[Advertisements⬇️]

SANADIN SONKI CHAPTER 9 - Bankinhausanovels
Mon. Mar 27th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

SANADIN SONKI CHAPTER 9

 

 

 

Yana gama fitowa a mota ne Mumy ta kama hannun shi suka fara tafiya zuwa cikin hall d’in, sai da suka kusan shigewa hall d’in tukunna Fadilah ta dawo daga duniyar tunanin da ta fad’a da sauri ta bi bayan su don tana Buk’atar jerawa da Sabeer.

Bayan sun shiga ciki ne Mumy da Sabeer suka zauna waje d’aya sai wani 6a66ata rai yake, gaba d’aya hayaniyar duk ta isheshi ya gaji ga ‘yammatan da suka dame shi da hayaniyar su kowacce tana kok’arin cusa kanta a wajen shi, amman yanda kasan da dutse suke magana haka yake share su, Gashi kowacce da nata gift’s da takawo mishi, Mumy sai wani murmishin jin dad’i take ganin yanda ake son d’anta.

Gaba d’aya Mumy ta mance da 30 minutes kawai Sabeer yace zai yi, bata ankara ba taga sun d’auki wajen 25 minutes a wurin ai kuwa da sauri ta kallo inda Sabeer yake zaune yana danna wayar shi gefen shi kuma Fadilah ce ke faman yi mishi surutu tana wani karairaya da iyayi ita a dole so take ta birge Sabeer, k’arasa wa Mumy tayi wajen ta dafa kafad’ar shi cikin k’aramin sautin magana tace
“Son kazo ka yanka cake ”
Daman gaba d’aya a takure yake da yabar wajen don haka ya mik’e tsaye Mumy taja hannun shi har zuwa inda aka ajiye cake, knife Mumy ta bashi suka rik’e tare tukunna suka yanka nan Mumy ta bashi a baki shima ya bata, nan kuma kowa ya fara bashi kyautar gift nashi da zai bashi Sabeer sai faman jan tsaki da 6ata rai yake ganin har ya k’ara 5 minute akan 30 minutes d’in da zai yi, sai kallon Mumy yake yana son sun had’a ido dashi yayi mata magana, amman tak’i yarda su had’a ido kwata kwata saboda tasan halin d’an nata gashi duk wanda zai bashi gift idan baisan shi ba sai ya tsaya gabatar da kanshi.

D’ago kan da zaiyi ya kalli Mumy akayi sa’a ita ma ta kallo inda yake da ido yayi mata alamar ya gaji gashi time d’in da ya d’auka ya wuce yana nuna mata agogon hannun shi gashi kuma ‘yammatan da suka bi suka dame shi Sabeer dai yaga ta kanshi tamkar zai fashe da kuka haka yake ji duk Mummy ce ta ja mishi, Mumy tamkar ta fashe da dariya haka taji lokacin da ta ga Sabeer yanda ya koma amman sai ta danne dariyar ta tare da marairaice mishi fuska da ya d’an yi hak’uri na d’an wasu minutes, daga nan kuma aka fara ciye ciyen abubuwan ci dana sha, a wannan lokacin Sabeer ya zame ya tafi abin shi gaba d’aya a wani gala6aice yake kanshi har ya fara ciwo.

Shiga mota yayi driver yaja shi sai gida, yana parking ya fito daga motar ya nufi side d’in su, kai tsaye bedroom d’in shi ya nufa yana shiga ya fara cire kayan jikin shi yana wurgi dashi sai da ya cire komai sai iya dogon wandon shi ya bari tukunna ya shige toilet, shower ya sakarwa kanshi na tsayin 2 minute kafin ya fad’a cikin bath tub ya fara wanka bayan ya gama ne ya d’aura alwalar sallahr ishha tukunna ya fito daga toilet.

Wata white jallabiya ya sanya cikin nutsuwa ya gabatar da sallahr ishha bayan ya idar ne bai wani tsaya yin wata addu’a ba ya mik’e tsaye tare da cire jallabiyar ya kwanta daga shi sai three-quarter a jikin shi kwanciya yayi saman bed yana mai runtse idanun shi hannun shi d’aya saman goshin shi ya dafe, a hankali ya wani bacci mai nauyi yayi awon gaba dashi daman ya gaji sosai.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Mumy koda ta duba bata ga Sabeer ba tasan ya tafi, don haka nan ta sallami friends nata da wad’anda suka zo, kowa ya tafi gida tukunna ta shiga mota zata rufe murfin motar taji an rik’e, cikin d’an mamaki ta jiyo don ganin wane, had’a ido tayi da Fadilah fuskar Mumy cike da mamaki tace
“Fadilah daman baki tafi gida ba ”
Cikin marairaice fuska Fadilah tace
“ni Mumy bin ki zanyi fah acan zan kwana ”
Murmishi kawai Mumy ta saki don tasan dalilin kwanan Fadilah a gidan nata, cikin kulawa Mumy tace
“alright dgter shigo mu tafi ”

Fadilah jiki na rawa ta shige cikin motar ta zauna burin ta kawai a yanzu da tunanin ta shine yanda zata shawo kan Sabeer ya amince da ita ya aure ta ko suna hutawa da junan su, don ita Fadilah bata da ra’ayin aure a zuciyar ta sai da taga Sabeer, ita kawai ‘yar aji dad’in rayuwa ce bata tunanin makomarta anan gaba matsayin ta na d’iya mace.

Hira suke tsakanin Mumy da Fadilah har suka k’arasa gida driver yana yin parking suka fito a motar direct part d’in Mumy suka nufa, suna shiga cikin parlourn babu kowa amman a gyare yake tsaf dashi sai tashin k’amshin turaren wuta yake da air freshener, upstairs suka nufa nan Mumy ta nunawa Fadilah room d’in da zatayi amfani dashi, amman sai Fadilah tace
“Mumy ina ne bedroom na Sabeer naje mu yi hira kinsan har yanzu yak’i sake min sosai ”
Murmishi Mumy ta saki tare da nuna mata wani d’an corridor da hannunta tace
“kin ga bedroom d’in shi can nasan yanzu yana ciki ” tana gama fad’in haka Mumy ta nufi hanyar da zai kai ta bedroom nata ta bar Fadilah anan.

Wani dad’i ne ya kama Fadilah cikin rawar jiki ta juya zata nufi room d’in Sabeer sai ta kalli kayan jikin ta wani d’an Tunani tayi kad’an kafin ta juya kuma da sauri ta koma bedroom d’in da Mumy ta nuna mata.

Da sauri ta shige bathroom ta fara yin wanka bata dad’e ba ta fito babu batun yin alwala balle sallah, cikin sauri ta gyara jikin ta sannan ta shirya cikin wata white d’in sleeping dress tsayin ta iyakar shi cinya mai siririn hannu sannan ta d’ora ‘yar saman ta wadda take har k’asa sai dai gaban ta a bud’e yake sai ‘yan igiyoyin rigar da ake d’aure wa, perfumes ta sanya masu matuk’ar k’amshi da tada hankali sannan ta fito zuwa room d’in Sabeer.

Tura kofar room d’in tayi ta shiga tare da rufe kofar ta jingina bayan ta a jikin ta, shak’ar k’amshin turaren Sabeer tayi tare da lumshe ido tana sauke ajiyar zuciya, kafin ta bud’e idanun ta a hankali ta zube su akan Sabeer da yake baccin shi hankali kwance, wani shu’umin murmishi ta saki tana mai k’arasa wa wajen bed d’in, hankalin ta kwance ta cire ‘yar saman rigar ta tukunna ta haye kan bed d’in.

Kallon Sabeer take tamkar wata kura taga nama, sai wani had’iyar yawu take musamman da takai eyes nata kan kirjin Sabeer a hankali ta d’ora hannun ta inda take Buk’atar ajiye shi a cikin jikin Sabeer ta fara shafawa cikin kwarewa da gwanin ta….

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]