[Advertisements⬇️]

SANADIN SONKI CHAPTER 10 - Bankinhausanovels
Mon. Mar 27th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

SANADIN SONKI CHAPTER 10

 

 

 

 

Sabeer yana tsaka da yin sleeping nashi mai dad’i yaji tsikar jikin shi yana tashi, wani yanayi yana shigar shi a hankali mara fasaltuwa ya rasa tantanci shin mafarki ne ko ido biyu yake jin haka.

Fitinannen k’amshin Fadilah ne ya cika kofofin hancin shi har takai da ya fara kok’arin bud’e idon shi, gaba d’aya Sabeer ya gama tsorota don yana tunanin ko aljanna ce ta zo mishi tun da a lokacin ya tabbatar da ba mafarki ba ne kuma yasan wace mace ce zata zo mishi a wannan daren idan ba aljanna ba, har jiki shi ya fara d’an rawa don Sabeer akwai tsoro dakyar ya iya yunk’urin bud’e idon shi ya zuba su akan Fadilah da take kok’arin kissing lips nashi, don ta had’a fuskar ta da tashi daf take da ta had’e lips nasu waje d’aya.

Zaro ido Sabeer yayi cike da tsantsar mamaki yana kallon ta, ranshi a 6aci sosai so yake ya tuna inda ya santa, amman kafin ya tuna d’in tuni Fadilah ta had’e bakin ta da nashi, wasu abubuwa take yiwa Sabeer wanda duk d’a namiji cikakke mai lafiya bazai iya jurewa ba, tuni Sabeer ya fara sakin layi yana mayar mata martanin abin da take mishi.

Tuni Fadilah an saki jiki sosai tayi luf a jikin Sabeer tana mai kar6ar sak’onnin da yake aika mata dashi cikin rawar jiki, sun yi nisa cikin wannan yanayin sosai kamar wanda wutar nepa taja haka Sabeer yaji a jikin shi wanda ya haddasa mishi barin jikin Fadilah da sauri ya mirgina can k’arshen bed d’in, yana mayar da wani irin numfashi tare da sauke ajiyar zuciya.

Kafin kuma ya fara tunanin abin da ya kusan faruwa a yanzu tsakanin shi da Fadilah, zumbur ya mik’e tsaye yana furta kalmar innalillahi wa’inna ilaihir raju’un yana dafe da kanshi cikin zuciyar shi yana mai godewa Allah da ya tseratar dashi daga hannun wannan shaid’aniyar ‘yar iskar yarinya.

A zuciye yayi kan Fadilah wanda idanun ta a lumshe tana jiran Sabeer ya fara aiki gaba d’aya cikin wani buk’atuwa take dashi, don ta d’auka ya tsaya cire 3quater d’in jikin shi yake, don haka ita ma sai ta fara kok’arin k’arasa cire sleeping dress d’in jikin ta daman gashi room d’in babu haske sosai, don haka bata ga tahowar Sabeer wurin ta ba bata kai da gama cire rigar ba a fusace yakai hannun shi saman fuskar ta ya wanka mata mari har guda biyu wanda sai da Fadilah taga wasu star’s a idanun ta jinta ya d’auke na wucan gadi, don tun da Maman ta ta haifeta ba’a ta6a yi mata irin wannan marin ba, kafin ta dawo hayyacin ta daga marin Sabeer ya zage iyakar k’arfin shi ya hau dukan ta da belt, tuni Fadilah ta fara ihun kuka da neman agaji da k’arfi sosai take ihun wanda ya sanya k’arar ihun ta ya tashi Mumy da Daddy daga baccin su, a kid’ime suka fito daga bedroom d’in Daddy suka yo d’akin Sabeer don tanan haka suke jin k’arar ihun.

Da k’arfi suka tura kofar suka shiga hankalin su a tashe sosai, ganin duhu ne ya sanya Daddy kunna bulbs d’in room d’in tuni haske ya gauraye d’akin, hango tilon d’an su suka yi yana dukan Fadilah cike da fusatar da basu ta6a tsammanin yana da ita ba.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Da sauri Daddy ya nufi wajen shi yana cewa
“Son What wrong with U? ”
Amman Sabeer bai kula shi cigaba yake da dukan ta kawai wanda yanzu babu bakin kuka sai hawayen da suke zuba cikin idanun ta, ganin bazai tsaya da dukan ya sanya Daddy rik’e shi gam a cikin jikin shi tare da kallon Mumy yace
“Janye Fadilah ki fitar da ita ”
Jiki ba kwari Mumy take kok’arin d’aga tana kallon fuskar d’an nata wanda take hango kwantaccen 6acin rai akan fuskar tare da wasu hawaye da suke zuba a kan fuskar tashi gaba d’aya sai taga ya rikid’e mata ya zama wani mutum na daban kamar ba Sabeer ba, gashi idanun shi sunyi ja da fuskar shi, jikin Mumy gaba d’aya yayi sanyi haka ta ja Fadilah suka fita daga bedroom d’in ta tana tunanin me ya had’a Fadilah da Sabeer har yayi mata wannan mugun dukan.

Bayan sun fita daga bedroom d’in Daddy ya zaunar da Sabeer kan bed amman sai Sabeer ya zame ya zauna akan lallausan carpert d’in d’akin ya dafe kanshi da dukka hannu biyun yana hawaye wai yau shine yake kok’arin aikata zina wannan wacce irin bak’ar rana ce a wajen shi.

Bottle d’in faro Daddy ya d’auko a frige tare da glass cup ya tsiyaya a ciki tukunna ya rufe bottle d’in ya d’ora saman frige sannan ya k’arasa wajen Sabeer ya dafa mishi kafad’a tare da d’ora mishi bakin cup d’in a tsakanin lips nashi bai yi musu ba ya bud’e bakin ya sha ruwan sosai tukunna ya zame bakin shi ya kwanta a k’asan yana d’ora kanshi saman k’afafun Daddy.

Hannun shi Daddy ya sanya yana shafa lallausar suman kan Sabeer sun d’auki wajen 5 minute a haka, tukunna Daddy yace
“Sabeer sanar da ni abin da ya faru tsakanin ka da Fadilah har kayi mata wannan mugun dukan? ”
dakyar Sabeer ya iya bud’e bakin shi yace
“Ba komai ”
Hangame baki Daddy yayi yana kallon shi cikin mamaki har zai sake magana sai ga Mumy ta shigo room d’in cikin tashin hankali zata fara magana Sabeer ya dakatar da ita yana cewa

“Mumy leave me alone please”
Zata matso kusa dashi da sauri ya tashi ya koma saman bed ya kudundune cikin blanket zuciyar sai wani tafasa take sosai yake jin haushin Mumy don yasan duk ita ce ta nuna mata room d’in shi, kallon Daddy Mumy tayi ta marairaice fuska hannun ta ya rik’o tare da cewa
“Yana buk’atar hutu ne na fuskanci ranshi a 6ace yake sosai ”
Cikin damuwa Mumy tace
“Yanzu bai fad’a maka abin da ya faru nima Fadilah tak’i fad’a min sai kuka kawai take”
Ta k’arasa maganar tamkar zata fashe da kuka, cikin kwantar da hankali Daddy yace
“Ki bari zuwa gobe nasan ya huce zai yi bayani amman nasan Fadilah tayi mishi laifi babba ”

Haka suka fito duk jikin su a sanyaye sosai baccin ranar basu iya bacci ba tsakanin Sabeer, Mumy, Daddy da kuma Fadilah kowa sai juyi yake akan bed da tunani kala kala cikin zuciyoyin su.

Bayan sallahr asubah ne Sabeer ya fito daga side d’in su cikin shigar white T-shirt da 3quater yellow ya shiga motar shi k’irar Benz driver yaja shi, sai da suka yi tafiya mai d’an nisa tukunna driver yace
“Yalla6ai ina zamu je? ”
D’an shiru Sabeer yayi yana tunani kad’an kafin yace
“Ina son ka kaini d’aya daga cikin wani k’auye mai kyau da ke makwabtaka da mu ”
D’an murmishi driver d’in yayi tare da cewa
“Angama yalla6ai ”
Yana gama fad’in haka ya nufi wata hanya, yayin da Sabeer ya kishingid’a a bayan motar a hankali yake jin zuciyar shi na yin sanyi… 19/20

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]