SANADIN SONKI CHAPTER 7

SANADIN SONKI CHAPTER 7

 

 

 

 

Family d’in Alhj d’an fillo asalin su irin fulanin nan ne wanda suke da arzik’i sosai na dukiya da ababan kiwo, Alhj Ahmad d’an fillo shine d’a d’aya a wajen mahaifin shi da mahaifiyar shi sai ‘yan uba k’annen shi su uku dukka mata shi d’aya ne namiji mazauna garin adamawa state, shi yasa mahaifin shi ya tsaya akan bashi ilimin boko, duk da su ma matan ya sanya su a makarantar iyakar su secondary ya aurar dasu.

Bayan Ahmad ya kammala karatun shi na fannin Lafiya ya samu aiki sai iyayen shi suka aura mishi wata Hauwaa wadda ta kasance ‘yar uwar shi ce, watannin su uku da aure iyayen shi suka yi accident a hanyar su ta zuwa airport don zuwa k’asa mai tsarki domin gabatar da hajji, dukannin su suka rasu, mutuwar ba k’aramin girgiza Ahmad da matar shi Hauwaa tare da sauran ‘yan uwan su tayi ba, sosai mutuwar ta shige su amman haka suka rungume hak’uri don sunsan haka Allah ya tsara zata faru.

Bayan shekara d’aya da rasuwar iyayen shi matar shi Hauwaa ta haihu ‘yan biyu suka samu, sunyi matuk’ar murna da farinciki, inda suka bar musu sunan su na Hassan da Hussein, sun cigaba da rainon yaran su cikin kulawa, watan su uku da haihuwa Hassan ya rasu sakamakon zazza6i mai zafi da ciwon ciki da yayi wanda kwanaki biyu yayi yana jinya a hospital ya rasu, sosai mutuwar Hassan ta bige su don sai zafin mutuwar iyayen shi ta dawo mishi sabuwa a lokacin, haka suka dangana suna masu bawa Hussein kulawa.

Hussein yana da shekara hud’u Dr Ahmad d’an fillo ya samu transfer zuwa Malam Aminu kano teaching hospital, ba 6ata lokaci ya tattara komai nasu suka dawo garin Kano, sai da ya fara zama a gidajen hospital d’in kafin ya gina nashi gidan, don zaman garin Kano yayi mishi dad’i.

Bayan an gama mishi ginin suka dawo cikin sabon gidan su a lokacin Hauwaa ta haifi d’an ta na biyu Omar, bayan shekara biyu ta sake haihuwar Usman, daga Usman sai Aminu sannan autar su Fadilah, sun cigaba da rainon yaran su cikin kulawa da k’auna makarantu masu kyau da tsada Dr Ahmad d’an fillo ya sanya yaran shi, sai dai sun fi bawa boko mahimmanci fiye da ilimin Islam, a lokacin Dr Ahmad d’an fillo ya tsunduma harkar business sosai wanda nan da nan kud’i sosai suka fara samuwa ba kad’an ba.

Haka lokaci ya cigaba da tafiya yaran shi dukka sun girma kowannen su ya gama karatun shi yana aiki, Hussein business d’in da mahaifin shi yake ya tsunduma a ciki, Omar kuma yana aikin Bank, Usman kuma a wani babban company na abokin Dr Ahmad d’an fillo yake aiki a matsayin GM na company d’in, sai Aminu da yake lecturing a BUK, sai k’aramar su Fadilah da take karatun degree a wannan lokacin, wanda gab take da ta kammala har an sanya lokacin auren ta da wanda zata aura, iyayen shi masu kud’i ne shima haka yana da kud’i abokin yayan ta Omar ne, lokacin da ya nuna yana son ta sosai iyayen ta suka yi farinciki da hakan, saboda suna da kud’i don Dr Ahmad d’an fillo da ‘ya’yan shi basa harka da talakan mutum sai ta kama, don akwai su da kyamar talaka harkokin shi sai da masu kud’i ‘yan uwan shi.

Shiyasa ba 6ata lokaci aka sanya lokacin auren Fadilah da Mustapha, bayan ta kammala degree d’in ta aka yi biki sosai sun kashe kud’i a bikin, bayan auren Fadilah suma Yayannin ta kowanne ya fito da matar aure duk yaran masu kud’i ne daman gashi akwai su da kyau irin na fulani ga kud’i kuma da wayewa, sai da ban da Babban Yaya Hussein don shi harkar neman kud’in shi ya sanya a gaba bai fiye, kuma iyayen nashi sam basu tak’ura mishi ba da yayi aure, kafin bikin ne Dr Ahmad d’an fillo ya gina k’aton gida mai d’auke da part’s biyar kuma kowanne part babba ne sosai kuma upstairs ne, an kashe kud’i sosai a wannan gidan kafin bikin suka koma can da zama abin su.

 

Sai da Omar, Usman da Aminu suka haifi yara kowanne biyu biyu kuma kowanne yaro da tazarar shekara wajen uku a tsakani,tukunna Hussein ya kawo matar da zai aura Dr Faridah cikakkiyar likitar mata ce wato gynecology a k’asar India tayi karatun ta, iyayen ta masu kud’i ne sosai ne kuma abokin Dr Alhj Ahmad d’an fillo ne sosai da sosai, lokacin da Dr Ahmad d’an fillo yaji d’an shi Hussein Dr Faridah zai aura ba k’aramin farinciki suka yi ba shi da Hajja Hauwaa, nan aka sanya lokacin biki two weeks kawai, an kashe kud’i bana wasa ba a wannan auren, don su kansu matan Omar, Usman da Aminu sun san an auro matar so kuma ta gaban goshin surukan nasu don yanda suka ga ana ji da ita tun kafin ta shigo gidan.

Dr Faridah Bashir kyakkyawa ce kuma wayayyiya ce sai dai akwai ta da wulak’anci ba kad’an ba, gata kuma ta tsani wani talaka ya ra6e ta, kanta kawai ta sani, ga nuna tak’ama da tsantsar ak’idar Boko, kuma mahaifin ta hospital babba ya bud’e mata nata na kanta don su biyu kad’ai Allah ya bashi daga Faridah sai k’anwar ta Zahra, ga zata auri mai kud’i don Hussein duk yafi ‘yan uwan shi kud’i, wad’annan halayen nata su suka k’ara mata matsayi cikin zuciyar surukin ta Dr Ahmad d’an fillo fiye da sauran surukan nashi, yana ji da ita matuk’ar gaske.

Bayan auren Hussein da Dr Faridah sai da suka yi wajen shekara uku ko 6atan wata bata ta6ayi ba, sosai hankalin su ya tashi nan aka shiga ziyartar asibitocin k’asashen waje domin bincikar lafiyar su, amman k’alau suke lokaci ne bai yi don komai kud’in ka sai lokacin da Allah ya nufa zaka samu abu zaka same shi, balle haihuwa da lafiya wanda kud’i baya ta6a siyan su sai lokacin da Allah yaso zai baka, gajiya sukayi da zuwa hospitals suka zubawa sarautar Allah ido tare da tsananta addu’a sosai a wajen Ubangiji, Dr Ahmad d’an fillo da Hajjah Hauwaa suma duk’ufa da addu’a suka yi sosai don suna k’aunar son ganin jikan su na wurin Hussein da Dr Faridah.

 

Sai da suka kwashe shekara hud’u da aure kafin Allah ya bawa Faridah ciki, murna da farinciki bazai fad’u ba irin wanda suka yi, nan suka dunga rainon cikin cikin so da k’auna.

Bayan wata tara Faridah ta haihu an samu baby boy kyakkyawan yaro dashi, anyi murna da farinciki sosai, ranar suna ansha taro an kashe kud’i duk wanda yaje sunan yasan an haifi d’an lele kuma d’an gata, anyi suna Lafiya an tashi Lafiya inda yaro yaci sunan shi Muhammad Sabeer wanda Dr Ahmad d’an fillo ya rad’a mishi sunan da kanshi, inda kuma ya bawa Dr Faridah kyautar wani gida babba mai kyau da wata had’add’iyar mota jeep duk gift ne na jin dad’in haihuwar Sabeer, Hajjah Hauwaa kuwa gift d’in sark’ar gold ta bata tsadaddu dasu tun daga sark’a, d’an kunne abin hannu (warwaro), sark’ar k’afa da kuma rings guda biyu kud’i sosai ta fitar ta siya mata su.

Haka Sabeer ya cigaba da girma ana ji dashi sosai, makarantar shi dukka a k’asar waje yayi su, Sabeer kyakkyawan matashin saurayi ne d’an shekara 27-28 ya had’u ta ko’ina ga kyau ga kud’i, sai dai sangartacce ne na ajin k’arshe gashi d’an shagwa6a don iyayen shi da kakannin shi sunyi matuk’ar sangartashi, so suke nuna mishi sosai gashi daman shi kad’ai Allah ya basu ba kwa6a ba harara duk abin da yake so suna yi mishi sosai, Sabeer bai ta6a neman wani abu ya rasa ba, duk abin da yace yana so jiki na 6ari ake yi mishi don kada ranshi ya 6aci, gata sosai yake samu gashi yanzu ya kammala karatun shi ya dawo gida.

**** **** ****

CIGABAN LABARI…

Yana fita daga side d’in nasu part’s d’in kakannin nashi ya nufa yana wani yatsina fuska tamkar wani mai jin amai, ya sanyo kanshi cikin babban parlour d’in sai ga wata house girl ta taho fita hannun ta d’auke da tire wanda saman shi jug ne mai d’auke da so6o sanyaye sai k’ananun cups akai guda biyu da d’an wani bowl guda uku ‘yan manya d’aya na d’auke da cup cakes, d’aya kuma egg rolls sai na k’arshen samosa, irin tazo zata wuce ta kusa da Sabeer sai tsautsayi ya sanya tsantsin tiles ya kwashe ta gaba d’aya tayi baya kayan hannun ta kuma suka yi kan Sabeer.

Unexpected yaji saukar abu mai sanyi da d’umi a jikin shi sai wani cup d’aya da ya fad’o kan k’afar shi ya had’u da tiles ya tarwatse har ya yanki Sabeer a k’afa kad’an jini ya fito, baisan lokacin da ya bud’e baki ya kwalla wata k’ara mai k’arfi tare da yin wani tsalle don ba k’aramin firgita yayi ba don ko kula da tahowar ta bai yi ba, ga zafin yankewar da yayi.

Hajjah Hauwaa tana bedroom d’in ta taji k’arar d’an lele da sauri ta tashi ko takan d’an kwalin ta bata bi ba tayo downstairs da d’an gudu irin na tsofaffi a rud’e.

House girl d’in nan kuwa tuni ta tashi daga fad’uwar da tayi a k’asa duk da kuwa zafin da taji na fad’uwar haka ta daure ta tashi ta tsugunna tana kuka tare da bawa Sabeer hak’uri, don tun kafin ya dawo ake jan kunnen su da 6ata mishi rai su kiyayi 6acin ran shi, sai gashi yau tsautsayi ya ritsa da ita daga dawowar shi jiya.

Sabeer tsalle da ihu kawai yake yi, a dai dai lokacin Alhj Ahmad d’an fillo ya sanyo kanshi cikin parlour ranshi a 6ace, saboda bak’on da yayi yana jiran a kawo musu abin ta6awa a baki ba’a kawo ba shine ya taso da kanshi, abin kamar a mafarki yaji ihun Sabeer aikuwa da sauri ya k’arasa parlourn jiki na 6ari.

Lokaci d’aya Alhj Ahmad d’an fillo da Hajjah Hauwaa suka shigo parlourn, wajen Sabeer gaba d’aya suka yi cikin matuk’ar tashin hankali don sam basu kula da house girl d’in da take durk’ushe tana zunduma kuka.

Alhj Ahmad d’an fillo janyo Sabeer jikin shi yayi ya rungume shi cikin rawar murya ya fara cewa
“Sabeer what happened to U?
“waya ta6a min kai? ”
Duk wannan tambayar Alhj Ahmad d’an fillo yayi ta a rud’e.

Cikin sangarta da salon shagwa6a Sabeer ya nuna jikin shi da k’afar shi da take fitar da jini, a kid’ime suka kalli jikin nashi da k’afar shi saboda tsabar rud’ewa sai yanzu suka kula, cikin tashin hankali Hajjah Hauwaa tace

“wa yayi maka wannan rashin mutuncin Sabeer? ”
Ta fad’a tana mai dafe kirjin ta tare da zaro idon ta waje, Alhj Ahmad d’an fillo kuwa saboda tsabar tashin hankali kasa magana yayi sai zuciyar shi da take bugawa da k’arfi.

Hajjah Hauwaa ta kama hannun Sabeer tare da cewa
“Sabeer open your mouth and explain me please ”

Bai yi magana ba sai hannun shi da ya d’aga dakyar ya nuna saitin da ‘yar aikin take tsugunne tana kuka jikin ta na rawa, zaro idanun su suka yi lokaci d’aya sannan Alhj Ahmad d’an fillo ya bud’e baki cikin tsawa mai matuk’ar firgita wa yace
“keeee zo nan ”

‘yar aikin a kid’ime ta tashi ta nufi inda suke tsaye, jikin ta na matuk’ar rawa ga hawaye na zuba a idanun ta, hannun ta gaba d’aya a saman kanta don tasan ita yau ta ta, ta k’are….13/14

About Ismail

Check Also

BAKAR INUWA CHAPTER 23

Ganin taƙi cin komai Anne ta kira sunanta. Ta ɗago domin amsawa taci karo da …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *