[Advertisements⬇️]

TANA RAINA CHAPTER 8 - Bankinhausanovels
Sun. Mar 26th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

TANA RAINA CHAPTER 8

 

 

Bayan su suhail sun dawo gidane suka sami mum a palo, bayan sun zauna ne kamal ya dauki ruwa a frigj yasha sannan yamikawa suhail mayasha, mum tana ta binsu da kallo tace lfy kuwa kodai baku sami mai girkin bane? Kamal yace mum samu mum nan dai suka bata lbrn abinda ya faru, sosai mum itama abin ya bata tausayi, tace Allah sarki Allah ya jikanta yanzu dai za’a d’auki lokaci kafin tazo, can se idonta yakai kan hannun suhail, tace suhail me nake gani a hannunka, suhail ya shafi gurin yace cizon da yarinyan tayitamin ne lokacin dana rik’e hannunta, shi kansa kamal baisan da batun cizonba se yanzu dayaga hannun suhail yayi jah kuma ya kunbura, mikewa suhail yayi ya shiga d’aki ya watsa ruwa sannan ya fito ya goga mantileta a hannun nasa seya kwanta yana tunanin abunda ya faru, kamal ne ya shigo shima wankan yayi,yazo ya zauna kusa da suhail fiskar sabreen kawai yake gani dana munira, mamakin irin kyawu na sabreen yakeyi, yace suhail amma kaga fiskan sabreen kuwa, gashi dai kauyene amma har ana samun kyawawa haka, gaskya irin kyawun sabrin sedai a kasar larabawa da indians bade nigeria ba.
Suhail yayi murmushi yace abokina ni gaskya banganta sosai ba, saboda gabad’a kukanta ya d’aga min hankali, kamal yace dama na tuna hakan a raina wlh, yauzu me abin yi? Suhail yace se ranan da za’ayi uku semu koma muyi musu gaisuwa, tunda wani sati zanyi tfy zuwa ranar da za’ayi bakwai seka sake komawa kaji me kakan nata zaice. Haka za’ayi suhail Allah ya kaimu.
Haka sabreen ta kasance cikin kuka koda yaushe, nasiha sosai malaman kauyen nasu suke mata harta dena kukan, amma dai ba’a rasa ganin hawaye a fiskanta. Kullum zaka ganta tare da munira dan a gidansu take zaune, maganganu masu kwantar da hankali munna take mata harta d’an ci abinci kad’an, amma idanunta sun kubura dan kukan mamminta.
Yau ne za’ayi uku, suhail da kamal suka shirya cikin fararen shadda dasu akayi addu’oi sakamakon sunzo da wuri, bayan an gamane suka sake keb’ewa da kakan sabreen sukace sunaso su mata gaisuwa, kaka da kansa yaje ya kirata, himar suka saka ita da munira suka fito lokacin kaka yaje gaisawa da wasu. Kamal ne ya fara magana yace sabreen ya hakuri, kanta ta d’ago tace Alhamdulillah tana kallon kamal din, yace Allah ya jikanta, tace ameen sannan ya juya gun munira suna gaisawa se suhail yace sabreen ya hakuri, kai ta d’ago don kamar taso ta gane muryarsa, idonsu na had’uwa ta ganeshi tana masa kallon mamaki, Alhamdulillah tace dashi, yace toh Allah ya jikanta da rahama, ameen tace nagode sosai harda yar mirmushinta😊. Suhail ma kallonta yakeyi har cikin ido, se kuma ya kau da kansa yace kamal muje koh, kamal yace to sabreen ya sunan kawarki ne, sabreen tace sunanta munira, ok dukkanku kuna da suna masu dad’i mu😊, sabreen tace mungode Allah ya bada lada tana kallon suhail shida yake kokarin wucewa gun motansa yace ameen mum d’inmu tace amik’a mata gaisuwa agareku, sabreen tace mungode sosai, murmushi suhail yayi mata sannan ya kira wasu yara tare da bud’e but na motarshi yara suka fara shigowa da kayan abinci juice, taliya, indomie dasu buhun shinkafa. Sabreen ta kalli kamal tace wannan fa, kamal yace sadakace muka kawo muku, hawayene yake fitowa daga fiskarta daidai lokacin suhail ya karaso, hanki ya ciro a aljihunsa ya mika mata, hannu tasa ta karb’a tana kallonsa har cikin ido tana zancen zuci, duk lokacin da nake cikin wani hali se in ganka agun ya akayi kazo nan kuma? Suhail ne ya katseta da cewa shide mamaci babu abinda yafi bukata irin addu’a kukanki azabane agunta sabreen, dad’in zancen nashi taji atake tare hawayenta da hankinsa sannan ta mika mishi tace mungode sosai Allah ya bada lada, ameen sukace se suhail yace ki rik’e nabar miki😊, itama murmushin tayi tace se anjumanku sannan tajawo hannun munira suka wuce gida. Kamal se binsu da leke yakeyi, suhail ne ya janyo rigansa yace inaga dai ba k’alau kakeba, gaisuwafa mukazoyi ba kallonsuba malam, dai dai lokacin kaka ya k’araso yana musu godiya sannan sukaci gaba dayin magana. Sabreen kuwa mamaki takeyi ya akai suhail yazo nan🤔, maman munirace tace sabreen wannan fa suwaye suka kawo, sabreen tace sune wanda muka gaisa dasu yanzu nima ban sansuba sedai mu tambayi kaka idan ya shigo k’ila shiya sansu😉.
Bayan kaka yayi sallama da kowane saiya shigo gidan su muniran, nan gaya kayan abinci kam dewa. Baban munirane yake tambayan kaka suwaye suka kawo wannan sadakan haka? Nan kaka ya kwashe lbrn had’uwansu dasu suhail tas ya gaya musu. Munira tayi saurin juyowa ta kalli sabreen, sabreen ta kyafta mata ido😉 sannan ta fara murmushi a zuciyarta tace to meyasa yake nemana, kodai d’ankwalina zai bani? Alhamdulillah tunda baiga fiskanaba, kuma koda naje yin aiki a gidansu bazan tab’a sanar dashiba tunda nidai nasan ba’amin fyad’eba kuma ina farin ciki zan koma makaranta dan haka na amince zanyi musu aikin☺15/16

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]