta taɓe baki kamar dai ba haka ta so ba, tace, “na ji ki amma dai ban yarda ba, domin wlh ina ji a jiki na akwai abinda ya faru a gidan ta, uhm Ni zan faɗa miki wace ce Yusra a kan tsanar da tayi miki”.

“Ya isa don Allah, Ni dai ba na son zancen nan, wlh kai na ciwo yake yi, daƙyar ma na ƙariso”. Ɗahira ta ƙare maganar da dafe kanta, sosai take takaicin wannan sabon halin da ta gano na Shakira, “meyasa ma tun farko ta kasa gane ita ɗin me fuska biyu ne? Yanzu da ba don Fadila ta faɗa mata halin ta ba, haka zata zauna tana bugan ruwan cikin ta, tana nuna tamkar ta damu da ita, amma kuma a baɗini ba haka bane, Allah ya kyauta ya ƙara nuna mana maƙiyar mu a fili..

Maganar Shakiran ne ya dawo da ita guntun tunanin da ta afka

“Bari in sawo miki abinci ki ci”.

Har ta miƙe Ɗahira tace da ita, “bar shi kawai, Ni bazan iya cin komai ba”.

“Kenan dai da gaske ne Yusran ta cika miki ciki da abinci?” Shakiran ta faɗa cikin dariya, sai dai a zuciya baƙin ciki ne tamkar ya karta

Murmushi Ɗahira tayi tace, “ina mijin naki mu gaisa tunda rowan sa kike min?”.

Dariyan ta sake kwashe wa dashi tana faɗin, “wlh kuma kin yi rashin Sa’a ne, domin yanzu ya fita, shaf kuma na manta ban ce masa ya tsaya zaki zo ba, sai ku gaisa”.

“Haka kawai ki tsayar da shi don zan zo? A’a gwara ma da baki yi ba, wataran zamu haɗu ai, nima ba daɗe wa zan yi ba yanzu zan tafi”.

Hararan ta Shakira tayi tana miƙe wa tace, “kan bu..! Wlh babu inda zaki je yanzu, daga zuwan ki? Ki bari zuwa anjima don Allah”. Ta ƙare maganar sanda ta isa gaban Fridge ɗin ta, drinks ta ɗauko mata, ta haɗo da Cup ta kawo gaban ta ta ajiye akan Centre table da ta janyo, tsiyaya mata tayi ta miƙa mata

Ɗahira bata yi musu ba, ta amsa ta soma sha

Ita kuma ta koma ta zauna tana ce mata, “ɗazu muka yi waya da Fadila ai, take tambaya na baki zo ba har yanzu? Shi ne nace mata ai yau Hajja ta kira Ni ta sanar min zuwan naki”.

Murmushi kaɗai Ɗahira tayi tana ci gaba da sipping Juice ɗin ta, a ranta jin ta kawai take yi, kuma ta san manufar ta, shiyasa ma ko magana ba ta son Yi, Allah-Allah take yi ta bar gidan ma, sabida gaba ɗaya haushin Shakiran take ji, ga kanta dake faman sara mata zuciyar ta duk babu daɗi, duk surutun da Shakiran take mata ba ta tanka ta, har dai ta gaji itama ta dena, sai suka koma zugun suna kallo

Nan Ɗahira ta tashi tace mata “zata tafi,” har waje ta rako ta tana bata saƙon gaisuwa wajen mutanen gida. Motan ta na fita ta koma cikin gida da sauri ta wawuri waya don kiran YUSRA.

⚫⚫⚫

Sanda Ɗahira ta isa gida, tana shiga parlour’n su ta tarar da Aunty Zulaiha da Fadil zaune, da fara’an ta ta isa kusa da ita tana faɗin, “laa Aunty kin zo ne?”

Itama cikin fara’an tace da ita, “wlh kuwa, ina zuwa ai Aunty Amarya tace min kin fita zuwa gidan su Shakira da na tambaye ta”

“Wlh kuwa Aunty, Ina Ilham ɗin?”

“Tana wajen Kaka, kinga wanda ya kaita nan ya bar ta can”.

Kallon Fadil tayi tace, “To je ka ɗauko min ita”.

“Kai Aunty Ɗahira ki bari mana zuwa anjima in ɗauko ta, yanzu fa kika dawo”.

Hararan sa tayi sai dai bata ce komi ba, ta tashi tsaye tana faɗin, “Aunty bari in rage kayan jikina sai in zo dai muyi hira, bari in shiga ɗakin Mama”.

Tun kafin ma ta ƙarisa Fadil yace mata, “tana kichen ai”.

Kichen ɗin ta wuce, ta sanar mata ta dawo, ita kuma tayi mata sannu da zuwa, sanann ta wuce ɗakin su ta sauya kaya zuwa jan doguwar riga me taushi mara nauyi, sannan ta sake fitowa, nan ta zauna sukai ta zuba hira da Aunty Zulaiha

Itama Aunty Amarya da ta fito zama tayi tana taya su hiran, lokaci bayan lokaci tana zuwa dubo girkin ta

Tashi Ɗahira tayi tace, “bari dai in je ɗauko ta tunda yaron nan ba zuwa zai yi ba”. Ta ƙare maganar da dungure wa Fadil kai

Turo baki yayi yana cewa, “Kai Aunty! Kai Aunty! Ki bari to yanzu zan je ɗauko ta”.

“A’a ba na so bar shi, ai ina da ƙafa ko?”.

Aunty Zulaiha na musu dariya tace, “ai nima yanzu zan yi haraman tafiya, dama duba ƙanwar Baban Ilham ɗin ya kawo Ni, to shi ne na biyo gida”.

“Eyya kina nufin Maman Sumayya?” Cewar Ɗahiran tana kallon ta

“Wlh ita fa, har a asibiti an kwantar da ita, ai asibitin mu ne ma aka kwantar da ita, baki sani ba ashe?”

“Wlh kuwa ban da labari, wani ciwo take yi?”

“Ciwon ƙoda ne take fama dashi, amma yanzu an sallame ta ai”.

“Allah Sarki! Allah ya bata lafiya yasa kaffara ne”.

“Amen amen”. Daga Aunty Zulaiha har Aunty Amarya da ta fito daga kishen yanzu suka amsa.

Ɗahira fita tayi ta wuce Part ɗin Kaka, inda ta same shi a ɗakin sa yana Sallah, Ilham kuma na wasa a ƙasa da kayan wasan da Kaka ya zube mata, dayake ba ya rasa kayan wasa a wajen sa, sabida ita da Jinior ɗan wajen Aunty Zainab, duk idan sun zo suna kawo masa su, sai ya zube musu kayan wasan saboda kar su riƙa masa kuka.

Ɗaukan ta tayi, ta hau mata wasa tana shilla ta tare da mata rawa

Lokacin da Kaka ya idar ya kalle ta yana murmushi yace, “dayake ai akwai me gadon zinare waje na, ga shi kin biyo ta”. (sunan Umma Ilham ɗin taci, Bilkisu, kuma sunan Mahaifiyar Kaka ne dama Umma taci)

Dariya Ɗahira tayi tana tashi daga kan kujeran ta dawo gefen gadon sa, tunda dama gadon ya fi kusa da wheel chair ɗin sa, tace dashi, “kai Kaka.. dama ai ina zuwa duba ka, kwana biyu ne kawai ban samu na shigo ba, amma yanzu ɗin ma ai sabida kai na zo”.

Murmushi yayi yace, “naga alama ai”.

Dariya ta sake yi tana cewa, “baka yarda ba ko?”

“Na yarda Matata, to ya ƙarfin jikin?”

“Alhmadulillah Kaka, ai yanzu na samu lafiya har na kere ka ma”.

“Ah Masha Allah Abu yayi kyau, fata na kenan dama Matata ta fi ni lafiya”. Ya faɗa yana dariya

Itama tana taya sa

Lokacin ne Aunty Zulaiha ta shigo tana faɗin, “Mata da Miji sun haɗu waje ɗaya, hira ba ya ƙare wa, to na zo ɗaukar ɗiya ta zan wuce”.

“Kai Aunty yanzu fa na zo”. Cewar Ɗahira tana ɓata fuska

Shi kuma Kaka yace, “Ja’ira ko kunya ta ma ba kya ji kin zo ɗaukar ɗiyar ki ko?”

Dariya ta kwashe dashi tana cewa, “Kaka wani kunyan ka zan ji? Tafiya fa zan yi, amma idan kana so in bar maka ita, ai Ni abu me sauƙi ne a waje na, wlh sai in tafi in bar maka, gaba ta kai Ni wai gobaran titi a Jos”.

“To ban ce ba, ɗauki ɗiyar ki ki tafi, me zan yi da wannan mummunan ɗiyar taki?”.

Dariya suka saka gaba ɗaya, ganin yanda Kaka ya taƙume fuskar sa yana kallon Ilham kamar ya ga kashi

Aunty Zulaiha tace, “ai Kaka kai ta biyo wlh, kaima ka sani, kar ka wani tsine ta. Kuma Maman ka ce babu ruwana”.

Taɓe baki yayi yace, “jaaa can da Allah! Ki ɗauki ƴar ki ki wuce kin ji, duk kin cika min kunne da surutu”.

“Shikenan Kaka, kora ta kake yi ko? Babu damuwa ai, dani kake zancen wlh”. Cewar Aunty Zulaihan tana ƙarisa wa ta ɗauki Ilham tana saɓa ta a baya

Dama sun saba irin haka sosai, kusan a jikokin gidan, Kaka da Aunty Zulaiha sun fi wasan jika da Kaka, idan suka haɗu waje ɗaya bakin ɗayan su ba ya shiru.

Tashi Ɗahira tayi, tace wa Kakan “zata je ta raka ta”. Sannan suka fice tare.

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

*WASHE GARI*
*12:30pm.*

Shigowar motan Usman ɗin cikin asibitin, yasa Ayush buɗe motan Safra tana leƙa wa, sai kuma ta juyo ga Safran dake latsa waya tace da ita, “Ga shinan ya shigo”.

Ɗago kai Safra tayi, tana bin waje da kallo tana faɗin, “ina yake?”

“Wannan motan”. Ayush ta nuna mata motan Usman da ya ƙariso kusa da na su ya tsaya

Da ido Safra tabi motan da kallo, shi kansa motan ba ƙaramin burge ta yayi ba, bare kuma sanda tayi tozali da mamallakin Motan, hohoho ai da sauri ta buɗe motan ta fito tana sake ƙare masa kallo

Itama Ayush fitowan tayi tana bin sa da kallo tamkar zata cinye sa, a duk socond ɗaya ƙaunar sa na ƙara ruruwa a zuciyar ta, sosai yayi mata kyau tare da ƙara mata kwarjini fiye da kullum, yana sanye cikin ƙananan kaya ne, wanda koda yaushe shigan da ya saba yi kenan, sai ƙyalli yake yi, kai da gani kasan hutu da jin daɗi ya zauna masa, kuma duk wanda ya kalle sa ya san cewa ba ƙaramin haɗaɗɗen Guy bane, sosai yake da son gayu fiye da tunanin mutum, shiyasa yake fita daban duk inda ya shiga, yana zama tamkar wani tauraro me haska waje, bare shi Fari ne, ga kyawu na ban mamaki.

Duk abun nan be ma san suna yi ba, tafiyan sa kawai yake yi ya shige cikin Hospital ɗin, fuskar sa kamar dai yanda take babu fara’a, illa kwarjini da take dashi, wanda idan ka kalle sa dole ne fuskar tasa ta burge ka, duk da kuwa babu ko ɗigon annuri, amma kwarjinin sa shi yake ƙara masa kyau.

“Gaskiya Ayush dole ne ki haukace saboda wannan Guy ɗin, Ni kaina ba ƙaramin tafiya da imani na yayi ba a kallon farko duk da Maza ba sa burge Ni, bare ke da kika saba ganin sa kullum”. Cewar Safra tana kallon Ayush ɗin

Numfashi Ayush taja, kafin tace, “hmm yanzu kin yarda da Ni Ko?”

“Ƙwarai kuwa.. shiga mota mu je, ina da hanyar da za mu ɓullo masa, idan ya san wata ai be san wata ba, na saba haɗuwa da irin waɗannan guy ɗin masu murɗaɗɗen hali, kuma mun ci galaba a kansu”. Ta yi maganar tana taunan cwhengum

Murmushi Ayush tayi, kafin suka koma cikin motan, Safra taja suka bar Hospital ɗin.

 

.

 

_Ko Me Za su shirya? 🤔 Muna dai biye da su ai._
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR’S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER’S ASSO*📖
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA’S FAMILY*_

*NASIHA*
_Muna iya lura cewa ga al’ada in an Kira talaka zuwa fadar sarki yakan gyara fuska, ya yi ado don ya sami kyakkyawar maraba daga Sarki. To, in haka ne, ina ga in ya tashi zuwa tsayuwa gaban Ubangijin sa? Bawan da aka neme shi ya zo gaban Ubangiji, Sarkin sarakuna, mamallakin mamallaka, lalle kam ya fi kamata ya gyara kansa saboda wannan muhimmin muƙami. Ya kamata ya gyara kansa ta tsarkake tufafin sa da jikin sa, ya fito cikin kama mafi kyawu, kamar dai yadda aka umurci musulmi duka a cikin suratul A’ARAF, aya ta 31:_
_”ya ɗiyan Adam! Ku riƙi ƙawar ku a wurin ko wane masallaci”_
_Allah yasa mu dace._

.

*EPISODE Thirty Three*

“Kina da kuɗi a tare da ke? Domin kai tsaye wajen Malami na za mu wuce”.

Kallon ta Ayush tayi, sai kuma ta girgiza mata kai alamun “A’a” kafin tace, “Malami kuma Safra? Wanne irin Malami? Me kuma zamu yi a can?”

Dariya tayi still tana taunan cwhengum ɗin ta tace, “neman biyan buƙata mana Ƙawata, Ai dole sai da haka, don wlh bari kiji, irin waɗannan Guy ɗin ba naki bane, kee wlh bazan yi kaffara ba, idan har kika ce ta haka zaki jawo hankalin sa, babu taimakon Malamai, to, zaki dauwama baki yi aure ba, domin wlh sai kin ruɓe a gidan ku. Yanzu dai za mu wuce wajen Malam, inyaso zan ranta miki kuɗi idan muka dawo ki bani”.

Ayush dai ta kasa cewa komi illa kallon titi da take yi, tana me tunani a zuciyar ta, “anya wannan hanyar da ta ɓullo wa kanta me ɓulle wa ne? Domin tasha jin yanda mutanen da suke zuwa wurin boka suke ƙare wa, to amma dogon burin ta fa? Hakan na nufin muddin bata nemi taimako wajen su ba, to, har abada baza ta taɓa auren Usman ba?..”.

Kai tsaye hanyar Zaria suka nufa, sun kusa shiga Zarian, sai suka karya kwana suka bi wata hanya, tafiya miƙaƙƙa suka yi a cikin hanyar me kama da jeji, domin ko kaɗan babu gida gaba bare baya. Sun yi tafiya sosai kafin suka soma hango ƙauyaku, inda suka sauka a wani ƙaramin gida da aka zagaye shi da kara, sai bukka da aka yi su da yawa a wajen, shiga suka yi gidan, inda Ayush sai kalle-kalle take yi tana biye da Safra dake tafiyan ta kai tsaye, ba tare da wata fargaba ba, ga duk kan alamu ta saba da zuwa

A bakin wani bukka dogo suka dakata, inda Safra ta hau faɗin, “an gaishe ka Malam, an gaishe ka Malam”.

Daga ciki dariya ne ya biyo baya, inda yace, “Hajjaju Safra da baƙuwar ta, maraba da zuwa, za ku iya shigo wa”.

Shiga Safra tayi, inda Ayush ke biye da ita

Yana da faɗi cikin bukkan, babban mutum ne fari sol yake zaune a gaban wani ƙaton ƙwarya baƙi, yana ɗaure da zanin atamfa a jikin sa yayi tamkar yanda ƴan Saudiya suke yi idan za su yi aikin hajji, sai gashin kansa me yawan gaske tamkar na mace, ya zubo masa har kafaɗun shi

Da kallo ya bi su dashi har suka zauna, kafin yace, “an sanar min da zuwan ku tun kuna hanya, kuma na san abinda ya kawo ku”.

Ayush ce kawai tayi mamaki da kalaman sa, ban da Safra da ba yau ta soma zuwa ba

Kallon Ayush ɗin yayi yana faɗin, “yanzu me kike so ayi masa?”

Kallon Safra tayi, itama kuma ta gyaɗa mata kai alamun “ta sanar masa”

“Malam ina ƙaunar sa matuƙa, kuma so nake yi a saka mishi ƙauna ta yaji duk duniya babu wanda yake so face Ni, ina son ya zo min da buƙatar auren sa”.

Tsare ta da ido yayi tamkar be san me take cewa ba

Sai ta kalli Safra a tsorace, sabida ba ƙaramin tsoro jajayen idanun sa suke bata ba, musamman da ya ƙure ta da su tamkar zai cinye ta

Hannun ta Safra ta kama tana son kwantar mata da hankali

Muryan sa suka ji yana cewa, “kee yarinya! Idan har aka zo nan ba a shigo min da tsoro, tun wuri ki dena jin tsoro na, idan ba haka ba, to zan saka miki wasi-wasi a zuciya, kuma duk abinda zan miki baza ki taɓa ganin dai-dai ba”.

Da sauri Ayush ta gyara zaman ta tana cewa, “kayi haƙuri, bazan sake ba”.

“Da yafi miki”. Ya faɗa yana taɓa hannun sa a cikin ruwan dake gaban sa cikin ƙwarya, zane ya soma yi na ɗan mintoci, kafin ya ɗago yana kallon ta yace, “leƙo nan”.

Matso wa tayi ta tura kanta ta yanda zata ga cikin ƙwaryan, Usman ta gani zaune a Office ɗin sa, yana shingiɗe a kan kujera idanun sa a rufe, kujeran na faman juya sa

“Wannan shi ne ko?”

Da sauri ta gyaɗa masa kai tana faɗin, “eh shi ne Malam”.

Ci gaba yayi da zanen sa na ɗan wani lokaci, kafin ya ɗago yana duban su yace, “kina da rabon auren sa, sai dai a nan gaba, domin na ga gagarumar matsala tana kunno wa daga dangin sa, suna shirin aura masa ƴar uwan sa nan ba da jima wa ba. Kuma na duba duk yanda za’a yi, babu ta yanda za’a hana auren nan, dole ne sai ya aure ta”.

“Malam kana nufin dai sai ya auri wata kafin ya aure ta?”

“Eh haka nake nufi”.

“Amma meye mafita Malam?”. Safra ta sake tambayar sa

Numfashi yaja kafin yace, “wannan yarinyan ƙaddaran sa ce, kuma dole ne sai ya aure ta babu yanda za’a yi, bazan iya muku aiki ba yanzu har sai sanda aka yi auren nasu, sannan ku dawo akwai abin yi, a nan ne nake da daman raba su ke kuma ki shiga, in har ba haka ba kuwa, babu ta yanda zaki aure sa tana cikin gidan sa”. Ya ƙare maganar da nuna Ayush da duk ta gama firgita da jin abinda yake faɗa

“Yanzu Malam babu abinda zaka iya yi a kai? Ya kamata kayi wani abun, domin mun san zaka iya ne”.

Cikin amon muryan sa yace, “babu abinda zan iya a kai yanzu, duk abinda kuke so ku dawo bayan auren su, a nan ne zan iya muku komi, ku tashi ku tafi”.

Da sauri suka tashi sabida jin tsawan da ya danƙara musu, suka fice suka nufi motan su, hawa suka yi suka bar wajen, babu me magana cikin su har sanda suka fito bakin titi

Da damuwa a fuskar ta tsantsa Ayush tace, “yanzu ya za mu yi? Ga shi mun zo wajen Malamin, memakon samun mafita, sai faɗa min abinda ya ɗaga min hankali yayi, kuma ya ƙi mana aikin”.

Numfashi Safra taja kafin tace, “ke a naki tunanin, wace ce yarinyan da kike ganin za’a haɗa su aure?”

“No bazan taɓa sanin hakan ba gaskiya, domin Familyn su babba ne, kinga babu ta yanda zan yi in gane wacce zai aura, kuma kwanan nan duk ƙannin sa suka yi aure na cikin gidan su, illa mutum ɗaya ce wacce yanzu tana gida bata yi aure ba, ban san kuma meyasa ba”.

Murmushi Safra tayi tace, “tabbas ina ji a jiki na, ita ce za’a haɗa su aure, sai dai baza mu fara aiki a kan hakan ba, har sai mun tabbatar da maganar Malam, kar ki damu idan sun san wata basu san wata ba, tunda Malam ya gaza wannan aiki, uhmmm makircin mu shi ne zai yi aiki a nan”.

“I don’t understand?” Ayush asked looking at her

“I mean. duk ta hanyar da za mu bi don hana yiwuwar hakan za mu yi, domin cin ma burin mu, ke dai kawai ki tabbatar kin samo yarinyan ko wace ce, a nan ne zan tabbatar miki da shirin mu a gaba, inyaso sai mu koma ga Malam ya saka mishi ƙaunar ki a zuciya”.

 

 

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

*AFTER TWO WEEKS*

Gaba ɗaya ahalin gidan suna zaune a babban Parlourn gidan, yau har da Aunty Zulaiha da Aunty Zainab duk sun samu zuwa taron Familyn da suke gabatar wa a duk ƙarshen wata, haka ma Shakira da Yusra duk sun hallara, har Sa’adatu tana a cikin parlour’n, kasancewar itama yanzu ta zama ƴar gida

Abba ya soma buɗe taro da addu’a, inda Kaka ya bi su bayan ɗaya yana jin matsalolin su, tare da tambayar zaman nasu a gidajen mazajen su. sai da komi ya nitsa kafin ya kira sunan Usman

Usman dake zaune a gefen Baffa kan two seater, ya amsa mishi yana me ɗago kai ya kalle sa

“Ina muka kwana a zancen mu na auren ka?”

Dama ya san kwanan zancen, duk da an kwana biyu ba’a tayar da maganar ba, shiyasa ya sake ɗaure fuska, cike da isa yace, “har yanzu ban samu wacce tayi dai-dai da ra’ayi na ba Kaka, Ni a gani na gwara a dena zancen aure na yanzu, because I’m not ready to do it now.”

Big Dady ne yayi ninyan magana, sai Kaka ya katse masa hanzari da faɗin, “to shikenan, tunda baka shirya ba, ai mu mun shirya aurar da kai yanzu”. Sai ya juya ga Ɗahira yace, “What about the My wife? Are you still silent?”

Gyaɗa masa kai tayi kanta a ƙasa tana wasa da kwalliyan rigan ta

“To duk wani dama da Yakamata mu baku mun rigada mun baku, tunda har yanzu baku samo abokan zaman ku ba, mun yanke shawara Ni da iyayen ku, Kai Usman, da ke Ɗahira, za mu haɗa ku aure a tsakanin ku, ina fata dai…”

Zumbur Usman yayi ya miƙe yana dakatar da Kaka da faɗin, “haba Kaka! What are you saying? Dani da wa zaka haɗa aure?”

“Dan uban ka With you and your younger sister Ɗahira”. Cewar Big Dady yana tsare Usman ɗin da kallo

Huci Usman ɗin ya soma, kafin yace, “It is not possible at all. You must change your mind soon. I will never marry this girl.” Yana gama faɗa yayi hanya zai fice

Big Dady yace dashi, “Wlh if you go out, ranka zai ɓaci, come back and sit down, ka dawo nace ka zauna ko baka ji bane?”

Lumshe idanun sa yayi yana dakata wa daga inda yake, dunƙule hannun sa yayi yana faman huci, kafin kuma ya juya a zuciye ya dawo inda yake da zama ya koma ya zauna, gaba ɗaya fuskar sa ta haɗe tayi murtik, jira kawai yake yi ya amayar da abinda ke cikin sa.

Hannun ta da Kaka ya riƙo, shi ya dawo da ita hayyacin ta, ta ɗago kai tana kallon sa da idanun ta da suke zubar hawaye tun soma jin zancen Kaka

Hannun ta ya sake riƙe wa ƙam yana faɗin, “Nafeesa mene ne ya saka ki Kuka?”

Kasa magana tayi illa kallon sa da take yi, sai da taji saukar muryan Abbun ta ne kafin ta sake ƙifta ido tana mayar da idanun wajen sa, jin abinda yake cewa ya tabbatar mata ba mafarki take yi ba

“Sakarci ne irin nata, amma in ba sakarci ba meye na kuka a wannan maganar?” Ya ƙare maganar yana balla mata harara

Gaba ɗaya mutanen wajen, idan ka ɗauke Sa’adatu da tayi murnan jin zancen nan, sai kuma su Abba da su sun san da maganar, amma babu wanda haɗin nan yayi masa daɗi, musamman Hajja da take jin tamkar ta shaƙe Kaka da maganar ya fito daga bakin sa, baƙin cikin ta ma har ya fi na Hajiya da take uwar Usman ɗin

Ita kanta Aunty Amarya bata san meyasa ba, sam ta ji zuciyar ta ta karye da wannan haɗin, tana ji a ranta tabbas ɗiyar ta zata shiga wani hali a kan wannan auren, tamkar dai wani abu zai same ta, “shin sun manta da cewa Ɗahira da Usman ba sa shiri ne suke son haɗa su aure?” Tayi wa kanta tambayar a cikin ranta..

Muryan Big Dady ne duk ya dawo da kowa hayyacin sa, yace dasu, “mun tsayar da ranan auren nan da wata ɗaya me zuwa, don haka ban yarda ko inji ko in gani wani ya yi maganar akasin abinda muka faɗa ba, sai kowa ya soma shiri tun yanzu, za ku iya tafiya”.

Baffa ne ya riga kowa tashi ya bar parlour’n yana me riƙe da kansa

Da sauri Sa’adatu ta miƙe tabi bayan sa zuciyar ta fari karrr, ko ba komi tana gani an kawo mata ƙarshen matsalan ta

Ɗaya bayan ɗaya kowa ke tashi ya bar parlour’n, ban da Usman da Ɗahira da suke zaune tamkar an dasa su a wajen

Ganin haka yasa Aunty Amarya da zata wuce, ta nufi wajen ta ta ɗago ta, tare da riƙe mata hannu suka bar parlour’n

Shi kuwa Usman yana zaune ya haɗa kai da hannayen sa yana faman huci, gaba ɗaya idanun sa sun kaɗa sun yi jazur

Babu wanda ya kula shi a cikin su Abba, har sai da kowa ya watse, inda Abba ya gungura Kaka zuwa ɗakin sa, Big Dady na biye da su a baya yana amsa waya

While Abbu na zaune be tashi ba, sai da ya ga kowa ya bar parlour’n kafin ya miƙe ya iso gaban Usman, hannu ya saka ya dafa sa yana me kiran sunan sa

Ɗago jajayen idanun sa da har sun tara hawaye yayi, ya kai duban sa ga Abbu yana me taune haƙoran sa da ƙarfi, take jijiyoyin kansa suka fito raɗo-raɗo

Shi kansa Abbu jikin sa sai da yayi sanyi da yanayin da ya gansa, be iya ce masa komi ba illa kallon sa da yake yi

Hakan yasa Usman ya ɗauke idanun sa, yana miƙewa tsaye ya doshi ƙofa ya bar parlour’n

Da kallo Abbu ya bi shi da shi har ya fice, a ransa yana ayyana “shin wani irin tsana ne me ƙarfi da Usman yake yi wa ƴar sa? Anya baza su yi kuskure ba idan suka haɗa su Aure?” Babu me ba shi amsa, dole ya saki ajiyan zuciya ya juya ya nufi ɗakin Kaka ransa duk babu daɗi.

 

 

 

.

 

 

_too chakwakiya … now the game will start … Just follow me to hear how it will go … Don’t forget your comments it will make me more typing._
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR’S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER’S ASSO*📖
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA’S FAMILY*_

*TUNATARWA*
”’Manzon Allah ya ce mana, “tsabta kam ita ce rabin imani kuma ita ce mabuɗin Sallah. Abu na farko da ake buƙata kafin a shiga sallah shi ne tsarki, tsabta ta zuciya da jiki, ta tufafi da kuma wurin yin sallar.
Sallah ibada ce ta ruhu, kuma a cikin ta ne Bawa yake ganawa da Ubangijin sa, yake tsayawa a natse a gaban sa yana yabo yana godiya, yana roƙon Allah ya shiryar da shi bisa ga tafarki madaidaici. Saboda haka bai kamata Bawa ya shiga wannan ganawa ba sai bayan ya shirya kansa da kyau, ya tsarkake jikin sa da tufar sa da wurin sallar sa. Zai yi alwala in ƙaramin tsarki ya kama shi; in kuwa babban tsarki ne sai ya yi wanka don kuwa ta haka ne zai haɗa tsarkin jiki da na zuciya a lokacin ganawar sa da Ubangiji.
Allah yasa mu dace.”’

.

 

*EPISODE Thirty Four*

Direct Aunty Amarya ɗakin ta ta wuce da Ɗahira, suna shiga ta zaunar da ita kan kujera tana kiran sunan ta

Sai dai ga duk kan alamu Ɗahira tayi nisa a duniyar mu ba ta jin ta. Sai da ta saka hannu ta riƙo mata kai tana shafa mata fuska, kafin taja numfashi tana ware idanun ta da suka sauya launi a kan ta

Ita kanta Aunty Amarya ta tsorata da yanayin kallon da take mata, shiyasa tayi saurin cewa, “Ɗahira Are you all right?” Ta ƙare maganar tana ɗan ƙara girgiza ta

Sai kawai gani tayi ta ƙame alamun ta sume idanun ta a buɗe, sosai hankalin Aunty Amarya ya tashi, babu shiri ta hau girgiza ta tana hawaye cike da ruɗu, sai kuma ta miƙe zata yi waje, har ta kai bakin ƙofa ta sake dawowa tayi cikin Toilet, domin tana ganin be kamata a san halin da ɗiyar ta take ciki ba, musamman yanda ta san ba ita kaɗai bace a sashin, yanzu sai aje ana yamaɗiɗi da maganar kuma ta daban

Ruwa ta ɗibo ta zo ta shafa mata a fuska, sai da tayi haka sau uku kafin Ɗahira ta farka, sai dai tana buɗe ido tayi arba da fuskar mahaifiyar ta sai ta fashe da kuka, nan da nan Aunty Amarya ta sake ruɗe wa, tayi saurin ajiye Cup ɗin hannun ta a ƙasa tana tambayar ta “what’s going on?”

Cikin kuka Ɗahira tace, “Mama don girman Allah kiyi min rai! idan har ba mafarki nake yi ba, ki taimake Ni ki je ki cewa su Abbu ba na son Ya Usman, wlh Mama Mutuwa zan yi idan na aure sa, Mama ba ya ƙauna ta ko kaɗan, Ni ba na son sa wlh bazan iya auren sa ba, ki taimaka min Mama, ki ce musu kar su haɗa mu, sam-sam ba mu dace ba Mama”. Sosai take kuka har da majinu

Riƙe ta Aunty Amarya tayi cike da tsantsan tausayin ta, cikin sanyin murya tace, “I don’t know what to say to you Ɗahira, amma abinda zai fito daga baki na be wuce haƙuri zan baki ba, kiyi haƙuri ki ɗauki ƙaddaran ki, tunda iyayen ki sun rigada sun yanke wannan hukuncin; ki daure kiyi musu biyayya kinji?”

Girgiza kanta ta soma yi tana ci gaba da zubar da hawaye, tace, “Mama ko kin manta da waye za’a haɗa aure na? Aure fa za’a haɗa Ni dashi, Yaya Usman da ya tsane Ni tun ina tsumman goyo na, yanzu shi ne zan aura a matsayin miji na? Please Mom help me I can’t marry him, I like Yaya Baffa .. ”

 

Shigowar Abbu da sallaman sa, shi ya hana Aunty Amarya jin ƙarisan zancen nata, bare kuma dama tana kuka ne tana maganar, hakan yasa ba lallai ka fahimta ba. kallon sa kawai take yi bayan da ta amsa mishi sallaman nasa

Zuwa yayi ya zauna a kan hannun kujeran, inda suka saka Ɗahira a tsakiya dake faman kuka sosai, ta haɗa kanta da gwiwa tana ta rerewa, hannu yasa ya ɗago kanta yana kallon ta cike da tausayin ta yace, “Mama na, please stop crying. Stop kinji.. alfarma zan roƙa wajen ki, duk da na san ba kya son Usman, Amma Ina son ki amshi maganar nan hannu bibbiyu, kiyi mana biyayya kinji? Mu iyayen ki muka ga dacewan haɗa ku, abinda mun daɗe muna fatan haɗa zumunci, duk da bamu so mu yi wa ɗayan ku tilas ba, amma kuma ga shi mun aiwatar a kan ku, sakamakon rashin kawo naku zaɓin da baku yi ba, mu a ganin mu wannan haɗin da muka yi shi zai kawo daidaito a tsakanin ku, hakan ne ya ƙara bamu ƙwarin gwiwa, don Allah ɗiya ta ki daure ki amshi wannan haɗin da muka yi muku, ba na son ko kaɗan wani abu ya fito daga gare ki da sunan ɓata shirin iyayen ki kinji?”

Tsamm Aunty Amarya ta miƙe tayi hanyar waje tana me share hawayen tausayin ɗiyar ta, “kenan babu shakka dole sai an yi auren nan? Tana ji tana gani dole za’a ɗaura wa ɗiyar ta ƙwalli ɗaya wanda ba ta so” ba ma wannan ne matsalan ba, mutumin da ya fi tsanar ta da kowa shi zata aura, to taya zata ji daɗin rayuwa? gaskiya wannan abun da cutar wa ga ɗiyar ta

Da kallo Abbu ya bi ta dashi har ta fice, shi kansa ƙarfin hali yake yi domin babu yanda zai iya, wannan shawaran ba shi ne ya bayar ba, shi dai kawai ya bayar da yardan shi ne don biyayya ga mahaifin sa, amma yana ganin tabbas wannan haɗin akwai cuta wa ɗiyar sa, da yana da halin da zai samo mata wani, da tuni ya samo mata kafin hakan ta faru..

Numfashi yaja yana saka hannu ya ɗago kan Ɗahira da har yanzu take ta sharɓan kuka, kallon ta yake yi cike da tausayin ta yace, “yanzu shin Nafeesa ba mu isa kiyi mana biyayya bane?”

Ɗago jajayen idanun ta tayi tana kallon sa, cikin dauriya da cije kukan ta ta girgiza masa kai, sai dai tana son yin magana amma ta kasa

“But why don’t you accept the destiny God has chosen for you? Why not accept your parents’ choice?”

Shiru tayi tana shashsheƙan kuka, sai kuma daƙyar ta iya buɗe baki tace, “Abbu.. na.. na amin ce.. zan.. yi muku biya..yya”.

Yace, “Alhamdulillah, this is what I want to hear from you, insha Allahu baza kiyi dana-sani ba, kuma ko yaushe ke ce a sama in Allah ya yarda, albarkacin biyayyan nan da zaki yi mana, Allah zai daidaita tsakanin ku, zaku yi alfahari da junan ku, Allah ya miki albarka kinji? Share hawayen ki”. Ya ƙare maganar yana saka yatsun sa yana share mata

Itama hannun ta ta saka tana share wa

Yace da ita, “yanzu ga yi can ana kiran sallah, ki tashi ki je kiyi kinji? Kar kuma in dawo inga kina kukan nan kinji Mamana? ki sanya dangana a ranki”.

Ɗaga masa kai kawai tayi har ya fita bata ce komi ba, yana fita ta kwanta tana lumshe idanun ta tare da ci gaba da tsiyayar da hawaye

Yau wani irin baƙar rana ce a rayuwan ta da tazo mata? Ba ta jin zata iya kai wa zuwa anjima a yanda take ji, taya ma zata iya rayuwan aure da mutumin da tafi tsana a rayuwan ta? Sannan shima ya tsane ta fiye da kowa? Taya?

“Ya ilahi! Wannan wani irin mummunan ƙaddara ce ta zo min? God I beg you! If I am asleep, O God, wake me up quickly.” Ta ƙare maganar tana me fashewa da kuka, kukan da ke fitowa can cikin zuciyar ta, tare da saka mata raɗaɗi me zafi, babu wanda zai iya gane halin da take ciki, sai wanda ya tsinci kansa a irin wannan yanayin, tamkar dai ranta zai fita take ji sabida tsaban ƙunci da baƙin cikin dake tattare da ita.

 

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

“I’m so happy Hajja wlh, Ni wannan haɗin da aka yi yayi min dai-dai, domin kuwa ta hakan ne Ɗahira zata ɗanɗani wulaƙanci a rayuwan ta, Ni na tabbata babu ta yanda za’a yi Ya Usman ya ƙaunace ta, I know Kare ma sai ya fi ta daraja a gidan shi”. Shakira ta ƙarisa maganar nata cike da farin ciki da ya nuna a fuskar ta

Cikin ɓacin rai Hajja ta kalle ta tace, “dalla rufe min baki, kin san kuwa abinda zai faru a wannan auren da kike murna? To bari kiji muddin ina numfashi sai na wargaza auren nan, Ni da nake neman hanyar da zan fitar da uwar ta gaba ɗaya a gidan, a’a sake neman gindin zama suke yi a gidan, tun farko a raina ke nayi Wa sha’awar auren Usman, amma hakan be faru ba..”

“Ni kuma Hajja?” Shakira ta faɗa tana me ƙwalalo ido waje tare da dafe ƙirji

Dogon tsaki Hajja taja tana cewa, “meye kuma haka?”

“Yo Hajja do you know what you are talking about? Ni fa kike wa fatan rayuwa da wancan miskilin mara mutunci? Ina sam.. Allah ya kyauta wlh, gwara ma da Allah yasa nayi aure na; ba Ni ce aka haɗa Ni dashi ba”.

Tashi Hajja tayi fuuu ta wuce ta bar Part ɗin, don sosai Shakiran ta ɓata mata rai

Ita kuwa Shakira taɓe baki tayi tana gyara zaman ta tace, “lallai kam Hajja ban san ba kya so na ba sai yanzu, ina Ni ina auren wannan mutumin? Kenan in ƙarike rayuwa ta a cikin uƙuba da rashin jin daɗin Rayuwa? Ina sam”.  Sai kuma ta kwashe da dariya tana cewa, “ai wlh haɗin nan ya min daɗi, uhmmm ina tausaya miki Ɗahira, kin shiga bakin mayunwacin zaki, me fitar dake kuma ban ganshi ba, haka zaki dauwama kina me dana-sani a rayuwan ki”.

 

⚫⚫⚫

Direct Hajja part ɗin Hajiya ta wuce, can kuwa ta gan su zaune da Yusra ran su duk a ɓace, musamman ma Yusra da take ta zagin Ɗahiran, tana aibata ta, sannan a cewar ta, “sam bazai yiwu Ɗahira ta auri Yayan ta ba, duk hanyar da zata bi sai tabi don ganin ta hana wannan auren”.

Shigowar Hajja a dai-dai lokacin ne Aunty Zainab ta fito daga ɗakin Hajiya take ce mata, “ke wace iriyan sakarya ce? Do you know what you are saying? Ɗahiran ƴar uwan ki kike aibata ta? Wai shin Yusra me ta tare miki ne da kike tsanar ta?”

Turo baki Yusra tayi tace, “wlh Aunty baki san halin wannan munafukar bane, sam na tsane ta sabida ko kaɗan ba ta da hali me kyau..”

“Will you shut up your mouth?” Aunty Zainab ta daka mata tsawa

Hajja tace, “to ai gaskiyar ta ta faɗa, shin ke baki san kitumurmuran da A’isha da ɗiyar ta suke ƙulla wa ɗan uwan ku bane? Wlh muddin kuka sake ya aure ta tabbas sai A’isha ta shanye shi”.

“Haba Hajja wai don Allah me bayin Allan nan suka tare muku ne duk kuka bi kuka tsane su?What is wrong with this marriage? Ke kanki kin san Aunty Amarya ba mayya bace bare ta shanye shi, kawai kin ɗaura mata karan tsana kuna ta aibata su”.

Wannan karon Hajiya ce tayi magana da cewa, “Zainab, shut up before I hurt you. Shashashan Yarinya ana faɗa miki Gaskiya kina kare su, to Ni sam ko da babu abinda za su yi masa, ban amince da wannan auren ba, sabida ba na son shi da ita”.

Kallon mahaifiyar nata kawai Aunty Zainab take yi, sosai ranta ya ɓaci da irin wannan abubuwan da take ji yau a gidan su, “wannan wani irin tsana ce? Mene ne aibun su da ake ganin laifin su? Kai sam bazai yiwu ba, baza ta zira ido ta ga gidan su na ƙoƙarin rabewan kai ba, dole ne ta sanar da Dady”. Juyawa tayi ta shige ɗakin Hajiyan, ta sumfuci Jinior dake barci ta goya shi, ta ɗauki gyalen ta da jakan ta ta fito, bata bi ta kansu ba ta wuce ta bar gidan.

Ita kuwa Hajja zama tayi tana ta ƙara ingiza Hajiya a kan “lallai-lallai kar ta yarda da wannan auren, kar ta soma ayi wa ɗan ta auren dole tunda shima ba ya so”.

Nan ake yin ta fa.. chakwakiya.

 

 

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

Shi kuwa Usman tsaban ɓacin rai da jin maganar nan, yana fita daga General parlor barin gidan yayi, tuƙi kawai yake yi ya rasa ina zai je sai faman huci yake yi, yayi tafiya me nisa kafin ya tsaya yana gangarawa gefen titi, a zuciye ya buga sitiyarin motan yana cewa, “impossible.. I will never marry this girl, I hate her! I hate her so Much! zan iya kashe ta ma idan har na ganta a gida na”.

Gaba ɗaya idanun sa sun kaɗa sun yi jazur, tamkar zai haɗiya zuciya sabida ɓacin rai, jijiyoyin kansa sun fito raɗo-raɗo, haka ya kama gashin kansa ya matse yana me kiran sunan Kaka, sai kuma ya matse bakin sa cikin amon muryan sa yace, “wlh muddin kuka haɗa auren nan sai na kashe muku ita, gaba ɗaya sai kun yi dana-sanin haɗa Ni aure da ita”. Ya ƙare maganar da dukan sitiyarin motan da mugun ƙarfi yana ihu, sai kuma ya kifa kansa saman motan yana me sakin numfarfashi, cikin slow voice yace, “I hate her! Then I will killed her”.

 

 

 

.

 

.

_Hmm akwai jan aiki fa.. kuna ganin su Kaka ba su yi ganganci ba? Wani irin hali Ɗahira zata shiga? Shin maƙiyan ta suna yin nasara kuwa?_
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR’S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER’S ASSO*📖
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA’S FAMILY*_

.

 

*EPISODE Thirty Five*

Usman be dawo gidan ba sai dare, yana shigowa parlor ya tarar da Hajiya na zaune tana tsimayen shigowar sa, domin kuwa a lokacin wajen ƙarfe 12:00pm ne na dare

Yana shigowa tayi zumbur ɗin zuwa wajen sa, cikin tashin hankali tace, “Ina ka je ne tun ɗazu ina buga wayan ka ban samu ba?”

Kallon ta kawai yake yi amma be ce komi ba, gaba ɗaya ransa a ɓace yake har yanzu, zuciyar sa gaba ɗaya ba ta masa daɗi, shiyasa ma ko kaɗan bazai iya buɗe bakin sa ba, bare yayi magana

Zata sake yin magana, sai suka ji muryan Big Dady yana cewa, “Ka dawo?”

Gaba ɗaya kallon sa suke yi kamar yanda ya kafe su da ido, yana tsaye a bakin ƙofar ɗakin sa

Shiru Usman yayi yana me kawar da kai daga kallon sa

“Dama kai nake jira, daga ke har shi a gidan nan zan yi mummunan saɓa muku, muddin kuka ce za ku ja da maganar auren nan, duk abinda kike faɗa min a kan a janye auren nan, to wlh muddin ina numfashi sai an yi sa, sakaran banza sakaran hofi, kuma wlh idan har baka dena nuna wa Daughter irin tsanar nan ba, Ni da kai ne a gidan nan, zan ga uban da tayi maka ka tsane ta”. Yana ƙare maganar ya juya ya shige ɗakin sa

Usman be bari ya ƙara Socond ɗaya ba shima ya wuce ɗakin sa da sassarfa, yana jin Hajiya na kiran sa amma ina sam ya ƙi waigo wa

Itama cikin ɓacin rai ta nufi ɗakin Dadyn, tana shiga ta tarar da shi zaune gefen gado yana shirin kwanciya, ta ƙarisa wajen sa tana cewa, “wai me kake nufi da zaka saɓa mana a kan maganar nan? Ina ce yaron nan ba ya ƙaunar yarinyan? Kowa yasan da cewa jinin su be haɗu ba a gidan nan, kuma kafi kowa sani, amma sabida tada zaune tsaye ake son tauye wa ɗana haƙƙin sa, Ni fa bazan goyi bayan gaskiya ko ƙarya ba, Ni ɗana kawai na sani, abinda yake so shi nake so, tunda ya nuna ba ya son haɗin nan, kun hana sa ya faɗi ra’ayin sa, amma ai fuskar sa ta nuna muku ba ya so, to wlh bazai yiwu ba, a kan ɗana babu abinda bazan yi ba”.

“Wato kina so ki nuna min wuyan ki ya isa yanka Asiya? Har Ni kike tsayawa a gaba na a kan wannan maganar kike son gaya min magana ko? To kar ki fasa, ki je kiyi duk abinda za ki yi, amma aure ne babu fashi, tunda kuka nuna ba ku son auren nan, to yanzu ne na ɗau ɗammaran sai ya aure ta, wlh bari kiji ko bayan raina bazan taɓa yafe wa ba muddin Usman be auri Ɗahira ba, idan kin ga ba’a yi ba kuwa, to ɗayan biyu ne, ko Allah ne be yi nufin matar sa ba ce, ko kuma Baba ne ya hana, shi ne kawai zan iya bin umarnin sa a duniyar nan, kuma ki ɓace ki bani wuri kar ki sake tanka wa tun kafin raina ya ɓaci”.

Dole Hajiya ba don ta so ba ta juya ta wuce ɗakin ta, amma a ranta ta ɗau alwashin muddin ɗanta ba ya son auren nan, to itama baza ta taɓa son Ɗahira ba, sai ta muzguna wa rayuwan ta.

 

⚫⚫⚫

A wannan dare a cikin Usman da Ɗahira babu wanda yayi barcin farin ciki, zan iya cewa gaba ɗayan su a zaune suka kwana.

Washe gari ma Ɗahira da zazzafan zazzaɓi ta tashi, sosai hankalin Aunty Amarya ya tashi, gani take yi wani abu zai sami ɗiyar ta, tunda ta san halin ta, abu kaɗan ke ɗaga mata hankali ya fitar da ita cikin kamannin ta. Tasa Abbu tayi gaba tana kuka a kan “ya taimaka a warware auren nan, tunda dai Ɗahira ba ta so, be kamata su yi wa ɗiyar su auren dole ba”. Gaba ɗaya tarikice wa Abbu ya rasa yanda zai yi da ita, dole ya fito ya barta cikin ɗakin ya nufi ɗakin Ɗahira

Tana kwance ta ƙudundune cikin bargo sai rawan sanyi take yi, tun daga bakin ƙofa yana jin yanda haƙoran ta suke karkarwa

“Ya subhanallah..” Abbu ya faɗa yana zama bakin gadon, gaba ɗaya ya ruɗe da yanda ya ganta

Cikin sauri ya yaye bargon yana cewa, “Mamana kina jina?”

A lokacin ne ta buɗe idanun ta da suka kaɗa suka yi jazur ta sauke kan su daga Abbu har Aunty Amarya da ta shigo ɗakin a yanzu, sai hawaye take yi

Kallon sa Aunty Amarya tayi tace, “Abbun Zulaiha don Allah ka taimaki ɗiya ta, kana ganin yanda take yi ko? Shikenan ka ga zan rasa ta?” Tana maganar ne duk a rikice

Shi kansa Abbu tsaban tausayin Ɗahira ce ya kama shi, yace da Aunty Amarya “ta taimaka mata ta shirya ta su tafi asibiti, don be kamata su zauna a gida ba,” sannan ya tashi ya fice.

Kai tsaye asibiti suka wuce har da Aunty Amarya, inda tuni Umma ta je ta shafa wa mutanen gida halin da ake ciki, daga Hajja har Hajiya babu wanda ya damu, ita Hajiya ma ko a jikin ta, domin ta ɗanta take yi, tunda ya shige ɗaki a daren jiya ya ƙi fitowa, juyin duniya ta buga masa ƙofa ya buɗe amma ya ƙi, Usman da kwai kafaffiyan zuciya, idan yace ba ya son abu ba ya so ne kawai, idan kuma aka matsa mishi tabbas rayuka ne za su ɓaci.

 

 

⚫⚫⚫

Hajja kuwa shiri ma tayi ta wuce gidan ƙawar ta Hajiya Sa’ima.

“Ya na ganki duk a firgice ƙawata? Lafiya dai me ke faruwa?” Cewar Hajiya Sa’ima tana kallon Hajja da ta buga tagumi

“Hmm Ina fa lafiya? Wlh baƙin ciki ne yake son kashe ni a kan A’isha”.

Dariya Hajiya Sa’ima tayi tace, “wai ke kam har yanzu baza ki bar baiwar Allan nan ta huta ba? Ina ce yanzu Safiyya tayi auren ta har da yaran ta, kuma ke kanki kin fi kowa sanin tana jin daɗi a gidan mijin ta, to mene ne dole sai ta auri Mijin A’ishah?”

Hajja tace, “baza ki gane ba, wlh duk wanda yaci dani tuwo miya yasha, hankali na bazai taɓa kwanciya ba har sai na ƙuntata wa A’isha, sai na ɗaiɗaita ta sannan hankali na zai kwanta, buri na kawai yanzu in ga tabar gidan nan. Ba ma wannan ba, yanzu ta ɗiyar ta nake yi, kin san cewa yanzu za’a haɗa auren su da Usman?”

“Haba dai?” Cewar Hajiya Sa’ima tana kallon ta

“Wlh kuwa, ai tuni iyayen sun haɗa auren nan, kuma kin san halin Kaka, shi ya tsara wannan abun, sannan tunda yace za’a yi to tabbas sai anyi, tunda Ƴaƴan sa baza suyi masa musu ba, abinda yake so shi suke so”.

Cike da baƙin cikin jin zancen Hajiya Sa’aima tace, “to shi Usman ɗin yana son ta ne dama?”

Dayake itama tana wa ɗiyar ta kamun Usman, burin ta kenan ɗiyar ta ta shiga gidan, shiyasa maganar be mata daɗi ba

“Ki bari dai, Usman ba ya son ta, haka Hajiya ba ta son auren, tunda duk yanda zan yi nayi don ganin naga ta tsane ta, kuma buri na ya cika, yanzu abinda nake so shi ne tsayar da auren nan, ba zan taɓa bari ayi auren nan ba, gwara taje ta auri wani a waje hankali na zai fi kwanciya, da ace ta auri ɗan gida, hakan na nufin wata rana A’isha da ɗiyar ta…”. Sai tayi shiru saboda baƙin cikin abinda take son ƙarisawa

“Kin kawo kuka gidan da ya dace, ai tun farko abinda ya kamata kiyi kenan, ina da hanyar da zan taimaka miki wajen raba auren nan, akwai wani Malami a can hayin mu, wlh an bani labarin sa aikin sa kamar yankan wuƙa ne, ai kawai wajen sa zamu je ayi wa tufkar hanci”.

“Hajja tace, “ke Ni ban ƙi aje wajen duk wanda za’a je ba, koda Boka ne, in dai buri na zai cika, idan ba Allah ya tsare Ni ba, da tuni a kan ɗana baƙar ƙaddarar nan zata faɗa, da tuni Baffa zata aura”.

“Ke dan Allah?” Cewar Hajiya Sa’ima tana ƙwalalo ido waje

“Wlh kuwa, ke dai bari, A’isha gaba ɗaya ta gama siye ƴan gidan nan, asirin nata kuma so tayi ta mallake min ɗana, ɗiyar ta ta aure sa, amma sai da nayi da gaske sannan Baffa ya bar zancen, har yanzu kuma ba wai dena son ta yayi ba, sun rigada sun ba shi a ruwa ya sha”.

“Jar uba..! To wlh zama be kama ki ba Fatu, tashi mu je kawai, ai wani kissa duk da zaki yi yanzu bazai yi aiki ba, tunda itama a tsaye take, watarana ma yanda kike son ganin ta fice a gidan, ke zata fitar wlh, ai yanzu kai ya waye sai ana yi ana neman taimako wajen malamai”.

Hajiya Sa’ima tana yafa gyalen ta, suka fito suka hau motan Hajja Fatu suka bar gidan, suka nufi gidan Malam.

 

 

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

Yanda jikin Ɗahira yayi tsanani, dole aka bata gado

Su Big Dady duk hankalin su ya tashi da wannan ciwon na Ɗahira, sai dai babu wanda yayi yunƙurin sanar wa Kaka, kuma sai da suka kira gida suka yi musu gargaɗi

Duk kawaicin Aunty Amarya sai da tayi ta sharan hawaye a gaban su Big Dady, sosai hankalin ta ya tashi, musamman yanda wajen awanni biyu da kawo Ɗahira amma babu ci gaba, jikin ta sosai yayi zafi, suman da tayi kuwa babu iyaka, daƙyar aka samu numfashin ta ya dawo aka sanya mata oxygen, sannan aka saka mata ƙarin ruwa, zazzaɓin ne yayi mata mummunan kamu.

 

 

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

Su Hajja sun isa gidan Malam, inda suka samu ganin sa, sannan suka sanar masa abinda suke buƙata
Hajja ta so tace a hana auren ne, sai kuma taga idan tayi haka bata ci riba ba, sai tace a ƙara rura wutar ƙiyayyar da Usman yake yiwa Ɗahira, bayan an yi auren yayi mata sakin wulaƙanci tare da wulaƙanta rayuwan ta, sannan tana son itama Aunty Amarya tabar gidan, ayi mata saki kamar yanda za’a yi wa ɗiyar ta

Duk kuɗin da Malam ya buƙata, haka Hajja ta lale ta bashi, tunda tana da su, kuɗi ba matsala bace wurin ta, burin ta kawai haƙan ta ta cinma ruwa..

 

***** **** **********

Su Big Dady ba su san takamaiman abinda ke damun Ɗahira ba, tunda daga Abbu har Aunty Amarya babu wanda ya faɗa musu, shi da kansa ma Abbun yayi mata gwaje-gwaje, inda ya gano damuwa ce ya haifar mata da wannan mugun zazzaɓin, kasancewar ta me raunin zuciya, wanda nan da nan damuwa yake kwantar da ita.

Sai da aka kwana biyu, lokacin har Ɗahira tana iya gane mutane, saboda zafin zazzaɓin ya sauka sosai, sannan ne aka sanar wa Kaka

Duk da haka sai da ya tashi hankalin sa matuƙa, sosai yake ƙaunar Ɗahira a cikin jikokin sa, shiyasa ko ya ya ne abu ya same ta, sai ya shiga tashin hankali matsananci

Yanda yaga jikin nata kuma da sauƙi, sai yaji ɗan dama-dama a zuciyar sa, ya tambaye su Abbu “ciwon me take yi?”

Abbu yace, “zazzaɓi ne kawai”.

Da haka aka ci gaba da kula da Ɗahira, kwanan ta biyar ta ƙara aka sallame ta. Koda suka dawo gida, daga Aunty Amarya har Abbu babu wanda yake barin ta ta zauna ita kaɗai, zaunar da ita Abbu yayi yayi mata nasiha sosai, wanda sosai ya ratsa jikin ta ainun, har tana jin zata iya yin musu biyayya, koda kuwa waye suka kawo gare ta, sai da Abbu ya sake yiwa Aunty Amarya kashedi, ta dena barin ta tana zama a ɗaki tana yin tunani, hakan zai saka damuwar nata yariƙa yawa har ya haifar mata da matsala, kuma ya hana ta zuwa aiki gaba ɗaya, yace “sai ta warke sosai”

Shiyasa koda yaushe tana ɗakin Aunty Amarya suna hira, ko tayi ta mata nasiha tana faɗa mata tayi ta roƙon Allah, idan Usman ba alkhairi bane a rayuwan ta, wlh Allah maji roƙon Bawa ne, kuma yana jin ta zai amsa mata

Da haka ne Ɗahira take samun sauƙi a cikin ranta, kasancewar ba ta zama ita kaɗai bare ta samu halin yin tunanin dake addabar ruhin ta, wuni suna tare da Aunty Amarya, ko aiki take yi sai ta kira ta ta taya ta, ko kuma Aunty Amarya tace mata “ta fito Parlour su zauna da Fadil su yi hira ko kallo,” dayake Fadil me surutu ne shiyasa yake addabar ta da surutun shi, ko bata so sai ta biye mishi, yayi ta saka ta magana, hakan yasa kaso mafi yawa cikin damuwar ta take gushe wa

Yanzu sallan dare shi ne abun yin ta, koda yaushe tana kai kukan ta wajen Allah ne, da zaran aka ce dare yayi, to bata da sukuni, damuwar ta gaba ɗaya zai dawo mata, ta dinga kuka kenan tana ibada tana kai kukan ta wajen rabbi, Wanda shi ne kawai zai fid da ita a halin da take ciki, a kuma kullum ranan duniya sake jin tsanar Usman take yi a ranta, tana sake jin tabbas idan ta aure sa tamkar ta gama rayuwar farin ciki ne a rayuwar ta. Amma kuma babu yanda zata yi tunda auren nasa shi ne ƙadddaran ta, baza ta iya bijire wa iyayen ta ba, haka Allah ya so.

 

 

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

Fannin Baffa kuwa, al’amarin sa yayi ƙamari, duk yanda ya so ya cire Ɗahira a cikin ransa ya gaza, damuwa sosai yake ciki, dole ya koma shan giyan sa, don gani yake yi wannan hanyar ne kaɗai zai bi don samun sukunin zuciya, kullum ranan duniya sai yaje mashaya ya sha, ko kuma ya siyo ya zuba a ɗakin sa ya ɓoye, idan dare yayi ya rufe ƙofan sa ya sha yayi tatul ya kwanta barci

Hakan sai ya soma saka Sa’adatu a cikin ƙunci, domin ko kaɗan yanzu Baffa ba ya da lokacin ta, ta rasa yanda zata yi, har ƙaran sa ta kai wajen Hajja, amma duk faɗan da Hajja tayi masa be fasa ba, yanzu ta kansa kawai yake yi, sai yaga dama yake kula Sa’adatu, shiyasa duk auren ma ya soma fita ranta, tunda yanzu be da time ɗin ta, da zaran dare yayi zai rufe ƙofan shi ya barta, kuma har yanzu bata san yana shaye-shaye ba.
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR’S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER’S ASSO*📖
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA’S FAMILY*_

_Wannan shafin naki ne Shugaba adila, *SAFNA ALIYU JAWABI* Allah yaja da ranki ya kare ki daga sharrin maƙiya, Allah yasa kifi haka Amin ya allah._ 🙏

.

*EPISODE Thirty Six*

Lokacin da Ayush ta samu labarin maganar auren Usman da Ɗahira, hankalin ta idan yayi dubu, to, ya tashi, domin gani take yi tabbas idan har Usman Ɗahira zai aura, to ta rasa shi, domin babu ta yanda za’a yi Usman ya saki Ɗahira ya aure ta, ya ma za’a yi a haɗa su? Ɗahira tafi ta komi da komi, kyawu, nasaba, kuɗi, da komi ma Ɗahira tafi ta, ko kaɗan bata kama ƙafan kyawun Ɗahira ba, class da komi tafi ta, tasan babu namijin da zai samu kamar Ɗahira ya so ya rabu da ita, dole hankalin Ayush yayi matsanancin tashi, ta samu Safra da maganar ta sanar mata komi

Dariya kawai Safra tayi tace, “yanzu mene ne zai baki tsoro Ayush? Ni kam zan so ganin Lucky Babe ɗin nan da har ta samu the Handsome Guy ɗin ki, ina ga itama ta haɗu gaskiya tunda har ya zaɓe ta matsayin mata”.

Ayush wayan ta ta ɗauka, ta lalubo pic ɗin Ɗahira, wanda suka ɗauka tun waliman da aka yi musu da za su fara aiki, ta nuna wa Safra tana cewa, “Look, kema kin san tunda a family ɗin su ta fito dole zata haɗu, wlh yarinyan nan muddin ta aure sa na rasa shi”.

Sosai Safra ta yaba da kyawun Ɗahira, bata taɓa tunanin zata ganta haka ba, babu abinda ya ƙara tafiya da hankalin ta ya shagaltar da ita irin Sky Green eyes ɗin ta, baki kawai ta riƙe tana faman faɗin, “Wow!”. Sai kuma ta kalli Ayush tace, “Truly the girl is Very Very beautiful! She is very close, ta burge Ni”. Ta ƙare maganar da shafa fuskar wayan tana murmushi. Sai kuma ta sake kallon Ayush tace, “amma kina ganin haɗa su aka yi? Ba soyayya suke yi ba?”

“I don’t know”. Ayush tafaɗa fuska cike da damuwa

Murmushi Safra tayi tace, “tabbas wannan sai aikin Malam, ba na tunanin Usman zai taɓa son ki idan har yana tare da wannan kyakykyawar yarinyan, abu ɗaya kawai zamu yi yanzu, kamar yanda na sanar miki, dole mu san yanda zamu yi mu ɓata ta wajen sa, i mean sharri da tuggu shi ne nasaran mu, duk hanyar da zamu bi sai mun raba su dole”.

“But how? Bayan kin san ƴar uwan sa ce, kuma ya san halin ta”. Ayush ta sake faɗar haka har a time ɗin zuciyar ta cinkushe da damuwa

Killer smaller Safra ta saki, kafin tace, “Let’s try, yanzu abinda zaki yi, ki nemo mana wanda zai yi mana aikin nan”.

Sai a lokacin itama Ayush ta saki murmushi tace, “I have someone to do the work for us.”

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

“Kai Aboki na, kasan kuwa cewa wannan Babe ɗin taka zata yi aure?” Cewar Dr. Sabo dake zaune gaban table ɗin Dr. Sa’id yana juyawa a kujeran

Ɗago kai Dr. Sa’id yayi daga rubutun da yake yi, ya bi sa da kallo yana cewa, “wa kenan?”

“Oh you don’t know? I’m surprised. I mean Dr. Ɗahira Mana, duk a tunani na kai zaka yi wuf da ita wlh, amma fa kayi rashin Sa’a wlh da ka bari ta suɓuce maka duk da Nasan halin ka”. Dr. Sabo ya ƙare maganar yana dariyan shaƙiyanci

Sosai maganar ta bugi zuciyar Dr. Sa’id, cikin wani irin yanayi yace, “Please are you serious or joking?”

“Haba wlh da gaske nake yi, her cousin will also marry Dr. Usman, magana ma har ta baza ko ina a Hospital ɗin nan”.

Shiru Dr. Sa’id yayi

Dr. Sabo yace, “yanzu haka ma two weeks ya rage Ina ga bikin, but wlh ina maka jaje da rashin samun ta, duk a tunani na tuni kun rigada kun daidaita, aure kawai ya rage, ashe ba haka ba”.

Ajiyan zuciya Dr. Sa’id ya saki, kana ya dube sa yace, “ba abinda ke raina ba kenan, in fact ma ban taɓa tunanin auren ta ba, sabida kasan halin matata, baza ta taɓa yarda na sake aure ba, but Ni dama da wata manufa nake son ta, Amma kuma ga shi ina ga Ina son rasa dama ta”.

Dariya Dr. Sabo yayi yace, “well Dama nasan abunda zaka ce kenan, but ban taɓa tunanin itama tana ɗaya daga cikin irin ƴan matan ka da zaka yi wannan rayuwan da ita ba, duba da yanda ita ba halin ta kenan ba, ashe dai kana nan kana target ɗin ta ne”.

Murmushi Dr. Sa’id yayi yana shafa sajen sa yace, “yarinyan ce ta wuce tunani na wlh, kallon farko da nayi mata nayi tunanin bazan sha wahala wajen samun ta a hannu ta zama nawa ba, but duk yanda na so tafi ƙarfi na, uhmmm yarinyan tayi ne Dr. That’s why nake son duk yanda za’a yi na ƙulla alaƙa da ita, koda kuwa bata saba ba, nayi alƙawarin sai na cika buri na akan ta, sai na maishe ta nawa, a kaina zata san daɗin rayuwa. Kuma auren ta ba yana nufin zan kasa cika burina bane”. Sai yayi shiru yana ɗago da kansa daga jikin kujeran, ya ɗaura hannayen sa biyu saman table ɗin yana ɗan buga wa yace, “yanzu ma aka soma, wlh idan har na cika Dr. Sa’id Khan mayen Mata, sai na ɗanɗana yarinyan nan, domin hankali na bazai taɓa kwanciya ba sai na ganni tare da ita a kan gado ɗaya. Har yanzu ta kasa barin ruhi na ya samu sukuni, ta shiga rayuwata da yawa”.

Murmushi Dr. Sabo yayi yace, “tirƙashi akwai aiki kenan Dr.”.

Murmushi kawai Dr. Sa’id yayi, sai kuma yace, “baza ka gane bane. Let’s stop talking now, I will call her now nayi mata murna, yanzu sabon salon zai fara”.

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

Biki nata ƙarato wa, inda tuni an soma shirye-shirye ko ta wani ɓangare

Gefe ɗaya kuma Ɗahira har yanzu fama take yi da kanta, domin a tsaitsaye take rame wa sabida zullumi, ko yaushe ba ta jin daɗin jikin ta, yau ciwo gobe lafiya

Duk yanda Aunty Amarya tayi don ta kwantar mata da hankali, amma abun ya citura, ta kasa cire damuwa a ranta, gaba ɗaya ta rame sosai, sai haske da ta ƙara da girman idanu a waje, dama ba auki ne da ita ba, kamar ta karye take jin ta tsaban siranta, yanzu kuwa har tafi Da sirance wa

Har yanzu kuma bata koma bakin aikin ta ba, dole Abbu ya hana ta koma wa, tunda har yanzu ba ishashshen lafiya ne da ita ba, tarigada ta saka abun a ranta yana ta cutar da ita.

********

Gefe ɗaya kuma Usman shima yana cikin tashin hankali, musamman da yaga auren yana ta ƙarato wa, tabbatan dole sai an yi, shiyasa gaba ɗaya ya shiga  damuwa tsantsa, ko abinci ba ya ci duk ya hana kansa sukuni, gaba ɗaya ma ya dena zama a gida, sai dare yake dawowa. duk yanda Hajiya tayi don ta samu ta kwantar masa da hankali, ya ƙi sauraron ta, shiyasa kullum ranan duniya sake jin tsanar Ɗahira take yi, ga shi ko gayya taƙi yi, ba ta shirin komi na bikin, duk yanda kuwa ta so da cin zaƙin bikin ɗan ta mafi soyuwa a ranta. A ganin ta baza ta iya taron biki tana murna ba, ɗan ta kuma yana cikin damuwa, ga shi Big Dady ko bi ta kansu ba ya yi, ya bar su ya zira musu ido daga ita har shi Usman ɗin, kuma ya hana su sake zuwar mishi da zancen.

⚫⚫⚫

*ONE WEEK AGO*

Yau ma kamar kullum yana zaune a Office ɗin sa, ya haɗa kansa da table yana ta faman tunani, dama nan ne wajen zaman sa koda yaushe, tun safe idan ya zo ya rufe kansa a Office ɗin, sai dare yake koma wa gida.

Nocking ɗin da aka yi masa, shi yasa ya buɗe jajayen idanun sa da suka kumbura ainun sabida rashin barci, da kuma ɓacin rai, be motsa ba har sai da yaga me Nocking ɗin ya dame sa, tsaki yaja yana ɗago kansa yabi ƙofan da kallo, gaba ɗaya fuskar sa ta gama haɗe wa tayi jazur sabida tsantsan damuwa, da gani kasan ba a cikin mood ɗin sa yake ba

Lumshe idanu yayi yana buɗe baki a hankali ya ba da iznin shigo wa, sai dai babu yanda za’a yi aji sa, dole ba don ya so ba ya sake ɗaga murya ya ba da iznin shigo wa

Wani staff ne ya shigo ciki, tare da gaishe sa cikin girmamawa

Sai dai yanda kasan kamar dutse haka Usman yayi banza da shi, illa rikitattun idanun sa da ya kafa masa

Duk ya ruɗe ɗan saurayin sabida Mayun idanun sa da ke kallon sa, ya matso yana miƙa masa envelope, sannan ya sanar masa, “wani ne yace a ba shi”

Be ce masa komi ba, yayi masa alamun ya ajiye masa

Ajiye masa yayi a saman table kamar yanda ya ba shi umarni, kafin ya fice da sauri

Da kallo Usman ya bi envelope ɗin da shi, yana mamakin mene ne a ciki? Da Kuma wanda ya aiko?

Tsaki yaja yana sake gyara zaman sa kan kujeran, ya saka white hand ɗin sa ya ɗauka ya soma buɗe wa, hotuna ne ya zaro guda biyar

Hoton farko dake saman sai da ya ɗauke numfashi na wucin gadi sabida munin hoton, Ɗahira ce kwance tsirara da wani ƙaton gardi suna manne da juna babu kaya suna aikata masha’a

Saurin lumshe idanun sa yayi yana jin wani tashin zuciya na son kama shi, take a nan ya saki sauran hotunan zuwa ƙasa ba tare da ya gani ba, sosai zuciyar sa take tafarfasa da abinda ya gani

“Yanzu wannan sheɗaniyar yarinyan karuwa, ita ce su Kaka za su aura min?” Yayi maganar a maƙoshi yana jin tamkar ya haɗiya zuciya ya mutu tsaban baƙin ciki

Hoton yabi da kallo daga ƙasa, sai yayi saurin kawar da kansa saboda ganin sauran da suka ninka wanda ya gani muni, kifa kansa kawai yayi a saman table ɗin yana riƙe da kansa dake faman sara masa, tuni idanun sa sun juye sun sake zama ja sabida tsaban ɓacin rai, a fili ya furta, “na tsane ki sosai fiye da komi dake duniyar nan! dama tun ba yau ba na rigada nayi tunanin hakan a Raina”. Sai yaja dogon tsaki yana tunanin yanda zai yi, “anya bazai ɗau hotunan ya nuna wa iyayen sa ba, wataƙil ma ya samu damar tsere wa auren?” Zuciyar sa ta raya masa hakan

Take kuwa ya saka hannu ya kwaso hotunan, ya mayar dasu cikin envelope ɗin, miƙe wa yayi tare da wayan sa a hannu da keey ɗin motan sa ya bar Office ɗin.

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

Tana kwance a saman gadon ta tayi samɓal da ƙafafuwan ta, sai ta kifa cikin ta ta tusa kanta ƙasan pilow, a hankali take fitar da numfashi ɗai-ɗai.

Fadila ce ta turo ƙofan ta shigo da sallama a bakin ta, da kallo tabi Ɗahiran dashi har taƙariso bakin gadon tana zama tace, “Sister lafiya dai?”

Ɗahira da taji muryan Fadila tamkar daga sama, domin mugun tunani ta afka da gaba ɗaya ma ba ta cikin duniyar mu, da sauri ta zaro kanta dake ƙasan pilow tabi Fadila da kallo da manyan idanuwan ta da suka gama sauya kala suka yi jazur tamkar tayi kuka, ga shi sun faɗa sosai, hakan yasa idanuwan suka sake fito wa waje suka yi ƙwala-ƙwala

Nan da nan Fadila ta ruɗe da ganin ta a haka, tace,”lafiya Sis? what’s going on? What’s wrong with you looking at your eyes have changed color?”

Murmushin ƙarfin hali Ɗahira take yi, ta tashi zaune tana kallon ta da kyau, kafin tace, “nothing Sis, yaushe kika zo?”

“Ya zaki ce min babu komi? Kin kuwa ga yanda kika koma? Ciwo kika yi ne ko wani abun ke damun ki?” Fadila ta sake faɗa tana ƙare mata kallo, ganin yanda ta ƙara ƙarmashe wa sabida tsaban rama har ƙasusuwa ake gani ta wuyan ta

Stil dai murmushin tayi mata tace, “ciwo nayi Sister”.

“Amma shi ne baki sanar dani ba, babu wanda ya kira Ni ya faɗa min? tun yaushe kike ciwon ne da kika rame haka?”

Ɗahira dariya tayi me bayyana haƙora, wanda idan ka kalla kasan cewa na dole ne, tace, “kin sauya ƴar uwa, yau ke ce kike jero min waɗannan tambayoyin?”

Hararan ta Fadila tayi tace, “Seriously, it’s not a joke. I’m asking you ciwon meye kika yi ya mayar dake haka?”

“Hmmm ciwo ne kawai, zazzaɓi”.

Kallon ta Fadila tayi, sai tace, “ko dai kan maganar auren ki ne? Of course there is something going on. nayi mamakin jin cewa an haɗa ki da Ya Fodio, na kira wayan ki duk ba ta shiga, meyasa Sister kika yarda da auren nan tunda kin san ba kya son shi? In fact ma ba kwa shiri ke dashi?”

Shiru Ɗahira tayi bata ce komi ba

Fadila ta sake cewa, “I know wannan raman yana da nasaba da auren ki, ban ji daɗi ba gaskiya yanda na ganki haka..”

Shigowar Fadil ne yasa Fadila yin shiru, duk kan su suka bi shi da kallo har ya ƙariso ciki

Hannayen sa biyu cikin aljihun wandon sa yake kallon su yace, “Aunty Ɗahira Kaka na neman ki”. Sai kuma ya mayar da idanun sa kan Fadila yana dariyan tsokanan da zai mata yace, “ke kuma nan kika yo daga zuwa? ga shi can mijin ki na bilayin neman ki, ashe ke kin zo nan kin maƙale, halan kewar ɗakin kika..”

Bugun da ta kai masa ne, yasa shi guduwa ba tare da ya ƙarisa zancen nasa ba, sai da ya kai bakin ƙofan ɗakin yana dariya yace, “to ki dai fito ga shi can yana neman ki cwhengum ɗin naki, sai kace ba yanzu kuka rabu ba”.

“Fadil ba ka da kunya ko?” Cewar Ɗahira tana murmushin zancen sa

“Ki ƙyale sa, zan gyara masa zama wlh kafin in tafi, ai kasan hali na?” Fadila ta faɗa tana tsare sa da idanu fuska a kirne

Be sake cewa komi ba ya fice da sauri, don yasan yayi tsokana, gwara ya fece tun kafin ta kama shi

Ɗahira tace, “ga shi har an kira Ni ba mu gaisa ba, bari in dawo sai mu gaisa”.

“Ok Nima Ina Nan zuwa wajen Kakan yanzu ai”. Cewar Fadila tana tashi tsaye

Tare suka fita daga ɗakin.
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR’S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER’S ASSO*📖
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA’S FAMILY*_

*HADHISI *
_Aisha (may Allah be pleased with her) was quoted as saying, “The Messenger of Allah (may peace be upon him) married her when she was six years old, and she was nine years old with him, and Allah took her life when she was eighteen years old.” Reported by Muslim._

.

 

*EPISODE Thirty Seven*

K.B ne da Aunty Amarya a Parlour’n zaune, ita kuma Umma tana kichen tana shirya abincin ranan da bata kammala ba

“Ƙanwa ta ashe kina ciki kin maƙale ina ta tambayar ki?” Cewar K.B yana kallon Ɗahira da suka ƙariso wajen tare da Fadila

Dariya tayi tace, “Yayana anya baka neme Ni ba dai, Tunda ai Mama ta san ina ɗaki”.

“Aff to ai yanzu ne na soma maganar taki”.

“To magana ta fito fili kenan”. Tafaɗa tana dariya

Zama Fadila tayi gefen sa, don ita Aunty Amarya har ta tashi ta shige ɗaki ma

Gaishe sa Ɗahira tayi

Ya amsa yana cewa, “wai ƙanwa ta ciwo kika yi kika rame haka? Ko dai zullumin auren ne?” Yayi maganar cikin barkwanci

Murmushi kawai tayi

While Fadila tace, “Nima haka na gani yaya, wai ciwo tayi”.

Tashi Ɗahira tayi tace, “bari dai inje in dawo Kaka na kira na sai muyi magana, I have something to talk to you about. yaushe Shamsiyya zata zo ne?”

Taɓe baki yayi yace, “to ki dai kira mijin ta ki tambaye sa, amma bani ba, tunda Ni ga nawa tazo”.

Dariya kawai tayi ta wuce ta bar su nan. Ta san halin K.B idan ta biye mishi babu inda zata je

Part ɗin Kaka ta wuce kai tsaye, tana shiga ɗakin sa da sallama

Ya amsa mata yana zaune kan gadon sa yana duba wani ƙaton littafi na addini

“Taho Mata ta”. Yayi maganar yana kallon ta da murmushi a kyakykyawar face ɗin sa

Taho wa tayi ta zauna gefen sa tace, “Kakus nayi kewar ka”. Ta ƙare maganar da jan gemun sa

“Me too My wife, bayan ma yanzu kin dena nema na, har sai na aika a kira ki kike zuwa, yanzu kenan idan kinyi auren ma haka zaki guje Ni ko?”

“Eyya Kaka wlh No, I will never run away from you, idan ba ka a rayuwa ta ai kamar babu Ni ce”. Tayi maganar tana langaɓe kai

“To amma ciwo kika sake yi ne bani da labari, naga duk kin sake rame wa ne sosai?”.

“kai Kakus, sai dai idanun ka ne suka gane maka haka, amma ai dama can haka nake”. Tayi maganar tana dariya

“Anya ba zullumin rabuwa dani kike yi ba?”

Dariya sosai wannan karon take yi

Shima yana taya ta, sai kuma yace, “faɗa min gaskiya Ɗahira, do you want this marriage or not?”

Kallon sa tayi tana tsayar da dariyan, sai kuma ta yafa wa fuskar ta murmushi tace, “Kaka idan ma ba na son auren ai bazan ƙi muku biyayya ba, kana tunanin zan watsa muku ƙasa a ido ne? Never. Ba na fatan wannan ranan tazo”.

Murmushin jin daɗi yayi, sosai yaji daɗin kalaman ta, amma sai yace, “Mata ta a kan farin cikin ki babu abinda bazan iya ba, ko yau ake ɗaura auren ku kika ce baki so, to zan dakatar dashi, Na san yanda kuke da Fodio, ko kaɗan jinin ku be haɗu ba, tabbas nasan sai kinyi haƙuri dashi kafin komi ya daidaita, amma kuma hakan da nayi shi ne naga ya dace, wannan hanyar ce kaɗai zai sa ku dawo kuna shiri, domin ba na son nan gaba bayan ba na raye iyali na kansu ya rabu, zan so tun ina da rai inga kun shirya kan ku, kun dawo kuna ƙaunar junan ku, wannan shi ne burina, domin ba na jin daɗin yanda tun kina ƙarama yake nuna miki tsana”.

Hannayen sa ta riƙo, idanun ta cike da hawaye, tace, “wlh Kaka zan yi muku biyayya ko waye kuka kawo min a matsayin miji, bare kuma ɗan uwa na. Na rigada na ɗaukar maka alƙawari da kai da iyaye na zan yi zaman auren nan da zuciya ɗaya, fata na kawai Allah ya bani ikon yin biyayya a gare ku da miji na”.

Tafin da Fadila take yi ne yasa suka juyo suna kallon ta, “oh ka ga masoyan asali? an haɗa kai ana ta ƙus-ƙus”. Tayi maganar cikin sigan tsokana, duk da kuwa sai da ta gama jin abinda suke cewa ta shigo

Kaka yace, “Miskila kin fi mahaukaci ban haushi saukar yaushe?”

Dariya tayi tana zama kan drowern gadon tace, “yanzun nan babu daɗe wa Alh. Kaka, ya gida? na same ku lafiya?”

Yana murmushi ya amsa mata da cewa, “alhmadulillah.. Ina Kakan nawa, shi dai ya kawo ki ko?”

“Shi ya kawo Ni, yana waje tare da Ya Baffa”.

“Masha Allah, ya wajen su Rabi’atu (Hajiya Ikram) komi lafiya?”

“Lafiya lau Kaka, suna gaishe ka da kyau-da kyau, sai jibi za su zo su”.

A lokacin ne shima K.B ya shigo, nan suka shantake gaba ɗaya ana ta hira da Kaka, har Ɗahira da ba jin daɗin jikin ta take yi ba, sai dai ta saki jiki sosai tana ta saka musu baki, daga ƙarshe K.B ne ya soma tafiya, tunda dama yau ne zai koma, sai ranan biki ya dawo

Su ma daga baya fitowa suka yi, Fadila ta wuce sashin Hajja don ta gaishe su, ita kuma Ɗahira tayi Part ɗin su

A Hanya suka haɗu da Usman yana taho wa, tunda ta gansa gaban ta yayi muguwar sara wa, tayi saurin kawar da kai daga kallon sa, rabon da ta gansa tun ranan da aka ce za’a haɗa su aure, sai yanzu

Shima dai tunda ya ganta yayi matuƙar ɗaure fuska, zuciyar sa na wani irin tafarfasa saboda ganin ta da yayi

Suna zuwa dai-dai juna yace da ita, “ta biyo sa”.

Sarai Ɗahira taji me yace, duk da kuwa babu wanda zai ce yayi magana, sabida yanda yayi maganar a ciki, kuma kansa na kallon hanya babu wanda zai ce da ita yake yi, ita kuwa taci gaba da tafiya tana jin ƙirjin ta na bugawa da sauri-da sauri

Ji tayi kawai an jawo ta baya an haɗa ta da bango, wanda sai da yasa ta saki ƙara saboda buguwan da ƙashin ta yayi, zaro idanu kawai tayi tana kallon sa kamar zuciyar ta zata faso ƙirjin ta ta fito tsaban tsoro

“Ni nake kiran ki kike banza dani?” Yayi maganar a zuciye tamkar zai kai mata bugu

Runtse ido tayi da sauri jikin ta na rawa

Cikin ɗacin rai yace, “shashashan yarinya ballagaza, sauran maza, tun wuri ma ki je ki ce baki son auren nan, idan ba haka ba wlh sai na halaka ki kika shigo gida na, na tsane ki ba na ƙaunar ki! kuma bazan taɓa son ki ba, ƴar iska kawai”.

Yanda ta ƙwalalo masa idanun ta dake zubar da hawaye, ji yake yi kamar ya saka hannu ya ƙwaƙulo su, sai dai dauriya da yake yi sabida ba ƙaramin jin tsanar ta yake yi ba. saurin janye hannun sa daga riƙe mata kafaɗa yayi, yana matsawa da sauri tare da tofar da yawu, ciki-ciki yace, “ƙazamiya.. wai a rasa ma wanda za’a aura min sai sauran maza irin ki? tirrr dake”. Ya buga mata wani banzan kallo ya wuce da sauri

Zame wa tayi a nan ta haɗa kanta da ƙafafun ta ta soma kuka, kuka me taɓa zuciya, har wani rawa jikin ta yake yi, kalaman sa ne suke yawo a cikin kunnen ta, “me yake nufi kenan? Bayan tsanar da yayi mata yanzu kuma kallon ta yake yi ƴar iska? Har da kiran ta ƙazamiya. Karuwa?”

“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un”. Take faɗi kawai, while zuciyar ta tamkar ta fashe tsaban takaici

Da sauri ta ɗago kanta tana share hawayen fuskar ta, tuna wa da tayi a hanya take, kuma kowa zai iya ganin ta idan bata tashi ba. Miƙe wa tayi tana sake share hawayen ta, ta nufi Part ɗin su zuciyar ta cinkushe da baƙin ciki, har wani jiri-jiri take gani a hanya, Allah yasa babu kowa a parlour’n, sai tayi saurin shige wa ɗakin su, Toilet ta shige ta rufe kanta tasha kukan ta ma’ishi, sannan ta wanko fuskar ta tare da ɗauro alwala ta fito

Tana tayar da Sallah Fadila ta shigo ɗakin, dama kiran ta ta shigo yi don su ci abinci, tunda taga tana sallah sai ta koma.

 

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

Ɗakin sa ya wuce kai tsaye, ya faɗa kan gadon sa yana me lumshe ido, shi kaɗai yasan me yake ji a duniyar nan, da ba don kalaman Dadyn sa da yake tunawa ba, wlh da tuni sun neme sa sun rasa ya bar ƙasan, sai dai ya rigada yace masa, “muddin be bari an yi auren nan lafiya an gama lafiya ba, to wlh sai yayi dana-sani a rayuwan sa, domin wlh sai yayi mugun saɓa masa”.

Dogon tsaki yaja yana miƙe wa zaune, ya ɗauki envelope ɗin da ya ajiye sa saman drowern gadon sa tun dawowar sa, ciro wa yayi ya hau yaga hotunan ɗaya bayan ɗaya, zuciyar sa na ci gaba da tafarfasa tamkar zata ƙone, ko wani daƙiƙa sake jin tsanar Ɗahira yake yi, wanda ko ada be ji makamancin irin sa ba, a yanzu kuwa ji yake yi da za’a ba shi wuƙa ya yanka ta, sai yayi mata gutsi-gutsi yayi filla-filla da naman jikin ta

Yana gama wa ya kwashe ya zuba a basket ɗin dake bayan ƙofan sa, ya shige Toilet don yin alwala.

 

 

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

A hankali gida ya soma cika da mutane, sabida ƙaratowar biki, ƴan uwan Aunty Amarya duk sun cika Part ɗin su tun ana saura kwana uku biki, dayake itama ƴar dangi ne babu laifi duk sun zo

Duk wani shiri da ake yi na Amare Ɗahira bata a ciki, su Fadila da su Firdausi, da sauran ƴan matan Familyn su suke yin komi, ita dai tana ɗaki sai dai ta ƙule taƙi fitowa, gaba ɗaya ma ba jin daɗin jikin ta take yi ba, saboda zazzaɓi da take fama da shi, shiyasa babu wanda ya takura mata, gyaran jiki ma tace “ba ta so” dole aka ƙyale ta, daƙyar ta bari ana gobe bikin aka yi mata saloon da lalle.

Washe gari 27 April 2021. Aka shaida ɗaurin auren *DR. USMAN NOOR AL’AMEEN* tare da Amaryan sa *DR. NAFEESAT AL’AMEEN AL’AMEEN (ƊAHIRA).* bikin da ya tara dubbannin jama’a, sai mu ce masha Allah

Daƙyar Usman ya halarci ɗaurin auren nan, ana gama wa aka neme sa aka rasa, dama be gayyaci kowa ba, bare abokan sa ma ba ƴan nan bane, sai dai wasu sun ji labari kuma sun halarta, sai dai shi be ma gansu ba ya arce.

Ana ta neman Ango an rasa, haka dai aka gama gaishe-gaishe ƴan uwa da abokan arziƙi aka soma watse wa.

Cikin gida ma ana ta shagulgulan biki, babu abinda za’a yi a bikin, tunda daga Amaryan har Angon babu me halarta, Ɗahira na fama da kanta, tunda tun sanda aka ɗaura auren jikin ta ya rikice, dole aka ɗaura mata drip aka yi mata alluran barci don zuciyar ta ya huta, dayake Abbu ne ya duba ta shiyasa ya gane damuwa ce kawai da yayi mata yawa

Lokacin da ta tashi har ɗakin ya shiga, ya zauna daga shi sai ita, yayi mata nasiha me ratsa zuciya, kuma ya roƙe ta “ta dena saka damuwa a ranta, ta riƙe auren ta da amana, tayi biyayyan aure”, nasiha sosai yayi mata wanda take ta faman kuka.

An rigada an shirya mata Part ɗin ta ya tsaru, dayake duk na gida ne, Big Dady da Abba suka ɗau nauyin yin mata komi, an shirya mata ɗakin ta irin na ƴan gata, komi sai dai ace Masha Allah.

Zuwa dare aka kai ta ɗakin auren ta, wanda tasha kuka ba Ni da kuka ba, aka watse aka bar ta ita kaɗai tunda baza a kwanan mata ba.

Sai da Big Dady ya kira wayan Usman ya shaida masa “muddin be kwana a gida ba tare da matan sa ba, sai ya saɓa masa”. Kuma ya basa umarnin yayi maza-maza ya dawo gare ta.

 

 

*******

Be dawo gidan ba, sai ƙarfe 01:00am. Na dare. Lokacin tuni Ɗahira tayi barci abin ta, bayan ta gama kwankwaɗan kukan ta son ranta, wanda ya haddasa mata zazzafan zazzaɓi, daƙyar ma barcin ya kwashe ta tana ƙudundune a kan gadon ta.

 

 

.

 

 

 

 

_to nan ake yin ta fa, ya zaman Ɗahira da Usman zai kaya? Wani irin zama za su yi a rayuwan auren su? Hmm ku dai gyara zama kawai Ni dai abinda zan ce muku kenan, yanzu ne za’a soma chakwakiyar._
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR’S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER’S ASSO*📖
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA’S FAMILY*_

*NATSUWA A SALLAH*
_Sallah babbar matsala ce. Ganawa ce tsakanin Bawa da mahaliccin sa, Ubangiji maɗaukakin sarki. Saboda haka ana buƙatar cikakkiyar natsuwa, a tattara hankali wuri ɗaya domin wannan ganawa ta musamman._
_A cikin ayoyi biyun farko na suratul Mu’uminun ana faɗa mana cewa:_
_”Lalle ne, muminai sun sami babban rabo, wanɗanda suke a cikin sallar su masu tawali’u ne.”_
_Watau, Muminai wanɗanda idan sun tsaya yin Sallah sai gaɓoɓin su da zukatan su su natsu, babu wani abu mai shagaltar da su daga ambaton zatin Allah maɗaukakin sarki, to, irin su suke rabban ta. Natsuwa cikin sallah da ƙasƙan da kai ga Allah su ne alamun imani na gaskiya da Tauhidi tsantsa, don kuwa ko yaushe bawa yayi kusa da Ubangijin sa sai ya haɗa jin tsoron sa, musamman ma dai a sallah inda yake ganawa da shi, yake tunawa da girman sa. Allah yasa mu dace._

 

 

.

*EPISODE Thirty Eight*

*WASHE GARI*

Tunda aka yi sallan asuba Usman be dawo gidan ba, be kuma bari kowa ya gansa ba ya bar masallacin.

Ita kuwa Ɗahira tunda ta tashi tayi sallan asuba itama, ta sake komawa barcin, dayake akwai zazzaɓi a jikin ta shiyasa har gari yayi haske bata farka ba, sai da taji hayaniyan ƴan biki da wasu suka zo su sake ganin ɗakin nata, kasancewar a lokacin za su tafi, shi ne ta farka, lokacin 12:00pm.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Har ciki suka shiga suna ta mata tsiya, ganin ta da suka yi tana ta barci

Ita dai bata ce musu kanzil ba, illa murmushi da take tayi, sai kuma daga baya ta gaishe su.

Ba su wani jima ba suka yi mata sallama suka tafi.

Sake koma wa tayi ta kwanta, don sosai kanta yake sara mata sakamakon tashin ta da suka yi, ta rufe ido kenan taji an hankaɗo mata ƙofan ɗaki, da sauri ta buɗe idanun ta tana bin Yusra da ta shigo da kallo

Ita kuwa sai faman taɓe baki take yi tana girgiza jiki, sai kuma ta mayar da idanun ta kan Ɗahiran tace, “baƙar munafuka! burin ki ya cika kin auran min Yaya, to wlh ki saka a ranki, kamar auren nan ya rabu ne, ba ke ba zama a gidan Yaya Usman, domin ba ya ƙaunar ki, ba kuma zai taɓa ƙaunar ki ba, wlh dani dake yanzu ma muka soma ƴar tsama”.

Yanda ka san t.v haka Ɗahira take bin ta da idanu, har sai da ta dire Aya kafin ta tashi zaune tana bin ta da kallo sosai, ko kaɗan ba ta jin daɗin Jikin ta, kuma har ga Allah ba ta son ta biye mata, amma kuma gani take yi idan har ta bar ta ta tafi bata mayar mata da martani ba, to, tabbas nan gaba ma zata dawo tayi mata irin wannan cin mutuncin, kuma zata ga kamar tsoron ta take ji, don haka ta saki guntun murmushi tana kallon ta tace, “wa kike da suna? Yusra ko? Ni ba sa’an yin wasan ki bane, tun wuri ki kama kanki, domin shiru-shiru ba hauka bane, wlh ina ƙyale ki ne kawai don Ni ba Kaza bace da zan zauna kullum ina sa’insa da ke, na san mutuncin kaina; na kuma san kima ta, amma wlh muddin kika sake shigo min gida na, kika yi min irin wannan halin karnukan, zan baki mamaki Yusra, zan nuna miki Ni ba’a sha na a warke, domin zan nuna miki ainihin hauka na wlh”.

Shewa Yusra ta saki tana tafa hannu tace, “an yi miki duk abinda zaki yi ki yi, ai Ni dama so nake yi ki ɗau mataki sai in San kin cika ke tatacciyar mara mutunci ne, kuma ke baki isa ki hana Ni zuwa gidan ɗan uwa na ba wlh, kin yi kaɗan, nonsense…”

“Wai hayaniyan me nake ji ne? What’s going on here?” Cewar Fadila da ta shigo da sauri, dama Breakfast ta kawo musu shi ne ta jiyo kamar hayaniya

Ɗahira tace, “Ask her to come and find me in my room,”

Tsaki Yusra taja tace, “wlh mu zuba dani da ke”. Tana faɗa ta juya ta fice.

Ƙarisowa Fadila tayi bakin gadon tana zama tace, “wai me ke faruwa ne? Me ya haɗa ki da ita?”

“Babu komi Fadila, kin san halin ta ba tun yau ba, ban san me na tsare mata ba ita da Yayan ta suka bi suka tsane Ni, ban san me nayi musu ba”. Ɗahira ta ƙare maganar cikin damuwan da ya nuna a muryan ta

Ajiyan zuciya Fadila ta sauke, sai kuma tace, “ki yi haƙuri da duk halin su, Ni ban san meyasa Yusra take wannan ɗabi’an banzan ba, amma yanzu ba ta Ita zaki yi ba, ta Mijin ki zaki yi, duk hanyar da ya dace shi zaki bi domin samo soyayyar shi, ke ba yarinya bace Ɗahira, kin san abun kuma da ya dace, batun tsana ko rashin sa duk be taso ba yanzu, yanzu kun zama ɗaya ke da shi, aljannan ki kawai zaki nema, kar ki soma ki biye mishi, na san zaki iya ƴar uwa, haƙuri shi ne zai sa ki cin ma Nasara kinji? Domin auren ku muna fata mutu ka raba ne”.

Murmushi Ɗahira ta saki tana jin hawaye na son cika mata idanu, sai tayi saurin kawar da kai tana ɗan rufe idanun ta tare da komar da su

Fadila tace, “yanzu ina Angon naki? Ga abinci can na kawo muku sai ki je ki tashe shi. Amma kin ban mamaki fa”.

Kallon ta Ɗahira tayi da son ƙarin bayani

“Kya waro min Ido mana, ji be ki don Allah mana, kin zauna har sha biyu da rabi baki yi wanka kin shirya ba, ta hakan ne zaki dai-dai ta gidan ki?”

Wannan karon dariya Ɗahira tayi, sai ta tashi kawai ba tare da tayi magana ba, domin sosai take jin jikin ta babu daɗi

“To Ni bari in tafi, zuwa anjima zan sake leƙo ki, zuwa gobe insha Allahu duk zamu tarkata, na san ma yanzu su Momy suna nan shigo wa”. (Tana nufin mahaifiyar K.B Hajiya Ikram) tunda ta koma can sai ya zamana itama Momy take ce mata kamar sauran ƴaƴan ta, saɓanin a baya da suke kiran ta Gwaggo Rabi.

Har Fadilan zata fice, sai Ɗahira tace mata, “ta zo mata da maganin ciwon kai”.

Amsa mata kawai tayi Sannan ta fice

Ita kuma ta shiga wanka, sai da ta fito ta shirya cikin atamfa baƙa da kalan fari da coffee, ɗinkin riga da zani raffer, tayi kyau sosai, sai dai yau komi bata shafa a fuskar ta ba duk da kasancewar ta me son kwalliya, ɗankwalin kawai ta ɗaura ta fito Parlour

Da kallo kawai take bin ko ina, har ta isa kan dainning ɗin, duba abinda aka kawo musu tayi, sai kuma ta juya ta nufi ɗakin da ta gani kusa da na ta, tsaya wa tayi a bakin ƙofa tana tunanin shiga ko a’a, don ta san nan ne ɗakin Usman, sosai gaban ta yake faɗi, don har yanzu bata san wani irin zama za su yi ba

Bismillah tayi kawai ta tura ƙofan da sallama, bayan tayi Nocking ba’a amsa mata ba. Sai dai babu kowa ciki, sai da ta gama ƙare wa ɗakin kallo gunun ban sha’awa irin nata komi da komi, sai dai kayan ɗakin ta ya fi yawa tunda ita mace ce, amma har ta colours ɗin ciki iri ɗaya ne

Fitowa tayi ta koma kan dainning ta hau yin breakfast ɗin ta, sai dai har ta gama a tunani tayi Breakfast ɗin

Ɗaya daga cikin ƙannin K.B suka kawo mata maganin da tace a kawo mata, amsa tayi tasha ta zauna a kan kujera tana faman tunani

A haka sauran mutanen gida sukai ta shigo wa ganin ɗaki, da masu tafiya da waɗanda sai gobe za su tafi, ƴan Maiduguri dai duk yau suka watse

Daga ƙarshe su Shamsiyya da Shakira, Firdausi, Salma da sauran sa’annin ta duk suka cika sashin, suna ta hira

Tun Ɗahira ba ta biye musu har dai ta saki jiki ana ta yi da ita, tuni ta wartsake abun ta

Suna ta tsokanar ta wai “daga aure ango ya tafi ya bar ta,” masu kare mata suna yi, har da Shakira Iyayen gulma, ita dai sai dai ta bi su da dariya kawai.

Sai magriba duk suka watse suka bar ta, ta shiga tayi sallan magriba, sannan ta dawo Parlor, tunda nan ya ɗan fi haske, da wayan ta ta haska tayi zaman ta tana ci gaba da faman tunanin ta, babu abinda ke tsaya mata a rai, sai yanda za su yi zama da wanda ya tsane ta; itama kuma ta tsane shi

Kafin a kira sallan isha’i aka kunna musu gen, tunda duk generator ɗin su haɗe yake dana Part ɗin Baffa

A lokacin ne aka sake kawo musu abincin dare, tana amsa ta ajiye saman dainning ta wuce ɗakin ta ta rufo ƙofa, alwala tayi ta gabatar da sallan isha’i, sannan tayi shafa’i da wutri, ta roƙi Allah buƙatun ta, sannan ta sauya kaya zuwa rigan barci doguwa tayi kwanciyar ta, da haka tana tunani har barci ya ɗauke ta.

 

 

*********

Kamar jiya, haka ma yau Usman sai ƙarfe 01:00am. Ya dawo gidan. Ko kallon ɗakin ta be yi ba ya shige nasa, wanka yayi ya sauya kaya zuwa na Barci, dama ya rigada yayi sallan sa a masallaci, sai yayi kwanciyar sa, tare da kitsima abubuwan da yake son aiwatar wa, don samun mafita daga wannan kaddararren auren.

Washe gari haka ya sake tsallake wa ya fice a gidan, shi fa sam ganin ta ne ba ya son Yi ma, shiyasa yake fice wa. Ga shi Big Dady yace masa kar ya soma ya ga ƙafafun sa a Hospital idan har ba two weeks yayi ba.

 

A yau duk sauran mutanen da suka zo biki suka watse, dama duk yawanci ƴaƴan Kaka ne su Hajiya Ikram da Hajiya Laila, sai ƴaƴan su wasu  da ba su tafi ba, sai kuma ƙannin Kakan, su Hajiya Baseera da Hajiya Hannatu (Ihsan). Duk dangi na kusa ne. Kuma duk yau suka gama watse wa

Aunty Zulaiha CE kawai ta kai yamma, itama don tana jiran mijin ta ne, da zata tafi sai da tazo har Part ɗin Ɗahira, a nan take ce mata “ta shirya taje Part ɗin su Usman ta gaishe da Hajiya, idan da hali ma ta zauna a can sai zuwa dare ta dawo”

Tana tafiya ta shirya kamar yanda tace mata, doguwar riga abaya baƙa ta sanya, me kwalliya sosai a gaban rigan na flower, sai ta yane kanta da gyalen abayan, ta saka turare a jikin ta tare da takalmi ta fito riƙe da wayan ta

Tana fito wa Part ɗin ta suka haɗa idanu da Baffa dake zaune saman farandan gidan sa, ya haɗe ƙafafu ya ƙura wa Part ɗin nata idanu yana faman tunani. Ganin ta yasa ya sauke ƙafafun ƙasa yana mata murmushi

Sosai taga ya sauya mata, gaba ɗaya ya rame ya rage haske, sai ƙasumba da ta ga ya ajiye, kamar dai ba shi ba ɗan gayen nan

Murmushi tayi masa itama, tana ƙarisa wa inda yake ta gaishe shi

Amsa wa yayi yana cewa, “amarya ba kya laifi.. ko da kin kashe ɗan masu gida”.

Dariya tayi tana ɗan rufe fuskar ta tace, “kai Yaya ka dena don Allah ba na so. Ina Sa’ada tana nan mu gaisa?”

“A’a ta fita, tana Part ɗin Hajja”.

“To bari inje Yaya”.

Daga nan ta wuce tayi ƙofan da zai sada ta da gidan su

Da kallo Baffa yake bin ta dashi, sai ya lumshe idanu yana jin hawaye na cika masa idanu. har yaushe zai jure da abinda yake ji? Yanzu ta zama matar ɗan uwan sa amma soyayyar ta ƙara wanzuwa yake yi a ransa

“Ya Allah ka cece Ni, ya Allah ka bani baiwar Allan nan idan har alkhairi ne ita a rayuwa ta..”

“Da wa kake yi ne haka?” Cewar Sa’adatu da ta tsaya gaban sa tana kallon sa, sai dai bata san me yake cewa ba

Buɗe idanun sa yayi yana kallon ta, sai kuma ya kawar da kai yana miƙe wa ya shige cikin parlour’n su

Itama bin bayan shi tayi fuskar ta tuni ya nuna damuwa, yanzu sam Baffa ya dena kula ta, sai tayi magana sau dubu be amsa mata ba.

 

⚫⚫⚫⚫⚫

Da sallama Ɗahira ta shiga Part ɗin Hajiya, sai dai babu kowa a ciki, sai ta samu wuri ta zauna tana aza idanun ta kan t.v dake aiki

Kamar shuɗewar mintuna biyar sai ga Hajiya ta fito riƙe da Plate a hannun ta daga kichen. Ganin Ɗahira sai tayi kicin-kicin da fuska ta nufo cikin parlour’n

Da sauri Ɗahira ta zamo daga kan kujeran, ta zauna a ƙasa tana gaishe ta

Sai da ta zauna ta ɗan kalle ta a fizge, kafin tace, “Lafiya”.

Jiki a sanyaye Ɗahira ta sake duƙar da kanta ba tare da ta sake cewa uffan ba

Itama Hajiya bata sake kula ta ba, ta soma cin abincin ta.

Har ta gama Ɗahira bata ɗago kai ba, tunanin kawai yanda zata iya rayuwa da su take yi, da kuma yanda suka tsane ta, nan da nan taji idanun ta sun ciko da hawaye, bata ankara ba taji sun soma zubo wa, saurin saka hannu tayi ta share tana ɗan ɗago kanta tabi Hajiyan da kallo, wanda ta fito daga kichen ajiye Plate ɗin; ta wuce ɗakin ta

Ɗan ajiyan zuciya ta sauke tana me lumshe idanun ta. sallaman Usman da yayi ciki-ciki ne ya saka ta ware ido sai a kan sa

Wanda shima ya sauke nasa idanun yana bin ta da wani irin kallon da ta kasa fassara shi.
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR’S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER’S ASSO*📖
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA’S FAMILY*_

 

*EPISODE Thirty Nine*

Saurin ɗauke kanta tayi daga kallon sa, ta duƙar da kanta tana jin gaban ta na matsanancin faɗuwa, ko kaɗan ba ta ƙaunar su haɗa idanu, saboda kallon da yake mata sosai yake cutar da ita.

Takowa yayi ya shige ɗakin Hajiya

Sai a lokacin ta sake ɗago kanta, ta ɗan kalli hanyar da ya bi, sai kuma tayi zugum ita kaɗai a parlour’n, ta rasa me zata yi, kar kuma ta tafi tayi laifi, sai ta tashi kawai ta shige kichen ɗin Hajiyan, duba wa tayi ko akwai wanke-wanke tayi, amma ƴan ƙwayoyi ne. Dayake ɗazu kafin su Aunty Zainab su wuce duk sun wanke.

 

Wanke sauran tayi ta kife ta fito tana gyaran mayafin ta, sai kawai idanun ta suka faɗa cikin na Usman dake zaune saman dainning, saurin ɗauke kai tayi tana takowa ciki ta zauna a ƙasa kusa da kujera, bata sake ɗago kai ba bare ta kalli inda yake. Har ya gama tana nan a haka, sai da tajiyo sahun ƙafafun sa ya wuce ya nufi ƙofa kafin ta ɗago kai tabi shi da kallo, ƙare masa kallo kawai take yi har ya fice, kafin ta saki ajiyan zuciya tana ɗago hannayen ta ta soma murɗa su tana tunani

Fitowan Hajiya yasa ta ɗago kai ta bi ta da kallo

Ita Hajiya ma tayi tunanin ta wuce tun ɗazu, shiyasa bata ce mata komi ba tayi ninyan juyawa

Sai Ɗahiran tayi saurin ce mata, “zata tafi”.

Kanzil bata ce mata ba ta shige ɗakin ta

Sai jikin ta ya sake yin sanyi ƙalau, miƙe wa kawai tayi ta wuce gidan su, gaba ɗaya ranta babu daɗi, bata san tun yaushe Hajiya ta sauya mata ba, amma da sosai suke mutunci da ita.

Tana shiga parlour’n suka sake haɗa ido da Usman dake zaune yana latsa waya, ya ɗago kai yana kallon ta

Janye idanun ta tayi da sauri, ta nufi hanyar ɗakin ta

“Zo nan”. Yayi maganar tamkar ba da ita yake yi ba, yana ci gaba da latsa wayan sa

Ɗan juyowa tayi tana kallon sa, sai kuma ta taka ta nufe sa, durƙusa wa tayi gaban sa tace masa “ga ta”.

Tamkar ba da shi take yi ba, be ɗago ba bare ya kalle ta, sai ma sake tamke fuskar nan nasa da kullum take a haka yayi, ya ɓata lokaci a haka be ɗago ba, be kuma ce mata komi ba

Ɗahira har ta gaji, sabida durƙuson da tayi ƙafafun ta sun soma mata zafi, jure wa kawai take yi, amma gaba ɗaya ba ta jin zata iya jure irin wannan wulaƙancin nasa, “don me ya kira ta kuma yayi banza da ita?” Sai kuma ta miƙe kawai ta nufi ɗakin ta

Bata san cewa yana biye da ita a baya ba, tana isa bakin gadon ta sai ji tayi an janyo ta baya, kasancewar gyalen ta ya riƙe ya shaƙe mata wuya, babu shiri ta waro ido waje tana kallon sa

While shima kallon nata yake yi fuska babu fara’a, cikin izgili da taƙaman sa yace, “kin dai ƙi jin magana ta? Sai da kika shigo gida na ko? To yau zan nuna miki banbancin Ni da kwaratan ki, sai kin gummaci zaman wuta da zaman gida na, domin sai na ɗai-ɗai ta rayuwan ki, sai kin yi dana-sanin zuwan ki duniya”.

Tuni Ɗahira ta soma hawaye sabida shaƙan da yayi mata, bata so yin magana ba, sai kuma tace, “meyasaka ka tsane Ni ne Ya Usman? Me nayi maka ne? Ko na tare maka wani abun ne?”

“Uban ki ki kai min! Na ce ubanki ki kai min”. Sai ya zaro mata idanun sa da suka juye suka yi ja yace, “na tsane ki! na tsane ki! Na tsani na buɗe ido na ganki, taya ma zan bari kiyi rayuwa a ƙarƙashi na?”

Sosai wannan karon Ɗahira take kuka, jin yanda ya zagar mata uba, babu abinda yafi ƙona mata rai sama da haka, sai ta saka ƙarfi ta janye gyalen ta idanun ta na zubar da hawaye

Bata ankara ba sai ji tayi ya falla mata mari, kafin kace me ya sake sakar mata wani, sai ya tura ta saman gadon yana cewa, “yau sai na kashe ki ko zan huta a rayuwa na”.

Sosai Ɗahira ta gigice da marin da yayi mata, lokaci ɗaya ta zaro ido ganin ya nufo ta gadan-gadan, wani ƙara ta saki tana me miƙe wa a saman gadon ta wuntsila can ɗaya side ɗin, sai gata ta faɗo ƙasa tim, duk da haka bata haƙura ba ta miƙe da sauri tana neman wajen ɓuya, gaba ɗaya ta fita hayyacin ta lokaci ɗaya, saboda ba kaɗan ba marin da yayi mata ya gigita ta, har kumatun ta sun kumbura

Sake fashe wa tayi da kuka da ta gansa kusa da ita

Janyo ta kawai yayi ya wurga ta saman gadon, ko kaɗan babu tausayi a lamarin Usman, domin sosai yake sake jin wutar tsanar ta na ƙara ruruwa a zuciyar sa, ji yake yi idan be kashe ta ko ya wulaƙanta rayuwan ta ba, bazai taɓa sukunin zuciya ba

Hawa yayi kan gadon ya soma janye mata gyale

“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un.. me.. me.. kake yi haka? Don Allah kayi haƙuri”. Tafaɗa da rawan baki tana son ƙwatan kanta

Falla mata wani marin yayi da yasa dole ta nutsu waje ɗaya, ta saki wani marayan kuka tamkar ranta zai fice

Be dakata ba sai da ya cire mata gaba ɗaya kayan ta, tuni idanun sa sun juye, sai ƙara hautsina yake yi da tsantsan tsanar ta

Ita kuwa numfashi kawai take sauke wa, tana addu’a a zuciyar ta sabida abun da ke shirin faruwa da ita, domin ko kaɗan baza ta iya jure wa ba, ita da take amsar wa ƴaƴa mata haƙƙin su idan aka yi musu fyaɗe, shi ne yau ita za’a yi wa

“Ya Allah ka taimake Ni”. Tafaɗa a ƙasar ranta hawaye na ci gaba da kwaranya a fuskar ta tamkar an kunna famfo.

Tofar da yawu yayi ya mirgina ya tashi, zuciyar sa tamkar ta ƙone sabida baƙin cikin abinda yake shirin aikata wa, bayan yasan ita wace ce, taya ma yayi wannan tunanin gangancin da yake son haɗa jiki da ita?

Tsaki yaja yana kallon ta da jajayen idanun sa, ganin yanda take rufe jiki, sai ya saka hannu ya janyo blanket ɗin yana cewa, “ƴar iska! Uban wa kike son ɓoye wa jikin naki? Bayan da kin gama tallata sa a waje meye kuma yayi saura? Babu abinda zai burge Ni a nan bare inyi sha’awar ki, gwara ma tun wuri ki sauya tunani. Na tsane ki! kuma wlh sai kin yi dana sanin aure na, sai na azabtar dake yanda ko an ce su sake bani auren ki sai sun yi kuka”.

Kuka sosai Ɗahira take yi, tana riƙe da blanket ɗin da ya riƙo ƙam, ta hana sa janye wa

Tsaki ya kuma ja ya fice a ɗakin, har ya shige ɗakin sa, sai kuma ya dawo cikin nata ɗakin

Wani irin zabura tayi cike da tsoro tana kallon sa

Shi kuwa ko bi ta kanta be yi ba, ya sanya hannu ya cire keey ɗin ɗakin, sannan ya janyo ƙofan ya rufe ta ta waje

Wani marayan kuka ta saki har da shashsheƙa, sosai ta takure kanta tana ta kuka, tafi awa a haka bata dena kukan ba, sai da taji gaba ɗaya jikin ta ya ɗau zugin zafi kafin ta haƙura. Lallaɓa wa tayi ta sauko daga kan gadon, har ta ɗauki rigan ta zata mayar, sai kuma ta ajiye ta shiga Toilet, ruwa me zafi ta haɗa ta gasa jikin ta, daƙyar take iya yin komi, tana yi hawaye na kwaranya a fuskar ta, sai da ta gama ta ɗauro alwala ta fito, wani doguwar rigan ta saka mara nauyi me ruwan ƙasa, ta saka Hijab ta tayar da Sallan magriba da ya wuce ta, sai ta haɗa dana isha’i

Har ta idar da sallan kuka take yi, ko kaɗan ta kasa yin shiru. Ta daɗe tana roƙon Allah kafin ta sallame sallan, ta kifa kanta a gwiwowin ta taci gaba da rera sabon kukan ta

Maganar Fadila da tayi mata tun ana gobe bikin su, shi ne ya dawo mata a rai. “Ta sani cewa dole ne sai tayi haƙuri da rayuwan auren ta, amma bata taɓa tunanin wulaƙancin da zai mata zai kai haka ba, yanzu har da yunƙurin mata fyaɗe a matsayin ta na matar sa ta sunna kuma ƙanwar sa. Sannan yake jifan ta da munanan kalamai, wai wani irin tsana ne yake mata? Me ta tare masa ne? Me tayi masa?”

Sai ta ɗago kai tana share hawayen fuskar ta da ya gama kumbura yayi suntum, kasancewar ta fara gaba ɗaya tayi jazur sawayen yatsun sa sun fito, cikin rawan murya a fili take cewa, “ga shi tun ba’a yi nisa ba na tuna maganar ki Fadila, amma ba na tunanin wannan auren zan jure azabar shi har na ba wa maƙiya na kunya, wlh bazan iya ba sam”. Ta ƙare maganar ta da fashe wa da sabon kuka

Buɗe ƙofan da taji ana ƙoƙarin yi ne, yasa tayi tsit tana bin ƙofan da kallo hawaye na kwaranya a saman fuskar ta, wanda tayi zaton shi ne ya shigo

Shima a kanta ya sauke idanun sa, sosai yaji wani sanyi a ransa duba da yanda ya ganta, ci je leɓe yayi a ransa yace, “kaɗan ma kika gani, sai na wahalar da rayuwan ki, sai na wulaƙanta ki”.

Takowa yayi ya isa gaban dressing mirror inda ya ƙilla idanu ya ga wayan ta. ɗauka yayi kawai ya fice a ɗakin, ya sake rufe ta, domin ba ya son ko kaɗan ta gudu ta kai ƙaran sa, shiyasa zai mata horo da haka, kuma nan ba da daɗe wa ba zai san abun yi, domin ba ya so a fuskanci komi sai ya gama gana mata azabar da ya tanadar mata, yayi wa kansa alƙawari sai tayi dana-sanin rayuwan ta.

Ita kuwa Ɗahira ko ci kanka bata ce masa ba har ya fice, domin wani irin baƙin ciki da zallan tsanar sa ke nuƙurƙusan ta, shiyasa baza ta iya tambayan sa ina zai kai mata waya ba.

Ta jima a nan zaune tana kuka, gaba ɗaya ta fita hayyacin ta, har wajen ƙarfe 10:30pm. tana nan a haka, zazzaɓi me zafi ya rufe ta, dole ta rarrafa ta isa inda ta ajiye sauran maganin da tasaka a kawo mata jiya, ta ɗauka ta isa ga Fridge ta samu ruwa, sai dai bata sha ba sai da ta kora drinks ɗin da ta gani a ciki, domin ba ƙaramin yunwa take ji ba, ga shi mugun can ya rufe ta, tana tunanin wannan wani irin mugu ne da zai rufe ta a ɗaki? To me yake nufi da hakan? Shi ne bata sani ba.

Tana gama shan maganin ta kwanta, sai dai ta kasa barci sai juye-juye take yi, daƙyar barci ɓarawo ya sace ta.

 

Washe gari koda ta farka da safe, sabida yunwan dake cin ta ta nufi ƙofa don ta fita ta nemi abinci, amma sai taji ƙofar a garƙame, wani irin jijjiga ƙofan ta hau yi tana kiran sunan sa, nan da nan hawaye suka soma zuba a kyakykyawar fuskar ta da ta gama kumbura, ta sauya kamanni. dama ba ƙwarin jiki ne da ita ba, sai ta zube a nan ta hau rusa kuka, sosai take kuka tana kiran sunan sa ya zo ya buɗe ta.

Amma Usman yana zaune a Parlour Yana jin ta be ko motsa ba, illa gyara kwanciyar sa da yayi ya ci gaba da latsa wayan sa, sai ma da yaji ta ishe shi sai ya kunna t.v ya ƙure ƙaran

Hakan ya tabbatar wa da Ɗahira yana nan zaune yana jin ta, wani irin kuka ta saki tana zame wa ta kwanta a wajen, ta ma rasa wani irin tunani zata yi, illa zuciyar ta dake ta faman zugi tamkar ta faso ƙirjin ta, “ashe ya shirya mata mugunta ne shiyasa ya ɗauke wayan ta, domin kar ma ta nemi wani ta waya”

Kukan ta tasha ta tashi zaune, shiru kawai tayi tana tunani hawaye na zubo mata, “me zata yi masa ta huce? Tana ga baza ta iya zaman auren nan ba, dole ne yau ta fita ta koma gida, dole ne kowa ya san halin da take ciki, da dai ta zauna a gidan sa ta gummaci a raba auren nan tun yanzu, ta matuƙar tsanar sa! kullum sake jin tsanar sa take yi a rai, domin ba shi da tausayi ko kaɗan.

Miƙe wa tayi riƙe da cikin ta dake faman ciwo, ta nufi Fridge ta buɗe, drinks ta ɗauka tasha sosai, ta kwanta saman gado tana ta faman tsiyayar da hawaye.

Wasa-wasa wunin ranan currr Usman ya ƙi buɗe ta, tun tana ɗaukar abun da wasa har taga ta kusa mutuwa saboda yunwa, domin bata da abun sha sai drinks, gaba ɗaya cikin ta ya gama ƙulle wa

Shi kuwa yana Parlour ko jirgau be yi ba, sallah kawai yake tayar dashi, duk wanda ya zo neman ta sai yace musu “tana barci”. Har da masu zuwa ganin ɗaki ƴan cikin anguwa, da friends ɗin ta na wajen aiki, duk sai da Usman ya kora su, aka aiko Fadil da abinci, ya amsa ya rufe ƙofan, ya kuma je ya ajiye be ci ba be kai mata ba.

A haka Ɗahira ta kwana a mawuyacin hali, ga yunwa ga zazzaɓin da koda yaushe yana jikin ta, sakamakon damuwa da kukan da take wuni yi.

Da safe ta gwada buɗe ƙofan, sai taji ya buɗu, da sauri ta koma ta saka Hijab a saman kayan barcin ta ta fito da zumman zuwa gidan su ta faɗa wa iyayen ta komai, domin baza ta iya zama cikin uƙuba ba.

Sai dai tana zuwa ƙofan Parlour ta ganshi a garƙame, lumshe idanuwan ta tayi hawaye na zubo mata, cikin muryan kuka tace, “Allah na roƙe ka, ka fitar dani daga hannun wannan azzalumin bawan naka”. Sai ta fashe da kuka. Juyawa tayi ta koma kan kujera ta kwanta tana ta rera wa, sai da tayi ma’ishi wanda daƙyar ma take iya numfarfashi saboda yunwan dake cin ta. Tashi tayi ta nufi saman dainning ganin cololi an jera, sai dai tana buɗe wa tsami ya bugo ta, sabida abincin tun na jiya ne da aka aiko mata, juya wa tayi ta koma kichen, a wahalce ta gama girka indomie, a kichen ɗin ta zauna ta hau ci hannu baka hannu ƙwarya, duk jikin ta rawa yake yi, babu abinda take yi sai zubar da hawaye, gaba ɗaya tausayin kanta ya kama ta, “yanzu idan a haka zata ci gaba da rayuwa ya zata yi? Babu dole fa auren nan.”

Sai da taji ta cika cikin ta fam kafin ta haƙura, tasha ruwa ta tashi ta fito, kan dainning ɗin ta nufa ta kwaso komi ta kai kichen, sai da tagama wanke gaba ɗaya cololin kafin ta wuce ɗaki, wanka tayi ta sauya kaya ta haye kan gado.

Tun daga ranan haka Ɗahira take rayuwa, kullum tana gwada fita amma ina ƙofan rufe yake, ba ta da aikin yi sai dai ta kwanta tayi ta faman tunani, tun abun na damun ta har ta haƙura, ga shi ya raba ta da wayan ta bare ta kira Maman ta, gaba ɗaya tayi kewar su, kullum tana zaune cikin kaɗaici, ko kallo ba ta yi, sabida tun farko ma bata saba ɓata lokacin ta wajen kallo ba, ga shi ba ta sanin sanda Usman yake shigo wa da sanda yake fita, wataƙil ma ba a gidan yake kwana ba, shiyasa ta tashi tsaye wajen kai wa Allah kukan ta, shi ne ya jarabbe ta da wannan ƙaddararren auren, kuma shi ne zai fid da ita, domin bata da tsimi ko dabara, idan Allah yayi nufin Mijin ta me shiryuwa ne ya gane kuskuren sa, ita me iya biyayya ne ta zauna dashi kamar yanda iyayen ta suka zaɓa mata, amma muddin yaci gaba da wulaƙanta ta, to, dole ne zata sanar wa su Kaka a raba auren, domin baza ta iya zama ba.

A haka har suka yi sati biyu da auren nan. A ranan da suka cika sati biyun ne, Usman ya koma aiki, har Office Big Dady ya Kira sa yace masa, “ya kamata ya bar matar sa taci gaba da zuwa aiki”. Be ce masa komi ba illa gyaɗa masa kai da yayi

Sai da ya dawo Direct ya wuce wajen Kaka

Kaka na murnan ganin sa yana cewa, “ina ya baro matar nasa? ya hana ta zuwa ta gaishe shi tunda aka yi aure”.

Taɓe baki yayi yace, “Ni Kaka zuwa nayi in sanar maka zamu tafi hutun amarci (Honeymoon) Ni da ita”.
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR’S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER’S ASSO*📖
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA’S FAMILY*_

*NATSUWA A SALLAH*
_Manzon Allah mai tsira da aminci, ya ce, “sallah ba kome ba ce illa miƙa wuya da tawali’u…” Kuma ya ƙara da cewa, “Bawa bai samun ladan sallar sa sai gwargwadon abinda ya hankalta daga sallar.” Watau, gwargwadon natsuwar mutum cikin sallah gwargwadon darajar da yake samu gun Allah. Don haka ne ma ma’aikin Allah ya ce, “Allah ba ya juya wa Bawa baya yana cikin sallah matuƙar bai waiwaya ba; idan ya waiwaya kuwa, sai Allah ya bijire masa.”_
_Babu abin da yake kawo waiwayo cikin sallah kuwa sai gafalar Bawa da muƙamin Ubangijin sa, watau ya zama tamkar wanda ya tsaya yana ganawa da Ubangijin sa alhali zuciyar sa tana shagale da wani abin dabam. A kan wannan matsala ne Allah yake ce wa Manzon sa, da al’ummar sa ma, a cikin suratul A’ARAF aya ta 205:_
_”Kada ka kasance daga gafalallu.”_
_In muka lura sai mu ga cewa ta ya ya kuwa gafalalle zai iya tunawa da muƙamin Ubangijin sa yana cikin wannan hali na rashin kula har wani abin tsoro ya auku? Bugu da ƙari, daman can ga shi Allah ya yi umarni a cikin suratul Ɗ.H., aya ta 14 da cewa:_
_”Kuma ka tsayar da Sallah domin tuna Ni”._
_In mutum ya Yi haka, ana fata ya rabban ta._
_Allah yasa mu dace._

.

*EPISODE Forty*

Washe baki Kaka yayi yace, “to to kai da Ɗahiran ce za ku tafi hutun?”

“Eh mana Kaka”. Yayi maganar yana yatsina

“To Masha Allah Abu yayi daɗi, masha Allah”. Kakan ya sake faɗa cike da farin ciki, domin ba kaɗan ba yaji daɗin hakan, tabbatan dai suna zaman lafiya. Sai kuma ya sake kallon Usman ɗin yace, “But when are you going? And what country are you planning to go to?”

“Tomorrow evening .. We will go to Turkey .. because can nake da gida.. na fi son zaman can”. Yayi maganar tamkar ba ya so

“Masha Allah.. to Allah ya Kai ku lafiya, zan sanar da iyayen naka ko, ita kuma zuwa goben ya kamata tayi wa kowa sallama”.

Tashi tsaye Usman yayi yana faman taɓe baki, kafin yace, “ai ba sai kace ba Kaka, she will come to greet you”.

“Ja’irin yaro ka ganka ko? Kai dai ba’a yin abun arziƙi da kai Fodio”. Cewar Kaka yana murmushi

Shi kuwa be ma bi ta kansa ba ya bar ɗakin. Kai tsaye Part ɗin iyayen shi ya wuce, babu kowa a Parlour, sai ya wuce ɗakin sa ya ɗauro alwala, da zai tafi masallaci ne suka ci karo da Hajiya, gaishe ta yayi ya wuce da sauri sabida har an gama kiran sallan magriba, kafin ya kai za su iya tayar wa.

Sai bayan isha’i ya koma gidan su. Yana shiga parlour’n ya mayar da ƙofan ya rufe, kai tsaye ɗakin sa ya wuce ya yi shirin kwanciyar sa, zama yayi kan gado ya ɗauko Lapton ɗin sa yana dannawa, a haka har dare yayi nisa, sannan ya kwanta barci.

Itama Ɗahira tuni tayi barcin ta, tunda babu abinda take yi sai kwanciya, iyakan tayi girki iya bakin ta ta cinye ta ɗauraye abun da ta ɓata ne, dayake ba shigo musu ake yi ba ko shara ba ta yi tunda babu inda yake ɓaci, ɗakin ta kawai take kakkaɓe wa ta share.

 

 

*TOMORROW*

Tana kwance a kan gadon ta tayi ɗai-ɗai, daga ita sai shimi fara da gajeren wandon sa shima fari, ta rufe gashin kanta da hula me raga-raga ja, babu abinda take yi sai tunanin ta yanda za’a yi ta koma aikin ta, zuwa yanzu ya kamata ta koma bakin aikin ta ko don ta riƙa ɗebe kewa, tunda babu abinda take yi yanzu a gidan.

Buɗe ƙofan da aka yi yasa ta ɗago kanta tana aza manyan idanuwan ta a kansa, saurin kau da kai tayi daga kallon sa

While shima tunda ya shigo ya sauke ido a kanta, ya ɗauke kansa yana jan dogon tsaki tare da haɗe rai

Tsakin kamar a tsakar kanta yayi, itama sai taci magani zuciyar ta cike da baƙin cikin ganin sa

“Put on the Hijab and follow ME”. Abin da ya faɗa kenan ya juya ya fice

Shiru tayi tana tunani, tamkar baza ta yi abinda yace ba, sai kuma ta tashi ta buɗe wardrobe ɗin ta ta zaro dogon Hijab maroon Colour, ta saka a jikin ta ta nufi ƙofa ta fice.

Yana zaune a Parlour, ganin ta sai ya tashi ya nufi ƙofa ya fice

Bata yi wani tunani ba tabi bayan sa, a haka suka ƙarisa cikin gidan su

Kai tsaye Part ɗin Kaka suka wuce, inda suka same sa kamar ko yaushe yana zaune a kujeran sa yana karatun jarida

Ganin su ba ƙaramin farin ciki ne ya ɗarsu a zuciyar sa ba, nan da nan ya washe baki yana musu maraba

Tuni Ɗahira ta isa wajen sa ta rungume sa, sai ta fashe da kuka tsaban farin ciki, domin ji take yi tamkar an ciro ta a kurkuku yau ta sami sake

“A’a Mata ta ya haka? Ko duk kewar nawa ne da kika yi?”

Bata yi magana ba illa ɗago kai da tayi tana kallon sa

Sai ya sakar mata murmushi yana cewa, “kin ganki kuwa? Duk kin sauya gaba ɗaya kin rame, halan ciwo kika yi?”

Usman dake tsaye bakin ƙofa kamar an dasa shi, ya harɗe ƙafafu yana kallon su, yayi saurin cewa, “to ba dole ka ganta ta rame ba tunda ta rabu da hanjin rayuwan ta, ko rashin ganin ka zai saka ta rama, ga ta nan dai ku gaisa ka ba Ni ita zamu wuce”.

Dariya Kaka yayi yace, “ban san sanda ka lalace ba Fodio”. Sai kuma ya mayar da kallon sa kan ta yace, “to mata ta Ubangiji Allah ya kai ku lafiya ya dawo daku lafiya, abinda zan ce kawai ki kula da kanki kinji? Kuma ki yo min tsaraba sosai kar ki ce kin manta dani”.

Kallon sa kawai take yi da mamaki, sai kuma ta buɗe baki da ninyan tambayar sa

Usman ya katse ta da faɗin, “tashi mu je, You are wasting my time”.

“Kai dai ja’irin yaro ne Usman, tafiyan da ba yanzu za ku yi ba shi ne duk kabi ka ishe ta, ka bari mana mu gaisa sosai mana”.

Shi Usman gani yake yi kamar zata iya ɓallo masa ruwa, shiyasa yayi saurin taho wa yaja hannun ta suka fice

Da sakakken baki kawai tabi sa tana kallon ikon Allah

Suna fita ya yi saurin sakin hannun ta kamar ya riƙe ƙaya, domin abinda yaji kamar ana jan sa da electronic, be kalle ta ba yace, “ki mai da hankali ki sanar da su game da zaman mu, wlh sai na ɓalla miki rayuwa biyu”.

Idon ta ta waro kawai tana kallon sa, “to wannan ko dai ya samu taɓin hankali ne?” Tafaɗa a ranta tana me sake ƙwalalo idanu waje

Kallon ta yayi ganin kamar ba ta bin shi a baya, yanda idanun sa suka shige cikin nata sai yayi azaman ɗauke kai, domin ba kaɗan ba ya tsani su haɗa ido, wani irin faɗuwar gaba ne me haɗe da tsoro yake riskan sa a koda yaushe, shiyasa ya tsane ta sosai. Daure wa kawai yayi ya dalla mata harara, kamar zai yi magana sai kuma ya fasa ya juya yaci gaba da tafiya

Sai tabi bayan sa kawai tana kitsima abubuwa a ranta, sai kuma maganar Kaka ya dawo mata, “to ina za su je ne da Kaka yake musu addu’a?”. Babu me ba ta amsa dole taci gaba da bin bayan sa. Part ɗin su taga sun bi, sai farin ciki tsantsa ya cika ta

Suna shiga suka ci karo da Aunty Amarya zaune a parlour’n ita kaɗai, babu kowa ma sashin, tunda Abbu yana Hospital, Fadil kuma yana school, sai Kuma Umma da ta tafi anguwa

Da gudu Ɗahira ta ƙarisa wajen Maman ta tana me kiran sunan ta tare da fashe wa da kuka

“A’a mene ne haka kuma? Wannan wani irin sakarci ne?” Aunty Amarya tayi maganar tana riƙe ta

In a tears, Ɗahira she said, “I miss you Mama! Miss U so Much.”

Murmushi Aunty Amarya tayi, sai ta kalli Usman da ya samu wuri ya zauna har da harɗe ƙafafu yana latsa waya, tace, “ashe za ku yi tafiya? Ɗazu nake ji wajen Abbun su”.

Sai lokacin ya ɗago kai ya kalle ta, guntun murmushi ya saki kafin ya bata amsa a taƙaici, yana me gaishe ta

Ta amsa cikin fara’a tare da sanya musu albarka, da musu fatan alheri

Ɗahira fa kanta ya gama ƙulle wa, “da wannan mutumin ne za su yi tafiya? To zuwa ina?” Wannan tambayoyin ne bata sani ba, duk da tana son tambaya sai kuma ta fasa. Tana ɗago kai suka haɗa ido dashi, ya sakar mata wani kallo da sai da gaban ta ya faɗi, da sauri ta ɗauke kai tana mayar wa wajen Maman ta

Aunty Amarya tace, “So take care of your self? May God protect you and bring you peace.”

Daga ita har shi babu wanda ya amsa. Illa miƙe wa da yayi yace, “tashi mu je. Za mu tafi Mama”.

“To madalla, a dai ta addu’a Allah ya tsare”. Aunty Amarya tafaɗa cikin fara’a

Usman fa ya kasa ya tsare ya ƙi tafiya sai da Ɗahira, don shi gani yake yi kamar zata faɗa mata wani abun, shi kuma ba ya son kowa ya fahimci komi yanzu ba tare da ya wulaƙanta rayuwan ta ba, inyaso sai a saka shi ya sake ta da hujja, domin ya san muddin su Big Dady suka san wani abu, za su hana sa tafiya ko ina ne, sannan za su saka mishi ido, haka kuma zai ci gaba da zama da ita ba halin saki.

Ɗahira ko jirgau bata yi ba don ba ta da ninyan tashi ma. Sai da Aunty Amarya tace mata, “ta tashi su tafi”. Kafin ta miƙe cike da ƙunan zuci tabi bayan sa, tamkar ta koma ta sanar wa mahaifiyar ta halin da take ciki, sai kuma ta ga hakan be dace ba, gwara taci gaba da haƙuri, Allah shi zai mata maganin komi, da sannu Allah zai saka mata. Idan Allah yayi auren su ba daɗaɗɗe bane nan kusa za su rabu da yardan Allah

Kai tsaye Part ɗin Hajiya suka wuce, inda suka tarar da ita a parlour

Da sauri Ɗahira ta duƙa har ƙasa ta gaishe ta

Tsaban takaici ma Hajiyan bata amsa ta ba, illa ɗaure fuska da tayi tana kallon Usman tace, “na ji wani zance wai za ku tafi Turkey yawon cin amarci? Har yaushe ta shanye ka da zaku tafi cin amarci da ita? Yaushe ka soma son ta ma?”

Usman be tanka ba, don be da ma alaman tankawan

Ɗahira kuwa tuni ta sad da kanta ƙasa tana maimaita kalaman Hajiyan tamkar karatu, domin ta kasa ma fahimtar me take nufi

Tsawan da Hajiyan ta daka wa Usman ne ya dawo da Ɗahira cikin tunanin ta, da sauri ta ɗago kai tana kallon Hajiyan

“Ke tashi ki wuce”. Yayi maganar idanun sa a kan Ɗahira fuska babu walwala

Tana mayar da idanun ta kansa, ya ɗauke nashi idanun daga gare ta

Ta san babu da wanda zai yi sai da ita, don haka ta miƙe ta fice ta nufi hanyar gidan su.

Kai tsaye ɗakin ta ta wuce ta zube saman gado, shiru tayi tana faman tunani, “ta fa kasa gane me mutanen gidan suke nufi, shin da gaske ne tafiya za su yi da shi ko kuma fahimta ne bata gama yi ba? Amma kuma ga abinda Mahaifiyar sa tace, ma’ana dai da ita yake son tafiya? Anya?” Sai kuma ta miƙe zaune kamar an zare mata laka, a ranta take tambayar kanta, “shin meyasa yake son yin tafiya da ita? Sai dai idan akwai abinda ya shirya yake son aiwatar wa a game da ita, idan ba haka ba mutumin da ya tsane ta ba zai taɓa tafiya da ita wani waje ba. Tabbas a cikin zuciyar ta ta kasa yarda babu komi a zuciyar Usman”.

Shigowar sa cikin ɗakin ne yasa tabi shi da idanu

Fuska a ɗaure ba tare da ya kalle ta ba yace, “ki shirya kayan ki.. by 03:00 pm. We’ll go”. Da gama maganar nasa ya juya da ninyar fice wa

Amma sai tayi saurin cewa, “Where are we going? Ni fa I don’t understand.”

Be ce mata komi ba bare ya juyo, ya ficewar sa.

Ɗahira ta jima a nan zaune bata iya tsinana komi ba, sai kuma daga baya da ta ga bata da sauran dabara sai ta miƙe ta soma shirya kayan ta a cikin ɗan ƙaramin akwati, ba wani kaya da yawa ta zuba ba tunda har yanzu bata tantance inda za su je ba, duk da ta ji su Kaka ɗazu sun faɗi yawon cin amarci, amma ta san yanda suke zaune shiyasa ma bata saka maganar a rai ba, ta san sai masoyan asali ke irin wannan tafiyan amma ba su ba.

Bayan ta gama ta zare Hijab ɗin jikin ta, sannan ta sauya kaya zuwa Arabian gwon baƙa da kwalliyan stones, sosai rigan ta haska fatar ta ta ƙara mata kyau ainun, duk da sosai zaka ga raman da tayi matuƙa, amma kuma ta sake kyau saboda hutu da ta ɗan samu waɗannan satikan ba tare da ta taɓuka komi ba

Tana gama wa ta fito Parlour, zaman ta tayi tana jiran kuma next me zai ce tayi. har ƙarfe ukun ta gota be fito ba

Sai uku da rabi sannan ya fito cikin shirin sa, sosai yayi kyau kamar ka sace sa ka gudu, shigan dai da ya saba na ƙananan kaya shi yayi, wandon me ruwan ƙasa jeans, sai farar riga da aka yi harafin U a gaban rigan da coffee colour, kayan sun yi masa kyau sosai sun kuma haskaka skin ɗin sa, musamman ma da yayi amfani da coffee Cumbas sai ya ƙara haɗe wa, kansa ba hula sai kwantaccen gashin kansa baƙi siɗik da ya sha gyara har zuwa sajen sa suna shaining. Shima yana jaye da ƙaramar Trolly wanda tafi na Ɗahira ƙanƙanta, ba kaya ya zuba ba abubuwan buƙatar sa ne a ciki, irin su laptop da sauran su, saboda  yana da komi a can, kayan sawan sa ma na can daban ne

Jan Trollyn yayi ya nufi ƙofa zai fice

Ganin haka itama Ɗahira sai ta fito ta biyo shi, tana fita ta ganshi tsaye bakin ƙofan, sai tayi saurin jan Trollyn ta tayi gaba

Shi kuma komawa ciki yayi rai a haɗe ba tare da ya kalle ta ba, jin ƙai ya hana sa furta komi bare ya saka ta taje ta kashe kayan wutan gidan, ya gummaci shi yaje yayi da ya furta mata

Har ɗakin ta sai da yaje ya kashe komi na na’ura, sannan ya fito, ya rufe gidan ya nufi parcking space, inda Ɗahira ke tsaye tsakankanin motan ta da na shi; rana sai faman gasa ta take yi, dayake ba inuwa a wajen, sai faman jan tsaki take yi cike da takaicin sa, “don me ya saka ta ta fito sannan ya shanya ta a waje ya koma ciki? Miskilin mutumi kawai”. Ta sake jan dogon tsaki tana ɗago kai, sai ta ganshi gab da ita yana taho wa, da sauri ta ɗauke kai daga kallon sa duk da shi ba ita yake kallo ba, amma sarai yaji tsakin da tayi, shiyasa ya sake tamke fuska kamar hadarin kaji, irin ba mutuncin nan

Boot ya buɗe ya saka Trolly ɗin sa, sannan ya bar shi a buɗe ya shige motar sa

Hakan yasa itama Ɗahira ta saka nata a ciki, sai ta rufe ta zo tayi tsaye a gefen motan tana tunanin inda zata shiga

Horn ya danna mata da ƙarfi, dole yasa ta buɗe gaba ta shige tayi zaman ta, shi kuma yaja motan yayi bakin Gate Yana sake cin magani, sai dai miskilanci ya hana sa tanka wa bare ya faɗa abinda ke ransa

Ita kuwa duk a takure take da ganin su waje ɗaya cikin mota, tunda hakan be taɓa faruwa ba

Haka zalika shima hakan yake ji, shiyasa ya ke tsula gudu shaf-shaf suka kai, don kawai ya ƙosa ta fice masa a mota.

Suna kai wa airport wani abokin Usman ɗin ya zo ya tarbe su, shi Usman ɗin ya saka yayi musu komi da za su buƙata, ko passport da za’a yi wa Ɗahira sai dai ya samo picture ɗin ta a wayan Fadil.

Jira kaɗan suka yi aka kira su, suka shiga jirgin. Kujeran su na side ɗin juna ne, ita tana ɓarayin dama a kujeran hanya, sai wata a gefen ta a lungu. Shi kuma yana gefen hagu ne a lungu, shima yana tare da mace ce a gefen nasa. A haka jirgin nasu ya tashi ba tare da magana ta sake shiga tsakanin su ba, tamkar ma dai ba tare suke ba, domin babu wanda zai ce ma suna da alaƙa da juna in ba kaman da suke yi ne zai tona asirin su ba.

Ɗahira lumshe idanun ta kawai tayi ta jinginar da kanta saman kujeran, ba yau ne karon farkonta na hawa jirgi ba, shiyasa bata nuna ƙauyanci ko wani tsoro ba, sabida ita ɗin wayayyiya ce, lokacin da suka gama secondary School gaba ɗayan su yaran gidan Kaka ya biya musu kuɗin hajji suka je suka sauke farali.

Ɗahira ko kaɗan bata ji daɗin tafiyan nan ba, domin baƙin cikin ta bata yi sallama da su Abbu ba, ya kamata ace ya bari sun dawo kafin su tafi, amma kuma babu hali, but tun farko da ya faɗa mata da wuri tun jiya ya kamata taje cikin gidan tayi wuni tare da yin ma kowa sallama cikin natsuwa. Amma kuma Allah ya haɗa ta da murɗaɗɗen mijin da babu me iya saka shi bare hana shi, ita gaba ɗaya ma tsoro ya kamata don bata san me zai faru ba idan suka je inda babu kowa nata, yanda yake da baƙin halin nan bata san ya zaman nasu zai kaya ba.

 

 

 

 

.

 

 

_To mu ma zamu bi ku muga ya za’a kaya. Shin wani irin zama zaku yi a can ɗin? Meye a zuciyar Usman?_

 

_wanda yaga yana da kuɗin jirgi sai ya biyo mu ato, don Ni ba Ni dashi gaskiya, bazan iya biya muku gaba ɗaya ba._ 😜🤣🤣
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR’S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER’S ASSO*📖
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA’S FAMILY*_

.

*EPISODE Forty One*

Kafin jirgin su ta sauka, tuni Ɗahira da Abokiyar zaman ta sun zama ƙawaye, domin sosai suka sha hira a tsakanin su, inda har suka yi sauyin number, Ɗahira ta amshi Numban nata cikin takarda kasancewar babu wayan ta a hannu

Ita yarinyan ne ma ta rubuta mata a wani memo ta bata, sai ta kwashe nata cikin wayan ta. Matashiyar budurwan wacce zata yi sa’anni da Ɗahira, tana karatu ne a can Turkey, kuma tana zaune ne wajen Sister ɗin ta dake aure a can tare da Mijin ta, sunan ta Zakeeya. Kasancewar ƙasa ɗaya za su je shiyasa hiran nasu tayi tsaho har suka zama kamar sun san juna.

 

Jirgin na sauka a ƙasar Turkey, cikin birnin Istanbul, sallama suka yi akan za su nemi juna bayan sun natsa, in yaso sai su san muhallin juna su riƙa ziyartar junan su, duk da ita Ɗahira bata sanar mata asalin abinda ya kawo ta ƙasar ba, hasali ma ko ce mata su biyu ne tare da Mijin ta bata sanar mata ba

Koda suka sauka jirgi ma, ita Zakeeyan ta soma mata sallama ta wuce, har tayi mata tayin tafiya a motar su, amma tace, “a’a suna tare da wani ne”. Da haka suka yi sallama.

Ɗahira jan Trollyn ta tayi ta isa inda Usman ke tsaye yana tare Taxi, shi be ce mata komi ba duk da ya ga yarinyan da suke ta hiran, motan kawai ya hau, itama ta shiga baya suka zauna waje ɗaya, babu me motsin kirki cikin su har suka isa muhallin Usman ɗin, Plate ne gidan ƙarami na zaman mace ɗaya, kuma mallakin Usman ne, tunda anan ya sauna lokacin da yake aiki.

Fita suka yi suka shiga gidan, Ɗahira na biye dashi ita dai tana ta kallon abubuwan burge wa, gaba ɗaya anguwan ya tafi da imanin ta, shiru babu wani hayaniya, zai yi wuya ka haɗu da mutum ma, dama ita Ƙasar Turkey Yana ɗaya daga cikin ƙasashen dake matuƙar burge ta, musamman mutanen ciki ma’abota addinin musulunci, da shigan da suke yi.

 

 

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

Tunda Hajja Fatu ta dawo tacid da mummunan labarin nan na tafiyan su Ɗahira ƙasar waje, sai hankalin ta yayi mugun tashi, domin bata da labari ko kaɗan, ko su su Big Dady da suka sanar wa matan su da safe Kaka ya faɗa musu, lokacin sun je gaishe shi. To sai suka dawo suka sanar wa matan su, yayinda Abba kuma ya wuce Hospital, tunda ya san cewa Hajja Fatu tuni ta tafi asibitin, kuma da ya je can be samu ya sanar mata ba har sai da suka dawo, lokacin su ma sun ji labarin har sun tafi, sai sukai musu fatan alkhairi kawai.

Kai tsaye ɗaki ta wuce sanda Abba ya sanar mata a parlour ya fice, wayan ta ta ɗauka jiki na rawa ta kira Ƙawar ta Hajiya Sa’ima, nan take shaida mata abinda ke faruwa

Itama Hajiya Sa’ima baƙin ciki kamar ya karta, ta ma kasa yin magana

Hajja Fatu tace, “yanzu ji be abinda ke faruwa, mu da muka je neman taimako waje Malam ya hautsina musu zaman auren, daga ƙarshe ya yi mata sakin wulaƙanci, amma kin ga sakamakon tafiya ma suka yi, ta ya idan ya tsane ta daga yin aure zai ɗauke ta wai fita hutun amarci, anya kina ganin aikin Malamin nan yana ci? Ki duba fa ki gani, ita kanta Mahaifiyar ta da na saka ayi min aiki a kanta, shiru kake ji babu wani hayaniya a tsakanin su da zai nuna min suna faɗa”.

Ajiyan zuciya Hajiya Sa’ima ta sauke, kana tace, “Wlh nima abinda nake tunani kenan, amma kuma Wlh Ni na yarda da aikin Malamin nan tabbas yana ci, sai dai kuma idan akwai maƙarƙashiya ce, ke da kanki kin ce itama uwar ba zaune take ba, to kin ga baza muyi mamaki ba da abinda za mu gani, amma Ni nan nake ganin aikin Malam, duk da Ni ban taɓa zuwa wajen sa ba sai a wannan lokacin, ƙawata da nake raka wa ina ganin yanda take watayawa a gidan mijin ta, kuma kin san kishiya ce da ita, amma yanzu tuni ta bar gidan duk sabida aikin da Malam yayi mata, yanzu ita take juya gidan, duk abinda tace shi Mijin nata yake yi”.

“To yanzu ya kike ganin zamu yi?”

“Ai zama be gan mu ba, koma mishi zamu yi, idan ma akwai matsala a sake sabon aiki, domin muddin kika zauna ke ruwa sai sha”.

Hajja Fatu tace, “haka ne. Amma ki bari zuwa gobe idan na fito aiki sai mu je”.

“To shikenan Allah ya kai mu rai da lafiya”.

Da haka sukai sallama. Inda Hajja Fatu ta miƙe ta nufi sashin Hajiya don sake jin ƙwaƙwaf tare da zigin da ta saba.

Oh Allah ya raba mu da halin Hajja Fatu, HASSADA mugun ciwo.

 

*********

Hajiya Sa’ima kallon ɗiyar ta Zeena tayi, tace, “kin gani ko? Dama nace zata kira Ni, amma kuma maganar tafiyan nan nasu ya girgiza Ni fa”.

“Hmm Mama ke ya girgiza ko Ni? Wlh baki ji yanda ƙirji na yake suya ba da jin zancen”. Cewar Zeena tana kumbura fuska kamar zata yi kuka

“To ki kwantar da hankalin ki, ai yanzu za’a sake sabon aiki, kin ga mun yi da Malam dama in sake karkato ta ta dawo, to ga shi ita da kanta ta neme Ni, duk kuɗin da zata bayar ayi wa uwar aiki, sai a mayar dashi kanki, zai miki aikin da shi da kanshi Usman ɗin sai ya zo ya duƙa yana kuka ki aure sa, ita kuma matsiyaciyar can (tana nufin Ɗahira) watan wahalan ta ne ya kama, da ƙafan ta zata gudo saboda azaba, daga nan kin ga shikenan tana dawowa iyayen suka san halin da ake ciki za su ce ya sake ta, kin ga burin mu ya cika, da zaran ya sake ta ke kuma zaki bayyana a wajen sa kamar yanda Malam yace, faƙaɗ”.

Dariya Zeena ta saki tace, “Wow har kin sa naji Daɗi Mama, Wlh ina mugun son Bawan Allan nan, muddin ban aure sa ba to mutuwa zan yi”.

“Ba ma za’a kai da haka ba ɗiya ta, aure babu fashi dake dashi, idan har Ni mahaifiyar ki ce, to, Wlh ko zan yi yawo tsirara ne sai na cika miki burin ki. Ke kaɗai ce fa dani, idan ban miki ba wa zan ma?”

Farin ciki ne sosai ya cika Zeena, tana ji a ranta da kalaman Maman ta tamkar ta cika burin ta ne, “waiii! Wa ya ganta gidan Dr. Usman Noor Al’ameen, a gaskiya sai ta zuba ruwa a ƙasa tasha ranan don murna. Hohoho!”.

 

 

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

Itama Ayush ta shiga tashin hankali jin labarin tafiyan su Usman wani ƙasa, su da suke burin raba auren don me zai tafi ya ɓata musu aiki? Ga shi ba su ji sakamako ba a kan Hotunan da suka tura masa, duk da suna kyautata zaton aikin su yana yi, amma kuma tafiyan nan ya rusa mata gaba ɗaya lissafin ta, dole ta nemo Safra ta sanar mata komi

Itama kanta Safran abun ya girgiza ta, domin tun sanda suka biya wani saurayi yayi musu aikin haɗa hoton nan suka aika, sai ta koma Zaria school ɗin ta, shiyasa bata san wainar da ake toya wa ba, duk da suna waya da Ayush ɗin, but bata taɓa tunanin shirin su zai ƙi tasiri a ƙanƙanin lokaci ba, ga shi kuma tsaban rashin samun nasara har tafiya suka yi tare, a ranta tana tunani “an ya ma Usman ɗin ya buɗe hotunan ya gani?” Domin ta tabbatar babu namijin da zai ga matar da zai aura a wannan mummunan yanayin be rabu da ita ba, ko da son ta shi ne ajalin sa ƙariƙon mamaye masa zuciya.

Ce ma Ayush ɗin tayi, “ta shirya idan ta samu lokaci ta zo Zarian su je wajen Malamin, tunda dama ce musu yayi “idan aka yi auren alokacin ne zai raba, ita kuma Ayush ta shiga”. To yanzu tunda aikin su be yi ba za su koma masa, da fari ma ya soma saka soyayyar Ayush ɗin a zuciya tun wuri Usman ɗin ya san da ita, kafin a raba auren.

Washe gari Ayush shiri tayi da wuri ta wuce Zaria, domin ko wajen aiki ba ta jin zata iya zuwa idan bata je ta san matsayan ta ba.

Koda ta sauka masaukin Safra, sai da ta huta taci abinci sannan suka ɗauki hanyar da zata fito da su Zaria, daga nan kuma suka karya kwana har zuwa gidan Malam

Suna isa bakin Bukkan yayi musu iso zuwa ciki. Bayan sun zauna sun kai gaisuwa wajen sa

Ya amsa yana bin su da kallo, sai yace, “kun dawo kenan?”

“Eh Malam.. yanzu aikin muke so sosai Malam, Dan Allah ko nawa ne zamu biya domin kayi mana aikin me kyau”. Cewar Ayush cikin damuwa

Dariya ya saki yace, “kee yarinya dama wa yace miki ba na aiki da kyau? Ki ajiye kalaman ki wataƙil zai miki amfani a can gaba amma ba anan ba”.

“Ran Malam ya huce”. Cewar Safra tana ɗaga masa hannu alamun jinjina

Be ce komi ba ya soma musu aiki, sai can kamar mintuna 20 ya dube su yace, “ina ga aikin nan fa yana da sauƙi a waje na, amma a wajen ki yana da wuya, idan kuma kika aiwatar da abinda nace miki; tamkar shan ruwa ne zaki same shi”. Sai ya ja numfashi yana miƙo mata wani baƙin kwalba, sannan yaci gaba da cewa, ” riƙe wannan zaki je ki zuba jinin farkon saduwa dake da za’a yi, idan kin zuba sai ki nemi gashin kansa da naki sili ɗaya kacal, ki ɗaure su waje ɗaya, sannan ki saka shi cikin jinin, idan kika yi haka to sai ki dawo min da kwalban, Ni kuma zan saka aljanu su kai min tsaunin da mutane ma ba sa shiga, za su birne shi a ƙasan teku. Daga ranan babu wata mace da zai taɓa so idan ba ke ba, ke har mahaifiyar shi sai da amincewar ki zai nuna mata so, ke kaɗai zai ƙaunata kamar hauka, kuma daga ƙarshe Son ki shi ne ajalin shi. batun kuma rabuwa da matar sa, da zaran kin aikata abinda nace auren su zai warware”. Hhhhh ya ƙare maganar yana ɓaɓɓaka wani mahaukacin dariya

Daga Ayush har Safra tsimi suka yi suna kallon sa, babu wacce tafi ruɗe wa sama da Ayush, domin kalaman Malamin ba kaɗan ba ya gama hautsina ta

Safra tace, “amma Malam kamar ya ka ce “Son ta zai zame mishi ajali?”

Dariyan ya kuma saki, kafin yace, “ki adana kalaman ki har sai kin ga irin mahaukacin ƙaunar da zai mata, a nan ne zaki gane tabbas son ta shi ne zai zamo ajalin sa”. Ya ƙare maganar yana ci gaba da dariyan sa

Sai alokacin Ayush ta ɗan ƙifta idanu, kamar ta dawo daga duniyar tunanin da ta tafi, cikin rashin kuzari tace, “amma ban gane ba Malam, idan mun yi aure da shi ne zan samu jinin bayan ya kusance Ni Ko kuwa?”

“Ba shi nake nufi ba, taya zaki aure sa idan baki aikata abinda nace miki ba? Bari kiji; yarinyan dake tare dashi tamkar wata garkuwar shi ce, akwai bala’o’i da yawa da ake jifan sa dashi, amma kuma albarkacin ta yana zuwan masa da sauƙi, ya rage naki ki je duk wajen wanda zaki je ya kusance ki baya ga shi”.

Zata sake magana Safra ta katse ta da faɗin, “to babu damuwa Malam, insha Allahu zaka ji mu ako yaushe, yanzu ba ya gari, za mu ɗau lokaci kafin mu sake dawo wa”.

Gyaɗa kansa kawai yayi yaci gaba da surƙullen sa

Sai Safran ta kalli Ayush ta raɗa mata “ta fito da kuɗin a ba shi”.

Babu musu ta zuge jakan ta ta fito da kuɗin ciki gaba ɗaya, dubu ɗari biyu ne, ta ajiye masa

“Ranka ya daɗe! Ga kuɗin, muna godiya sosai”.

Ɗago kai yayi ya kalli kuɗin, sai kuma ya kalle su yace, “za ku iya tafiya. Fatan Nasara”.

Tashi suka yi suka fice, inda babu me magana har sanda motan su ta fito daga hanyar ƙauyen suka hau titi

“Yanzu Ni ya zan yi? Kai na ya ƙulle Wlh, ta ya zan aikata Zina abun da ban taɓa yi ba? Sannan kuma taya zan je gidan sa ba da budurci na ba?”

Dariya kawai Safra tayi, sai dai bata ce komi ba taci gaba da tuƙin ta

Hakan yasa Ayush ta sake kallon ta tace, “kin yi shiru? Don Allah ki bani shawara, ga kuma wani babban aikin; wai tsigo gashin kansa, mutumin da ba shi a ƙasa, ko yana nan ma ta ya zan tsigo gashin sa?”.

A wannan karon ma dariyan Safra ta sake kwashe wa dashi, sai kuma tace, “ashe har yanzu baki waye ba? Wlh duk ɗauka na ke fa bugaggiyar wayayyiyar nan ce”.

Sake juyo da kanta sosai Ayush tayi tana kallon ta, sai dai ta kasa cewa komi

“Ke yanzu don kawai yace miki ki je ki kusanci wani shi ne ya zama abun tashin hankali? Ina ga fa ba abun ɗaga hankali bane, kuma gashin kansa duk yanda za’a yi mu samo ai dole ne zamu samo, sai dai dole sai mun bari ya dawo nan, sabida ko mun je can bamu da dabaran da za mu iya aiwatar wa bare mu samu, amma anan akwai hanyoyi da dama, kar ki damu ƙawalli zan taimaka miki har sai burin ki ya cika, tunda jini na ya haɗu dake Wlh ko me kike so zan taimaka miki, ki share batun nan, duk sanda aiki ya tashi da zaran ya shigo gari zan haɗa ki da alhazawan da sai kin jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya, domin sai wanda ranki ya kwanta dashi zaki darza, sannan kuma uhmmm kuɗin da zaki samu ko? Hhhhh ba’a magana, Allah lokaci ɗaya zaki faso gari, daga ranan ma kin samu sana’ar yi, ke da kanki zaki koma neman su, ga ki kina auren The Young handsome Guy, ga kuma kuɗi ya zauna miki, kin zama Hajiyan kan ki, Allah zaki ce na faɗa miki”.

Shiru Ayush tayi a wannan lokacin ma, sai dai tana kallon Safran, tambayar dake yawo a ranta “ita meyasa bata nemi mazan ba sai ita zata haɗa ta da su?” In fact ma ta sha jin tana cewa “Maza ba sa burge ta” sannan ma bata taɓa jin tayi maganar namiji ba in ba yanzu ba, ashe tana da alaƙa da su? Duk da tasan Safra ƴar gata ce tana wadaƙa da kuɗi, amma bata san muhallin da zata ajiye ta ba, iyayen ta ne masu kuɗin? Ko kuma samari take bi suke ba ta? Shi ne bata sani ba.

 

 

 

.

 

_🤷 Ni ma dai ban sani ba, amma bari fans su baki amsar ki, don na san su akwai su da tunanin hasasowa. 😂_
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR’S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER’S ASSO*📖
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA’S FAMILY*_

*TUNATARWA*
”’Manzon Allah mai tsira da aminci, ya yi mana bayani a kan sallah da abin da Bawa yake iya samu. Cewa ya yi, “Yana yiwuwa mutum ya kawo sallah ga baki ɗayan ta amma a ba shi lada wadda ba ta wuce sudusin ta ko ushurin ta ba.” Abin da yasa haka kuwa shi ne  rashin nutsuwa cikin sallah.
Allah yasa mu dace.”’

.

*EPISODE Forty Two*

Kyakykyawar parlor’n tabi da kallo, a ranta tana ayyana tsantsan kyawun sa da tsaruwan sa, duk da ba kaya ne me yawa a ciki ba, saboda kun san yanayin tsarin tura wa, basu cika saka karikitai kamar mu a gida ba, amma haɗuwar sa sai kin yi kamar zaki zubar da yawu tsaban kallo. Hotunan sa ne har guda uku a ƙusurwa-ƙusurwa na ɗakin, babu me cewa shi ne sai idan ka yi masa kallon tsab, sabida mugun haɗuwar da yayi, tamkar dai ɗan ƙasan; ba ɗan Nigeria ba, uwa uba ga shi da skin irin nasu, ga kyawu da ya haɗa, ga kuma kayan da ya saka duk nasu ne.

Ɗahira ta saki baki tana kallon Parlor tamkar wata ƴar ƙauye. Sai jin takun takalman sa tayi daga bayan ta, da sauri ta waiga tana kallon sa

Ba ita yake kallo ba, da alamu ma har ya shiga ɗakin sa, duba da har ya cire rigan saman Jikin sa; yana sanye da Singlet da dogon wandon da ya zo da shi, fuska babu walwala ya nemi wuri ya zauna a ɗaya daga cikin tsararrun kujerun parlor’n

Ɗauke kai tayi tana haɗiyar yawu a hankali sabida jin maƙoshin ta ya bushe, tsayuwan taci gaba da yi a inda take, tunda be ce mata ga inda zata shiga ba, sabida ba wani ɗakuna ne da yawa a gidan ba, daga ɗakin sa sai irin sa na baƙi, sai kuma kichen me haɗe da store har biyu da ƙofa ta baya da zai kai ka Garden ɗin gidan, sai kuma Toilet a parlor’n guda biyu shima.

Tana nan tsaye ya ƙi ya ce mata komi, dole ta ajiye wani ƙyaliya nata ta kalle sa tace, “ina ne ɗakin da zan zauna?”

Uffan be ce mata ba, ya ci gaba da latsa wayan sa, har sai da ta cire rai da zai yi magana, sannan ya ce, “baki da muhallin zama a gidan nan, taimako ɗaya zan miki”. Sai ya ɗago kai yana kallon ta, hakan yasa suka haɗa idanu, kallon kallo kawai suke wa juna, ko wanne na cike da juriyan kallon ɗan uwan sa, domin yanda gaban su ke wani irin bugawa a tare sai ka ɗauka suna jin bugun zuciyar junan su, shi nashi har da wani tsoro ne ya mamaye sa, wanda duk idan dai ya kalli ƙwayan idanun ta masu Colour’n nan, to sai hakan ya ziyarce shi

Wani irin ɗaure fuska ya sake yi, sai tayi saurin sad da kanta ƙasa, domin itama ta kasa ci gaba da kallon sa

“Ga lungu can, nan zaki riƙa kwana”. Ya nuna mata wajen kichen da hannun sa, sannan ya ci gaba da magana, “ko a parlor’n nan ban yarda in ga ƙafafun ki ba”.

Sosai zuciyar Ɗahira ke suya da maganar nan nasa, sai dai ta kasa cewa komi illa sake duƙar da kanta da tayi, take hawaye suka soma sintiri a saman kyakykyawar fuskar ta sabida jin rainin hankalin sa da baza ta iya ɗauka ba, “wai me yake nufi ne? Ni ce zan riƙa kwana a can kamar almajira?”

Shi kuwa tuni ya miƙe ya shige cikin ɗakin sa, ko a jikin sa. Wanka ya shiga yayi ya soma rama sallolin da ake bin sa. Tunda kwana suka yi a hanya.

Tamkar gunki haka Ɗahira ta ƙafe a inda ya bar ta, ko motsin kirki ta gaza yi, lumshe idanu kawai tayi hawayen ta na ci gaba da zubo mata. Har ya fito tana nan tsaye a wajen bata jirga ba

Kallon ta kawai yayi ya taɓe baki, sai da yaje kichen ya haɗa tea kafin ya dawo cikin parlor’n, zama yayi yana harɗe ƙafafu, sai ya ɗauki wayan sa ya soma latsa wa yana sipping coffee ɗin.

Babu daɗe wa aka yi Nocking a bakin ƙofan, sai ya bayar da iznin shigo wa

Wani matashi ne ya shigo, shi ne me kula masa da gidan, kuma shi ne ya gyara gidan tun da ya kira sa yace “zai zo” har girki shi yake masa

Gaishe sa yayi bayan da ya durƙusa a gaban sa alamun girmamawa

Cikin miskilanci tamkar bazai yi maganar ba ya amsa mishi, kana ya ƙara da cewa, “daga yau ka zauna ka huta, ina da me aiki”. Yayi maganar cikin turanci

“Ok sir thank you”.

“You can go”.

“Ok sir”. Ya sake faɗi yana me miƙe wa tsaye ya fice.

Ɗan ɗago kai yayi ya kalli setting da Ɗahira take, sai ya taɓe fuska yana ci gaba da sipping coffee ɗin sa, kamar shuɗewar mintoci a ƙalla goma, ya ajiye Cup ɗin a saman table, kana yaci gaba da latsa wayan sa. Daga ƙarshe ma kwanciya yayi saman kujeran yaci gaba da abinda yake yi.

Yanda ƙafafun ta ke zugi nan da nan suka soma rawa sabida gajiya, dole ta janye ƙafafun ta ta isa inda ya nuna mata, ajiye Trollyn ta tayi a wajen, sannan ta buɗe ƙofan da take kyautata zaton Toilet ne, ta shige. Zama tayi a ciki tasha kukan ta ma’ishi, kana ta share hawayen ta tare da ɗauro alwala. Tana fitowa babu shi cikin parlor’n, ƙarisa wa tayi wajen Trolly ɗin ta ta zuge ta ciro Hijab, sannan ta zare gyalen da tayi Trollyn dashi ta saka Hijab ɗin, cikin parlour’n ta ƙarisa ta soma sallah saman tattausan carpet ɗin dake shimfiɗe a wajen, rama sallolin da ake bin ta tayi. Har ta idar ta soma kwararo addu’a tana kai wa Allah kukan ta, bayan ta ida sai ta shafa tayi zaman ta a wajen, ta jima tana zaune a wajen ga zafi ya ishe ta, dayake ba’a kunna masa Gen ba, sai ta tashi ta cire Hijab ɗin ta ninke, ta nufi Trolly ɗin ta taja shi zuwa ɗakin kusa da nashi, sai dai a kulle yake, hakan yasa ta tsaya tana tunanin mafita, domin baza ta iya kwana a inda ya nuna mata ba tamkar wata almajira, ko bata da gata sai haka

Juya wa tayi ta mayar da akwatin, sannan ta shige Toilet ɗin, wanka take son Yi Amma babu ruwa me zafi tunda babu wuta, sai ta fito ta nufi kichen inda taga ya bi ɗazu, tana shiga kuwa ta sami komi a dai-dai, ta kunna gas ta matsa ruwa a famfon kichen ɗin; ta ɗaura. Sai da yayi zafi ta sake tare da sirka wa, har ta koma ta shige Toilet bata sake jiyo motsin sa ba, wanka tayi ta fito. Ta duba kayan ta cikin Trollyn ta ta koma Toilet ɗin ta saka, riga da skert ne ƴan kanti, sun yi mata kyau sosai sun lafe a jikin ta, kasancewar bata da jiki

Ta rasa yanda zata yi da kayan da ta cire, sai ta fito dasu ta ninke ta mayar cikin akwatin nata, janyo akwatin tayi ta nufi cikin parlour’n, tayi zaman ta kan kujera, sai dai gaba ɗaya tunani ya addabe ta, ga yunwa da ta soma ji, amma rashin jin daɗin yanayin yasa baza ta iya girki ba.

Tana nan zaune kamar mintuna 20, sai ta jiyo buɗe ƙofa, sai dai bata motsa ba tunda ta san shi ne

Kallo ɗaya yayi mata ya ɗauke kai, ba tare da ya ce komi ba ya sanya ƙafan sa ya fice, a ransa yana murmushin mugun ta, “tabbas zai koya wa yarinyan nan hankali, bata san waye shi ba har yanzu. Nan gaba ko yace kar tayi wani abun; to baza ta tsallake umarnin sa ba”.

Tana ganin ya fita, sai kuma ta tashi ta nufi kichen ɗin, dube-dube ta hau yi, wasu abubuwan duk bata taɓa ganin su ba, amma dayake tana karanta wa sai ta gane amfanin su, nan tazaƙulo indomie ta dafa, daga mai sai gishiri ta saka, saboda duk sauran kayan girkin su ba iri ɗaya bane, ta san ko da ta saka ba daɗi za su yi mata ba, sai dai a hankali zata soma gwadawa ta ga ko zata iya ci, amma yanzu yunwa take ji baza ta zauna tayi abinda baza ta iya ci ba.

Tana gama wa ta fito Parlor tayi zaman ta tana ci, sai da ta gama sannan ta koma ta wanke komi ta mayar muhallin sa, still ta sake koma wa Parlour tayi zaman ta, tunanin rayuwa kawai take yi tare da kewar gida, ga shi babu waya a hannun ta bare ta sa ran zata kira su, shiyasa ta yanke shawaran yana dawowa zata ce “ya bata wayan ta”, tunda dai ba nashi bane.

Ganin duhu ya soma yi ta duba agogon hannun ta taga magriba tayi, sai taje tayi alwala ta dawo, ta tayar da sallan ta, tana idar wa ta duƙufa addu’a, ta jima a wajen har lokacin isha’i yayi, ta gabatar. Ga duhu ko ina dole ta soma jin tsoro, tunda ba inda ta saba da shi ne ba, nan ta ƙudundune a kujera ta rufe idanun ta ta hau karatun Alqur’ani a hankali da muryan ta me tsananin daɗi, a haka har ta soma jiyo motsin buɗe ƙofa, tayi shiru tana buɗe ido tare da kallon wajen

Usman ne ya shigo riƙe da wayan sa yana haska wa, tunda ya shigo ya ƙyalla hasken kanta idanun sa suka sauka cikin nata idanun, yanda ya ga idanun suna wani ƙyalli sun sauya kala sai yayi saurin ɗauke kansa gaban sa na matsanancin faɗi, rufe ƙofan kawai yayi ya nufi ɗakin sa, domin so yayi tun yau ya soma mata tijara, amma ganin ƙwayan idanuwan ta bazai iya zuwa ba

Yana shige wa ta rufe idanun ta, “wai da gaske dai mutumin nan be da imani anan zai bar ta ta kwana?” Tafaɗa a ranta. Numfashi taja ta gyara kwanciyar ta tana sake ƙudundune wa, bata sake motsi ba illa tunani da take ta faman yi, sai daga baya ta samu barci daƙyar ya sumfice ta.

Washe gari ta farka a makare, ƙarfe 07:00am. A lokacin, shaf-shaf tayi alwala ta gabatar da sallan ta, ta zauna nan tana ta lazimin safe, sai da gari yayi haske sosai kafin ta miƙe ta nufi kichen, a tunanin ta ko ya fita ne tunda bata ji motsin sa ba, ga shi har sha biyu tayi, amma haka nan ta soma haɗa musu Breakfast har da shi, ruwan tea ta haɗa sai arish da ta soya, ta kwashe ta kai saman dainning, ta zo ta sake duba kichen ɗin ta ɗauko kayan haɗa tea ɗin, duk ta kai kan dainning ɗin. Sai da taje tayi bruch kafin ta zo ta haɗa tea ɗin ta sha da arish ɗin, tunda babu ko bread bata gani ba

Bayan ta gama ta tashi ta je ta ɗaura ruwan zafi, yana ɗumi ta sake tayi wanka ta shirya a Toilet ɗin, yau ma riga da skert ta saka na kanti, rigan t.shirt ne me gajeren hannu ja, ta zauna mata ɗas ta yi mata matuƙar kyau, sai ta saka skert Robber light green, irin me tsagin nan ta baya, sai da ta ɗan yi kwalliya kaɗan tunda sabon ta ne, gaskiya tayi mugun kyau matuƙa, musamman yanda take kyakykyawar nan. murmushi kawai tayi tana zaro siririn gyale ta yafa a kanta zuwa wuyan ta, sai ta zauna a kan kujera, a ranta tana tunanin ko ta tashi ta gyara parlor’n ne?

Buɗe ƙofan da Usman yayi na ɗakin sa, shi ne yasa ta ɗago manyan idanuwan ta ta sauke a kanshi, tare da dakata wa daga miƙewan da tayi ninya

haka zalika shima kallon ta yake yi, lokaci ɗaya ya ɗauke kai yana cin magani, da alamu dai fita zai yi saboda a cikin shirin sa yake

Takowa yayi ya isa wajen kujerun

Duƙar da kanta tayi kawai tana jin gaban ta na faɗuwa

“Keee”. Yayi maganar a maƙoshi yana ja

Ɗago kai tayi tana kallon sa, yanda ya tsare ta da ido da fuskar sa tamkar hadarin kaji, daga gani ba mutunci a tare dashi, hakan yasa ta ɗauke kai itama tana shan kunu, domin bata san da me ya zo ba

Zama yayi be sake cewa uffan ba, don be san ma ta ina zai fara ba tsaban miskilanci, ga shi matsanancin haushin ta yake ji, tare da sake jin tsanar ta me ƙarfi a ran sa, “ko uban wa zata yi wa kwalliya?” Ya faɗa a ransa yana sake kallon ta

“Ki tashi ki je ki ɗauko min Trolly ɗin ki”. Yayi maganar tamkar ba shi ba

Sai da ta kalle sa kafin kuma ta ɗauke kai tana me mamaki. Amma bata ce komi ba ta miƙe ta nufi wajen kayan ta, janyo wa tayi ta kawo masa har gaban sa

“Buɗe shi”. Ya sake bata umarni

Ita dai bata ce uffan ba sai mamaki da ke son kashe ta akan “me zai yi mata da kaya?”

Tana buɗe wa ya sake ce mata “ta fito da duk komi dake ciki”.

Hakan kuwa ta sake yi

Ɗaya bayan ɗaya ya saka ta tana ɗaga kayan, don shi bazai iya saka hannun sa ya taɓa kayan ta ba

Idan ta ɗaga sai ya ce “ta ajiye gefe,” wani kuma yace “ta mayar cikin akwatin”. Karkatakaf sai da ya gama zaɓe ƙananun kayan dake ciki, sai atamfa da Abaya kaɗai da yace ta zuba cikin akwatin

Ita dai duk yanda yace tayi hakan take yi, arziƙin ta ɗaya bata biye wa miskilancin sa ta fito da under-Wears ɗin ta ba, da yanda ya saka take ɗai-ɗai da kayan ta; da ta sha kunya

“Waɗannan kaɗai kike da damar saka wa a gida na, nan ba gidan karuwan ki bane da zaki zo kina saka min ƙananan kaya, and daga yau aikin gidan nan gaba ɗaya ya dawo kanki, ko ina na cikin gidan nan kullum Ina son ki share shi tsab, ko alamun datti ba na son gani, zan bar miki keeys ɗin ɗakunan, kuma daga yau inda nace ki koma nan zaki koma, kar in sake ganin ƙazantaccen jikin ki ya zauna min a cikin parlor. sauran aiki ya rage naki, ki bi ko kar ki bi, idan ba haka ba zan baki mamaki Wlh”.

Tun sanda ya soma magana ta ɗago kai tana kallon sa, sakin baki kawai tayi tana bin sa da ido domin mamakin sa ma ya kusa kashe ta. Ganin yana shirin tashi tace, “ban gane me kake cewa ba fa? Ni fa matar ka ce ba baiwar ka ba. fine naji aikin gidan zan yi tunda dama aiki na ne, amma meye haɗin ka da kaya na da sai ka zaɓa min waɗanda zan saka? Kuma da kake cewa ba gidan karuwai na bane, amma ai naga Gidan Mijina ne, kuma idan ma nayi karuwancin iyawa ne, kasan da haka ka aure Ni, so ba abun damuwa bane”.

Sosai yayi mamakin furucin nata

Ita kuwa ƙarfin hali ne ta azawa kanta har ta iya faɗan waɗannan kalaman, domin ba ƙaramin tsoro ne cike a zuciyar ta ba, amma kuma tana gani idan har taci gaba da shiru ba ta mayar masa da amsa, tabbas ya samu damar kullum yana sakar mata magana yana cusa mata baƙin cikin sa.

Kallon ta yayi da idanun sa da suka soma sauya kala, domin maganar nan ma da yayi me yawa ba ƙaramin dauriya yayi ba, amma kuma tsaban rashin mutunci irin nata take maida masa martani, “ke nan baza ta bi umarnin sa ba?” Ci je leɓen sa yayi yana bin ta da kallo, sai kuma ya ɗan saki guntun murmushi yace, “me yi ba ya faɗa, don Allah idan kin cika ke ƴar uban ki ne, ki tsallake umarni na”.

Sosai ranta ya ɓaci da zagin uban ta da yayi, sau biyu kenan hakan ke faruwa. Shiyasa cikin ɓacin rai da baƙin cikin sa tace, “ba dai uba na ba wlh, domin ya fi ƙarfin ka har da zaka zauna kana zagin sa..”

Bata ajiye numfashi ba ya ɗaga hannu ya falla mata marin da sai da taga taurari suna shawagi a idanun ta, ɗif tayi kawai ta dena gane abinda ke duniyar.
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR’S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER’S ASSO*📖
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA’S FAMILY*_

_SAƘON GAISUWA GARE KU MASOYA NA *Usman Aliyu Ahmad, Adama Aliyu, Nana Aliyu, Prencess Teema, Maryam Muh’d, Hafsah, Amina Umar Abdullahi, Zainab Muh’d Hussain, Fatima Bintu Muh’d, Sadiya, Asma’u, Lawisa, Rahma,* da ma waɗanda ban lissafo su ba, duk ina gaishe ku, kuma ina godiya da soyayyar ku gare Ni._

.

*EPISODE Forty Three*

Bata gama dawowa duniyar gigitan da ta shiga ba. ya duƙa a gaban ta ya shaƙo mata wuya, cikin ɓacin rai yace, “idan har na sake magana kika mayar min da martani makamancin haka, Wlh sai na binne ki da ranki a gidan nan, idan kin isa ke tatacciyar mara kunya fitsararriya ce ke, ki sallake umarni na, zaki ga yanda zan yi biji-biji dake a gidan nan..” sai ya datse harshe ba tare da ya gama faɗin abinda yake son faɗa ɗin ba, miƙe wa kawai yayi bayan da ya dungurar mata da kai. Har ya taka zai fice, sai kuma ya dawo yana kallon ta da ɗaurarriyar fuskar sa da ba mutunci, cikin tsawa yace da ita, “biyo NI da kayan nan”. Ya nuna kayan ta dake zube a ƙasa

Ɗahira da gaba ɗaya duniyar ta juya mata sabida tsaban gigicewan da tayi da marin da yayi mata, tuni hawaye sun gama wanke mata fuska, tana me riƙe da kumatun ta da ta kasa saki. A tsorace ta tashi tabi umarnin sa kamar yanda yace mata ɗin, domin gani take yi kamar zai sake mata marin nan da yayi mata, ko kuma fiye ma da hakan, domin ko kaɗan bata ga alamun ɓurɓushin imani a tare da shi ba.

Kai tsaye cikin ɗakin sa suka wuce, inda ya nuna mata cikin wardrobe ɗin sa ta zuba kayan, sannan ya rufe da keey ya ɓoye keey ɗin

Ita tuni ta fice da gudu ta isa inda ya nuna mata makwancin ta, wani irin rushewa da kuka tayi tana me haɗa kai da gwiwa ta soma rera wa, zuciyar ta na wani irin tafarfasa da ƙara jin tsanar Usman a ranta.

Shi kuwa tuni ya nufi ƙofa ya ficewar sa, ya kulle ta ta waje, domin ya san cewa zata iya guduwa, tunda ita ba yarinya bace, kuma ita ba jahila bace.

Kuka sosai Ɗahira take yi kamar ranta zai fita, gaba ɗaya idanun ta sun juye sun yi jazur sun kumbura, haka ma fuskar ta da inda ya mare ta ya kumbura suntum, sai shatin yatsun sa da suka fito raɗo-raɗo, haka fuskar ya sauya kamanni, abun ku da farar mace ya sake yin ja

A zuciyar ta babu abinda take yi sai Allah wadai da shi, tare da ƙara rura wutar tsanar sa.

Har dare Ɗahira na zaune a wurin tana ta kuka, babu abinda ke tashin ta sai Sallah, kuma duk idan tayi sallan sai ta roƙi Allah ya saka mata, ya kuma fitar da ita cikin hannun sa, sosai zazzaɓi ya rufe ta saboda kukan da ta sha, nan ta nannaɗe da zani tana ta rawan ɗari.

Usman kuwa be dawo ba sai wajen sha biyu, kuma ko kallon inda take be yi ba ya wuce ɗakin sa.

A haka Ɗahira ta kwana a mawuyacin hali.

Washe gari haka Usman ya tsallake ya bar gidan ba tare da ya damu da ya bi ta kanta ba

Wannan abun ya tabbatar mata da cewa, tabbas Usman ba shi da ɓurɓushin imani, be da ɗigon imani ko kaɗan, kuma ba zai taɓa tausaya mata ba, duk da tana jin jiki, amma hakan be sa ta ƙi bin umarnin zuciyar ta na guduwa ba. Sai dai kash bata san cewa ya rufe ƙofan ba, tunda ta jijjiga yaƙi buɗuwa ta hau rusa kuka kamar ranta zai fita, nan wani sabon ciwon ya sake kama ta, da ƙyar ta isa ɗakin sa ta hau dube-duben inda zata samu keey, amma duk ta duba babu, dole ta zo ta kwanta a makwancin ta, taci gaba da kukan ta.

A ranan ma sai dare Usman ya dawo

Sanda ya shigo, daƙyar ta iya buɗe idanun ta da suka yi mata nauyi tsaban ciwo tana bin shi da kallo, dayake akwai hasken NEPA, ko motsin kirki a lokacin ba ta iya yi, hawaye kawai ke tsiyaya a face ɗin ta. Ganin zai wuce ɗaki be kalli inda take ba, sai ta buɗe baki murya na rawa tace dashi, “Please.. Please.. help.. me”.

Kallon inda take yayi, sai ya kawar da kai ya shigewar sa ɗaki, ko kaɗan be ji tausayin ta ba, illa ma manta shafin ta da yayi yaci gaba da harkokin sa.

Ita kuwa tuni ta sake sakin wani sabon hawayen me tsananin raɗaɗi da baƙin ciki, “Allah gani gare ka! Allah kai ne gata na, Allah ka fitar dani hannun wannan azzalumin”. Kuka kawai taci gaba da yi a wannan halin da take zaton mutuwa zata yi, domin azaban da take ji baki ma bazai iya faɗa ba. Daga ƙarshe ma da jikin nata ya sake rikice wa, sai ta hau kwarara amai daga kwancen da take, amai kawai take kwarara wa kamar zata zubar da hanjin cikin ta, domin kuwa babu komi a cikin nata, babu abinda taci tun marin da yayi mata jiya

Yanda take kwarara aman har ɗakin sa sai an ji, amma dayake tuni yayi barci be ma san tana yi ba

Tuɓus jikin ta yayi, wanda tuni ta fita a hayyacin ta, tamkar dai ba ta numfashi haka ta koma. A haka har washe garin Allah yayi.

 

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

*NIGERIA*

Kamar yanda Hajja suka tsara za su koma wajen Malam, sun koma, inda ya sake musu sabon aiki bayan ya caska kuɗin sa wajen Hajja, “aikin dai a ƙara rura wutar tsanar da Usman yake yi wa Ɗahira ne, a haddasa musu rashin zaman lafiya, kullum ya riƙa ganin ta kamar baƙar kumurci, babu abinda zai riƙa shiga tsakanin su illa cin mutunci da zagi, daga ƙarshe ya koro ta da sakin wulaƙanci”, inda ta sake bayar wa aka yi mata aiki akan Aunty Amarya, sai dai suna baro wa wajen, Hajiya Sa’ima ta koma ta sauya sabon aiki, kuɗin da za’a yi wa Aunty Amarya aikin, ta saka aka yi wa ɗiyar ta, sannan ta ƙara masa kuɗi me yawa, a haka suka rabu akan zai yi mata aikin da Usman da kansa zai zo wajen ɗiyar ta neman auren ta, ba shi da wata mata a duniya illa Zeena

Hajiya Sa’ima ta tafi tana farin ciki, ta koma gida ta ba wa ɗiyar ta labari. Nan itama ta hau murna da farin ciki, tana ganin burin ta nan ba da jima wa ba zai cika.

***********

A fannin su Kaka kuwa, sun soma shiga damuwa da jin har yanzu Usman be kira ya sanar musu saukar su ba, haka ma Aunty Amarya da Abbu sun fi kowa damuwa, saboda jin shiru daga ɗiyar su, babu wani waya, ga shi duk an kira layin su be shiga, Numban da Usman ɗin ke amfani dashi idan ya je can an kira shima ba ya shiga

Kaka duk ya ɗaga musu hankali, abu kaɗan yace, “har yanzu Matata bata neme Ni ba?”.. “Shin matata ta kira kuwa? Ko kuma Fodio be kira ba?”.. ga shi a lokacin jikin sa duk ya ƙi daɗi, shiyasa suke dangana wa ga zafin ciwo ne, saboda yanda ya matuƙar damuwa akan “yana son jin halin da Ɗahira take ciki”

Babu yanda za su iya su Big Dady, sai dai kwantar masa da hankali da suke yi, suna ƙara ba sa haƙuri a kan “za su kira, ƙila wani abun ne ya dakatar da su”.

 

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

*TURKEY*

Fitowar sa kenan daga ɗaki cikin shirin sa na kamar kullum, idanun sa akan ta suka faɗa, hakan yasa ya tsayar da saka link ɗin rigan sa da yake yi yana sake kallon ta, lokaci ɗaya sai ya ɗauke kai yana jin wani tuƙuƙin baƙin ciki na shigan sa, tare da wani tashin zuciya na taso masa, sakamakon ganin ta cikin amai da yayi. Rasa me ma zai yi yayi, sai kuma ya taka ya nufe ta tamkar zai haɗiya zuciya ya mutu tsaban baƙin ciki, yana zuwa inda take ya sanya ƙafa ya tokare ta yana faɗin “Keeeee” cikin tsawa

Sai dai bata san ma yana yi ba, domin tuni ta sume ba ta ko numfashi

Ganin bata motsa ba, sai ya mayar da idanun sa kanta yana noƙe hanci har da saka hannu ya toshe hancin nasa, sake tokarin ta yayi, sai ya ga alamun ba ta numfashi, tsaki yaja me ƙarfi yana juya wa ya shiga Toilet ɗin parlour’n, ruwa ya ciko cikin bucket, yana fito wa ya sheƙa mata a jiki

Lokaci ɗaya ta kawo wani irin numfashi a matuƙar firgice tana kiran sunan Maman ta

Ƙafa ya saka ya taka nata ƙafan Yana murzawa

Wannan dalilin ne yasa ta dakata daga kiran sunan Maman ta da take yi; sakamakon zafin da ya ziyarce ta, nan ta buɗe idanun ta da suka gama rine wa suka yi wani irin kore tamkar dai ba na ɗan adam ba, saboda yanda ƙwayan idanun nata suka kasance ba baƙi ba, ta zuba masa su kamar zata cinye sa

Hakan yasa lokaci ɗaya tsoron da ya saba ji ya tsarga masa fiye da yanda yake ji a ko wani lokaci idan ya kalle ta, nan ya janye idon sa tare da ƙafan sa ƙirjin sa na faman dukan uku-uku

Ita kuwa kuka ta fashe da shi da ɗan sautin muryan ta da ya rage mata, sosai take kuka wanda ke fita a hankali yana yi yana ɗauke wa

While shi kuma yana jin kamar ana sake tsaga zuciyar sa ne ana ƙara masa wutar tsanar ta, kukan nata na shigan kunnen sa kamar wuta, yana sake jin wani tuƙuƙi a zuciyar sa tare da wani nauyi, ji yake yi tamkar idan be mata dukan tsiya ya ɗaiɗaita ta a lokacin ba, bazai samu sukunin zuciya ba, sai dai kuma ko kaɗan ba ya son sake kallon inda take, hakan yasa ya juya ya nufi ɗakin sa da sassarfa yana kame kansa da ya soma sara masa

Lumshe idanun ta tayi tana jin wani irin zafi dake ruruwa a ko ina na sassan jikin ta da zuciyar ta, yayinda take jin numfashin ta na son ɗauke wa, hakan yasa ta buɗe ido tare da ƙwalalo su waje tana sakin nishi da sauri da sauri, tamkar wacce tayi tseren gudu ko me athma, yanda take fizgar numfashin kamar zata shiɗe, lokaci ɗaya kuma ya fizge mata ta sake sume wa gauu…

 

****

Shi kuwa yana shiga ɗakin sa ya zauna bakin gado yana riƙe da kansa, abinda yake ji a zuciyar sa baki ma bazai iya misalta shi ba, gaba ɗaya ya yamutsa gashin kansa ya rasa sukuni, idanun sa kuwa duk sun yi jazur kamar an yi masa duka, lokaci ɗaya ya saki kan nasa ya miƙe a firgice ya nufi ƙofa zai fice…

 

_babu yawa. Manage Please._
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR’S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER’S ASSO*📖
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA’S FAMILY*_

.

*EPISODE Forty Four*

Yana sake koma wa wajen ta ya ga alamun ta sake sume wa, juya wa kawai yayi ya sake ɗibo ruwa ya watsa mata

Hakan yasa ta farfaɗo numfashin ta ya dawo, sai dai idanun ta suna rufe ta kasa buɗe wa, illa kuka da take yi ƙasa-ƙasa tana riƙe da kanta, sai faman rawan sanyi take yi haƙoran ta na karkarwa

Ko kaɗan ba ya jin zai iya taimaka mata saboda zallan tsanar ta da yake ji a ransa, juya wa ya sake yi ya koma ɗakin sa, magani ya ɗauko mata ya zo ya jefa mata, cikin kausashshiyar murya da zaka gane yana a cikin ɓacin rai, wanda daƙyar ma maganar take fita yace da ita, “ki gaggauta tashi ki gyara min gida. Kar in dawo na ga baki gyara nan wajen ba, kar na dawo baki cire min ƙazantar nan naki ba na maimaita miki.. “sai yayi shiru yana juya wa ya yi waje ya fice

Ɗahira bata motsa ba tana nan yanda ya bar ta, illa kuka da take tayi, sosai take kukan har da su shashsheƙa, ta rasa meyasa Usman ya tsane ta, mene ne tayi masa a rayuwa da yake nuna mata wannan zazzafan tsanar? Tana a cikin halin mutuwa ko rayuwa amma shi ko kaɗan ba ya tausayin ta, shin yaushe ne zai tausaya mata? Har yaushe ne zata fita a cikin wannan uƙuban nashi? Me yake nufi da ita ne? Idan so yake yi ya kashe ta meyasa bazai kashe ta a lokaci ɗaya ba sai ya gana mata azaba haka? Ba ta jin zata iya yafe wa Bawan Allan nan, har ABADA! Baza ta taɓa yafe mishi ba domin ya cutar da ita.

Ta shafe fiye da awanni uku bata iya motsa wa daga inda take  ba, sabida ko kaɗan bata da ƙwarin jiki, ga tsananin ciwon da take fama dashi, amma don kar ya dawo ta fuskanci wulaƙancin sa, tana kuka ta yunƙura ta tashi daƙyar, jikin ta gaba ɗaya ya tsume sai karo da haƙori take yi tana ƙanƙame jiki, hawayen nata ma sun kafe illa kukan zuci kawai da take yi, daƙyar da jan jiki ta isa Fridge ta sanya hannu ta buɗe ta ɗauki ruwa, maganin da ya ajiye mata ta ɗauka tasha ko don wai zata samu sauƙin ciwon da take fama dashi, sai ta sake rarrafa wa ta isa inda gaba ɗaya ruwa ne sharkaf da aman ta a wajen, kallon wajen take yi tana tunanin ta ina zata fara, baza ta taɓa iya wa ba saboda zazzaɓin da take fama dashi, daga ƙarshe zube wa tayi nan ta dinga sheƙa wani aman, ga tsananin yunwa dake addabar ta, jikin ta sai faman rawa yake yi, majinu na tsiyaya ta hancin ta

Sake rarrafa wa tayi ta kwaɓe kayan jikin ta gaba ɗaya, ta sauya wani rigan daƙyar, rufe kanta tayi ta ƙudundune tana ci gaba da rawan sanyi, gaba ɗaya duniyar tayi mata zafi ta rasa inda zata saka kanta, addu’a kawai take yi a ranta Allah ya kawo mata mafita, tunda take bata taɓa shan wahala makamanciyar irin ta yau ba. Runtse idanun ta tayi tare da tamke bakin ta zuciyar ta na ƙuna, duk second ɗaya tsanar Usman na sake ruruwa a ranta, tana jin har abada baza ta taɓa yafe masa ba, sai Allah ya saka mata.

Wasa-wasa har dare Ɗahira tana cikin wannan mawuyacin halin, ta kasa taɓuka komi, a haka ta wuni zurr komi bata saka a cikin ta ba, ta kasa ma tashi bare ta samu abinda zata saka a cikin ta, tana jin sai dai ya kashe ta domin baza ta iya yin komi ba.

A haka ya zo ya tarar da ita zaune cikin ruwan aman tana ta rawan sanyi. Tunda ya shigo ya sauke idanun sa a kanta ya haɗe giran sama dana ƙasa yana jin zuciyar sa na sake ƙunci, take ya nufe ta gadan-gadan yana cewa, “baki ji abinda nace miki bane kafin in fita? Ke me taurin kai baza ki yi abinda nace miki ba ko?”

Ta ma kasa yin magana illa kallon sa da take yi, domin ji take yi idan ma ta tanka sa tabbas zuciyar ta zata buga da baƙin ciki, shiyasa ta rufe idanun ta tana jiran abinda zai yi mata

Tsawa ya daka mata yana cewa, “ki tashi ki gyara min gida ko in ci uwar ki a gidan nan”.

Sosai ta tsorata da tsawan da yayi mata, ta zabura zata tashi, sai dai ta kasa sabida rawan da jikin ta yake yi, da zaran ta yunƙura zata miƙe sai ta zame ta bugu a tyles ɗin parlour’n, hakan yasa ta fashe da kuka tana rawan baki, tana son furta masa baza ta iya ba amma ta kasa

Hannu yasa ya janyo ta kiiiiiiiii… ya ingiza ta cikin Toilet ɗin

“Maza ɗauki mopper ki gyara min gida ko in Yi biji-biji dake yanzu”. Ya sake daka mata tsawa

“Me..yasa.. ba ka da tau..sayi ne wai? Me.. me nayi maka.. ne? Ka bar Ni na koma ggida tun..da..” sai ta kasa ƙarisa wa saboda kukan da take yi

Idanun sa jawur ya aza kanta yace, “ai baki ga komi ba daga abinda na shirya miki, Ni dai kika aura ko?” Sai ya karkaɗa kai kafin yace, “Wlh daga ke har waɗanda suka aura min ke sai na sa ku kun yi dana-sani, kamar yanda kika ƙuntata min rayuwa, ke ma sai na ƙuntata miki”. Sai ya juya da ninyan fice wa, har ya fita ya dawo ya sake nuna ta da yatsa yace, “ki gyara min gida a karo na ƙarshe..” ya juya ya fice da sauri. Direct ɗakin sa ya wuce ya shige Toilet, shower ya kunna ya shiga ruwan na zubar masa daga sama zuwa ƙasan shi, zafin da yake ji a zuciyar sa ji yake yi kamar ana ƙara masa icce yana ruruwa, duk da ruwan sanyin dake dakan jikin sa, amma ji yake yi ko kaɗan babu sauƙi, dauriya me dauriya ya gwada yin sa amma ina, kawai sai ya fashe da kuka, domin ji yake yi idan be je ya kashe ta tsaban tsanar da yake mata ba, bazai taɓa sukuni ba, abinda yake ji tun ɗazu kenan amma ya kasa daure wa

Nan tunanin addu’a ya faɗo masa, ya soma lalubo abinda zai faɗa, daƙyar harshen sa yake iya faɗin, “innalillahi wa’inna ilaihi raji’un…” Ya ƙame ƙam a wajen yana ci gaba da karanta wa a ƙasan zuciyar sa, ya daɗe a haka kafin ya soma jin abunda ke zuciyar sa yana lafa masa, daƙyar ya tuɓe kayan jikin sa ya yi wanka ya fito, a haka ya zube kan gadon sabida rasa inda yake masa daɗi a jiki.

Ita kuwa baiwar Allah Ɗahira tunda ya bar ta take kukan ta, sai da tayi ma’ishi kafin ta yunƙura ta tashi, a duƙe- a duƙe ta soma kwatanta aikin ko zata iya, har dare ya tsala tana abu ɗaya, gaba ɗaya ta gama jiga ta, har faɗi take yi tsaban wahala, sai ta tashi taci gaba, aikin da zai ɗauke ta mintoci, sai ga shi ta shafe tsawon daren tana yi, daga ƙarshe ta zube a ƙasa tare da rufe jikin ta, taci gaba da rawan sanyi, bata ko runtsa ba sabida azaban ciwo, a haka safe ya cin mata, zuwa lokacin baza ka taɓa gane Ɗahira ce ba, sabida yanda gaba ɗaya ta zabge tayi wani irin muguwar rama, idanuwan nan nata sun sake fito wa sun koɗe sun yi zawur, dama ga ta ba auki ba haka ta sake sirance wa gunun tausayi, tamkar wata ƙaramar yarinya ce a kwance a wajen

Har haske ya gama fito wa bata iya tashi ba, yunwa ke addabar ta amma ta kasa yanda zata yi ta nemi abinci, jikin ta yayi zauu kamar garwashin wuta, sai karo take yi da haƙora.

A haka Usman ya fito da shirin sa, tunda ya kalli inda take sau ɗaya ya tabbatar da ta gyara wajen, sai ya ɗage kai yai ficewar sa.

Lumshe idanuwan ta kawai tayi tana sake lafe wa a ƙasa, bata san wani tunani ya kamata tayi ba, bata taɓa tunanin akwai wani rayuwa da zata iya shiga har taji tana ƙaunar mutuwar ta ba, sai a wannan gaɓar, tayi dana-sanin amince wa da auren nan, tabbas da tasan irin azabar da zata tarar kenan; da tayi guduwar ta, da dai ace ta zauna da wannan mara tausayin, ko kaɗan bata taɓa tunanin ƙiyayyar da yake mata ya kai har haka ba, da ya gummaci ganin mutuwar ta da rayuwar ta, tabbas yau tana kaico da rayuwar ta da ta kasance a ƙarƙashin maƙiyin ta tana me neman lahirar ta, kuma bata da hanyar da zata iya kufce wa hakan

Sai ta sake fashe wa da wani irin kuka me ban tausayi dake fito wa daga can ƙasar zuciyar ta yake ƙara mata raɗaɗi da ƙunci me ciwo, tuna wa da tayi da iyayen ta, sai dai ga shi tayi musu nisa babu yanda za’a yi ta fita ta koma gare su, suna can ba tare da sun san halin da take ciki ba. Tasha kukan ta ma’ishi babu me rarrashin ta, inda ta wuni curr a kwance bata san inda kanta yake ba, domin kuwa wani sabon zazzafan zazzaɓin ne ya sake rufe ta, abun ka da bata saba da damuwa a rai ba, haka ta wuni zuciyar ta na mata zafi kamar ana soya mata, daƙyar take iya numfashi, har dare kana wani wahalallen barci ya sure ta, wanda be da maraba da suma, domin kuwa gaba ɗaya numfashin ta ba ya fita da kyau, idan ta ja numfashi sau ɗaya; sai ta shafe fiye da second biyar kafin ta sake jan wani.

 

***** ***** *****

Sai wajen ƙarfe 10:40pm. Usman ya shigo gidan, be kalli inda take ba ya wuce kai tsaye ɗakin sa, zama yayi gefen gadon sa yana zare Cumbas ɗin ƙafafuwan sa haɗe da socks ɗin, yana gama wa ya cire wrest watch ɗin hannun sa ya ajiye, sannan ya miƙe ya kwaɓe kayan sa ya shige Toilet, wanka yayi ya fito ɗaure da alwala, sallan isha’i yayi da be samu yayi ba, sai ya koma kan sofa ya zauna yana latsa laptop ɗin sa, har yayi kamar mintuna biyar, ko me ya tuna ya miƙe ya ɗauko wayan sa dake ajiye gefen bed side, ya soma latsa wa, kai tsaye WhatsApp ya shiga yana bincike a kan sakon da Friend ɗin sa ya turo masa, a nan tunanin mutanen gida ya faɗo masa, sai ya ɗan dakata yana kame goshin sa, shaf ya manta da wani kiran gida a rayuwar sa, ga shi har suna son wuce sati ɗaya da barin gida ba tare da ya kira ba, tabbas ya san akwai matsala, domin ya san yanzu haka suna nan sun damu, duba da yanda ba shi kaɗai bane ya taho. Tsaki yaja yana fita daga WhatsApp ɗin, shiru yayi yana tunanin Numban wa zai kira

Still tsakin ya kuma ja tuna wa da yayi ba Numban sa da yake amfani bane a wayan, tabbas ya san sun neme sa ba su same sa ba, Kai tsaye Numban Hajiya ya rubuta ya kira

Tana ɗauka abin da ta soma tambayar sa, “shin ina ya shiga tsawon wannan lokacin be kira su ba?”

Be bata amsa ba, sai ya soma gaishe ta a daƙile kamar yanda ya saba

Amsa wa tayi tana sake jeho masa tambayar farko

Sai yace mata, “wai be samu time bane, sabida ya koma Hospital ɗin da yake aiki yana ci gaba da zuwa har sanda za su dawo”.

Ajiyan zuciya kawai ta sauke, ko kaɗan bata damu ta san halin da Ɗahira ke ciki ba, sai ce masa tayi “to yaushe kenan kake sa ran dawowa?”

“Kamar nan da Two months”.

Dogon tsaki taja, cike da ɓacin rai tace, “wato ta shanye ka shi ne zaka kai har wannan lokacin baka dawo ba? Uwar me kuke yi da baza ka dawo ba sai ka kai lokacin nan?”

Shiru yayi mata be tanka ba

Kamar yanda itama bata sa ran zai tanka ɗin ba, amma sai ta sake cewa, “ina magana kayi min shiru, ko cin amarcin ne har yanzu baka gama ba sai zuwa nan da two months ɗin?”.

“Momy na ce miki aiki na koma shiyasa”. Yayi maganar kamar zai yi kuka

“Mtsww! dalla rufe min baki, meye amfanin aikin tunda ka ajiye? To, Ni ban amince ka kai tsawon wannan lokacin ba, yarinyan da ba ka so meye kuma na zuwa da ita wani waje? Ka gaggauta shirin dawowa tun yanzu domin hutun ya isa haka, kuma ka kira Dadyn ka yanzu domin suna ta neman ka su ma basu same ka ba, ga Kakan ku can har rashin lafiya ya yi amma baka da labari”.

“Ok”. Kawai yace mata saboda be da abun cewa, ba kuma wai don ya yarda zai yi abinda take so ɗin bane na game da dawowar sa

Sallama suka yi, inda ya mayar da akalan kiran ga Mahaifin sa, ringing biyu ya ɗauka, gaishe shi ya soma yi

Amma Big Dady be amsa ba, sai ya fara jeho masa tambaya kamar yanda Hajiya tayi masa, “me ya tsayar dashi tsawon lokacin nan ba tare da ya kira gida an ji sun sauka lafiya ba?”

Be da amsar faɗa masa, illa shiru da yayi

Nan kuwa ya dinga mishi faɗa, ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, sannan daga ƙarshe yace masa “ya ba wa Ɗahira wayan”.

Duk da maganar ta bugi Usman, amma hakan be sa ya nuna akwai wani ruɗe wa a tattare dashi ba, illa gyara murya da yayi ya ce masa, “uhmmm Dady tana barci yanzu haka, sabida nan dare ya soma nisa”

“Ok ka tabbatar gobe idan ta tashi ka haɗa Ni da ita”.

“To”. Ya amsa masa

“Ka kira wayan Kaka sabida yanzu ba na gida bare na faɗa masa ka kira”. Cewar big Dady

Amsa mishi yayi, sannan suka yi sallama. Inda ya kira Kaka. A lokacin Fadil ke zaune dashi tunda jikin nasa da sauƙi, sai abinda ba a rasa ba

Nan Kaka yayi murna da jin suna lafiya, ya tambayi Ɗahira yace, “a bata wayan”

Sai ya faɗa masa yanda yace wa Big Dady.

Koda suka gama wayan tsaki yaja fuska babu walwala, ya ajiye wayan, kasa ci gaba da aikin yayi sabida ransa duk a ɓace yake, ya tashi ya sauya kaya zuwa gajeren wando da Singlet ya kwanta.

*WASHE GARI*

Da safe da ya tashi, zuwa ƙarfe 09:00am. Ya gama shirin sa, ya fito Parlour, inda Ɗahira take kwance ya kalla, sai ya kawar da kai yana tamke fuska kamar an aiko masa da saƙon mutuwa, kai tsaye kichen ya nufa, ya haɗa coffee ya shanye a kichen ɗin, sannan ya fito ya nufi ƙofan fita, har ya buɗe ƙofan; ko me ya tuna ya dawo da baya ya nufe ta

Tana nan kwance kamar yanda ta kwanta tun jiya, tun barcin da ya ɗauke ta a yammacin jiya bata ko motsa ba, kallo ɗaya kayi mata zaka gane tana shan matuƙar wahala, daga gani ba barcin lafiya bane, duba da yanda take haɗa gumi tana fitar da numfashi da ƙarfin gaske, kuma duk da uwar gumin nan da take yi amma hakan be hana jikin ta rawan ɗari ba.

Yana zuwa kusa da kanta, ya sanya ƙafa ya bugi kan nata

Wani irin zabura tayi tana sakin ƙara, lokaci ɗaya ta buɗe shanyayyun idanun ta da suka kaɗa suka yi jazur suka shige ciki tsaban kumburan da suka yi, dafe kanta tayi saboda sara matan da yayi lokaci ɗaya, sai wani jiri da ya kawo mata mamaya lokaci ɗaya ta koma yanda take tana me runtse idanun ta da suka soma ruwan hawaye, ko kaɗan ta kasa buɗe ido balle ta kalli inda yake, duk da kuwa ta san shi ne a kanta sabida ƙamshin turaren sa da ta jiyo, kuma ta san babu wanda zai mata haka sai shi

“Get up and sit down”. Yayi maganar kamar ana masa tilas, sai dai yanda muryan nasa ta fita hakan zai saka ka gane a cikin ɓacin rai yake

Bata motsa ba don bata da ƙarfi ko na sisin kobo, kamar dai an zare mata laka a jikin ta take ji, kamar kuma ana yayyanka naman jikin ta saboda mugun ciwon da yake mata, ga rashin sabo na kwanciyar ƙasa, duk ya bi ya haɗe mata ya saka mata wani irin ciwo me wuyan fassara, ji take yi tamkar dai ta mutu ta huta

Tsawa ya daka mata yana sake bata umarnin tashi

Babu yanda ta iya dole ta soma yunƙurin tashi, hawaye na ambaliya a fuskar ta tamkar ana tsiyayar wa daga famfo, gaba ɗaya jiri take ji, hakan yasa daƙyar ta tashi zaune tana ƙanƙame jikin ta, komi ganin sa take yi bibbiyu, ba ma tasan takamaiman inda yake tsaye ba, domin ba ta gane komi, ga hawayen da ya cika mata ido fal

Shi kuwa wayan sa ya zaro cikin aljihu, sannan ya latsa yana kallon ta yace, “za kiyi waya da mutanen gida, ko kaɗan ba na son ki nuna wani alama da zai saka su gane halin da kike ciki, idan kuwa kika yi haka..” ya ci je ƙasar bakin sa yana sake tamke fuskar sa, “wlh summa tallahi sai na binne ki da ranki a gidan nan, kuma kar kiyi tunanin idan kin faɗa musu kin sha ne”.

Wayan ya miƙa mata bayan ya kira Numban Big Dady, sannan ya bata umarnin ta amsa

Jiki na rawa ta miƙa hannu tana laluba inda zata ji wayan, nan ta cafke wayan da hannun sa

Da sauri ya zame nasa hannun saboda jin wani abu da ya tsarga masa daga kwanyan sa har  ƙafafun sa, har wani ƙanƙame jiki yayi yana lumshe ido saboda jin yanayin abinda da ya kasa fassara mene ne

Ba don Allah yasa ta rigada ta riƙe wayan ba, da tuni tasha ƙasa. Kara wayan tayi a kunne jin muryan Big Dady na faɗin, “Hello.. Hello”.

“Hel..llo.. Daddddy..”. Tafaɗa da wani irin murya tana me fashe wa da kuka lokaci ɗaya.
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR’S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER’S ASSO*📖
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA’S FAMILY*_

.

*EPISODE Forty Five*

Zaro mata ido Usman yayi, lokaci ɗaya ya damke dantsen hannun ta tare da matse wa da ƙarfi yana caka mata ƙumba; ta yanda zata ji zafi

Sosai kuwa taji zafin da har yasa ta saki siririyan ƙara tana hawaye

Sake zare mata idanu yayi yana ɗaura hannun sa saman baki alamun tayi shiru

Kallon sa kawai take yi tana tsiyayar da hawaye ba tare da ta amsa tambayoyin da Big Dady yake jero mata ba, Sai da ya sake kiran sunan ta a karo na uku kafin ta amsa shi tana faɗin, “na’am Dady. I miss You so Much!” Tayi maganar cikin rauni tana ci gaba da hawayen ta

“What’s the matter, daughter? What’s wrong with you? Did I hear you? Did you tell me if there was a problem?”

Still idanun ta suna kallon Usman da ya kasa ya tsare yana mata gargaɗi, gaba ɗaya ya ɗaure fuskar sa alamun babu imani. Hakan yasa taji tsoro sosai, domin ta san ko ta sanar wa Dady dole ne yayi mata abinda yayi ninya, tunda ba kusa suke ba, kafin su koma gida ya gama aiwatar da duk abinda yake so, ƙarshe ma ta ƙara wa kanta uƙuba, don haka sai ta daure still cikin raunin murya na wacce take jin jiki sosai tace,”Daddy, it’s all right, okay,”

“I don’t agree. Let me know if there’s a problem, ko akwai abinda yake miki ne?”

Girgiza kanta tayi kamar yana  ganin ta, wasu sabbin hawayen suna sake sauko mata, murya a matuƙar sanyaye tace, “Daddy I’m not feeling well”.

Big Dady yace, “subhanallah… Garin ya? Ya aka yi be kai ki asibiti ba? Ba shi wayan.. ba shi wayan”.

Bata ce komi ba ta cire wayan a kunnen ta ta miƙa masa, a lokacin sosai wani kukan ya taho mata, sai tayi saurin saka hannun ta ɗaya ta rufe bakin ta tana shashsheƙan kuka me fita da sauti kaɗan-kaɗan, kasancewar ɗaya hannun nata yana riƙe dashi ya ƙi saki sai sake matse mata yake yi, wanda shi tuni ma ya manta da hakan, daɗi da taushin skin ɗin ta ya shagaltar dashi, har ya mayar da abin kamar wasa yana ta faman matsa mata dantse, while ita kuma zafin hakan take ji

Big Dady ce masa yayi, “yayi maza-maza ya kai ta asibiti, idan har be kai ta ba wlh sai yayi mummunan saɓa masa”. Ce masa ma yayi “suna zuwa asibitin ya haɗa sa da doctor ɗin”.

Hakan da Usman yaji ne yasa yace mata “ta shirya su je” da ya gama wayan, sannan ya tashi ya fice

Ita kuma daƙyar ta iya miƙe wa jiri na ɗiban ta, bango ta dafe sannan ta soma bin bangon har ta kai bakin ƙofa, ko bi ta kan ta rufe jikin ta bata yi ba, sabida ba ta cikin hayyacin ta, daga ita sai doguwar rigan less me ruwan Powder, kanta kuma babu ɗankwali illa gashin ta dake ɗaure da ribom baƙi, amma duk ya tuttuge ya mitsitstsike kamar na mahaukata

Tana fita ta tsaya tana faman haki, sabida gani take yi kamar zata faɗi idan har ta rabu da bango, kuma ga shi dole sai ta rabu da bangon zuwa haraban gidan, hawaye kawai take saki tana gunjin kuka

Usman dake cikin mota yana faman jiran ta, nan ya danna mata horn da ƙarfi yana faman kallon ta daga cikin mota, kuma duk a yanayin halin da yake ganin ta hakan be sa ya ji tausayin ta ba, yana gani kamar wannan shi ne dai-dai da hukuncin da ya kamata ya ɗauka a kanta, babu tausayi a tsakanin su bare taimako, ko wani hali take ciki ita ta ja wa kanta

Daƙyar a duƙe- a duke ta soma taho wa wajen motan, sosai ta sake fashe wa da kuka sabida yanda take ji, kafin ta kai motan sai dai ta ƙarisa da rarrafe, sabida ƙafafun ta sun gaza ɗaukar ta, tana isa ta dafe motan sannan ta buɗe ƙofan baya ta shige

Be ce mata komi ba ya ja motan ya nufi kan titi, kasancewar gidan babu Gate sai compound da ƙaramin ƙofa me raga-raga, kuma motan nasa na fake ne a ta wajen ƙofan a ɗan ƙaramin haraban wajen

Ƙudundune wa tayi sosai tana rawan sanyi, coz yanda motan ta ɗau sanyi sabida a.c, sai karkarwa take yi da haƙoran ta tana faman sakin sauti me ƙara

Tsaki yaja a daƙile yace da ita, “ki yi min shiru a wajen nan”.

Tamƙe bakin ta tayi, amma duk da haka haƙoran ta karo suke yi, sai dai sautin na fita a hankali, kuma ya sauya ƙara, tamkar dai wacce aka toshe wa baki tana gunjin ceton rai

Be sake ce mata komi ba har suka kai wani kyakykyawar asibiti da babu nisa da su, fita yayi ba tare da ya tanka ba

Itama sai ta saka hannu ta buɗe ƙofan ta fita, a duƙe take tafiya kamar zata faɗi tana sake sabon hawaye sabida azaba

Shi tuni yayi gaba abin sa

Hakan yasa wata nurse da ta hango ta, ta taho da sauri ta taimaka mata, tana tambayar ta, “are you sick?”

Ɗahira bata amsa mata ba, illa kuka da ta saki me tsuma ran me sauraro, domin tamkar dai jira take yi dama ayi mata maganar; ta fashe da kuka

“Sorry! Sorry!”. Abinda take ta faman ce mata kenan har suka shige cikin Hospital ɗin

Usman dake tsaye bakin wani Office yana jiran shigowar ta, nan ya hange su da nurse ɗin, har ta zo nurse ɗin zata gibta shi domin bata san tare suke ba, sai yace mata “ta tsaya”.

“Doctor are you together?” Cewar nurse ɗin tana kallon sa

Fuska babu fara’a ya ɗaga mata kai yana shige wa cikin Office ɗin

Hakan yasa Nurse ɗin ta taimaka mata suka bi shi ciki tana me mamakin halin sa, duk da kuwa dama sun san haka yake, “they were sick together but he came and left her outside?” Take tambayar kanta a ranta

Suna shiga ciki, Doctorn dake gaisa wa da Usman ya kalle su, sai kuma da sauri yace, “Beha what’s wrong with her?”

“I don’t know Sir, but they seem to be together”.

Sai Doctor ɗin ya kalli Usman yace, “Doctor, are you together?”

Fuska a ɗaure Usman yace, “Yes. I brought her to check on her”.

“Ok. Beha help and calm her down”.

Kamar yanda yace ɗin, haka Nurse ɗin tayi, ta nufi kan gadon dake cikin Office ɗin ta kwantar da ita, sannan ta ɗauki excuse wajen doctor ɗin ta fice.

“Doctor Man amma ya aka yi haka ka bar ta har ciwo ya yi mata zafi haka? daga gani tana shan jiki, kai fa doctor ne”. Cewar Doctor ɗin cikin turanci dake tsaye yana kallon Usman

Gajeren tsaki Usman yaja yace, “Please ka duba ta, ba surutu nace kayi min ba”. Shima ya maida masa da turancin

Doctor ɗin be ce komi ba, illa kaɗa kai da yayi ya nufi gadon da Ɗahira ke kwance, ya san halin abokin sa sarai, shiyasa be yawaita binciken ba ya ƙyale sa. Fara duba ta yayi, duk wani taimako na gaggawa ya bata, domin ya ɗau tsawon mintuna arba’in yana duba ta, inda daga bisani ya ɗaura mata drip ya dawo kan kujeran sa ya zauna, kallon Usman dake ta latsa waya yayi kamar babu abinda ke damun sa a rayuwa, kana yaja numfashi yana ɗaura hannayen sa da ya haɗe su waje ɗaya a saman table ɗin sa, cikin harshen turanci yace, “Amma doctor ya aka yi ka bar pation a tare da kai ta shiga wannan mummunan yanayin baka kawo ta Hospital ba? Yarinyan tana cikin wani mawuyacin hali, zazzaɓin jikin ta yayi tsanani sosai, ga kuma damuwa dake damun ta matsananciya a zuciyar ta, wanda hakan zai saka ta samu matsala, domin idan taci gaba da zama a haka da yawan damuwa a ranta, tabbas komi zai iya faruwa, kuma duk baka ɗau mataki ba, why?”

Ɗago Kai Usman yayi yana kallon sa da fuskar sa kamar kullum, cikin miskilanci irin nasa yace, “wannan be shafe ka ba, tunda ka duba ta shikenan, zaka iya ba mu sallama mu wuce”.

“Sallama kuma? Kana jin fa abinda na faɗa, jikin ta yayi tsanani da yawa sosai Doctor, dole zata zauna a nan har ta warware, baza mu iya bata sallama ba”.

Miƙe wa Usman yayi yana saka wayan sa cikin aljihun wandon sa, kana yace, “fine. Sai ka riƙe ta har sanda ka so, Ni ka ga tafiya na bani da time ɗin ku”.

“But doctor Wai ba ƙanwar ka bace? na ga kun yi kama sosai, amma yanda kake nuna wa kamar da akwai matsala”. Cewar Doctorn cike da mamakin Usman ɗin

Shiru Usman yayi yana kallon sa, sai kuma ya juya zai fice don a ganin sa be da lokacin sa, har ya kai bakin ƙofa sai kuma ya dawo yana ciro wayan sa ya kalle sa, “Please Doctor Shamel I will call my Daddy, he will ask you about this girl, Please and please I don’t want you to tell him anything, just tell him her body is easy “.

Sosai mamaki ya sake cika Doctor ɗin, sakin baki kawai yayi yana bin Usman da kallo cike da al’ajabin halin sa

Miƙa masa wayan yayi bayan ya kira Big Dady

Inda Doctor ɗin ya amsa ya kara a kunne yana me gaishe da Big Dady cike da girmamawa irin nasu

Nan Big Dady yake tambayar sa halin da Ɗahira ke ciki

Inda Doctor ɗin ya sanar masa “da sauƙi jikin nata, zazzaɓi ne kawai ke damun ta”

Hankalin Big Dady ya ɗan kwanta, inda ya roƙi Doctor ɗin “da ya kula da ita sosai, kuma kar ya bata sallama da wuri har sai ta warware sosai”.

Murmushi Doctorn yayi yace, “ok Sir, dama ba yau zan sallame ta ba”.

Daga nan dai sun ɗan sake tattaunawa, inda suka yi sallama. Doctor ɗin ya miƙa wa Usman dake tsaye ya tsare shi da ido wayan sa

Shi kuma ya amsa ya tusa cikin aljihu, be ce komi ba ya juya yayi ficewar sa

Girgiza kai kawai Doctorn yayi a ransa yana cewa, “Dr. Man problems”. Sai ya mayar da idanun sa kan Ɗahira dake barci tana fitar da numfashi a hankali, dayake yayi mata alluran barci ne, da alamun dai ta fara jin daɗin yanayin ta sabida yanda numfashin nata yake fita, kau da kai yayi kanta yaci gaba da aikin gaban sa.

Zuwa dare ta farka, duk da jikin babu sauƙi sosai, amma tunda tana ƙarƙashin kulawar likita ne tafi da, an sauya mata ɗaki ita kaɗai ce.

Da safe ko da Usman ya zo Hospital ɗin ko zuwa duba ta be yi ba, kasancewar asibitin da yake aiki ne

Doctor Shamel har office ya bi sa yana masa maganar Ɗahiran, da kuma yanda ya ga be je ya duba ta ba

Amma Usman ko bi ta kansa be yi ba, ce masa ma yayi “kar ya ƙara masa magana idan har ba sallaman ta zai yi ba”.

Shi dai Doctor Shamel sosai yake mamakin wannan hali na Usman, ya san dai yarinyan tabbas ƙanwar sa ce, duba da yanda suke mugun kama, amma kuma abinda be sani ba “meye ta zo yi nan?” Shi ne abin da ke masa yawo, duk da ya san Usman ɗin ya bar Hospital ba ya aiki, dama yana mamakin dawowar sa da cewan “zai yi two months a ƙasar, that’s why ya dawo aiki kafin ya tafi,” to amma kuma yana kyautata zaton akwai abinda suka zo yi da ƴar uwan tasa. girgiza kai kawai yayi ya cire tunanin a ransa tunda be shafe sa ba. Sosai yake ba wa Ɗahira kula wa, inda take samun sauƙi a hankali

Gefe ɗaya kuma Big Dady ya kira har sau biyu don yaji jikin ta, amma sai Usman yayi masa ƙaryan “tana barci” don yaƙi haɗa su

Abbu ma ya kira tunda Big Dady ya basa Numban Usman ɗin, shima the same haka yace masa, “she was asleep at the time.”

Sanda Big Dady ya sake kira, a lokacin Ɗahira tayi kwana biyu a asibitin, sosai ta samu sauƙi sai dai abinda ba a rasa ba, a lokacin ne Usman yaje har ɗakin nata ya bata wayan su gaisa da Big Dady

Lokacin Ɗahira na kwance ta juya wa ƙofa baya, tana sanye cikin fararen kaya na mara sa lafiyan Hospital ɗin, tunani me zurfi take yi idanun ta a buɗe ta ƙure wa waje ɗaya ido, babu abinda take kitsima wa illa yanda zata gudu daga Hospital ɗin nan a yau

Shi kuwa shigowar sa Direct gaban gadon ya isa, ya tsaya yana bin bayan ta da kallo, sai ya ɗauke kai yana haɗiyar yawu cike da ƙunci a zuciyar sa da ya rasa shi kwana biyu, tamke fuska yayi sosai kana yace, “keee”.

Hakan yasa ta ɗan yi firgigit ta dawo hayyacin ta, sai tayi saurin juyo wa tana kallon sa, sosai ƙirjin ta ya buga saboda kawai sauke idanun ta da tayi a kansa, zuciyar ta nan da nan ta sauya bugu kamar zata faso ƙirjin ta tsaban buga wa da ƙarfin da take yi. Ƙyafta idanu ta hau yi sai tayi saurin janye su daga kallon sa, sakamakon kallon da yake sakar mata da yanda take ji

Shima be ce komi ba illa latsa wayan sa da yayi ya kira Big Dady, ya miƙa mata ba tare da ya ce uffan ba

Ɗan ɗago kai tayi ta kalli wayan, kana kuma ta saka hannu ta amsa tana me kara wa a kunne, a lokacin Big Dady ya amsa call ɗin yana faɗin “Hello Daughter”

Kallon sa tayi ganin yanda ya tsaya mata ƙiƙam kamar zai faɗo mata, sai dai ya mayar da fuskar sa na mara sa mutunci, wanda kamar ƙiris yake jira. haɗiye yawu tayi tana sauke kai ta amsa da “na’am Dady”. Cikin sanyin murya irin na mara sa lafiya

Nan Dady ya soma tambayar ta jikin ta

She replied, “Very easily Daddy, sai dai missing ɗin ku da nake yi”.

Murmushi yayi yace, “kar ki damu Daughter ai kun kusa dawowa, ke dai kawai ki kula da jikin ki kinji? ba na son in sake jin an ce min baki da lafiya, na san halin ki idan kin saka damuwa ne a ranki yake saka ki ciwo, duk idan kin ji wani abu na damun ki just tell your brother kinji?”

Lumshe idanu tayi wasu zafafan hawaye suna zubo mata, lokaci ɗaya ta gyaɗa kanta kamar yana ganin ta, cikin raunin murya tace, “to..” tana datse baki jin kuka na son kufce mata

“Yauwa Daughter, bari in ba wa Abban ki ku gaisa, muna tare da Baba ne (Kaka)”.

“To”. Ta sake amsa wa cike da murna, domin sosai take son jin muryan kowa a gidan su, musamman Maman ta da Abbun ta, tayi kewar su matuƙa

Gaisa wa suka yi da Abba, inda shima ya tambaye ta jikin ta, sannan yayi mata nasiha sosai a kan biyayya ga miji, tare da ƙara haƙuri a rayuwa

Ita dai jin sa kawai take yi, a ranta tana jin kamar ya san halin da take ciki, “ina ma zata iya sanar da su halin da take ciki?” Amma tsoro da fargaba ya hana ta furta abinda take son faɗa

Daga nan Kaka ya amshi wayan, sun jima suna waya, inda take ta mishi shagwaɓa a kan “ita lallai lallai tana son dawowa gida ta gan shi” sosai take kuka a wannan lokacin domin ta kasa tsayar dashi

Usman dake tsaye yana kallon ta, hannu ya saka ya dalla mata a gefen kumatu

Inda ta saki ƙara tana ƙara ɓare baki

Kaka da duk ya ɗauki abin nata kawai tsaban rigima ne irin nata, sai yayi dariya yace, “ki yi haƙuri Mata ta, duk da kina kewa ta amma na san Real Mijin ki ya fi Ni buƙatar ki, ki yi haƙuri har ku dawo kinji? nima nayi kewar ki sosai, ji nake yi kamar in biyo ki nima”. Shima ya ƙare maganar ta sigan wasa

Kuka ta sake fashe wa dashi, tana shirin magana Usman ya ƙwace wayan

Inda ya kara a kunne yana cewa, “wai tsoho meye haka kake saka ta kuka?” Ya ƙare maganar da dalla mata harara

Ita kuwa sake fashe wa da wani sabon kukan tayi

hakan yasa ya saka hannu ya damƙe mata baki tare da hancin ta

Zaro idanu tayi ganin zata shiɗe, nan da nan ta soma kokawar cire hannun sa tana son shaƙar numfashi, amma ina ya saka ƙarfi sosai ya tamke ta yanda baza ta iya ƙwace wa ba, sai uhmmm.. uhmmmm take yi tana dukan hannun nasa, tare da sake ware idanun ta dake tsiyayar hawaye sosai

Tsaki yaja yana sauraron Kakan dake masa tsiya, a daƙile yace, “kar ka cinye min kuɗi na sai an jima”. Ya katse kiran ba tare da ya jira cewar sa ba. Maida hankalin sa yayi kanta yana kallon ta da fuska a ɗaure, sai kuma ya janye hannun sa yana sake sakar mata wani banzan kallo

Ita kuwa cikin kuka tace, “wai don Allah me nayi maka da zafi haka da kake son kashe Ni? Idan har ka tsane Ni ne meyasa baza ka ɗauki wuƙa ka daɓa min ba a kan wahalan da kake ba ni?” Cikin tsawa ta sake cewa, “ka sake Ni mana tunda ba ka ƙauna ta, wlh nima ba na son ka ko kaɗan, I hate you more than anyone in this world! Sai Allah ya saka min bazan taɓa yafe maka ba! I hate you so much USMANNN”. Ta ƙare maganar da wani irin kuka me ban tausayi

Sosai ransa yayi mugun ɓaci da maganganun da ta faɗa masa, ba kaɗan ba yaji ɗacin yanda take kallon ƙwayar idanun sa take sanar masa ba ta ƙaunar sa, “ita wace ce da ta isa ta kalle sa ido cikin ido tace masa ba ta ƙaunar sa” a zuciye ya saka hannu da ninyan cafke mata gashi, sai wayan sa ta soma ƙara, wanda hakan ya dakatar dashi yana bin wayan da ido

Mahaifin ta ne ya kira, sai ya ja dogon tsaki yana daka mata tsawa.

💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR’S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER’S ASSO*📖
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA’S FAMILY*_

.

*EPISODE Forty Six*

“Wlh idan baki rufe min baki ba sai nayi ƙasa-ƙasa dake a nan, bar ganin kina kwance a nan sai na ɓalla miki ƙasusuwa, mahaifin ki zai yi magana da ke, idan kika sake kika yi wani motsin da zai sa ya gane wani abu.. uhm wlh I will teach you a lesson”.

Cak ta tsayar da kukan nata jin ya kirayi mahaifin ta, da sauri jikin ta na rawa ta kai hannu ta amshi wayan da yake miƙo mata, muryan mahaifin ta taji ya doki kunnen ta, sai ta lumshe idanu tana me tsiyayar da hawaye, cike da sanyin murya take gaishe sa zuciyar ta cinkushe da kewar sa

Nan ya tambaye ta jikin nata?

Ta amsa mishi tana faɗin, “taji sauƙi sosai”. Kana ta soma jero masa tambayan “ina su Maman ta da su Umma? Har Fadil sai da ta tambaya”

Abbu yace mata, “babu su Fadil kusa, amma ga Maman ta su gaisa”.

Jin muryan Maman ta sai ta fashe da kuka tana me kiran sunan ta

Daga can Aunty Amarya tace, “har yanzu dai kin kasa girma ko? Kukan na mene ne?”

“Nayi kewar ku ne sosai Mama, don Allah ki saka baki ya dawo dani”.

Aunty Amarya ta gane wa take nufi, sai tace mata, “ke baki da baki ne? Duka-duka yaushe kuka tafi? Idan kin yi haƙuri nan ba da jima wa ba kamar yau ne za ku dawo, Allah ya muku albarka baki ɗaya”.

“Amin Mama”. Ta amsa ta tana me share hawayen ta da bayan hannu

Daga nan Aunty Amarya sallama tayi mata

While Usman ya amshi wayan sa, sai da suka yi magana da Abbu kafin ya kashe wayan. Ya dube ta fuska a tamke yace, “tashi mu je”.

Ko kallon sa bata yi ba, illa sake haɗe kai da gwiwa da tayi ta saki wani Marayan kuka, domin wayan nan da suka yi ba ƙaramin fama mata zuciya yayi ba, sosai take kuka kamar ana yanka ta, har wani shashsheƙa take yi

Hakan yasa ran Usman yayi mugun ɓaci, ya daka mata tsawan da ya razana ta lokaci ɗaya

A dai-dai lokacin ne Doctor Shamel ya shigo ɗakin, da mamaki yake bin Usman da kallo, sai yace, “what’s going on?”

“Ka bamu sallama zamu wuce gida yau”.

Murmushi Doctor Shamel yayi, cikin harshen turanci yace, “my friend ban da abun ka ka barta mana ta samu sauƙi, ka ga har yanzu da sauran rashin lafiya a tare da ita”.

Usman be kalle sa ba ya saka hannu ya riƙo nata, jan ta ya soma yi dole ta sauko a kan gadon tana ci gaba da kuka

Dr. Shamel yace, “Oh Man, leave her. Don’t hurt her. You see her crying. Maybe it’s her body.”

Shi dai be saurare sa ba tuni yayi waje da ita, be sake ta ba har sanda ya isa da ita motan sa, ya buɗe mazaunin gaba ya tura ta ciki, sannan ya rufe ya saka lock

Babu abinda Ɗahira take yi sai kuka tana me tsine masa a zuciya, har ya koma cikin asibitin ya dawo bata dena kukan ba

Yana shigo wa ciki ya daka mata gigitacciyar tsawar da dole ta ɗauke kukan cak a lokaci ɗaya

Be yi magana ba ya kunna motan ya nufi bakin Gate, sosai zuciyar sa take masa ƙunci, gaba ɗaya jin sa yake yi babu daɗi, yanda yayi ta ɗaga mata murya yana mata tsawa sai duk hakan ya saka masa ciwon kai, hakan yasa ransa ya sake ɓaci matuƙa, a wuya kawai yake yana jiran yayi maganin ta

Sai dai Allah be sa ta sake ko ƙwaƙƙwaran motsi ba, illa ajiyan zuciya da take ta sauke wa idanun ta a lumshe, yayinda ta ɗaura kanta saman cinyoyin ta.

Suna isa gida tana jin ya tsayar da motan ta ɗago kai, sai ta buɗe motan ta fice da sauri, tana jin sanda ya ja dogon tsaki amma ko bi ta kansa bata yi ba, haka ta nufi ciki da sauri, sai dai dole ta tsaya har sai da ya zo ya buɗe ƙofan, jefa mata magungunan ta yayi dake cikin leda, sannan ya buɗe ƙofan, sai da ya tasa ƙeyan ta ciki kafin shima ya shiga

Tuni ta isa wajen kayan ta ta nemi wuri ta zauna saboda har yanzu tana ɗan jin jiri

“Ki gyara min gida tunda ke ƙazamiya ce, daga yau ba na son in sake ganin baki yi aikin da ke kanki ba, sannan wankin kaya na suna nan ki wanke min su na zuba miki a kan gado na, akwai igiyar shanya cikin Toilet ɗina ki shanya a ciki”. Yana gama maganar yayi waje ya fice, tare da rufe ta ta waje

Lumshe ido kawai tayi tana me jingina bayan ta da bango, sosai ranta ke suya sai dai babu yanda ta iya, ta san haka zata ƙare da uƙuban sa har sanda Allah zai yi su koma, “yau har akwai ranan da wani zai iya buɗe baki yace mata ƙazamiya?” Sai ta ɗan yi murmushin da yafi kuka ciwo tana me buɗe idanun ta, babu yanda zata yi dole ne tayi masa abinda yace, ko da kuwa wani ciwon ne zai kama ta, domin dai ta san wulaƙancin da zata fuskanta sai yafi halin da take ciki.

Sai da ta ɗan samu hutu sosai, kana ta tashi ta shiga kichen, tea ta haɗa me kauri ta zo ta buɗe magungunan ta, inda ta cire Waɗan da zata sha, ta shanye da tea ɗin, sannan ta miƙe ta wuce ɗakin sa, gaba ɗaya babu ƙarfi a jikin ta, amma haka ta daure ta kwashe wankin da ta gani a saman gadon, Allah yasa ba masu yawa bane, ta nufi Toilet da su, akwai engine machine a ciki, amma ko da ta gwada yi a ciki ya ƙi yi; domin ya lalace. Sai ta cire ta saka a bucket, komi na buƙata akwai a wurin, haka ta zauna ta wanke masa tas har Singlet da ƙananan wanduna, zuciyar ta na tafarfasa har ta gama, shanya masa tayi kana ta fita ta je ta kwaso nata ta wanke a Toilet ɗin, sannan ta shanya a Toilet ɗin Parlour, tana gama wa ta gyara masa ɗakin sa, duk da babu datti sai dai gadon da ya yamutsa

Bayan ta gama ta share Parlour ta Yi moping, zuwa lokacin gaba ɗaya ta gama gajiya, kamar dai wani zazzaɓin ne ke son kama ta; tunda bata gama warke wa ba, zama tayi ta huta sannan tayi alwala ta gabatar da sallan azahar, kasancewar sauran sallolin da ake bin ta duk tayi su a Hospital, sai ta ɗan kishingiɗa zuwa sallan Asar.

Sai biyar ta farka, nan kuwa ta sake jin daɗin yanayin ta, wanka tayi tare da Sallah, ta shiga kichen ta yi ma kanta girki sannan taci ta koma tayi shimfiɗa ta sake kwanciya, tana nan tana tunani har magriba tayi, sai da tayi sallah kafin ta soma muraji’ar Al’ƙur’ani, da kai take yi domin bata san inda zata samu ƙur’ani ba, dayake akwai hasken NEPA ko ina, hakan yasa ta ɗan ji daɗin zaman bata ji tsoro ba, sai da aka yi isha’i kafin ta kwanta tayi lamo, yanda tunani ya cika mata zuciya sai ta tashi zaune ta ɗauko ruwa ta sha magungunan ta, sannan ta haɗa dana barci da aka saka mata, sai ta koma ta sake kwanciya, babu daɗe wa barci ya sure ta, dama haka tafi so domin ba ta ƙaunar ya dawo ta ganshi.

Sai goma na dare kamar yanda ya saba dawowa ya dawo, be bi ta kanta ba ya shigewar sa ɗaki, shima shirin barcin sa yayi ya kwanta abin sa.

 

*WASHE GARI*

Sai da ta bari ya bar gidan kafin ta tashi tayi wanka ta shirya cikin riga da skert na atamfa, sai ta saka Baby Hijab ta shiga kichen, Breakfast tayi wa kanta taci ta koma ta zauna, yanda ta ga babu abinda take yi sai zaman banza da tunani, hakan yasa tayi ta karatun Alkur’ani, kasancewar ta ba ma’abociya son kallo ba, ko kaɗan be dame ta ba, idan har ba wani ya kunna ta zo wurin ba, to ko kaɗan ba ta bi ta kai bare ta tuna dashi

Kuma zaman gidan ma yayi mata daɗi tunda Usman ba ya zama, sai hakan ya saka ta farin ciki ainun, gwara kar ya dawo tayi ta zama ita kaɗai da ta ganshi a cikin gidan.

 

 

 

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

 

*NIGERIA*
Fitowa tayi daga ɗakin majinyata na yara, kai tsaye ta nufi Office ɗin Hajja Fatu

Ita kuma a lokacin tana shirin fita daga Office ɗin nata

Safna tayi saurin dakata wa tana me ce mata, “Dr yaron nan fa ya farka, yanzu time ɗin ba shi maganin sa ya yi, kuma na duba lockern gadon sa babu komi”.

Tsaki Hajja Fatu taja, tana bin Safnan da harara tace, “ke dai wlh baza ki taɓa sauya wa ba, ban san wani irin yarinya ce ba, common dalla shige ki ɗauka ga yi can, Ni Bani da time ɗin ki”. Da gama faɗar hakan; sai ta wuce ta tafi

Murguɗa baki Safna tayi tace, “kai wannan Matar kullum jaraba, bazan sauya ba ko baza ki sauya ba? Ni ban san me na tare miki ba wlh”.

A Haka Safna take ta mita a ranta har ta ciro maganin cikin wani kwali da ke ajiye tsakar Office ɗin, domin ta duba ma’ajiyar maganin bata ga komi ba, tana buɗe kwalin sai ta ga kamar shi ne, bata tsaya bincika wa ba tayi waje da sauri. Kai tsaye ɗakin yara ta wuce, inda ta je kan wani yaro dake kwance magashiyan Mahaifiyar sa na riƙe da shi, haɗa maganin tayi ta ba shi, sannan tayi masa alluran da ta haɗo dashi, kana tayi wa matar sallama ta wuce gadon gaba, duk sai da ta tabbatar babu wani matsala kafin ta fito ta nufi Office ɗin ta, haɗa kayan ta tayi tunda lokacin tashi yayi, tana fito wa ta wuce Lifter tayi downstairs. A reception suka kusa cin karo da Baffa, tayi saurin matsa wa tana ba shi haƙuri

Be bi ta kanta ba ya yi waje abin sa, motan sa ya hau ya bar Office ɗin, gaba ɗaya idan ka kalle sa duk ya gama sauya wa, tamkar ba shi ba, yanzu kwata-kwata ba ya da fara’a, be son yawan yin magana bare dariya, wuni yana kaɗaita kansa yana faman tunanin Ɗahira, har yanzu yayi iya yin sa ya kasa cire ta a rai.

Yana zuwa gida kai tsaye ɗakin sa ya wuce ya buɗe ya shige

Ƙaran buɗe ƙofan nasa ne ya janyo hankalin Sa’adatu dake zaune a ɗakin ta, sai ta fito ta nufi ɗakin nasa kanta tsaye, domin yau so take yi ayita ta ƙare; ta gama gajiya

Shiga ɗakin tayi ko sallama

Baffa dake duƙe a bakin Fridge yana shirin buɗe wa domin ɗaukan win ɗin sa, sai ganin ta yayi a cikin ɗakin sa, hakan yasa ya dakata da abinda yake yi yana bin ta da mugun kallo

Ƙarisowa inda yake tayi tana cewa, “Baffa Ni fa na gaji da abubuwan da kake min a gidan nan, na gaji wlh, yau sai dai ka faɗa min matsayi na a wurin ka, don bazai yiwu ina zaune a matsayin matar ka ba amma ka maishe Ni tamkar ba kowa ba, babu wani zaman soyayya, kullum ba na sanin halin da kake ciki, idan ka saka ƙafa ka fita ba ka dawo wa sai sanda ka ga dama, kuma idan ka dawo sai ka ƙule ɗakin ka ka rufe kanka baza ka bar Ni na shigo ba, kai kuma ba ka zuwa ɗaki na, ba ka cin abinci na, wannan wani irin rayuwa ce? In CE dai aure na kake yi ba wani abun ba?”

Da mugun kallo kawai yake bin ta be da ninyan cewa komi, haka ya miƙe ba tare da ya buɗe Fridge ɗin ba yayi bakin gado ya zauna

Hakan da yayi mata sai ta zuciya ta isa gaban sa tana girgiza tace, “wai don Allah me nayi maka ne da zafi da ka dena min magana? Wlh idan har baka sauya ba zan bar gidan nan, tunda kai ba ka ƙauna ta ai iyaye na suna so na”.

“To dama na riƙe ki ne? Ki fi ruwa gudu mana, ki fice min a ɗaki da Allah ina da abin yi”.

Kuka ta fashe dashi tace, “wlh bazan fita ba, sai ka faɗa min abinda nayi maka ka sauya min, idan ba haka ba ƙaran ka zan kai wajen Abba tunda ka dena jin maganar Hajja”.

Miƙe wa yayi ya kama hannun ta ya ja ta zuwa waje, ya tura ta yace, “ki je ki sanar wa Baban Abba ba Abba ba, dama Ni na gaji dake”. Ƙofan ya maida ya rufe, har da saka keey

Nan Sa’adatu ta dinga dukan Ƙofan tana kuka tana faɗa masa magana, “wai don ya ga ya gama da ita dole yace zai yar da ita, to wlh sai ta zubar da cikin jikin ta don baza ta haife sa ba”.

Yana jin ta amma be tanka ba, illa ma ɗauko win ɗin sa da yayi ya hau kurɓa wa

Har ta ƙarishe fitinar ta ta shige ɗakin ta, harhaɗa kayan ta ta hau yi tana kuka, bayan ta gama ta ja Trolly ɗin zuwa wajen motan ta, “wlh yau sai na bar gidan nan, na gaji da wulaƙancin da Baffa yake min kuma Hajja ta kasa ɗaukar mataki, babu dole auren”. Ta faɗa tana ci gaba da kukan ta, tana saka kayan ta ta shige taja motan ta ɗauki hanyar Lagos, duk da ta san dole dare zai yi mata a hanya amma hakan be shafe ta ba, Fatan ta kawai ta isa gidan su ta sanar wa da Momyn ta komi.

 

Shi kuwa Baffa be ma san wainar da take toya wa ba, ƙarshe ma da giyan ta bugar da shi; barci ya hau yi, be tashi ba kuwa sai dare, alwala kawai yayi ya nufi masallaci ya gabatar da sallolin da ya wuce sa, inda daga nan ya wuce Part ɗin iyayen sa

A nan Hajja take tambayar sa “ina Sa’adatu?” Domin yau kwata-kwata bata shigo sun gaisa ba

Sai ma lokacin shi ya tuna da ita, sai yace mata, “tana ɗaki”.

“To amma dai kana kula da ita ko? Ka san me ƙaramin ciki dole sai ana bata kula wa, kuma har yanzu ƙorafin ta ɗaya ne ka ƙi ka koma yanda kake, kaji tsoron Allah Baffa, wlh akwai ranan da Allah zai tambaye ka”.

“Hajja ki dena min irin haka don Allah, ai kullum jin tsoron sa nake yi, da ba na jin tsoron sa da bata kawo iyanzu a ɗaki na ba”.

“Au iyeeeee? Me kake nufi to?”.

Kumbura baki yayi yana shafa ƙeya yace, “to ke ne ai Hajja da wani magana, ke ma kin san ba na son ta, ban taɓa son ta ba, ga wacce zuciya ta take so can amma kika liƙa min ita”.

Hajja tace, “lallai kam wuyar ka ta isa yanka Al’ameen, yau kuma rashin kunya zaka yi min? Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un, Allahumma ajirni fi musibatin..”

Miƙe wa kawai yayi ya fice ba tare da ya sake tanka mata ba

Sai kawai Hajja ta fashe da kuka tana cewa, “eh lallai A’ishah, kin rantse sai kin ga bayan ɗana, yanzu ji be yanda kika mayar min dashi, gaba ɗaya ya dena min biyayya kamar baya, ko kaɗan yanzu ba ya jin kunyan faɗa min duk abinda yake so; duk a dalilin ɗiyar ki, Allah ya isa tsakani na dake A’ishah, insha Allahu sai kema kin ɗanɗana abun da naji, kuma wlh Al’ameen ya fi ƙarfin ki har abada, bazai taɓa auren ɗiyar ki ba, da yardan Allah zan tashi masa tsaye sai dai duk wani sharri ya koma miki. Kai kuma mu zuba dani da kai zan gyara maka zama, Allah ya kai mu goben har gidan naku zan zo in ci uban ka hankali kwance”.

 

 

 

**** ***** *****

Baffa kuwa yana koma wa gidan su, kai tsaye ɗakin sa ya wuce, be duba ko Sa’adatun tana nan ba, ko ta aikata abinda tace zata yin na tafiya gida ba, shi dai be bi ta kanta ba tunda dama tuni ya daɗe da fita shirgin ta, ɗakin sa ya shige, sai da ya kora kamar yanda ya saba sannan ya haye gadon sa, haka yake ta sambatu yana kiran sunan Ɗahira har barci ya sure sa.

 

 

28/6/2021.
💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR’S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER’S ASSO*📖
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA’S FAMILY*_

.

*EPISODE Forty Seven*

Washe gari Hajja Fatu da ta gama shirin ta na zuwa Office, sai ta biya ta gidan su Baffa, sai dai kuma bata cid da Sa’adatun a ɗakin ta ba, kai tsaye ƙofan ɗakin Baffa ta hau buga wa, domin a zaton ta suna ciki tunda ta ga motan Baffan be fita ba, kuma ko kaɗan bata kula da babu na Sa’adatun ba; tunda ta san babu inda zata je

Kiran sunan sa take yi daga shi har Sa’adatun

Baffa dake kwance be gama wartsake wa daga giyan da ya sha jiya ba, shiyasa yayi lattin tashi, sai hayaniyar Hajja ce ya farkar da shi, dole ya miƙe yana saka riga a jikin sa, ƙofan ya nufa yana ɓame bottles ɗin rigan, guda uku kacal ya saka ya buɗe ƙofan yana faɗin, “wai Hajja lafiya? Me ke faruwa ne?”

“Biyo ka nayi in ci maka mutunci, ina ita Sa’adatun? Ta fito duk ta faɗa min abinda kake mata, Wlh idan ka sake naji mummunan abu wlh yau Ni da kai ne. ka kira min ita mana ka tsaya kana kallo na”.

Wuce ta yayi zai nufi ɗakin Sa’adatun

“Ina kuma zaka je? Ba tana ɗakin ka ba?”

Gajeren tsaki yaja kafin yace, “ba ta ciki tana ɗakin ta”.

“To ba ta ciki; na duba ban ganta ba, me ke faruwa ne? Ina zata je da safen nan ba tare da ka sani ba? Yanzu ma na kula kamar ba motan ta a waje”.

“To Ni Hajja ina Nasan inda zata je?”

Zata yi magana wayan ta ta soma ringing, ciro wa tayi cikin jaka tana cewa, “ka nemo ta wlh ko inci ƙaniyar ka Baffa, ban son shashanci”. Wayan ta amsa ganin sunan Dr. Zubairu

“Hello”.

“Dr. Na iso na ga Office ɗin ki a rufe”.

“Eh ban fito ba wlh, yau nayi late na tsaya yin wani abun, amma ka jira Ni yanzu zan taho ai kayan naka suna office ɗina”.

“Ok to ba damuwa, sai kin zo”.

Daga haka suka gama wayan, inda tabi bayan Baffa da ya shige ɗakin Sa’adatu don duba ta.

Sai dai kuma gaba ɗaya sun duba Part ɗin babu ita, dole Hajja ta ɗauki waya ta kira Numban ta, sai dai ba’a amsa ba har sai da tayi Three missed calls, memakon taji muryan Sa’adatun, sai muryan Mahaifiyar ta taji

Hajja tace, “Amina ya aka yi wayan Sa’adatu ya zo hannun ki? Me ke faruwa ne wai nan mun neme ta ba mu same ta ba?”.

Cike da faɗa Hajiya Amina tace, “ina kuwa zaki sani Yaya tunda yaron ki be faɗa miki ba, to Sa’adatu ta dawo gida domin ta gaji da abinda yake mata, kuma na gode da abinda kika min Yaya na gode, babu damuwa”. Tana gama faɗar haka ta katse kiran ba tare da taji me Hajjan zata ce ba

Juyowa Hajja tayi ta kalli Baffa tace, “innalillahi wa’inna ilaihi raji’un! Baffa yanzu me kayi mata da har ta tafi gida? Me ya haɗa ku?”

“Hajja babu abinda ya haɗa mu, nima ban san sanda ta tafi ba”.

“Dalla rufe min baki, ashe ban isa da kai ba? Yanzu har sai da kayi sanadin da Sa’adatu ta tafi gida? Ka nuna min ban isa ba ko? To wlh yau na baka ka je ka ɗauko ta tun wuri tun kafin mutanen gida su ji zancen nan, idan ba haka ba zan mummunan saɓa maka”. Daga haka ta fice fuuuu ranta a ɓace tayi gida, tana zuwa motan ta kawai ta ɗauka ta fita.

A hanyan layin gidan ta haɗu da Shakira a cikin motan ta, nan Hajja ta danna mata horn tana faka wa

Itama Shakiran dayake ta gane motan Hajjan, sai ta tsaya tana me fito wa ta nufi motan

Lokacin har Hajjan ta fito tana bin ta da kallo tare da tambayar ta “me tazo yi da safen nan bata wuce asibiti ba?”

“Hajja wlh yaji na yo”.

“Innalillahi… Yau na shiga uku na, yaji kika yo kamar ya Shakira? Kina nufin kin baro gidan mijin naki? To uban me yayi miki?”.

Baki a zumɓure tace, “wlh Hajja na gaji da abinda Sahabi yake min, kullum be da lokaci na, yanzu ya kai har wulaƙanci yake min, ko yaushe yana waya da mace, kuma idan nayi magana ya dinga min faɗa kenan, yau har mari na yayi don kawai na tanka masa saboda na ga an turo masa text, kuma mace ta turo masa da daren jiya, wai ya fito su haɗu, shi ne ya mare Ni, wlh Hajja bazan koma ba dole sai na ɗanɗana masa azaban da ya ɗanɗana min”.

“Uban azaba zaki ɗanɗana masa, angaya miki ana wa namiji haka ne? To wlh idan wani ne zai ce sai dai ki shekara a gida baki dawo ba, kuma da kike tunanin zai biyo ki sai dai ki ji ya sake wani auren ya bar ki banza kawai, dalla ki kama hanya ki tafi, wlh kar ki soma ki shiga gidan nan idan ba so kike mutanen gida yau su yi min dariya ba, ina fama dana Baffa ke kuma kin dawo, ki kama hanya ki tafi ko”. Ta ƙare maganar da daka mata tsawa

“Wlh Hajja babu inda zan je, sun daɗe ba su yi miki dariyan ba, ina faɗa miki mari na yayi kina ce min za’a miki dariya, babu inda zan je wlh”. Wuce wa tayi wajen motan ta zata shiga

Sai Hajjan tayi saurin ƙarisawa wajen ta tace, “yi haƙuri to, yanzu mu wuce Hospital in yaso sai in sama mana mafita, amma ba na son ki shiga gidan nan a san abinda ya faru, ki kwantar da hankalin ki Sahabi kamar ya dawo tafin hannun ki ne, dani yake zancen”.

Da wannan kalaman Hajja ta shawo kan Shakira, sanna suka shiga mota suka wuce Hospital, Kai tsaye Hajja Fatu Office ɗin ta ta wuce, tana shiga ta ciro wayan ta ta danna wa Hajiya Sa’ima kira, nan ta sanar mata “anjima kaɗan tana nan zuwa ta raka ta wajen Malam”.

“To babu matsala, sai kin zo”. Cewar Hajiya Sa’ima

Suna gama wayan Dr. Zubairu ya shigo Office ɗin

Hajja Fatu tace dashi, “to ga kayan naka nan, amma dai ka san yanda zaka yi ka fita dashi Hospital ɗin nan ba tare da an ganka ba, ka san mutane yanzu sai ace magungunan asibiti ka sata”.

Dariya Dr. Zubairu yayi yace, “ai bani da matsala dacta, ba ma yanzu zan fita da shi ba sai zuwa magriba idan an shiga Masallaci, sannan zan dawo in ɗauka, yanzu Office ɗina zan kai”.

“Yauwa hakan ma yayi, sai na ji ka zuwa anjima, yanzu ina son na gama duba patiens ɗina ne domin akwai wurin da zan je”.

Yace, “to shikenan, dama akwai maganar da zamu tattauna, idan kin samu lokaci sai ki kira Ni kawai”.

“Ok”.

Da haka ya fice

Ita kuma ta ɗauki wasu files ta fice, kai tsaye patiens ɗinta taje ta duba, bayan ta gama ta dawo Office, waya ta ɗauka ta kira Safna, tana zuwa tace mata “taje ta ba wa Maman yaron nan takardan sallama”.

Amsa tayi Safnan tana shirin fita

Sai kuma Hajja ta kira wo ta tace, “zuwa anjima ina ga shima ɗayan yaron na kusa dashi za’a sallame sa, so bazan daɗe ba idan kinga jikin nasa da sauƙi sosai sai ki ba shi sallama”.

“To”. Safna tace da ita tana fice wa.

Awanni biyu Hajja Fatu ta ƙara a asibitin kafin ta wuce gidan ƙawarta, kai tsaye bata zauna ba suka wuce wajen Malam, inda Hajja ta zube masa kuɗi don ayi ma yaran ta biyu aiki, ko kaɗan ba ta son a sake samun ɓaraka a tsakanin su, ita Shakiran a kama mata Sahabi sai yanda tayi da shi, shi kuma Baffa a saka mishi ƙaunar Sa’adatu a rai su zauna lafiya kar wani abu ya sake faruwa.

Daga nan gida kawai ta wuce bata koma aiki ba.

Ta dawo babu daɗe wa Abba ya shigo a rikice, cikin tashin hankali yace da ita, “ke ɗauko gyalen ki mu wuce Hospital”.

Hajja tambayar sa ta soma yi “lafiya?”. Itama duk hankalin ta a tashe

Tsawa ya daka mata yana faɗin, “baza ki ɗauko mu wuce ba ko kuwa? Idan mun je can kya ji”.

Jiki na rawa Hajja ta rataya gyalen ta tabi bayan sa, a motan sa suka nufi asibitin, be sake ce mata komi ba har suka kai Hospital ɗin. Kai tsaye Office ɗin Big Dady suka wuce, a nan suka ga mutane cirko-cirko har da ƴan sanda, ga Safna durƙushe sai kuka take yi

Da kallo Hajja take bin su dashi hankalin ta a matuƙar tashe, “shin me ke faruwa?” Tambayar dake yawo a ranta kenan babu me amsa mata

“Yauwa officer wannan ita ce me kula da yaron”. Cewar Big Dady yana kallon ASP

“Ok”. ASP yace yana kallon Hajja, sai kuma yace, “kin gane waɗannan?”

Sai a lokacin ma Hajja ta kalli inda wasu Mata da miji dake tsaye suke, macen na kuka sosai itama. Ta gane matar sarai, sai ta gyaɗa kanta domin ta kasa magana

“Ok sun kawo ƙara da cewan sanadiyar ku ɗanta ya mutu, domin bincike ya nuna an ba wa ɗan ƙwayoyi a matsayin magani, wanda hakan yayi sanadin mutuwar sa, ko da suka koma gida sai ciwo rigigim ya kama ɗan, sun kai sa asibiti mafi kusa dasu domin ceto yaron su, a can aka gano an ba shi ƙwayoyi, kuma ita wannan ( ya nuna Safna) ita ce wacce ta ba shi magani a jiya kenan, in ji Mahaifiyar yaron, ita kuma tace “a Office ɗin ki ta ɗauko maganin.” Yanzu binciken da muke yi ya aka yi ƙwayoyin maye masu bugarwa suka shiga Office ɗin ki har aka ba wa yaro ya mutu a sanadin haka?”

Yanda jikin Hajja Fatu ke rawa baza ka ce ƙafafuwan ta za su ɗauke ta ba, sosai ta zaro idanu waje lokaci ɗaya ta jiƙe sharkaf da zufa, ta ma rasa me zata ce illa gaban ta dake faman buga wa kamar zai faso ƙirji

“Baza ki yi magana ba kin tsaya kina kallon Mutane? Ya aka yi ƙwayoyi suka shigo asibitin mu?” Cewar Abba yana daka mata tsawa

Sai kawai Hajja ta fashe da kuka tsaban rikice wa

Cike da baƙin ciki Abba zai sake magana, sai Abbu ya ce da shi, “yi haƙuri don Allah Yaya, a bi komi a hankali”.

ASP yace, “Amm… Ina ga fa dole sai dai mu wuce Station; don maganar nan baza ta yiwu a nan ba, wannan matsalan babba ce ya kamata mu wuce can, akwai yiwuwar a kulle Hospital ɗin nan gaskiya domin babu abinda zan iya”.

“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un”. Abinda su Big Dady suke faɗa kenan. Gaba ɗaya hankalin su ya tashi, ba wai kullewan ba, kar a ɗaga wa mahaifin su hankali, tunda sun san yanda yake matuƙar ji da asibitin nan, wannan babban matsala ne, kisan kai ta hanyar ƙwaya? A matsayin magani?
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR’S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER’S ASSO*📖
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA’S FAMILY*_

.

*EPISODE Forty Eight*

Kai tsaye Police station suka wuce gaba ɗaya, inda a can ne Hajja Fatu tayi bayani dalla-dalla, ta yanda ƙwayar suka kasance a asibitin, ta taimaka wa Dr. Zubairu ne wajen shigo da su tare da magungunan asibitin

Nan Abba yayi kamar zai make ta sabida faɗa, sosai ya zuciya ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba

Sai da Big Dady da Abbu suka yi ta tausan sa kafin ya haƙura

Nan aka tura ƴan sanda domin su je su kamo Dr. Zubairu, amma sai dai ba’a same sa ba tuni ya gudu, illa ƙwayoyin da aka kwaso a Office ɗin sa.

ASP yace musu, “za’a kama Hajja Fatu a matsayin wacce ta taimaka domin yin safaran ƙwayoyi, wanda yayi sanadin kisan kai, ita kuma Safna an sake ta domin bata da laifi”. Sai dai sosai suka ja mata kunne a kan sakacin ta ne duk da haka ya ja wannan abun, tana a matsayin likita amma ba ta lura da abinda zata iya ba Patients ɗin ta

Shi Abba tunda ya ga abun ya zo da sauƙi tunda an sasanta baza a kulle asibitin ba, ya wucewar sa ya tafi, be damu a saki Hajja ko kar a sake ta ba

Inda su Big Dady su suka tsaya kai da fata suka yi ta cukui-cukui har suka shawo kan matsalan, to, abin ka da akwai kuɗi, komi a ƙasar mu idan kana da kuɗi to zaka iya yi, nan suka samu aka ce za’a saki Hajja tunda ba ita ce asalin wacce ta shigo da ƙwayoyin ba, kawai da taimakon ta ne hakan ya faru.

Kafin ma a sallame su har an kamo Dr. Zubairu, sosai yaji kunya sanda suka haɗu da su Abbu, musamman ma Big Dady tunda shi ne  abokin sa ƙwarai, haka yake ta sissinne kai kamar muna-fuki

Su kuwa basu bi ta kansa ba suka ficewar su. Kai tsaye gida suka wuce, sai da suka koma ne suka sanar da Kaka duk abinda ya faru

Gaskiya be ji daɗi ba, domin ya nuna ɓacin ran sa matuƙa a kan Hajja, wanda su kansu sun sha mamaki, duba da yanda Kaka yake son Hajja Fatu sosai, kasancewar ta ɗiyar abokin sa kuma ɗiyar ƙanwar sa, amma kuma sun san yanda yake matuƙar ƙaunar asibitin sa ba ya son ko kaɗan wani abu ya faru, yanzu idan duniya suka ji shikenan za’a fara ma asibitin baƙin fenti. Sosai yayi mata faɗa daga baya ya haɗa su yayi musu nasiha sosai ganin Abba yana ta kumbura da shirin ya aikata wani abun

Abba dai be bar wajen ba sai da ya kafa mata sharaɗi, domin yace “dole sai ta bar aiki,” amma Kaka ya hana sa, shi kuma yace, “to idan haka ya sake faruwa wlh dole ba ita ba aiki a ko wani asibiti ba Asibitin su kaɗai ba, idan kuma tace a’a sai dai ba a ƙarƙashin sa take ba, tunda da sa hannun ta ake son ganin bayan asibitin su, da goyan bayan ta ake shigowa da ƙwayoyi tare da maganin asibiti, nan gaba ma da ita za’a haɗa baki da maƙiyan su don ganin bayan asibitin”.

Abba fa ya shaƙa sosai, ba don Kaka ba babu me tanƙwara shi, sai dai su rabu da Hajja Fatu. Tunda shi Abba duk a cikin su ya fi su zafi, yana da sauƙin kai matuƙa, amma idan ya tashi faɗa ba ya ji ba ya gani, duk wani rashin son raini irin na mahaifiyar su shi ya biyo ta, ba ya shiga harkan mutum, to, kaima kar ka shiga nasa, yanzu zaka ga haukan sa matuƙa, shi kuwa Abbu sak Kaka ne babu ruwan sa, yana da sauƙin kai, haka ma Big Dady, shi kam ya fi su haƙuri, duk da shi ne babba yana da haƙuri matuƙa, idan ka ga yana faɗa kawai yana yi ne domin gyaran ƴaƴan sa, amma duk abinda zai faɗa zai yi wuya ya aikata shi a zahiri, idan ma kayi masa abu kafin zuwa anjima ya manta ransa yayi sanyi, sai dai idan zai ɗaure maka fuska domin ka koki gaba, shima sak halin Ummin sa ya biyo babu ruwan sa.

Da haka magana ya watse, ranan dai Hajja ta ga banu, domin a zaune ta kwana, sosai hankalin ta ya tashi, ƙarshe ma washe gari ƙin zuwa aiki tayi.

A ranan ne shi kuma Baffa suka dawo da Sa’adatu, tunda tun jiya da Hajja ta ba shi umarnin zuwa ya ɗauko ta be je ba sai sakaliyan yamma, to, a can ya kwana yau suka dawo.

Fannin Shakira ma tun a asibiti Sahabi yaje ya bata haƙuri suka koma gida

Wannan dalilin ne yasa Hajja ta ɗan samu sukuni da matsalolin ta, tana ga kamar aikin Malam ya ci tunda ga shi komi ya zama normal Kan yaran ta, sai dai matsalan yana ga Abba, domin tun abin be sake kallon inda take ba, ya ƙi mata magana ya dena cin abincin ta, hakan yasa tayi tunanin why not ta Kai shi wajen Malam domin magance mata matsalan ta, wannan tunanin zuciyar nata tabi ta wuce kanta tsaye wajen Malam ko bi ta ƙawarta bata yi ba, shi ne kaɗai wanda zai iya mata maganin matsalan dake shirin afkuwa ita da mijin ta, wanda tana ganin ɓaraka ne babba da rashin yarda yake shirin Kunno Kai a tsakanin su, wanda kuma hakan ne babban tsaiko ga rayuwan ta, yardan Miji ya fi komi a rayuwar aure.

 

 

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

*TURKEY*

A kwanakin nan da suka shuɗe, Ɗahira tayi rayuwar ƙunci ba ni da ƙunci ba, ko kaɗan ba ta da walwala, ta zama tamkar wata wacce bata da gata, ta rame tayi baƙi kamar ba ita ba, bata da aiki kullum sai kuka da saka damuwa a ranta, ta kasa saba wa da halin da take ciki, komi na gidan ita take yi, da ta tashi da safe zata gyara gidan tayi wa kanta abinci domin shi ko bi ta kanta be yi bare tasa ran idan tayi abinci zai ci, bare kuma bata taɓa kwatanta hakan ba, ta gummaci ta girka ta zubar da tayi masa girki, ita take masa wanki da gyara ɗakin sa ko ina, idan ma bata yi ba ranan ya dinga caɓa mata magana kenan, kuma yace “idan bata yi ba sai yaci uban ta”. Kalman cin uban ta shi yake matuƙar ɓata mata rai ainun, sai ta zauna tayi kukan ta son ranta ta share hawayen ta, haka zata yi masa wankin ta shanya masa a Toilet ta gyara masa ɗaki ko ina, domin ba ta son ko kaɗan ya sake taɓa lafiyan jikin ta, a haka take ta ƙare wa tana ciwo a tsatstsaye, kullum fama take yi da kanta sakamakon damuwan da ta kasa cire wa a ranta, kuma tun ranan da ya bata waya suka gaisa da ƴan gidan su be sake bata ba, sosai take buƙatar jin muryan ƴan gidan su amma ba hali, dole ta haƙura domin ko magana ba ta ƙaunar tayi masa bare ta tambaye sa wani abun

Duk idan taje gyara masa ɗaki, sai tayi binciken ko zata samu keey ɗin ƙofa, amma duk inda ta duba bata taɓa cin karo dashi ba, haka zata mayar masa da komi a muhallin sa ta gyara masa ta koma inda ya zame mata ɗaki, kusa da kichen. Idan damuwa yayi mata yawa sai dai tayi ta karatu, da dare kuma ko ishashshen barci ba ta samu illa sallah da take faman yi ko yaushe tana kaiwa Allah kukan ta

Rashin zaman Usman a gidan ya fi mata komi daɗi, tunda idan ya fita tun safe ba ya dawowa Sai dare, wani lokacin ta ɗan sami barci ya fizge ta, wani lokacin kuma idanun ta biyu zai shigo, ita yanzu har ta saba da duhun gidan, domin sabida tsaban mugunta irin nasa ya lalata komi na na’uran gidan, ko NEPA babu a gidan, bare dama ita ba gwanar kallo bane bare ya ɗebe mata kewa, haka take rayuwar ƙunci da duhu a gidan, koda da safe ne gidan babu wani haske sosai, sai idan ta yaye cootin, wani lokacin kuma sanyi ya addabe ta ta rasa yanda zata yi, dole ta mayar ta rufe.

Yau ma tana kwance kamar kullum, ko kaɗan ba ta jin ƙwarin jikin ta, daƙyar take iya taɓuka wani abun saboda rashin ƙarfin jiki, ga ta ba auki ba

Tunda ya fita take kwance ta kasa yin komi, ko karya wa ta kasa, tunani ne kawai ta afka tana ta faman yi. Can kuma sai ga hawaye ya silalo mata a kunci, sai ta yunƙura ta miƙe ta nufi kichen kamar zata faɗi, ruwa ta samu ta dafa ta haɗa tea me kauri, shi ne ta samu ta ɗan sha ko zata samu ƙwarin yin aiki

Tana gama wa ta dawo parlour’n tana bi da kallo, ganin ba wani datti ne ba sai ta wuce kanta tsaye ɗakin sa, nan ne yayi mutsu-mutsu da gadon sa, duk ya jefar da kayan sa, haka ta tattare sannan ta gyara gadon, ta wuce Toilet ta wanke masa, wankin sa dake shanya tun jiya da tayi masa ta kwashe ta ninke, sai ta ɗaura masa a kan gado, kana ta koma Parlour ta shiga wanka, tana fito wa ta zira riga da skert ko lotion bata shafa ba, rabon ta ma da shafa wani abu a gidan nan tun lokacin da tayi ciwo, komi yanzu ya fitan mata a rai

Tana zaune tana gyara kayan nata tana mayar wa cikin akwati, sai ta jiyo motsin buɗe ƙofa, tsayawa tayi kawai tana kallon ƙofan, ta san ba ya dawo wa da rana shiyasa tayi mamaki

Shi ne kuwa ya shigo ciki, wani saurayi na biye dashi a baya. Be bi ta kanta ba ya shige ɗaki, yayinda saurayin nan sai bin ta yake yi da kallo, sai kuma ya gaishe ta da harshen turanci

Amma ko ci kanka bata ce mishi ba, illa ɗauke kai da tayi fuskar ta babu fara’a taci gaba da abinda take yi.

Usman ne ya fito da Trolly  babba ya miƙa wa saurayin, dayake shi yake ba wa gugan kayan sa, duk kwana uku zai haɗa masa kayan ya zo ya amsa da safe kafin ya fita, yau kuma be zo ba sai yanzu, shi ne ya kira sa ya sanar masa zuwan sa, wannan dalilin ne Usman ya dawo domin ba shi kayan.

Saurayin fita yayi da Trolly bayan sun Yi sallama, shi kuma ya koma ɗakin sa.

Sanda Ɗahira ta gama gyara kayan nata, sai ta rufe Trolly ta janye sa gefe, kana ta koma ta jingina da bango ta lumshe idanuwan ta, ta hau tunanin da ya zame mata jiki, ko ta so bari ba ta iya wa.

Can sai Usman ya fito da waya ya nufo inda take

Takun takalman sa dake tafiya da ƙarin bugun zuciyar ta, shi yasa ta buɗe idanu da sauri ta sauke su kansa

Fuskar sa ɗaure tamau ya miƙo mata wayan ba tare da ya ce uffan ba

Kamar kar ta amsa, sai kuma tayi tunanin ko gida ne, da sauri ta miƙa hannu ta amshi wayan, ilai kuwa gidan ne, mahaifin ta ne a kan layi.

Yana kanta be tashi ba har ta gama wayan da mutanen gida

Itama ko kallon sa bata sake yi ba, kuma bata yi wani abun da zai saka yayi mata magana ba, bare ya sauke mata tijara, iyakan gaisuwa ya haɗa ta dasu bata ce musu komi ba

Amsar wayan sa yayi ya wuce kan kujera, zama yayi yana ta faman latsa wa

Ita kuwa haɗe ƙafafun ta tayi ta rufe idanun ta, sai ga hawaye, “Allah gani gare ka, Allah ka fitar dani a hannun wannan azzalumin bawa naka, na tsane shi!”. Tafaɗa a hankali zuciyar ta na ƙuna kamar ta fashe. Motsin sa taji, sai ta ɗago kanta tabi bayan sa da kallo da har ya shige ɗakin sa, wani ƙunci ne ya sake tokare mata maƙoshi, sai ta lumshe idanu tayi shiru tana sauraron bugun zuciyar ta, bata ƙara motsa wa ba har sanda taji motsin fitan sa. A haka ta wuni har dare bata sake tashi ba, illa sallah da ke tayar da ita, ko abinci taƙi ci a haka har dare yayi ta kwanta, nan da nan yau barci ya ɗauke ta saboda ta tara shi da yawa bata yi ba.

Bata farka ba sai washe gari ƙarfe 07:00am. Sosai taji daɗin barcin da tayi, sai duk wani gajiya ya saukar mata, sosai ta ɗan ji sauƙin kan nata, miƙe wa tayi ta shiga Toilet ta ɗauro alwala, sai da ta gabatar da sallah tayi lazami sosai har wajen tara da rabi, sannan ta miƙe ta shiga kichen, Breakfast ta haɗa sannan ta ɗaura ruwan wanka, a nan kichen ɗin ta karya tunda a nan take cin abincin ta

Ruwan na zafi ta sake ta kai Toilet, sai da ta sirka shi yanda take so kafin ta fito ta hau tuɓe kayan ta, ta cire riga tana shirin ɗaura zani sai ji tayi ya buɗe ƙofa

Usman ne ya fito cikin shirin sa da ya saba ko yaushe na ƙananan kaya, babu ƙarya ya ƙure wanka yau, sosai yayi kyau sai tashin ƙamshi yake yi. Da kallo ya bi ta ganin yanda ta ƙudundune jiki lokaci ɗaya ta tsorata, har tana zame wa ƙasa saboda tsaban tsorata

Ita duk bata yi tunanin yana gidan ba, tunda da safe yake fita shiyasa ta cire kayan a Parlour.

Shi kuwa tsaki yaja me sauti, ya sake ɗaure fuska tamau ya fice da sauri abin sa.

Ajiyan zuciya ta sauke bayan ta raka bayan sa da harara, “ɗan iska. Allah ya isa tsakani na da kai”. Ta faɗa a fili tana shige wa Toilet. Wanka tayi ta sanya doguwar riga ja, tayi Rolling da gyalen sa, kai tsaye ɗakin sa ta nufa, sai da ta gama share masa tana shirin fita ta hangi wardrobe ɗin sa kamar be gama rufe wa ba, da sauri ta ƙarisa har tana cin tuntuɓe, tana jan shi ya buɗe, washe baki tayi kai tsaye bincike ta soma yi ko Allah zai sa taga keeys ɗin gidan, tunda be taɓa barin wardrobe ɗin sa a buɗe ba, ilai kuwa sai taci Sa’a ta samu keeys da yawa a ciki, har da passport ɗin su a ciki, nan jikin ta ya hau rawa tsaban farin ciki, da sauri ta kwashi keeys ɗin ta fita da gudu, ƙofan ta nufa ta hau gwada mukullan, nan ta samu na ƙofan, sai ta buɗe ta watsar da mukullan a nan, ko mayar masa bata bi ta kai ba, passport ɗin ta na hannu ta wuce wajen kayan ta taja Trolly ɗinta ta fice da gudun ta, domin ba ƙaramin rawa jikin ta yake yi ba, gani take yi kamar kafin ta fita zai iya dawowa gidan.
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR’S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER’S ASSO*📖
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA’S FAMILY*_

.

*EPISODE Forty Nine*

Tafiya take yi tana waigen bayan ta, duk ta gama tsorata matuƙa, ta san haɗuwar su dashi bazai mata daɗi ba, ita kuma tarigada ta ɗau alwashin sai dai tayi yawo cikin ƙasar nan, amma baza ta taɓa koma wa gidan sa ba, ko bata sami taimako ta koma ƙasar su ba sai dai tabi duniya

Har ta fice a layin gidan, ta yanki hanya ɗoɗar, tafiya me nisa tayi Kafin ta samu wata mata me shago a bakin titi, nan ta tuna da Numban Zakeeya ƙawarta da tayi a cikin jirgi, wani zuciyar tace mata “ta gwada neman taimako ko Allah zai sa a dace”. Da sauri ta isa wajen ta tana maida numfashin gajiya, kafin ta ƙarisa wajen ta sai da ta ɗan samu ta daidaita kanta, sannan ta isa tana mata sannu da harshen turanci

Matar kallon ta tayi, duk da ba wani turanci ta iya ba, amma tana ji kaɗan-kaɗan, ta amsa mata cikin fara’a tana tambayan ta “me take so?” Cikin turancin

Nan Ɗahira tayi mata bayanin “don Allah ta taimaka mata da Aron waya, ita baƙuwa ce yau ta sauka, amma wayan ta ya faɗi, ta rasa ya zata yi ta isa gidan da tazo, tana buƙatar yin waya dasu ko za su san inda take”.

Matar bata wani tsawaita ba, duba da yanda taga Ɗahiran duk tayi laushi ta wani yamushe, da alamun tana matuƙar buƙatar taimako, nan tausayin ta ya kamata ta, ta ɗauki wayan ta miƙa mata tana bin ta da kallo kamar zata haɗiye ta

Ita kuwa bata damu da kallon da take mata ba, jiki na rawa ta buɗe jakar ta a ƙaramin Zip ta ciro takardan, kofewa tayi a wayan tayi kira, ba’a ɗau lokaci ba kamar ana jira aka ɗauka

Muryan mace taji tayi sallama

Sai Ɗahiran ta amsa mata tana cewa, “da Allah da Zakeeya nake magana?”

“Ita ce. wace ce?”.

Cikin Hausa take magana don kar matar taji me take cewa, ganin yanda idanun ta ke yawo a kanta, “suna na Ɗahira, Ni ce wacce muka haɗu dake a jirgi last three weeks, kin tuna Ni? Har muka zauna waje ɗaya muka yi exchanging number”.

Cike da ɗoki Zakeeya tace, “Laa Ɗahira ke ce? Wlh nayi tunanin baza mu haɗu ba, sabida yanda nake ta kiran wayan ki ba ya shiga, kuma ke baki kira Ni ba”.

“Haka ne. Amma ina buƙatar taimako, don Allah ki taimaka min”.

Yanda tayi maganar yasa Zakeeyan ta gane akwai matsala, nan da nan ta tashi hankalin ta tana tambayan ta “me ya faru?”

Ɗahira tace mata, “maganar ba ta waya bace, ki taimaka ki zo ki tafi dani in yaso sai muyi maganar”.

“Ok.. ok aina kike yanzu?”

Tambayar matar nan tayi, ita tayi mata kwatancen inda take

Zakeeyan tace, “gata nan zuwa yanzu, basu da nisa da wurin ma”.

Sosai zuciyar Ɗahira tayi mata sanyi a wannan lokacin, gani take yi zata iya tsira ba tare da Usman ya sake ganin ta ba. Matar ta miƙa wa wayan tana ta mata godiya sosai kamar zata yi kuka.

Babu jima wa kuwa sai ga Zakeeya a motar ta, da sauri ta fito ta nufo Ɗahiran

Itama Ɗahiran wajen ta ta nufa domin ta shaida ta

Sosai Zakeeya take ware idanun ta a kan Ɗahira gani take yi kamar ba ita ba, har sanda suka kusanci juna ta gane tabbas ita ce, amma kuma yanda ta sauya mata fiye da tunani, ga baƙi da tsananin rama da tayi, duk ta bushe kamar babu jini a jikin ta. Cikin sauri ta riga ta magana da tambayar ta, “Ɗahira ke ce? Ke ce haka meke faruwa ne?”

“Don Allah mu je sai in Yi Miki bayani, ke kaɗai na sani a ƙasar nan ina buƙatar taimakon ki Zakeeya”.

Jiki na rawa kuwa Zakeeyan taja hannun ta ganin har ta soma hawaye, motan ta buɗe mata ta shiga daga ita har kayan ta, itama ta zagaya ta shiga taja motan da sauri. Sun yi tafiya me nisa babu me magana cikin su

Kai tsaye Zakeeya gidan su ta wuce da ita, suna isa suka fito taja hannun ta suka yi ciki

Auntyn Zakeeyan na zaune a Parlour suka shigo Zakeeya na sallama

Amsa mata tayi tana bin su da kallo, ganin ta da baƙuwa sai ta bi su da ido har suka zauna, kana kuma ta soma tambayar Zakeeyan “aina ta samo ta kamar ƴar ƙasar su?”

Zakeeya tace mata, “eh Aunty, ƴar Nigeria ce, domin a jirgi muka haɗu da ita sanda na dawo nan, tana buƙatar taimako ne shi ne ta kira Ni”.

“Ok Allah Sarki, Allah yasa dai lafiya baiwar Allah? Sannu ko? Zakeeya kawo mata ruwa tasha naga kamar hankalin ta a tashe yake har kuka take yi”.

Zakeeyan bata amsa ta ba illa miƙewa da tayi da sauri ta kawo mata ruwan

Duk da Ɗahira tana buƙatar ruwan domin ta jiƙa maƙoshin ta, amma yanzu ba tashi take yi ba, burin ta kawai abinda ke cikin zuciyar ta ya cika, na ganin ta a ƙasar ta na haihuwa, daga nan ne hankalin ta zai kwanta

“Ki sha ruwa kinji?” Cewar Zakeeya tana dafa mata kafaɗa

Kallon ta Ɗahira tayi lokacin kuma wani sabon hawayen ya Kunno mata, cikin rawan murya tace, “wlh ba na jin zan iya saka wani abu a ciki na idan har ba a ƙasa ta na ganni ba, don Allah don Allah ku taimaka min na koma ƙasa ta, bani da kowa a nan, ku taimaka min da kuɗin jirgi, wlh idan na koma zan tura muku kuɗin ku, Ni dai fata na na bar ƙasar nan”.

Sosai kansu ya ɗaure da zantukan ta

Cikin al’ajabi Auntyn tace, “baiwar Allah bamu gane ba? Me ke faruwa ne kiyi mana bayani kinji don Allah yanda zamu fahimta”.

Ba ta jin zata iya ɓoye musu komi, sabida tana ganin kamar idan suka ji labarin ta za su taimaka mata, don haka ta basu labarin komi game da rayuwan ta wajen Yayan ta da ya kasance miji a gare ta

Sosai suka tausaya mata, Zakeeya har da hawaye sai da ta zubar mata

Nan Auntyn tace, “za su taimaka mata, zuwa gobe da yardan Allah zata koma gida”.

Amma Ɗahira sai ta roƙe su “su taimaka a yau ta bar ƙasar, baza ta iya ko ƙwaƙƙwaran mintuna bane, tunda ta samu ta gudo gwara ta koma ga iyayen ta hakan zai fi mata, su taimaka mata idan za’a samu jirgi ta bar gidan”.

Auntyn bata yi musu ba, sai ta kira mijin ta ta shaida masa komi

Nan yace mata, “ga shinan zuwa”. Babu jima wa kuwa sai ga shi ya zo, shi ne ma yaje ya nema mata jirgin, sai dai ba’a sami wanda zai je Direct to Nigeria ba dole za’a yi biye-biye wasu ƙasashe, kuma da yamma zai tashi. Direct to Nigeria kuma sai zuwa dare za’a samu

Ɗahira tace, “tana so, gwara ta tafi wani ƙasan, baza ta iya jira har dare ba,” wataƙil ma ya biyo bayan ta,” abinda take tsoro kenan.

Haka suka taimaka mata har ta bar ƙasan, sosai Ɗahira take kuka sabida wannan karamci nasu, idan ba Allah na son ta ba, kuma sun kasance mutanen kirki, da bata san ya zata yi ba, sosai tayi musu godiya tana kuka

Amma su sun ce “sun yi mata don Allah ne ba sai ta biya ba tunda suna da halin yi, kuma kasancewar ta ƴar ƙasar su me buƙatar taimako”.

Itama Zakeeya sai da tayi kuka da za su rabu, jin ta take yi tamkar ƴar uwan ta, ga tausayin ta da take ji, Allah ne ya haɗa jinin su.

 

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

Usman kuwa be koma gida ba sai dare kamar yanda ya saba, yana taɓa ƙofan zai buɗe yaji ta a buɗe, mamaki ne ya kama sa ya shiga yaci karo da mukullai a bakin ƙofa, da kallo yabi wajen, sai kuma yabi parlour’n da kallo zuciyar sa na hasaso masa faruwar wani abu, da sauri ya isa cikin parlour’n yana faman kiran sunan Ɗahira, shi kansa be san cewa ya san sunan ta har haka ba, domin tunda yake be taɓa kiran sunan ta ba, tun tana ƙarama bare yanzu, sai ji yayi bakin sa na furta wa

Ko ina ya duba a gidan be ganta ba, wanda har wardrobe ɗin sa ya duba, nan yaga babu password ɗin ta, zargin sa ya tabbata guduwa tayi, duk da hankalin sa be tashi ba amma ya kasa haƙura sai da yabi bayan ta ko zai ganta, sosai ya ƙudurta a ransa “muddin ya ganta sai ya ci uwar ta yau ba uban ta kaɗai ba”.

Duk inda yabi da mota be ganta ba, ko me kama da ita be gani ba, dole ya isa wajen wani Abokin sa suka nufa airport tare, dayake shi yana da hanya, ya san nan da nan za’a bincika masa idan ta hau jirgi, duk da ba ya tunanin zata iya barin ƙasar da sauri haka, ba kuɗi ne da ita ba bare ƴan uwa

A lokacin ne ma jirgin da zata ɗaga zuwa Nigeria Direct zata tashi, nan abokin ya saka a duba musu list ɗin masu tafiya, amma babu sunan ta, sai ya tambaya “ko akwai wanda ya tashi kafin wanann?”.

Nan ne aka faɗa musu “akwai wanda ya tashi ƙarfe 04:00pm. Amma kuma ba Nigeria kaɗai zai wuce ba.” Koda aka bincika sai aka samu sunan ta

Usman be iya cewa komi ba illa jan abokin nasa da yayi suka shiga mota suka yi gaba

Abokin na tambayar sa “amma lafiya?” Tunda be san makaman zancen ba

Sai Usman yace masa ,”ƙanwar sa ce yarinyan ya neme ta ya rasa, shi ne yake bincike ko ta koma gida ne”.

Koda ya koma gida kwanciyar sa yayi domin ko kaɗan be saka damuwa a ransa ba, hakan ma shi yafi masa, gwara da ta gudu da ƙafar ta, fargaban sa ɗaya kawai yanda iyayen sa za su ɗau fushi dashi, amma ya shirya musu dama tun farko, kuma yanzu bazai koma gida ba har sai sanda suka huce, in yaso sai ya koma musu tare da takardan sakin ta. zuwa da safe ma zai sauya Simcard don kar ma su neme sa su samu. A haka yayi barcin sa cikin kwanciyar hankali har da munshari, babu abinda ke damun rayuwar sa.

 

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

*NIGERIA*

Kwana biyu su Ɗahira suka yi a jirgin kafin suka isa Nigeria, sun sauka ƙarfe 03:30pm. Amma kasancewar akwai hadari garin; sai ka zata yamma ne sakaliya, kowa sai haraman wuce wa gida yake yi tunda hadari gadan-gadan ne ya taso, dayake farko-farkon damina ne.

Itama kanta tsaye wajen masu Taxi ta nufa, amma duk wanda ta taya ba sa ɗaukan ta tunda kowa ta kansa yake yi ganin har an fara yayyafi. Sai ta fito bakin titi tana ci gaba da tare wa, zuciyar ta gaba ɗaya ta tsinke burin ta kawai ta ganta a gida

A lokacin da ruwan ya sauko sosai, a time ɗin ne ta samu wani me kirki ya faka ya ɗauke ta, lokacin gaba ɗaya ta gama jiƙe wa sai rawan ɗari take yi

Shi kansa me taxi ɗin har ya wuce ganin ta cikin ruwan ne ya tsaya, koda ya ɗauke ta be jirga a wajen ba tunda ana tsula ruwan ne. Wajen mintina goma sha biyar kuma sai ruwan ya tsaya cak, sai ɗan yayyafi da ake yi jefi-jefi, hakan yasa ya tada motan ya nufi inda ta sanar masa.

Suna isa bakin ƙofar gidan su kamar an yi mata bishara da gidan aljana, fita tayi tace masa, “zata kawo masa kuɗin yanzu”.

Yace, “babu damuwa yana jira”.

Ƙwanƙwasa Gate ɗin tayi, gateman ya buɗe mata

Shima be wani gane ta sosai ba, har yace, “baiwar Allah daga ina..?”

Ta katse sa da cewa, “Hamisu Ni ce Ɗahira, don Allah ka sallami me motan can”.

“To.. to Hajiya, to sannu da zuwa, sannu an dawo lafiya?”. Yafaɗa jikin sa na rawa tsaban murna

“Lafiya lau”. Tace dashi tana shige wa da sauri ta doshi cikin gidan

Tun daga nesa ta hangi Mahaifin ta da Big Dady suna tsaye a bakin ƙofan shiga gidan suna magana

Su ma sai suka tsaya kawai suna kallon ta ganin ta jaye da akwati, duk tunanin su sai ya tafi ga Ɗahira ce wannan? Duk da sun hangi wannan ɗin tamkar bata da haske kamar Ɗahira, kuma sun san cewa Ɗahira ba ta ƙasar nan, ba yanzu zata dawo ba bare su ganta a nan, amma kuma sak tafiyan ta da yanayin ta ya basu ita ce.

Ilai kuwa itan ce don basu gama hasashen nasu ba ta gurfana a gaban su, mamaki zalla ne ya cika su ganin tabbas ita ce, sai suka buɗe baki suna bin ta da kallo ko wanne ya kasa furta komi ganin yanda tayi mugun sauya musu

Ita ko nan da nan hawaye ya wanke mata fuska, cikin rawan murya tace, “Abbu.. Dady..” sai tayi shiru tana me fashe wa da wani irin kuka me shiga zuciya

Sosai hankalin su yayi mugun tashi, lokaci ɗaya kamar an tsikare su suka yo kanta ko wanne yana me riƙo mata hannu da tambayar “me ke faruwa? Ina Usman ɗin? Ya aka yi ta dawo?” Haka suke jero mata tambayoyin ba tare da sun jira ta amsa musu ba.

 

 

 

.

_Mu haɗu jibi don jin ya za’a kaya, idan kuma bani da aiki za ku iya samun update gobe, amma fa sai naga ruwan comments, shi ne kawai zai ɗan saka min ƙwarin gwiwan muku._
💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR’S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER’S ASSO*📖
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA’S FAMILY*_

.

*EPISODE Fifty*

Ganin ta kasa magana sai rusa musu kuka take yi kamar ranta zai fita, sai hankalin su ya sake tashi matuƙa, inda Big Dady ya riƙo hannun ta suka nufi cikin gidan

Shi kuma Abbu ya janyo mata akwatin ta yabi bayan su, zuciyar sa tamkar zata tsinke, gaba ɗaya ya rasa ma takamaiman tunanin da zai kama wanda zuciyar sa ke bijiro masa da afkuwan sa ga ɗiyar sa.

Kai tsaye General parlour suka nufa, inda Kaka da Fadil ke zaune suna hira, Kaka na shan dariyan shirmen Fadil ɗin da yake ba shi, shigowar su yasa duk suka bi su da kallo, inda Kaka yake tambayar su “lafiya?” Yana kallon Ɗahira don be gane wace ce ba, saboda fuskar ta na ɓoye jikin Big Dady

Sai da suka zauna, Big Dady ya zaunar da ita gefen sa, kana yace ma Kaka, “Baba Ɗahira CE muka ganta ta dawo, kuma mun tambaye ta amma sai kuka take yi, Allah yasa ba wani abun Usman yayi mata ba?” Ya ƙare maganar da ɗacin rai, domin tuni hasashen sa ya ba shi duk yanda aka yi Usman ya muzguna mata, amanar da suka ba shi be riƙe da gaskiya ba, duba da yanda suka ga Ɗahiran ta koma

Shi kuwa Kaka jin furucin Big Dady, sai nan da nan jikin sa ya soma rawa, hankalin sa yayi mugun tashi, ya soma kiran sunan ta yana faɗin, “Mata ta, Mata ta ke ce? Ya aka yi kika dawo? Sanar damu don Allah, wani abun ne ya faru? Zo kusa dani”.

Da sauri ta miƙe ta isa wajen sa tana durƙushe wa ta sake fashe wa da kuka, domin yau ji take yi duk wani baƙin cikin da ta ƙunsa na zaman ta dashi suna dawo mata, yau take iya amayar da duk abinda ta ƙunsa, kukan kawai shi ne zai kawo mata sauƙi a gare ta

Duk yanda suka so tayi magana, Ɗahira ta kasa yi, riris take kuka kamar ana yanka ta, har wani shashsheƙa take yi tana faman ajiyan zuciya

Wanda hakan ba ƙaramin ɗaga musu hankali yayi ba, musamman Kaka da jikin sa sai rawa yake yi, sai ma a lokacin yake iya ganin yanda ta koma, ta fita hayyacin ta gaba ɗaya kamar ba Ɗahiran da suka sani ba, kowa ya ganta ya san cewa wahala ne ya mayar da ita hakan

Shi kuwa Fadil tuni ya sheƙa a guje ya garzaya ya sanar wa Aunty Amarya, domin yanda yaga Ɗahiran na yi har kuka sai da ya fashe dashi

Nan da nan itama sai Aunty Amarya ta saki tuƙin tuwon da take yi, gaban ta na matsanta faɗi tayi General parlourn da sauri

Umma na take mata baya ita da Fadil, domin lokacin da Fadil ɗin yake sanar wa Aunty Amarya tana zaune a Parlour tana ji, kai tsaye sai da ta wuce ta shafa wa su Hajja Fatu da Hajiya labarin dawowar Ɗahira, kana suka wuce can parlour’n.

Suna shiga suka ga yanda su Big Dady suka tasa ta gaba suna rarrashi, a lokacin har da Abba da shigowar sa kenan ya jiyo kuka daga parlour’n, shi ne ya garzayo da sauri don ganin waye ne

Aunty Amarya kuwa ta kasa zama saboda ganin tilon ƴar ta yanda ta koma, nan da nan hawaye suka cika mata idanu zuciyar ta na sake tsintsinke wa, dama tun farkon tafiyan su hankalin ta be taɓa kwanciya ba, kullum da ita take kwana kuma take tashi, sosai taji a jikin ta ɗiyar ta ba ta cikin kwanciyar hankali, a kullum ranan duniya sai tayi mata addu’ar kariya da zaman lafiya ita da mijin ta.

Su Umma kuwa murna na ciki an kasa fito dashi fili, ko wanne sai zuba idanu yayi yana kallon ta, musamman Hajja da tafi kowa murna, tuni zuciyar ta ta bata aikin Malam ne yaci, kuma tabbas ta san cewa da takardan saki ta taho, dama abinda take burin ya faru kenan, kuma ga shi ya faru, yau tsaban murna ai sai ta zuba ruwa a ƙasa tasha.

Daƙyar Abba ya rarrashe ta tayi shiru, sai sakin ajiyan zuciya take yi tana shashsheƙa

Shi kuwa Big Dady tuni ya yi kiran wayan Usman amma a kashe ake ce masa, hakan yasa zargin sa ya sake tabbata, shi ne ya sake tambayar Ɗahiran abun da ke faruwa

Sai a lokacin ta samu bakin fallasa musu duk zaman da suka yi, kama daga farkon kai ta tun suna gidan nan, har rayuwar uƙuban da tayi a can Turkey, tana Yi tana wani sabon kukan da ya taho mata ta kasa tsayar dashi

Sosai Aunty Amarya a wannan karon take zubar da hawaye tsaban tausayin ɗiyar ta da kuma raɗaɗin da take ji a zuciya

Haka zalika shima Fadil sosai yake taya Yayar tashi kukan tausayin ta

Su Big Dady kuwa sun kasa cewa komi, ko wanne zuciyar sa tafarfasa kawai take yi da jin abinda Usman ya aikata, haƙiƙa da yana wajen nan ne, yau da sai sun taru sun yi masa ɗan iskan duka, komin girman sa kuwa tunda be wuce duka ba, ƙanwar sa jinin sa ita ce yayi wa wannan riƙon, wanda kashi me ɗoyi ya fita daraja a wurin shi, yanzu da ace bata gudo ba sai ta mutu zai kawo musu gawan ta? Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un

Kaka ne kaɗai ya iya yin magana a wannan lokacin, duk da shima ɗin sosai ransa yake a matuƙar ɓace, duk son da yake yiwa jikokin sa, ba ya haɗa su da son da yake yiwa Ɗahira, zai iya ɗaukar mummunan mataki a kan abinda Usman yayi mata da ace yau yana gaban sa. Cewa yayi, “aje a duba ta domin be yarda da lafiyan ta ba, maybe wannan uƙuban da ya bata yayi sanadin sanya mata ciwo, saboda yanda ta koma, idan kuma hakan ya faru, Wlh sai yayi mummunan saɓa wa Usman, domin sai ya ga fushin sa da be taɓa gani ba”.

Daga Abba har big Dady su ma faɗan suka hau yi, domin sai yanzu bakin su ya iya buɗe wa tsaban ɓacin rai, Abbu ne kaɗai be iya cewa komi ba, amma baƙin cikin abinda Usman yayi wa ɗiyar sa, har hawaye yake share wa tsaban ɓacin rai, haƙiƙa yau da ba don akwai na gaba da shi ba, da be san me zai yanke a kan Usman ba, sai dai kawai ya bar komi wajen ƴan uwan sa, domin ya san duk matakin da zai iya ɗauka, za su ɗauka a kan shi, kuma idan ma ya ɗau mataki ya nuna ba ya da kara kenan, ƴan uwan sa basu isa da ɗiyar sa ba sai shi.

A ɗakin kaka aka duba Ɗahira, sannan aka sanya mata drip, bisa umarnin Kaka, domin yace, “babu inda za’a matsa mishi da ita, a barta ya riƙa ganin ta ko zai samu kwanciyar hankali da raɗaɗin da yake ji a zuciya”. Dole a ɗakin zata zauna, domin har alluran barci an yi mata domin samun hutu, tunda sun ga matsananciyar damuwar dake zuciyar ta na barazanar kawo matsala ga zuciyar ta, ga kuma ulcer da suka gano tana fama dashi, wanda ada bata dashi ko kaɗan

Hakan ya ƙara ɗaga wa su Big Dady hankali, haƙiƙa Usman ya cutar da ita, kuma tabbas maganar sa ya tabbata, tunda har ya ce “sai sun yi nadamar aura mishi ita da suka yi” to, tabbas yau sun yi matuƙar nadama, haɗin zumunci be amfana musu komi ba sai tsantsan nadama da dana-sani a rayuwa, haƙiƙa sun cutar da Ɗahira wanda ba sa jin za su iya yafe wa kan su har sai ita ce ta yafe musu, me ake yi da irin wannan auren na ƙaddara, sun ɗau duk wani laifi sun ɗaura wa kan su, duk wani abu su ne sila.

Aunty Amarya ta kasa fita a ɗakin Kaka, ko kaɗan ta kasa jirga wa wajen ɗiyar ta, duk dauriyan ta, da kuma kawaicin ta yau ta gaza ɓoye abinda ke ranta, domin daga baya ma kuka sosai ta dinga yi, dole Abbu ya koma rarrashin ta, ƙarshe dai Umma ta koma ta ƙarisa musu girkin daren, domin Aunty Amarya bata da juriyan ƙarisa wa, ta ɗiyar ta take yi a yanzu ɗin.

A wannan ranan mutanen gidan sun kwana cikin ƙunci ne matuƙa, sai dai ƙalilan su da suka kwana cike da murnan abinda ya faru, ko Hajiya sai da taji ɗanta be kyauta ba, domin abinda yayi sai dai mara imani, bata taɓa tunanin ƙiyayyar da yake mata zai iya aikata mummunan abu makamanciyar haka ba, duk a ganin ta suna zaune lafiya, kawai son zuciya ne ya saka ta take nuna kyara ga Ɗahiran, da kuma zigi da yayi tasiri a zuciyar ta, wanda ada ko kaɗan ba ta jin tsanar ta, amma lokaci ɗaya ta ɗaura mata karan tsana, ga shi abinda ɗanta yayi ya fi komi muni, haƙiƙa har kunyan kanta take ji, “shin da wani ido zata sake kallon iyayen Ɗahira?” Yau sosai take nadama ga bin son zuciyarta. Kuma tunda ta koma ɗakin ta take kiran Layin Usman amma a kashe ake sanar mata, tayi kiran har ta gaji don kanta ta bari.

 

Washe gari sanda Ɗahira ta farka, gaba ɗaya yaran gidan ta gani a ɗakin Kakan har shi, illa Fadila da ba ta wajen, itama taji labarin komi, domin tuni Umma ta kira ta ta shafa mata, kuka sosai tayi tsaban tausayin ƴar uwan nata, tana jin kamar tayi tsuntsuwa ta ganta a kusa da ita, amma babu hali.

Baffa ne ke zaune gefen ta ya riƙe mata hannun da ba’a yi mata ƙarin ruwa ba, su ma su Aunty Zainab da Aunty Zulaiha suna kan gadon zaune, sai Shakira dake kan drowan gadon, Kaka kuma yana can ɗaya side ɗin zaune a saman Wheel chair ɗin sa, ya zuba tagumi yana ta faman kallon ta. Inda Yusra ke zaune a can kujera, ita kanta duk taurin ranta yau dole ta tausaya wa Ɗahira, har tana jin zuciyar ta na karye wa tsaban tausayin ta, kamar ba Ɗahiran su ba, Ɗahira ƴar gayu wacce idan ma ka ganta tsaban haɗuwar ta baza ka taɓa cewa zata taɓa ƙasa ba, ita ce ta zama haka, ta zama tamkar wata almajira tsaban lalacewar da tayi, duk farin ta tsaban wahala sai da tayi baƙi, har da ƙuraje suka feso mata a fuska, wanda ada bata dasu ko ɗaya, gaskiya ta sha wahala tunda har ta koma haka kamannin ta suka sauya.

Yusra daga ita har Shakira suna da ciki, Sa’adatu ce kaɗai nata ma ya fi ƙanƙanta, don ita ko watanni biyu be kai ba, itama Fadila tana can tana fama da nata, ciwo sosai ma take yi har yanzu

Ita Sa’adatun tunda taji labarin dawowar Ɗahira ƙin zuwa tayi, tana ganin sanda Baffa ya fice amma ko bi ta kansa bata yi ba, taci gaba da kallon ta.

Baffa shi ya soma ganin farkawan ta, don haka ya sake riƙe hannun ta sosai cike da jin daɗi yana kiran sunan ta

Hakan ya ankarar dasu, sai duk suka bi ta da sannu ko wacce tana murna

Ita kuma Ɗahira kallon su kawai take yi ta kasa furta komi, duk da a ƙasan ranta daɗi ne ya cika ta

Duk sannun da suke mata ta kasa amsa wa

A lokacin ne Fadil ya shigo ɗakin, ganin ta farka sai ya fita a guje don sanar wa da Aunty Amarya, tunda dama ita tace masa, “idan ta farka ya zo ya sanar mata domin ta kawo mata abinci”. Tare suka dawo ɗakin da Fadil ɗin, ya riƙe mata coolarn abincin

A lokacin har Ɗahiran ta tashi zaune da taimakon Baffa, har ta buɗe baki tana amsa musu gaisuwar nasu tana murmushi

Kaka sai tambayar ta inda ke mata ciwo yake yi, “idan da akwai ta sanar mishi sai a sake duba ta?”

Murmushi tayi masa tana kallon sa tace, “tsoho me ran ƙarfe, babu abinda ke damu na yanzu, tunda har na ganku kusa dani hakan ya fiye min komi Wlh”.

Sallaman Aunty Amarya suka amsa da suka shigo a yanzu ɗin

Taƙarisa ta zauna inda Baffa ya tashi ya bata wuri, a nan take mata “ya jikin?”

Ɗahira ta kalle ta kamar zata yi kuka tace, “da sauƙi Mama na, babu abinda ke damu na”.

“To shagwaɓa ya tashi ko? An ga Mama”. Cewar Aunty Zulaiha tana dariya

Su ma sauran duk taya ta suke yi, har Ɗahiran da idanun ta suka cika da ƙwalla

Aunty Zulaihan ta sake cewa, “amma fa kar kiyi kukan don Allah kin ji ƴar ƙanwa ta?”

Gyaɗa mata kai tayi, tana kai hannu ta share hawayen tace, “to bazan yi ba”.

Kaka yace, “ai idan akwai ki dole sai kin saka ta kuka, sai dai idan ba Zulaiha bace ke”.

Dariya duk kan su suka yi

Aunty Zainab ta amshi coolarn daga hannun Fadil ta zuba mata abincin

Sai da Shakira ta taimaka mata ta shiga Toilet ɗin Kaka ta wanke bakin ta, kana ta soma cin abinci ana zuba hira, ita dai bata sake magana ba sai dai ta riƙa bin su da murmushi

Kaka sai da ya kore su a kan “suna damun ta” amma sun ƙi tafiya

A lokacin ne Hajiya itama ta kawo nata abincin, tayi mata “sannu da jiki?”

Yanda Hajiya ta saki fuskar ta ne, sai duk Ɗahira taji daɗi, a ranta tana mamakin sauyawan ta, wani zuciyar nata kuma tace mata, “ƙila tausayin abinda ɗanta yayi miki ne”. Gyaɗa kanta tayi kamar da wani take yi

Abincin Hajiyan duk kowa ya ɗiba suna ci ana ci gaba da hira, ita dai Hajiya tuni ta juya ta fice

Babu daɗe wa su ma su Big Dady suka shigo, sai a lokacin ne wasu suka rage suka koma Parlour

Sannu da jiki suka yi mata cikin kula wa sosai

Ɗahira ta amsa su cike da fara’a

Big Dady yace, “Daughter babu wani abinda ke damun ki yanzu ko? Kina jin ƙarfin jikin?”

“Eh Dady, alhmadulillah babu komi”.

“Ok to ga Maganin ki sai ki sha yanzu, idan kin gama Baffa kayi mata wannan alluran barcin, don ya kamata ta samu hutu sosai, in yaso idan ta tashi sai tayi sallolin da ake bin ta, amma yanzu kam hutun ta ake buƙata, ku ma ya kamata ku bar ta haka ta huta”.

Abinda Big Dady yace hakan suka yi, duk suka fita suka bar ta. Inda Baffa ya anshi maganin da alluran ya riƙe domin idan ta gama ya bata.

Bayan ta gama cin abincin sai ya bata maganin, sannan yayi mata alluran, babu jima wa kuwa barcin ya sure ta.

 

Zuwa yamma kuma duk su Aunty Zulaiha suka wuce gidajen su.

💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR’S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER’S ASSO*📖
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA’S FAMILY*_

 

*EPISODE Fifty One*

Washe gari Hajja Fatu ta tashi da tashin hankali ne, tun sassafe aka kira ta da wayan Shakira aka sanar mata bata da lafiya, a lokacin tana tsaka da shirin tafiya Office ne, domin har Abba ya wuce, nan ta zari mayafi jiki na rawa tayi gidan Shakira ba tare da ta sanar da kowa ba

Koda ta Isa ta cidda ƙanwar Sahabi ne ita kaɗai da Shakiran, dama ita ta kira ta tafaɗa mata rashin lafiyan da ta zo ta tarar da Shakiran a mawuyacin hali, ga shi Sahabin ba ya nan ya fita tun safe shima, a lokacin ne ciwo gadan-gadan ya taso mata, Allah ya jeho ƙanwar Sahabin ta biyo ta gidan domin ta amsa kuɗi wajen Yayan ta sai ta wuce school.

Sosai hankalin Hajja Fatu ya tashi da ganin Shakiran na ta zubar da jini, gaba ɗaya ta gama fita hayyacin ta. Nan ta saka ƙanwar Sahabin ta taimaka mata suka kai ta cikin motan ta, sannan taja suka nufi asibiti, yayinda ƙanwar Sahabin kuma ta koma gida don sanar da mahaifiyar su.

Suna isa asibiti a rikice Hajja taje ta kira nurse’s, aka ɗauke ta a Wheel chair, emergency Ward’s aka wuce da ita aka soma bata taimakon gaggawa

Hajja duk ta rasa tunanin da zata yi ma, sai faman goge gumin dake tsatstsafo mata a goshi take yi, duk da kuwa garin babu zafi luf-luf ne kamar za’a yi ruwa ma. Ruɗun da ta shiga be bari ta sanar wa kowa ba

Sai Baffa ne da yazo wuce wa ya hange ta a wannan yanayin, sai faman sintiri take yi tana kaɗa hannaye, nan ya iso wajen ta yana tambayan ta abinda ke faruwa ya ganta a nan? Tunda ya san ba nan ne Office ɗin ta ba

Kallon sa tayi kamar zata yi kuka tace, “Shakira CE babu lafiya, an kira Ni na je na ganta a mawuyacin hali tana ta zubar da jini, tamkar ma bata da rai”. Sai ta fashe da kuka tsaban shiga tashin hankali, fatan ta kawai Allah yasa ba wani abu bane zai sami ɗiyar ta, su kenan mata su biyu, idan ta rasa ta bata san ya zata yi ba

Jin abinda Hajjan ta faɗa sai shima hankalin nasa ya tashi, nan ya soma tambayar ta “to garin ya hakan ta faru? Ina Mijin nata?”

“To wa ya san inda mijin nata yake, ƙila yana wajen aiki ne, amma Ni da naje babu shi”.

“To bari in faɗa ma su Abba, ina zuwa”. Yafaɗa da sauri yana yin gaba.

 

Sanda likitan dake duba Shakira ya fito, sai duk suka nufa wajen sa, kama daga kan su Abba har su Yusra duk suna wurin, sai kuma mahaifiyar Sahabin ita da ƙannin sa biyu maza, tambayar sa “jikin nata suka yi?”

Likitan yace, “yanzu babu wani matsalan dake damun ta su kwantar da hankalin su, ɓari tayi shi ne yaja mata zuban jinin, amma da zaran ma ta farka komi normal ne sai abinda ba’a rasa ba”.

Kowa alhmadulillah yake faɗa, ba kamar Hajja Fatu da duk ta fi su shiga tention

Nan Doctor ɗin yace, “za su iya shiga su ganta”. Kafin nan yace, “yana son ganin su Abba a keɓe”.

Su ukun duk ka suka bi shi, sai da suka shiga Office ɗin nasa suka sami wuri suka zauna

kafin likitan yace, “am.. DOCTOR’S gaskiya yarinyan nan ba haka kawai cikin jikin ta ya zube ba, naga kun yi yawa ne shiyasa ban faɗa muku matsalan a waje ba, akwai ƙwayoyin da tasha su wanda su suka zubar mata da cikin, ba don Allah ya tsare an kawo ta da wuri ba wlh da an sami matsala, domin ƙwayoyin suna da illa sosai, saboda suna aiki a jikin mace in two minutes, ƙarfin sa yana sa mace ta sami matsala a mahaifar ta, ko kuma wasu matsalan dai wanda ba ma fatan hakan”.

Duk shiru suka yi da jin bayanin likitan

Inda yaci gaba da faɗin, “amma ya kamata ta kiyaye gaba, domin idan ta sake amfani dashi abinda ake gudu zai faru ne”.

“Ok mun gode Dr. Bashir, babu matsala yanzu zamu iya tafiya?” Cewar Abbu kenan yana kallon sa

“Eh babu komi, duk wasu magunguna mun rigada mun bata tasha, da zaran ta tashi zata farka da kuzarin ta insha Allahu”.

Sallama suka yi masa suka fito, babu wanda ya sake tayar da maganan har suka je suka duba ta suka fito, Office suka wuce tunda a lokacin tana barci ne. Sai bayan ta tashi ne Big Dady da Abbu suka dawo a tare, a lokacin babu kowa wajen ta sai Hajja Fatu

Don haka Big Dady bayan sun yi mata sannu da jiki sai yace da ita, “ke Shakira tashi zaune zamu yi magana”.

Tashi tayi kamar yanda yace mata, kanta a ƙasa ganin yanda suke bin ta da kallo, har wani zillo gaban ta yake yi domin gani take yi tamkar tayi laifi ganin yanda suka ɗaure fuskar su

Hajja dai itama shiru tayi tana jiran jin abinda zai faru

Big Dady yace, “ya aka yi kika sha maganin zubar da ciki? Dama ashe baki da hankali bamu sani ba?”

“Zubar da ciki kuma?” Inji Hajja Fatu tana bin su da kallo, kana kuma ta mayar da idanun ta kan Shakiran don itama taji amsar nata

Ita kuwa zare idanu tayi tana ƙifƙifta su, sai kuma ta fashe da kuka sosai kamar an yanka ta

Hakan yasa Abbu yace, “bayani zaki yi mana ba kuka ba, ba ma son sakarci kinji ko? Yanzu da ba don an kawo ki asibiti da wuri ba; bamu san matsalan da zai same ki ba, sai dai Allah ya rufa asiri ya tsare babu abinda ya faru dake, amma kin rasa cikin tunda hakan kika fi so”.

Cikin kuka tace, “wlh wlh Abbu wlh ku yarda dani ba Ni ce na sha maganin zubar da ciki ba, wlh sai dai idan Sahabi ya saka min a wani abun nasha, amma wlh ban sha komi ba”.

Hajja Fatu da tsaban takaici ya cika ta na jin an zubar mata da cikin jikan ta, tace, “Dan uban ki taya Sahabi zai baki maganin zubar da ciki ki sha? Idan ba ke ce kika san irin magungunan ba shi Sahabi taya zai baki ki sha?”

“Wlh Hajja shi ya bani, dama can ba ya son cikin, yayi-yayi in zubar amma naƙi na ce masa ina son Abu na, Amma sai da ya san yanda yayi ya zubar min”.

Big Dady yace, “to ya isa haka, kiyi shiru, but yau kin sha wani abu ne da safe da kika tashi?”.

Gyaɗa masa kai tayi sai tace, “eh nasha fura dana tashi, lokacin ina sha babu jima wa naji ciki na yana murɗa wa, daga nan ne na fara jin ciwo”.

Jinjina kai suka yi kafin suka sake mata sannu tare da kwantar mata da hankali sosai, sannan suka fice.

 

Suna fita Hajja ta soma mata faɗa a kan “meyasa tun farko da yace zai zubar da cikin bata zo ta sanar mata ba? Ai da tayi wa tufkar hanci, amma ga shi yanzu ya cuce su ya zubar da cikin”.

“Hajja wlh ban yi zaton abun zai kai haka ba, da fari da ya tayar da fitinan sai an zubar faɗa muka yi tayi dashi, daga ƙarshe yace min ya haƙura, tunda mun yi hakan dashi ne tun lokacin da cikin yake ɗan wata ɗaya da muka gane ina da ciki, ashe wayau yayi min akwai abin a zuciyar sa har yanzu”. Ta ƙare maganar tana me fashe wa da sabon kuka

Hajja rarrashin ta ta hau yi kawai tunda me afkuwa ya riga da ya afku, sai dai kuma a koke gaba.

 

Mutanen gida duk sun zo tunda labari ya je musu Shakira na asibiti, Ɗahira ne da Kaka kawai basu samu damar zuwa ba, Ɗahira na fama da nata jikin, tunda yanzu sosai zazzaɓi ya rufe ta, ko kaɗan ba ta jin daɗin jikin ta, ƙarin ruwa ake ta mata, duk da yanzu alhmadulillah ba kamar jiya da ta kwana dashi ba.

 

 

Har yamma yayi babu Sahabi babu labarin sa, kuma duk ƴan uwan sa suna ta zuwa gaishe ta, zuwa dare aka sallame ta tunda jikin da sauƙi babu wani abu, kai tsaye su Big Dady gida suka wuto da ita, sun yanke shawaran baza ta koma ba har sai Sahabi ya zo ya same su.

Be zo ɗin ba sai washe gari da rana, lokacin duk suna Hospital, Hajja Fatu ce kawai bata je ba ta zauna kula da Shakiran, wajen Kaka ya soma zuwa ya gaishe sa

Kaka ya amsa shi kamar babu wani abu tunda shima be nuna komi ba, illa neman gafara da ya nema a kan rashin zuwan sa a jiya ya duba ta, wai “akwai babban abinda ya tsayar dashi ne.”

Waya Kaka ya ɗauka ya kira su big Dady ya sanar musu da zuwan Sahabi wai “ya zo ɗaukar matar sa”.

Tare da Abbu da Big Dady suka taho, don shi Abba ƙin zuwa yayi, suna zuwa suka tarar dashi har yanzu yana tare da Kakan, har an ajiye masa abin motsa baki. Bayan sun gaisa dashi

Sai Big Dady yace, “Sahabi abinda yasa muka nemi ganin ka kaima mun san ka sani, jiya matar ka ta yi ɓari har ta kwanta a asibiti amma ka kasa zuwa ka duba ta, Dalili kuwa shi ne saboda baka ɗauke ta da wani muhimmanci ba, sannan kuma saboda kai ne ka jawo musabbabin ciwon nata, kar ka manta mu nan gidan likitoci ne da ko wane fanni mun san matsalar sa, a tunanin ka idan har ka zuba mata magani a abun sha tasha cikin ya zube baza mu gane bane? To, kayi wa kanka ƙarya, don me idan ba ka son ciki zaka bari ku ɗauka? Idan da wani matsalan ya sami ɗiyar mu wato ba ka da asara ko?”

Gumm Sahabi yayi kansa a ƙasa, har gumi ya haɗa domin be yi tunanin sun gano shi ba, ga shi kai tsaye suke tuhumar sa da shi ne ya saka mata, be da kuma da yanda zai yi

Abbu ya amshe maganar da cewan, “ai Yaya babu maganar yana so ko ba ya so, tunda har yayi aure to dole ne ya haihu kamar yanda Annabi yace mu hayayyafa domin yayi alfahari damu, idan be son haihuwar babu dole sai ya sakar mana ƴar mu, idan ba haka ba wata rana zai je ya naƙasa mana ita kuma shi be da halin biyan mu, kayi magana ka tsaya ka sunkuyar da kai? Amma wlh ka bamu kunya bamu zaci haka a gare ka ba, ka watsa mana ƙasa a ido”.

Kaka dai duk yana sauraron su be ce komi ba

Haƙuri ya soma basu Sahabin yana cewa, “insha Allahu bazai sake ba, wannan ma kuskure ne amma wlh yana son matar sa”. Duk ya gama haɗa gumi ya nuna musu nadamar sa a fili

A nan ne Kaka ya saka baki, inda yayi mishi nasiha me ratsa zuciya, kafin yace, “ya tafi zuwa gobe sai ya zo ya tafi da matar sa, amma yau dai ya bar ta a nan tunda zata fi samun kulawa”.

Godiya sosai yayi musu kana ya miƙe ya bar gidan, be ma nemi ganin Shakiran ba ya wuce.

 

To al’amarin haka dai ta faru, zuwa gobe Shakira ta koma gidan ta.

 

 

Inda rayuwa taci gaba da tafiya sannu a hankali, kwana na wuce wa haka satikai, har ga shi yau wata ɗaya da dawowar Ɗahira daga Turkey, kuma har yanzu babu labarin Usman gaba ɗaya, wayan sa ma ba ta shiga. Zuwa yanzu Ɗahira ta samu lafiya sosai, ta koma kamar ba ita ce ta dawo ƙoɗai-ƙoɗai ba, ta murje tamkar bata yi wani ciwo ba, tunda tana samun kulawa sosai, yanzu haka ma har ta koma bakin aikin ta duk sabida ya ɗebe mata kewa, tunda ko yaushe neman hanyar da zai ɗebe mata kewa suke yi, su Abbu sosai suke iya ƙoƙarin su wajen sun saka ta cikin nishaɗi, alhmadulillah kuma komi na tafiyan mata normal, don ita har ta manta ma ta taɓa yin aure, ko Usman ɗin ba ta tuna wa bare auren dake kanta, jira kawai take yi yanzu ya dawo mata da takardan sakin ta, aure kuma ta cire sa a ranta tuni, ko idan zata sake aure ba yanzu ba.

 

Yanzu sosai suka sake jone wa da Baffa, don shaƙuwar su ta yanzu har tafi na da.

 

Hajja Fatu sai dai ta zuba musu idanu babu yanda zata yi dasu, domin dai duk faɗan da take masa ba ya sauraron ta, shi a ganin sa kusantar Ɗahira na rage masa raɗaɗin da yake fama dashi, tunda har giyan nasa ya dena sha sosai, duk yanda ya lalace ya bar ƙasumba a fuskar sa yanzu duk ya gyara, ya koma ɗan gayen nan nashi da duniya ta san shi, burin sa yanzu kawai Usman ya dawo ya bata takardan sakin ta, a lokacin shi kuma zai fito ya nuna wa kowa shi zai aure ta, ya shirya tsaf ko wani irin Fitina ne ma a yi.

 

Ana haka sai ga Usman ya dira a ƙasan, ba da sanin kowa ba ya hayo taxi ta kawo sa gida, ana sauke sa ya nufi gidan su, ta Gate ɗin gidan ya shiga, har ya isa Part ɗin sa babu wanda ya ganshi ba ya ga me gadin da ya buɗe masa Gate.

 

Gaba ɗaya Part ɗin yayi ƙura sosai, kusan wata biyu babu wanda ya sake shiga tun tafiyar su, be bi ta kai ba ya wuce kansa tsaye ɗakin sa, wanka ya soma yi ya fito ya sanya jallabiya ya soma ramukon sallolin sa, yana idar wa yabi lafiyan gado sai Barci, da zummar idan ya farka sai ya je gidan su ayi duk abinda za’a yi, ya shirya wa ko ma meye ne, bare ma ya san cewa yanzu sun sauka daga fushin da suke yi dashi, cikin kwanciyar hankali yake barcin sa babu abinda ke damun ruhin sa.

 

 

 

 

 

 

_Yanzu aka soma wasan fa, ku gyara zama kawai._
💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR’S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER’S ASSO*📖
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA’S FAMILY*_

 

*EPISODE Fifty Two*

Bayan ya tashi daga barcin alwala yayi ya gabatar da sallan la’asar da ake kira a lokacin, bayan ya idar sai ya shirya cikin ƙananan kaya kamar yanda ya saba ko yaushe, riga baƙa da blue ɗin wando jeans, kayan sun haska shi sosai domin sosai suka yi masa kyau, komin sa yana yi ne a natse a kuma sanyin yanayin sa, turare ya feshe jikin sa dashi kana ya ɗauki wayan sa ya saka a aljihun bayan wandon sa ya fito daga gidan, hannayen sa zube cikin aljihu yana bin yanayin garin da kallo, da alamu hadari ne ke son haɗuwa domin har an fara yayyafi kaɗan-kaɗan duk da akwai rana be gama shige wa ba, murmushi kawai yake saki wanda samun ka ga yayi sa aiki ne, yana bala’in son wannan yanayin na damina, a ransa yana jin daɗin dawowar sa a dai-dai, ya san yanzu can kafin daminan su tayi nisa nan sun sha ruwa sosai

Tafiyan sa a natse yake yi har ya isa cikin babban gidan su, kai tsaye Part ɗin su ya wuce, yana tura ƙofan da sallama a bakin sa

Hajiya dake ƙoƙarin zama a kan kujera domin fitowar ta kenan daga ɗaki ta idar da sallah, da zummar idan ta huta ta tashi ta ɗaura girkin dare, sai jin sallaman ɗan nata tayi kamar a mafarki, hakan yasa tabi sa da kallo don ta kasa amsa mishi sallaman ma

Shi kuwa murmushi ya sake saki, sabida haka kawai yake jin sa cikin farin ciki, duk da a wani ɓangare na zuciyar sa yana jin wani irin buga wa da take yi tamkar wani abu na shirin samun sa, amma hakan ya ɗaura dalilin ne kan dawowar sa da gamuwar sa da iyayen nasa, amma kuma duk abinda za su yi shi dai a shirye yake

Muryan Hajiyan ne ya dawo dashi hayyacin sa

“Usman idon ka kenan?”

Takowa yayi ya zauna a kan kujeran dake kallon inda take tsaye

Hakan yasa itama ta zauna tana shirin magana

Sai ya riga ta ya gaishe ta

Amsa wa tayi fuskar ta babu wani walwala tace, “yanzu ka kyauta kenan? Abun da ka aikata ka kyauta mana kenan Usman ina tambayar ka?”.

Shiru yayi kawai be ce mata komi ba, illa shafa ƙeyan sa da yake yi, sai dai ya rage walwalan dake fuskar sa

Cike da takaicin halin sa tace, “wlh kai da Dadyn ka tunda irin tarbiyyan da muka baka kenan, ka jira shi ya dawo zaka ka hukuncin da za su yanke a kanka”. Tana faɗa ta tashi tayi hanyar kichen

Shi kuwa da kallo ya bi ta har ta shige, kana ya miƙe ya nufi kan dainning ganin cololi da yayi a jere, sai da ya buɗe yaga akwai abinci kafin ya zauna bayan ya zaro wayan sa daga aljihu, zuba abincin yayi a Plate ya soma ci, latsa wayan yake yi yana faman zira abincin kaɗan-kaɗan a bakin sa, duk da yunwa sosai yake gallabar sa amma hakan be sa ya ƙi wa abincin cin yanga ba.

 

Be gama cin abincin ba Big Dady ya shigo parlour’n da sallama, babu inda idanun sa ya sauka sai kan Usman dake shirin kai abinci bakin sa a wannan lokacin, ido kawai Big Dady ya zuba masa

While shi kuma tuni ya tashi tsaye yana gaishe shi daga inda yake

Be amsa mishi ba illa tahowa da yayi cikin parlour’n, fuskar sa murtik yake kallon sa har ya shigo ciki sosai, kana kuma ya ɗauke kai yana kwaɗa wa Hajiya kira

Hajiya ce ta fito daga kichen da sauri tana amsa mishi, kana kuma ta ɗaura da mishi sannu

Sai be amsa ba ya jeho mata tambayar “me wannan yaron yake min a nan? Ban faɗa miki saƙo na duk ranan da ya dawo kar in sake ganin ƙafafun sa a nan ba?” Be bari kuma Hajiyar tayi magana ba ya mayar da idanun sa kan Usman dake tsaye har yanzu kansa a ƙasa, “fitar min a gida dan uban ka, kai wato baka da mutunci ko Ban isa da kai ba? Wuyan ka yayi kaurin da har zamu zaɓa maka abu, amma ka ce mun yi kaɗan, dole sai ka nuna mana iyakan mu, to, saƙon da ka aiko ta tafaɗa mana ta sanar mana, cewa “sai mun yi dana-sani ko?” Eh tabbas mun yi dana-sani wlh ba sau ɗaya ba, yanzu zaman uban me kake min a wajen nan?”

Sumui-sumui Usman yazo zai wuce ya fice

Big Dady ya dakatar dashi, “dan uban ka ina takardan nata?”

Shiru yayi

Nan kuwa Big Dady ya zuciya ya daka masa tsawa, “da kai nake magana kayi min shiru?”

Cikin sanyin murya yace, “ban rubuta ba”.

Ƙwafa yayi kafin ya zauna yana cewa, “kar ka sake in sake maka magana a karo na biyu”.

Juya wa Usman ɗin yayi ya fice.

 

Hajiya dake tsaye duk ranta babu daɗi, ta san dama za’a rina duk da tabbas kamar yanda Usman ke hasashe ne fushin da suka ɗauka sun huce, amma da a lokacin ne ta san faɗan da zai sha sai ya fi haka, tana matuƙar son Usman duk cikin yaran ta, shiyasa ko kaɗan ba ta ƙaunar wani abu ya shiga tsakanin su da mahaifin sa, duk da shi ya jawa kansa. Ajiyan zuciya ta sauke kana ta sami wuri ta zauna tana kallon Dadyn, tace, “Dadyn Zainab don Allah ka sassauta wa wannan yaron, abinda ya faru ya rigada ya faru, yanzu sai dai mu ce Allah ya kyauta na gaba..”

Katse ta yayi da faɗin, “dalla rufe min baki, duk ba ke kike ɗaure wa yaron nan gindi ba, kar ki manta fa duk wani rashin ƙaunar auren nan da kike yi a baya yana raina kuma ban manta ba, ta yiwu da haɗin bakin ki yayi ma Daughter wannan abun da yayi”. Ya ƙare maganar yana miƙe wa cikin zafi ya wuce ɗakin sa

Sosai Hajiya ta shiga damuwa da jin zancen sa, “innalillahi wa’inna ilaihi raji’un yanzu Ni yake zargi na saka Usman abinda yayi?” Shiru tayi kawai duk jikin ta yayi sanyi domin ta kasa tashi ma tayi abinda ke gaban ta, zuciyar ta na nadamar abinda ta aikata tun farko na nuna ƙiyayyar auren, yanzu ga shi hakan na son jawo mata matsala da mijin ta, yana zargin ta da ita ce ta ziga Usman, kuma babu yanda za’a yi ta kare kanta tunda tun farko ta nuna ba ta ƙaunar auren.

 

 

⚫⚫⚫

Usman kuwa yana fita gida ya koma ya ɗauki motan sa ya fice, be damu da dauɗan motan ba so yake yi kawai ya samu relif a zuciyar sa, gaba ɗaya yanzu jin sa yake yi wani iri, abinda yake ji a ƙasar zuciyar sa dake buga wa tana sake taso masa tana mamaye zuciyar, tsaki yaja a ransa yace, “kai fa kace zaka iya ɗaukar duk wani abinda zai faru? Ba ga shi yanzu faɗan Dadyn naka ya wuce ba, saura kuma nasu Kaka suyi nasu su gama”. Da wannan tunanin nasa ya ɗan samu ƙwarin gwiwa, sai dai yanayin da yake ji a zuciyar sa kwata-kwata ba ya jin daɗi, ya fi jin hakan duk sanda ya haɗu da wancan yarinyan (yana nufin Ɗahira. Fargaba da tsoro a zuciyar sa) amma abun mamaki yau kuma ba ta kusa dashi amma yake ji. Kamar an ce ya wulƙa idanun sa gefen daman sa, ai kuwa sai ga ta tazo ta wuce sa a motan ta, be yarda ita bace sai da yabi motan da kallo ta mirror, kuma tabbatas ya gane ita ce tunda ya ga fuskar ta, sosai ya haɗe rai ganin motan nata ta faka a bakin titi, sai ya ɗauke kai yana jin kamar ya koma ya sanar mata tun yanzu ya sake ta, sai dai kuma ba ya ƙaunar ganin fuskar ta, gwara idan ya koma gida ya rubuta sakin ya miƙa wa Dady, haka ya ƙara wa motan wuta yana jin kamar ya ciro zuciyar sa ya jefar tsaban abinda yake ji.

 

 

⚫⚫⚫⚫⚫⚫

Ɗahira kuwa da ta faka motan ta a bakin titi fito wa tayi, duba tayan ta soma yi abinda take zargi ne tayi faci, sai taja dogon tsaki cike da takaici, “oh Allah ka taimake Ni, wlh motan nan kin yi min wulaƙanci tunda kika tsaya min a hanya, yanzu ya zan yi?” Sai ta sake jan tsaki tana koma wa cikin motan, wayanta ta ɗauka tana neman Numban bakaniken su, amma a kashe ake ce mata, maida akalan kiran tayi kan Numban Baffa, shi kuma ba service, gaba ɗaya duk ta damu domin ta san ruwa zai iya riskan ta a nan, dole ta yanke shawaran hawa keke napep ya ƙarisa da ita gida, inyaso ta bar motan a nan me gyara yazo ya gyara. Jakan ta ta ɗauka ta fito ta rufe motan da keey, kana ta ƙarisa bakin titin sosai don ta samu abun hawa, kasancewar hanyar babban titi ne ba kasafai suke tsaya wa ba, duk yawanci ma akwai mutane shiyasa tasha wahalan samu. Tana nan tsaye sai mota ta faka a ɗan nesa da ita kaɗan, kallon motan tayi da kyau, ta gane ko na wane ne, na Dr. Said ne tunda yanzu ma kafin ta fito sai da suka yi sallama dashi a wajen motan nasa, kafin ma ta gama tunanin nata

Sai gani tayi Abokin sa Dr. Sabo ya leƙo yana mata alama da hannu ta taho

Nufan wajen tayi kanta tsaye, tana isa sai ta leƙa gaban domin tayi masa magana, sai dai ba shi ne a motan ba, wani mutum ne sai Dr. Sabo a gaban, murmushi tayi tace, “sannu Doctor ai nayi zaton Dr. Said na ciki ne?”

Shima yana murmushi yace, “a’a ba ya ciki, amma ki shiga sai mu sauke ki ko? Ina ce motan taki ce ta samu matsala?”

Gyaɗa kai tayi tace, “eh tayi faci ne”.

“Ok ki shiga kawai mu sauke ki”.

Godiya tayi masa ta buɗe baya ta shige, suna jan motan suka tafi.

Usman da yaje ya kewayo zai koma gida duk a kan idanun sa Ɗahiran ta shiga cikin motan, taɓe baki yayi yana bin bayan su, a ransa yana mamakin “ita wannan yarinyan har yanzu bata dena abun tsiyan nata ba?” Tsaki yaja a fili ya furta “karya kawai, idan da kun san abinda na sani a game da halin ta wlh da baku yi fushi dani ba”. (iyayen sa) Yayi maganar yana sake haɗe ransa tamkar da wani yake yi a gaban sa.

 

Sanda suka isa layin anguwar su memakon yaga motan ta shiga cikin anguwan nasu, sai yaga taci gaba da tafiya, be yi mamakin hakan ba illa shige wa layin gidan su da yayi, amma a ransa sai yayi tunanin “why not yau ya samu hujjar da zai gabatar wa iyayen sa a matsayin abinda ya saka yaƙi yarda da zaɓin su? Idan ya bi su ya gano abinda suke yi sai ya ɗauka a waya ya nuna musu”. Wannan shawaran ta zuciyar sa ita yayi na’am dashi a lokaci guda, sai ya juya motan nasa nan da nan yabi hanyar da suka bi, ko kaɗan ba ya hango motan tasu, hakan yasa ya ƙara Speed sosai, ai kuwa sai ga su har ya kamo su yana bin su a baya ba tare da sun sani ba.

 

 

****** *******

A cikin motan kuwa tunda Ɗahira ta shiga ciki bata yi tunanin akwai kuma wani a baya ba, sai da ta zauna kafin ta kula dashi, har taji tsoro tana shirin magana ya rufe mata hanci da baki da handkerchief, Lokaci ɗaya numfashin ta ya ɗauke tayi luuu ta zube jikin sa

Dariya suka kwashe dashi duk kan su, shi kuma yana gyara mata zaman ta da kyau

Wanda ke tuƙin yana ci gaba da dariyan yace, “ai wlh aikin nan da muka yiwa Dacta dole sai ya ƙaro farashi, don bazai yiwu ba muna ganin wannan zuƙeƙiyar budurwan kyakykyawa da ita muna gani mu barta ba tare da mun dangwali fa’ida ba”.

Dr. Sabo yace, “kai ina ruwan ka? Kana ji fa ya ce auren ta zai yi idan sun tafi can, ka dena haka don Allah”.

“Ai don na san yace hakan ne shiyasa baza mu siɗe masa kwanon ba, dole ne fa ya ƙaro mana kuɗi idan dai muka kai ta, domin duk wanda muka yi masa wannan aikin yana barin mana siɗi, amma shi babu abinda zai bar mana”.

Na bayan yace, “haka ne wlh, domin wlh oga wannan yarinyan tana da farashi kamar yanda kace, ka ganta kuwa?”. Ya ƙare maganar yana shafa fuskar Ɗahira da bata san ma yana yi ba

Dr. Sabo dai be ce musu komi ba illa ƙoƙarin kiran Dr. Said da yake yi, sai dai layin ba ya shiga saboda yanzu hadari sosai ya haɗu, garin yayi duhu sai iska da aka fara, ɗagowa yayi yana kallon me tuƙin yace, “layin sa fa ya ƙi shiga, ina yace zamu same sa a hanyan?”

“A’a ai be faɗa mana ba, sai dai idan zamu juya da ita mu kai ta gidan da muka haɗu dashi”.

Shiru dai Dr. Sabo yayi yana ci gaba da gwada layin, sai kuma yace, “wlh ka san Allah ba don ta ganni cikin motan nan ba baza ta hau ba, komawan mu akwai matsala, kawai ka faka a can mu nemi service mu rabu da alaƙaƙai tun kafin ƴan sanda su cafke mu, Ni wlh ban ma san ya aka yi na biye wa Dr. Said a wannan shirin nasa ba, da ya zo yayi kayan sa da kansa”.

Faka motan suka yi a gefen titi, domin har sun kusa fita cikin gari sun tasar wa hanyar Zaria, dama a hanya suka yi da Dr. Said ɗin zai amshi Ɗahiran ya wuce da ita Zaria, a can iyalan sa suke, daga can yake zuwa nan aiki, shirin da suka yi ya saka a sato masa Ɗahira ne domin yaje ya ajiye ta a wani gidan sa da yake dashi a Zarian ba inda matar sa take zaune ba, dawowar Ɗahiran a bakin aikin ta ya sake shige mata sai da suka ƙulla alaƙa, domin tun sanda ya sake ganin ta burin da ke ransa ya sake taso wa, dama yana kwaɗayin ta sosai, sai kuma zuciyar sa ta raya masa why not ya sace ta ta zama nasa kawai? Da taimakon wani abokin sa ya ba shi ƙwarin gwiwan ya sace Ɗahira ya ajiye ta a ɓoye ta zama tamkar matar sa, kuma zai riƙa zuwa wajen ta ne ba tare da ta san shi ne ba. Hakan yasa ya faɗa wa Dr. Sabo ƙudurin sa, shi kuma ya samo masa waɗannan mutanen domin su yi masa aikin, tunda dama kidnapping shi ne sana’ar su, da kuma yiwa yaran mutane Fyaɗe idan sun sace su.

 

 

 

******

Usman dake bayan su yana ganin duk abinda ke faruwa, da tsayar da motan nasu da kuma fitowar da suka yi har su uku, suka ɗan yi gaba suna ɗaga wayoyin su, hakan ya gane suna neman service ne, sosai wannan abun ya ba shi mamaki, har a ransa ya ɗarsa zargin su lokaci ɗaya, “kar dai ace kidnappers ne su? To me zai saka taje wajen su da kanta?” Wani zuciyar nasa tace masa, “ta yiwu neman taimako take a wajen su tunda motan ta tayi faci”. Sai yayi shiru kawai yana tunanin abun yi, duk yana kallon su, kuma be damu su juyo su hange sa ba, tunda tazaran su babu nisa da inda yayi parking

Lokaci ɗaya yabi shawaran zuciyar sa, sai ya fito ya nufe su, ba tare da fargaba ko wani tsoro ba, shima wayan sa na hannun sa yana shirin neman layin wani daga cikin ƴan gidan su ya sanar musu da abinda ke faruwa, amma kuma wayan babu service, gaba ɗaya kiran da yake yi taƙi zuwa. Yana isa wajen motan duk basu san da zuwan sa ba tunda suna ta gaban motan ne sun juya wa motan baya. Leƙa motan yayi, ilai kuwa zargin da yake yi haka ne, kwance ya ganta tamkar matacciya ba ta numfashi, lokaci ɗaya ya saka hannu ya janyo ta tare da saɓata a kafaɗa yana juya wa da sauri ya nufi motan sa

A lokacin ne aka saki ruwa me ƙarfi wanda yaja mutanen suka juyo don shiga motan su su samu mafaka, kawai sai suka hangi Usman har ya kusa isa motan sa ɗauke da Ɗahira a hannun sa, basu tabbatar ba sai da suka duba cikin motan suka tabbatar da ita ce, ai kuwa nan suka bi bayan sa da gudu, ɗaya daga cikin su ya ciro bindiga ya soma harba masa

Take a nan Usman ya ƙara da gudu, yana isa motan ya buɗe ya ajiye ta a wajen me zaman banza, shi kuma ya zagaya ɗaya side ɗin da gudu yana duƙa wa don kar su same sa ya shige yaja motan, saboda ruɗewa ma kasa yin reverse yayi sai ya Yi kansu

Ganin haka sai suka dare don neman ceton ransu

Shi kuma tuni ya yanki jeji da gudu

Ɗaya daga ciki yace, “Mu bi shi mana me muke jira? Kaji min ɗan isa har yana da ƙarfin halin biyo mu ya ɗauke ta?”.

Tuni sun isa motan su sun shige, amma Dr. Sabo ya kasa bin su, gaba ɗaya ya ruɗe domin gani yake yi asirin su ya tonu, duk da be gane Usman bane amma ya san cewa duk wanda ya biyo bayan su ya san su, shiyasa duk ya ruɗe

Su kuwa tuni sun tafi sun bar shi a wurin sun bi bayan Usman

Usman dake tuƙi a cikin sunkuru, neman hanyar da zai yi ya fita titi yake yi, sai buga uban tsaki yake yi cike da dana-sanin abinda yayi, sai yanzu ma hankalin sa ya dawo jikin sa ya tuna wacce yazo ceto, maƙiyiyar sa wacce ya tsana a duk faɗin duniyar nan, ji yake yi kamar ya tsaya ya buɗe motan ya jefar da ita don haushi, sai dai yana tsoron kar su kama sa su harbe sa tunda yana hangen sun kusa kamo shi ma, sosai yake gudu a sunkurun ga ruwa da ake zuƙa wa a yanzu ɗin, titi ya nufa da gudun sa ko kaɗan be damu da ruwan ba, fatan sa kawai ya fita titi don yaji daɗin guje musu, sai dai be kula ba ashe ta wajen gada ya biyo, babban magudanan ruwa ne a wurin. santsin ruwa dana ciyayi suka ja shi ya karkace hanya lokaci ɗaya motar tasa ta gangara ƙasan gadan dake cike da ruwa, duk ƙoƙarin da yayi don ganin ya samu ya fita kafin motan ta shige sosai amma ya kasa, lokaci ɗaya suka afka ciki ji kake yi cindimm..

 

Ba don Allah yasa su ma sun ja wawan burki ba, da tuni tasu motan su ma ta afka, domin uban gudun da suka shanyo, dole suka ja birki lokaci ɗaya, ganin motan Usman har ta nitse ai tuni sun juyar da nasu sun bar wurin, inda Dr. Sabo yake suka je suka ɗauke shi suka gudu.
💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR’S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER’S ASSO*📖
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA’S FAMILY*_

 

*EPISODE Fifty Three*

Aunty Amarya shiru-shiru taji yau Ɗahira bata dawo kamar yanda ta saba ba, domin tunda ta koma bakin aiki, to, ba ta wuce 05:30pm. Take dawowa gida, ko shida ba ta kaiwa yanzu, bare yau ana ruwa tayi tunanin zata dawo da wuri. hankalin ta duk ya tashi hakan yasa bayan ta idar da sallan magriba sai ta fito Parlour ko cire hijabin jikin ta bata yi ba, zama tayi tana jiran Abbu ya dawo masallaci sai ta sanar masa, dayake wayan ta ta lalace kwana biyu, to, bata samu an gyara mata ba

Zaman ta babu daɗe wa Fadil ya shigo da sallaman sa

Tana amsa mishi sai tace, “yauwa Auta zo ka kira min Numban Yayar ka, har yanzu bata dawo ba ban san me ya tsayar da ita ba”.

“To Aunty bari in ɗauko wayan a ɗakin Umma na bar ta da zan je Masallaci”. Wuce ta yayi da sauri ya shiga ɗakin Umma dake sallah ya dauko ya dawo

Koda ya kira wayan a kashe ne, yayi try har sau biyu a kashe ake ce masa, sai ya kalli Aunty Amarya dake kallon sa ko ƙyafta idanu ba ta yi, duk da tana jin an ce wayan a kashe, amma ta kasa magana, yace da ita, “Aunty a kashe ne fa”.

“Sake kira min, me ya sami wayan nata da zata kashe? Ai yaci ace ta dawo yanzu ko?”

“Haka ne Aunty, yanzun ma ga shi a kashe”.

A lokacin Abbu yayi sallama ya shigo parlour’n

Duk suka amsa mishi suna bin shi da kallo

Shima ganin su cirko-cirko sai yace, “lafiya me ke faruwa?”

“Wlh ba lafiya ba Abbun Zulaiha, Ɗahira CE har yanzu bata shigo ba, kuma na san idan wani wuri taje dole zata faɗa mana, sannan wayan ta ba ya shiga ma”.

“To fa subhanallah.. amma kin san halin ta akwai son aiki, yanzu haka ta samu wata patient ne hakan ya tsayar da ita wajen duba ta, kin san ta ai”.

“To yanzu shikenan Abbun su baza a bincika a gani ba? ka san fa bata taɓa kaiwa haka ba, yanzu ana shirin kiran sallan isha’i fa”. Cewar Aunty Amarya cike da damuwa

Abbu yace, “ki kwantar da hankalin ki don Allah, bari in saka takwara ya bi ta ya gano mana ko lafiya, kai Fadil kira min Baffa”.

“To Abbu”. Fadil ya amsa mishi yana fice wa

Itama Umma a lokacin ta fito tana tambayar abinda ke faruwa

Aunty Amarya ta sanar mata

Sai cewa tayi, “to Allah ya kyauta, Allah yasa dai lafiya”.

“Amin”. Inji aunty Amarya tana zama, tunda tun sanda aka soma zancen ta tashi tsaye

Shima Abbu zaman yayi yana ɗaukan wayan sa don ya gwada kiran ta

Yayinda Umma ta wuce kichen don kwaso abinci ta shirya a dainning.

Sanda Baffa yazo, Abbu ya sanar masa “yabi bayan Ɗahira asibiti ya dubo ta”.

Da Fadil suka tafi a lokacin ruwan ya ɗan tsakaita. sun je har asibitin an tabbatar musu da tafiyan ta, hankalin su sosai ya tashi da jin ta daɗe da tafiya ma tun biyar da ashirin yau ta fice.

 

Sanda za su dawo gida ne Baffa ya hangi motan ta a kan hanya, tunda da za su je be kula ba saboda ba ta side ɗin suka biyo ba, nan suka fito da sauri suka nufi motan, duk sun duba babu ita ga shi motan ma a rufe ne, a nan ne hankalin nasu ya sake tashi ainun

Cikin sauri Baffa yace wa Fadil, “su yi maza su wuce gida”.

Da sauri suka shige motan ya figa suka yi gida, suna isa suka tarar da Abbu ma a haraban gidan yana waya

Saurin katse wayan yayi ya nufe su yana tambayar Baffa “kun ganta? Ina take?”

Nan Baffa ya sanar masa da komi

Ai nan Abbu shima ya ruɗe yana faɗin, “innalillahi wa’inna ilaihi raji’un.. me ke faruwa ne?”

Su Big Dady da suka fito za su tafi masjid, suka tambayi ba’asi, da jin abinda ke faruwa su ma hankalin su ya tashi ainun, Abba dake da Numban wani abokin sa ɗan sanda, tuni ya kira shi ya sanar mishi abinda ke faruwa.

 

Kan kace me kowa yaji labarin rashin dawowar Ɗahira, nan da nan Hankula suka sake tashi, ba kamar Kaka duk ya gama ruɗe wa, basu so ma faɗa mishi ba, amma kuma ganin har ƙarfe goma tayi babu labarin ta duk inda aka je, dole suka faɗa mishi. Gida dai ya rikice ana neman Ɗahira babu ita babu labarin ta, duk an kira dangi “ko sun ganta?” amma babu wanda yace, “ta zo”, hanya an bi ya kai sau goma amma babu ita, ƴan sanda kurɗa-kurɗa an baza su amma ba’a dace ba

Sai da wajen sha daya tayi kafin Hajiya ta lura shima Usman be dawo ba, dayake mutanen gidan har yanzu basu ji labarin dawowar sa ba, Big Dady be sanar musu ba, sai nan itama Hajiya ta ruɗe ta soma kiran layin sa, amma shiru shima a kashe, ta kira Big Dady ta sanar mishi

Shima tun yana ɗaukan abun da wasa, domin ko kallon inda take be yi ba sanda ta sanar masa, sai kuma abun ya soma damun sa ganin lokaci na ja, a nan ne yake sanar ma su Abba “ai shima Usman be dawo ba”.

Duk sun yi mamakin maganar nasa, basu kai ga magana ba Hajiya ta ƙariso wajen tana kuka tana sanar wa Big Dady “har yanzu ta kasa samun layin Usman, kuma ta je gidan shi babu motan shi babu shi a ciki”.

Abba yace, “dama ya dawo ne ashe?”

Sai a nan Big Dady ya tuna basu sani ba su, shi ne yake sanar musu da dawowar sa ɗazu.

 

Abu kamar almara an nemi su Usman ba’a samu ba, a wannan daren babu wanda ya runtsa a gidan nan sabida tashin hankali, kowa tunanin yanda mutane biyu aka rasa su a lokaci ɗaya, sai kuma duk tunanin su Big Dady suka koma kan “ko dai Usman ne ya ɗauke ta suka koma can Turkay ɗin?” Wannan tunanin yasa Big Dady safiyar Allah na yi yace, “zai je domin yaci uban sa a can, wlh idan har da gaske ne tunanin nan nasu Usman ya kaɗe a wurin shi,” sosai ransa ya ɓaci sai faɗa yake yi

Ganin haka yasa Kaka yace, “kar yaje, Baffa yaje shi ya gano musu”.

Wannan dalilin ne yasa Baffa ya shirya aka nema masa jirgi na ƙarfe 10:00am a ranan ya wuce TURKEY.

 

 

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

Duk yanda ya so ya buɗe ƙofan motan ya fice ya kasa, har sai da motan ta gama nitsewa zuwa ƙasa, kokuwa yayi ta yi amma ya gaza, ba don Allah yasa ya iya ruwa ba da tuni babu numfashin sa, amma duk da haka yanayin awannin da suka ɗauka a haka cikin motan babu jan numfashi bare iska sai duk ya galabaita, ya rasa ya zai yi har numfashin sa ɗauke wa yake yi kamar zai shiɗe

daƙyar da siɗin goshi ya samu ya buɗe ƙofan motan, har zai fice ya tuna da ita, nan ya dawo ya janyo ta suka fito daga cikin motan, sai dai yanda ake tsula ruwa ya kasa yanda zai yi ma yayi iyo, take a Nan ruwan yayi gaba dasu saboda yanda ruwan yake gudu sosai, ta cikin gadan wajen yabi dasu yay gaba dasu, dayake wajen makwararan ruwa ne na sassa-sassa dake tafiya ya isa babban kogin dake can wani yankin jeji dake cikin Kadunan.

Tun Usman na sanin halin da yake ciki, har shima numfashin sa ya ɗauke gaba ɗaya

Ita kuwa Ɗahira har yanzu bata farka ba ma bare tasan inda take.

A haka har garin Allah ya waye, inda wajen hantsi wani Tsohon Mutum yazo gaɓar ruwa zai ɗiba ruwan a tulu, a nan ya tsince su tamkar matattu ruwa ya fito da su bakin gaɓar ruwan, sosai hankalin tsohon nan ya tashi, nan ya nufe su cike da mamakin ganin su, sai da ya gama taɓa su ya tabbatar da tabbas suna da rai, sannan ne ya koma cikin ɗan ƙaramin ƙauyen nasu, ya kira wasu samari suka zo suka taimaka masa ya kai su gidan shi, aka zube su cikin ɗaya daga cikin bukkan gidan

Duk mutanen ƙauyen sun fito sun nufi gidan Tsohon nan me Suna Baba Jaure suna ganin ikon Allah wajen su Usman, sun zame musu kamar t.v, duk da ba wai bambanci ne dasu ba, sai dai su sun kasance ƙauyawa ne futuk makiyaya, kuma garin ɗan ƙarami ne a tsakiyar ruwa take, sannan kuma da jeji a kewaye dasu, Baba Jaure shi ne babba a cikin ƙauyen, kuma shi ne me faɗa aji, tsoho ne sosai kuma be da iyali.

Sai da Baba Jaure ya kore su saboda sun cika mishi gida sun hana shi ya duba su, sannan ne suka fita suka bar shi, shi kuma nan ya soma bincika su dayake shi masanin magunguna ne, duk sai da ya gama duba su ya gano raunukan da suka ji, kuma da alamu sun sha ruwa sosai domin daƙyar ma ake iya gane suna numfashi

Ita Ɗahira ta sami karaya a duka ƙafafuwan ta, tare da rauni a ƙafan ta na dama

Shi kuma Usman ciwuka kawai yaji, da alama shi be sha wahala kamar ta ba, sai dai tafin hannun sa na dama ta kwaye kamar dai cizon wani dabba haka, tunda har rami tayi, sai kuma a goshin sa nan ma yaji rauni.

 

Sai da ya gama duba su kafin ya shiga rumbin ajiye magungunan sa, ya haɗo wanda zai yi musu amfani da shi, nan ya jiƙa na jiƙa wa wasu kuma ya niƙa su da turmi, sannan ya saka musu a ciwon, yayi wa Ɗahira ɗaurin karayan ta, shi kansa sai da ya tausaya mata, domin ba ƙaramin karaya bane taji, da ace idanun ta biyu azaban da zata sha Allah kaɗai zai sani, sai dai har ya gama ko alamun motsi bata yi ba, hakan ya ƙara tabbatar mishi tana cikin wani yanayi wanda farfaɗoWar ta sai Allah ya yi, domin ita ko numfashin ma ba ta yi sai da ya taɓa hannun ta yake ganin jijiya na harba wa.

 

 

 

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

Baffa ya je can Turkay ya dawo musu da labari mara daɗi a kan basu je can ba, wannan labarin ya sake ɗaga musu hankali matuƙa, bare da suka ga kwanaki nata tafiya babu labarin su, yau ga shi kusan kwana shida babu su babu wani bayani daga bakin ƴan sanda

Tuni Aunty Amarya da Kaka sun kasa jure wa sun zube an kai su asibiti, yanzu haka an kasa samun kansu, domin tunda suka sume basu farfaɗo ba, duk wani taimako an basu amma an kasa shawo kansu

Ita kuma Hajiya na gida sai faman kuka take yi, ko abinci ta dena ci saboda halin da take ciki

Bazan iya misalta muku halin da waɗannan bayin Allan suke ciki ba, haƙiƙa sun ga iftila’i a cikin ƙanƙanin lokaci, ɓacewar mutane biyu, ga kuma halin da su Kaka suke ciki, domin shi Kaka ma numfashi ba ya yi a halin yanzu sai da oxygen

Tuni ƴan uwa dangi na nesa dana kusa labari ya kai musu duk sun zo, har Fadila da take cikin halin lalura sai da aka zo da ita, duk da cikin ta yanzu har ya soma girma amma kullum ciwo kamar yanzu ta samu cikin, duk ta rame abun tausayi, yanzu tana lafiya, anjima sai aga jikin nata ya rikiɗe an tafi da ita asibiti, an rasa dai me ke damun ta, likitoci sun ce ita nata cikin haka yake, zuwan nasu ma sai da aka yi mata ƙarin ruwa saboda rigigim ta kwanta ciwo, duk da rashin ganin su Ɗahira ne ya yi matuƙar ɗaga mata hankali, sai kuka take yi, daga nan kuma sai jikin ya rikice.

Halin da ahalin nan suka shiga sai innalillahi wa’inna ilaihi raji’un, abin tausayi idan ka gansu.

Ƴan sanda sun je har asibiti sun yi bincike, dayake akwai ccTV Camera a asibitin, sun duba kuma sun ga tabbas a ranan Ɗahira ta bar asibitin a cikin motan ta, Dr. Said ne mutum na ƙarshe da ta zanta dashi a haraban Hospital ɗin, daga nan ta hau motan ta ta fice

A lokacin shi kuma murmushi yayi yana bin motan nata da kallo har ta fice, kana ya zaro waya yayi waya, duk da ba sa jin abinda yake cewa amma duk rashin gaskiya ya nuna a tare da shi, sai kuma suka ga ya shiga tashi motan ya fice.

Wannan dalilin ne yasa aka je neman Dr. Said amma ba’a ganshi ba, domin tun ranan da abin ya faru be sake zuwa asibitin ba, hakan ya ƙara ɗarsa zargi daga zukatan ƴan sandan. Sai suka je har Zaria suka cafke shege, da yasha matsa sai ga shi ya faɗi gaskiya

An sha wahala kafin aka kamo sauran mutanen da suka yi aikin tare da taimakon Dr. Sabo tunda shi ne ya sanar musu inda suke, sun yi bayanin komi da ya faru a ranan da suka ɗauki Ɗahira, har wanda ya zo ya taimake ta da kuma faɗa wa ruwa da suka yi

A nan ne aka gane Usman ne tunda sun yi bayanin motan nashi, kuma zahiri shi ne.

Koda aka je wajen an yi duk wani bincike tsawon kwana da kwanaki, amma motan su kawai aka gani a cikin ruwan, inda suka tabbatar dole su Usman sun rigada sun mutu a ruwan, tunda babban makwararan ruwa ne dake tafiya wani ƙaton tafkin kogi, daga can ma akwai yanki-yankin ruwa dake da alaƙa da wajen, takamaime dai baza a gane inda suke ba a cikin ruwan nan, duk wanda ya faɗa kuwa sai dai mutuwa ne bazai iya fitowa ba

Wannan bayanin da ƴan sanda suka yiwa su Big Dady sun sake ɗaga musu hankali, domin har kuka sai da suka yi sosai a wannan gaɓar, shikenan an rasa su sun mutu. Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un! Mutuwar da ya girgiza ahalin gaba ɗaya, wanda sanadin haka ne Fadila tayi ɓarin cikin ta lokaci ɗaya, shi kuwa Baffa ranga-ranga aka wuce dashi asibiti yana aman jini, ga su Kaka su ma dake asibitin har yanzu ba’a sallame su ba, ita dai Aunty Amarya ta farka, amma da jin wannan bayanin sai ta sake zube wa a sume, dole aka koma basu taimakon gaggawa, su kansu su Abba sun kasa taɓuka musu komi, su ma suna ji da kansu.

Su Dr. Said kuwa suna hannu za su girbi abinda suka aikata, domin har an miƙa su kotu babu ɓata lokaci.
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR’S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER’S ASSO*📖
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA’S FAMILY*_

 

*EPISODE Fifty Four*

A Waɗannan kwanakin da su Usman suka yi a wannan ƙauyen, har yanzu suna a yanda suke basu farfaɗo ba, Baba Jaure na ci gaba da kula dasu sosai yana musu magani, inda tuni ya gano suna tare da sihiri gaba ɗayan su biyun, tunda shi mutum ne me saurin gane sihiri, kasancewar sa wanda yayi gwagwarmaya da aljanu, tun farko su suka buɗe mishi idanu har yake bayar da magunguna, sai ya tafi jeji yayi kwana da kwanaki yana haɗo magunguna, shiyasa duk ƙauyen nasu shi ke basu magani, tamkar shi ne likitan su, kuma shi ne kariyan su har suka kasance a cikin ta har yanzu

Wannan dalilin ne yasa yake haɗa musu wasu maganin na karya sihiri yana shafa musu a jiki, dayake akwai nasha sai ya riƙa zuba musu a baki, duk da yana zube wa amma ya san wasu suna shiga cikin nasu.

Ana haka Usman ya farfaɗo ya tsinci kansa a wannan yanayin da ya kasa banbance a cikin duniya yake ko a maƙabarta? Wurwurga ido kawai yake yi yana zare su a cikin ɗan ƙaramin bukkan da suke kwance, nan idanun sa suka faɗa kan Ɗahira dake kwance tamkar matacciya, da kallo ya bi ta da shi ko ƙyafta wa ba ya yi, yana son tuna me ya faru har yake kwance a nan kusa da ita, be gama dawowa tunanin shi ba yaji motsi a waje, ƙofan yabi da kallo

A lokacin ne Baba Jaure ya shigo da wani kwanon sha a hannun shi, shima ganin Usman zaune sai hakan ya saka shi farin ciki, nan da nan ya yalwata fuskar shi da murmushi yana me ƙarisowa kusa dashi tare da mishi sannu

Amma yanda ka san gunki haka Usman yake bin shi da ido, ko motsi ya gaza yi illa idanun sa da suke juya wa

“Yaro ka kwantar da hankalin ka kaji? Ba cutar da kai zan yi ba, alhmadulillah tunda ka tashi. amshi wannan ka sha”. Ya miƙo masa kwanon shan hannun sa

Usman be motsa ba bare ya amsa, a lokacin tunanin sa ya dawo duk ya tuna abinda ya faru, sai kawai yayi saurin saka hannun sa a kanshi yana shafa wa, sai da ya taɓa ɗin yaji zafi ya ratsa shi, yayi saurin janye wa yana bin hannun shi da kallo, lokaci ɗaya ya ruɗe cikin tashin hankali ya kalli Baba Jaure yace, “ina ne nan don Allah? Me ya faru damu ne?”

Baba Jaure be ce komi ba sai da ya zauna yace, “kayi haƙuri ka kwantar da hankalin ka sai in Yi maka bayani”.

Shiru Usman yayi yana bin hannun sa da kallo, yanda duk aka barbaɗa mishi wani baƙin abu da babu kyan gani, dashi aka cike ramin da hannun sa yayi, sosai yake jin azaba na ratsa shi har ruwan hawaye ne ke cika mishi idanu, sai dai kuma dauriya irin nashi bazai iya kuka ba, amma sosai yake jin azaba. Da kallo kawai yabi Ɗahira dashi yana kallon ƙafafuwan ta da suke a ɗaure alamun sun karye, shiru kawai yayi ya gaza ɗauke idanunsa a kanta, lokaci ɗaya yaji hawayen dake idanun sa sun zubo, sai yayi saurin kawar da kansa yana saka ɗaya hannun sa ya share

Baba Jaure dai duk yana kallon sa be sake ce mishi komi ba, amma tausayin sa ne sosai a ransa, a lokacin sai yace, “yau kwanan ku goma a waje na sai yanzu da ka samu kai ka farfaɗo, na tsince ku a gefen kogi ne cikin mawuyacin hali, wanda ita ƴar uwan taka ta samu karaya a duka ƙafafuwan ta sai raunuka. kai kuma ka samu ciwo a kanka da hannun ka”. Shiru yayi

Usman dake bin shi da kallo tun soma maganar nasa yace, “amma ina ne nan don Allah?”.

Murmushi Baba Jaure yayi yace, “kar ka damu zaka sani, nan wani yanki ne dake cikin jeji, kuma zagaye muke a ruwa”.

Duk da Usman yana son sake mishi magana amma ya kasa buɗe baki yayi, illa hannun sa da yake tabi da kallo yana cike da raɗaɗin azaba

Ganin yayi shiru be ce komi ba sai yace, “ga magani ka sha”.

Still shiru Usman yayi kuma be ɗago ya kalle sa ba

Sai shima be sake cewa komi ba illa tashi da yayi ya koma gefen Ɗahira, a nan ya ɗibi maganin a cikin tafin hannun sa yana zuba mata a baki

Da kallo kawai Usman yake bin shi dashi yana yamutsa fuska, har ya gama yaga ya soma shafa mata magani a raunukan ta

Sai da ya gama yace mishi, “ka sha maganin nan, shi zai taimaka maka wajen rage raɗaɗin da kake ji, kaji ko?”

Gyaɗa kansa Usman yayi, ya amshi maganin ya kafa kai ya sha

Baba Jaure fita yayi, sai ga shi ya sake dawowa da wani kwanon, ya miƙa mishi ya sake ba shi umarnin yasha

Hakan kuwa yayi ya amsa yasha, wannan duk ɗaci amma be ce komi ba har ya gama sha

Sai ya sake fita, zuwa can ya dawo mishi da fura ya bashi

Usman amsa yayi ya kafa kai ya shanye domin yana buƙata

Sai da ya gama Baba Jaure yace mishi “zai fita zuwa jeji, bazai daɗe ba zai dawo”.

Shi dai Usman be ce mishi komi ba har ya fice, kana ya mayar da idanun sa kan Ɗahira, kallon ta kawai yake yi kamar ya sami t.v, abinda tunda yake be taɓa mata ko kallon second uku bane, a ƙasan zuciyar shi yana jin wani abu na taso mishi me kama da tausayi, ita yake tausayi ko kuma kanshi yake tausayi ya kasa sani, sai ya ɗauke kai kawai yana mayarwa kan hannun shi, duk idan ya kalli yanda hannun nasa yayi rami sai kawai yaji hawaye suna son cika mishi idanu, “kenan nashi azaban nafila ne a kan yanda ita take ji? Ko ya ya take ji?” Ya yiwa kansa tambayar yana me sake mayar da idanun sa kanta

Kamar zata yi magana haka fuskar ta tayi, sai dai kuma babu inda nata yake motsi, har ta numfashin ma ba ya ganin tana yi

Sai yayi saurin kai hannun sa mara ciwon ya tsinci kansa da aza shi saman ƙirjin ta, memakon yaji bugun zuciyar ta, sai nashi ne tayi wani irin buga wa sabida saukar hannun sa a saman ƙirjin ta. Saurin janye hannun nasa yayi yana ɗaura wa a kan nasa ƙirjin, lokaci ɗaya ya lumshe idanun sa yana me ci je leɓen ƙasan bakin sa, sosai yake jin bugun zuciya wanda yaja tsawon lokaci a haka ya kasa taɓuka komi, so yake yi ya sake ɗaura hannun sa don yaji bugun numfashin ta, domin be ji komi ba sanda ya saka, amma kuma tsoro ya hana shi mayar wa, haka kawai yanayin da yake ji a jikin sa yasa ya kasa buɗe ido bare ya mayar da hannun sa a ƙirjin ta

Tsawon mintuna biyar kafin ya buɗe ido yana bin ta da kallo, shiru kawai yayi shi be dena kallon ta ba; shi kuma be yi abinda yake ninyan yi ba. A haka har Baba Jaure ya dawo ɗakin, a nan ne ya samu kanshi da tambayar Baba Jaure, “ita yaushe zata tashi?”

Baba Jaure da ya sami wuri ya zauna yace, “gaskiya tana cikin wani hali sosai, ta fi ka shan wahala shiyasa zai yi wuya ta farfaɗo yanzu, sabida tasha ruwa da yawa, amma idan an dace tunda ina bata maganin da ya kamata tasha, insha Allahu zata tashi ba da jima wa ba, sai dai mun yi haƙuri”.

Usman kallon sa yayi yace, “ina son mu koma gida saboda a bata taimakon gaggawa”.

Baba Jaure yace, “yaro ba na tunanin za ku samu barin nan wajen a nan kusa”.

“Meyasa?” Yayi masa tambayar har yanzu yana bin sa da kallo

Gyara zama sosai Baba Jaure yayi kana yace, “kamar yanda nace maka ne nan wani yanki ne dake cikin jeji, muna cikin tsakiyar ruwa ne gaba ɗaya ƙauyen namu, kuma gaskiya mutanen cikin ta ba sa fita idan har wannan lokacin ya yi, ma’ana lokacin damina ba ma iya fita zuwa cikin gari, sakamakon yanda ruwa ya tabaibaye mu, sai idan damina ya wuce shi ne hanya zata kafe har mu sami hanyar wuce wa, amma idan muka sake muka bi ta cikin ruwan a cikin kwale-kwale, to, mutuwa ake yi, Ni kaina nasha mamakin ganin ku kun fito daga cikin ruwan ba tare da kun rasa ranku ba, saboda gaskiya ruwan nan duk wanda ya faɗa ko ya sake ya shiga ciki, yana ji yana gani za’a janye shi a nemi gawan sa a rasa, wanda na tabbatar da cewa mutanen ruwa ne suke hana mu fita duk sanda aka ce damina yayi, dole duk wani zirga-zirga muna yin ta ne ba lokacin damina ba, zamu shiga cikin gari mu nemi duk abinda zamu iya buƙata, sabida ana fara ruwa mu da fita har sai damina ta ƙare, to ka ga kuwa fitan ku cikin garin nan sai bayan damina idan muna da rai Zaku yi ta zama har lokaci yayi”.

Usman kasa ce mishi komi yayi sabida tashin hankalin dake tattare dashi

Baba Jaure yace, “amma ina son ka faɗa min abinda ya faru da ku har kuka tsinci kanku cikin wannan ruwan? Da kuma alaƙar dake tsakanin ku”.

Usman samun kansa yayi da faɗa mishi gaskiya, ma’ana “ita matar shi ce wasu suka sace ta, shi ne ya biyo bayan su wannan tsautsayin ya faɗa musu,” duk abinda ya faru dai sai da ya faɗa mishi

Jinjina kansa Baba Jaure yayi cike da zallan tausayin su yace, “haƙiƙa na tausaya muku, kuma Allah yasa da rabon zaku sake tsawon rai a gaba shiyasa har kuka samu kuɓuta. Allah ya kyauta gaba, sai kayi ta addu’a har sanda matar taka zata farka, amma mene ne sunan ka?”

“Usman”. Ya sanar mishi a taƙaice

“Ita kuma fa?”

Sai da Usman ya ɗago kai ya kalle shi kafin tunanin shi ya kai ga Ɗahira, a hankali ya buɗe bakin shi yace, “NAFEESA”. Sai ya samu kanshi kuma da maimaita sunan a ranshi

Baba Jaure dai fita yayi ya barshi a ɗakin

While shi kuma ya haɗa kanshi da ƙafafuwan shi sai ya hau faman tunani, tunanin kawai yanda zai iya rayuwa a nan yake yi, sai tunanin dangin shi suka faɗo mishi, lumshe idanun sa kawai yayi yana ta tunani cikin ranshi.

 

 

Tun ranan da ya farka ko ƙofar ɗaki ya ƙi fita bare ya ga yanayin garin, kullum be da aikin yi sai tunani da kallon Ɗahira, a kullum gani yake yi kamar zata yi magana ko kuma motsi, amma dai yanda take har yanzu haka take

Baba Jaure shi ke zuwa ya shafa musu magani, idan yazo yana jan Usman da hira amma shi komi ba ya iya ce mishi, sai dai ya riƙa sauraren shi

Yau ga shi kimanin kwana biyar kenan da farfaɗowar shi, ganin har yanzu Baba Jaure be ce mishi idan zai yi wanka ya fito ba, sai shi yayi masa maganar “yana son yayi wanka”.

Baba Jaure yace masa, “idan zai iya to bari ya ɗumama mishi ruwan, dama yana jiye mishi ciwukan shi ne kar ya taɓa ruwa”.

Bayan ya ɗumama mishi ruwan ya sanar mishi

Sai Usman ya tashi ya fito, da kallo kawai yake bin gidan, fili ne fetete da aka zagaye shi da kara, sai bukkoki kusan guda shida a jere har wanda suke ciki, sai kuma ɗaya dake can gefe ƙato, da alamu shi ne ban-ɗaki

Baba Jaure ya Yi masa nuni da wajen

Sai ya taka ya wuce ya shiga, tsaban ƙyamƙyami irin na Usman ya kasa yin wankan, duk da babu komi a bayin domin a tsaftace yake. Haka ya wanke fuskar shi da bakin shi, sai kuma ƙafafuwan shi ya watsar da ruwan ya fito, fuskar shi duk babu alamar fara’a, yana jin taya ya ma zai iya rayuwa a nan babu kulawa babu wanka

Baba Jaure da kallo ya bi shi dashi har ya shige bukkar, sai ya saki murmushi kawai yaci gaba da rubutun shi cikin allo, sosai ya gama kula da halin Usman, shiyasa be damu da wannan ɗaurewar fuskar nashi ba, domin tunda ya tashi be taɓa ganin haƙoran shi a waje ba, ko da kuwa magana zai yi ba ya buɗe baki sosai a ciki-ciki yake yi.

 

Usman kuwa yana shiga mayar da kayan sa yayi zuciyar sa duk babu daɗi, sai yayi kwanciyan sa a gefen Ɗahira, yayi rigingine yana bin ta da kallo, yanda yake jin zuciyar sa da ya kalle ta sai ya ɗan samu sauƙi, sai kuma tunanin ta suka fara mishi yawo a zuciya, babu abinda yake tuna wa sai rayuwan da suka yi a can Turkay, da kuma abubuwan da yayi mata, sai kawai ya tsinci kansa da tambayar kansa “shin meyasa yayi mata wannan muguwar tsanar da har ya saka shi ya ƙuntata mata da yawa har haka? Anya shi ne kuwa?” Sai kuma wata zuciyar nasa tace, “to wa kake tunanin zai yi mata bayan kai? Ko ka manta tun sanda aka haife ta ka ɗaura mata karan tsana har zuwa kuwa wannan lokacin?” Sai ya lumshe idanun sa yana sake buɗe wa a kanta, a ransa ya furta “amma meyasa yanzu ba na jin tsanar nata sosai kamar yanda nake ji a zaman da muka yi a turkey?” Hasali ma yana jin wani irin tausayin ta ne a ƙasan ransa tare da nadamar abinda yayi mata

Saurin tashi yayi yana tankwashe ƙafafuwan sa, sai ya buga tagumi idanun sa a kanta, the more Yana tuna abubuwan da yayi mata the more Yana jin zuciyar sa na zafi, meyasa ya zama mugu mara tunani a wajen ta? Shi ya ma kasa tuna wani abu ne mummuna da tayi masa da har yayi mata mugun tsanar nan? Ya san dai tun sanda aka haife ta ya kalli cikin idanun ta, faɗuwar gaban da ya same shi tare da wani irin tsoro duk shi ne ya haddasa mishi tsanar ta, ko kaɗan ba ya ƙaunar ya ganta kusa dashi wannan dalilin ne yasa yake muzguna mata ko don ya rage haushin ta a zuciya, sosai ta hana ma rayuwar sa sukuni tun soma girman ta, shiyasa a lokacin da ya gama karatun shi na secondary School shi ya matsa wa Kaka dole ya tura su Turkay karatu shi da Baffa, ba don komi ba sai don nesanta kanshi da ita, sabida har a mafarkin sa zuwan mishi take yi, ba ta da aiki sai tsorata shi da waɗannan idanuwan nata, wanda yake ganin kamar da gayya take yi tunda ta san be son Kallon ta, shi har ya fara mata kallon aljana, sai dai kasancewar shi shima mugu ne shiyasa duk sanda ya same ta yake kiman ta, a cewar sa “ai ko ita aljana ce wlh sai ya rama abun da take mishi a mafarki,” duk inda ya same ta duka ke haɗa su, har ya zamo idan ta ganshi ba ta iya zuwa wajen sai idan babu shi, idan kuma suka haɗu a hanya gudu take yi, sabida muddin ya kama ta dukan mutuwa yake mata. Iyayen su tun ba sa damuwa har dai kowa ya gane tsana ce kawai Usman yake mata, sun yi faɗan sun yi faɗan don ya dena dukan ta amma ya ƙi, shiyasa a lokacin da suka gama karatun su suka dawo, sai Usman ya nemi “a barshi ya koma can yayi aikin sa tunda an yi masa tayi”.

 

To shi kuma Kaka be ja da zancen ba ya bar shi, ba don komi ba sai don ba ya son ya takura wa Ɗahira, saboda a lokacin har ya soma kiman ta duk da da girman ta a time ɗin, su ma sun dawo hutu daga Zaria  lokacin suna karatu a ABU, daga sun haɗa ido da ita a ganin shi na farko da yayi mata, ita kuma tuni ta tsere sabida ganin sa don bata yi tunanin yana ɗakin Kaka ba, shi ne fa ya tashi a lokacin tsam yabi bayan ta, su Kaka duk basu san me ya tayar dashi ba, tunda a ganin su ta girma ta wuce duka a wurin sa

Ashe shi Usman har Part ɗin su ya bi ta ya zaƙulo ta a ɗakin su yayi mata shegen duka, ba komai ya saka shi haka ba sai yanda ta faɗar masa da gaba har yana datse haƙora, ga kuma mugun tsoron da ya riske shi a lokacin, don a time ɗin ta zama ƴan mata idanun nan sun ƙara girma da kyawu

Aunty Amarya ita tazo ta ce ce ta tana tambayar sa abinda tayi masa, kasancewar ta ba me son faɗa da hayaniya ba shiyasa bata nuna ɓacin ranta a kan abinda yayi wa Ɗahira ba

Shi kuwa be ce komi ba ya juya ya fice a zuciye

Fadil ya shafa da gudu ya sanar wa su Kaka. Mafarin kenan Kaka ya amince da komawar sa can Turkay yayi aikin sa, duk da suna da buƙatar sa a nan sabida suna da asibitin su, amma kuma hakan shi ne zai kawo sauƙi wajen Ɗahira, su baza su iya hana Usman ba tunda duk faɗan da zaka yi masa wlh bazai dena ba, abinda yayi ninya kawai shi yake aikata wa, da ace faɗa zai saka Usman ya dena dukan Ɗahira da tuni ya dena, amma ga shi ashe abun gaba yayi ba baya ba.

Tunda ya tafi kuma sai Ɗahira bata sake saka shi a idon ta ba, a lokacin sosai ya koya mata tsanar shi, bata da maƙiyi a duniya sama dashi, ko da ya dawo hutu to zata bar gidan Idan har lokacin su ma suna gida, ko ta tafi gidan ƙanwar Kaka Hajiya Hannatu (Ihsan) ko kuma ta koma Zaria can Soba dangin Maman ta tayi zaman ta har sai sun koma school, ita da ta dawo gidan sai kuma wani hutun idan Usman ba ya gida, bata ƙara yarda sun sake haɗuwa ba sai dawowar sa gaba ɗaya da yayi wanda kuma sun gama school, lokacin tana ganin baza ta iya juran waɗannan abubuwan da yake mata ba…

 

 

Numfashi Usman yaja sanda yaji muryan Baba Jaure Yana mishi Magana.
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR’S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER’S ASSO*📖
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA’S FAMILY*_

.

*EPISODE Fifty Five*

Bayanin Farko da aka sanar musu a kan Baffa ya yi matuƙar ɗaga musu hankali, ya kamu da ciwon zuciya, ga kuma shaye-shayen da yake yi wanda yayi mishi illa sakamakon ya sha wanda ya fi ƙarfin shi

Ai hauka ne kawai Hajja Fatu bata yi ba jin wannan bayanin

Su kuwa su Abba basu yarda da result ɗin ba daga farko, domin a cewar su “ɗan su ba ya shan giya, sannan babu abinda ke damun sa da har ciwon zuciya zai kama shi,” duk da sun san cewa shi ciwon zuciyan Allah na saka maka haka kawai, jarirai ma da ake haifa suna iya kamuwa da ciwon zuciya, amma da suka yi gwajin da kansu sai suka fi yarda tunda ga result zahiri, ga shi kuma ciwon yayi masa mummunan kamun da ya shiga coma lokaci ɗaya, innalillahi wa’inna ilaihi raji’un, tashin hankali ba’a saka mishi rana, ban san ya zan kwatanta muku halin da suka shiga ciki ba, sai dai kamar yanda suka yarda da Allah sun kuma yarda da ƙaddara, shi ne yasa komi yazo musu da sauki. A yanzu dai Aunty Amarya ita jikin nata da sauki duk da ba dena kuka tayi ba, sai dai tana kukan zuci wanda ba ta jin nan kusa zata dena, ɗiyar ta ɗaya tilo Allah ya amshi abin sa

Kaka kuwa da Baffa ba’a magana a kan jikin su, gwara-gwara Kaka yana iya farka wa amma dai da oxygen yake numfashi.

Jikin Fadila da sauki shiyasa ana sallaman ta Big Dady yace “su koma da ita gida”.

K.B ya wuce da ita, duk da tana ta kuka a kan “baza ta je ba”.

An yi zaman makoki duk da babu gawan su, an yi musu zaman makoki har kwana bakwai aka yi addu’a, sannan kowa ya watse, su kuma su Kaka suna asibiti ana ci gaba da kula da su.

Alhmadulillah ana samun sauƙi daga Kaka, tunda yanzu har yana iya magana, jikin sa da sauki sosai, sai dai Baffa ne jiya iyau, har yanzu tunda aka kai shi be farfaɗo ba.

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

Da sannu da sannu Usman ya saba da rayuwar ƙauyen nan da ya tsinci kansa a ciki, tun ba ya sakin jiki da Baba Jaure har dai yanzu sun saba sosai, ya kan gaji da zama a cikin ɗaki har ya fita wajen gidan ya sha iska, ya riƙa kallon mutanen garin da zirga-zirgan su, duk da ya ƙi sakin jiki sosai da su illa Baba Jaure, don wani lokacin har jeji yana raka shi, amma be cika zuwa sosai ba, babu abinda ke faɗo masa a rai illa Ɗahira, ya kan ji hankalin sa be kwanta ba duk idan zai yi nesa da gidan, sai yaji kamar wani abun zai same ta, shiyasa sai idan ya gaji sosai ne yake iya bin Baba Jaure cikin jejin

Ya zama abun kallo ga mutanen ƙauyen, duk da ba wasu mutane ne da yawa ba, ba samarin ba ba ƴan matan ba kowa so yake yi ace ga shi yana mu’amala da Usman, sai dai ya ƙi sakin musu fuska, wasu samarin idan har suka ganshi a waje har zuwa suke yi su zauna wai “sun zo taya shi hira,” ga su da shegen surutu dole sai sun yi mu’amala dashi kamar wasu mayu, duk da wulaƙanta su da yake yi, don idan suka soma mishi zuba ko ci kansu ba ya ce musu, ko abin dariya suka yi sai dai ya kawar da kansa idan yana jin dariyan, daƙyar yake iya murmushi wanda basu san ma yana yi ba, iya kanshi dasu gaisuwa da amsa sallama, su da farko ma abin mamaki yake ba su, ayi mutum ba ya magana ba ya dariya, amma kuma dayake iyayen naci ne dasu sun ga ɗan birni zubin ƙetare, su hakan ma daɗi yake musu tunda sun zauna dashi

Su kuwa ƴan matan ma ko kallo basu ishe shi ba, idan za su wuce sau dubu su gaishe shi ba ya kallon inda suke, amma gobe idan sun ganshi a wurin baza su fasa gaishe shi ba, shiyasa yanzu ma ya rage fita, sai dai yayi zaman shi a cikin gidan wajen Baba Jaure yana kafa mishi idanu yana aiki.

Abin mamaki tunda Baba Jaure yace mishi ya riƙa shafa wa Ɗahira magani yana bata na shan, be yi masa musu ba, shi yake bata kullum yana kula da ita, wani lokacin ma har yana ɗan wanke mata jiki da tsumma, shi kansa abinda yake yi wlh mamaki yake ba shi tsantsa, be san meyasa ba yanzu kwata-kwata ba ya jin tsanar ta kamar da, hasali ma zallan tausayin ta yake ji

Be san cewa tuni asirin dake tasiri a jikin su an karya musu ba, tsanar da aka saka mishi na Ɗahira tuni Baba Jaure ya karya sihirin, kuma har yanzu be fasa basu na tsari ba, sai dai shi Usman ɗin duk a tunanin shi magungunan raunukan da suka ji ne.

 

***** ****** *******

Yau ma kamar kullum shi da kanshi yaje ya ɗauko maganin ya soma shafa mata, dayake Baba Jaure ya fice zuwa jeji tun ɗazu, yana yi yana kallon fuskar ta da be gajiya da kallo, har ya rame fuskar nata sosai ko da gani ka san tayi jinya

Motsi yaga kamar tana yi sai ya tsaya yana bin ta da kallo, sai kuma cikin sauri ya soma kiran sunan  ta a hankali yana faɗin, “Nafeesa.. Nafeesa”.

Kamar daga sama take jin muryan, wanda daƙyar ta iya motsa hannayen ta jin ƙafafuwan ta sun riƙe sosai ta gaza motsa su, sai kuma ta soma juya kanta a hankali

Ganin haka yayi saurin saka hannun sa yana riƙe nata, ya ci gaba da kiran sunan ta a zaƙe da son ganin ta buɗe idanu, sosai yaji wani irin farin ciki ya tabaibaye shi dashi kanshi be san na mene ne ba, yau har so yake yi yaga waɗannan idanuwan nata masu ba shi tsoro da fargaba, sunan ta ya sake kira yana matsa mata hannun ta da ya riƙe gam a cikin nasa

Idanun ta ta soma buɗe wa a hankali tana sake rufe su, a haka har ta ɗan buɗe su kaɗan tana ganin dishi-dishi, tayi kamar mintuna biyu ba ta iya ganin komi, kafin kuma ganin nata ya soma dawowa, ta soma gane abinda ke cikin ɗakin, kana kuma ta sauke idanun ta a kansa, wanda sai da ta sake rufe idanun ko gizau yake mata, kafin kuma ta sake wartsake su a kanshi, kallon kallo kawai suke ma juna yayinda ta tsayar da idanun ta a kanshi ƙyam

Shi kuwa fuskar shi yalwace da murmushin da ya daɗe be yi ba yake kallon ta, don ya ma kasa yin magana

Wani irin zabura tayi lokaci ɗaya tamkar mahaukaciya tana yanka ihu, ihu sosai take yi tuni ta ɗage ƙafafuwan ta tana son tashi da gudu

Hakan da ya gani ne tuni hankalin sa ya tashi, nan ya saka hannu yana riƙe ta yana faɗa mata “ta tsaya”.

Amma ina ihu kawai take yi sosai hawaye tuni sun yi mata caɓe-caɓe saboda azaban da ya ziyarce ta, sai a lokacin ma tabi ƙafafun nata da kallo, ai nan ta sake haukace wa a kuka, ga shi jikin ta babu ƙarfi amma yanda ka san mahaukaciya haka take son fizge jikin ta a jikin sa

Shi duk a tunanin sa haukan ne ya same ta, shiyasa lokaci ɗaya ya ruɗe ya riƙe ta gam yana faman kiran sunan ta da faɗin “ta natsu don Allah”. Shi ba komi yake jin mata ba illa ɗaurin dake ƙafafun ta kar ta goce.

A lokacin ne Baba Jaure ya shigo da saurin sa, domin ihun nata ne ya jiyo tun daga wajen ya taho da saurin, shima ya ruɗe sosai ganin yanda take yi, saurin saka hannu yayi ya riƙe ta yana faɗin, “dakata mana ƴar nan, me kike yi haka? Ki zauna don Allah kin ga akwai karaya a ƙafafuwan ki”.

Amma ina azaba ya hana ta jin kalaman Baba Jaure, duk da ta dena motsi da ƙafafun, amma kukan ta sai ƙaruwa yake yi har da su majinu

Baba Jaure duba ƙafan yayi yaga dole sai an sake sabon ɗauri, cike da tausayin ta yace, “amma me ya faru ne da ta tashi a firgice haka? Ka ga dole sai an sake sabon ɗauri”.

Usman be iya cewa komi ba, shi dai yana riƙe da ita da tayi lagwab kanta a jikin sa sai kuka take yi sosai

“Yanzu je ɗauko min wani magani a ɗaki na yana nan a kwalba ka kawo min”. Baba Jauren yace dashi yana kallon sa

Tashi Usman yayi yana aza kanta a saman shimfiɗan da take kai, yayi saurin fice wa

Shi kuma Baba Jaure sai bata baki yake yi duk da ba ta fahimtar sa, azaba da zugin ciwo ya hana ta saƙat, riƙe mata ƙafafun yayi don kar ta motsa duk da tana son ƙwace wa

Bayan Usman ya dawo da maganin ya miƙa wa Baba Jaure

Shi kuma ya amsa yana taɓa ƙafan ɗaya wanda ya san shi ne ya goce

Sai ta yanka ihu tana janye ƙafan, tana faman girgiza kai da son magana amma ina ta kasa

“Kai Usman sai dai ka riƙe min ita a sake sabon ɗauri, idan ba haka ba ƙafan nata zai yi tsami da yawa”.

Gyaɗa kai Usman yayi kamar ƙadangare, ya duƙa ya riƙo mata hannaye gam ya ɗaura kan ta a jikin sa

Duk yanda taso ta ƙwace amma ina ta kasa, azaban da ya sake ziyartan ta tuni ta buɗe baki tana roƙon Baba Jaure yayi mata rai, kuka sosai take har da majinu yayinda ta koma kiran sunan Usman tana roƙon sa “ya taimake ta”.

Usman har sai da yayi mata ƙwalla tsaban tausayin ta, shi kansa be san ma yayi ba

Shi kuwa Baba Jaure ya ƙufe sai da ya gama gyaran tas kafin ya ƙyale ta, sannan ya kalle ta yace, “sannu baiwar Allah, kiyi haƙuri kinji? Kuma kar ki sake motsa ƙafafuwan nan tunda kin ga wahalan da kika sha, muddin kika sake gotar wa dole a sake sabon ɗauri idan ba so kike yi ki dauwama a karye ba. Allah ya ƙara lafiya kiyi haƙuri”.

 

Ɗahira wanda tasha azaba tayi sharkaf da zufa, inda majinu da hawaye suka yi mata caɓe-caɓe a fuska, fuskar nan tayi jazur kamar tattasai tsaban wahala, yanzun ma gunjin kuka take yi sosai ta lafe kanta a jikin Usman sai faman sakin numfashi take yi

Shi kuwa Usman ƙam ya riƙe ta yana shafa mata kan alamun rarrashi, ya kasa cewa komi illa tsaban tausayin ta dake cin sa a rai, ji yake yi kamar ya mayar da ciwon jikin sa, sosai yake jin tausayin ta na tsarga masa ta ko ina a jikin sa, yana bin jiki da ɓargon sa, wanda har ji yake yi tsigan jikin sa na tashi.

 

Baba Jaure tashi yayi ya fita, sai ga shi ya dawo da fura cikin kwanon sha, ya miƙa wa Usman yace, “ga shi ka bata Idan zata iya sha, ki daure kinji ki sha”.

Amsar kwanon Usman yayi

Baba Jaure ya fice a ɗakin

Shiru yayi yana tunanin yanda zai iya lallaɓa ta tasha maganin, kamar mintuna biyar da fitan Baba Jaure sai ya saka hannu ya mirgino kanta yana kiran sunan ta a hankali kamar wanda ke raɗa

Bata amsa mishi ba domin idanun ta ma a rufe suke ruf, hawaye sai sake tsiyaya suke yi, sai ta mayar da kanta ƙasa ta kwantar tana ci gaba da shashsheƙan kuka

Sake kiran sunan ta yayi yana cewa “ta tashi tasha furan”.

Duk yanda yaso tayi magana ko ta buɗe idanun ta amma ta ƙi

Ko kaɗan ba ta ƙaunar ta sake tozali da fuskar sa, Da ya san abinda take ji a game dashi da be kusanto inda take ba, da ya san yanda muryan sa ke sauka cikin kunnen ta yana sake ƙara mata wutar tsanar sa da haushin sa da be ci gaba da mata magana ba, da ace zata iya yin magana a yanzu ɗin da ta faɗa masa “ta tsane sa fiye da kowa a duniyar nan! ba ta son ganin sa ba ta son taimakon sa, shi be da wani amfani a duniyar ta,” zata faɗa mishi “dashi da dabba a wajen ta ɗaya suke”. Sai dai kuma ina baza ta iya ba, baza ta iya buɗe ido ta kalle sa, duk azaban da take ji kaɗan ne da yanda take ji a zuciyar ta, sosai zuciyar ta take tafarfasa tsaban tsanar da take mishi.

 

Usman tashi yayi ganin taƙi kula shi, sai ya kai ma Baba Jaure yace mishi “taƙi sha”.

Baba Jaure ya dawo ɗakin da furan, sai ya bar Usman a can waje. Zama yayi yana cewa, “ɗiya ta”.

Sai a lokacin Ɗahira ta buɗe idanuwan ta da suka kaɗa suka yi jawur

“Kar ki sake gardama idan na baki abu kinji? Lafiyar ki ake nema miki, idan babu abinci baza ki samu sauƙi ba, yau kimanin wata ɗaya kenan kina a wani hali baki farfaɗo ba sai yanzu, mijin ki ya damu ƙwarai, ki daure ki samu lafiya ko shima hankalin sa zai kwanta, bari in Kira shi ya baki”.

Cikin muryan kuka tace, “a’a don Allah Baba Kar ka kira shi, wlh mutuwa zan yi, ba na ƙaunar taimakon shi idan har shi zai taimake Ni, shi ba miji na bane”. Sai ta fashe da kuka me tsuma rai, da ya san yanda kalman mijin ta ya bugi zuciyar ta; da ko da wasa bazai sake ambata mata ba

Baba Jaure cike da mamaki yace, “ba mijin ki bane? Amma ya ce min shi mijin ki ne?”
💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR’S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER’S ASSO*📖
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA’S FAMILY*_

 

*EPISODE Fifty Six*

 

“Shi ba miji na bane, bani da alaƙa dashi”. Tayi maganar cikin kuka

 

“To ya isa haka, bar kukan kinji kar ki saka wa kanki wani ciwon, bari in taimaka miki ki sha furan”.

 

Gyaɗa masa kai kawai tayi tana faman sauke ajiyan zuciya akai-akai

 

Kallon ta kawai yake yi cike da tausayin ta, sai ya gyara mata kanta ya ɗan ɗago ya saka mata matashi, sai da ya bata ruwa ta kuskure bakin ta kafin ya hau kafa mata furan tana sha

Duk azaban ciwo ya ishe ta shiyasa kaɗan tasha tace masa, “ya ishe ta”.

Dole ya ƙyale ta be matsa mata ba, sannan ya bata wani magani tasha ya mayar da ita ta kwanta sosai, yace mata, “ta kwanta tayi barci ko zata samu hutu”.

Bata ce mishi komi ba har ya fita, sai ta mayar da idanun ta ta rufe har yanzu sai faman ajiyan zuciya take saki, fuskar ta tayi jazur da ita sai hawaye dake kwance sun bushe mata.

 

 

 

**********

Baba Jaure kuma da ya fita a can gefe ya ga Usman ya zauna ya haɗa kai da gwiwa, kallon sa kawai yayi sai ya kawar da kansa, be ce mishi komi ba duk da yana son mishi tambayoyi, amma ya bari zuwa lokacin da Ɗahira zata samu nutsuwa hakan zai fi mishi. Ɗaki ya shige abin shi

 

Shi kuwa Usman be ma san da fitowar sa ba, illa tunani da ya faɗa hankalin sa na ga Ɗahira, zuciyar shi na matsa mishi da tunanin ta amma shi yana son kauce wa, sosai yake ƙaunar taimaka mata saboda tausayin ta da yake yi, ya san ba don ciwon dake jikin ta ba ba ya jin zai ji abinda yake ji a kanta, shiyasa duk wani tunanin da yake nata ya barshi ne a kan TAUSAYI kawai, kuma da zaran komi ya wuce zai dena matsa wa kansa

 

Sai a lokacin ya ɗago kai yana kallon Baba Jaure da ya fito daga ɗakin sa, sai yayi saurin tashi idanun sa a kansa yace, “ta sha furan Baba?”

 

Murmushi yayi masa yace, “eh na bata ta sha, amma yanzu na san ƙila tayi barci”.

 

Yana ganin yanda Usman ɗin ya saki ajiyan zuciya har da lumshe idanu, sai yace mishi, “zai fita yaje ya dawo”.

Har Baba Jaure ya fice be ce mishi komi ba, koma wa yayi ya zauna yana ci gaba da tunanin sa, gaba ɗaya zuciyar sa ta matsa mishi yaje ya duba ta, ko da fuskar ta ne ya kalla but ya daure ya ƙi zuwa. A nan ya zauna har sanda Baba Jaure ya dawo

 

Sai yace mishi, “daga yau zaka fara kwana a wancan bukkan kaji?”

Da kallo ya bi shi be iya ce mishi komi ba, sai dai mamaki da ya cika sa

Shi kuma Baba Jaure ya gane sarai yana son ƙarin bayani, amma ya ƙi sake ce mishi wani abun, idan ba tambayar sa yayi da bakin sa ba shi kuma bazai tanka sa ba, sai ya wuce abin sa ya bar shi.

 

Har aka kira sallan magriba Usman na zaune a wurin be jirga ba, sai daga baya ya tashi ya ɗauki mazubin ruwa yayi alwala ya fita zuwa Masallaci

Baba Jaure tuni shi ya fice ma, tunda dama shi ne liman.

 

 

Bayan an idar da sallah ya koma gida, kai tsaye ɗakin da Ɗahira take ya wuce, da sallama a bakin sa wanda shi kaɗai yaji kayan sa ya shiga ciki

Idanun ta biyu amma suna lumshe, motsin da taji yasa ta buɗe su a kanshi, sai suka shige cikin nasa

Da sauri ya janye nashi idanun saboda yanda yaji gaban sa yayi muguwar faɗi tamkar zai fito waje, har yana runtse idanu

Sai da ta sakar mishi wani banzan kallo da be san ma tana yi ba kafin ta ɗauke nata idanun, ta mayar dasu ta rufe ruf

Dauriya ya aza wa kansa ya sake kallon ta, ganin idanun ta a rufe sai ya taka a hankali ya shiga ciki ya zauna a gefen ta, shiru ne ya biyo bayan zaman nashi be ce uffan ba illa kallon ta da yake faman yi

Har a cikin jikin ta tana jin irin kallon da yake mata, wanda har ta kasa jure wa ta buɗe idanuwan ta a kansa tana mishi wani kallon da ya kasa fassara wa

Sai dai ba kaɗan ba kallon ya shige sa ainun, sai ya janye nashi idanun ba tare da ya ɗauke su a kan fuskar ta ba, cikin cool voice da be taɓa sanin yana dashi ba yace, “zaki yi sallah ne sai in taimaka miki”.

 

Shiru babu amsa

 

Sai ya kalle ta yaga har yanzu idanun ta na kanshi tana mishi wannan banzan kallon da ya kasa gane kallon mene ne, sai dai kuma yanda ya daure ya kasa cire nashi idanun a kanta, tuni ya gane kallon tsantsan tsana ne, sake maimaita abinda ya faɗa mata yayi ba tare da ya ɗauke idon sa a kanta ba

 

Rufe idanun ta kawai tayi kafin tace, “ba na buƙatar taimakon ka har abada, Please ka taimaka ka tashi min a nan wurin saboda kana cutar dani da yawa”.

Yanda ka san gunki haka Usman ya koma a wurin, ya gaza ina zai saka kalaman ta bare yayi musu filla-filla ya gane me take nufi, sai dai juya su da yake yi amma kuma ya gaza tunani ƙwaƙƙwara, sai dai zuciyar sa na cike da mamaki tsantsa

Tsawon lokaci yana wurin be iya jirga wa ba, kuma be tashi ya fita ba, amma idanun sa har yanzu suna kafe a kan fuskar ta

Sai ta ware nata idanun a kanshi cike da baƙin cikin kallon da yake mata tace, “dalla ka tashi ka bani wuri a nan, na ce maka ba na buƙatar taimakon ka, wlh gwara na ruɓe a nan da ka taimaka min”.

Da yatsa ya nuna kanshi yace, “Ni kike faɗa wa haka Nafeesa?”

Wani irin juya idanu tayi cike da harzuƙa kuka na son kufce mata tace, “who you are?” Na faɗa idan ka so kar ka bar Ni da rai kaji ko?”.

Shi sosai kalaman ta suka bashi mamaki shiyasa yaji sa wani iri wanda ya kasa taɓuka komi, jin sa yake yi komi nasa yayi sanyi, memakon kalaman ta su sanya shi baƙin ciki sosai kamar yanda a baya suke saka shi, sai dai kuma wannan karon ko kaɗan ba haka ba, duk da yaji zafin kalaman ta, amma yana ganin ya ƙi mata wani abun ne domin ganin ta cikin lalura, amma da ba don haka ba…

Muryan Baba Jaure ne ya dawo dashi tunanin sa, “Fito mana Usman mu je Masallaci”.

Be ce komi ba ya tashi ya fice, har yayi Sallah be da wani kuzari

Ko da ya dawo zama yayi a waje ya haɗe kai da gwiwa

Baba Jaure da ya shigo ya soma tambayar sa “me ke damun sa?”

Amma sai yace mishi “babu komi”.

Yace, “ka wuce wancan bukkan ka kwanta kaji? Ka tashi a waje ka ga garin yana kaɗa wa”.

 

Be yi musu ba ya miƙe ya nufi ɗakin da ya nuna masa, ya shige yayi kwanciyar sa, sai dai ya gaza hana kansa tunani, be san meyasa ba kalaman ta kawai suke dawo masa, duk inda ya juya muryan ta yake ji ya rasa ya zai yi, duk da ya san cewa komi zata iya masa sakamakon abubuwan da yayi mata a baya

 

Ƙarshe tashi zaune yayi ya sake haɗa kansa da ƙafafu yaci gaba da tunanin sa, yana jin sanda ruwa ya ɓarke kamar da bakin ƙwarya amma be motsa ba, ga sanyi dake shigan sa saboda rashin rufa da be yi ba.

 

A haka har garin Allah ya waye Usman yana zaune digirgir, wanda shi kansa ya sha mamakin wannan al’amarin, domin duk yanda ya so ya hana kansa tunani ya samu barci ya gaza, haka ya tashi jiki babu ƙwari ya fita yayi alwala suka wuce masallaci shi da Baba Jaure, sai da ya dawo ne ma ya samu barcin ya ɗan sure shi cike da mafarkai kala-kala.

 

 

 

 

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

 

Sanda labarin mutuwar Usman ya riski Ayush hauka ne kawai bata yi ba, tayi kuka sosai kamar baza ta dena ba, wanda har sai da ta kwanta ciwo ranga-ranga domin ba ƙaramin shigan ta mutuwar yayi ba, dole iyayen ta suka ɗauke ta suka wuce da ita asibiti, kwanan ta biyar sannan ta soma samun sauƙi, sai dai sauƙin a jikin ta ne amma ba a zuciya ba, zuciyar ta ta rigada tayi tabon da baza ta taɓa warke wa ba, bata shirya rasa Usman a rayuwar ta ba, ko kaɗan bata taɓa kawo wa kanta zai mutu ba tare da ta cika burin ta a kanshi ba, ita kanta bata san soyayyar da take mishi ya kai haka ba sai da ya mutu, ƙarshe dai ko da aka sallame ta suka koma gida ta dena walwala gaba ɗaya ta rame, mahaifyar ta tayi-tayi ta faɗa mata abinda ke damun ta amma ina taƙi, sai dai kullum tana cikin tunani da kuka, ko abinci ta dena ci, kuma ta dena zuwa aikin ta.

 

Safra har gida tazo ta duba ta, itama ta bata baki sosai amma Ayush taƙi jin ta, har tace mata, “idan har wani saurayin ne wanda ya fi Usman zata samo mata, amma yanzu ta cire damuwa a ranta tana cutar da kanta”.

Ayush kallon ta tayi tana zubar da hawaye tace, “baza ki gane bane Safra, na rigada na saka shi can cikin zuciya ta da fitar shi zai yi wuya a gare ni, har yanzu ji nake yi a jiki na be mutu ba, na kasa yarda wlh, taya Usman ɗina zai mutu ba tare da na aure sa ba? Taya? Gaba ɗaya rayuwa ta na tsara ta ne dashi, abubuwan da nake gani a mafarki na yanzu duk sun rushe baza su gasgata ba”.

“Hmm Ayush dole ki yarda ya mutu tunda iyayen sa ma sun yarda, batun kuma ki cire sa a ranki wannan kuma me sauƙi ne, sai dai idan ke ce kika ƙi hakan, duk da na san na ɗan lokaci ne dole ki manta shi, akwai waɗanda suka fi Usman komi a duniya zaki same su, kar ki hana wa kanki jin daɗin rayuwa a kan ɗan ƙanƙanin abu Ayush, ki manta shi please, ke Kinga yanda kika koma ne?” Ta ƙare maganar tana sake bin Ayush ɗin da kallo

Numfashi kawai Ayush taja ba tare da ta sake cewa uffan ba, domin ta san duk abinda zata faɗa Safra baza ta taɓa gane wa ba, gwara tayi shiru ta ƙyale ta zai fi

“Zan tafi muje ki raka Ni, amma wlh ki sauya tunani tun kafin ki naƙasa kanki, aikin da kike matuƙar so ga shi har kin dena zuwa saboda wannan damuwar taki, idan baki yi wasa ba zaki rasa komi naki wlh”. Cewar Safran tana tashi tsaye

Itama Ayush tashi tayi ta bi ta suka fita

Mahaifiyar Ayush dake zaune tana tankaɗe Safra tayi mata sallama sannan suka fice

Har ƙofar gida ta raka ta sannan suka rabu, Ayush ta dawo ciki, ita kuma Safra ta shiga motan ta taja ta tafi.

 

 

 

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

Kaka ya samu sauƙi har an sallame sa, sai dai abinda ba a rasa ba, inda za’a ci gaba da kula dashi a gida ana ba shi magunguna, duk ya koma wani iri kullum maganar sa ɗaya Ɗahira, mutuwar ta ta shige sa ba kaɗan ba, duk da ba ita kaɗai ba har Usman ɗin, amma ya fi jin mutuwar Ɗahiran.

 

Shi kuma Baffa har yanzu ba ya sanin su waye a kanshi, jiya iyau ake har yanzu

Babu wanda ya kai Hajja Fatu shiga damuwa, ta koka ta koka har ta gaji, duk da ta san mutuwar Ɗahiran ne ya saka ɗanta shiga wannan matsanancin halin, amma bata yi nadama Ba, ji take yi da Ɗahira zata dawo duniya a yanzu haka; wlh da babu me ƙwatan ta a wurin ta, domin tasha alwashin sai ta salwantar da rayuwar ta me munin gaske, har yanzu kuma bata fasa tsine mata a zuciya ba, kullum da ita take kwana take tashi, gaba ɗaya ta sauya wa Aunty Amarya fuska, ko gaisuwar ta ba ta amsa wa, har habaici take mata, ta kasa ɓoye ƙiyayyar ta yanzu a fili, ƙiri-ƙiri take faɗa mata “ɗiyar ta ne tayi silan shigan Baffa a wannan halin, kuma wlh idan be tashi ba ta rasa shi sai taga abinda zata yi mata, daga yanzu babu mutunci a tsakanin su”.

Aunty Amarya takan bi ta da kallo ne kawai, tun abun yana bata mamaki tana ganin kamar wasa ne, sai kuma taga eh lallai Hajja Fatu da gaske take yi, sai kuma abun ya soma damun ta, “meye haɗin Ɗahira da Baffa da zata yi silan shigan sa cikin wannan halin har ya sha giya? Ta san dai babu soyayya a tsakanin su, shaƙuwa ce kawai wanda kuma Allah ne ya haɗa jinin su, tunda tana ganin ga shi jinin su ya haɗu, amma kuma Allah da ikon sa ba sa shiri da Usman, to taya ya zata ɗaura wa ɗiyar ta wannan zargin?” Ta kasa jure wa sai da ta sanar wa Abbu

Shi kuma Abbu sai yace mata, ” ta ƙyale ta tayi ta kanta, kuma duk abinda zata ce kar ta soma ta kula ta”.

Da wannan maganar na Abbu Aunty Amarya tayi amfani, duk wani haushin karen da Hajja Fatu take yi ba ta kula ta, iya kan nata ido ne.

 

 

 

 

 

 

_ku yi haƙuri babu yawa, so kuyi manage._
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR’S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER’S ASSO*📖
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA’S FAMILY*_

 

*EPISODE Fifty Seven*

 

*AFTER THREE WEEKS*

A wannan kwanakin da suka shuɗe Ɗahira ta sha wahala sosai, bazan iya misalta muku azaban da ta fuskanta ba, tabbas karaya babu daɗi, barin ma ita da take mace me rauni, kuma har ƙafafu biyu, duk juriyan ta ta kasa jure wa, sai da ta sake goce ƙafa ɗaya Baba Jaure ya sake gyara mata, azaban duniya ta sha shi har suma tayi, tasha kuka kamar zata tsiyayar da hawayen ta, domin a ranan ma kwana tayi tana kuka taƙi cin komi

Daga Baba Jaure har Usman sun kasa rarrashin ta, shi Usman ma har sai da yayi mata hawaye, sosai yake jin tausayin ta na tsarga mishi ta ko ina a jikin sa, yana jin dama zai iya da ya dawo da ciwon jikin sa.

A haka Baba Jaure yake ta rarrashin ta yana bata bakin “ta jure idan ba haka nan ba sai dai a yanke mata ƙafafun muddin basu warke ba”.

A haka kwanaki suke ta shuɗe wa Ɗahira na a wannan halin, amma duk da zafin ciwon nan ba ta bari Usman ya taimake ta, idan har ba Baba Jaure ne zai taimaka mata da wani abun ba, to, ta gwammace kar tayi, gaba ɗaya ta tsani ma ganin sa kusa da ita, baza ta taɓa manta abinda yayi mata ba, shiyasa duk idan ta ganshi sake jin tsanar sa take yi a zuciya, ya riga ya dasa mata tsanar shi me girma a rai, wanda duk duniya ba ta jin akwai mahalukin da tafi tsana idan ba shi ba, da ace za’a bata bindiga da tuni ta harbe shi

Shi kansa Usman yana mamakin wannan halin da take nuna mishi, duk da azaban da take ciki amma haka take iya nuna masa tsana tsantsa, ya kula ko kaɗan ba ta son ta buɗe ido ta ganshi, duk maganar dake bakin ta haka take yaɓa mishi ba tare da taji shakkun shi ba.

Baba Jaure dai da yaga abun yayi yawa sai ya kira Usman zuwa ɗakin da Ɗahira take kwance, yace mishi “ya zauna”.

Bayan ya zauna ya dube sa yace, “wai ya alaƙar ku da Nafeesatu ne? Ina son in San tsakanin ku?”

Shiru Usman ɗin yayi, sai ya kalli Ɗahira wacce ta rufe idanun ta tayi kamar bata san dasu ba a ɗakin

“Faɗa min mana ina magana? Ko ba kai kace min matar ka bace?”

“Eh Mata ta ce”. Yayi maganar bayan ya mayar da idanun sa kan Baba

“Amma ya aka yi ke Nafeesatu kika ce min ba mijin ki bane? Kuma na kula kwata-kwata ba kya son ya taimaka miki, idan be taimaka miki ba a wannan halin da kike ciki wane ne zai taimaka miki? Kina buƙatar taimako sosai domin ke abar tausayi ce, Shin ko wani abun yayi miki?”

Buɗe idanun ta tayi da suka soma tara ruwan hawaye, ga zuciyar ta dake mata ƙunci da jin kalmar da Usman ya faɗa, shiyasa sai da ta kalli Usman ɗin ido cikin ido kafin tace, “Baba shi ba miji na bane, ban san shi ba, bani da wani alaƙa da shi a rayuwa ta”.

Usman tsimi yayi ya kasa ɗauke idanu a kanta, ko kaɗan be ji daɗin abinda ta faɗa ba, sai ya lumshe idanun sa kawai yana haɗiyar yawu

Shi kuwa Baba Jaure jinjina kansa yayi yana sake kallon ta da kyau, sai kuma ya kalli Usman ɗin yace, “yanzu maganar wa zan yarda? Kai kace min Mijin ta ne, ita kuma tace min bata sanka ba. Amma ya aka yi kuke kama da juna, daga ganin ku kuna da alaƙa da juna?”.

Usman da ya buɗe ido yace, “Baba wlh ita Mata ta ce kuma ƙanwata, jini na ce ita..”

Cikin kuka Ɗahira ta katse shi da faɗin, “wlh Ni ba miji na bane shi, sam Ni ba na ƙaunar sa ko kaɗan, na tsane sa fiye da komi a duniyar nan! kuma takardar saki na zai bani”.

Kamar zuciyar sa zata ƙone a wannan karon sabida jin kalmar tsana a bakin ta, sosai yaji ciwon kalmar, shiyasa a harzuƙe yace, “to Ni nace miki ina ƙaunar ki ne? Ko cewa nayi bazan sake ki ba? Idan ba don laluran ki ba baki isa ki zauna kina gaya min wannan maganar ba ban yi ƙasa-ƙasa dake ba”.

“An faɗa maka kai waye? Ka sake Ni yanzu ba sai anjima ba, banza kawai..”

Hannu ya kawo zai wanka mata mari jin zagin da tayi masa, saura ƙiris hannun sa ya kai fuskar ta sai ya dunƙule, cike da wani irin fushi yake kallon ta yace, “Ni kike zagi.. Ni?” Ya nuna kansa da hannu idanun sa jawur har jijiyoyin kansa suna tashi

Sosai Ɗahira ta tsorata har tana janye jikin ta, domin ta manta ma da wani karaya a ƙafan ta, lokaci ɗaya ta saki azababben ihu

Salati kawai Baba Jaure yake yi domin ya kasa komi illa kallon su da yake faman yi, sai da yaga Ɗahira ta saki kukan ne nan ya matso yana cewa, “subhanallah mene ne me ya same ki? Kin taɓa ƙafan ko?”

Yanda take kuka kamar ana yanka naman jikin ta sai duk jikin Usman ya soma rawa, shima ya matso kusa da ita sosai amma ya kasa cewa komi illa kallon ta da yake yi

“Kun gani ko ba kya jin magana, ban ga ranan da zaki bar ƙafan nan su warke ba sai kin ja ma kanki, kai kuma Usman da girman ka kake biye mata?” Sosai Baba Jaure yake bala’i kamar zai ari baki, sai da ya haɗa su tass yayi musu masifan kafin ya kalle ta yace, “ba na son shashanci daga yau kar in sake ganin kin goce ƙafafun nan, kuma duk wani taimako da ya kamata zai riƙa taimaka miki tunda Ni ba zama nake yi ba, kinji ko kar in sake ganin kinyi wani abun da kanki?”

Gyaɗa kanta tayi tana shashsheƙan kuka

“Mu je waje Usman”. Yace dashi yana fice wa

Shima bayan sa yabi ya fita

Ita kuma Ɗahira kamar an kunna ta sai ta ɓare baki taci gaba da kuka sosai

Daga waje suna jin ta amma babu wanda ya tanka, sai dai sosai kukan ta ke shigan Usman, ji yake yi kamar ya shiga ya rarrashe ta amma ya san hakan bazai taɓa yiwuwa ba, baza ta taɓa mishi kallon arziƙi ba, shi kansa har tsoro take ba shi saboda bala’in ta, “ko dama haka take?” Yake tambayar zuciyar sa. “ko kuma zafin ciwo ne ya mayar da ita hakan ba”. Wata zuciyar tace mishi haka.

 

Daga ranan dole Ɗahira take bari Usman yana taimaka mata da wani abun idan babu Baba Jaure, sai dai ko magana ba ta mishi, shima haka, sun zama tamkar kurame, ko shekara za su yi a wuri ɗaya baza ta tanka shi ba, ko ya tambaye ta tana buƙatar wani abun ba ta kula sa, ta gummaci ta zauna har Baba Jaure ya dawo

Abun da ke ba wa Usman haushi tun sanda ta soma ba-haya (kashi) dayake ba’a bata komi sai Nono gudun kar ta riƙa ba-haya, sai ta bari Baba Jaure na nan sannan zata nuna tana buƙatar yi, shi ke taimaka mata, ta gummaci shi ya taimaka mata da Usman ya taimake ta, shiyasa abun ya soma ba wa Usman haushi, yana a matsayin mijin ta ai shi ne ya kamata yaga jikin ta ba wani ba, shiyasa da abun ya dame sa wajen kwana huɗu da bata yi ba, sai kawai ranan na biyar ɗin dai ya cire baki ya tambaye ta “ko tana jin Kashi ko fitsari ne ya taimaka mata?”

 

Sosai tambayar ya baƙanta mata rai, sai ta kalle sa kamar zata make shi tace, “ba na ji ko dole sai nayi?”

Tsaki yaja yace, “na san kina ji tunda kin kwana biyu baki yi ba, sai dai idan Ni ne ba kya son na taimaka miki sai Baba Jaure”.

 

“Allah ya kiyaye na nemi taimakon ka, abubuwan ma da kake min da zaka fasa da nafi kowa murna, ba na ƙaunar ganin ka wlh ko kaɗan a kusa dani, ji nake yi kamar zan haɗiye zuciya na mutu, mugu azzalumi kawai”.

A zuciye yace, “Nafeesa Ni kike faɗa wa haka? Wato kina ganin ina ƙyale ki shi ne yasa kike faɗa min duk abinda kike so ko?”

“An faɗa ɗin, ka kashe Ni ka huta shi ne zan san ka isa”. Ta ƙare maganar tana sakar masa kallon tsana

Hannun sa ya saka ya murɗe mata baki yana cewa, “bakin zan fasa ko zaki dawo hankalin ki kisan da wa kike magana, Ni ba sa’an wasan ki bane, ina ƙyale ki ne kawai domin ina tausaya miki”.

Kuka ta fashe dashi jin ya murɗe mata baki sosai

Ganin tana kuka sosai sai ya sassauta riƙon amma fuskar sa a ɗaure yace, “ke ki shiga hankalin ki kisan da wanda kike magana, Ni ne Usman kuma na san baki manta halina ba, wlh bar ganin kina halin lalura biji-biji dake zan yi”.

 

Bata iya cewa komi ba illa kuka da take faman yi

Ganin haka sai yaja tsaki yana tashi zai fice

Ƙasa-ƙasa tace, “mugu azzalumi Allah zai saka min wlh, kuma kashi ne bazan yi ba, kuma ma ina jin yi har da fitsarin ma”.

Dariya taso ba shi sai dai be juyo ba yayi ficewar sa

Ita kuma taci gaba da kukan ta tana yi tana tsine masa a ranta

A haka har Baba Jaure ya dawo, yana shigo wa ya ganta tana kuka ya tambaye ta ba’asi

Sai tace mishi, “Usman ne ya murɗe mata baki sannan ya falla mata mari”. Har da riƙe kumatun ta tana me fashe wa da wani kukan

Salati kawai Baba Jaure yake saki yana faɗin, “ashsha.. be kyauta ba, wannan ai mugunta ne, ba ya ganin halin da kike ciki ne?”. Sai kuma ya koma kwaɗa wa Usman ɗin kira

Usman dake waje duk yana jiyo ƙaryan da Ɗahira ta shirga mishi, ci je leɓe kawai yayi yana jinjina kansa, sai ya miƙe ya nufi ɗakin ba tare da ya amsa ba, yana shiga idanun su suka shige na juna

Sai ta balla mishi harara tana kawar da kanta

Shi kuma fuskar nan a ɗaure kamar ko yaushe yake sauraron faɗan Baba Jaure ba tare da ya ɗauke idon sa a kanta ba, duk da kuwa ba kallon sa take yi ba, “zan kama ki ne yarinyan nan zai fita ai, zan mare ki sai ki sami faɗa mishi da hujja tunda ke baki da mutunci”. Yayi maganar a ranshi

Sai da Baba Jaure ya gama mishi faɗan kafin yayi ficewar sa be ce komi ba

Ita kuma sai a lokacin ta dawo da kallon ta ga Baba Jaure tace mishi, “tana buƙatar zata yi fitsari”.

“To kuma sauri nake yi ina da rubutu a gaba na, meyasa baki ce Usman ɗin ya taimaka miki ba?”.

“Baba na Ce mishi amma yace bazai taimaka min ba, shi ne dalilin da yasa ya mare Ni”.

Baba Jaure yace, “be kyauta ba kuwa, bari in taimaka miki to, zan yi masa magana daga yau bazai sake ba”.

Taimaka mata yayi ya ɗan ɗaga ta ya saka mata wani Robber me faɗi, sai ya koma bakin ƙofa har sai da ta gama ta gyara kafin ya dawo shi kuma ya gyara mata kwanciya ta yanda baza ta motsa ƙafafuwan ba.

 

Duk abinda ta sake faɗa a kunnen Usman ya faɗa, kaɗa kai kawai yayi ya yi ficewar sa a gidan, ransa babu daɗi duk haushi ya cika sa, haka kawai yake jin haushin Baba Jaure Wanda be San dalili ba, “don me shima zai yarda ya riƙa taimakon ta bayan ga shi shi ne mijin ta? Ai wannan ma cin zarafin sa ne da kuma keta mishi haddin aure”. Sosai zuciyar sa ke a ɓace shiyasa ya nufi jeji kansa tsaye don keɓe kansa, amma wani zuciyar nasa tana faɗa masa, “kai meye naka na jin haushi bayan sakin ta zaka yi? Ko ka manta ka tsane ta ne? Sannan ma Baba Jaure ai kamar Kaka yake a wurin ta, halin lalura ne ya kawo haka dole sai an taimaka mata”. Dogon tsaki kawai yaja a fili ya furta, “to Ni ina ruwa na.. yayi mata wanka ma idan zai iya be shafe Ni ba”.
💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR’S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER’S ASSO*📖
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA’S FAMILY*_

 

*EPISODE Fifty Eight*

Sannu a hankali Ɗahira ta soma jin sauƙi, domin babu laifi yanzu tana iya ƙoƙarin ta wajen jure wa da zaman nata, ba ta motsa ƙafafuwan kullum kaffa-kaffa take yi, a haka rayuwa taci gaba inda kusan watanni huɗu kenan da soma jinyan nata, yanzu har ta soma taka wa

Baba Jaure ya haɗa mata sandan nan guda biyu da zata riƙa dogara wa

Tun ba ta iyawa da taimakon Usman da Baba Jaure ya saka shi yana koya mata tafiyan, har yanzu tana iya fita zuwa waje wani lokacin ba tare da taimakon shi ba, zaman jinya ba wasa ba, gaba ɗaya ta sauya tamkar ba ita ba, tayi wani irin haske kamar mara jini a jiki, sai kuma ƙara ramewa da tayi a fuska, sai kuma ɗan kumbura da tayi a jiki, sai dai jikin nan nata luwai-luwai kamar ka taɓa jini ya tsiyaya, saboda zama wuri ɗaya da ta jima tana yi, duk ta sauya dai. Yanzu haka har wanka tana yi da kanta, inda Baba Jaure ya samo mata itama kayan su na Fulani tana sauya shiga.

 

Ga shi yanzu har sun gabatar da azumi a wannan ƙauyen, sai dai ita Ɗahira bata samu tayi ba saboda halin da take ciki, an yi sallah an gama lafiya kuma sun yi farin ciki matuƙa kasancewar sun fita sun kalli wasan sallan mutanen ƙauyen.

 

Duk da gefe ɗaya kuma gaban su da Usman kullum daɗuwa take yi, kusan kullum sai sun yi faɗa, ita bakin ta bazai yi shiru ba babu ranan da baza ta sanar mishi ta tsani ganin shi a rayuwar ta ba

Shi kuma hakan na mishi zafi sosai, sai ya biye mata suyi ta yi tana ƙara ƙona mishi rai, shi kuma a ganin shi yana ƙyale ta ne don halin lalura, ba don haka ba zane mata jiki zai yi, amma duk da haka tsaban mugunta be fasa mangare ta ba ko kuma ya kwaɓe mata baki idan tana gaya mishi maganar da yayi mishi ɗaci a zuciya.

 

Yau ma tana zaune a waje tana shan iska

While Usman na zaune can gefe ya buga tagumi yana bin ta da kallo, sai dai a baɗini tunani ya faɗa be ma san idanuwan sa na kanta ba

Ita kuma ganin yaƙi dena kallon ta tun ɗazu sai taja tsaki tana yinƙura wa zata tashi

Tsakin nata ya dawo dashi hayyacin sa, sai ya bi ta da kallo kawai har ta miƙe, ganin ta nufi ƙofar gida zata fice sai yace, “ina zaki je?”

Bata juyo ba bare ta tanka shi, taci gaba da ɗingisa wa a hankali zata fice

Shima sai be sake ce mata komi ba ya kawar da kansa gare ta, ya ɗaura tunanin sa daga inda ya tsaya.

 

Ɗahira na fita ta soma bin garin da kallo, tun ranan sallah da ta fita sai yau ta sake saka ƙafafuwan ta a wajen, shiyasa kawai take ta bin ko ina da kallo, yanda ko ina yayi kore sharr da bukkokin gidaje sai ya bata sha’awa, tamkar dai babu kowa a garin haka wajen ya ɗaɗe, takawa ta soma yi tana ci gaba da tafiya tana kallon ko ina, jefi-jefi kuma ta soma ganin Mutane, yara a waje suna wasa da kuma hayaniyar mutanen cikin gida

Yanda suke wasan ne sai ya ɗauke mata hankali ta shagala tana kallon su

Suna ta wasan ƴar gala-gala ne maZan su da matan su, sai dai sun raba ne idan mata suka yi sai maza su yi, kowa yana son ace su ne gwani. Duk basu lura da ita ba duk tsayuwar ta

Har ta soma gajiya tana shirin juya wa sai sandan nata ya gurɗe zata faɗi, sai ji tayi an tare ta ta faɗa jikin mutum. Da sauri ta ɗago kai tana kallon sa zuciyar ta na wani irin bugawa a lokaci ɗaya da nashi, waro ido tayi kawai tana kallon shi tana ɗauke numfashi tsamm sabida yanda taji wani abu ya tsarga mata a cikin jikin ta wanda baza ta iya fasalta shi ba

Shima haka zalika abinda taji shi ya ziyarce shi, shi nashi ma har wani nauyi zuciyar tashi tayi mishi tare da tsantsan tsoron da ya saba ziyartan shi a duk sa’ilin da ya haɗa ido da ita, sai dai kuma yanda yake jin wani iri kamar an manne masa idon cikin nata ya kasa ɗauke su a kanta

Illa ita ce da tayi ƙoƙarin fizgar kanta sa’ilin da ta gama tantance a jikin wanda take, wani irin fisga tayi wa kanta saboda haushin ganin ta a jikin sa da saura ƙiris ta gurɗe ta zube ƙasa

Sai ya ƙara azamar riƙo ta da sauri yace, “ke kina da hankali kuwa?”

Wani kallo ta sakar masa cike da baƙin ciki ta kasa ce mishi uffan, ta sake yinƙurin janye jikin nata da ƙarfi duk dan ta raba kanta dashi

Yana shirin sakin ta ganin abinda take so kenan, sai sandan ta ɗaya ya faɗi, dole ta ɗage ƙafa ɗaya don baza ta iya ba da ƙarfin ta a ƙafafuwan gaba ɗaya ba, tuni hawaye sun cika mata ido saboda azaban da take ji tayi saurin ƙanƙame mishi hannu, shi kuma sai ya duƙa ya ɗauko mata sandan

Yaran wajen tuni hankalin su ya dawo gare su sun tsaya suna ta kallon su kamar wasu t.v

Su kuwa basu san ma suna yi ba, domin tuni Ɗahira ta bizge sandan nata ta daidaita su ta soma ɗingisa wa a hankali

Yanda take yi ne kamar zata sake faɗi sai yayi saurin kawo hannu zai sake tare ta yana cewa, “Please kiyi a hankali manaaaa”. Ya ƙare maganar cikin jan kalman ƙarshen in a cool voice

“Kar ka sake taɓa Ni?” Tayi maganar hawayen idanun ta na sauko mata a kunci. Sai ta sake janye jikin ta sosai kafin tace, “ko kaɗan ba na buƙatar taimakon ka. Ko ka manta a baya ma baka taimaka min ba sai yanzu? So please zan iya da kaina ba tare da taimakon ka ba, kar ka sake yinƙurin taimaka min na roƙe ka”.

Kalaman ta sun ba shi haushi sai yace, “kina tunanin zaki iya wani abun ne ba tare da taimako na ba? Idan da ban taimaka miki ba babu yanda za’a yi ki kawo yanzu a raye. Waɗannan mutanen da suka ɗauke ki da tuni yanzu sun aikata nufin su a kanki da ban amso ki a wajen su ba, so ki iya bakin ki Please ba na son cika baki, kar kuma ki ga ina kula ki ki ce komi ne zaki riƙa faɗa min”. Yaja dogon tsaki yayi gaba abin shi fuuuu kamar ana tunƙuɗa shi

Ita kuwa da kallon banza ta bi shi hawaye na sake kwaranya a fuskar ta kamar an kunna famfo, tana jin zuciyar ta na mata ƙuna da maganganun sa. Shiyasa ko jirgau ta kasa yi duk da kuwa yanda yaran nan suka mamaye ta suna bin ta da kallo sai surutu suke yi, amma ba ta jin su illa bin hanyar da yabi da kallo da take yi ta kasa ɗauke idanun ta..

 

 

“Nafeesatu lafiyan ki kuwa? Me ya fito dake waje?”

Maganar Baba Jaure da yayi ya dawo da ita tunanin ta. Saurin kallon sa tayi

Sai ya sake cewa. “Subhanallah.. kuka kike yi lafiyan ki me ya faru? Ina Usman ɗin?”

Duk bata iya amsa mishi tambayoyin ba illa hannu da ta sanya tana share hawayen ta

Yaran ya kalla yace, “kai ku tafi kuyi wasan ku kunji ko?”

Hakan yasa suka dare a wajen sai dai basu tafi ba sun tsaya suna kallon Ɗahira

Shi kuma hannu yasa ya gyara mata sandan da kyau yana cewa, “zaki iya tafiyan dai ko?”

Gyaɗa mishi kai tayi sannan ta soma tafiyan a hankali yana biye da ita a baya.

 

 

Suna shiga gidan ya nufi ɗakin da Usman yake kwana ganin be ganshi a waje ba

Yana ciki kuwa ya kwanta idanun sa a rufe, sai dai tunani ne fal cikin ransa da kuma haushin Ɗahira da yake ji, sosai ransa yake a ɓace

Nan Baba Jaure ya ɗaura masa da faɗan “barin ta da yayi ta fita ita kaɗai”.

Kanzil be ce mishi ba har ya gama ɓaɓatun shi shi kaɗai yabar wurin.

 

 

Itama Ɗahira tuni ta shige ɗaki ta zauna tana ci gaba da zubar da hawaye, baƙin ciki ne sosai ke nuƙurƙusan ta na rashin mayar mishi da martani har ya tafi, ga tsantsan tsanar shi dake ƙara rufe ta, ta tsani ta buɗe idanun ta ta ganshi kusa da ita, babu abinda ke tuna mata illa rayuwar ƙuncin da tayi sanadiyar shi, da kuma azabtarwan da yayi mata. Ita a yanzu burin ta su koma gida su Kaka su amsar mata takardan sakin ta. Nan kuwa kewan ƴan gidan su ya cika ta, ta kwanta nan tana ta murƙususu tana faman tunani.

 

A kwana a tashi kamar yau ne suka zo cikin wannan ƙauyen, sai ga shi sun shafe kimanin watanni shida a karkaran, wanda ciwon Ɗahira ne ya tsayar da su har wannan lokacin domin tuni an samu hanya, shiyasa tana warke wa suka yi haraman tafiya

 

Inda sosai Baba Jaure ya nuna rashin jin daɗin sa, domin ba kaɗan ba ya shaƙu da su a wannan watannin da suka yi tare da shi, bare shi ba me kowa ba, shiyasa rabuwar nasu zai yi masa ciwo, sosai yayi musu nasiha a kan riƙe addu’a domin shi ne takobin mumuni, duk wani halin da suke ciki su dage su riƙa kare kan su da addu’a don suna da maƙiya masu bin su da sharri, sannan yayi musu nasiha kan zamantakewar aure da ya taɓa musu zuciya ainun, kuma yace “idan da hali su zauna su sasanta su riƙe auren su hannu bibbiyu, duk wani saɓani dake tsakanin su su yi ƙoƙarin ganin sun daidaita kan su, domin ba ƙaramin dace wa suka yi da juna ba”.

A sanda yake faɗan wannan kalaman nasa har ɗago kai Usman yayi yana kafe Ɗahira da ido, inda yake son ganin abinda yasa Baba Jaure ya faɗi hakan, a kuma ƙasan ranshi yana jin wani nishaɗi da be san na mene ne ba, ko kaɗan memakon maganar tashi ta ba shi haushi sai be ji hakan ba, har yana ji a ransa a yanzu zai iya yin ma iyayen sa biyayya ya riƙe ta a matsayin matar sa ba tare da ya sake ta ba, wanda kuma a ganin sa Nasihan Baba Jaure ne ta taɓa masa zuciya ainun har yayi wannan tunanin

While ita kuma Ɗahira ko kaɗan bata yi tunanin wai zata iya ci gaba da rayuwa da shi ba, ta rigada ta saka wa ranta zaman su ya ƙare har abada, shiyasa ko ɗar bata ji ba a zancen Baba Jaure, kamar yanda yake shiga ta wannan kunnen haka yake fita ta wancan kunnen, har ya kuma gama ɗin. Sai dai zuciyar ta fal da kewar sa da za su yi, har a ranta ta ƙudura wata rana zata kawo mishi ziyara ko da ita kaɗai ce.

 

Sun fito inda Baba Jaure yayi musu jagora suka yi sallama da mutanen ƙauyen, daga nan aka ɗauke su a motan ɗiban kaya aka fita dasu har titin da zai kai su cikin gari, inda aka sauke su suka sami abin hawa suka miƙa gida, zuciyar ko wannen su cike da wani irin farin ciki da murna na ganin yau za su koma su haɗu da ahalin su. Ɗahira tsaban zumuɗi bakin ta ya ƙi rufuwa sai wani zillo take yi ta kasa zama waje ɗaya

Inda Usman kawai kallon ta yake yi yana sake jin wani irin nishaɗi a ranshi

Dayake waje ɗaya suke zaune kuma motan a cike take fal, ita tana ƙarshen baya; shi kuma yana kusa da ita, sosai suka matsu da juna

Amma hakan be sa Ɗahira ta damu ba, ta ma manta shaf illa tunanin gida da take yi da ƙosawan su kai

Sai shi ne da zuciyar sa ta hana sa sukuni, da kuma yanayin da yake ji sanadiyyar haɗuwar cinyoyin su wuri ɗaya, lumshe idanu kawai daga ƙarshe yayi yana amsar baƙon yanayin da ya zo mishi, wanda ya kasa fassara ko mene ne, tare da tunanin abinda ya kasa ɓace mishi a rai.

 

_Fans ku sanar dashi idan kun sani._

 

 

 

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

 

Kwana biyu kenan da farfaɗowar Baffa, wanda ya sanya ahalin farin ciki matuƙa, duk da jikin sa babu daɗi sosai amma kuma sun ji daɗi matuƙa. Haka aka ci gaba da kulawa dashi sosai kuma alhmadulillah yana samun sauƙi, tunda har ya soma magana kaɗan, sai dai abin mamaki babu abinda yake faɗi sai sunan Ɗahira, maganar tashi kenan Ɗahira.  Ɗahira, wanda hakan ya ɗaure wa su Big Dady kai, “ko dai ya san ta mutu ne?” Tambayar da suke wa kansu kenan

Ganin abin nashi gaba yake yi kullum maganar nasa kenan,  sosai hakan ke ƙona ran Hajja Fatu, cike da haushi kuwa tace dashi, “gwara ma ya cire ta a ranshi, idan ba haka ba sai dai shima ya mutu yabi ta”.

Maganar nata ta taɓa shi, duk da yana jin jiki haka ya ɗago yana tambayar ta fuskar shi sharɓe da hawaye, “don Allah Hajja meyasa kike wannan maganar? Yanzu kenan kina nufin baza ki bani damar auren ta ba ko da Usman ya sake ta?”

“To wa ya faɗa maka an gansu? Ai ina ce ɓacewar nata ne ya sanya ka wannan halin? To yanzu haka kimanin watanni shida kenan ba’a samu inda suke ba, mu har mun yi jana’izar su tuni…”

Tarin da ya sarƙe shi ne ya tsayar da ita daga maganar ta. Yanda yake yi tuni hankalin ta ya tashi ta ruɗe lokaci ɗaya tana kiran sunan shi

A lokacin ne su Big Dady suka shiga dai-dai da lokacin da ya fara aman jini

“Subhanallah.. innalillahi wa’inna ilaihi raji’un.. what’s going on?” Inji Abbu da duk ya ruɗe shi ke riƙe da Baffan

Hajja Fatu da duk ta ruɗe ta karaɗe ɗakin da kuka, hakan ya jawo hankalin Abba dake waje yana amsa call be shigo ba, shima nan ya faɗo ɗakin yaga halin da Baffa ke ciki, sai sambatu yake yi yana kiran Ɗahira. Dole suka soma ba shi taimakon gaggawa cike da ruɗewa ganin yanda yake yi. Daƙyar suka samu suka tsayar da jinin suka saka mishi oxygen don ba ya iya numfashi da kyau

Al’amarin da ya ƙara ɗaga hankalin su kenan, duk sun shiga damuwa suna murna ya samu sauƙi ashe zai koma gidan jiya

Inda gefe ɗaya Hajja sai faman kuka take yi, tana dana-sanin sanar mishi da abinda ke faruwa, ga shi itama zata rasa ɗanta.

 

 

Kwanan sa ɗaya ya samu ya farka, sai dai jikin babu sauƙi ko kaɗan, lokacin su Big Dady duk suna kanshi suna sake duba shi

Sai ya soma musu kuka yana tambayar su “da gaske ne Ɗahira ta mutu?”

Sosai suka yi mamakin ya aka yi ya sani

Nan Abba tunanin sa ya ba shi Hajja ce ta sanar mishi, ranshi ya ɓaci sosai amma babu yanda zai iya yace, “kayi haƙuri ka san duk me rai mamaci ne, ƙaddaran su kenan kuma babu me tsallake wa..”

Big Dady katse shi yayi yana cewa, “haba Abubakar ka dena maganar mana, ka ga ashe shi ne silan tashin ciwon shi me zai sa ka riƙa mishi bayan kana ganin halin da yake ciki?”

Baffa dake riƙe da gefen ƙirjin sa yana kuka kashirɓan yace, “wlh nima bazan iya rayuwa babu ita ba a duniyar nan, ina son ta Abba don Allah ku nemo min ita, bazai yiwu ace Ɗahira ta ta mutu ba. Tana raye don Allah ku nemo min ita Kar in mutu”. Sai ya fashe da wani sabon kukan yana cewa, “Hajja ta cuce Ni ta raba Ni da ita, amma yanzu bazan iya haƙura ba sai na aure…” Sai ya fara tari be ƙarisa ba, nan da nan jini ya soma zubar masa ta baki

 

Tashin hankali ba a saka mishi rana.

 

 

Duk taimakon da su Abba suka so ba shi amma abin ya citura, tuni zuciyar sa ta gama bugawa lokaci ɗaya numfashin sa ta ɗauke daga jikin sa, wanda hakan ya tabbatar musu da Baffa ya rasu, ya tafi ya bar duniyar.

 

Sai suka daskare kawai ba tare da sun san meye next abinda za su yi ba, amma tuni hawaye ya wanke musu fuska

Barin ma Abba da shi ya kasa tsayuwa waje ɗaya, sai kai komo yake yi cikin tsantsan tashin hankali, ƙwaƙwalwan sa ta kasa yarda Baffa ya rasu, sai ya taho kawai ya sake taɓa shi yana son tabbatar wa, cikin raunin murya yake cewa, “Baba na.. Baba na Ka tashi mana don Allah ka tashi.. Ɗahira tana raye bata mutu ba, ka tashi kaji Ni zan baka ita babu me raba ka da ita, da ka sanar min tun farko ai da tuni na aura maka ita, ka tashi kaji don Allah ka tashi”.

 

Da su Abbu suka fahimci sambatu ne kawai yake yi sai suka kama shi suka zaunar suna tausan shi, inda gaba ɗaya hawaye suke yi kashirɓan, sun kasa fita su sanar wa mutanen gidan dake bakin ƙofa suna jiran su.

 

Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un.. innalillahi wa’inna ilaihi raji’un.. kullu nafsin za’ikatul mauti 😭😭

 

Bazan iya fasalta muku halin da ahalin nan suka shiga ba sanda labarin mutuwar Baffa ya riski kowa. But think for yourself.
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR’S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER’S ASSO*📖
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA’S FAMILY*_

 

*EPISODE Fifty Nine*

Motar na sauke su suka hau keke napep ta nufi dasu gida, har suka kai babu me magana a cikin su, kowa tunanin da yake yi daban dana ɗan uwan sa.

 

Tun sanda suka doso layin gidan su suka ga mutane cike fam, wasu a zaune a cikin rumfa wasu kuma a tsaye, wasu kuma cikin motocin su inda gaba ɗaya wajen cike yake da ababen hawa

 

Al’amarin da ya soma tayarwa su Usman hankali kenan, duk suna tunanin abinda ke faruwa a ƙofar gidan su mutane suka taru haka. Daga gate ɗin su har babban Gate ɗin gidan duk an buɗe mutane nata ɓulɓulowa, wasu na shiga wasu na fita.

 

Shima me napep ɗin da yaga ya kasa kutsa motar tashi sai ya sauke su a wurin, inda tuni Ɗahira tayi gaba tabar Usman da biyan kuɗi, shima sai ya biyo bayan ta yana bin mutanen wurin da kallo, duk yaga waɗanda ya sani cikin dangi, amma dayake wurin maƙil ne ba kowa yake kula dasu ba, bare kuma yanda duk suka sauya duk kan su.

 

Ƙwaƙwalwan su fa ta kasa ɗaukar abinda kunnuwan su suke jiye musu wajen mutanen dake gaisuwa, don tuni maganganun wasu mutanen ya faɗa kunnen su inda suke gaisuwa suna faɗin sunan Baffa

Tuni Ɗahira ta ƙara sauri tana ƙoƙarin shigewa gidan

A lokacin ne kuma su Big Dady dake zaune a rumfar ƙofar gidan suka hange su, gaba ɗayan su tashi suka yi suna bin su da kallo, tabbas su Ɗahira suke gani, su ne suka dawo basu mutu ba

Usman dake shirin shiga gidan shima ya hange su nan yayo wajen su yana ɓashe baki

 

Sai suka tsaya kamar gunki suna bin shi da kallo sun kasa kataɓus, mafarki ne ko gaske shi ne abinda suke son sani, Waɗanda suka cire rai da tsammanin dawowar su; su ne yanzu suke gani a gaban su.

 

 

*******

Ciki kuwa Ɗahira sanda ta shiga ta sake tabbatar wa da tabbas zaman makokin Baffa ake yi, inda ta zo shiga Part ɗin su taji Aunty Zulaiha na kuka tana buga waya tana sanar wa wasu daga cikin dangin mijin ta, tana ce musu “har an yi jana’izar sa yanzu aka dawo ma”.

Cak ta tsaya a inda take tana jin wani abu ya tsarga mata, so take yi ta ƙarisa inda Aunty Zulaiha ke tsaye ta juya baya amma ina ƙafafuwan ta sun gaza ɗaukar ta, saboda ruɗu da tashin hankalin da ya riske ta, sai kawai ta zube a wajen ta faɗi a sume.

 

Wanda yayi dai-dai da juyowar Aunty Zulaiha tana shirin koma wa ciki, ganin mace zube bata tabbatar da ko waye ba sai ta nufe ta da sauri, ta mirgino da fuskar ta sai fuskar Ɗahira ya bayyana gare ta. Wani irin ja da baya tayi muryan ta tana rawa tace, “Ɗa..hiraa”. Sai kuma ta tashi da gudu ta shige part ɗin tana ihun kiran mutanen gidan da son sanar musu “Ɗahira ta gani”.

 

Gidan mutuwa fa ya rincaɓe da ganin dawowar su Ɗahira, don tuni su Abbu su ma sun shigo tare da Usman, lokacin an wuce da Ɗahira ɗakin Aunty Amarya, sai dai duk wani taimako da aka bata bata farfaɗo ba. Hankula sun ƙara tashi, dole aka bar zancen bin ba’asi zuwa dare lokacin an nitsa da shigowar jama’a.

 

Sanda Ɗahira ta farka kuka tay ta yi; domin ba kaɗan ba mutuwar Baffa yayi mugun taɓa ta, ko magana ta kasa ma kowa sai kuka, abinci ma taƙi ci duk ta fita hayyacin ta, sai dai rarrashin ta da ake ta faman yi.

 

Sai dare jama’ar gidan suka taru gaba ɗayan su har da su Hajiya Laila Hajiya Ikram da yaran su, da duk wani me ruwa da tsaki sai da suka cika General parlour fam, kowa so yake yi yaji labarin abinda ya faru dasu

Usman ne ya basu labarin komi, don ita Ɗahira har yanzu ba ta iya magana, tana jikin Aunty Zainab sai zubar da hawaye take yi wanda suka kasa tsaya mata tun farkawan ta, har yanzu gani take yi ƙarya ne Baffa be mutu ba, ji take yi kamar zata ganshi cikin jama’ar parlour’n, shiyasa sai ware ido take yi tana kallon mutanen ciki.

 

Sosai aka tausaya musu da wannan iftila’in da ya same su, barin ma Ɗahira ita da ta shiga mugun yanayi, karaya har biyu a ƙafafu wanda tasha jinya ba kaɗan ba, sai sannu suke mata suna “ta auna arziƙi Allah ya kyauta gaba”. Sai dai su Aunty Zulaiha su amsa amma ita ko uffan ta kasa cewa.

 

Da haka aka tashi a taron, duk yanda Kaka yaso ya gana da Ɗahira sai dai ya haƙura kasancewar ba ta cikin mood ɗin ta, ranan mutane da yawa basu runtsa ba a gidan nan, kar ma ace Hajja Fatu, domin mutuwar Baffa ya taɓa ta ainun, tasha kuka har ta gode wa Allah, duk tayi yaushi itama maganar ma ba ta iya yi

Yayinda Sa’adatu tana can asibiti ana jinyan ta, tunda tun sanda aka sanar musu rasuwar Baffa ta zube, ga tsohon cikin ta haihuwa ko yau ko gobe, duk da watan sa takwas ne amma yayi mugun girma, wasu ma cewa suke kamar ƴan biyu zata haifa saboda girman cikin, sai dai dayake likitoci ne gidan tuni an bincika an ga ɗa ɗaya ne a ganin su.

 

Washe gari kuma sai aka tashi Yusra babu lafiya, naƙuda gadan-gadan yazo mata, ba’a ma kai ga kaita asibiti ba ta silliɓo ɗan ta namiji. Kowa ya yi murna duk da ana cikin baƙin ciki.

 

Ranan bakwai ɗin Baffa da ya kasance kwana shida da haihuwar Yusra aka yi sunan ɗan nata, kasancewar duk wasu za su tafi a ranan ne, Sulaiman yayi musu kara inda ya saka wa yaron sunan Baffa. Al’ameen. Za su na kiran shi da Little Baffa.

 

Fannin Ɗahira kuwa gaba ɗaya ta sauya har ciwo sai da ta kwanta sabida damuwa, sai da Aunty Amarya tayi da gaske kafin ta soma shawo hankalin ta, sannan ta koma tana cin abinci har tana iya magana

Yau ma ce mata tayi “taje ta yiwa Hajja Fatu ta’aziyya tunda bata je ba,” ga shi dama Hajjan ba lafiya ne da ita ba

Shi ne ta tashi ta fita, sai da taje wajen Kaka kafin ta wuce Part ɗin Hajja, lokacin da ta shiga babu kowa kasancewar kowa ya watse, har Shakira ta koma gida, dayake yau kwana takwas kenan

Bayan tayi sallama taji babu kowa sai ta wuce ɗakin Hajja Fatu, sai da ta sake sallama kafin ta shiga ciki

Hajja dake kwance saman gadon ta duk ta wani rame sai kace ba ita ba, mutuwar babban ɗa kamar Baffa ba wasa ba. Tana ɗago kai taga Ɗahira ce sai tayi kicin-kicin da fuska zuciyar ta na ƙuna

Ita kuma sai ta taho ta zauna a kan drowan gadon tana gaishe ta tare da mata “ya jikin?”

Ai kuwa tuni Hajja ta yunƙura ta cafke wuyan Ɗahiran ta maƙure ta, cikin hayagaga take cewa, “kutumar uban ki dake da jikin matsiyaciya annamimiya, burin ki ya cika kin raba Ni da ɗana shi ne ke kika dawo ko? To wlh kamar yanda ya mutu kema wlh sai kin bi shi bazai taɓa yiwuwa ki kashe min ɗa ke kuma ki dawo ki ci gaba da rayuwa ba, wlh baki isa ba”.

Idanun Hajja fa sun rufe sai zagin Ɗahira take yi kamar zata kashe ta

Gaba ɗaya idanun ta sun fito waje taji shaƙa tana neman taimako

Amma Hajja taƙi sakin ta sai ƙunduma mata zagi take yi ta uwa ta uba tana faɗin “itama sai ta kashe ta”.

Hayaniyar su ne ya shigo da Abba ɗakin, domin shigowar sa kenan Part ɗin ya jiyo zagin da Hajja take ƙunduma wa, yana shigowa yaga abinda ke faruwa sai ya nufe su da mugun sauri ya ɓanɓare Hajja Fatu yana falla mata mari. “Baki da hankali ne Fatima kashe ta zaki yi? Me tayi miki?” Sai kuma ya koma kan Ɗahira da ta faɗi ƙasa tana ƙaƙarin amai kamar zata mutu, gaba ɗaya fuskar ta ya jiƙe sharkaf da hawaye domin ta ma kasa kukan. Ɗago ta yayi yana mata sannu

Amma Hajja ta soma faɗin, “wlh tallahi sai naga bayan ta babu wanda ya isa ya dakatar dani tunda tayi min sanadin mutuwar ɗana, sai na kashe ta nima”.

Tsiya fa sai ya kaure daga ita har Abba sabida jin kalaman ta da take faɗa wa Ɗahira

Lokacin ne Hajiya ta shigo taga me ke faruwa, domin hayaniyar har Part ɗin ta dayake sun fi kusa. sai taje ta sanar wa Big Dady, kankace me gida ya ɗauka da abinda ya faru, har an kai maganar wajen Kaka

Shi kuma Abba dole sai da ya matsa Hajja ta faɗi abinda yasa take son ganin bayan Ɗahira, tunda ya gane ta san komi, kuma dama ya ƙyale ta ne tun ba yau ba domin a fice taron jama’a, yana son tambayar ta ta sanar mishi alaƙar dake tsakanin Ɗahira da Baffa da har basu sani ba

Dole da ta ga bala’in sa ta faɗi gaskiya ita ta hana Baffa ya auri Ɗahira wanda sanadin haka ya faɗa shaye-shaye sannan ya kamu da ciwon zuciya

Da jin haka sai Abba ya miƙe ya kife ta da maruka har uku, duk yanda su Big Dady suka so su dakatar dashi amma ina ya gagara, be jira wata-wata ba yace, “ya sake ta”.

Tashin hankali kenan da ba’a saka mishi rana, yau ga Hajja Fatu a tsaka me wuya, domin lokaci ɗaya ta kurumce gidan da ihun ta saboda abinda bata taɓa zaton zai faru bane.

 

 

 

 

 

 

 

_So ku yi manage please._
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR’S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER’S ASSO*📖
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA’S FAMILY*_

.

*EPISODE Sixty*

Take a nan Kaka ya saka shi ya mayar da ita ɗakin ta, kuma yayi mishi faɗan saurin ɗaukar fushi abin duk be kai haka ba duk da tana da laifi, amma Allah ne ya ƙaddara wannan hanyar ne silan mutuwar Baffa

Ba da son ran Abba ba ya mayar da Hajja Fatu, amma a ranshi ya ƙudura aniyar sai ya ƙaro aure, don bazai yiwu ya ci gaba da zama da ita a matsayin mata ba tana ƙunsa mishi baƙin cikin ta, ita kenan kullum haɗa mishi jaraba sai kace ita kaɗai ce matar aure a gidan, babu me nemo magana sai ita.

Ataƙaice dai aka sasanta komi, inda Kaka yayi mata faɗa sosai ya kuma ce “kar ta sake zargin Ɗahira da ita ce silan kashe Baffa, idan kuma zata yi hakan sai dai ta zargi kanta tunda ita ce taja komi”.

Bayan an ƙarƙare maganar sai Big Dady yace ma Usman “ya miƙo mishi takardan sakin Ɗahira”.

Duƙar da kanshi yayi yace, “Dady kuyi haƙuri a kan abinda nayi muku baya wlh nayi nadama, insha Allahu yanzu zan yi muku biyayya gwargwadon iyawa ta, na yarda zan zauna da ita kamar yanda kuka zaɓa min ita”.

Ɗahira da kanta ke cinyoyin ta tana ƙananun kukan ta saboda har yanzu raɗaɗin zafin shaƙan da Hajja Fatu tayi mata be barta ba, bata san sanda ta ɗago a firgice tana kallon Usman ɗin cike da haushin jin kalaman sa ba

Bata kai ga magana ba Big Dady ya riga ta da cewa, “wannan zancen banza zancen hofi kake mana a nan, tunda har ada ka nuna mana bamu isa da kai ba kaƙi zaɓin mu, to yanzu baka isa kace zaka wulaƙanta mu ba, saki ne babu fashi dole ne sai ka sake ta dan uban ka”. Ya ƙare maganar nasa a zafafe kamar zai kai mishi duka

Kaka da ya kafe Usman ɗin da ido sai yace, “abinda za’a yi yanzu a bar maganar nan ba yanzu ne ya kamata mu yi shi ba, muna ji da raɗaɗin mutuwa a yanzu mu bari zuwa nan gaba, yanzu kowa zai iya tafiya”.

Duk tashi suka yi suna fice wa, inda Ɗahira da duk ta cika tayi fam da jin rainin hankalin Usman, sai bin shi da kallo take yi tana son su haɗa ido, sai dai shi tuni ya yi ƙofa yayi ficewar sa. Da sauri tabi bayan sa tana zuwa ta bangaje shi ta wuce

Sai ya tsaya kawai yana kallon ta cike da mamakin abinda tayi masa

Ita kuma sai da tayi taku kamar uku kafin ta jiyo tana kallon sa ta balla mishi harara cike da haushin sa da tsanar sa tayi gaba abinta ba tare da ta tanka shi ba

Sai abin ma ya bashi dariya ya kasa tafiya har sai da ta ƙule, sannan ya taka ya wuce Part ɗin iyayen sa yana jin zuciyar sa na sake cika da nishaɗi, fuskar shi kuma yalwace da kyakykyawar murmushin da sai ya jima kafin yayi shi, be san meyasa ba duk wani yanayi da yake ji a kanta yanzu yake burin jin sa a ko yaushe, musamman bugun zuciyar sa da sauyin yanayin da yake ji a jikin sa, yana son ya kalli idanun ta yaji tsoron nan dake riskan shi wanda ada yaƙi jini, har dariya yake yanzu yana mamakin wai me ke kawo hakan. Shi fa be taɓa jin yanayin da yake ji a kan yarinyan nan wajen wani ba, shiyasa ada yayi wa abun mummunan fassara, wanda yana ganin idan ba ita mayya bace taya zata riƙa bashi tsoro da faɗar masa da gaba? Har kuma ya riƙa mafarkin ta haka kawai. sai duk ya tsangwami kansa a kan lallai-lallai sai ya raba kanshi da wannan yanayin, wanda kuma yanzu kusantan da suka yi da juna na ɗan zaman nan da suka yi a ƙauyen nan, yasa ya soma saba wa da yanayin har yana jin ya riƙa kansacewa a haka idan har zai ganta kusa dashi.

 

 

_Mu je zuwa._ 🤣

 

 

 

⚫⚫⚫

Ɗahira na zuwa Part ɗin su ɗakin ta ta shige ta zauna a kan gadon ta

Sai ga Aunty Amarya itama ta shigo da sallaman ta

Amsa mata tayi tana kallon ta kamar yanda itama take bin ta da kallon, kana kuma tazo ta zauna kusa da ita

Tace, “meyasa baki sanar min soyayyar dake tsakanin ki da Baffa ba?”

“Mama Ni kaina ban san shi ne wanda muke soyayya dashi ba, sai daga baya na san hakan bayan mun rabu. Kuma naga hakan be da amfani tunda Hajja ta rigada ta raba mu, idan kuka sani baza ku ji daɗi ba”.

Ajiyan zuciya Aunty Amarya ta saki kana tace, “haka ne. Amma ba na son ki saka damuwa a ranki ko kaɗan tunda kin san halin kanki, duk wani abu yanzu ki bar shi ya wuce, kuma ki mayar da hankalin ki wajen ibadan Allah kina neman kariya wajen sa, domin Ni yanzu abubuwan tsoro suke sake bani, baki tare wa kowa komi ba ke kuma ba fin su kika yi ba amma maƙiyan ki sun yi yawa Ɗahira”.

Murmushi Ɗahiran tayi tace, “insha Allahu Mama zan kasance me neman kariya wajen Allah na, na san shi zai kare Ni”.

“Batun kuma Usman kar shima ki saka shi a ranki, babu me miki tilas a wannan lokacin domin su kansu su Kakan ba mara su hankali bane da za su sake saka ki ki koma gidan sa, babu wanda zai tilasta ki sai da yardan ki kinji?”

“Mama idan har da yarda na ne kuwa bazan taɓa koma wa gidan shi ba, ki dena ma zancen nan domin Ni na cire sa a raina tuni wlh, dole ne sai ya sake Ni don bazan taɓa zama dashi ba”. Tayi maganar kamar zata yi kuka

Murmushi Aunty Amarya tayi tana shafa kanta, kana kuma ta tashi tsaye tana cewa, “ki tashi ki je ki sake cin abinci don ɗazu ina ganin ki baki ci da yawa ba”.

Itama Ɗahiran tashi tayi tana cewa, “to. zan yi wanka ne yanzu zan fito, don Allah Mama ki turo min Fadil yazo min da wayan shi”.

Amsa mata tayi Aunty Amaryan tana fice wa

Inda ita kuma Ɗahira ta ɗauko tawul ɗin wankan ta tana shige wa Toilet.

 

 

 

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

An sallami Sa’adatu daga asibiti, sai dai ko da iyayen ta suka so su tafi da ita Legos, Kaka yace, “A’a a nan zata zauna har sai ta haifu sannan zata koma”. Dole ba don sun so ba suka haƙura, inda ta dawo Part ɗin Hajja ana kula da ita

While Yusra itama tana gidan sai tayi arba’in zata koma, abun mamaki kuma tunda Ɗahira ta dawo sai kuma duk idan suka haɗu sai tayi mata magana

Da fari hakan ya saka Ɗahira tunani da tsantsan mamaki, amma kuma duk idan taje duba little Baffa sai tayi ta janta da hira, ba ita kaɗai ba har Hajiya, sai duk abin yayi mata banbaraƙwai wai na miji da suna Inna ta Hajara. Duk da a zuci hakan yayi mata daɗi amma kuma da ta tuna ko suna yi ne don ta koma gidan Usman sai ta soma jin haushin su, daga baya sai ta ɗauke ƙafa da zuwa, amma kuma haka Yusra take biyo ta har ɗakin ta wai “ta ji ta shiru bata zo taga Little ba”. Tun ba ta kula ta har dai ta saki jikin ta tunda a ganin ta hakan ma sauƙi ne ga rayuwar ta, ace yau maƙiyin ka ya koma masoyin ka

Fannin Usman kuma basu sake haɗuwa da shi ba, kuma ko kaɗan ba ta ƙaunar haɗuwar nasu ma.

 

 

***********

 

Rayuwa taci gaba da tafiya inda har an yi sadakan arba’in ɗin Baffa

Inda ita kuma Yusra ta gama jegon ta ta koma gida itama.

Sai a lokacin ne Ɗahira ta samu damar koma wa bakin aikin ta, inda taci gaba da aikin ta cikin salama da kwanciyar hankali, sai dai har yanzu kewan Baffa na maƙale a ranta, ta kan tuna sa wani lokacin tayi ta zubar da hawaye tana mishi addu’a, kuma har lokacin bata sake jin ɗuriyan Usman ba, ga shi ba’a sake yin zancen sakin ta ba, itama shiyasa bata sake kula maganar ba, tunda dole ne dai sai ya sake ta, ko kotu ne sai an je babu wanda ya isa ya saka ta ta koma gidan Usman.

 

Gefe ɗaya kuma Usman shima ya koma aikin sa, sai dai be taɓa neman Ɗahira domin ya ganta ba, tunda sosai zuciyar sa ke addabar shi da son ganin ta, ba kaɗan ba tunanin ta ya gallabi ruhin sa, tun yana ganin abin da sauƙi, har kuma dai ya kasa jure wa yau ya yanke shawaran zuwa Office ɗin ta ya same ta, ko da ganin waɗannan idanuwan nata ne masu firgitar dashi domin yaji sanyi a ranshi, a lokacin da yake tunanin yana zaune ne a Office ɗin sa yana ta faman murmusawa. Sai kuma ya tashi ya fito ya nufi Office ɗin ta

Nocking yayi

Sai ta ba shi iznin shiga

Ya buɗe ya shiga yana bin ta da kallo

Ɗahira da kanta ke kan files tana duba wa, ƙamshin turaren sa kawai ya ziyarci hancin ta sai taji wani muguwar faɗuwar gaba ta ziyarce ta, da sauri ta ɗago don tabbatar da shi ɗin ne wanda take hasashe

Ilai kuwa shi ne yana tsaye a bakin ƙofan, shi be shigo ba kuma be fita ba idanun shi a kanta

Sai ta ɗauke idanun ta tana jin zuciyarta na ci gaba da bugawan sauri kamar zata faso ƙirjin ta, take a nan yanayin jikin ta ya sauya lokaci ɗaya taji yayi mugun sanyi har tana jin yanda hannayen ta suka soma rawa

“I want to talk to you”. Yayi maganar har yanzu yana tsaye a bakin ƙofan be ɗauke ido a kanta ba

Bata motsa ba bare ta sake kallon sa, illa ɗaure fuskar ta da tayi tana me jin baƙin cikin sa da tsanar sa me girma a zuciya

Takowa kawai yayi ya zauna ganin bata kula shi ba, sai da kamar soconni uku suka shuɗe kafin ya buɗi baki yace, “wani alfarma nazo nema wajen ki, na san zaki yi mamaki sosai but ki ɗauka tamkar zan yi hakan ne domin faranta ran iyayen mu, ki amince muci gaba da zama a matsayin mata da miji domin yiwa iyayen mu biyayya kamar yanda suka so tun Farko..”

Be ƙare maganar ba ta ɗago tana kallon sa da idanuwan ta da suka cika fal da hawaye, cikin rawan murya da za’a gane ƙiris take jira ta saki kuka, ba wai don komi ba sai don ƙuncin da kalaman sa suka saka ta, tace dashi, “kai har kana da bakin da zaka zo waje na kace in koma ɗakin ka domin muyi wa iyayen mu biyayya? Kar ka manta tsanar da nake maka ya zarce tunanin ka, kai ka koya min tun ban san kaina ba. har gobe bazan taɓa manta azaba da wahalan da ka bani ba, idanun ka sun rufe saboda tsantsan tsanar da kake min, ka manta cewa Ni ƙanwar ka ce kuma jinin ka, ka gallaza min uƙuban da na gummaci mutuwa ta da rayuwa ta, taya ya kake tunanin zan iya yafe wa har in koma in Yi rayuwar aure da kai? Never wlh. Har abada bazan taɓa manta abinda kayi min ba, yana nan daram a cikin zuciya ta wanda kullum ƙara jin tsanar ka nake yi a cikin ta, I hate you Usman I will never go back to your house .. ”

Tsawa ya daka mata saboda jin maganganun ta da suke ƙona masa zuciya da ya kasa jure wa. Sai kawai yaga ta fashe mishi da dariya ga kuma hawaye suna ɗiga a fuskar ta, sai ya saki baki yana kallon ta cike da mamakin ta

Ido cikin ido take kallon sa bayan ta tsayar da dariyan nata lokaci ɗaya tace, “Hi Guy gate out of my office baza ka zo kayi min iko a nan ba”.

“Ni kike kora?”

“Eh kai. WHO ARE YOU?”

A fusace ya tashi yana nuna ta da yatsa yace, “zan nuna miki kuwa Ni wane ne, kuma zan tabbatar miki da cewa baki isa kici galaba a kaina ba”. Sai ya saki guntun murmushi yace, “gida na ne dai baza ki koma ba har kike furta min munanan kalaman nan ko? To zan ga yanda zaki yi kiyi auren da igiyar aure na, muddin ba gida na kika koma ba baza ki taɓa aure ba wlh, sai dai ki mutu da aure na a kan ki babu wanda ya isa ya saka Ni na sake ki, ba wai don ina son ki ba sai dan in sauke miki wannan iskancin da yake kanki, dole ki koma gida na kuma dole ki amsa sunan mata ta”.

Fashe wa tayi da kuka cikin ƙunan zuciya tace, “wlh ƙarya kake yi mugu azzalumi, Ni ba matar ka bace, dole ne sai ka sake Ni”.

Dariya ya saki lokaci ɗaya saboda ganin yaci galaba da saka ta baƙin ciki kamar yadda ta saka shi

Lokaci ɗaya ta tsayar da kukan nata ganin dariya a fuskar sa wanda tunda take bata taɓa ganin shi yayi ko da murmushi ne ba. Sai gani kawai tayi ya zagayo ta gefen ta har yana ranƙwafo wa saitin kunnen ta

Yace, “Mata ta ce ke wlh, kuma dole sai kin amsa sunan nan, babu wanda ya isa ya raba aure na dake ko waye..”

Da sauri ta tashi saboda jin tsigan jikin ta ya tashi gaba ɗaya ta rasa sukunin ta, hakan yasa suka yi karo da juna kansu ya bugu, sai duk suka riƙe goshin suna kallon idanun junan su, nata idanun sun yi luhu-luhu suna zubar da hawaye kamar wanda aka kunna famfo.

Hannu ya saka ya…

 

 

 

 

 

 

 

 

_kai na gaji mu haɗu next page sai ku ji ya za’a kaya. Amma ku bi Ni bashi zuwa jibi._
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR’S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER’S ASSO*📖
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA’S FAMILY*_

 

*EPISODE Sixty One*

Hannu ya saka ya janyo ta jikin sa yana kallon ta

Wanda ita lokaci ɗaya ta rufe idanun ta jikin ta ya soma rawa ta soma ƙoƙarin ƙwace kanta

Murmushin mugunta ya saki yana sake manna ta a jikin sa, a hankali ya furta. “Na san baki manta abinda ya faru ba a ƙauyen Baba Jaure. So Kar ki tunzura Ni in sake maimaita wa wlh, ki kama kanki ba na son rashin kunya, ba wai na sauya bane daga hali na bane, sai dai na sassauto ne wanda Ni kaina ban san meyasa tsanar da nake miki na dena ji ba”. Sai yayi shiru yana saka hannun sa ya shafi fuskar ta yace, “kina burge Ni yanzu shiyasa. Ki kula”. Ya sake ta ya fice abin sa.

Wani irin kuka me ƙara ta saki tana zame wa a ƙasan wajen jikin ta na ci gaba da rawa. “Allah ya isa tsakani na da kai Usman, ka gama dani wlh ka cuce Ni! bazan taɓa yafe maka ba mugu azzalumi kawai!”.

Kuka sosai take yi ta kasa tashi a wurin, ji take yi da zata iya da sai ta faffalla mishi mari ko zata samu sukunin ƙuncin da yake ƙunsa mata.

 

Bata tashi a durƙushe a wurin ba sai da taji ana mata Nocking, a tunanin ta ko Usman ɗin ne ya sake dawowa shiyasa ta ɗauke kukan nata cak tana jiran shigowar sa tayi masa rashin mutunci, tana ga hakan kaɗai zai saka ya fita harkan ta, domin ta tsane shi ko kaɗan ba ta son ma wata magana ta sake shiga tsakanin su. But sai taji shiru ba’a shigo ba illa Nocking ɗin da aka ci gaba da yi, dole ta tashi tana share fuskar ta tare da daidaita nutsuwar ta, ta ba da iznin shigo wa tana zama a kan kujera

 

Ayush da Safra ne suka shigo Office ɗin idanun su a kan Ɗahira da itama ta ɗago rinannun idanuwan ta tana bin su da kallo

Kallo ɗaya da tayi musu ta gane Ayush, sai ta saki fuskan ta kaɗan tayi musu Bismillah

Zama suka yi suna murmushi duk kan su

Ayush tace, “na san baki gane Ni ba ko? Ni ce Dr. Ayush Abdulkarim friend ɗin Dr. Baffa”.

Yaƙe Ɗahira tayi tace, “Na gane ki mana. Ai na san ki a Hospital ɗin nan”.

“Haka ne. Wannan ƙawata ce sunan ta Safra, mun zo miki ta’aziyya ne, sai kuma taya ku murna a kan dawowar ku”.

“Allah Sarki Nagode sosai”.

“Allah ya jiƙansa Allah ya gafarta masa”. Suka haɗa baki ita da Safran suka faɗa

Ɗahira ta amsa da “Amin Amin”. Tana jin idanun ta suna ciko wa da hawaye.

“To zamu tafi, sai kuma mun sake kewayo wa”.

Daga nan sallama suka sake yi sannan suka fice.

 

Suna fita Ayush ta kalli Office ɗin Dr. Usman, ji take yi kamar ta ganshi ya fito

Safra ta dafa mata kafaɗa tace, “zo mu wuce don Allah, ai komi ya kusa zuwa ƙarshe tunda ga shi Allah ya bayyana su basu mutu ba, so yanzu burin mu zai cika, kar ki soma ko da da wasa ki je Office ɗin sa sai sanda muka cika aikin mu. Yanzu abun da ya kamata mu shiga jikin ita matar tashi, ta hakan ne zamu samu muna shiga gidan su har mu samu gashin kanshi, wannan hanyar shi ne me sauƙi da zamu bi, dole sai mun zama ƙawayen ta”.

Murmushi Ayush tayi tace, “gaskiya ne ƙawalli, ziyaran gaba kuma gida za mu kai mata”.

“Ashe kin gane. Mu je mu ƙarisa maganar a mota akwai wani Alhaji da na samo miki, na san zaki fi jin daɗin harka dashi yana da kuɗi sosai. Kin san ya kamata mu soma shirye-shiryen biki ma tun yanzu”.

Dariya suka yi har da kashe wa suka yi gaba cike da nishaɗi, barin ma Ayush da bakin ta yaƙi rufuwa, tun ranan da bayyanar su Usman ɗin yazo kunnen ta, kullum ba ta iya barci tsaban murna.

 

 

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

Fannin Abba kamar yanda yayi ƙudirin sake aure ashe be fasa ba abun na ranshi, har ya sanar wa su Big Dady da Kaka, inda Kaka yaso ƙin amince wa tare da tausan sa “ya haƙura yaci gaba da zama da ita a haka”. Amma shi yace, “dama shi yana da burin sake auren, kuma ya rigada ya yi niyya”. Dole Kakan ya ƙyale shi tare da saka mishi albarka a kan maganar

To abu kamar wasa sai ga shi Abba ya samo wata bazawara dake cikin anguwan nasu, yaran ta biyu duk ka yara ne, na farkon ma sa’an Fadil ne, mijin ta ya rasu ne wajen shekara biyu, Abokin shi yayi mishi hanyar ta, don haka tuni Abba ya amince da batun nata

Har aka saka rana Hajja Fatu bata sani ba, domin yaƙi sanar mata, sati Uku aka saka, sai da ya rage saura sati ɗaya sannan ne ya sanar mata, shima don taga yana kwashe kayan ɗakin shi yana mayar wa ɗakin Baffa ne, don a ɗakin nasa zai ajiye ta

Nan fa Hajja ta tashi hankalin ta a kan “sai ya faɗa mata dalilin sa na cire kayan shi ya mayar can”.

Shi ne yake faɗa mata, “aure zai yi”.

Bazan iya fasalta muku haukan da Hajja Fatu tayi ba, tayi borin tayi kukan domin ya fasa auren

Amma sam yace, “bata isa ba tunda yayi ninya”.

Wannan dalilin ne ya kawo saɓani a tsakanin su me girma har Hajja tayi yaji ta koma gida. Ko kwana bata yi ba Hajiya Hannatu (Ihsan) ta dawo da ita, tace, “sam wannan shirmen ba dai a gidan ta ba, kuma wlh muddin ta tafi wani wuri yaji; zata haɗu da fushin ta”. Dole ba don taso ba Hajja ta zauna a gidan, amma fa fitina yaƙi ƙare wa a dole sai Abba ya janye auren nan

Sai dai kuma babu abinda ya fasu sai ci gaba da bikin ake yi, domin har Kaka ya zaunar da ita ya kwantar mata da hankali amma ta ƙi ji, dole suka zira mata ido tayi ta gaji ta bari.

 

Ana saura kwana huɗu bikin ne Sa’adatu ta haifi ɗiyar ta mace ƙatuwa, abun mamaki duk girman cikin nan kuwa, domin har ya zarta wata tara kowa yayi tunanin ƴan biyu ne, sai dai Allah ya nuna ikon sa ashe mace ce. Dole aka ɗaga bikin zuwa ranan suna sai a haɗa ayi tare.

 

 

*SUNDAY*
Ranan biki da ya kasance ranan suna, an raɗa wa yarinya sunan Hajja Fatu, Fatima za su na kiran ta da Zahra

Gida ya cika maƙil tubarakalla, mutane sai dai suka tare a sauran Part ɗin, amma Hajja ta hana kowa shigo mata sashi, Shakira ma bata zo ba saboda tana taya uwar ta kishi

Su kuwa duk yaran gidan suna sashin su Ɗahira, dayake yafi girma nan, a nan suka shantake suna ta hira. har da su Fadila da su Salma ita ma da babyn ta ita da Shamsiyya duk sun zo

Ɗahira na cikin su ana ta washe baki, duk kansu sun yi ankon kamfala doguwar riga me ruwan zuma da ratsin fatsi-fatsi na milk

Yanzu haka ma abinci suke ci shi ne suke ta shewa

Uwar surutu Firdausi ta kalli Ɗahira tace, “wai ke yaushe ne mu kuma zamu dawo musha sunan ɗan mu? Kin wani ƙaƙabe tunda kika shige gidan Yaya Usman kin ƙi sulluɓo mana ɗa”.

Dayake su ba su da labarin zaman da suka yi, iyakan iyayen su suka ji labari

Ɗahira hararan ta tayi tace, “sai ranan da kika yi naki auren kika fara sulluɓo ɗanki kafin Ni in diro nawa”.

Dariya suka yi

Inda Salma ta amshe zancen da faɗin, “ai wannan rasa kunyan ba yanzu ba, zaki sha wahala kuwa idan kika ce zaki jira ta”.

Gyara zaman ta Firdausin tayi tace, “faɗa mata dai, sai kun yi yara bibbiyu ko uku-uku kafin Ni nawa ke tafe”.

Su Aunty Zulaiha dake zaune saman gadon Fadila na da, sun yi ɗai-ɗai suna ci a saman, a tare suka haɗa baki ita da Aunty Zainab wajen faɗin, “keee Firdausi kiji tsoron Allah, da gaske kike yi?”

Sai duk ɗakin suka kwashe da dariya

Yusra da ta bigi bayan Firdausin tana cewa, “ai kuwa da kin shiga uku kuwa, kiyi ta zama a gida babu Aure, ko da kuwa da gaske kike yi zan sami Gwaggon namu in kitsa mata ayi-ayi kema kin ƙosa tunda shigowa cikin manya kike yi kina kwasan gulma”.

“Oh su Yusra manya, wlh kin daɗe baki ce mata ba, ga ƙuda can zai riga ki”. Cewar Firdausin tana fuske wa

Ɗahira tace, “wai ba batun wasa ba da gaske kike yi don Allah?”

“Da gaske ne mana”. Tafaɗa tana kai loman tuwon ta

Sai duk suka tsaya suna kallon ta

Shamsiyya da ta miƙe da kwanon tuwon ta, dayake ita kaɗai take ci tace, “kin ga banu kuwa, ki zauna har sai kin tsofe”. Ta ƙare maganar da fice wa

Salma tace, “ku kun dauka da gaske ne? Ku dena biye ma wannan wlh an kusa saka mata rana, domin Ni da Daddy muka yi zancen nan kwanaki da naje gida”.

Sai Firdausin ta ɗaka mata duka a cinya tace, “wato dama ke kika ziga shi ko? Ashe shiyasa yazo min da zancen in turo Wanda nake so, ga babban muna-fuka a gefe ina tare da ita”.

“Kambu… Ni kika duka Firdausi? Dan Allah Ɗahira riƙe min yaron nan wlh sai na rama, zan ga dani dake waye muna-fuka kina so kina kaiwa kasuwa”.

“To kaji kun fara ko? Dama babu daman ku haɗu waje ɗaya”. Inji Aunty Zulaiha

Ita kuma Firdausi tunda taga ta yunƙuro ta tsame hannun ta cikin tuwon ta ruga aguje tabar ɗakin

Salma na mara mata baya tana cewa, “wlh ko cikin Momy kika koma sai na ƙwaƙulo ki na rama, gwara ma ki tsaya”.

Me za su yi ƴan ɗakin ba dariya ba, sosai suke dariya. Inda Aunty Zulaiha take ta kwaɗa wa Salma Kira a kan “kar ta bi ta ta dawo”. Amma ina tuni ta fice

Ɗahira dake ta faman dariya tashi tayi tana girgiza yaron Salman tace, “ai gwara ta bi ta ta zane mata jiki tunda Firdausi ta raina ta, kamar ba yayar ta ba”.

Aunty Zulaiha tace, “to ai ga shi nan ta bar miki wannan yaron me shegen kukan jaraba, kema ki bi ta wlh duk ya kure mana kunne”.

“Haba Aunty. Kema fa kin kusa haihuwar ba’a san ke kuma wanda zaki haifa ba, kin manta goyon Ilham da idan kika zo da ita gidan nan har Abbu sai yayi Magana tsaban jaraban kukan ta?”

Ai kuwa sai suka koma yiwa Aunty Zulaiha dariya

Ita kuma tana cewa, “dalla can ina Ilham tayi kukan wannan yaron, ai wlh ita idan kin ga tayi kuka sai dai abinci take nema”.

Ajiye yaron tayi tsakiyan su tace, “to ga shi ku riƙe mata shi, tunda ku ne babu yara a hannun ku bari inje in dawo”.

Har ta juya zata tafi caraf Aunty Zulaiha ta riƙe mata hannu tace, “dawo. Dawo nan babu inda zaki tafi ki bar mana yaron nan wlh, ki bari uwar sa ta dawo”.

Su Yusra sai dariya suke musu da Shamsiyya da ta dawo sawo miya

Inda ita kuma Ɗahira ta nace sai ta tafi ta bar musu

“Ke wlh bar ganin yanzu kin soma kumari ba fi na ƙarfi kika yi ba, yanzu sai in zaune ki a nan, ki ɗauke shi kinji ko?”

Kama haɓa Ɗahiran tayi tace, “kai Aunty har da kuma sharri. Don Allah wlh yanzu zan dawo zan je wajen Kaka ne”. Tayi maganar cikin marairaice fuska

Hararan ta tayi kana ta kalli Aunty Zainab da itama dai dariya take musu tace, “gane min hanya Zainab, wannan yarinyan ba tayi ƙiba ba?”

“Tayi mana, wlh da gaske Ɗahira kin yi kumari kamar ba ke ce silindiyan gidan mu ba, duk ɗauka na ma yanda kike kamar a huren nan babu abinda zai saka ki ƙiba, amma tunda kika dawo ƙauyen can naga kin sauya sosai, da alamu furan ruga ya karɓe ki dole in ce aunty Amarya ta nema miki fura ya zama abincin ki idan har tana son ɗiyar ta ta zama irin mu tubarakalla”. Aunty Zainab ta ƙare maganar nata da dariya

Sai duk kan su suka fashe da dariya kowa na faɗin, “ai wlh da gaske ne yanzu duk ta sauya”.

Itama dai Ɗahiran murmushi kawai tayi don ta san zancen su ba ƙarya bane

Fadila da ta shigo ɗakin yanzu take cewa, “wai me ake tattaunawa ne babu mu?”

Nan Shamsiyya take sanar mata suna dariya

Sai itama tayi dariyan tana cewa, “kin ji sister ki riƙa addu’a kina tofa wa wlh, idan ba haka ba sai dai ki tashi ki ga kin tsiyaye tsaban idanu dake yawo a kanki, ba dama dai aga mutum yayi kumari yayi ɗan kumatu sai a saka shi gaba, dama waye yace baza kiyi ƙiba ba? ai ba haka zaki zauna ba kamar ana ɗiban ki ana miya. komi da lokacin sa”.

 

 

Da haka dai suka yi ta hiran su inda suka canza zancen kuma da labarin Amaryan da za’a kawo musu, kowa na faɗin albarkacin bakin shi.

 

Da yamma aka kawo Amaryan Abba me suna Jamila, tare da yaran ta guda biyu Suhail da Abdulra’uf, an sauke ta ɗakin Abba inda aka gyara mata shi aka cika mata maƙil da kaya sai son barka. Su kuma yaran ta za suna kwana a ɗakin Shakira na da, don Abba har ya saka an gyara musu

Babu abinda ya kai wannan baƙin ciki wajen Hajja, tamkar ta mutu sai dai babu yanda zata yi ne, tana ji tana gani wata banza ta zo zata mallake mata gida, ina bazai saɓu ba dole ne sai ta samar wa kanta mafita.

 

 

Haka a ranan dai aka sha biki duk aka watse don ba wanda ya kwana sai ƴan nesa.

 

 

*************

Washe gari Usman na Office ɗin shi wani staff ya shigo kamar yanda ya saka a nemo mishi shi

Gaishe shi yayi cikin girmamawa kafin yace mishi, “ga shi ya zo”.

Kallon shi Usman ɗin yayi sosai, kana kuma yace, “kai ne wanda aka taɓa aiko ka da envelope ka kawo min?”

“Eh Ni ne”. Ya amsa shi shima idanun shi a kanshi

“Ok zaka iya gane wanda ya aiko ka?”

Shiru yayi na ɗan daƙiƙu, kana yace, “eh insha Allahu idan har na ganshi zan iya gane shi”.

“Ok you can go”.

Fita yayi a Office ɗin

Shi kuma Usman ɗin sai ya jawo drowan table ɗin shi ya yago pepper a jikin wani memo, rubutu yayi kafin ya ɗago pepern yana kallo, tabbas idan be manta ba wannan address ɗin shi ne ya gani a jikin pictures ɗin, sake ƙura wa peppern idanu yayi yana sake nazartan rubutun, sai kuma ya lumshe idanun sa yana jan numfashi, ya buɗe su yana cije leɓen bakin sa, kana kuma ya ajiye takardan tare da ɗaura biron akai.
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR’S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER’S ASSO*📖
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA’S FAMILY*_

 

*EPISODE Sixty Two*

 

 

*AFTER TWO WEEKS*

Yana cikin ɗaura agogon sa daga hannun sa na hagu, sai yaji wayan sa ta soma ƙara, sai da ya ɗan leƙa ya tabbatar da wanda yake tsimaye ne kafin ya ɗauka yana karawa a kunne

Daga can mutumin yace, “ranka ya daɗe! gani tare da su na gama aikin”.

“Ok turo min address ɗin”. Daga haka ya kashe wayan yana ajiye wa

Ci gaba yayi da ɗaura wrest watch ɗin, bayan ya gama sai ya miƙe daga bakin gadon shi da yake zaune, takalman sa ya zira cover shoes baƙi sannan ya ɗauki wayan sa ya zira a aljihun gaban rigan shi ya fito ya rufe gidan ya fice, kai tsaye Part ɗin iyayen shi ya wuce, yana shiga da sallama ciki-ciki

Hajiya ta amsa mishi da ke zaune a kan dainning tana yin kari

Wajen ta ya nufa ya zauna a ɗaya daga cikin kujerun, sannan ya gaishe ta a miskilancen da ya saba

Amsa mishi tayi tana bin shi da kallo, sai kuma dai tace, “ina zaka je da safen nan?”

Hannu ya saka yana haɗa tea yana bata amsa, “zan je wani wuri ne”.

Bata sake mishi magana ba haka suka zauna Kamar kurame

Sai kuma can yace, “Dady ya tafi ne?”

“Eh ya fita tun ƙarfe 06:30am. Amma kai ya batun maganar ku da Ɗahira? Ka san cewa ya zura maka ido ne yaga iya gudun ruwan ka da ya neme ka kaƙi kazo, ya kamata tun wuri ka kawo mishi takardan yarinyan nan kafin haɗuwar ku, idan kuma ka ce baza ka sake ta ba kamar yanda kace ɗin ne, to, tun wuri ka neme shi ka ba shi haƙuri, don na san shi ne yafi ɗaukan zafi, idan kuma ba son zama da ita kake yi ba gwara ka sake ta ka dena cutan ƴar mutane da auren ka a kanta”.

Shiru yayi be ce komi ba, illa shan tea ɗin shi da yake yi, amma kuma abaɗini juya kalaman Hajiyan yake yi

Ganin be kula ta ba itama sai ta tashi ta wucewar ta ta bar shi nan

Be ƙara mintuna biyu cikakku ba shima ya tashi ya fice, kai tsaye gidan su ya koma ya ɗauki mota ya fice, a lokacin ne ya duba wayan sa yaga address ɗin hotel ɗin da aka turo mishi, sai ya wuce can.

 

Har ciki ya shiga da motan shi yayi parking, kafin ya fito sai da ya saka baƙin glasses a fuskar sa sannan ya fita ya nufi room ɗin da aka turo mishi, yana zuwa dai-dai ɗakin yayi Nocking

Sai ga wani saurayi ya buɗe mishi ƙofan

Ya shiga yana bin ko ina da kallo ta cikin glasses ɗin sa yana yatsina

“Suna cikin wancan ɗakin”. Cewar saurayin kanshi a ƙasa

“Ka tabbatar su ne?” Yayi maganar yana kallon sa fuska a ɗaure

“Eh wlh su ne suka bani aikin, bazan manta su ba tunda na san ɗaya daga ciki”.

“Ok mu je”. Yafaɗa yana yin gaba cikin bedroom ɗin

Shi kuma mutumin yabi bayan shi jiki na rawa

Da shigan shi ya sauke idanun sa a kan Safra da Ayush dake zaune an ɗaure musu hannu da ƙafa kuma an rufe musu baki, zare idanu kawai suke yi ganin Usman sai zufa ya fara keto musu tsaban tsorata fiye da yanda suke a farko

Sai da ya gama ƙare musu kallon wulaƙanci fuskar sa babu alamar rahama, sarai ya gane fuskar Ayush tunda ba yau ba ya rigada yayi making ɗin ta, kai komo ya riƙa yi yana sake bin su da kallo, sai da ya mula kafin yace, “wato ku ne sheɗanun da har ƙananan ƙwaƙwalan ku ya saka muku tunanin ku shiga gona ta ko?” Sai ya ci je baki yana saka hannayen sa cikin aljihun wandon sa kana yaci gaba da faɗin, “har kuna iya ɗaukar picture ɗin ƴar uwan ku mace ku yi mata wannan ƙazafin saboda cikan burin ku? To yau zan maida sharrin ya koma kanku, ku sani da kyau Ni Usman ba na yafiya ko misƙala zarratan ga ire-iren ku…” Sai ya datse haƙoran sa be ƙarisa abinda yake son faɗa ɗin ba, ɗan jan numfashi yayi kana ya kalli mutumin yace, “ka tuɓe kayan su gaba ɗaya ba na son ganin komi a jikin su, sannan ka ɗaukar min su hoto kowacce kuma da fuskar ta a ciki. Ko wacce sai na kaima uwarta ta gani, idan kuma babu me uwa a cikin ku na san kuna da uba da dangi…” Sai ya sake yin shiru yana bin su da kallo da idanun sa da suka soma canza kala. “Common kayi min abinda na sa ka ka tsaya kana kallo na, saura kaima zan dawo kanka”. Yayi maganar cikin tsawa

Da sauri jiki na rawa mutumin ya nufe su ya soma cire musu kayan

Ko waccen su na tsiyayar da hawaye kamar ƙasa ta tsage su shige ganin cin mutuncin da yau za’a musu. Har Ayush da zuciyar ta ke cike da ƙaunar Usman ɗin amma yau sai da taji dama bata san shi a rayuwar ta ba, da wani ido zata kalli dangin ta muddin abinda ya faɗa ɗin ya aikata musu? Wayyo.. wayyo kaico da wannan ranan a wurin su

Usman na wurin be jirga ba har aka gama cire musu kayan su kaf, kana ya miƙa wayan shi mutumin ya amsa ya soma ɗaukan su hotuna

Haka suke kuka amma babu halin roƙo sabida bakin su dake rufe

Sai da ya gama tass kafin ya amshi wayan shi ya tura wa mutumin a tashi wayan

Kallon shi yayi yace, “ka tabbatar kayi min aikin da na saka ka nan da gobe, ina son hotunan su fi na yarinyan muni haka nake son gani, kuma kayi zaman tsare su nan da kwana biyu kafin ka sake su, ko abinci ba na buƙatar ka basu illa ruwa, wannan aikin kawai zaka yi min na yafe maka, idan ba haka ba ka san sauran zancen…” Daga haka ya juya ya fice abin sa

Yana shiga motan shi yaja yayi gaba, agogon hannun sa ya duba yaga ƙarfe 09:20am. Ne, duk da yanzu ba time ɗin shiga Office ɗin sa bane, kuma yana da wurin da zai je amma yana buƙatar ya sanya Ɗahira a idanun sa, don haka can Hospital ɗin ya nufa. Yana yin parcking ya fito ya shige, kai tsaye Office ɗin ta ya wuce ba tare da yayi Nocking ba ya buɗe ya shige

Da sauri ta ɗago kanta tana zuba mishi idanun nan nata masu saka shi a wani mawuyacin hali

Ɗan lumshe nashi idanun yayi yana buɗe wa a kanta

A lokacin tuni ta ɗaure fuska tamau tana jiran taji me yazo mata a Office

Sai ya ɗan sosa kansa yana kawar da ƙwayan idanun sa a kanta, domin yanda ta kafe sa da kallo kamar zata haɗiye shi ɗanye, hakan yasa yaji gaba ɗaya natsuwar sa ya gushe wanda ya saukar masa da kasala nan take, ɗan ƙasa-ƙasa yake kallon ta cike da isa da sanyin murya can ƙasa yace, “ina son zamu yi magana ne Nafeesa, ki bani aron hankalin ki, na san…” Dole ya tsayar da maganar ganin ta tashi ta nufi Toilet zata shige, sai yayi saurin taka wa ya isa wajen ta, tana buɗe ƙofan caraf ya riƙe mata hannu

Lokaci ɗaya ta juyo tana kallon sa hawaye na cika mata ido, cike da haushin sa tace, “Please Yaya Usman ina ganin girman ka kar ka saka nayi maka abinda baka zata ba, wlh wlh idan har baka fita harka na nayi rayuwa ta Ni kaɗai ba duk abinda nayi maka kai kaja”.

Murmushi yayi memakon yaji haushi, sai ya sake riƙe mata hannun gam yana haɗa shi da nashi ta cikin yatsun ta, a hankali yace, “common Babe ba hayaniya ne ya kawo Ni wajen ki ba, neman sulhu ne… Kuma kin san an ce sulhu alkhairi… Anyway ki manta komi Nafeesa ki yafe min, haƙuri nazo baki dama ba wani abu ba, na san nayi miki ba dai-dai ba wanda yasa nake ta faɗan abubuwan da na san ba haka bane”. Sai yaja numfashi a hankali yana kallon fuskar ta sannan yace, “ki amince ki koma ɗaki na mu rufa wa junan mu asiri kinji?”

Hannun ta tayi ƙoƙarin janye wa amma yaƙi saki, cike da yanayin fusata a muryan ta tace, “to Ni na ce ba na ƙaunar ka! ba na ƙaunar zama da kai ko dole ne? Ko kana tunanin don ka san wace ce Ni a yanzu wani abun alfahari ne a wuri na? Da sanin ka da rashin sa duk ɗaya ne a wuri na. Usman bazan taɓa zama da kai ba domin na tsane ka fiye da yanda kake zato..”

Hannu ya saka ya rufe mata bakin ta sabida ya gaji da jin waɗannan munanan kalaman nata, sosai zuciyar sa ke tafarfasa da jin ɗaci a cikin ta wanda tuni har idanun sa sun soma yin ja suna ƙyallin ruwa

Hannu ta sanya zata janye nashi hannun

Sai kawai ya janyo ta ya haɗe bakin su wuri ɗaya

Lokaci ɗaya gaba ɗayan su suka ji su a wani irin yanayin da basu taɓa shigan shi ba, wanda har ita tsaban tsuma tuni jikin ta ya fara rawa, sai kuma tashin zuciya da nan da nan sai ga amai ta guntso shi ta bakin ta ya shige nashi

Ai sai yayi saurin sakin ta yana tare aman ba tare da ya shige can cikin shi ba

Ita kuma tuni ta shige Toilet ɗin da gudu ta dinga kwarara shi kamar zata amayar da kayan cikin ta

Da gudu yabi bayan ta ba tare da ya damu da abinda tayi masa ba, domin ko kaɗan be ji ƙazantan hakan ba, illa ma son duba halin da take ciki da yake yi. Da kallo kawai yake bin ta da ya shiga ciki yanda yaga tana kwarara aman sai duk tausayin ta ya shige sa, yana son taɓa ta amma kuma ya kasa ƙarisawa wajen ta

Sai da tayi har ta gama sannan ta samu ta kuskure bakin ta

Shima sai a lokacin ya samu ya isa wajen ta yana mata sannu

Bata ce komi ba ta juya zata fice da sauri

Sai da yaga fitar ta kafin shima ya samu ya wanke bakin shi, ya ɗauki tissue Yana goge hannun sa ya fice

Ashe tana bakin ƙofan ta kasa jirga wa saboda jirin dake son kwasan ta ƙasa

Yana buɗe ƙofan ta faɗo mishi a jiki. Yayi saurin tare ta yana tambayar ta. “Lafiya me ke damun ta?”

Wani kallo ta watsa mishi cike da baƙin cikin abinda yayi mata, kana ta janye jikin ta ta nufi table ɗin ta a hankali ta soma haɗa kayan ta cikin jaka, tana gama wa ta juya ta fice ta bar shi nan tsaye yana bin ta da kallo

Ya jima a Office ɗin be iya ko motsi ba, sai daga baya jiki a sanyaye ya fito ya rufe mata Office ɗin ya wuce nashi ranshi duk babu daɗi.

 

 

********

Kai tsaye gida ta wuce, tana shiga parlour’n su da sallama, babu kowa ciki, sai ta wuce ɗakin Maman ta

Lokacin tana sallah

Sai ta fito ta wuce ɗakin su, a kan gadon ta ta zauna tana me zame jakan ta daga kafaɗan ta, shiru tayi tana riƙe da kanta, gaba ɗaya ba ta jin daɗin jikin ta, musamman idan ta tuna abinda Usman yayi mata sai ta fara jin aman na taso mata, ga kuma jirin da take ji kaɗan-kaɗan. Tsaki taja kawai tana tashi ta wuce Toilet, wanka tayi kafin ta ɗaura alwala ta fito, sai ta shirya cikin riga da wando na Pakistan blue da ratsin ruwan goro, sallan azahar ta gabatar sannan ta tashi ta sake komawa ɗakin Maman

Aunty Amarya lokacin tana tsaye tana ninke sallayan ta amsa mata sallaman tare da gaisuwar da tayi mata, sannan itama tace, “har kin dawo haka da wuri yau?”

Zama tayi a kan kujeran ɗakin kana ta amsa ta da cewa, “eh Mama, ba na jin daɗin jiki na ne shiyasa”.

“Amma kin sha magani?”

“A’a”.

“To maza tashi ki je kici abinci sai ki sha, me ke miki ciwo ne?”. Aunty Amaryan tafaɗa tana kallon ta

Shiru tayi don baza ta iya cewa ga inda ke mata ciwo ba, kawai ba ta jin daɗin yanayin ne sam, sai kuma zazzaɓi dake son kama ta kaɗan-kaɗan

Jin tayi shiru sai tace mata, “kin yi shiru ina magana?”

“Mama zazzaɓi ne kawai”.

“Ai ba kawai ba ne, gwara a tare shi tun kafin ya kwantar dake, je ki ci abincin”.

“To”. Ta amsa ta tana tashi ta fice

A lokacin Umma na zaune a parlour’n

Sai tace, “Umma sannu da huta wa”.

“Ɗahira kin dawo? Lafiya ko?”

“Lafiya lau Umma, yau dai ba na jin daɗe wa ne shi ne na dawo in huta”.

“Ai kuwa dai gwara ki riƙa huta wa da aikin nan, ayi mutum kullum babu hutu dole ki gaji”.

Murmushi kawai Ɗahiran tayi tana zama saman kujeran dainning, ta soma ɗiban abincin ta zuba a Plate

Ita kuma Umma tuni ta mayar da hankalin ta ga kallon ta, tana kallon maimaicin LABARI NA da ake yi

Ɗahira da har ta soma cin abincin sai duk tunanin ta ya koma ga abinda Usman yayi mata yau, sai ta soma jin zuciyar ta na tashi, duk yanda taso ta daure amma ta kasa, da sauri ta tashi ta wuce ɗakin ta, ta shiga Toilet ta dinga kwarara aman kamar zata amayar da hanjin cikin ta, ga shi babu komi a cikin nata shiyasa duk ta gama galabaita, sai da ta gama kafin ta wanke bakin ta ta tashi ta fito, kan gadon ta ta dawo ta zauna sabida gaba ɗaya jikin ta babu ƙarfi

Kamar mintuna biyu da zaman ta kafin ta tashi ta fito Parlour

Umma da kallo take bin ta cike da tuhuma tace, “lafiyan ki ƙalau kuwa Ɗahira? Kamar naji kina ƙaƙarin amai ko?”

Hannun ta ta cire daga bakin ta tana bata amsa da faɗin, “lafiya lau Umma, abincin nan ne be min daɗi ba shi ne ya saka Ni amai”.

“To fa?” Umma tayi maganar tana waro ido waje, sai kuma ta koma taɓe baki tana sake bin ta da kallo

Ita dai Ɗahira tuni ta wuce ta zauna, memakon taci gaba da cin abincin sai ta tsaya juya cokalin, sai kuma daga baya ta tashi ta wuce ɗakin Maman ta

Da ta tambaye ta “taci abincin?”

Sai tace mata “Eh”.

Sai ta ɗauko mata first eid box ɗin maganin su, ta ciran mata na zazzaɓin ta miƙa mata

A nan tasha sannan ta kwanta a doguwar kujeran ɗakin.

 

 

Abu kamar wasa sai Ɗahira ta wuni a ranan tana amai

Tun Aunty Amarya bata sani ba har ta gane, dole ta buga wa Abbu waya ta sanar mishi halin da Ɗahiran take ciki, tunda duk ta sha magani har da na tsayar da aman amma yaƙi tsaya wa. Sai daga baya kuma zazzaɓi ya rufe ta ciwo sosai.

 

Da sauri ya nufo gidan, yanda ya ganta sai yace, “kawai a wuce da ita asibiti”.

Lokacin duk mutan gida sun ji labari, Kaka ne kaɗai ba’a faɗa mishi ba.

 

 

Da isar su asibiti aka fara bata taimakon gaggawa, wata likita ce me duba ta

Kamar mintuna talatin sai ta fito ta buƙaci ganin su Abbu

Sai da suka shiga suka ga jikin nata da sauƙi sosai, don lokacin idon ta biyu ana mata ƙarin ruwa, sannan sai suka wuce wajen likitan.

 

Sanda ta faɗa musu result ɗin Ɗahiran ya matuƙar girgiza su, a tare suka furta, “ciki?”

Murmushi tayi likitan tace, “eh mana DOCTOR’S ko kuna mamaki ne?”

“Amma kin tabbatar Dr. Maryam?” Cewar Abba

“Eh ƙwarai ciki ne da ita har na tsawon three months, I congratulate you all”. Ta ƙare maganar still tana murmushi

“Ok mun gode Doctor, babu dai wani abu dake damun ta ko?” Big Dady yayi maganar

“Babu gaskiya, sai dai fatan Allah ya raba lafiya”.

 

Fitowa suka yi suka wuce ɗakin da Ɗahiran ke ciki

A lokacin Yusra ta cire ma Ɗahiran drip ta shiga Toilet

Sai ita da Aunty Amarya suke ɗakin zaune

Bayan sun shigo ne Abbu ke tambayar “Ɗahiran fa?”

Yusra ce ta ba shi amsa da “tana Toilet”.

“Ok”.

 

Aunty Amarya ta tambayi Abbun abinda ke damun Ɗahiran?

Shi ne yake sanar mata

A lokacin Hajiya da Umma da kuma Aunty Jamila Amaryan Abba suka shigo ɗakin, sai maganar ya faɗa kunnen su

Kowa mamakin cikin yake yi duba da yanda suka san ba zaman lafiya ne a tsakanin su ba. Sai dai kowa yayi gum ya bar mamakin sa a ciki tunda dai sun san mace da mijin ta bare su yi zargi, hakan na nufin daga can ƙauyen da suke abun ya faru…

 

 

Ɗahira dake shirin fitowa, tana jin abinda Abbu ya faɗa ai sai tayi taga-taga zata faɗi, tayi saurin jingina da bango jikin ta na rawa sosai, wani irin gumi ne ya soma keto mata nan da nan hawaye suka soma zirya a fuskar ta, bakin ta na rawa daƙyar ta furta, “ciiiik..cikiiii”.

 

 

😲🤔
_Flash Back…_
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR’S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER’S ASSO*📖
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA’S FAMILY*_

 

*EPISODE Sixty Three*

Ta san cewa wannan watan ne kawai bata ga period ɗin ta ba, amma bata ɗau abun da wani tunani ba tunda wani time ɗin tana tsallaken wata. amma taya har tana da cikin wata uku ba tare da ta sani ba?

“Ya ilahi… Allah kasa mafarki nake yi ba gaske ba”. Tayi maganar tana zubar da hawaye sosai daga fuskar sa

Sai kuma ta lumshe idanun ta lokaci ɗaya abinda ya faru a wancan ranan ya dawo mata, tabbas ranan na ɗaya daga cikin ranakun da baza su taɓa gushe wa a duniyar rayuwar ta ba…

A ranan Baba Jaure ya tafi jeji da yammacin ranan wanda yace musu “sai zuwa gobe zai dawo”

Zuwa dare sai ga hadari ya haɗu. Tana zaune tana ɗan matsa ƙafafun ta tana bin su da magani

Sai ga Usman ya shigo ɗakin. Zama yayi yana bin ta da kallo wanda ita tuni ta kawar da nata idanun tunda tayi mishi kallo ɗaya tana sake haɗe rai

Kamar ta tambaye shi abinda ya shigo dashi ɗakin, sai kuma taga wahalar da kanta zata yi kawai

Kamar shuɗewar mintuna biyu duk idanun sa na kanta, sai kuma ya buɗi baki yace, “kawo in taya ki”.

Shiru tayi masa bata kalle shi ba bare ya sa ran zata tanka shi

Sai ya taɓe baki yace, “don ma kin samu ina kula ki shiyasa kike min abinda kika ga dama ko? Yayi kyau”. Yafaɗa yana ɗauke kai

Duk bata kula shi ba, domin yi ma tayi kamar babu shi a ɗakin.

 

Ruwan ne ya sake kece wa kamar da bakin ƙwarya, sai ta ɗaga kai ta kalli ƙofan, sannan ta mayar da idanun ta kanshi tace, “Malam ka fita zan kulle ƙofa”.

“To na hana ki ne?” Yayi maganar ba tare da ya kalle ta ba

A fusace tace, “ka san dai bazan iya kwana da kai a ɗakin nan ba ko? Ko ka fita ko in fice in bar maka”.

Ɗan kallon ta yayi yaga alamun fa a sama take, sai be ce komi ba ya tashi ya fice

Taja tsaki tana raka shi da harara wanda be san ma tana yi ba, lallaɓa wa tayi ta tashi a hankali ta isa ƙofan ta tura shi, kana ta koma ta kwanta a shimfiɗar ta, ta ɗan jima tana tunanin da ya zame mata jiki, wanda ba komi bane sai tunanin mutanen gidan su, sai kuma daga baya tayi addu’a ta shafa ta juya kwanciya tare da rufe idanun ta, babu jima wa kuwa barcin ya fizge ta.

 

 

 

******

Fannin Usman kuwa tunda ya fita sai yayi tsayuwar sa a tsakar gidan ruwa na ta dakan shi, sai da yayi sharkaf wanda ya ɗau kusan mintuna goma a cikin ruwan, kafin ya samu ya wuce ɗakin kwanan shi, kayan jikin shi ya cire ya sauya da wani riga da wando farare na Fulani, sai kuma ya kwanta yana ta faman tunani, gaba ɗaya zuciyar sa ta hana shi sukuni babu abinda yake tuna wa sai Ɗahira, da sanda lokacin bata farfaɗo ba yana wanke mata jiki, har tunanin sanda ya ganta babu riga a can Turkay sai da ya faɗo mishi, shi kansa be san yana murmushi ba tsaban nishaɗin da yake ji a ranshi.

 

Duk yanda yaso ya jure abinda yake ji game da feeling ɗin ta amma abun ya citura, bare yanda ruwa ya dake shi duk tsigan jikin sa ya gama tashi. ƙirr idanun sa sun kasa barci, dole ya miƙe ya bi umarnin zuciyar sa a kan zuwa ɗakin ta, shi kansa be san meyasa ba amma yana son zuwa gare ta ko da kallon fuskar ta ne ya riƙa yi, ya san a yanzu tayi barci shiyasa ya lallaɓa ya wuce ɗakin nata kanshi tsaye

A hankali ya tura ƙyauren ya shige, akwai fitilan aci bal-bal da bata kashe ba, da sanɗa ya ƙarisa kusa da ita ya sauke idanun sa a kan fuskar ta. Ajiyan numfashi ya sauke yana matsawa kusa da ita ya sanya hannun sa a hankali ya soma shafa mata fuska

The more Yana shafa mata fuska the more Yana ƙara jin feeling ɗin ta. Duk yanda yaso ya daure ya koma tunda yayi mintoci a ɗakin yana ƙare mata kallo, amma ina tuni zuciyar sa ta ingiza shi yin abinda be taɓa tunanin mata ba. Wanda ya kasa controling zuciyar sa da gangan jikin sa ga abinda suke muradi a halin yanzu.

 

Kamar a mafarki haka take amsar saƙonnin nashi, tun tana iya jurewa domin a zaton nata lallai mafarkin ne, but a lokacin da ta farka tuni yayi nisan kiwon da bazai taɓa jiyo ta ba, duk yanda taso ta ƙwaci kanta amma ina ta gaza, haka take kuka tana roƙon shi saboda bata shirya zuwan ma wannan ranan ba, kuma ga wanda zuciyar ta ke cike da zallan tsanar sa, amma ta kasa cin nasara, dole tana ji tana gani ya raba ta da budurcin ta ba tare da ta iya ƙwatan kanta ba….

 

 

Kuka ta fashe dashi a sanda tazo nan a tunanin ta

Da sauri Yusra ta buɗe ƙofan bayin tana kiran sunan ta. Sai ta ƙarisa wajen ta tana riƙo ta ganin ta a zube a ƙasa. Duk tambayoyin da ta jero mata a kan sanin abinda ke damun ta, amma taƙi ƙo motsa wa bare ta tanka ta, dole ta kamo hannun ta suka fito

Duk ƴan ɗakin da kallo suka bi ta ganin yanda hawaye ke zuba a saman fuskar ta. Kuma duk tambayar da suka yi mata sai dai tace musu, “babu komi”. Sai gaba ɗaya tunanin su sai ya tafi a kan bayyanar cikin ne, duk da babu wanda ya kawo wani zargi wanda kowa zuciyar sa cike take da amince wa da cikin Usman ne, amma tabbas abun da ciwo a gare ta, kuma kowa ya gane abinda take ma kuka

Aunty Jamila ce kawai da bata gama sanin abinda ke faruwa ba, duk da ta san akwai saɓani a tare da su. Ita take ta faman rarrashin ta

Su Abbu dai fita suka yi a ɗakin. Inda Yusra ta mayar mata da ƙarin ruwan.

 

Mutanen gidan basu koma ba har sai da bayan sallan isha’i yayi, inda suka tafi tare da Ɗahiran tunda an bata sallama.

 

Suna koma wa Big Dady ya nemi Usman yazo ya same shi a part ɗin su. Nan ya titsiye shi a kan ya ba shi takardan sakin Ɗahira

Amma Usman babu kunya yace ma Big Dadyn, “shi fa yana son Matar sa yanzu bazai sake ta ba, bare kuma yanzu tana ɗauke da cikin ɗan sa, be ga wanda ya isa ya saka shi sakin ta ba”.

Marin shi Big Dadyn yayi saboda jin kalaman sa

Daga Usman ɗin har Hajiya dake zaune tana sauraron su sai da suka shiga shock sabida zallan mamakin sa. Maganar sa ne ya dawo da su hayyacin su

“Mutumin banza mutumin hofi, har kai ka isa ka faɗa mana abinda ya kamata? Da can meyasa baka ɗauke ta a matsayin matar ka ba sai yanzu? Tunda kai mara kunya ne duk abinda kayi mata kace zamu bar ka haka, a kan daughter babu abinda bazan iya maka ba in dai in ƙwato mata haƙƙin ta ne…”

Da sauri Usman ɗin ya tashi tun kafin ya gama jin zantukan nashi ya fice yana zubar da hawaye.

 

Hajiya da itama hankalin ta yayi ƙololuwar tashi a kan abinda Big Dadyn yayi, tace dashi, “haba Dadyn Zainab meyasa baza ka tausaya wa yaron nan ba? Wlh tunda har kaji ya buɗe baki ya ce yana son zama da matar sa, to, har zuciyar sa ne, kuma…”

“Ki yi min shiru Asiya baza ki koya min abinda zan yi ba, bari kiji wlh kema duk sanda na sake magana irin wannan kika sako min baki zaki ga abinda zan miki, tunda ke kike ɗaure masa gindi yake son mayar damu mutanen banza. Aure ne kuma babu fashi sai an raba shi”. Sai ya tashi fuuu ya wuce ɗaki ya bar ta a nan.

 

 

***********

Kai tsaye Part ɗin shi ya wuce, ya buɗe ƙofan ya shige sai kan gadon shi ya faɗa riƙe da kumatun shi har Yanzu, idanun sa na tsiyayar da hawaye kamar ba shi ne Jarumin nan me dakakken zuciya ba, samun ka ga hawaye a kyakykyawar fuskar sa sai an jima, amma yau sai ga shi a kan abinda be shirya masa ba yana zubar da hawaye, shi dai ya san cewa har zuciyar sa yanzu yana matuƙar jin ta, kuma bazai iya rabuwa da ita ba domin babu macen da ta cancanci zama dashi sai ita, ita kaɗai yanzu yake ganin ta dace da shi, ba zai taɓa iya zama da kowa ba sai ita, shiyasa kawai yake son daidaita komi ya wuce, amma kuma yana ganin ba sauƙi ne abun ba. Ya zai yi?

Ya jima a haka a wannan mawuyacin halin da ya kasa controling ɓacin ransa, babu abinda yake muradi yanzu illa ya saka ta a idon sa, amma kuma yanda yake ji bazai iya ko da motsa wa bane a wurin.

 

A wannan daren daƙyar barci ɓarawo ya sace sa. Be farka ba sai ƙarfe 09:00am. Komawar sa bayan sallan asuba

Koda ya tashi wanka ya soma yi fuskar sa duk babu walwala, har wani kumbura tayi fuskar saboda damuwa da rashin barci da be samu yayi ba

Yana shirya wa ya fice yayi Part ɗin su Ɗahira, da shigan sa da sallama

Aunty amarya da Umma dake karin safe suka amsa mishi suna bin shi da kallo cike da mamakin ganin shi

Shi kuwa be damu da kallon da suke mishi ba, daƙyar ya saki fuskar sa ya gaishe su yana tambayan Abbu?

Umma ce ta ba shi amsa da faɗin, “yanzu ya fita shi da Fadil ai”.

Sai ya ɗan shafa kansa yace, “Nafeesa fa?”

Sai duk suka tsaya suna kallon sa don basu fahimci da wa yake nufi ba

Tunanin ko Ɗahira ce yake nufi da Aunty Amarya tayi, shi ne tace mishi, “bata tashi daga barci ba”.

“Ok bari in duba ta”. Yayi maganar yana yin gaba ya shige ɗakin ta

Sai suka saki baki kawai suna bin shi da kallo cike da zallan mamakin rashin kunyan sa.

 

Shi ko, ko a jikin sa. Yana shiga ya ganta kwance daga ita sai doguwar riga mara nauyi me taushi da aka yi kwalliyan Flower’s a jiki, kalan fari da Green. Ba barci take yi ba tunda ta tashi tun ɗazu har tayi wanka, kawai koma wa tayi ta kwanta sabida ba ta jin daɗin jikin ta, ga tunanin cikin nan ya hana ta sukuni, tana tuna wa sai hawaye. Bata ji shigowar sa ba sai jin mutum tayi yana shirin hayo wa kan gadon. Kan ta farga ya haye abun shi. A firgice ta ciro kanta dake ƙarƙashin matashi saboda ba ƙaramin tsorata tayi ba, bata taɓa tunanin shi zata gani ba shiyasa ta saki baki zata kurma ihu sabida tsaban kiɗima

Take ya rufe mata baki da nashi yana janyo ta jikin shi

Duk iya mutsu-mutsun da take yi wajen ƙwatan kanta amma ina ta kasa, lokaci ɗaya hawaye ya wanke mata fuska tare da fashe wa da kukan da ba’a jin muryan ta sai gunjin kukan, sabida tsaban takaici da ya cika ta ta kasa motsa wa ma

Shi kuma sai da ya gama tsotsan bakin ta son ransa, sai da ya ga zai iya rasa tunanin sa kafin ya janye bakin nashi yana ajiyan zuciya idanun sa har sun sauya kala

Tuni ta tusa kanta a pilow ta saki wani kuka me cike da ƙunci da baƙin cikin abinda yayi mata

Kallon ta yake yi kawai be iya cewa komi ba, ba don dai ya san a part ɗin su yake ba babu abinda zai hana shi maimaita abinda yayi mata a baya, sai dai sosai ya daure ya zamo ta jikin ta har yana sakin mata nauyin sa ya sauka kan gadon. Sai da ya ɗan gyara gashin sa da rigan sa kafin daƙyar yace, “kiyi haƙuri kinji? Dama ganin baby na nazo Yi na kasa haƙura, tashi zaune mu gaisa”.

Ko motsi taƙi yi illa sautin kukan ta dake ƙara yawa

Ganin haka sai ya saka hannu kawai yana ɗaga rigan ta zai saka hannun sa ya shafa cikin ta yana faɗin, “to Ni bari in duba lafiyan Bab…”

Be ƙarisa ba da sauri ta tashi tana janyo hannun shi ta kama ta gantsara mishi cizo da ƙarfin ta

Ihu ya saki da ƙaramin murya yana ware ido, da sauri ya fizge hannun yana yarfe wa

“Mugu azzalumi ka fita a nan ɗakin ko in maka abinda ba ka zato”. Tayi maganar cikin ihu da hayagaga wanda ita kanta bata san cewa tana da irin wannan fushin ba

Sai ya saki baki kawai yana kallon ta

“Ka fita nace”.

“Ashe kin iya faɗa haka? To babu inda zan je tunda ke matata ce”.

Fashe wa da wani sabon kukan tayi da gudu ta tashi ta shige Toilet ta garƙame ƙofan

Duk yanda yaso ta buɗe ƙofan amma taƙi sauraron sa, illa kukan ta da yake jiyo wa kawai, sai ya wuce ya fice

Umma ce kaɗai a parlour’n, don tuni Aunty Amarya ta shige nata ɗakin saboda baza ta iya ganin abin kunyan nan da Usman yake shirin musu ba, tunda duk wani maganar su suna jiyo wa, sai dai basu fahimci me suke cewa ba illa hayaniyar su

Umman na ganin ya fice ta tashi ta shigo ɗakin Ɗahiran, ganin bata a ciki sai kukan ta da take ji a Toilet, sai ta taɓe baki tana bin gadon da kallo. “Oh dama wannan yaron haka kake ba ka da kunya?” Sai ta nufi kuma bakin ƙofan ta soma buga wa tana kiran sunan Ɗahira

But tana jin ta taƙi amsa wa

Dole ta fice ganin ta ƙi buɗe wa, a ranta tana faɗin, “muna-fukai zaku yi bayani ne daga ke har shi ɗin, ƴan iska kuna so kuna kaiwa kasuwa”.

 

 

 

 

_Barka da sallah FAN’S. Da fatan an yi sallah Lafiya? Allah ya maimaita mana. Amma dai ban san cewa gaskiya baku so na ba sai yanzu, Ko ɗan cin-cin ɗin nan babu wanda yace “Ummu Ɗahirah ga naki”. Babu komo ai_ 😭
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR’S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER’S ASSO*📖
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA’S FAMILY*_

 

*EPISODE Sixty Four*

Sai da tasha kukan ta son ranta kafin ta wanke idanuwan ta ta fito, a hankali ta taka ta isa kan gadon ta hannayen ta a saman fuskar ta, kwanciya tayi tana sake cusa kanta a jikin gadon, gaba ɗaya ta rasa me ke mata daɗi, Usman yana son zame mata matsala a Rayuwa, shin me yake nema da ita ne yanzu? Ada ba ya ƙaunar ta amma yanzu yana nuna wa duniya yana son zama da ita? Shin ko dai wani abun ne yake son sake aikata mata? Shi ne ta kasa gane wa

“Allah ya fi ka Usman baza ka taɓa cin nasara a kaina ba, duk yanda zan yi sai na bi domin rabuwa da kai”. Tayi maganar a fili tana share hawayen da suka soma sintiri a fuskar ta.

 

Tana nan kwance sai ga Aunty Amarya ta shigo jin ta shiru da tayi

“Lafiyan ki kuwa Ɗahira?”

Ɗago kai tayi tana kallon ta, sai ta gyaɗa mata kai tana cewa, “eh Mama”.

Ɗan ƙura mata ido tayi ganin yanda fuskar ta duk ta sauya idanun ta suka kumbura, kowa ya ganta ya san tayi kuka, amma ta san cewa hakan na da alaƙa da zuwan Usman ɗin, ba dai tace mata komi game dashi ɗin ba, sai cewa tayi, “ta fito ta yi Breakfast”. Sannan ta fice

Itama tashi tayi tabi bayan ta, saman dainning ta zauna ta zuba arish da egg ɗin dake wajen a cikin Plate, sai dai gaba ɗaya ta gaza kaiwa baki saboda kawai ƙamshin be mata ba, gajeren tsaki taja tana miƙe wa

A lokacin Aunty Amarya ta fito ɗaki tana kallon ta tace, “ina kuma zaki je baki ci ba kin zuba zaki tafi?”

“Mama bazan iya cin komi a wurin ba”.

“Saboda me? Ko tea ɗin baza ki haɗa ki sha ba?”

“Mama bazan iya sha ba wlh, na san ina sha zai saka Ni amai”.

Da kallo kawai Aunty Amaryan take bin ta, sai kuma tace, “to me zaki ci sai na dafa miki tunda baza ki zauna da yunwa ba?”

“A’a Mama bari zan yi da kaina”.

“To ki kula”. Tayi maganar tana juya wa ɗaki

Ita kuma Ɗahiran ta wuce kichen, kai tsaye inda suke ajiye ƙullun koko ta wuce ta ɗiba kaɗan, sai ta ɗaura ruwan zafi. Wake ta samu ta sirfe ta zuba kayan miya ta markaɗa a blender, lokacin har ta dama kokon ta ta sake a jug sannan ta gama haɗa ƙullun ƙosan ta, sai ta ɗaura mai a wuta ta soma soya ƙosan, tun a wutan tana tsame wa take haɗiye shi da zafi-zafin shi. Kafin ma ta gama ta cinye sai ɗan kaɗan da ta bari, ta zuba kokon a Cup ta zauna nan ta cinye sauran da kokon

Umma ce ta shigo ta same ta a kichen ɗin, sai ta dube ta tana murmushi tace, “a’a yau kuma kwaɗayin koko da ƙosai ake ne babu tayi?”

Murmushi Ɗahiran itama tayi tace, “eyya ai ban san zaki ci bane shiyasa na cinye, amma akwai raguwan kokon”.

“A’a wasa nake miki, ci abin ki ai ke ce me lalura”.

Duƙar da kanta Ɗahiran tayi bata ce mata komi ba, ta ƙarishe shanye kokon tana miƙe wa ta fice ta bar ta a kichen ɗin.

 

Ɗaki ta koma ta sanya Hijab ƙarami a jikin ta ta fito ta wuce ɗakin Maman ta, ce mata tayi “zata je wajen Kaka”.

“To ke da baki da lafiya kuma meye na yawo?” Inji Aunty Amarya

“Don Allah Mama bazan daɗe ba wlh, zamu yi magana da shi ne”.

“Ok sai kin dawo”.

Fita tayi ta wuce wajen Kaka. Tana shiga da sallama

Ya amsa mata cike da fara’a

Sai da taje har gaban sa ta ja mishi Gemu kafin ta zauna a gefen gadon shi tana faɗin, “My Kakus Ina kwana. Ya kuma tsufan?”

Dariya yayi yace, “ai na bar miki Mata ta, ke ce kike fama dashi, Ni kuwa kin ganni sumul ba kamar ke ba da kullum kina rashin lafiya. Ya jikin naki to? Iyayen ki ɗazu suke faɗa min abun farin ciki”.

Kwaɓe fuska tayi tace, “Ni Kaka ba wannan ba, Ni don Allah yaushe za’a raba aure na da Yaya Usman? Ka ga har yanzu ina ta zaune da auren shi yaƙi saki na”.

“Abinda kike so yanzu kenan?” Yayi maganar yana kallon ta

“Eh Kaka”.

“Shikenan kar ki damu zuwa anjima zan tara ku mu yi maganar”.

“Yauwa Kaka na, na gode”. Tayi maganar tana sakar masa kiss a hannun sa

Murmushi kawai yayi mata yana shafa kanta be ce komi ba

Sai ta ɗago ta kalle shi tace, “Kakus baka da wani abun motsa baki ne a ɗakin?”.

Dariya yayi yace, “ina dashi mana, Jiyan nan Dadyn ku ya kawo min kayan marmari suna nan a Fridge ki ɗauka”.

“To bari in duba in gani ko akwai abinda zan iya sha”. Tayi maganar tana tashi tsaye tayi wajen Fridge ɗin, lemo ɗaya kawai ta ɗauko ta dawo ta zauna

“Shikenan abinda zaki sha?”.

“Eh. Ya ishe Ni wannan kar in shanye maka”.

“Haba dai, tunda Ɗana yake so yasha ai babu damuwa, sai in saka ma yanzu a ƙaro miki idan kika shanye”.

Shiru tayi kawai bata ce komi ba taci gaba da ɓare lemon da hannu

Shi kuma Kaka sai yayi ta mata surutu duk a kan cikin nata, da idan ta haihu in dai na miji ne sunan sa za’a saka

“Kawai ina jin ka ne Kaka, amma ba daɗin zancen nake ji ba, kayi shiru don Allah”.

“Yo ko laifin Baban shi zai shafe shi ne?”

Ɓata fuska tayi tana tashi tsaye tace, “Ni dai na tafi. Sai anjima”. Bata jira cewar sa ba ta fice abun ta

Shi kuma sai kwaɗa mata kira yake yi yana faɗin “ta dawo”.

Dawowa tayi ta leƙo daga bakin ƙofan tace, “Kakus bazan sake zuwa ba yanzu sai kana ajiye min abun daɗi, tunda Babyn naka abun da yake so kenan”.

Dariya yake yi yace, “to shikenan, ai kuwa zan riƙa ajiye miki kar ki damu”.

“To byee na tafi zan dawo anjima ai”. Tayi maganar tana dariya ta fice

Shima still dariyan yake yi zuciyar sa cike da farin ciki. “Usman da baka yi wannan abun tsiyan ba ai da farin ciki na sai yafi haka, amma kuma ka rigada ka ruguza komi, duk da haka dai ina da rabon ganin ɗan ku tare, ko ba komi dole wata rana ku dena nuna wa junan ku ƙiyayya tunda kuna da ɗa a tsakani”.

 

 

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

Tunda yaje Office ya kasa sukuni, duk abinda yake yi tunanin sa na gare ta, babu abinda ke dawo masa a rai sai abinda ya faru tsakanin su ɗazu, shiyasa abu kaɗan sai murmushi kamar wani zautacce, sosai yake kewar ta tabbas yana buƙatar matar sa a halin yanzu, meyasa baza ta yafe mishi komi ya wuce ba tunda ya bata haƙuri? Tun sanda abun nan ya faru a ƙauyen Baba Jaure yake dana-sanin furucin da yake mata na ɓatanci, da kuma kallon ta da yake yi a matsayin mazinaciya, haƙiƙa yayi dana-sani mara misaltuwa, wanda har ya ɗau alƙawarin duk wanda ya kawo mishi pictures ɗin nan da ya sake dagula mishi lissafi a kanta dole ne sai ya fuskanci wulaƙanci me muni, bazai taɓa barin ko waye bane sai ya ɗau mata fansa, idan da ba shi ne aka ba wa hotunan ba shikenan za’a riƙa tunanin tabbas ita ce.

 

Shiyasa sai da yabi diddigin inda aka yi hoton, a can ne ya samu bayani a kan mutumin da ya zo aka yi mishi hoton, dayake sananne ne tunda ya saba zuwa wajen ana mishi, da ya kamo shi yaci uban sa kwanan sa biyu a rufe yana gana mishi azaba, inda kuma yayi mishi barazana a kan sai ya danƙa shi wajen hukuma muddin be nemo mishi waɗanda suka saka shi aikin ba. Wannan dalilin ne da yasa aka kamo su Ayush. Shi mutumin yayi musu wayau ne ya jawo su hotel ɗin a kan “baya ta haihu..” da suka zo kuma sai ya bugar da su daga ƙarshe ya ɗaure su….

 

Ajiyan numfashi Usman ɗin ya sauke yana ɗaukan wayan shi ya soma laluben numbobi, yana son jin muryan ta ko zai samu sukuni amma be san wa zai kira ba, be da Numban ta bare na Maman ta da zai iya kira, nan dai ya tuna dana Fadil sai ya danna mishi kira

Koda ya ɗauka sai yace mishi, “ya je ya kai wa Nafeesa wayan”.

Jiki na rawa Fadil ya soma inda-inda don be gane da wacce yake nufi ba

To abun ne ai yazo musu da sabon salo tunda dai kowa da Ɗahira yake kiran ta, babu wani me kiran ta da sunan ta, shiyasa wani lokacin ma suke manta sunan ta, amma shi da iyayi irin nasa dole sai ya bambanta kanshi da kowa

“Ka kai mata wayan ka tsaya kana min shirme”. Yayi maganar cike da ɗan tsawa

“Yaya ai ban gane wacce kake nufi ba”.

Tsaki yaja yace, “stupid.. Ɗahira”.

“Ai Ina school ban dawo ba..”

Be jira sake jin wani zancen nashi ba ya katse wayan yana ajiye wa cike da takaici, ba don ya so ba yaci gaba da aikin da yake yi, sai kuma ya tashi ya fice ya tafi duba patiens ɗin da yake da su.

 

 

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

Da dare Kaka ya sanya a tara mishi jama’an gidan, bayan kowa ya hallara sai yayi musu magana a kan “sakin da Usman zai yiwa Ɗahira ne, yanzu ya kamata ace ya bata takardan ta kowa ya huta”.

Big Dady yace, “nima nayi mishi maganar jiya, amma dayake shi fitsararre ne yake faɗa min maganar ma da bazai yiwu ba, wai “bazai sake ta ba a bar shi da matar shi”.

Kaka kallon Usman ɗin yayi da kanshi ke ƙasa. yace, “ai sakin ta ya zama dole kuwa Fodio tunda mu baza mu sake mata tilas ba, tunda ita take buƙatar a raba auren nan babu me matsa mata ta zauna da kai a wannan karon, tun farko abun da muka hango muku kenan sha’awar zaman ku tare har muka haɗa ku, amma kuma sai kayi watsi da umarnin da muka baka kaƙi mana biyayya, hakan yasa ka je ka gallaza mata son ranka, sai ga shi Allah ba azzalumin bawan sa bane kaima yanzu kana son zama da ita, to, ai ita ba jaka bace da zamu sake baka kaje ka sake maimaita mana abinda kayi a baya, maganin kar ayi kar a fara Allah ya haɗa kowa da rabon shi kaji ko? Yanzu ga ta nan ba sai ma ka sha wahalan rubuta wa ba sai ka sake ta kowa yaji, yaron ka kuma idan Allah ya sa ta haifa maka zata raina har zuwa yayen shi kafin ta baka kayan ka”.

“Kaka kuyi haƙuri da abinda nayi muku a baya wlh nayi nadama bazan sake ba, bazan iya sakin ta ba saboda ina son zama da ita, ko don abin dake cikin ta be kamata a raba mu ba..”

“Abun cikin ta ɗin uwaka? Usman kar ka ja mu kai maganar nan kotu wlh, idan har Daughter Bata yarda zata koma ba rashin sakin ta bazai hana mu baka ita ba, sai dai mu je kotu a raba”. Cewar Big Dady kenan cike da haushin Usman ɗin

Tashi Usman ɗin yayi yana faɗin, “Allah na rantse bazan sake ta ba, duk abinda za’a yi sai dai ayi baza a mayar min da ɗana Maraya ba”. Daga haka ya fice da sauri daga parlour’n ranshi a ɓace

Su kansu maganar Usman ɗin ta ba su dariya, wai Maraya

Abba ne yace, “abi komi a sannu babu maganar zuwa kotu, saki ne dai dole ya bata idan ya gaji bata koma ba”.

“To amma ai ita daughter za’a cuta zata yi ta zama da auren shi a kanta”.

Kaka yace, “kowa ya tashi ya tafi in yaso sai muci gaba da tattaunawa da ku ko?”.

Duk fita suka yi suka bar su Big Dady.

 

⚫⚫⚫⚫⚫

“Ba dai kuka kike yi ba Ɗahira?”

Ɗago kai tayi tana kallon Maman nata, sai ta saka hannu ta soma share hawayen ba tare da ta iya magana ba

Ajiyan zuciya Aunty Amarya ta saki tana zama kana tace, “Ɗahira ba na son kina saka damuwa a ranki, Ni abinda nake gani kiyi haƙuri ki koma gidan Usman tunda ya nuna yayi nadama yanzu, har ga Allah ina ganin soyayyar ki a idanun shi, tunda kuma ga abinda yace kiyi haƙuri ki yafe mishi ki koma ki zauna a ɗakin ki, hakan zai fi miki sutura ke da abinda ke cikin ki, Allah ma ana mishi laifi ya yafe bare ɗan Adam”.

“Mama ko na yafe mishi ni bazan iya zama dashi ba wlh, har yanzu ina ganin abubuwan da yayi min na kasa manta wa, shiyasa nake jin bazan iya sake zama a ƙarƙashin sa ba, idan har na koma gidan shi bazan taɓa jin daɗin zama dashi ba domin zuciya ta cike take da tsanar shi”. Ta ƙare maganar cikin kuka

“To ki yi shiru ai ba na ce ki koma bane tilas, babu wanda zai tilasta miki Ɗahira sai da yardan ki, Kinga ga Abbun ki can na Kira na bari inje, ki dena fa kukan nan na faɗa miki”.

 

“To”. Ta amsa ta tana koma wa ta kwanta

Ita kuma Aunty Amarya fita tayi, ganin babu shi a Parlour sai ta wuce ɗakin ta, a nan ta ganshi zaune a kujera, ta ƙarisa ta zauna tana cewa, “Ga Ni Abbun Zulaiha. Ina ɗakin Ɗahira ne muna magana”.

“Maganar me kuma?”

“Ka san bazai wuce na abinda ya faru ba, ta koma ɗaki tana ta kuka tunda abun kuka ba ya mata kaɗan ita”.

“Allah Sarki Mama na. Ni a gani na gwara ta bar abun nan ya wuce ta koma ɗakin ta hakan zai fi ai, tunda ɗan Adam ajizi ne Allah ma muna mishi laifi ya yafe bare mu Mutane, yanzu maganar da muka gama kenan da su Baba, Amma shi sam Yaya Noor yaƙi yarda”.

“Haka ne. nima abinda nake sanar mata kenan, tunda ka ga Usman ya furta hakan tabbas yana ƙaunar ta yanzu, kuma na tabbata duk abinda yayi mata a baya bazai sake aikata wa ba”.

Murmushi Abbu yayi yace, “ai maganar ƙauna ma bata taso ba yanzu tunda ga rabon jika mun samu, dama mata da miji sai Allah tunda ga shi a faɗan nasu ne suka sama mana jikalle”. Ya ƙare maganar yana dariya

“Kai Abbun su har da kaima?” Aunty amarya tafaɗa tana dariyan itama

“Eh mana. To ai gaskiya ce, kawai dai abinda zamu yi muyi ta tausan ta har ta amince ta koma, kin san ɗiyar taki halin ki ta biyo, wlh kuna da sauƙin kai, tunda ke kika manta abubuwan da ya yiwa ɗiyar ki kike son ta koma, itama na tabbata da ace zamu bata umarnin koma wa baza ta taɓa mana musu ba, sai dai na san hakan da cutarwa gwara mu lallaɓa ta har sanda taji don kanta zata iya koma wa, idan kuma mijin nata shi yayi ƙoƙarin shawo kanta shikenan, amma kar mu goyi da bayan ta wajen raba auren nan tunda be da wani amfani, Allah shi yaga abinda ya gani har ya kawo wannan cikin a tsakanin su, ni ina ga shi zai zame musu alkhairi”.

“Haka ne Abbun su, to Allah yasa mu dace”.

“Amin ya Allah. Yanzu ki kira min ita in tambaye ta kan wayan da tace take so”.

“Ka bari sai gobe mana tunda naga yanzu kamar ta kwanta ai”.

“To Allah ya kai mu, bari in duba Bilkisu ina dawowa”. Yayi maganar yana tashi ya fice.
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR’S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER’S ASSO*📖
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA’S FAMILY*_

 

 

*EPISODE Sixty Five*

Usman dai tunda ya fita gidan shi ya wuce kai tsaye, gaba ɗaya duniyar tayi mishi zafi ransa duk ya gama ɓaci, shi a ganin shi don yace “bazai sake ta ba ne”. Suke mishi haka, to su riƙe ta kar su barta ta dawo, shi kuma wlh bazai sake ta ba har sai sun gaji sun kawo ta da ƙafafuwan su, barin ma ƙasar zai yi tunda don suna ganin shi ne shiyasa suke mishi haka, tunda ya basu haƙuri ya ce zai zauna da ita meye kuma laifin shi a nan? Ko albarkacin cikin shi ai be kamata su raba auren ba. Wani zuciyar tashi tace, “amma ai kaima baka kyauta ba, ko kai ne a madadin ta zaka guje wannan auren, tabbas ka bata wahalan da in dai tana da hankali dole ta guje ka gaba ɗaya”.

“Amma to ai na bata haƙuri, kuma na gane kuskure na bazan sake ba”. Yayi maganar a fili yana hawaye. Sai ya mirgina kwanciyar sa yaci gaba da tunanin zucin shi dake ƙara mishi ƙunci da raɗaɗi, duk tunanin Ɗahira ya addabe shi ya rasa ya zai yi

Yau dai rana ɗaya ya tashi domin neman agaji a wurin Allah, abin da be taɓa yi ba, domin idan har ka ga Usman ya tashi da dare yana Sallah to tabbas yana cikin ƙunci ne sosai, yau dai ga shi haka ya tashi yayi ta jero salloli yana neman biyan buƙata wajen Allah, da kuma neman ya yaye mishi duk damuwar shi, Allah ya gani yanzu yana ƙaunar Ɗahira, yana jin son ta kamar ya kashe shi yanzu, be san ya aka yi ya faɗa wannan mugun son nata ba,  shiyasa gaba ɗaya sallan duk a kanta yayi

Be dena ba sai da kusan uku tayi, sai ya jira har aka yi sallan asuba yayi a wurin don bazai iya zuwa Masallaci ba, yanzu ɗin barci yake ji sosai, shiyasa yana gama wa ya kwanta.

Be tashi ba sai wajen goma na safe, wanka yayi ya shiga kichen daga shi sai gajeren wando ya haɗa tea ya zauna a Parlour Yana sha, duk gaba ɗaya tunanin sa ya tafi ga hukuncin da zai yanke

Bayan ya gama ya tashi ya mayar da kofin kichen, ya wanke kafin ya koma ɗaki, kayan shi ya soma haɗa wa a Trolly har ya gama, sannan ya shirya cikin ƙananan kaya farar riga me wuyan V da gajeren hannu, sai wando jeans blue colour crazy, gaban mirror yaje ya gyara gashin kansa kafin ya feshe ko ina na jikin sa da turare, ya ɗauki agogo ya ɗaura a hannun sa sannan ya zira takalman sa sandal da ya zaro su daga ƙasan gadon shi, ya ɗan share kasancewar da akwai ƙura yaja Trolly ɗin sa ya fito, sai da ya kashe komi kafin ya fice, kai tsaye wajen motan shi ya nufa yana shirin saka wa a Boot

Hajiya da ta fito ta ƙaramin ƙofan gidan su ta hange shi, kwaɗa mishi kira tayi tana nufo shi

Sai ya juyo yana kallon ta fuska babu fara’a, gajeren tsaki yaja yana ƙarisa tusa Trollyn cikin Boot ɗin sannan ya rufe, ya nufe ta ba tare da ya amsa kiran nata ba

“Ina zaka je haka da kaya? Ba dai tafiya zaka yi ba a kan maganar nan?”

Sai da ya ƙumshe baki ya saki iska kaɗan tare da sake haɗe fuska yace, “tafiya zan yi Mom, idan sun gaji da jira na sai su aiko min ita”.

“To a tunanin ka kana ganin hakan shi ne maslaha a wurin ka? Kar ka manta ita yarinyan nan ba ƙaunar ka take yi ba, memakon ka zauna ka gyara alaƙar ku a wajen ta shi ne kake son sake jagula lissafin ko? Kai a tunanin ka su Dadyn naka za su aiko maka da ita? to, ka dawo hankalin ka tun wuri ka sauya tunani ba na son shashanci kaji ko. Ka je Dadyn ka na kiran ka”. Daga haka ta juya ta wuce ba tare da ta jira jin ta bakin shi ba

Shi kuma yana tsaye ƙiƙam yaƙi jirga wa sai bin bayan ta da yake yi da kallo, har ta ƙule wa ganin shi be motsa ba, sai ma ya saka hannayen sa cikin aljihu yaci gaba da tsayuwar sa a wurin. Sai da ya mula dan kanshi kafin ya taka ya nufi hanyar da ta biyo, kai tsaye Part ɗin su ya wuce ya shiga da sallama

Big Dady na zaune a kujera yana kallon labarai a t.v, dayake yau Saturday ne basu da aiki, duk da ba hutu suke ɗauka ba amma ba sa zuwa Hospital ɗin sai yamma ko kuma duk sanda suke so, idan kuma ana buƙatan su suna zuwa su duba mara sa lafiya su dawo, sun dai ɗauki weekend ranan hutun su ne sai an buƙace su tunda akwai likitoci kala-kala.

Amsa mishi sallaman yayi ba tare da ya kalle shi ba

Shi kuma ya tako ya zauna a ƙasa jikin kujeran dake kallon wanda Big Dady ya zauna, be ce komi ba ya sadda kansa ƙasa

“Ina zaka je da Mom ɗin ka ta ganka kana saka akwati a mota?”

Shiru yayi ya kasa magana

“Da kai nake magana”.

“I’m traveling”.

“Ok to bani takardan nata tunda dai baza ka tafi da auren ta a kanka ba. I spoke and remained silent”.

“Dady don Allah kuyi haƙuri ku yafe min don Allah Dady, wlh ina ƙaunar ta yanzu bazan iya rabuwa da ita ba, ku sake bani dama Please zan je in nemi afuwar ta, na yarda idan har ba ta ƙauna ta zan rabu da ita dan girman Allah Dady kaji?” Ya ƙare maganar da rarrafo wa gaban Dadyn yana me riƙe mishi ƙafa hawaye na tsiyayan mishi

Duk ya kashe mishi jiki shiyasa yayi shiru kawai yana kallon shi, har ga Allah yana ƙaunar su ci gaba da zama a tare amma kuma shi yana yin hakan ne domin amsar mata haƙƙin ta, Usman ya zalunta mata be kamata ayi shiru a bar shi haka ba, sai dai tunda ya ce haka; zai ba shi dama ya je ya nemi amincewar Ɗahiran, idan har ita taga zata iya zama da shi shikenan, idan kuma tace a’a dole ne sai ya amsar mata takardan sakin ta

“Ya isa haka”. Yace dashi ganin yanda yake ta mishi magiya

Shiru Usman ɗin yayi kanshi a ƙasa amma hawaye be dena fita a idanun sa ba

Numfashi Big Dady yaja kafin yace, “tun farko Usman ba ka jin magana, mu iyayen ka mu zaɓa maka abinda muke ganin ya dace da kai amma ka nuna mana bamu isa ba, yanzu wa gari ya waya? Wlh Allah ne ya saka mata tun yanzu domin ka gane ɗan Adam ba abun wulaƙanta wa bane, a matsayin ta na ƙanwar ka jinin ka amma ka gallaza mata wannan azabar. Dama ɗaya tak zan iya baka kaje ka nemi amincewar ta, idan har ta yarda zata koma wajen ka falillahil hamdu, idan kuma tace a’a ka san baza mu taɓa mata tilas ba, ka tashi kaje”.

Lumshe idanun sa yayi jin abinda Dadyn yace, zuciyar sa cike da murnan da be san iyaka ba yace, “thanks Dad”. Sannan ya miƙe zai fice

“A haka zaka fita baka share hawayen naka ba?”

Ɗan juyo wa yayi yana murmushi ya saka hannu ya share hawayen, yana cire hannun sa suka haɗa ido da Hajiya dake bakin ƙofan ɗakin ta tana mishi murmushi, still shima murmushin yayi zai juya ya fice

Sai Big Dady ya sake cewa, “ina kuma zaka je baka yi Breakfast ba? Dawo ka karya zan aike ka Office ka ɗauko min saƙo dana manta da shi”.

Usman ɗin be ce komi ba ya juya ya nufi dainning ɗin, bakin sa bazai iya faɗin “a ƙoshe yake ba” shiyasa kawai yabi umarnin sa ya zauna don yaci abinda zai iya

Hajiya ƙarisa wa tayi ta zauna tana haɗa mishi Breakfast ɗin tana tsokanar shi

Shi kuma murmushi kawai yayi, da yaga zata haɗa mishi da tea yace, “ta bar shi ya sha”.

Big Dady dai na jin su be ce komi ba yaci gaba da kallon shi.

 

Har sanda Usman ɗin ya gama ya dawo wurin shi ya amshi keey ɗin office ɗin, tare da faɗa mishi abinda zai ɗauko mishi, shi kuma ya wuce ya fice

Bazai iya tafiya be ga fuskar Ɗahira ba shiyasa kai tsaye ya wuce Part ɗin su.

 

Duk suna zaune a parlour’n ban da Ɗahira dake kichen tana ma kanta faten tsaki da take sha’awan sha

Tana jin muryan Usman ɗin sa’ilin da yayi sallama yana gaishe da su Abbu, sai da gaban ta yayi muguwar faɗi tayi saurin dafe ƙirjin ta tana ƙwalalo ido, “kar dai ace wannan ɗan iskan ya zo maimaita min abinda yayi min ne jiya?” Tayi maganar a fili tana sauke numfashi kamar wacce tayi gudun tsere

Jin kamar hiran su da Abbu ne yasa ta matsa da sauri ta leƙa kanta, ta hange shi yana zaune a kujera sai dai ya juya wa ƙofan kichen ɗin baya, sai Umma da Fadil a wajen, Aunty Amarya kuma ta tashi ta wuce ɗaki

Ajiyan zuciya ta sauke sai kuma taja gajeren tsaki ta wuce taci gaba da abinda take yi, sai dai duk bata da cikakken nutsuwa domin har ta yanke shawaran zama a kichen ɗin idan ta gama sai tasha faten nata tunda taji kamar be da alamar tafiya. Ta gama kenan tana zuba wa a Plate sai ganin shi tayi a kichen ɗin, kafin ma ƙamshin sa ya shigan mata hanci har ta ga dogayen ƙafafun sa a gaban ta, da sauri ta ɗago kai tana ware manyan idanun ta a kan shi da suka yi fari tarr babu ko kwalli

Wanda kallon nan ba ƙaramin sagar mishi da jiki yayi ba, sai da ya wani lumshe idanu ya buɗe su daƙyar ya sake aro jarumta wajen kallon ta

Ita kuma tuni ta janye idanun ta ta sake haɗe rai tana zazzare idanun, a ranta tana mamakin rashin kunya irin na Usman, ko dama haka yake? Ya zai shigo mata kichen ya baro su Abbu a Parlour? tana son mishi magana amma kuma haushin sa yasa tayi gum don taga iya gudun ruwan shi. Tana gama zuba faten a Plate ɗin ta rufe sauran a tukunya ta sunguma na Plate ɗin zata fice

Sai yayi saurin saka hannu ya damƙe nata yana matsa wa gaban ta, cikin sanyin murya idanun sa na kanta yace, “Nafeesata babu gaisuwa haka ake yi? Ko don na zama maƙiyin ki shiyasa har yanzu bazan samu arziƙin da za’a iya gaishe Ni ba? Domin ki fa nazo”.

Da ya san yanda take ji da kasancewar su waje ɗaya da ko kaɗan be zo inda take ba, gaba ɗaya har raunin ta yana shirin fito wa sai dai sosai tayi Jarumtar dakewa, daƙyar ma take iya numfashi saboda yanda take ji a jikin ta, saurin janye hannun ta tayi ba tare da ta kalle shi ba tayi ƙofa ta fice da sauri

Shi kuma yabi bayan ta tana saka ƙafa a ɗakin ta shima yana saka wa

Dayake tuni Abbu ya fice wajen Kaka shi da Fadil, wannan dalilin ne ya samu ya biyo ta kichen. Ita kuwa Umma tana zaune ta hange su sun wuce ɗin, sai ta kama haɓa kawai ta saki wani ashar da ya suɓuce mata bata shirya ba.

 

 

Ɗahira dake shirin zama a ƙasan ɗakin sai ganin mutum tayi a gaban ta. Da sauri ta ajiye Plate ɗin tana faɗin, “lafiya wai? Ka san dai be kamata kana biyo NI ɗaki na ba ko?”

“A kan me? Ba ke matata bace?”

Tsaki taja tana cewa, “ka dena ma tunanin wannan tun tuni na tashi a matsayin matar ka, Please Malam fitan min a ɗaki kaji ko?” Ta ƙare maganar tana nuna mishi hanya fuskar ta a tamke kamar bata taɓa sanin mutunci ba

Sai yayi guntun murmushi ya kawo hannu zai shafa fuskar ta tayi saurin matsar da fuskar, “hmm kin yi min kyau sosai Sweety, meyasa kike son min tsaki ne ki dena kin ji ba na so? Kuma na zo ganin baby na ne ko kar in zo?”

Jin haka sai tayi shiru ta zauna ta saka hannu a faten ta soma sha a hankali, duk da a takure take amma bata ko nuna hakan ba a fuska, nuna wa ma tayi tamkar ma babu shi a wurin

Shi kuma sai bin ta yake yi da kallo yana sake ƙare wa jikin ta da ya tafi dashi kallon tsab

Dayake tana sanye da riga da skert ne ƴan kanti Robber, rigan me wuyan V irin nasa fara, amma nata kamar vest ne don ya fi taushi sosai, sai skert ɗin me santsi ja da Flower’s da aka yi da kalan fari, kanta sanye da hula na kayan

Sosai yanda yake bin ta da kallon yake shiga har can cikin jikin ta, gaba ɗaya ta rasa sukunin ta, duk yanda taso ta daure amma ta kasa sai ta ɗago kai tana bin shi da kallon harara cike da haushin kama sa da tayi yana mata wannan kallon maitan

Shi kuma sai a lokacin ya wani ajiye numfashi yana ware idanun sa da suka ƙanƙance suka soma sanja kala

Ranta duk a ɓace tace, “don girman Allah ka fita ka bani wuri kar wani yayi tunanin wani abu kake yi a nan, tunda kai baka da kunya Ni ina dashi”.

Sai kawai taga ya zauna a gaban ta, daƙyar ya furta, “nima zan sha”. Kafin ma ta ba shi amsa ya tsulma hannu a ciki ya soma kaiwa baki

Tsaban takaici da ya cika ta sai ta yunƙura zata tashi

Yayi saurin janyo ta ta koma ta zauna daɓas

Da kallo ta bi shi kamar zata yi kuka jin sai da ta bugu da ta koma ta zauna. “Wai kai ba ka iya sukuni ne sai kayi mugunta?” Tayi maganar a fusace tana banka mishi harara

Be ce mata komi ba illa ci gaba da yayi da shan faten, sai dai yana riƙe da hannun ta be saki ba

Fushi tayi ta kasa motsa wa bare tasha faten zuciyar ta sai tafarfasa take yi da haushin Usman ɗin, gaba ɗaya ya takura mata har hawaye sun soma taruwa a idanun ta, sosai ta kumbura tayi fam jira kawai take yi ta mishi bala’i, amma ganin yaƙi ce mata uffan ya zaƙe sai shan faten shi yake yi ya bar ta da tsinkewar yawu, sai da ta kalle shi kafin ta kalli Plate ɗin, sai ta saka ɗaya hannun nata ta janye tana faɗin, “wannan ai mugunta ne, ya za’a yi ka zauna kana shanye min faten ko kai ne me cikin?”

Sai kawai taga ya saki dariya yana kallon ta

Itama sai ta bi shi da kallon tana sake haɗe rai, idan yana dariya sosai yake mugun kyau sabida ba kasafai yake yin sa ba, shiyasa yake fita daban, ita kanta sai da yayi mata kyau, amma kuma tsaban neman magana irin nata sai ta dangwali faten ta shafa mishi a fuska babu zaton sa, a ranta tana faɗin, “yau zan yi maganin ka sai nayi maka rashin mutunci zaka fita a harka ta”.

Zaro idanu kawai yayi ganin abinda tayi mishi

Ita kuma tuni ta sake dangwalo wa zata shafa mishi a ɗaya kumatun

Sai ya riƙe hannun nata caraf ya haɗa su duka biyun, lokaci ɗaya ya haɗe rai yana shirin magana

Ta riga shi da faɗin, “wlh idan baka fita a nan ɗakin ba sai nayi maka wanka dashi gaba ɗaya a jikin ka, dama ai Ni ƙazamiya ce ko ka manta? So zan nuna maka ƙazanta na yanzu wlh, sakar min hannu”.

Murmushi yayi yace, “to kuwa zaki bi jikin nawa ki lashe shi tass, idan har kin shirya Bismillah”. Ya sakar mata hannun yana bin ta da kallo

Sai ta miƙe kawai tana shirin fice wa

Ya janyo ta ta faɗa jikin sa sai ga ta ɗare-ɗare a cinyan sa

“Ina zaki je kuma baki lashe abinda kika saka min ba? Wlh sai kin kwalɓe shi ko kuma in miki abinda baki yi expecting ba”.
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR’S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER’S ASSO*📖
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA’S FAMILY*_

 

 

*EPISODE Sixty Six*

“Baza kiyi abinda nace miki ba? Ina nan fa dake har sai kin saka harshen ki kin shanye shi, idan kuma ba haka ba kin ji dai Aunty na kiran ki ko. Kuma kin san ƙarshe zata shigo ne tunda zata yi tunanin na tafi, tazo ta ganki a cinya na”. Ya ƙare maganar da dariya

Ita kuma ta sakar mishi harara kamar zata yi kuka, ga shi tana son ta tashi amma babu hali ya kanannaɗo hannayen sa ta bayan ta ya riƙe ta gam, gaba ɗaya jikin ta yanzu babu ƙarfi sai rawa yake yi, ko kaɗan baza ta iya jure abinda take ji ba sai ta kalle shi kamar zata yi kuka tace, “dan Allah ka bar Ni..” sai tayi shiru ta kasa ƙarisawa

Lumshe idanun sa yayi yana matso da faukar shi kusa da nata, sannan ya buɗe yana kallon ta a hankali yace, “lashe min”.

Lokacin har hawaye sun soma zubo mata tace, “a’a bazan iya ba”.

“To Ni zan iya, ba na son ina ganin hawaye a fuskar ki, sabida yanzu Ni ba mugu bane a gare ki kinji ko?” Ya ƙare maganar da kai nashi bakin babu zato ya soma lashe mata hawayen

Da saurin ta ta janye fuskar baki na rawa tace, “meye haka wai? Ni fa..” sai ta kasa ƙarisawa saboda yanda jikin ta ke rawa ganin ya sake manna ta a jikin shi, da ƙarfi ta furta, “na shiga uku na”. Sai ta fashe mishi da kuka tana son ƙwace kanta da ko ta halin ƙaƙa

Shi kuwa be saurare ta ba yaci gaba da kai bakin sa jikin ta duk inda yake so

“Wayyo Allana.. wayyo Allana Yaya Usman dan girman Allah ka dena na tuba Dan Allah wani zai zo”. Tayi maganar tana kuka sosai gaba ɗaya ta rasa nutsuwar ta

“Dalla matsoraciya wlh ba komi zan miki ba, ƙamshin jikin ki nake so sai mu gaisa da Baby ko?”

Bata kai ga magana ba suka ga an buɗe ƙofan, gaba ɗayan su ƙofan suka bi da kallo suna bin Umma da ido kamar yanda itama ta hangame baki tana kallon su

Usman janye nashi idanun yayi tuni ya sake manne Ɗahira a jikin sa, har da ɗago ta ya matso da ita sosai jikin sa

Umma tace, “to Ɗahira fito Maman ki na ta faman kira kin zo kin maƙale a jikin miji”.

Da sauri Ɗahiran ta kalle shi kamar zata nitse a wajen, still tana hawaye cikin sanyin murya tace, “don Allah ka sake Ni bari inje kaji?”

Idanun sa da suka kaɗa ya buɗe yana kallon ta yace, “to zaki dawo?”

Kan ma ya ƙarisa ta soma gyaɗa mishi kai da sauri

Murmushi yayi mata yana sakar mata kiss a laɓɓa, sannan ya sake ta

Sai a lokacin Umma ta juya ta tafi tana buga salati tare da tafa hannu, “yau mu dai mun shiga uku a gidan nan muna ganin iskanci ƙuraratan”.

Ɗahira kuwa tuni ta fito ta wuce ɗakin Maman ta da sauri

Shima a lokacin Usman ɗin ya fito sabida ya san tunda ta tafi baza ta taɓa dawowa ba, yana jin abinda Umma ke faɗi be ce komi ba ya saka kai ya fice

Sai ta sake sakin salati tana cewa, “amma wlh Usman ba ka da ɓurɓushin kunya ko kaɗan, ka zo har sashin mu kace zaka nemi matar taka don jaraba? Bari dai Abbun su ya shigo dole fa a san abun yi, don bazai mayar mana da gida kantin karuwai ba, idanun mu suyi ta ƙone wa a banza”.

 

 

********

Ita kuwa Ɗahira da ta shiga ɗakin Maman ta, sai ta fashe mata da kuka tana faɗin, “wlh Mama zan bar gidan nan bazai yiwu Yaya Usman yazo yayi ta..” sai tayi shiru tana sake fashe wa da kuka tsaban takaici ya cika ta

Aunty Amarya kamar bata san komi ba tace, “wani Usman ɗin ba tun ɗazu ya fice ba?”

“Ina fa Mama, ɗaki na ya shiga, don Allah Mama Ni dai zan bar gidan nan bazan zauna kullum yana biyo NI ba”.

“To ki je ina kenan?”.

Sai ta matso hawaye tana cewa, “zan je gidan Kakalle (Baseera ƙanwar Kaka mahaifiyar Umma) ko kuma gidan Aunty Zulaiha ne”.

“To kema kin san bazai yiwu ba tunda ba lafiya ne dake ba ko?”

“Amma Mama ai su ma za su iya kula dani, kuma naji sauƙi wlh babu abinda ke min ciwo”.

“To Ni dai ban aike ki ba, idan kin tambayi Abbun ki ya barki shikenan”. Inji Aunty Amarya tana ci gaba da ninke kayan da take yi

Ɗahiran bata ce komi ba ta wuce Toilet ta wanke hannun ta tare da fuskar ta, sannan ta fito ta haye kan kujera ta kwanta har da juya bayan ta, take nan komi ya soma dawo mata, sai tayi saurin buɗe idanun ta tana jan dogon tsaki, jinta take yi kamar yana jikin ta har yanzu

Aunty Amarya dai na jinta bata ce komi ba taci gaba da abinda take yi.

 

Sai ga Abbu ya shigo ɗakin

Aunty Amarya ta amsa mishi sallaman da yayi

“Ah ah Mamana lafiya kika zo nan kika kwanta?”

Da sauri ta tashi tana faɗin, “lafiya lau Abbu, dama kai nake jira”.

“To gani Mamana Allah yasa dai ba wani abun bane?” Yayi maganar yana zama a gefen ta saman kujeran

Murmushi tayi tace, “dama zan tambaye ka ne ina son zuwa gidan Kakalle ko gidan Aunty Zulaiha in Yi kwana biyu”.

Ɗan ware ido yayi yace, “kai kai ban aike ki ba, ke da baki da lafiya?”

Cikin marairaice fuska tace, “Please Abbu wlh na warke kaji?”

“To shikenan, amma sai dai ki je gidan gwaggon nawa domin gidan Zulaiha yayi nisa da yawa, gwara can zata fi kula dake”.

“Yauwa na gode Abbu bari inje in shirya yanzu”. Tayi maganar cikin farin ciki tana tashi ta fita da sauri

Aunty Amarya tace, “ai da baka barta ba”.

“Kin san ba na hana Mamana abinda take so, ki barta taje hakan ma zai sa ta samu hutu kwana biyu, kin san idan tana nan zata ce zata koma wajen akin ta, amma yanzu can ba lallai Gwaggo ta barta ba, zan ma kira ta a waya in faɗa mata”.

“Haka ne”. Cewar Aunty Amarya tana tashi da kayan da ta gama ninke wa ta nufi wardrobe ɗin ta don zuba wa

Shi kuma tuni ya tashi ya fice.

 

******

Ɗahira da ta fita sai ta wuce wajen Kaka ta sanar mishi zata je gidan Hajiya Baseera tayi kwana biyu

Shima sai da yayi mata faɗan, “bata da lafiya be kamata taje ba”.

Amma takalallame shi da daɗin bakin ta tuni ya yarda, har yana bata saƙon gaisuwa

Fadil shi kuma nan ya maƙale mata sai ya bi ta, inyaso zuwa anjima shi zai dawo

Tace mishi, “ya biyo ta su je”.

Part ɗin su suka wuce, suka shirya, ita da kayan ta a ɗan jaka suka fito, Ali drever’n su shi ya tafi kai su tunda Aunty Amarya ta ce kar ta sake tayi tuƙi.

 

 

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

“Suhail kira min Auntyn ka a ɗaki”. Cewar Abba da ya fito daga ɗakin shi yana saɓa malin-malin

“To Abba”. Inji Suhail ɗin yana tashi da sauri bayan ya ajiye remote ɗin hannun shi

Shi kuma ƙanin shi me suna Abdulra’uf da suke kiran sa Abdul; da sauri ya tashi ya nufi wajen Abban yana faɗin, “Abba na nima zan je”.

Hannun sa ya riƙe suna zama, da murmushin sa yace dashi, “a’a Abdul, ai ba nan kusa bane inda zamu je, kuma ɗaurin aure zamu je. Ka bari dai zan yi muku tsaraba ko?”

Gyaɗa kansa yayi cike da murna

“To kaima kira min Maman ka a ɗaki”.

Abdul ɗin na tafiya, shi kuma Suhail ɗin ya fito da kuka, Direct wajen Abban ya nufa dake tambayar shi “me ya faru dashi?”

Cikin kuka ya sanar mishi “Hajja ce ta duke shi”.

“To kayi shiru kaji? Kayi haƙuri baza ta sake ba”. Abba yafaɗa duk ransa babu daɗi yana shafa mishi kai

Aunty Jamila da ta fito daga ɗaki ita da Abdul ɗin tace, “ah ah kukan me kake yi kai kuma?”

Be iya ce mata komi ba tunda kukan yaci ƙarfin shi

Sai ta kalli Abba tana ce mishi, “har ka fito Alhaji?”

“Eh na fito, ki rarrashe shi don Allah bari in zo”. Yace hakan yana tashi ya wuce ɗakin Hajja Fatu. Yana shiga ya ganta kishingiɗe tana sakace. Da kallo ya bi ta ranshi a ɓace yace, “Wai Fatima me kike so ki zama ne? In aiko yaro ya kira ki shi ne kika dake shi?”

Kallon shi tayi itama da fuska a haɗe tace, “kai baka da ƙafan zuwa ka kira Ni ne sai dai ka aiko min agola ɗaki? To wlh duk ranan da ya sake shigo min ɗaki; wlh tallahi sai na farfasa mishi jiki”.

“To idan kin fasa don Allah, tunda zaman lafiya ne ba kya so, to, ina dai-dai dake kar ki fasa kinji? Sannan idan kin so yau ma kar in dawo in tarar baki yi abinci ba, wlh ranki idan yayi dubu sai ya ɓaci, duk iskancin dake kanki zan sauke miki”. Yana gama faɗar haka ya fice da sauri

Tsaki ta ja ƙasa-ƙasa tace, “kaɗan ma ka gani, ai ka auro wacce zata yi maka amma ba Ni ba, daga yau ita sai ta ɗauke maka duk abinda nake maka”. Sai ta sake jan dogon tsaki tana ɗaukar wayan ta ta hau kiran layin Hajiya Sa’ima.

 

 

********

Abba na fita sallama yayi wa Aunty Jamila ya fice

Ita kuma sai taja yaran nata suka shige ɗaki tunda babu abinda za su ɗauka a parlour’n, dama haka suke yi sabida baƙin halin Hajja Fatu.

 

Tana shiga Abba ya dawo da ninyan ɗaukan keey ɗin motan shi, ɗakin sa ya shiga ya duba be gani ba, sai ya tuna jiya a ɗakin Hajja ya sauka, kuma ya tabbata ya bar shi can, sai ya wuce can ɗin don ya ɗauka, amma yana shirin buɗe ƙofan ya jiyo maganar ta, dayake ba a hankali take maganar ba kasancewar ta san ya fita

A dai-dai lokacin take faɗin, “Ni ba wannan ba Hajiya Sa’ima, maganar wancan matsiyaciyan da nake son a raba ta da Usman, gaba ɗaya na dena runtsa wa tunda yaron nan ya fara nuna yana son komar da ita ɗakin shi, kenan buri na bazai cika ba na mayar da ita bazawara?..” sai tayi shiru tana sauraron Hajiya Sa’iman. Kafin kuma tace, “so nake yi yanzu mu koma wajen Malamin nan ya yi min aikin da ya fi wancan, wlh muddin ina numfashi nayi alƙawari bazan taɓa bari A’isha da ɗiyar ta su yi rayuwar jin daɗi ba, ada naci wannan alwashin bare yanzu da suka yi min sanadin mutuwar ɗana da nake matuƙar so, a kan shi duk na rasa wata ƙima ta a gidan nan, shikenan min ɗana na miji amma na rasa shi, dole ne in sake sanya mummunan gaba da tsana a tsakanin su, ta yanda ko ya ƙi ko ya so sai ya sake ta, su kuma burin su na son su ga sun daidaita su bazai taɓa cika ba, har ita Hajiyan ma wannan karon sai na haɗa ta da Malam tunda ta nuna yanzu ta dawo da son tsinanniyar….”

 

Daga nan Abba ya dena ji ya juya da sauri jikin sa na rawa, gaba ɗaya jin sa yake yi a wani irin yanayi, cike da ɓakin ciki da tsantsan ɓacin ran da kalaman Hajjan suka saka shi, sai ya wuce kanshi tsaye ɗakin Kaka

Inda suna zaune su uku, shi da su Abbu suna zaman jiran Abban ya zo su wuce ɗaurin Aure.
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR’S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER’S ASSO*📖
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA’S FAMILY*_

 

 

*EPISODE Sixty Seven*

Yanda ya shigo musu ranshi a ɓace sai duk suka hau tambayar shi

Nan yake sanar musu da komi abinda yaji Hajja Fatu tana faɗi

Gaba ɗaya su kansu hankalin su ya tashi, “shin tun yaushe Hajja take wannan ɗabi’ar ba tare da sun sani ba? A ganin su dai suna zaune lafiya da Aunty Amarya, me ya jawo wannan mummunan tsanar?” Duk kan su sun shiga damuwa da rashin jin daɗin abun

Sai Kaka yace wa Abban, “ya je ya kira wo ta”.

Abba juya wa yayi ya koma can Part ɗin nashi, inda ya cidda ita tana wayan har yanzu bata gama ba, tsamo-tsamo ya kama ta tana wayan kansacewar ya bankaɗo ƙofan ne ya shigo

Sai duk ta daburce ta rikice ta rasa inda zata saka kanta. Yanda ta ga idanun sa sun kaɗa sun yi ja sai ta sake daburce wa, domin ta sadakar ma ya gama jin ta, tana shirin mishi magiya har ta duƙa a ƙasa

Sai ya dakatar da ita daƙyar ya furta, “ki ajiye kalaman ki ki biyo NI mu je”. Yana faɗa ya fice ya bar ta a wannan mawuyacin halin

Bata da tsimi bare dabara dole ta tashi tabi bayan shi zufa na keto mata, ta rasa ma wani addu’a zata kama tayi sabida tsaban tashin hankali, idan kuwa tabbas Abba ya ji abinda take faɗa ai ta kaɗe, shikenan asirin ta ya tonu, “wayyo Allah na na shiga uku Ni Fatu”. Bata sake rikice wa ba sai da taga sun shiga ɗakin Kaka

Kaka ransa a ɓace yace, “ashe ke mutumiyar banza ce Fatima? Duk Nasihan da muka yi miki ashe baki saduda kin zama mutumiyar kirki ba? Duk abinda ke faruwa tsakanin Usman da Nafeesa ashe duk ke ce kika jawo? Kina kuwa so ki gama da duniya lafiya? Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un.. har wajen Boka kike zuwa a kan kin ga kin muzguna wa bayin Allan nan wato? Shin ina hankalin ki yaje Fatima? Wlh yau ina tirrr da halin ki, ina tirrr da kasancewar ki ɗiya a wuri na”. Sai ya kalli su Big Dady yace, “kai ku kira min gaba ɗaya mutanen gidan nan domin kowa ya san me ke faruwa, wannan ba abun ɓoye wa jama’a bane tunda abinda kika zaɓa wa kanki kenan, har ita Ihsan ɗin ku kira min ita”. Kaka ya ƙare maganar cikin matuƙar ɓacin rai da zafi

Su kansu duk sun sha jinin jikin su ganin yanda Kaka ya nuna tsantsan fushin sa, abun da rabon shi da shiga irin wannan halin su kansu baza su iya tuna wa ba, ko kaɗan be da nuna fushi sosai ko da kuwa ranshi a ɓace ne, bare kuma duk sun san yanda yake son Fatima sosai, shi ne silan auren ta da Abba, don shi ya zaɓa mishi ita domin su cika burin su na son haɗa yaran su aure shi da Abokin shi kuma aminin shi Haidar, wato mahaifin ita Hajjan

Shiyasa ita kanta ta gama ruɗe wa sai kuka take yi, bata taɓa jin cewa akwai ranan da asirin ta zai tonu ba nan kusa sai yau, kuma bata taɓa tunanin zata yi nadama da sauri haka ba, gaba ɗaya jikin ta rawa yake yi ta san yau ta ƙare mata, raguwar igiyar auren nata ma duk za su ƙare.

 

A cikin mintoci har sun gama taruwa gaba ɗaya, har da su Shakira da aunty Zainab da kuma Yusra, Aunty Zulaiha CE kawai babu ita sabida ta fi su nesa shiyasa ba a kira ta ba, sai kuma Hajiya Hannatu mahaifiyar ita Hajjan da kuma Hajiya Baseera mahaifiyar Umma, tunda har ita an kira sun dawo ita da Fadil, Ɗahira kuma na can

Sai Usman shima da sai yanzu ya dawo daga aiken da Big Dady yayi masa.
 

Nan  Kaka ya sake sanar musu da duk abinda Hajja Fatu tayi, inda ya ɗaura da cewa, “ba don ƙasa ta rufe min Aboki na ba; wlh wlh baki isa ki sake zamar min a gida ba, duk da ke ɗiyar ƙanwa ta ce yau da sai na raba auren ki da Babana, sai dai ina tuna girman Amintar mu da Haidar, wanda ina ganin kamar na ci amanar shi ne idan yau na wulaƙanta ki, Fatima kin ci arziƙin ke ɗiyar aboki na ne ba ɗiyar ƙanwa ta ba, shiyasa a yau zan bar ki kici gaba da zama da ahali na, idan kin tuba don kanki, idan kuma kina ganin hassada dake cikin ranki zai kai ki kici galaba a kan A’isha da ɗiyar ta, to, mu zuba ga ki ga duniyar nan, Allah yana kallon ki, shi ne kuma yake nuna miki ishara a duk abinda kike yi, idan zaki hankalta tun yanzu ya kamata ki yi tunda ga shi Allah ya ɗauke miki ɗan ki ɗaya a kan wannan baƙin halin naki, kaɗan ma kika gani, bazan hana Babana ɗaukan mataki a kanki ba, sai dai ban yarda ya sake ki ba sabida albarkacin wanda kika ci, amma ki sani wannan shi ne damar ki ta ƙarshe Fatima”.

“Yaya wlh ban ji daɗin abinda kayi ba, ka bar ta ya sake ta shi ne kaɗai maslaha, zaman Fatima a gidan nan be da wani amfani, tunda ita abinda ta saran ma kanta kenan, wlh kin yi asara kin kuma bani kunya, bazan miki baki ba amma kaɗan kika gani, kuma in Allah ya yarda yanzu zaman Usman da Ɗahira aka fara, duk sharrin da kike bin A’isha da Ɗahira sai dai ya koma miki, da Allah suka dogara kuma baza su taɓa taɓe wa ba”.

Gaba ɗaya parlour’n tsit suka yi suna sauraron faɗan Hajiya Hannatu da take tayi ba sassauta wa, in  banda kukan Hajjan babu abinda ke tashi

Daga baya ma Hajiya Hannatun ita da Hajiya Baseera sukai ta mata faɗan tare, sai da suka wanke ta soso da Sabulu

Kaka ne ma ya tsayar da su ya ce, “ya isa haka”.

Sai a lokacin Abba yayi magana, inda ya ce, “daga yau ya soke aikin Hajja Fatun baza ta sake zuwa aiki ba ko da kuwa wani asibitin ne, kuma ya raba ta da Hajiya Sa’ima, idan har ta sake mu’amala da ita ya sani, to, daga ranan shi ya yanke alaƙar aure da ita”.

Babu wanda ya hana shi kuma a kan hukuncin nasa, gani ma suke yi kaɗan yayi mata, domin ba don da Kaka ya hana sakin ta ba; da tuni ta tsufa a gidan su

Haka kowa ya tafi yana tirr da halin Hajja Fatu, inda ita kuma ta sha kunyan duniya

Usman haka ya tafi duk ranshi a ɓace, ya so ya tanka amma ya san sai dai ran kowa ya ɓaci a wurin, shiyasa yayi shiru. Shi ya ɗauki su Hajiya Hannatu ya tafi da su, domin so yake yi idan zai kai Hajiya Baseera ya gano Ɗahira tunda ya ji suna faɗin, “tana can”.

 

 

********

Ɗahira na zaune a Parlour tun fitan su Hajiya Baseera ta tashi ta ɗauko lemo Mountain Dew ta hau sha, sai da ta kusa shanye wa kafin taje ta ɗauko mata madara na gari ta sake sauran lemon a Cup, sai ta dinga zuba madaran tana juya wa har sai da yayi kauri sosai, kafin ta saka cokali ta hau shanye wa

Dama kafin su fita ita da Fadil sun girka faten dankali sun ci tare, suna gama wa ne aka aiko kiran Hajiya Baseera shi ne suka koma tare.

 

Tana gama shanye wa sai da ta lanɗe kofin tass kafin ta kai kichen ta dawo ta kwanta a doguwar kujeran ta, kamar zata yi barci sai kuma ta sake jin kwaɗayin girka shinkafa, haka ta wuce kichen ta haɗa shinkafan ta me manja da ya ji daddawa da yaji zaƙwai, ta dawo Parlour ta ware ƙafafu tayi ta tusa wa a cikin ta, duk da ta ƙoshi amma tsananin kwaɗayin girkin ya hana ta sukuni, haka take ci tana jan majina saboda azaban zafi dana yaji, amma bata saurara mishi ba har sai da ta kusa cinye wa tass ya rage saura loma biyu

A lokacin ne su Usman suka shigo parlour’n da sallama, gaba ɗaya kallon ta suke yi ganin yanda take ta faman haɗa gumi ta warware ƙafafu Plate a gaban ta tana ta siɗe yatsu

Itama kallon su tayi, lokaci ɗaya ta haɗe rai ganin har da Usman, sai tayi saurin janye nata idanun tana saka hannu da sauri ta kwashe sauran ta cinye tana miƙe wa tsaye, da Plate ɗin ta wuce kichen ta je ta ajiye Sannan ta je Toilet, sai da ta wanke hannun ta da baki sannan ta ɗauraye fuskar ta kafin ta fito tana zama can kujeran dake kallon wanda suka zauna a tare, tace, “har kin dawo Kakalle?” Tayi maganar idanun ta a kan Hajiya Baseeran

Ita kuma sai da ta sauke numfashi kafin tace, “iy na dawo, na tsaya ina ganin ikon Allah ne Ɗahira, yanzu ba da zan fita ba kika gama cika cikin ki da abinci ba?”

Ɓata fuska tayi tace, “Kakalle wlh kamar ban ci komi bane, kuma na ga ai kun daɗe da fita”.

“Eh na ga alama ai, tunda ga shi nan daƙyar kike numfashi”. Hajiya Baseeran ta faɗa tana kallon Ɗahiran dake ta faman gyara zama ta gagara zama waje ɗaya don daƙyar take iya nishi, sai jan skert ɗin ƙasa take yi saboda ya tamke mata cikin

Shi Usman ma dariya ta ba shi, shiyasa ya kasa jure wa, domin tunda ya shigo da kallo kawai yake ta bin ta yana ganin ikon Allah

Ganin yana murmushi sosai sai ta tsargu ta kalle shi ta balla mishi harara tana tashi zata wuce ɗakin da ta sauka

“Ah ah Ina kuma zaki je? Ko sannu ma baki yiwa mijin naki ba kuma Kinga tare muka shigo?”

“Ina zuwa Hajjaju bari in cire wannan skert ɗin ya matse min ciki”. Tayi maganar tana shige wa ɗakin

Dariya Usman yayi yana kallon Hajiyan itama da take taya shi, yace, “wai lafiyan wannan yarinyan ƙalau, ko dama haka masu cikin suke da cin tsiya tun ba’a kai ko ina ba?”

“To ai ka san kowa da irin nashi, wani sai yana ƙarami ne ka ga ya fi cin abinci, wani kuma sai ya girma, to ƙila nata haka yake, ga ta nan fa har raman nata ya shige, har ta fi kyan kallo ma yanzu wlh, da kam kamar a hure ta, ko kai ai zaka fi jin daɗin ta a haka mata tubarakalla”.

Murmushi kawai yayi yana zaro wayan sa cikin aljihu jin an yi masa Text.

 

Lokacin Ɗahira ta fito ta sauya shigan ta cikin doguwar riga fara me gajeren hannu, tana da taushi sosai don kamar na Barcin nan ne, sai hula da ta sanya a kanta shima fari me tuntu a tsakiyar kai. Zama tayi tana faɗin, “me ya faru da aka kira ki Kakalle? Allah yasa dai lafiya?” Tayi maganar hankalin ta duk a kanta tana jiran jin abinda zata faɗa, don dama har da jiran ta take yi domin taji abinda ke faruwa, tunda ta so ta bi ta tace mata, “a’a baza ta je ba”. Kuma ta san ba lafiya ne ba, ba don haka ba da tuni ta shige ɗaki domin baza ta dawo ta zauna ba tunda ta ga da Usman suka zo

“To gagarumin abu ne dai ya faru, yau dai asirin Fatu ne ya tonu, ayi yarinya sam ta fita daban da ƴan uwan ta, wannan wani irin tsana ne haka?” Nan dai ta kwashe komi ta sanar mata, kana ta ƙara da faɗin, “Ni ina ga Ɗahira ba laifin mijin ki bane, a gani na gwara ki koma gidan ki ku ci gaba da zama tunda gaskiya ta bayyana, duk abinda yayi miki ba a cikin hankalin shi bane, taya ma kina a matsayin jinin sa zai nuna miki wannan rashin imanin? kema zaki gane tabbas ba a hankalin shi yake ba, abun da nake roƙon ki da shi ki manta komi ya wuce domin ki ba ma mara ɗa kunya, duk sharrin da take bin ki da shi ki nuna mata Allah ya fi ta, kar ki taɓa bata damar da zai saka ta cin ma burin ta”.

Ɗahira da take ta faman kuka tun jin labarin komi, sosai zuciyar ta ke mata zafi, “meyasa Hajja Fatu ta tsane ta? Me tayi mata a rayuwa?” Abinda take ta ambata a ranta kenan tana ƙara Volume ɗin kukan ta

Hajiya Baseera rarrashin ta ta hau yi tana faɗin, “Ke yanzu ba kuka zaki yi ba, yanzu kuka ya ƙare tunda kin gano musabbabin abinda ke faruwa, mijin ki kawai zaki riƙe gam kinji ko?”

“Amma Kakalle ai tun kafin Hajja Fatu ta shiga tsakanin mu ya tsane Ni, meyasa ya tsane Ni tun ina ƙarama ta? Ki tambaye shi meyasa? Ina son in sani. Idan har be faɗa min ba bazan taɓa ganin farin shi a idanu na ba”. Ta ƙare maganar tana kuka sosai

Usman da duk zuciyar sa ta karye da kukan da take yi, cikin raunin murya na wanda juriya ne kaɗai ya hana shi shima ya koka yace da ita, “na san nayi miki laifi Ɗahira amma kiyi haƙuri kinji? bani da hujjar da zan iya kare kaina a wajen ki, amma ina roƙon ki da ki sake bani dama, ki manta komi ya wuce, zan gyara Laifuka na nima, zan kuma mantar dake duk wani baƙin ciki na da kika ƙunsa, zaman mu tare ne kaɗai zai sa ki yafe min sannan ki manta komi a rayuwar ki, ina son ki Ɗahira! Ina matuƙar ƙaunar ki! bazan iya rabuwa dake ba ki yafe min kinji?”

Yanda Kalaman sa suke ratsa mata kunnuwa dole ne zuciyar ta ta karye, tana ji a ranta tabbas ta yafe mishi, sai dai baza ta iya buɗe baki tayi masa magana ba, baza ta iya ce mishi ta amince da zama da shi ba, tana ganin ya dace ta sake yarda dashi a karo na biyu? Har yanzu zuciyar ta bata gama yarda da shi ɗari bisa ɗari ba, tana ga kamar yaudaran ta yake yi, mutumin da ya tsane ta tun tana tsumman goyo har girman ta; kuma yanzu ya dawo ya ce yana son ta? Duk bakin da ya furta tsana ko da ya dawo ya furta so; to, kar ka taɓa amince wa da shi, domin ƙarya yake yi akwai manufa a zuciyar sa. sai ta sake fashe wa da kuka tana tashi da gudu tayi hanyar ɗaki ta shige

Da kallo suka bi ta har Usman ɗin domin ya kasa ma motsa wa, “Why can’t she forgive him?” Ya tambayi zuciyar sa, sai kawai ya lumshe idanu hawayen ciki suna sauka a dandamalin fuskar sa

Hajiya ce tace mishi, “ya bi ta ɗakin ya rarrashe ta, tunda shi saɓo-tumaki ne da zai zauna yana mata kuka, kar ma ya fito ɗakin ba tare da sun daidaita ba”. Sannan ta tashi ta wuce nata ɗakin

 

Shima kuma sai ya miƙe yabi bayan Ɗahiran, sai da ya tura ɗakin ya shige kafin ya rufo ƙofan har da saka keey.

 

 

 

_Nima dai na ware tunda an bar Ni a parlour._ 🙄
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR’S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA’IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER’S ASSO*📖
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA’S FAMILY*_

 

*EPISODE Sixty Eight*

A taƙaice please. Kuyi haƙuri sabida abubuwa sun yi min yawa dole zan taƙaita labari na daga nan, ba wai don ya ƙare ba, amma dai na san kowa na son jin ƙarshen labarin shiyasa zan taƙaita.

An kai ruwa rana kafin Ɗahira ta yarda ta koma gidan Usman, a lokacin cikin ta ya shiga wata na biyar ne

Sai da aka sake shagulgula isu-isu ƴan gidan kafin ta tare, inda aka gyara mata ko ina

A ranan dai Usman yayi kwanan farin ciki, yau ga shi ga Ɗahiran shi cikin sukuni, domin ta rigada ta sallama tuni ta yafe mishi komi ya wuce, tunda ta koma kuma biyayya take mishi kamar yanda aka santa, hakan ya ƙara jawo shaƙuwa me ƙarfi da ƙauna a tsakanin su

Inda Usman ɗin ya so su wuce TURKEY yayi hutun amarcin sa da ya ɗauka

Amma Kaka ya hana, ya ce, “dole sai ta haihu”.

Ba don ya so ba ya haƙura

Ita kanta Ɗahiran ma ba ta son zuwa sabida idan har suka je rayuwar da tayi a can ne zai dawo mata, amma bata ce mishi komi ba.

 

Cikin ta na wata shida Aunty Zulaiha ta haifi ɗan ta na miji, an yi suna inda yaron yaci sunan mahaifin mijin ta Aliyu, za su na kiran shi da Aiman.

 

Fannin Hajja Fatu kuwa don dole tayi ladab yanzu, domin ba kaɗan ba Abba yake gasa mata aya a hannu, duk wani jin daɗi yanzu yayi ƙaura a wajen ta.

Matsalan da Shakira take fuskanta wajen mijin ta Sahabi, zama dai ya ƙi daɗi, domin ashe har yanzu be dena bata ƙwayoyin hana samun ciki ba, ko ɓatan wata bata sake yi ba, sai da dubun shi ta cika ashe Allah ya bata ciki, daga baya da ya gane sai ya je ya siyo magani ya bata, ciki ya zube lafiya lau, duk a tunanin ta Allah ne ya ƙaddara hakan, domin yanda Sahabin ya nuna damuwarsa tsantsa dole ta cire tunanin komi, sai daga baya kawai ta kama shi yana waya da abokin shi, inda yake faɗa mishi komi “shi ne yake bata maganin hana ɗaukan ciki, don shi wlh be ƙaunar haihuwa yanzu sai nan gaba,” sanadin da aka yi ta fitina kenan, daga ƙarshe dai aka raba auren dole duk da rai be so ba, amma su Big Dady sun ce, “dole sai ya sake ta, ya je can ya auro wacce ba ta son haihuwar”. Ita kanta Shakiran hakan ya fi mata, domin burin ta yanzu kenan ta samu ciki, tunda ga shi duk ƴan uwan ta da yaran su, Fadila ma yanzu tana ɗauke da nata cikin, sai dai be kai wancan matsala ba, haka ma itama Aunty Zainab.

 

Ɗahira ta haihu lafiya ta samu Baby Boy, inda yaro yaci sunan Abbun ta, sunan Kaka kenan, Al’ameen, za su kira shi da sunan A’sim

An yi shagulgula an gama lafiya.

 

Sai kuma a lokacin ne aka yi bikin Firdausi ita da sauran ƴan uwan ta jikokin Granny, sun je sun kwana sun raɓashe.

 

Sai da Ɗahira tayi arba’in kafin suka tafi Turkay, satin su uku a can suka wuce Saudiya suka yi umra, sannan daga can suka wuce Dubai, sun yo wa ƴan uwa siyayya kala-kala inda suka dawo gida. Zaman su sai son barka, domin ƙauna tsantsa suke nuna wa junan su, gefe kuma ga ɗan su dake ta wayau tubarakalla.

 

Kwatsam sai aka wayi gari Kaka be da lafiya, ciwon kwana ɗaya don har ya samu sauƙi ma, ashe ciwon ajali ne, inda ya ce ga garin ku nan, mutuwar da ya girgiza ahalin nan gaba ɗaya, wanda sun daɗe basu manta bawan Allan nan ba.

 

Bayan wasu shekaru, yanzu Ɗahira har ta sake haihuwar ɗiyar ta mace me sunan Hajiya, Asiya, suna kiran ta da Huda.

 

Itama Fadila yanzu tana goyon ɗan ta na biyu ne me sunan Abbun su, duk ka yaran ta maza ne. Yusra ma ta sake haihuwar har da tsohon ciki yanzu. Shakira ta samu miji ta yi aure, sai dai a Zaria yake, kuma yana da mata ɗaya da yara biyu, suna zama lafiya babu wani hayaniya tunda yana da shi, kuma ya barta tana ci gaba da aikin ta. Itama Sa’adatu yanzu tayi aure a can Legos ɗin, har ta dawo da Zahra da tayi wayau Masha Allah, kamannin ta da uban ta sai ƙara fito wa yake yi, duk wanda ya kalle ta sai ya tuna da Baffa, Allah sarki rayuwa kenan.

 

*TAMMAT BILLAH… ALHMADULILLAH.. ALHMADULILLAH.. ALHMADULILLAH… Duka-duka a nan na kawo ƙarshen littafi na, abun da na faɗa dai-dai Allah ya bani ladan, kuskuren da nayi kuma Allah ya yafe min*

 

_saƙon gaisuwa ga masoya na bazan taɓa manta ku ba, na gode sosai da nuna min ƙauna da kuka yi, Allah ya bar mu tare har a aljanna, Love You fisabilillahi.. taku JIKAR LAWALI_ 🤩👄💘❤️💓

 

*DEDICATION to the family of GOMA’S Family, and to every family, joy and happiness be with them. Happy family❤️👨‍👨‍👧‍👧👩‍❤️‍👨*

 

_Mu haɗu a sabon book ɗina me suna *ABUL KHAIRI (LABARIN DEEBIZAH RETURN)* kar ku bari a baku labari._

 

 

 

 

*ƊANƊANO*

 

*ABUL KHAIRI*

Lumsassun idanuwan sa da suke cike taf da barci ya ware su a kan ta

Tana kwance gefen sa, hannun ta ɗaya saman ƙirjin sa da babu riga, barci itama take shararawa wanda yayi wa cuty face ɗin ta kyau matuƙa.

 

Idanu kawai ya zuba mata cike da takaicin ganin ta kusa dashi, sake ware idanuwan sa da suka sauya kala zuwa ja yayi, ya mayar dasu kan hannun ta dake ƙirjin sa, dogon tsaki yaja kafin ya saka hannayen sa biyu ya riƙo hannun nata ya sauke kan jikin sa ya yarfar dashi

Wanda hakan sai da yasa taji zafi sosai cikin barcin ta, babu shiri ta farka tana zare idanu ba tare da ta motsa ba

Shi kuwa tuni ya ma sauka akan gadon, yana gyara rigan zuwa jikin sa, tare da ɓame bottles ɗin gaban rigan da suke a buɗe gaba ɗaya

Kallon sa kawai take yi tana karantan yanayin sa, sai da ta gama ƙare masa kallo har ya gama abinda yake yi, ya zari makulle zai fice ba tare da ya sake kallon ko inda take ba, ai kamar ƙiftawar ido ta dira daga kan gadon tasha gaban sa da sauri, har da saka hannu tana kare sa alamun bazai wuce ba

Sauke idanun sa yayi akan ta cikin ɓacin rai da ya nuna a face ɗin sa, sai dai be iya ce mata komi ba illa kallon ta da yake yi yana sake haɗe rai

Ita kuma yatsina kyakykyawar fuskar ta tayi, kafin ta kafa masa manyan idanuwan ta tace, “Wai ina zaka je ne ka bar Ni bayan kasan me ya kawo Ni wajen ka? Bie babu inda zaka je wlh sai mun tsayar da maganar mu, tunda ka ƙi ɗaukar waya ta to na biyo ka”. Sai kuma taja numfashi tana ci gaba da faɗin, “Wlh idan har baka yarda da buƙata ta ba Bie, na rantse da Allah zan nemi mafita kamar yanda na faɗa maka, kasan kuma Ni ɗin ina da waɗanda suke jira na in Kai musu kain…”

“ZIYA..” Yafaɗa da ƙarfi cikin tsananin ɓacin rai da ya ninka wanda yake ciki, lokaci ɗaya farar fuskar sa ta sauya kala tayi jazur, haka ma jijiyoyin kansa sosai suka fito raɗau

Ƴar siririyan dariya ta saki tana kallon yanda gaba ɗaya ya sauya lokaci ɗaya, hakan kuma sosai ya faranta mata don tafi son yayi zuciya yabi ra’ayin ta, cikin yatsina tace, “kar ka yimin tsawa Bie, kasan bazan ɗauka ba, kuma kabar tunanin bazan iya rabuwa da kai bane, wlh akan haka sai mu raba hanya..”

Damtsen hannun ta da ya damƙe ƙam, shi ya hana ta ƙarisa maganar ta, domin sosai zafin ya shige ta

Matso da fuskar sa kusa da nata yayi yana huci, idanun sa sun sake yin jazur fiye dana da, cikin amon muryan sa me haɗe da fushi yace, “Wlh kinji na rantse miki idan har kika ba ma wani daman riƙe hannun ki; ba shiga jikin ki ba ma, wlh wlh sai kinyi dana-sanin sani na a rayuwan ki! bazan hana ki rabuwa dani ba, sannan bazan hana ki aikata duk abinda kike so ba, fine ki aikata kinji ko?” Yaƙarike maganar da girgiza ta yana ware mata jajayen idanun sa, sai kuma ya janye ta daga gaban sa ya nufi ƙofa dasauri ya fice

Duk da ba wani jan ta yayi ba sai da ta faɗi ƙasa, sabida rashin ƙwarin jiki, ƙofan tabi da kallo cike da tsoro a ranta, babu shakka tasan Kishin da yake mata zai iya aikata komi, idan tace komi tana nufin komi zai iya yi a kan ta, sai dai kuma ba ta tunanin zata nuna tsoro ko gajiyawa da buƙatan ta, domin baza ta zauna dashi ba ya biya mata buƙatan ta ba, sannan kuma ya hana ta zuwa inda za’a biya mata, tabbas zata ci gaba da tunzura sa don ganin ta cin ma burin ta

Itama miƙe wa tayi ta zura Takalman ta, sannan ta ɗau gyalen ta; ta rataya a kafaɗa tafice dasauri.

 

▪️▪️▪️

Motan sa ya gangarar da ita gefen titi, babu abinda zuciyar sa ke yi sai suya, iska kawai yake faman fesar wa daga bakin sa yana riƙe da sitiyarin motan, ya rasa meke masa daɗi a lokacin, sabida kalaman ta daga jiya zuwa yau sai kai komo suke masa a rai

Hannu ya saka ya soma hargitsa gashin kansa cike da tsagwaron KISHI dake cin sa, sai kuma ya kwantar da kansa jikin kujeran yana lumshe kyawawan idanun sa, ya jima ahaka be ɗago ba illa numfashi da yake sauke wa yana faman ci je leɓe, daga ƙarshe kuma yayi wa motan keey ya fige ta da gudu yayi gida.

Gate man na buɗe masa Gate ɗin gidan ya kutsa motan ciki, a parcking space yaja birki yana kashe motan, sai dai be yi yunƙurin fitowa ba illa ma gyara zaman sa da yayi yana dafe kansa.

 

▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️

Eyeglasess ɗin fuskarta ta sake gyara masa zama akan cikakkiyar kamilalliyar farar fuskar ta, murmushi yalwace a fuskar ta take kallon su tana magana, “Ba na son ku je ku zauna acan har in kira waya, idan kuwa kuka bari na aikata hakan, to Ni da ku ne, don kun san bazan sake barin ku zuwa ba”.

Da sauri Batool ta dafa gwiwowin ta, har da ranƙwafo da kanta tana faɗin, “Wlh Mamy baza mu daɗe ba, idan muka je ma muna gaishe ta da jiki zamu dawo”.

Jinjina kanta Mamy tayi kafin ta maida idanun ta kan Maimuna tace, “je ki kira min Aƙilun zan ba sa saƙo ne”.

Da sauri Maimuna ta tashi tafice daga ɗakin Mamyn, da gudu ta nufi hanyan parlour, ta buɗe ƙofan fita tana shirin saka kai waje taji tayi karo da mutum, kafin ta tabbatar da wanda suka ci karon, sai ji tayi an janye ta da ƙarfi an yi wurgi da ita gefe, ai babu shiri ta saki siririn ƙara jin ta faɗa a saman hannun ta, da sauri ta ɗago kanta tana bin sa da kallo idanuwan ta cike fal da hawaye

Shi kuwa be ma bi ta kanta ba, ya taka yashige fuskar sa a ɗaure tamau kamar be taɓa dariya ba

Bata dena kallon sa ba har ya shige ɗakin Mamy, sai taja majina tana matse idanunta hawayen ciki suka samu daman zubo wa, jiki babu ƙwari ta tashi tafice don kiran Aƙilu drever’n su.

 

Tura ƙofan yayi da sallama ciki-ciki

Mamy da Batool suka amsa mishi duk kan su suna juya wa ga ƙofan, dasauri Batool ta miƙe tanufi ƙofan tana mishi sannu da zuwa

Be amsa ta ba, ita kuma tafice abun ta

Tako wa yayi ya zauna a kan kujeran dake cikin ɗakin, hakan yasa yake fuskantan Mamy dake zaune gefen gadon ta tana kallon sa

“Baba na lafiya kuwa?” Ta tambaye shi cike da kulawa sabida sauyawan da tagani a tattare dashi

Sakin faukar sa yayi sosai yana ƙoƙarin dai-dai ta kansa, cikin ƙwaƙulo murmushi yace da ita, “Mamy lafiya ƙalau me kika gani?”

Hakan yasa tasaki murmushi wanda ya zame mata ɗabi’a, koda yaushe fuskar ta a sake yake cike da annurin fara’a, sake tsare sa da idanu tayi tace, “Baba na kana son ɓoye min halin da kake ciki ko? Jiya haka ka wuni da ɓacin rai, yanzu ma ga shi ka dawo a yanayin, but kana son ɓoye min, Why?”

Sosa Kansa yayi cike da basarwa yace, “Mamy babu komi fa, ki yarda dani, idan da akwai ke ce ta farko da zan sanar ma wa”.

Mamy ta murmusa cike da ƙaunar ɗan nata, shi dai daban yake cikin ƴaƴan ta, koda yaushe a zurfin ciki yake, idan har abu ba yayi tsamari bane, ba ya iya fitowa fili ya sanar musu su da suke iyayen sa, ya dinga ƙumbiya-ƙumbiya dashi kenan a ransa, sai dai wuni yana cikin ƙunci da ɓacin rai, wanda hakan ya jawo ba kasafai zaka ga yana shiga cikin jama’a yana walwala ba..

 

“Mamy har yanzu Abba be dawo bane?” Maganar sa ta katse mata guntun tunanin ta

“Be dawo ba, lafiya dai ko? In ce dai ba wani abun ka samo zaka bashi Ni ka hana Ni ba?”. Tayi maganar cike da barkwanci

Hakan ya saka shi sakin yalwataccen murmushin da yafito da jerin haƙoran sa

Sanyi taji aranta ganin ya ɗan saki ransa fiye da ɗazu ɗin, hakan yasa taci gaba da jan sa da hiran tsokana don dai tadawo mishi da walwalan sa

Shiyasa sau tari yafi ƙaunar kasancewar ta kusa dashi fiye da kowa a duniyar nan, tabbas uwa daban ce, a duk sanda yake cikin matsala, ita ke fara gane damuwar sa fiye da kowa dake gidan, that’s why yake tsananin ƙaunar mahaifiyar shi fiye da komi da kowa dake cikin duniya.

 

▪️▪️▪️

Koda Maimuna tadawo kiran Aƙilu drever, zaman ta tayi a Parlour batare da tayi yunƙurin komawa cikin ɗakin Mamyn ba.

Tana zaman itama Batool tafito tazauna gefen ta tana tambayan ta, “shin ta kira Aƙilun?”

Kafin ma taba ta amsa Aƙilu ya shigo yana baza idanuwa cikin parlour’n, hannun sa ɗaya riƙe da aswakin da yacire daga bakin sa ya ƙariso cikin parlour’n, ya zube ƙasa yana faman washe baki tare da yiwa Batool kirarin da ya saba

Ita kuwa nan ta biye masa suna kwasan dariyan Aƙilun daga ita har Maimuna, kasancewar sun fi saba wa da Batool ɗin, kullum suna cikin surutu da junan su, ita kuma Maimuna koda yaushe dama nata ido ne idan suna yi, sai kuma ta dara idan abun ya bata dariya, idan kuma sun sako ta sai ta tsulmiya baki, dayake ita ɗin ba me yawan surutu bane, bata da hayaniya ko kaɗan.

 

Lokacin ne Mamy da ABUL KHAIRI suka fito daga ɗaki

Kai tsaye ABUL KHAIRI hanyan ɗakin sa ya wuce ko kallon inda suke be yi ba

 

Mamy ne taƙariso cikin parlour’n ta zauna tana amsa gaisuwar Aƙilun, sannan ta kalli Maimuna tace, “Maimuna tashi ki haɗa wa yayan ku abincin sa ki kai masa”.

Amsa mata tayi da “Toh”. tana miƙe wa tsaye, ta kalli Batool tana mata alama da ido tabiyo ta

Maƙe kafaɗa Batool tayi tana mata dariya ƙasa-ƙasa

Sai Maimunan ta marairaice fuska tasoma tafiya, har da haɗe hannayen ta biyu alamun roƙo

Amma ƙiri-ƙiri Batool taƙi motsa wa, sai ma gwalo da tabi ta dashi

Babu yanda ta iya haka tanufi kichen jiki a sanyaye, tasan halin Yayan nasu yanzu abu kaɗan zaka yi masa kuskure yaci uban ka, bare ma shi da ya tsane ta fiye da kowa dake gidan, ko kaɗan bata san meyasa ba ya ƙaunar ganin ta ba, shiyasa ba ta son ma a aike ta wajen sa bare tayi kuskuren abun da zai haɗa su.

 

Ita Mamy tuni ta maida hankalin ta kan Aƙilu tana bashi saƙo, sai kuma tajiyo tana kallon Batool ɗin tace, “ke baza ki je ki shirya bane kin zauna? Ai kuwa idan Abban ku ya dawo ya hana ku fita babu ruwana, ki zauna kasa kunne kina ji na kar ki tashi ki wuce”.

 

Ai kuwa dasauri Batool ɗin ta tashi tayi hanyan ɗakin su tana faɗin “wlh Mamy Ni ban ma ji me kuke cewa ba”.

Itama Mamy bata tanka ta ba tamayar da hankalin ta ga Aƙilu tana sallaman sa.

 

Lokacin ne Maimuna ta fito daga kichen riƙe da Faranti a hannun ta, kanta tsaye tanufi ɗakin ABUL KHAIRI ta soma Nocking a bakin ƙofan, sai dai har ta gaji babu amsa, dole ta haƙura ta tura ƙofan ta shiga da sallama.

Yana zaune a bakin gadon sa idanun sa kafe a kan ƙofan, ashe duk yana jin Nocking ɗin but yaƙi amsa wa

Shiyasa tana shigowa idanun su suka haɗe cikin na juna, saurin sad da kanta ƙasa tayi gaban ta na matsanancin faɗuwa, ko kaɗan ba ta ƙaunar ta haɗa idanu dashi sabida kwarjinin da yake mata, shi kaɗai ne mutumin da idan suka haɗa idanu dashi take jin daban a cikin rayuwan ta, tana shiga wani yanayi da har yanzu ta kasa fassara shi

Jiki a sanyaye ta ƙariso cikin ɗakin, tanufi gefen sa inda Centre table ke ajiye gaban gadon da yake zaune, akai ta ajiye farantin muryan ta na ɗan rawa ta soma gaishe shi, tare da son isar da saƙon abincin daga Mamy

Amma kuma ko ci kanki be ce mata ba

Don haka ta juya da ninyan fice wa batare da ta kalle sa ba, sai jin saukar dakakkiyar muryan sa tayi yana faɗin, “Kee Ina zaki je da wani dogon goshin ki anan wajen? Wa kika bari ya zuba miki?”

Saurin juyowa tayi kanta a ƙasa ta duƙa ta soma zuba masa abincin a cikin Plate, sai da ta gama sannan ta zuba masa Coke cikin Cup; tunda tasan yana so sosai, kuma ko ta tafi zai iya dawo da ita, shiyasa tayi gwanintan zuba masa kar tayi laifi

Mi ƙe wa tayi da zumman tafiya, sai ji tayi an riƙe ta.

 

 

_wannan salon labarin na daban ne, ku kasance dani don jin cikakken labarin._

Zaku iya samu na a WATTPAD ɗina UMMUDAHIRAH. Please kuyi following ɗina na gode. 🤝

 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]