[Advertisements⬇️]

TANA RAINA CHAPTER 11 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

TANA RAINA CHAPTER 11

 

Lokaci nata fty har aunty Rukayya ta gama koyawa sabreen girki na tsawo 2month, sannan babu abinda zakace sabreen ta dafa makashi wanda bata iyaba, ta k’ware sosai itama yanzu sedai ta koyar da wasu, harta snacks da drinks na gida wabu wanda sabreen taba iyaba. Yaune kamal ya sallami aunty rukayya da kud’ad’e masu yawa wanda nima bansan adadinsu, sabreen suke tsaue da aunty rukayya suna bankwana, sabreen tace aunty rukayya ki bani number wayanki dukka dai bani da waya amma zanso kiban number’nki kakana yace jibi zai sayo min waya, aunty rukayya tace to badamuwa nan ta ciro card d’inta tabawa sabreen sannan tace gaskya kinada hankali da dad’in sha’ani sabreen Allah ya baki miji na gari😊, sabreen tayi murmushi tace ameen aunty rukayya bazan tab’a mancekiba nagode sosai Allah ya biyaki😀, aunty rukayya tace ameeen sannan tayiwa su kaka da kamal sallama ta tafi.
Duk hiran da aunty rukayya sukeyi da sabreen kamal yana jinsu, dan haka ya shirya zai fita se sabreen tabi bayansa tace yah kamal zaka fita ne, eh sabreen akwai wani abune, a’a dama inaso inyi maka godiyane akan girki dakasa aka koyamin nagode sosai😀, murmushi yayi yace bakomai sabreen nizan fita se dare zan dawo, ok dama inaso inje gurin munira ne tunda muka rabu bamu sake had’uwa ina kewarsu sosai☺, kamal yace to shikenan ki bari zuwa gobe semuje harda kaka koh, dad’i taji sosai tana maiyin murmushi wanda yake k’ara mata kyau tace nagode yah kamal Allah ya kaimu goben😊, ameen sabreen na tafi. Bayan kamal ya fitane ya kira aunty rukayya yake tambayarta ko sabreen ta tab’a gaya mata irin wayar da takeso, aunty rukayya tace eh toh akwai randa muke hira take cemin akwaia wayan malaminsu na secondary skul wai wayan yana da camera sosai idan ya d’aukesu hoto a ciki, tun daga ranan take son wayan a ranta samsung galacky x5, kamal yace toh shikenan nagode. Shagon waya ya tsaya ya saya mata sabuwar samsung x5 sannan ya wuce gunsu mum.
Kamar kullum se yaban isha kamal ya dawo bayan yaci abinci ne yazo palo yasamesu sunata hira, wayan daya sayawa sabreen ya mik’a mata gashi sabreen wayane na sayo miki na miki charging sannan nasa miki sim d’in MTN aciki, karb’a tayi hannun biyu tana farin ciki tare da cewa nagode yah kamal Allah ya biyaka da gidan aljannah, ameeen sabreen Allah ya bamu dukkanmu sannan kakama yayi masa godiya yace kamal kaibaka gajiyane, kud’adenka zasu kare dan Allah ya isa haka ka dena b’arnatar da kud’inka akanmu zaman da mukeyima kad’ai ya ishemu wlh ka mana gata sosai Allah ne kad’ai zai biyaka, kamal yace haba kaka bakomai wlh ni zanje in kwanta saboda da safe nakeso mu tafi dan kud’an yini acan zuwa yamma semu dawo, kaka yace to badamuwa Allah ya kaimu, wayarsace tayi kara ya d’auka tare da sawa a hands free yace hello abokina, suhail yace eyyy yane gwabro kak’i dai kayi aure koh, kamal yayi murmushi yace wannan ai bani kad’ai kake tsokanaba harda kanka, dariya suhail yayi yace toh garin yasu mum, kamal yace yanzu na dawo daga gunsu lfyansu lau ya pakistan, suhail yace lfya lau wlh mummy ce take cemin wai munk’i muyi aure semu tsufa ai mun rasa matan aure😀, kamal yayi dariya yace aiseka yi kafin nima nayi dan haka kai nake jira, suhail yace zan dawo ran friday insha Allah ya maganan su kakane dan mum tacemin ran wenesday mai girkinsu zata tafi, kamal ya kalli kaka da sabreen yace eh nima d’azu danaje ta gayamin kuma na tabbatar mata da cewa ran talata zan kawo mata mai girki, suhail yace ok to yaushe zakaje garinsu kakan? Kamal yayi murmushi yace gobe insha Allah, suhail yace to nagode abokina ka gaida su kakan inkaje, kamal yace suna jinka, suhail yace me kace? Kamal yace sorry nace zasuji😉, bayan sunyi sallama ne kaka da sabreen suke ta dariya😀, kunya kamal yaji seya mik’e tare da cewa seda safenmu😉, har yanzu dariya sukeyi sannan kaka yace to Allah ya tashemu lfy yace amenn sannan ya shige d’akinsa.
Washegari suka shirya tsab se k’auyensu, murna sosai mutanen k’aunuen sukayi da ganinsu kaka musamman ma nunna, tace sabreen me sirrin ne kin ganki kuwa yadda kika kara kyau se wani shek’i kikeyi, sabreen tayi dariya tace kema kin canjafa me sirrinne k’awas? Nan munira ta bata lbrn saurayin da tayi me suna ABUBAKAR SADDIQ shi doctor ne kuma yana da hankali sosai gashi yana kulawa da ita sosai kingama harya sayamin wayanmu galacky x5 sannan komai ya sayamin sena ajiyei miki naki kinga nan munira tayita nunawa sabreen kayan alkhairin da Abbakar yake mata harda iyayenta. Bayan ta gama ganine tace lallai k’awata kin paso gari Allah ya tabbatar da alkhairi ya kuma nuna mana bikin💃🏻munira tace amenn toya birnin bani lbr mana, sabreen ta kwashe lbrn birnin tun daga farkon zuwansu har karshe ta fad’awa munna sannan ta bata sayayyan kayan da kamal yayi musu harda k’arin jaka da takalmi nasu mama ma dabanne. Munna ta bud’e baki tana ganin abun duniya tare dayin godiya ita dasu mama sukaiwa kamal godiya sosai, munna tace kodai yana sonkine sabreen? Sabreen tace SO kuma, oho nidai bai tab’a gayaminba nima kuma bansa komai a rainaba, SUHAIL shine a raina amma kuma duk randa yah kamal ya furtamin cewa yana sona nad’au alk’awarin amince masa tare da bashi soyayyata danya cancanci hakan daga gareni kuma kowace mace zataso mutum irin yah kamal dan baida wata matsala wlh. Munna tace to Allah ya zab’a miki mafi alkhairi sabreen, ameen Amaryan abbakar mu zamu koma se wani lokaci kuma😀.
Bayan sun komane kamal yace to kaka seku shirya jibi talata zaku koma gidansu suhail ran laraba mai girkinsu zata tafi sabreen zata fara girki ran alhamis yayinda suhail zai dawo k’asar ran FRIDAY. Daga kaka har sabreen basuso hakanba, shima kamal d’in babu yadda zaiyine amma sam bayason tfyarsu, kaka yace toba komai Allah ya nuna mana, kamal yace ameen sannan ya wuce d’akinsa suma sukai nasu d’akin da tunani kowannensu yayi bacci😲😵😲23/24

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]