[Advertisements⬇️]
[Continue Reading⬇️]
TANA RAINA CHAPTER 9
Sabreen da munirane suna zaune a d’akinsu bayan sunyi sallan isha suna cin abinci, munira ta kalli sabreen tace dama shine suhail d’in? Sabreen tace eh shine bai ganenibane saboda nik’af ne a fiskata ranan. Munira tace to ai yakamata ki sanar dashi tunda kinga nemanki ne yasa suka sake dawowa nan d’in, sabreen tace a’a munna wannan maganar sirri ce tsakanin nida ke pls, munna tace to ai shikenan kika san koya kyasa ne yasa ya biyoki, gashi da alama masu haline kinga shikenan mun fito fari😜, dariya sukayi dukkansu sannan sukaci gaba da hiransu.
B’angaren suhail kuwa, tunda suka dawo kowa da tunanin da yakeyi, hafsat ne tazo ta samesu a palo tace yah suhail ina kukajene inata nemanku, suhail yayi murmushi yace munje gaisuwa ne hafsat akwai wani abu ne, a’a kawai dai dan ban ganku bane. Kamal yace nidai zan tafi gida seda safenku, suhail ya tashi ya rakasa hargun mota sukai sallama sannan ya dawo gun mum sukaita hira har zuwa 9pm kafin suka wuce donyi bacci. Shidai suhail yana ta kallon idanun sabreen a ransa dan yayi mishi kama dana wannan yarinyar, sedai na sabreen sun kumbura kuma sunyi jah, to shine dai yake kokonto akan kila kamace kawai, kuma kaka ya tabbatar musu da cewa babu yarinyar da akayiwa fyad’e a kauyen, ya shiga rud’ani sosai da haka yayi bacci…
[Advertisements⬇️]
[Continue Reading⬇️]
Yau wata guda kenan da rasuwan mammin sabreen. Shikuwa Suhail yana can pakistan kusan 3week kenan. Kamal ne a kofar gidansu munira yana jiran fitowar kaka da sabreen, can segasu sun fito suna rungume da juna suna kukan rabuwa, maman munirane taketa basu hakuri tana cewa munna kiyi hakuri aiba rabuwa kukayiba ‘yan watannine kawai zatayi seta dawo kinji, da kyar dai suka rabu kamal ya bud’ewa kaka gaba sannan sabreen ta shiga baya suka tafi tanata yiwa munira bye tana kwalla. Tunda suka fara tfy sabreen taketa kuka har suka iso wani gida mai kyau, hon kamal yayi aka bud’e suka shiga, bayan motan ya tsayane kamal yaje ya bud’ewa kaka dan sabreen kam harta fito tana rik’e da yar jakanta, kamal yace bissimillah kaka muje, kofa ya bude sika shiga k’aton palo mai kyan gani, anan suka zauna kamal yace sannunku da zuwa kaka😊, kaka yace yawwa sannu kamal, ruwa mai sanyi ya kawo musu tare da juice ya zuba musu, ahankali suka karb’a suka sha tare dayi mishi godiya. Kamal yace kaka nan gidan mahaifinane amma Allah yayi musu rasuwa shida mahaifin suhail a k’asar saudiya, iyayenmu aminan junane sosai suna business a wani kamfani dake pakistan, lokaci lokaci suna zuwa duba kasuwancin nasu. bayan rasuwansune mahaifiyata tayi aure a pakistan d’in, inda ni kuma nake zaune a gidan mahaifina, nida suhail mukaci gaba dayin business kamar dai yadda iyayenmu sukeyi, idan naje wannan karon, wani karon kuma suhail ne yake zuwa, mahaifiyar suhail tak’i yin aure sam tana zaune damu anan da kuma ‘yar yayan baban suhail wato hafsat, itama marainiyace dan bata da uwa bare uba. Mahaifiyar suhail ta rik’e hafsat kamar ‘yarta na cikinta, inda mu kuma muka zame mata yayyu. Matar da take musu girki d’anta ya samu aikin yine shine yace mamansa zata dena girki, shiyasa muke neman wanda zata dinga musu girki ana biyanta duk wata. Kaka yayi ajiyar zuciya yace Allah ya jikansu da rahama suka amsa da ameen dukkansu. Kamal yace na kawoku nanne saboda kace sabreen bata iya girkin zamaniba sena gargajiya, shine nakeso ku zauna anan koda na tsawon wata biyu ne na samo wanda zata dinga koyawa sabreen girke girken zamani idan ta iya sena kaiku gidansu suhail koya kagani kaka? Kaka yace bakomai kamal na fahimceka kuma na amince danna yaba da halaiyarku nasan bazaka cutar damuba zamu zaunan anan d’in harse ta gama koyon. Kamal yayi murmushi yace to alhamdulillah kaka ina tabbatar maka da cewa bazan tab’a cutar dakuba shiyasama nace mu taho tare dakai koda ruwa seka dinga ba flawer kaima ana biyanka. Godiya sosai kaka yayi sannan kamal yace muje in nuna muku masauk’inku, tare suka mik’e sabreen tana binsu a abaya, d’akin mummynsa yaba sabreen, sannan yaba kaka d’akin babansa, manyan d’akunane da komai a ciki, murna sosai sukayi tare da k’arayin godiya.
Kamal ne kwance a d’akinsa ya kira suhail a waya yace abokina se nanda 2month su kaka sasu zo, suhail yace toba damuwa Allah ya nuna mana, kamal yace amin sannan sukaci gaba dansu. Bayan sun gama wayanne kamal yace bazan iya sanar dakai suna gunaba abokina, harse sabreen ta k’ware sosai da girkin zamani anan, insha Allah gobe zanje inyi musu cefene sosai zuwa jibi RUKAYYA zatazo ta fara koya miki sabreen, da wannan shawaran kamal yayi bacci tare da jin dad’i a ransa wanda bansan dalilin saba😊😊😊17/18
[Advertisements⬇️]
[Continue Reading⬇️]