[Advertisements⬇️]

KHAIREEYAH CHAPTER 1 BY NANA FA,AD EESHA - Bankinhausanovels
Mon. Mar 27th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

KHAIREEYAH CHAPTER 1 BY NANA FA,AD EESHA

 

 

 

Tafiya take a buge akan titi kamar zata fad’i kasa, ga kwal6an(bottle) hernesy a hannun ta na dama, bottle na champagne a hannun ta na hagu, idan ta kurba Hernesy ta kurba champagne(giya/wine),da dare misalin karfe sha d’ayan dare a garin maiduguri, ko ina tsit sai motoci d’addaya da suke wucewa da yake garin ba kamar da ba kowa na shiga gida da wuri sabida condition na garin,wani mota neh ya zo da gudu yana mata horn amma inaa hankalin ta baya jikinta ta, kwasss motar ya kwashe ta tafad’i a kasa…

 

_Few years back_

(“`shekarun baya“`)

 

“Imrann, Imrann” wata yarinya ce wacce bazata wuce shekaru goma sha bakwai (17yrs) ba ita take ihun kiran sunan Imrann(tsaban ihun ta ni kaina sanda na firgita, ni nana kallo nabita dashi baki  bud’e)

 

Uniform na makaranta neh ajikin ta, riga fari da wani dan mini skirt light brown wanda bai kai gwiwa ba ahaka kuma wai sch uniform, wani shegiyar high heel neh a kafar ta bak’i da white socks d’inshi. Gashin kanta nan abude ta kama da ribons pink da blue had’addu, ta sha make up kamar ba makaranta zata ba,  wayan ta tacire acikin jakar ta kirar Samsung Galaxy S7 ta daga sama ta tura baki(Eesha ta cemi selphie zata dauka)bayan ta gama d’aukar hoto ta maida wayar a wani tsadadden jakar ta pink colour, sai waige waige take, wani ta hango yana wanke mota a gefe, wani dogon tsoki taja tace

 

Kai Garba (wani tsoho takira wanda a haifa yayi jika da ita) wai ina shegen driver nah Imraan neh baisan nayi latti din makaranta ba’

Tsohon nan wanda takira sa da Garba yace ”hajiya wlhy da kyar mukayi bacci jiya baya jin dadin jikinsa neh d’an nawa'”

Kallon uku saura kwabo ta watsa masa kan taja tsoki tace

” Garba da kai da yaron ka kullum sai kawo excuses mtsewwww, idan baza ku iya aikin ba basai mu nema wasu ba, ai duk Abba neh yake raga muku da zai bi shawara ta da tuni nayi outttt daku, Nonsense”..

Codein tazuba acikin coke tafara shaa tana had’awa da Roci agaban Garban ba kunya (nayi salati nagode wa Allah, yara kanana da shayeshaye duniya ta 6aci Allah ka bamu yaya nagari)

 

 

Shiga mota tayi ta tada ta danna horn da karfi mei gadi ya bud’e mata gate, fisgan motar tayi ta bar haraban dankareran gidan su, gudu take sharawa akan titi kamar na uban ta har takai wani Babban makaranta da aka rubuta CARE BAZE PRIVATE SCH,  tashiga tayi parking d’in motar ta, tafita a motar tana taku kamar hawainiya da hankali, ta wuce class direct

 

Tana shiga class aka fara ihun  “rude gurl, rude gurl” koh kulasu batayi ba ta zauna a seat dinta, ta cire wayar ta ajakar ta tayi posting hoton d’azu da ta d’auka a Instagram da Snap chat nan da nan tasamu kusan 2K likes, tana chating tana shan coke dinta..

Ba’afi minti biyu ba malamin physics yashigo, aji yayi tsit kowa ya kama kansa, ya fara lecture yaji kas kas karan cingam (chewing gum), juyawa yayi yana kallon su d’aya bayan d’aya yace

“Who the hell is chewing gum in my class”

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Daidai nan ta kara kakas da chewgum nata, kallo ya watsa mata ranshi yayi bala’in 6aciwa daman ya ki jinin yarinyan dan bata da tarbiya koh kad’an yace

” *Khairiya* getout of my class”

Cigaba da cin cingum nata tayi kamar bata ji shiba

Tsawa ya kara daka mata yace “I said get outtt of my class you Moron”

Tashiwa tayi ta d’auka roban coke nata wanda ta had’a da codein, ta d’au wayar ta, zuwa tayi dab kusa dashi, ta kallesa sama da kasa tace

“U can send me out of your damn class but let me warn you, don’t u ever i mean e–v-e-r call me a Moron u filthy fool”

Taja wani dogon tsoki ta fice a ajin, ajin ya d’au ihu ana cewa rude gurl rude gurl  (wa’iya zubillah)

Shiga motar ta tayi ta kuna ra6a (AC) tana jin music na lilwayne I feel like dying tana shan coke d’inta….

 

Can bayan malamin physics ya fita ta dawo ajin ta zauna, bata kara tashiwa a ajin ba sanda aka tashi a makarantar, fisgan motar ta tayi ta wuce wata had’addiyar shopping mall

Tana shiga tana cin cingum kamar irin tsofin yan bariki, ga codein yana aiki tana tafiya kamar zata fad’i ga wani baccin dayake fisgan ta (slow inji masu sha), bata san lokacin da ta buge wata tsohuwar mata ba duk suka fad’i har kasa..

Khairiya tana tashiwa tace ke wace irin bahuwar tsohuwa ce, baki kallo neh ehh tsohuwa, ta fad’a da tsawa

Mari taji mei rai da lafia akan kyakkyawan fuskar ta, aka kara mata wani marin, sanda aka wanke ta da mari lafiyayyu guda uku masu kyau yace

“Ke wace irin dabba ce, kinsha kwaya kin bugu shineh zaki bangaje mutum kuma kizo kina zagi”

Bud’e ido tayi ta kallesa mei kyau, ta nema baccin ma ta rasa, kallo ta bishi dashi tace

“Who the hell are you da zaka ta6a lafiya ta, kasan ni yar wacece, Sunana *Khairiya Ibrahim Muhammad*, yarinyan *Alhaji Ibrahim Muhammad Fu’ad mai Naira*, ka ta6o bala’i da masifa, sai kayi regretting mari nah da kayi, wlhy koh kai d’an gidan waye neh”

Cire wayar ta tayi ta danna kira, ana picking tace ” ina Nedd Grocery kuzo nan da minti biyu” ta katse wayan

Tsohuwar matar nan sai cewa take wa yaron da suke tare ” *Zil* mu wuce ni na hakura tunda ka mare ta ai shikenan ka rama mini muje gida pls dan Allah ”

Wanda tsohuwar takira da Zil yace “Haba Hajja kibari na koya mata hankali, yarinya ba tarbiya asaran haihuwa, tirrr wlhy na tausayawa iyayen ki”

“Kai neh iyayen ka sukayi asarar haihuwar ka bani ba, *You filthy wretch*” tofa masa miyau bakin ta tayi sai farar shaddan sa

Bai san lokacin da ya jata waje ba suka bar mall d’in, yafara jibgan ta, duk kokarin ta dan ta rama amma inaa karfin su ba d’aya ba, mutaneh suka zo raba wa amma yaki barinta, ana cikin haka motoci guda uku suka tsaya, manya manyan karti neh, idon su ja bakin su bak’i, da wuk’a da adda suka fito wanda ya nuna tabbacin ‘yan daba neh

Suna fita a cikin motar su suka hau kan saurayin wanda aka kira da *Zil* suka fara jibgan sa, sanda suka masa likis da duka jiki duk jini, kiran police akayi suna ganin police  suka hanzarta saka Khairiya a mota suka gudu

 

 

 

 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]