[Advertisements⬇️]
[Continue Reading⬇️]
SANADIN SONKI CHAPTER 5
Haka lokaci ya cigaba tafiya, zumunci tsakanin Suhaima da Jiddah ya k’aru sosai wanda takai duk weekend sai ta zo ganin Suhaima, sai dai Aliyu sam yak’i bata fuskar ta tambaye shi taje gidan su Jiddah, sai dai ita duk weekend k’afar ta yana hanyar zuwa gidan su Suhaima ko kad’an bata damu da rashin zuwan Suhaima gidan su ba, tasan komai lokaci ne akwai lokacin da zata zo mata gidan su, aminci sosai suke yi.
Haka Aliyu, Aliyah dasu Babaa Lantana da Baba Adamu duk sun saki jiki sosai da Jiddah, saboda kirkin yarinya ga kuma yanda take girmamasu, duk da sun san daga gidan kud’i ta fito, don da ganin irin sutturar da take sanya wa da irin motar da ake kawo ta a ciki kasan iyayen ta ba k’aramin masu kud’i ba ne, gashi indai zata zo kowa a cikin su da irin tsarabar da take kawo mishi, musamman Suhaima k’awar ta, yini guda cur zata yi musu suyi ta zagaya gonar Yaya Aliyu da wurin da ya ke6en ce don yi kiwo a ciki, sam Jiddah ko a fuska bata nuna tana kyamar su.
Ana cikin haka exam d’in su Suhaima ta fito taci wata makarantar secondary da take a birni, nan Yayan ta yayi mata ciko ciko ta samu gurbin karatu na jss 1.
Cikin k’ank’anin lokaci Suhaima ta fara zuwa makaranta, Jiddah tayi murna sosai da cigaban makarantar Suhaima, gashi kuma Jiddah idan tazo wani lokacin tana k’ara fahimtar da ita wasu abubuwan na fannin boko, ga kuma kwalliya da gayu da take koya mata, saboda Jiddah tana son duk ranar da Suhaima zata gidan su ya kasance ta iya komai na wayewa yanda ‘yan uwan ta basu su kyamace mata ko su raina saboda sanin halin su da tayi, sosai Suhaima ta mayar da hankalin ta tana karatu babu wasa, Aliyu ne mai kaita ya kuma d’auko ta daga makaranta yana alfahari da ‘yar k’anwar tashi.
*** *** ***
AFTER SIX YEARS
“Suhaima! Suhaima!! Suhaima!!! ”
Naga wata matashiyar kyakkyawar yarinya chocolate colour tana tsaye a tsakar gida tana kwallawa Suhaima kira, nima gaba d’aya na baza ido na hango fitowar Suhaima don na kwana biyu ban lek’o gidan ba daukan rahoto lol.
Wata kyakkyawar yarinya na hango tana fitowa daga d’aki da gudu jikin ta sanye da wata gown ash colour mai touch d’in red a jiki, gashin ta a sake ya kwanta a gadon bayan ta hannun ta na rik’e da veil na gown d’in shima red colour.
Da gudu ta k’araso wajen matashiyar yarinyar nan mai kiran ta, tana zuwa ta rungume ta tana dariya ita ma d’ayar dariya take, kafin kuma ta d’an ture ta tana 6ata fuska tace
“Ni ai nayi fushi Jiddah da ke ace ranar graduation d’ina ki k’i zuwa koh”
Wadda aka kirawo da Jiddah ta langa6e kai tare da cewa
“I’m so sorry friend kinsan a time d’in na tafi raka Ammi na london yin check off, nima kaina ban ji dad’in hakan ba please forgive me ”
Wani kyakkyawan mirmishi Suhaima ta saki wanda ya fallasa dimple d’in ta sannan ta rik’o hannun Jiddah tace
“Tsokanar ki nake besty kinsan Yayah Aliyu ya fad’a min ”
“Yawwa tawan har naji dad’i ”
Sake rungume juna suka yi suna dariya, Yaya Aliyu da Aunty Aliyah suna tsaye suna kallon su sai murmishi suke su ma.
A dai dai lokacin kuma driver d’in da ya kawo Jiddah ya fara shigo da kaya yana ajiye wa, sakin juna suka yi sannan a lokacin idanun Jiddah suka sauka akan Yaya Aliyu da Aunty Aliyah sunkuyar da kanta tayi cikin jin kunya tace
“Auuu Yaya Aliyu da Aunty Aliyah daman kuna nan, ai ni ban kula da ku ba ”
“Daman ina zaki kula damu hankalin ki yana wajen Suhaima ”
Cewar Aunty Aliyah tana rik’e ha6a, Yaya Aliyu kuwa ban da murmishi babu abin da yake.
Langa6e kai tayi cikin shagwa6a ta had’e hannayen ta biyu waje d’aya tare da cewa
“Afuwan Babban Yaya da Aunty na bazan k’ara ba ”
Dariya suka sake yi kafin Suhaima ta rik’e hannun Jiddah taja ta zuwa cikin wata rumfa wanda aka ajiye wasu kujeru na sak’i, zama ake akan su don hutawa, gaba d’ayan su suka zauna ana hira cikin farinciki da annushuwa, kafin daga bisani Jiddah ta d’auko wani kwali ta bud’e sai ga chocolate cake ya bayyana, nan ta ajiye shi saman table d’in da yake ajiye inda suke zaune, sannan ta tashi da sauri ta nufi kitchen.
Bata jima ba ta fito hannun ta rik’e da ashana, su dai bin ta da ido kawai suke, tana zuwa ta kunna ashanar ta sanya wutar jikin d’an candle d’in da yake tsakiyar cake d’in wanda ake sanyawa a jikin cake, kamo hannun Suhaima tayi sannan tace
“Are you ready? ”
Gid’a kanta Suhaima tayi fuskar d’auke da murmishi, babu 6ata lokaci suka hure wutar a tare sannan suka yanka cake d’in kowacce ta bawa ‘yar uwar ta a baki, sannan Suhaima ta bawa Aliyu ita kuma Jiddah ta bawa Aunty Aliyah.
“Happy graduation sister ”
Rungume Jiddah tayi tare da cewa
“thank you so much dear”
“Haba never mind ‘yar uwa”
[Advertisements⬇️]
[Continue Reading⬇️]
Daga nan Yaya Aliyu ya fita Aunty Aliyah kuma ta wuce kitchen, sannan Suhaima da Jiddah suka kwashe kayan da ta kawo wa Suhaima suka wuce cikin d’akin Suhaima, kan bed suka zube suna hira don sun jima basu had’u ba.
Yinin ranar hira sosai suke har Jiddah na bawa Suhaima labarin an kawo kud’in ta an sanya rana nan da two month’s biki su Abban ta suka sanya, da yake kuma Jiddah har ta shiga University tana level 2, mass com take karanta bata da ra’ayin sai ta gama schl zata yi aure, ta fison tana cikin karatun tayi idan yaso zata k’arasa a gidan ta da yake iyayen ta irin basu da shiga hak’ik’in yaran su a kan abin da suke so suna yi musu, sai dai idan abu bai yi musu wannan ne kuma akwai tashin hankali.
Suhaima ta taya murna sosai tare da yi mata fatan alkhairi tare da alk’awarin zuwa gidan su biki, d’an hararar ta tayi tare da cewa
“Ba daga baki ba fad’ar Allah yasa ki zo ”
Dariya ce ta tahowa Suhaima da sauri ta sanya hannu ta rufe bakin tana cewa
“Ni na isa ace bikin besty guda ban je ba, da ban yiwa kaina adalci ba ”
“Kada ki zo d’in yarinya kiga yanda ake rashin mutunci ”
“Ah Ah ma basai kinyi rashin m ba zan zo ba ”
Daga nan kuma ta fara kok’arin tafiya gida ganin yamma tayi, Yaya Aliyu da Aunty Aliyah sun taya Jiddah murna sosai na auren da zata yi sannan sun yi mata alk’awarin zuwa idan lokacin yayi, sannan tayi musu sallama ta tafi, har wajen mota Suhaima ta rako ta suka sake yin sallama sannan ta shiga motar ta rufe driver yaja motar suka tafi suna d’aga wa junan su hannu, sai da motar ta k’ule Suhaima ta daina hango ta tukunna ta sauke hannun ta tare da sauke numfashi ta wuce cikin gidan su zuciyar ta fal farinciki yau Jiddah tazo don rabon da tazo anyi wajen one month’s.
*** *** ****
Wata hamshak’iyar mata na hango tana rik’e handle d’in kofar wani d’aki tana bud’e wa tare da shiga ciki, kallo d’aya zaka yiwa matar kasan ta jik’u da naira, d’akin duhu dulum da ta shiga ciki.
Da yake ta lak’anci wajen makunnar bulbs na bedroom d’in sai ta k’arasa ta kunna nan take haske ya gauraye cikin d’akin, wow nice room na furta lokacin da naga had’uwar d’akin, komai na d’akin blue and white ne hatta fentin bangon d’akin gashi k’ato ne room d’in sosai.
Kai tsaye matar wajen tafkeken Italian bed d’in ta nufa, inda one and only lovely son nata yake sleeping hankalin shi kwance, ya lullu6e hatta kanshi da lallausan blanket wanda ya kasance shima blue ne and kwalliyar flower’s white ajikin shi.
Zama tayi gefen bed d’in tare da sanya hannun ta tana bud’e blanket d’in, har tayi nasarar bud’e face d’in, tubarkallah masha Allah nace a time d’in da na hango beautiful face d’in shi, bacci yake amman fuskar shi a sake tamkar wanda yake murmishi.
A hankali ta sanya hannun ta tana bubbuga shi a nutse tana cewa
“Hey son wake up ”
Sai da ta fad’i hakan sau biyu ana ukun ne ya fara bud’e lumshashshun eye’s nashi wanda dogayen eyelashes ya rufe su, ya kallo Mummyn tashi cikin muryar shagwa6a yace
“Why Mummy da zaki tashe ni a bacci, shiyasa sam ban so na dawo nigeria ba coz yanzu za’a fara sawa mutum headache ”
Ya k’arasa fad’i yana yatsine fuska, da kan ganshi kasan d’an shagwa6a ne na ajin k’arshe ma.
Murmishi Mummy ta saki tare da cewa
“Haba my son kasan yau ne na had’a partyn murnar dawowar ka gida lafia da kammala karatun ka koh”
D’an yatsina fuska yayi tare da sake 6ata fuska yace
“No need Mummy kinsan ban son hayaniya right? ”
Hannun ta ne saman gashin kanshi tana shafawa tace
“Nasan da haka son but kamar kai ka dawo daga wata k’asar ka kammala karatu cikin sa’a kace bazan had’a party ba I’m sorry to say son sai nayi ”
Bai kulata ba ya yaye blanket d’in jikin shi ya zuro k’afafun shi a k’asa tare da tashi tsaye daga shi sai short niker white colour irin skin tight d’in nan ya wuce toilet a fusace, don sam bai jin dad’in dage wa da Mummy tayi ba aka wannan party da ta had’a mishi.
Da murmishi Mummy ta bishi da kallo cikin so da kaunar shi tace
“Son d’an rigima kenan, bazan biye maka balle ka hanani nuna wa duniya cewar kai d’an gatan family d’in Alhaji D’an fillo ba ne gaba da baya ”
Tana gama fad’in haka ta bar bedroom d’in don ba k’aramin aikin son ba ne yasa ta a gaba ba sai ta shirya shi saboda tsabar gata da sangarta irin ta d’an nata SABEER… 9/10
[Advertisements⬇️]
[Continue Reading⬇️]