[Advertisements⬇️]

TANA RAINA CHAPTER 7 - Bankinhausanovels
Sun. Mar 26th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

TANA RAINA CHAPTER 7

 

 

Suhail da kamal ne a hanyan tfyansu kauyen su Sabreen, suna tafe suna hira har suka iso daidai gurin daya had’u dasu sabreen, se uace kamal a daidai nan ne amma dai mu kara gaba kadan, ahankali,suke tfy se suka hango hanya shiga garin sukai tfy kad’an se suka hangi kakan sabreen yana komawa rike da cefene a hannunsa, gunsa suka tsaya da motan tare da dayi masa sallama, bayan sun fitone suka gaishesa cikin girmamawa sannan sukace baba dan Allah muna tambayane, yace toh ina jinku, suhail yace wata yarinya nake nema ko Allah yasa ka santa, kaka yace menene sunanta? Suhail ya kalli kamal se kamal yace wato dai baba muma basusan komai game da itaba kawai dai mun gantane tanan tana sanye da riga da zani da kuma bak’in himar sannan tasa nik’af a fiskanta, kaka yace to gaskya bayin Allah bazan ganetaba, dama ace kun gayamin sunantane ko sunan mahaifinta ko kuma kamanninta,toda zan iya ganewa, suhail yace baba yarinyar an mata fyad’e jiya jiyan nan kuma dai muna kyautata zaton atanan take, kaka yace fad’e kuma subhanalillah to gaskya bata nan bane, domin duk abinda ya faru a kauyennan baya b’uya a masallaci ake sanar da koma menene, kamal yace to ai k’ila baza a iya sanar da magana irin na fyad’e ba, kaka yace za’a sanar ina tabbatar muku da cewa babu abinda yake b’uya a kauyennan namu, wai samari me kuke nema agun yarinyarnan ne, kamal yayi saurin cewa dama daga cikin gari muke, muna neman masu aiki ne, kaka yace wani irin aiki kuma, kamal yace mata dai wanda suke aikin wanke wanke da shara da kuma girki za’a dinga biyansu a wata. Kaka yace haba da gaske, ina da jikata nasan zatayi farin cikin hakan dan ta dad’e da gama secondary tana so taci gaba da karatu amma bamu da hali, tayita neman aikin a kauyennan amma bata samuba, sedai kuma aiyukan daka lissafo sunyi yawa, Suhail yace a’a dama girkine kawai zata dingayiwa mahaifiyata dan bata da lfy, kaka yaji dad’i sosai yace indai wannan ne shikenan jikata ta iya girki amma na gargajiya ne ko kuma ince namu na karkara sam bata iya naku na birnineba. Kamal yace ba damuwa muma ai muna cin abincin gargajiyan sosai dan haka ba matsala zamusa a koya mata😊. Kaka yace to shikenan kud’an bani lokaci inyaso seku dawo daga baya koh? Suhail yace to shikenan mun gode sosai baba, kaka yace bakomai nine da godiya nasan jikata zatayi farin ciki sosai dan haka sekun sake dawowa…wasu samarine suka karaso a guje suna haki suna cewa kaka gara da muka had’u dakai, Allah yayiwa mammin SABREEN rasuwa yanzu yanzun nan shine aka aikomu donmin muzo mu kiraka, 😳Innalillahi wa inna ilaihir raji’un dukkansu suka amsa, kaka yace me kace SALE, Mammi ta rasu😰? Sale yace eh kaka macijine ya sareta a bayan wuyanta kuma harta cika😭. Kaka yace ina sabreen jikata take a wani hali take ciki? Suhail ya kamo hannun kaka yace baba shiga muje tare, ba musu suka shige gabad’ayansu suka isa har kofar gidan inda suka iske mutane a cike. Fitowa sukayi dukkansu suka wuce cikin gidan, lokacin har matan makota sunyi mata wanka an suturceta kaka ya isa yayita mata addu’a sannan aka fito da gawanta zuwa waje nan akai mata sallah aka d’auketa dan kaita gidanta na gaskya sega sabreen ta fito a guje tanata kuka tana cewa kaka dan Allah karku tafi min da mammina ina sonta wlh karku kaimin mammina rami dan Allah ku tausayamin ita kad’ai ta ragemin fa kaka😭. Kowa ya tausayawa sabreen musamman kaka da iyayen munira, munirane ta biyota da hijabi danko d’ankwali babu akanta bare takalmi, gashin kanta duk ya tattashi kamar wata mahaukaciya, bayan munna tasa mata himar d’inne se take k’okarin janyota amma ta kasa, kaka yace da suhail dan Allah yaro taimaka ka mayar min da ita gida kaji, ba musu suhail ya kamo hannunta yana kokarin maidata gida seta gantsara masa cizo tana cewa dan Allah ka sakeni zasu tafimin da mammina nefa nika sakeni😭. Kuka sosai takeyi hakama munira, Suhail ya rasa meke masa dad’i sam bayaso yaji mace na kuka, ahaka har suka k’arasa kofar gidansu munira wata mata ta riko hannunta suka k’arasa da ita cikin gidansu muniran. Shi kuwa suhail hannunsa yayi jahjazir dan cizon da sabreen tayita mishi, binsu yayi mak’abartan akai mata komai sannan suka dawo sukai musu gaisuwa se suka tafi suna masu tausaya musu sosai😔😔😔

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]