[Advertisements⬇️]
[Continue Reading⬇️]
SALON SO CHAPTER 18
Bebyna ya za ayi na gaji da jin muryarki hasken
zuciyarta tare da jin lafiyarsu ita da bebyna.
Ta yi shashshekar dariya cikin kissa da jan hankali ta makale murya tare da lankwasar da murya ta yi
masa magana cikin yanga da marairaita.
“Honey na ka kwantar da hankalinka kalau muke
ni da bebynka, sai dai muna kewar dumin jikinka
na dan lokaci.”
“Okey, beby na kada ki damu karfe hudu zan dawo gida mu kasance tare zuwa wayewar gari ko beby
na?”
Ta ce “Um hum thank you Honey na, sai ka dawo
muna jiranka.
Ya sumbaci wayar ya huro mata isa ta cikin wayar,
ta shashshekar dariya da ta saukar wa da Haidar matsananciyar kasala yayi saurin ajiye wayar tare
da jan diguwar ajiyar zuciya.
Jawahir ta mike ta koma kicin ta debo fulas fulas
dinta ta malmala tuwon farar shinkafarta da ya
tuku ya yi luku luku da shi, kowanne ta malmala sai
ta sa alaida sannan ta jera acikin fulas din. Ta juyo hadaddiyar miyar wake da ganye wadda ta
dahu da hanta da koda da manja sai dan man kuli
kadan lallai jawahir kin iya hada abin da zai kara
muku jini da lafiya. Ta juye farfesun kifi irin ragon
ruwan nan ta zai zuba kamshi yake yi, ta bude
oben ta zaro gasashen naman ta da ya ji tumatir da albasa gashi yayi ruwa ruwa sai zuba kamshin
kayan kamshi yake yi. Ta hada lemon kwakwa da
madara sannan ta hada lemon abarba.
Kowanne ta zuba a jug ta cilla kankara ta rufe ta
kwashe kayan taje ta jere su a kasa yanda suke yi
yanzu saboda girman cikinta. Iya ce ta gyara mata kicin din da duk wajen da ya baci.
Jawahir ta shiga toilet ta tsalo wanka tare da tsala
kwalliya ta shafe shafe da hadaddun kamshi na
tururuka daban daban, simpil doguwar riga ta saka
me rubi biyu sai walwalin dutsunan jiki ne suke ta
zuba sheki. Ta dora sirrin mayafin akanta, ta futo falo ta zauna akan kafet ta mimmike kafafuwanta ta
wara su yayin da ta jawo rumote ta latsa TV ta
kama, ita kuma ta jingina da kujera tana kallo.
Haidar ya turo kofar tare da sallamar tasa, ya yi
saurin karasowa in da take ya zube a gabanta, ya
tarairayo ta jikinsa “beby na” ya shafa mararta ya ku ke ya beby na yana dawo na same ku beby na
komai lafiya ko?”
Cikin murmushi take daga kai tana amsa masa tare
da shafar sumarsa ta kansa.
“Sannu beby na zauna anan kada ki tashi na hau
sama na watso ruwa na zo mu fita muje mu ci abinci ko, ta daga kai.
Ya mike ya yi sama da sauri ya fada toilet be jima ba
ya fito ya shirya cikin kananan kayansa ya sakko,
ta mike ta taro shi ya rungume ta a barin damansa
“Muje restaurant mu ci abinci ko.?”
Ta langabe a jikinsa “Haba my love da raina da lafiyata na kasa yi maka girki har sai ka fita waje ka
ci? Honey na na yi mana girki.” Ya rike baki
“Bebyna bana hana ki wahalar da kanki ba? Daidai
sanda suka zauna gaban kayan abincin yana
bubbudawa, ta ce “Wallahi Honey na ba na son
naga ka ci girkin waje ko na wani wajen, shi yasa nake daurewa na yi maka da kaina.”
“San kyau bebyna, na gode Allah ya yi miki
albarka, ya raba ku da cikin nan lafiya”
Amin Honey na gode.”
Suna cin abinci Haidar yana zuba santi, jawahir tana
kyalkyala masa dariya. Da haka suka gama Haidar ne ya kwashe kayan, ya dawo ya same ta ta
kwanta kan kafet ya durkusa kanta yana yi mata
tausa sannu sannu yake matsa mata jikinta tare da
mulmula mata bayanta a hankali ta ke fadin “wash,
wash, tana limshe ido na son yin bacci.
Karar wayarsa ce ta sa ta bude ido, ya dauka “Hello Inna kina lafiya kwana biyu?”
Inna ta ce, “Lafiya lau nake ina jawahir din?”
“Ga ta kusa da ni.”
“Yauwa
[Advertisements⬇️]
[Continue Reading⬇️]
daman dai kan maganar da nafara yi maka ne, zan
zo na taho da jawahir don ta yi wankan gida”. “Haidar ya katse ta da “Haba Inna saunawa zan
gaya miki ne ni matata babu inda zata duk girman
gidan nan bai ishe ta wanka ba sai kun dauke min
ita, wanne hali kuke son saka ni?’
Ta daka masa tsawa “Kai marar kunya bana son
shashanci, haihuwar farin zaka yi wa wauta yaushe zamu barta ko mu ma wayaye ne irin ka.? Ta kife
wayar tana mita.
Jawahir ta dora kanta akan cinyar Haidar tana
shafa fuskarsa. “Honey na me yake faruwa ne, don
Allah ka daina damun kanka.”
“Bebyna ba dole na damu kaina ba, suna kokarin raba ni da ke, bebyna wai za ki iya tafiya wankan
gida ki bar ni a nan har tsawon kwana arba’in da
‘yan kai?
Ta girgiza kai cikin yanayi na tausayi da son ta yi
kuka “Honeyna ba zan barka ba bazan yarda su
raba ni da kai ba, babu in da zan bi su.” Daidai lokacin da ta dafe cikinta tana wash, wash!,
yayi saurin rungumarta cikin rikita yana cewa,
“Bebyna menene, me ya faru da cikin nawa.?
My love bayana, cikina, kuguna, duk ciwo suke yi.”
Da sauri ya buga wa direbansa waya ya ce ya fito
da mota zasu asibiti. Ya dakko jawahir direban ya bude musu bayan mota suka shiga, ya rife ya ja
suka nufi asibitin, abinka da lafiyayyen asibiti tuni
suka shigar da ita dakinta daban ita kadai a ciki
Haidar ya furgice ganin yanda jawahir take wahala,
gani yake kamar ciro cikin ya dawo da shi jikinsa
shi ya yi nakudar ya haihu. “My love” ta kirawo shi maganarta kasa-kasa ya
durkusa kanta yana jinta “My love kayi waya su
Mama su zo kada na mutu basu ganni ba.
Ya sake rungume ta yana ta mulmula mata bayanta,
“Ki yi hakuri bebyna, ba za ki mutu ba kin kusan
haihuwa. Idan ki ka haihu sai na yi musu waya su taho da
kwarin gwiwarsu yanzu kuwa idan na gaya musu
hankalinsu tashi zai yi su zo su cika asibitin ai ta
damunki.
“Wayyo Honey.” Ta kankame shi tana nishi likitocin
da suke kanta suna gaya mata ta yo nishi suna danna mata cikin a hankali tana yo nishi jariri ya
fado tare da tsala kuka. Haidar ya yi saurin
daukansa a cikin jinin ya na ta murna.
Likitar ta yanke masa cibiya ta karbe shi ta mika wa
nas don su gyarashi
Wata sabuwar nakudar jawahir ta kama ba jumawa ta sunkuto ‘ya mace ba da jimawa ba wani da
namijin ya kuma futowa.
Ikon Allah, Allah mai baiwa, Allah mai kyauta, har
da kari jawahir ta haifi ‘yan uku maza biyu mace
daya, ‘ya’yan kyawawa kamar ‘ya’yan indiyawa
don kyau da ja, Haidar duk ya rikice don murna waya yake ta bugawa kawai baya tsayawa
gaisuwa sai dai ya basu labarin jawahir ta haifa
masa kyawawan ‘ya’ya har guda uku.
Kafin ki ce meye wannan, tuni asibitin ya cika ya
zama filin barka barka tare da murnar samun
wannan kyawawan karuwar da aka yi. Kwanansu daya a asibiti aka sallame su don ba sa
mun hutun suke ba saboda jama’a da suke ta
tuttudowa ganin wannan kyauta da Allah ya yi
musu da ba kowa ake ba wa ba.
Nan kuma gaddama ta kaccame in da Inna ta daga
gida za a yo da jawahir da jarirai shi kuma Haidar ya ce babu in da za ‘a kai masa mata da ‘ya ‘ya, sai da
Abbansa ya daka masa tsawa ya nuna masa bacin
ransa a zahiri sannan ya bari aka tafi da su jawahir
da yaran gidansu.
Shi kuma Haidar ya yi fushi ya yi nasa gidan ransa a
bace, yana shiga gidan yaga bakinsa yau ba jawahir a ciki can kuma ya rinka hango ta tare da
‘ya ‘yansa ‘yan uku, haba wa, tuni wani sabon farin
ciki ya sake mamaye shi ya shiga wanka ya sake
sabon wanka ya zira farae shaddarsa sabuwa kal
mai laushi sai sheki take yi kamar boyel.40
[Advertisements⬇️]
[Continue Reading⬇️]