[Advertisements⬇️]

SANADIN SONKI CHAPTER 6 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

SANADIN SONKI CHAPTER 6

 

 

 

Yana fito wa daga bathroom yaga Mummy bata cikin bedroom d’in, ta6e fuska yayi kamar zai saki kuka ya dafe gishin shi yana cewa
“Oh my God shine Mummy kika gudu koh? ”
Yana gama fad’in ya k’arasa wajen tafkekiyar wardrobe d’in shi ya bud’e ta a kasalance, don Sabeer ba k’aramin sangartacce ba ne komai idan zaiyi a sangarce yake yi.

Dakyar ya iya d’auko wani white 3quater da T-shirt yellow mara hannu ya sanya su, tukunna ya k’arasa wajen dressing mirror ya gyara gashin kanshi sannan ya sanya perfumes different colour designer, masu matuk’ar k’amshi yana gama wa ya sanya hannun shi ya d’auko d’aya daga cikin favorite phone nashi.

Sannan ya nufi hanyar fita daga d’akin nashi, idan mutum ya kalle shi sai ya zaci irin jarumin namijin nan saboda k’irar k’arfi da yake da ita, amman idan mutum yasan irin yanda yake matsoraci gashi sangartaacce ne na ajin k’arshe, don iyayen shi ba k’aramin sangartashi suka yi ba gashi Shagwa66e6e ne.

Cikin takun tafiyar shi ta kalar Shagwa6a ya k’arasa sauka zuwa k’asan stairs, kai tsaye inda parents d’in shi suke ya nufa a dinning table inda suke breakfast, wajen dinning table d’in kanshi abin kallo ne ya had’u sosai gashi babba wanda a k’alla zai d’auki mutum goma.

Suna hango shi suka fad’ad’a fara’ar su kallon shi suke cikin so da k’auna tamkar yau suka fara ganin shi, a tsakanin Mummy da Daddy baza ka iya tantance wanda wani yafi k’aunar tilon d’an su ba, tashi Daddy tsaye yayi tare da yin hugging d’in shi har da wani bubbuga bayan shi kad’an yana cewa
“My lvly son good morning”
Cikin shagwa66iyar murya Sabeer yace
“Morning Dad ”
Bayan sun gama gaisawa Daddy yaja mishi kujera ya zauna, sannan yace
“Son me zaka ci Mummyn ka tayi serving naka ”
“Nothing”
D’an zaro ido yayi kad’an yana kallon Sabeer kafin yace
“What! Son kasan bazan barka da yunwa ba don haka oya tell me ”
Duk wannan maganar da suke Sabeer ko kallon inda Mummy take bai yi ba sai wani 6ata fuska yake tamkar irin wanda ake mintsina sannan aka hana mutum kuka haka Sabeer yake.

Ganin hankalin Daddy ya tashi ne yasa shi cewa
“Okay Daddy na don’t worry, a bani one cup of coffee ma”
“Yawwa Son ko kai fa ”
Sai lokacin hankin Daddyh ya kwanta but yasan an 6atawa Son nashi rai cox haka yake fushi da abinci idan an 6ata mishi rai.

Cikin murmishi Mummy tace
“I’m so sorry my son nasan dalilin fushin ka”
Ta k’arasa fad’a tana rik’o hannun shi cikin sigar rarrashi take mishi magana, kallon ta Daddy yayi tare da cewa
“Oh I know ke kika 6ata mishi rai, tun da naga yak’i kallon inda kike ”

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

“Bafa wani abun babba ne ba fah Daddy”
Cewar Mummy.
“Fad’a min abin da ya had’a ku ”
Murmishin dai har yanzu Mummy take tana had’a wa Sabeer coffee sai da ta gama had’a shi tukunna ta bawa Sabeer cup d’in a hannun shi, sannan ta kalli Daddy da har yanzu kallon ta yake yana jiran ta fad’a mishi abin da ya had’a ta lvly Son d’in shi.

Cikin yanayin k’sisina da karya murya tana wani fari da eye’s nata tace
“Daddy ka tuna lokacin da na sanar da kai idan Son ya gama karatun shi zan had’a mishi party na gayyato k’awaye na da abokanan arzik’i mu taya shi murnar kammala karatun shi lafiya, akan na sanar da shi fah ya fad’a min baya so shine ni kuma nace yayi hak’uri zan yi, shine fah yake fushi da Mummyn shi ”

D’an murmishi Daddy yayi don yasan halin Mummy wajen son nuna wa duniya d’an nata d’an gata ne duk abin da Sabeer yake so a wajen ta zata siya mishi indai akwai shi a duniyar nan, bata wasa da al’amarin Sabeer indai kuwa abin yayi mata tana rawar jiki zata yi mishi.

Kallon Sabeer yayi yaga ko kallon inda suk bai yi ba hankalin shi yana kan wayar time to time yana kur6ar coffee nashi tamkar baisan abin da suke magana akai ba.

Daddy ya rasa yanda zai yi baya son 6atawa d’an nashi rai haka kuma baya son ran Mummy ya 6aci, gashi ta zuba mishi eye’s d’in ta da suke matuk’ar rud’a shi sai wani salo na daban take mishi.

Da ido yayi wa Mummy alamar bari ya gwada rarraso shi, hannun Sabeer ya rik’o tare da cewa
“My son kayi hak’uri da abin da Mummyn ka zata yi, kasan saboda son da take maka shi yasa take yin komai don taga ta faranta maka rai, gashi ta gama kashe kud’i masu yawa domin tayi maka abun da zai sanya ka farinciki, please Son kayi hak’uri ka bata wannan damar kada kace a’a son ”

Shiru suka yi dukannin su suna jiran abin da d’an lele zai ce, cikin zuciyar Mummy tana addu’ar Allah ya sanya Sabeer ya amince, sai da ya k’arasa shanye coffee d’in shi tukunna ya mik’e tsaye har ya juya bayan shi zai tafi.

Gaba d’aya Mummy ta gama hak’ura da zai amince da party, sai kuma suka ji amon sautin muryar shi yana cewa
“Alright naji Mummy but 30 minutes only zanyi a wurin ”

Yana gama fad’in haka ya juya ya tafi, cikin Farinciki Mummy tace
“Yes! Daddy i can’t believe ya amince min”
Murmishi Daddy tare da cewa
“Daman kece baki bishi ta rarrashi ba kinsan d’an naki sometimes sai da rarrashi ”
Mik’e wa tsaye suka yi Mummy saboda jin dad’i tayi hugging d’in Daddy tare da bashi peck a cheek d’in shi.
Murmishi suka sakarwa junan su a lokaci d’aya, tukunna Daddy yace
“Hey Mrs Hussein d’an fillo thanks for ur fantastic kiss”
Fari da eye’s nata Mummy tayi tare da kama hannun shi suka nufi upstairs don ta shirya shi zuwa fita office.

WANE NE SABEER HUSSEIN D’AN FILLO?11/12

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]