[Advertisements⬇️]

SANADIN SONKI CHAPTER 11 - Bankinhausanovels
Thu. Oct 6th, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

SANADIN SONKI CHAPTER 11

 

 

 

 

Sai da ya daina ganin su tukunna ya dawo da idanun shi jikin shi inda yaga yanda ya jik’e sharkaf da ruwa, wani irin sanyi ne yake ji yana ratsa cikin jikin shi sosai.

“Yalla6ai kayi hak’uri don Allah kada ka fad’awa su Alhj da Hajia nasan korata zasu yi, ka rufa min asiri amman sam wannan yarinyar bata kyauta ba ”

D’an murmishi Sabeer yayi ya bud’e baki zai yi magana atishawa ta taho nan ya fara yin ta sai da ya jira ta sau 4 tukunna ta tsaya, driver sai sannu yake yi mishi gaba d’aya hankali shi a tashe.

“Don’t worry driver kwantar da hankalin ka mu tafi gida sanyi nake ji ”

Sai lokacin driver ya d’an ji hankalin shi ya kwanta, da sauri driver ya bud’e mishi kofar mota ya shiga sannan ya rufe tare da komawa driver sit ya zauna tukunna yayi wa motar key suka bar wajen.

Sanyi sosai Sabeer yake ji ga atishawar da yake faman yi but still idanun shi nakan hanyar da Suhaima tayi, sosai yake jin wani abu game da yarinyar da ya gani tsiwar ta ta birgeshi yana fatan ya sake sanya ta a cikin idanun shi anan gaba.

Har suka kusan k’arasa wa gida Sabeer na tuna abin da ya faru tsakanin shi da Suhaima yana wani murmishi shi kad’ai, abin ba k’aramin mamaki yake bashi ba ganin ta tsaye mishi a rai, gate man yana bud’e gate Sabeer ya hango ilahirin Iyalan Alhj Ahmad d’an fillo sun firfito suna tsaye kallo d’aya mutum zai yiwa Alhj Ahmad d’an fillo, Hajjah Hauwaa da Alhj Hussien Daddy da Hajia Faridah Mumy a karanto tsantsar tashin hankali saboda sun nemi d’an lele an rasa inda yake kuma ba’a san inda ya tafi ba ga wayar shi a gida ya barta, tuni jikin driver ya fara 6ari na tsoro.

A hankali Sabeer ya bud’e motar ya fito ko driven bai tsaya jira ba, suna ganin fitowar shi suka saki ajiyar zuciyar kwanciyar hankali tare da tahowa inda yake hankalin su a tashe ganin jikin shi jagwab da ruwa, cikin rud’ewa Alhj Ahmad d’an fillo ya rik’o kafad’un Sabeer yace

“Sabeer wane shege ne ya jik’a ka haka? ”
D’an murmishi Sabeer yayi kafin yace
“Ba damuwar ku bace kada wanda ya sake min wani tambaya ku rabu da ni and then kada wanda yace zai tak’urawa driver ya fad’a mishi ”

Yana gama fad’in haka ya jiyo zai tafi da sauri Mumy ta rik’o hannun shi tare da cewa
“Amman son…….. ”
Bata k’arasa fad’in abin da zata ce ba ya dakatar da ita da hannun shi tare da cewa
“Please Mumy ”
Ya zame hannun shi yayi gaba zuwa part d’in su, gaba d’aya jikin su yayi sanyi sosai kuma hankali ya tashi sosai musamman ganin shi a jik’e kuma yana ta atishawa, suna ganin driver ya wuce ta gaban su bayan ya gama parking motar basu da ikon yi mishi magana saboda kada su 6atawa Sabeer rai.

Sabeer yana shiga bedroom d’in shi toilet ya shige wanka yayi da ruwan d’umi tukunna ya fito ya gyara jikin shi tsaf cikin wani 3quater ash colour da T-shirt white mara hannu, fesa different perfumes yayi bayan ya gama ya kwanta tare da lullu6e jikin shi da lallausan blanket, lumshe idanun shi yayi tamkar mai jin bacci amman ba baccin yake tunanin kawai Suhaima yake ya dad’a tuno d’an k’aramin bakin ta tana mishi tsiwa, shi kad’ai yake juyi kan bed yana murmishi, yana tuna yanda ta watsa mishi ruwa ta gudu dakyar bacci ya d’auke shi mai nauyi zuciyar shi fal tunanin yarinyar da suka had’u da ita.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Duk wannan abin da yake Mumy na tsaye ta jikin window duk abin da yake tana kallon shi cike da mamakin murmishin da yake, tana tunanin me yake tunani haka yake irin wannan murmishin, ganin ya samu bacci ne yasa ta bar jikin windown zuciyar cike da tunani.

 

 

***** ******** *****

 

Suhaima sai da ta k’arasa kofar gida tukunna ta tsaya da gudun da take, sai da ta daidaita kanta sannan ta shiga gidan da sallama a nutsen ta, kamar ba itace mai gudu yanzu ba, Aunty Aliyah da ke zaune kan kujera tana wankin kaya ta amsawa Suhaima sallamar tana d’ago kanta ta kalle ta tare da cewa
“Suhaima sai yanzu kin dad’e yau hala surutun kuka yi aka tsayar da ku ”

Wata dariya ce ta kubce wa Suhaima ta fara yi har da rik’e ciki da hawaye, cikin mamaki Aunty Aliyah take kallon ta kafin ta kuma cewa
“Lafiya Suhaima dariyar me kike haka? ”

Amman Suhaima ba bakin magana sai da dariyar ta take, sosai Aunty Aliyah ta saki baki da hanci tana kallon Suhaima da ke dariya tamkar wata mahaukaciya har abin ya fara bata tsoro har ta fara tunani ko gamo tayi a hanyar makaranta, dakyar Suhaima ta tsayar dariyar saboda ganin yanda Aunty Aliyah ta fara rawar jiki na tsoro, zama tayi kan saman kayan wankin da Aunty Aliyah ke wankewa tace

“Aunty wani abu ne ya faru lokacin da nake tahowa gida shi yasa kika ga ina dariya ”

Ajiyar zuciya Aunty Aliyah ta sauke ta kwanciyar hankali don sai yanzu taji hankalin ta ya kwanta, kafin ta bud’e baki tace
“Me yafaru? ”

Nan Suhaima ta bata labarin abin da ya faru tsakanin ta guy d’in nan, don Suhaima bata iya 6oyewa Aunty Aliyah abu saboda shak’uwar da suka yi da juna sosai sun zama tamkar wasu k’awaye ko irin Yaya da k’anwar ta, sosai abin ya bawa Aunty Aliyah dariya don har yanda Sabeer yayi Suhaima take kwatanta mata, cikin dariya tace
“Allah ya shirya ki Suhaima, yanzu da ace ya kama ki fah ko ya mare ki ”

“Tabbb da sai na rama Aunty duk da yafi ni tsayi sai nayi tsalle na rama, amman fah Aunty kyakkyawa ne kingan shi tamkar wani balarabe mybe ma baya jin hausa shi yasa yake kallo na ”

“Uhm Allah dai ya kyauta, amman Suhaima ki daina irin wannan gangancin don kada ki tsokani wani wataran mara hak’uri ya cutar mana da ke ”

“Toh Aunty na daina insha Allah, har yanzu Yaya bai dawo ba? ”
“Eh bai dawo ba mybe akwai abin da ya tsayar dashi ”
“Allah ya dawo dashi lafiya ”
“Amin ”

D’an shiru suka yi na ‘yan minutes Aunty Aliyah na cigaba da wanki, can tace
“Ni kuwa Suhaima ina Jiddah ne kwana biyu shiru? ”
D’an murmishi tayi tare da cewa
“Aunty Jiddah tana nan lafiya, hidimar biki ce ta sanya ta a gaba amman mun yi waya da ita jiya da yamma a wayar Yaya ”
“Oh haka ne fah sauran kwanaki nawa auren ”

“Sauran 2 week’s fah Aunty gashi na rasa me zan siya mata matsayin gift’s ”
Suhaima ta karasa fad’a cikin yanayin damuwa.

“Kada ki damu anjima zamu yi magana yanzu kije ki cire uniform kizo ki karya tukunna”

“Toh Aunty ”
Tashi tayi ta nufi bedroom nata don canja kayan jikin ta, bayan ta canja kaya ne sai kawai ta k’urawa mirror ido tana kallon shi, ta fad’a tunani beautiful guy d’in da ta yi mishi tsiwa d’azu ta d’an jima tana tunanin shi a haka har sai da Aunty Aliyah taji ta shiru ta fara kwalla mata kira tukunna ta sauke ajiyar zuciya ta fito waje tana amsa kiran da take mata…22

 

 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]