[Advertisements⬇️]
[Continue Reading⬇️]
SALON SO CHAPTER 16
Abubuwan da mace zata ci su kara mata ni’ima ba lallai sai ta fitar da kudinta
ta sai masu tsada ba, a’a daidai ruwa daidai tsaki, kada ki ce to ke ma ina kika
ga kudin bayan ba baki yake yi ba, ke ba wani abu da za ki siya don gyara
kanki.
To gaskiya wannan rashin wayo ne ai kan ki zaki gyara duk sanda namiji ya
kusance ki ya ji ki zam zam da ke, tsindum da ke dole ne ya rinka tattalinki ya
na baki kyakkyawan kulawa saboda yana son biyan bukatarsa. Amma ke baki
gyara kanki va, kin zauna gundin murhu duk wuta ta kone miki dan ruwan da
yake jikinki, mijinki ya zo ya ji kamas, saboda Allah me kike ganin zai faru?
Dole darajarki ta ragu idonsa, amma idan kika dage da shan su lemo, kankana,
rake, aya gwanda, ayaba, dabino, cukui, inibi, zogale, zaitun, tumatur, kwakwa,
zuma, nono, madara, gurji, dafaffiyar gyada, da sauransu duk irin wannan ba
karamin taimaka mana suke ba na kara mana ni’imar jikinmu.
Ko nera koma ki ka bayar a siyo miki dan kifi ki yi romonsa da kayan kanshi da
alvasa da tumatur kika watsa wake a ciki ya dahu luguf da dan alaiyahu ki yi
shi romo romo shi ma yana taimakawa, ki sami danyar gyada gwangwani daya,
aya gwangwani daya, waken suya gwangwani daya, alkama gwangwani daya, ki
hada ki jika a markado miki ki ta ce shi kamar gasara ki rinka damawa kina sa
madarar ruwa kina sha za ki ga yanda zai taimaka miki ya sakar miki da ni’ima
a jikinki.
Kinga abu mafi sauki idan kika sami ayarki kika jikata ta juku ki ka kai markade
kizo ki tace kayarki ki kara sikari ki rinka sha zata kara miki ni’ima sosai.
To kinga iri iren abubuwan nan idan mace tana yi zata taimaka wa kanta don
kare wulakancin namiji. To idan kuma ta iya gamsar dashi ta san sirrika na iya
kwanciya da da namiji to zata mallake shi a hannunta har a rinka zargin ta
asirce shi ne.
Jawahir ta ce, “To Anty me zai hana murubutanmu ba za su rinka wayar wa da
mutananenmu kai ba, ko dan sanin irin wannan sirrikan kwanciya don su ma su
mallaki mazajensu a hannu a daina yawan mutuwar aure? Maza su daina fita
bariki neman matan banza su rinka tsayawa iya matansu na sunna kawai?
“To ai jawahir matsalar da ake samu kin gane ne, marubutanmu suna iya bakin
kokarinsu na ganin cewar sun ganar da yawancin mutane yanda rayuwar jin
dadi ta aure take, to amma kash! Wani abu da ake kuka dashi wai sai ace suna
bata tarbiyar yara, wai yara kanana suna diban lattattafai suna karantawa, suna
ganin abin da bai kamata ba, wanda gaskiya ni kuma ina ganin ba haka ba ne,
domin idan kinga yarinya ta lalace to dama can lalatacciyarce iyaye suna ina
‘ya ‘yansu suke fita su shiga gidan amare su rufe kansu suna ganin kaset din
blue film ko America, ko ibo, ko fim din Turawa da yake bayyanar da tsiraici
karara da yanda ake nuna soyayya ta kazamar hanya. Wasu ma tare da samari
suke gani to meye ma ba zai faru ba wajan wannan kallon wa’yansu yaran
kuma da ake batawa ba su da wayewar kan ma da za su yi karatun littafin ake
jansu ayi musu fade, shi kenan hanyar lalacewarsu ta samu.
Wasu yaran kuma rashin kulawa ta iyaye da rashin sa ido akan harkokin su ne
yake jawo hakan, wasu tsabagen kwadayi ne da rashin kamun kai da zubar da
tsantsar da darajarsu ta ‘ya ‘ya matar ne take jawowa.
Gaskiya bazan taba yarda ace wai karatun littafi yana sa ‘yan mata suna
lalacewa ba, saboda duk wata mace da ta san darajar kanta to in har ta
karanta littafi ina ganin zata yi kokarin kare mutuncin kan ta ta yi kokarin kai
budurcinta gidan mijinta, saboda ta karanta littafi taga yanda daren farko ya
kasance ga yarinyar littafin, mijinta ya same ta a cikakkiyar mace ta ga irin
tarairaya da
Kulawar da yake bata taga yanda yake sa
mata albarka har da wata dunkuleliyar kyauta da ya yi mata, to ni a ganina
kowace budurwa zata yi sha’awar hakan har ta yi kokarin kai budurcinta gidan
mijinta
[Advertisements⬇️]
[Continue Reading⬇️]
Abu na biyu ‘yan matanmu za su iya koyon kissa da shagwaba da kalolin girke
girke da yanda ake tarairayar namiji, zasu san abubuwan da suke kara wa mace
ni’ima wanda za su fara tsuma kansu tun kafin su shiga gidan auren, domin
idan ba’a littafin ba babu in da za su sami hakan saboda al’adar Bahaushe da
kunya babu uwar da zata iya zaunar da ‘yarta ta koya mata wa’yannan
abubuwan don zata yi mata aure, za dai ayi wa ‘ya fada ki bi mijinki ki yi masa
biyayya, to kin je kina ta biyayya yana wulakantaki ke baki san dalili ba to duk
wa’yannan abubuwa ne da bakya yi, amma aure ya samu tattali kissa biyan
bukata, shagwaba, ladabi da biyayya, iya girki, iya kwanciya, amfani da turaruka
masu kamshi da na tsugunno, ta cikin ikon Allah za’a samu zaman lafiya da
fahimtar juna a cikin aure.
Shi turaren tsugunno ana amfani da shi ne wajen turare gabanka ka tsugunna
akai hayakin yana shiga ciki to yana kara hade mace ne ya matse ta kamar
amarya.
Jawahir ta kawo gauron numfashi ta ce, “Anty na fahimce ki Allah ka ganar da
yawancin al’umma ko a sami zaman lafiya a tsakanin ma’auratnmu”
“To amin Jawahir.”
Ba jumawa Haidar da Ankul suka dawo suka ci abinci. Ankul ya ce da Anty
maryam ta tashi su tafi gida akwati guda jawahir ta yo wa Anty na tsaraba ta
dakko ta kawo mata suka rinka godiya tare da sa albarka.
Sai da Haidar da jawahir suka yi sati biyu a gidansu suna hutawa basu da aikin
yi sai wasanni da junansu su ci cima me kyau su sha me kyau suke ta sutura
me tsada su bada kamshi su manne da junansu suna faranta ran juna.
Yau sun cika sati biyu da dawowa don haka yau Haidar ya fara fita xuwa office,
jawahir duk ta damu kamar wanda zai je ya yi kwanaki a can sai da ya
lallabeta har da yi mata wayo sannan ya fice. Da yake ya dade rabonsa da
office din dole ya samu ayyuka kaca kaca sun yi masa yawa shi yasa bai samu
sukuni ba, sai na fadawa aiki kawai.
Haidar yana tafiya kuwa jawahir ta dauki mota ta tafi wani hadadden gidan
gyaran jiki tsadadde na ‘ya’yan wane da ‘ya’yan wance, aka yi mata gyaran
gashi aka gyara mata farce aka wanke kafar aka rangada mata kunshin fulawa.
Jikinta ya sha dulka da halawa, jikinta da fuskarta sai wani santsi da taushi
yake yi kamar auduga yana fitar da wani sihirtacce na kyau.
Tana komawa gida kicin ta shiga ta feraye doya ta dora a wuta ta debo
manyan busashen tarwada ta farke cikinta ta kan kare ta kwara masa ruwan
zafi.
Ta hade markade iya ta yi mata abu landa doyar ta dahu ta tsame ta mika wa
iya ta daka mata sakwara, ta hade miyar busashen kifin nan da ta ji onga, kori,
reko, mai da sauren kayan da su ke sa girki armashi, sannan ta cuko zallar
tsokar nama a firinji ta tafasa shi da albasa gishiri da dan magi.
Bayan ya tafasa ta kwankwatsa attaruhu albasa ta dakko tafasashen naman
nan ta hada a turmi ta daka.
Ta ciro shi ta rinka dunkulawa ta fasa kwai ta zuba gishiri onga reko ta dora
manta a wuta ya dau zafi ta rinka daukan dunkulan naman nan tana tsoma sha
a rwan kwan tana sa wa a manta na soyawa, ta gama wannan ta zo ta yanka
salak ta yi masa wanki sosai ta zuba a filet, ta yanyanka tumatur da albasa ta
gewayesu a saman salak da albasar ta kawo dafaffiyar hantarta da ta yi mata
kananan yanka ta zuba a kai.
Bayan ta yada salak, cream ta zuba heinze beans a tsakiya duk wanda ya kalli
hadin salak din dole yawunka ya tsinke, ta debo kayatattun fulas dinta ta zuba
komai taje ta jere su a santara tebir.
Ta debo fararen gobarta manya ta markada ta tace dusar ta markada kankana
da gwanda da ayaba a duk ta tace dusar ta hada akan ruwan gwaibar, ta
daddara rake ta matse ruwan ta hada akai, ta zuba ruwan kwakwa da ruwan
markadaddiyar aya ta zuba madarar ruwa gwangwani biyu ta kawo zumarta me
kyau ta zuba a ciki ta juya ta saka a firinji.38
[Advertisements⬇️]
[Continue Reading⬇️]