[Advertisements⬇️]

TANA RAINA CHAPTER 10 - Bankinhausanovels
Mon. Mar 27th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Bayan sabreen ta gama karyawane taje tayi wanka tasa d’inkin doguwar riga na atamfa ta d’aura d’ankwalinta sannan tasa farin himar komai bata shafaba ta fito. Kamal ya shirya cikin blue shet da black jeans yana zaune a palo yana jiran fitowanta, can segata ta fito da murmushi a fiskanta tace hamma kamal na shirya, kalonta yayi tare dayin murmushi yace toh muje, atare suka fito lokacin kaka yanaba flower ruwa sunata hira da mai gadi,segasu sabreen sun fito tace kaka zamuje mu dawo, kaka yace toh sabreen sekun dawo. Tunda suka fara tfy babu wanda yace komai acikinsu har suka karasa super market, nanne kamal yace muje sabreen😊, a hankali ta fito suka shiga se kallo takeyi dan bata tab’a zuwa super market ba. Kayan abinci suka saya sosai, sannan kamal ya kaita gun kayan sawa yace ta d’auki duk abunda taga ya mata kartaji kunya, nan sabreen tayita d’iban atamfofi da material da kuma dogayen riguns, ta kalli kamal taga yana can nesa da ita, gunsa ta nufa tace hamma kamal zan iya d’auka ko wanne 2? Murmushi yayi yace ko 5 5 nema ki dauka kinji😊, murmushin itama tayi sannan tace nagode ta juya yana binta da kallo yana murmushi, komai 2 take d’auka wai ita da muniranta. Bayan sun gama da kayane yace ta biyosa suje gaba, sun isa wani gun maiyukan shafawa suka nufa da turaruka, NATURAL HONEY shine mai d’inda take shafawa ita da munna, dan haka shima ta d’auki 2 sannan ta d’auki turaren FASIO shima 2 dasu body spray, kamal yace kayan kwalliya fa, sabreen tace sedai in d’aukawa munna danni bana kwalliya, murmushi yayi yace koda gazal da janbaki da hoda nedai ki dauka, dariya tayi tace hamma kamal ai to na d’iba kayan kwalliyan gaba d’aya kenan, yace eh idan kina kwalliya zakifi haka kyau, ba musu ta d’iba suka d’ibi takalmi da jaka, sayayya dai sukai sosai sannan suka wuce gun tela aka bashi d’in kaya kala 24 nata dana munna. Daga nan suka wuce gida, kaka ya tayasu shiga da kayan komai aka shiryashi a store, kayan,tea kuma suna daining drinks a frij, komaidai gun zaman suna nama akai kaisa babban friza. Sabreen ta nunawa kaka irin sayayyan daya mata ita da munna tace kuma munbada d’inkin kaya, kaka yayita masa godiya dasa masa albarka hakan yayiwa kamal dad’i sannan yabaiwa kaka takalma da turare yace kayanka anjuma zankai makasu d’inki, godiya sosai sukayi sannan kamal yace shizai fita zaije ya duba mum d’in suhail da hafsat ze zuwa dare zai dawo sabreen ki dafawa muku koma menene kinji, toh seka dawo😊.
A gidansu suhail kamal ya yini yayita bacci harseda yayi sallan isha sukaita hira kamar yadda suka saba sannan ya koma gida. Lokacin 8:30pm kaka suna zaune a palo suna kallon sunna TV kamal yayi sallama tare da shigowa, bayan ya zauna ne yace kaka sannunku da gida😊, yawwa kamal sannu da dawowa yaka barosu, lfyansu lau wlh, sabreen tace sannu da zuwa hamma kamal ga abincinka akan daining, yawwa sabreen ta bari naje nad’an watsa ruwa senazo naci girkin k’anwata😀. Bayan yayi wanka ya fitone yasa jallabiya tare da fesa turare ya wuce daining, sabreen ta mik’e taje ta zuba mishi tuwon shinkafa da miyar egushi yaji manja da dry fish ga nama😋, tunda sabreen ta bud’e kulan kamshi ya daki hancinsa take nyawunsa ya tsinke, da bissimillah ya fara cin abincin yana lumshe ido☺😊, sabeen ya kirata, tace na’am tare da mik’ewa, irin wannan miya mai dad’i aibase a samo mai koya miki girkiba domin ni ban tab’a cin miya mai dad’n wannanba, dad’i sosai taji tana dariya tare da cewa nagode amma ina bukata dai akoyamin wad’anda ban iyasuba na zamani. Kamal yace badamuwa gobe zatazo ta fara nuna miki kinji, tace toh Allah ya kaimu goben yace ameen.
Washe gari da safe RUKAYYA tazo bayan sun gaggaisa ne se suka wuce kichine da sabreen suka fara had’a breakfast, duk abinda RUKAYYA takeyi idon sabreen nakai har suka gama sukayi breakfast gabad’ayansu kuma sunji dad’in girkin nata😋. Haka sukayi na rana suka sake yin na dare, kullum kuma RUKAYYA so 3 takeyin abinci wato safe rana da kuma dare, seda tayi girki harna tsawon 1 week sannan tace sabreen ta sake maimaita duk abinda ta dafa na tsawon satin. Tsab kuwa sabreen tayi kamar yadda RUKAYYA takeyi kuma yayi dad’i sosai, Aunty rukayya shine sunan da sabreen take kiranta dashi, cikin k’ank’anin lokaci suka shaku da juna sosai kuma sabreen taci gaba dasa hankali akan koyan girkin. Shikuwa kamal dad’i yakeji sosai yana zuwa dubasu mum kullum dan acanma yafi zama se dare yake dawowa.21/22

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]