[Advertisements⬇️]
[Continue Reading⬇️]
SALOON SO CHAPTER 15
Jawahir ta shigo masa da kayan ciye ciye suka
shiga gaisawa. Faruk ya ce “Mutumin lallai naga
alamar ka warke har da tsarabar dan london ne ko jafan ko dan ijift ne ko America? Naga alamar
kamar jawahir tana da ciki ko?”
Haidar ya yi dariya ya ce “Ai ma ganinku nayi masu
tambaya yanxu kuwa kowa ya kalle ta yaga
shedar aiki ya yi kyau.
Suka kyalkyale da dariya tare da tafawa Faruk ya ce, “Bakinmu da nayi muku dai ya kama ku to Allah
ya raba lafiya, Ubangiji ta sa masu amfani ne ya
bamu masu albarka, don Hafsat tana can da nata
tsohon cikin.
Kai mutumin lallai kayu aiki, to Allah ya inganta
mana, Ubangiji ya raba su lafiya da shi. Bayan sun nutsu sun huta suka bude tsarabobi suka rinka bin
‘yan uwa da dangi suna rabo kowa aka bashi
tsaraba sai ya jinjina kudin da aka kashe masa.
Jikaken abu mai muhimmanci da tsaraba da mutum
sai yaga kamar shi suka yiwa tafiyar. Anty Maryam
ma da Uncle har gida suka zo yi wa su jawahir barka da kuma yi musu sannu da zuwa.
Da yake hutun su suka dakko zasu dade a nan a
gidan Ankul din suke zaune wanda ya zauna farkon
aurensa kafin aiki ya maida shi Abuja.
Jawahir ta
sha murna da ganin Antyna Maryam ta rungume ta suna ta dariya cikin jin dadi da walwala kamar sa
hadiye junansu.
Anty ki ce kin kusa haihuwa don naga cikin naki ya
yi tsini da yawa.”
Ta ce “Haka Ankul dinki yake cewa wannan cikin
ya fiye girma da yawa wai yana takura shi don na fiye langwai.
Jawahir tasa dariya ai gaskiya Anty sai yanzu na
gano sirrin da ya sa Ankul ya ke manne miki ko, na
ce ku ke manne wa juna, ashe haka rayuwar aure
take?
Hakika jawahir rayuwar aure aba ce mai dadi da nishadantarwa kwanciyar hankali da samun
nutsuwa. Amma fa duk wa ‘yannan abubuwan
basa samuwa sai ka yi da ce da abokin rayuwa
nagari.”
Haidar ya yi sallama ya shigo tare da cewa da
Maryam “Antynmu ai kin yi nauyi da yawa, da kin hakura da zuwan da sai muzo har gida mu gaishe
ku.”
Ta yi dariya tare da cewar ai bazan iya jure rashin
ganin diyata ba, yanda ake yi min zuzutun kara
kyan da tayi amma da nazo ai na gani idona ya
gane min kyakkyawar kulawar da ka yi ma ‘yata. Ya yi murmushi ya kalli jawahir ya ce, “Bebina zamu
fita da Ankul xuwa dare zamu dawo.” Ta
marairaice fuska kamar mai shirin kuka ya dafa ta
“Haba bebina mene ne kuma bana so ki bata ranki,
ba ga Antynki nan zata taya ki hira ba, sai mun
dawo zai dauke ta su ta fi. Ta yi murmushi yayin da ta juyo ta kalli Anty maryam. Ta ga ita ba ta saurari
su ma, hankalinta yana kan littafi tana karantawa.
Haidar ya riko ta suka yo falon tsakiya ya zauna a
kujera ya dorata kan cinyarsa “Meye damuwarki
babyna?
Ta yi rau rau da ido har sunkawo kwalla ta ce “Ni ba komai va ne ina tsoron kada Ankul ya sake
cewa ka dawo da Kausar ne, ba zan jure ganin
kana yi mata magana ba bare har ka shiga dakinta
ka kwana mun zama mu biyu da matsayi daya a
wajenka ta saki kuka.
Haidar ya rungume ta yana rarrashinta. “Kar ki damu Bebyna, daman can kaddara da
sha’awar kare kaina daga zina ita ta sani auren
Kausar, ki sa a ranki tsakanina dake mutu ka raba ne
takalmin kaza aurenmu auren zobe ne ba saki
ba yaji ba kishiya har avada.
Kuma na ji wai SULAIMAN BOMBOY za ta aura. Ta ce, “waye kuma SULAIMAN BOMBOY?” Ya ce wani yaro
ne dan karami amma ya nace wai shi a lallai sai ita.
Ta ce, “Um. Ta dako kai da sauri “Allah yayana?
Ya ce, “Sosai ma kuwa ta yi saurin kankame shi
tana sumbatarsa, cikin murna ya dako ta yana
dariya muje kada Ankul ya gaji da jira. Suka fito babban falo jawahir ta ce “Ankul ka bar
min Anty ta kwanar min anan.” Ankul ya girgiza kai
ya ce, jawahir kenan har yanzu
dai kina tare da kuruciya, to idan haihuwa tazo
kuma cikin dare ku yi yaya da ita, ku da kuke duk
farin shiga? Gaba daya suka sa dariya suka fice ita kuma ta
koma gun Anty maryam suka bude shafin hira. “Kin
gane ne Anty ni fa yanzu abun da nake tsoro
kada Haidar ya dawo da kausar don ban san yanda
zan yi ba, a da ban damu da aurenta sosai ba don
sannan ban damu da Yayan ba, amma anya yanzu yanda nake son Yaya Haidar muka shaku da shi
yake sona yana ririta ni yana tarairayata kamar kwai,
zan juri ganinshi da wata matar, wai! Naga
mace a rungume a kirjin Haidar, subhanallahi Allah
[Advertisements⬇️]
[Continue Reading⬇️]
ma ya kiyaye, Anty ai wuka zan soka mata ta mutu
nan take. Maryam ta tuntsire da dariya ta ce “Allah ya kiyaye
jawahir,” Anty maryam ta ce “Ai na gaya miki wasu
matan su suke jawowa kansu ake yo musu kishiya,
na farko akwai matan da girman kai da ji da kai
tsabagen muskilanci ya yi musu yawa, to yawanci
masu irin wannan halin sai ki ga har mazajensu na aure su ke yiwa ko suna mantawa a karkashin
mazajen su suke? Dole mazan su ne gaba da su, dole
ne duk matsayinki da jin kanki, ki sauke su ki
yiwa mijinki biyayya ko dan ki samu tsira ma ranar
gobe kiyama, domin aljannar mace ta na tafin kafar
mijinta sai ya daga zaki shiga. Abu na biyu kuma shine, kazanta, sai ki ga mace awaje dagwas
dagwas da ita amma da zarar ta yi aure ta haihu sai
kiga ta zama kazama. Ba za ta tsaya ta tsabtace
kanta ba bare abincinsu ko abin shansu.
Wasu matan za ki ga kudin da aka ba su na cefane
a ciki zasu raga su boye baza su yo cefanan na duka ba bare su sarrafa girkin yanda zai yi dadi. Sai
mace tai abinci garau garau ba wadataccan kayan
miya bare mai kiji abinci kadas babu dadi abinci
babu kyau a fuska.
Bayan ta gama girkin ba ta san tai wanka ba ta
gyara jikinta, a’a sai ki ganta daga ita sai daurin kirji tana ta fama da kaurin wuta. Da kin doshi dakinta sai
zarnin fitsarin da warin dauda. Kin kai wa namiji
abinci ya yi cokali biyu ko uku ya ji ya kasa ci ya
ture saboda rashin dadi.
Baruwanki da kwantar da murya bare ki bincike
shi me ya hana shi cin abincin, a’a ke babu ruwanki sai ki ja kwanon gabanki ki kama ci ko ki kirawo
yaranki ki ce kuzo ku dau abinci babanku ya rage,
babu ruwanki da damuwarsa.
Idan dare ya yi kina kwance cikin yaranki kin saki
baki kina munshari kin bude nono kin saka wa
yaron da kike goyo a baki kin riga kin sabar masa, sai da nono a bakinsa zai yi bacci, da maigidanki ya
zo ya taba ki don ki taso yana da bukatarki ki kama
miya kina faman zumburar baki ke an takura miki
kin gaji, daren ma ba za’a barki ki huta ba, saboda
Allah mijin nan naki waliye ne da ba zai bukataci
mace ba in har Allah ya kare shi daga sharrin zina? Ai kuwa dole ya yi kokarin karo aure ko dan ya
samu me debe masa sha’awa.
Jawahir ta ce, “Yanzu Anty kina ganin wa’yannan
dalilai zasu taimaka wajen yo wa mace kishiya?
Anty maryam ta ce “Kwarai kuwa ai wadannan su
ne kan gaba, idan mace ta zamo bata daraja mijinta bata ganin mutuncin iyayensa tana wulakanta masa
‘yan uwa da abokanan arzikinsa to yana kara
aure gudun kada ta rusa masa zumunci da ‘yan
uwansa.
Jawahir ta ce, “To ai Anti in kika yi la’akari da wasu
mazan kwata kwata ba su san darajar mace ba, sun dauki mace baiwarsu abar korewa sha’awarsu, don
wani namijin zaki ga namiji yana wasa da
dariya a waje ki ga yana tayiwa ‘yan mata fara’a
yana jansu da wasa, amma da zarar ya shiga
gidansa sai ki ga ya koma kamar mala’ikan
mutuwa ya murtuke fuska babu alamar fara’a bare wasa, da ya ci karo da kwano ko wani abu nata
akan hanya zai bal da shi, kuma yana da rufin
asirinsa amma sai ya ba wa iyalansa dan kalilan din
kudin da ba za su wadaci girkin gidansa ba, ba
ruwansa bai damu da matsalar da suke ciki ba, bai
ja su a jikinsa ba, bare su saki jiki da shi har su dinga bayyana masa damuwarsu. Anty duk irin
wannan ai rashin adalci ne da sanin
darajar mace ko?
Anty maryam ta ce “Haka ne jawahir amma ni a
ganina idan Allah ya hada ka zama da irin
wa’yannan mazan to sai ka iya zama da su. Na farko mace ta dasa wa zuciyarta hakuri, ta zamo
mai juriya da tawakkali, na biyu ta kasance me
yawan ibada tai ta addu’a tana kai kukanta ga
Allah, na uku ta samu sana’a komai kankantarta
kada ta raina ta ta rike ta hannu biyu.
Na hudu ta zamo mai kyautata masa da yi masa biyayya ko dan ta samu tsira ranar lahira. Na biyar ta
kasance me tsafta da kwalliya da kasancewa
cikin kamshi. Na shida ta kasance cikin koyon iya
kissa da kwantar da kanta tana kaskantar da kanta
ko yaushe tana nuna masa shi ne sama da ita, na
bakwai ta kasance doluwa marar wayo ta zamo me kau da kai da duk wani abu da zai mata, na takwas
ta zamo mace me iya kula da rayuwarta wato tana
cin abubuwan da za su kara mata ni’ima a jikinta.
Na tara mace ta iya kwanciyar aure ta gano wace
irin kwanciyar aure mijinta ya fi bukata, me da me
da me mijinta ya fi sha’awa a jikin mace, sai ta rinka gyara nata yanda zai rinka daukar hankalinsa yana
bashi sha’awa ba tare da na mace daban ya burge
shi ba.
[Advertisements⬇️]
[Continue Reading⬇️]