[Advertisements⬇️]

SALON SO CHAPTER 10 - Bankinhausanovels
Mon. Mar 27th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

SALON SO CHAPTER 10

 


Haidar da jawahir suna zaune a falo suna kallo

jawahir ta kama hamma Haidar ya jawo ta jikinsa

yana shafata ba dai bacci za ki yi ba ki bar ni.?”

Ta daga kai ka san ni da baccin wuri bari na je

daki na kwanta, “Ya langabe murya gaskiya ba za

ki tafi ki bar ni tun yanzu ba.”

Ya rungume ta ya gyara mata kwanciya a jikinsa

yana shafa kanta yi bacci a haka in na gama

kallo na kai ki dakinki. Cikin mintina kadan bacci

ya kwashe jawahir dadi ya cika zuciyar Haidar jin

jawahir rungume a jikinsa taushin fatarta da

kamshin jikinta shi suke dada sa shi nishadi.

Kausar ta yi sallama ta shigo falon ba dan sanin

muhimmancin sallama a addinin musulunci ba da

bai amsa mata ba. Ya dako kai ya kalle ta, “Ina

kika je sai yanzu da daddaren nan za ki dawo

bayan na ce ki dawo da wuri.?”

Ta kalle shi ta ja tsaki, “To ina ruwanka da

dawowata da wuri ko ba da wuri ba? Kai ba wani

cikakken namiji ba bare ka ce za ka yi kishina.”

Jawahir ta dan motsa ya sake rungume ta yana

jijjigata kamar yarinyar goye. Kausar ta yi tsaki

an dai fadi ba nauyi miskinin kawai kana

luguiguita yarinya kai ba wani katabus za ka iya

yi mata ba.” Ta shige dakinta Haidar kuwa ya yi

mata shiru ne gudun kada jawahir ta farka amma

ya ji haushin maganar da ta yaba masa. Da ya ji

kallon ma ya ginshe shi ba zai iya ci gaba da

kallon ba, don tsananin dacin da zuciyarsa take yi

Jawahir da tun shigowar Kausar ta farka ta ji duk

abin da kausar ta gayawa Haidar ranta ya yi

mugun baci, ba ta san sanda hawaye ya fara

zubo mata ba. Haidar da ya yunkura zai mike da

jawahir a kafadarsa sai ya kula hawayen da take

yi hankalinsa ya sake tashi ya kira sunanta,

“Jawahir lafiya?”

Tayi saurin zamewa daga jikinsa ta durkusa kasa

tana kuka ta fara rokonsa don Allah don Annabi

yaya ka yi hakuri ka yafe min abin da na yi maka,

ni na jawo maka matsalar da kake ciki wallahi

tallahi ba da niyya na yi maka haka ba kan

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

tsautsayi ne da kaddara, ina neman afuwarka da

gafararka ko na samu sassauci a zuciyata.”

Ya mike tsaye ya kamo kafadunta ya dago ta ya

rungume ta a jikinsa yana share mata hawayen,

“Yi shiru babyna daina kuka ba so ki kuma irin

wannan tunanin a zuciyarki, ki sani duk abin da

Allah ya yi zai samu bawa daman tun fil’azal

rubutacce ne, kuma babu wanda ya isa ya

kankare shi ko ya goge shi. Don haka ki kaddara

daman can Allah ya yi hakan za ta faru da ni, don

haka ni ba na so na ji kina cewa ke ce sanadi

kada ki kuma fada, ni na yarda da kaddara don

haka ba na zarginki da komai, ki kwantar da

hankalinki ba na son ganin ki cikin damuwa, kin ji

ko. Ta daga kai alamar amsawa, “To mu je ki

kwanta. Yana rugume da ita har dakinta, ya raka

ta tolet ta yi borush ya riko ta sai da ya kwantar

da ita a gadonta ya ja bargo ya rufe ta ya kunna

mata A.C ya sumbace ta a kumatu ki yi bacci

lafiya babyna. Ya juya ya fita ya nufi nasa dakin.

Yana fita jawahir ta mike ta dauko tsaleliyar rigar

baccinta ta saka ta shafe jikinta da humra. Ta

dade feshe dakin da Air Freeshner nan da nan

sanyin A.C da daddadan kamshi suka shiga tashi.

Ta matsa mouth freeshner a bakinta nan da nan

sanyayyen kamshi ya rinka fita ta haye gadonta

ta yi lumtsim da ita.

Haidar ya shigo wanka ya fito ya shafe jikinsa da

turare ya hau gado dan kwanciya amma ina

baccin ya gagara sai juyi yake yi yana tunano

lallausan jikin jawahir da taushinsa, ya san ina

bacci zai dauke shi, ya sa kayan baccinsa ya fito

ya rufe dakinsa ya nufi dakin jawahir.

Ya sa safayar mukullinsa ya bude dakin ya shiga

ya mayar ya rufe. Ya shiga cikin dakin nata

wanda sanyin A.C ya gama ratsa shi, ga man

nan na turarenta mai dadin kamshi yana tashi.

Ya kunna fitila ya yaye bargon da ta rufa ya kalle

ta cikin tsaleliyar rigar baccinta wadda ta kara

fito mata da sigar kyanta, baccinta take yi hankali

kwance.28/32

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]