[Advertisements⬇️]

KHAIREEYAH CHAPTER 5 - Bankinhausanovels
Mon. Mar 27th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

KHAIREEYAH CHAPTER 5

 

Hanyan Shagari lowcost suka kama, nan da minti goma suka isa dan gudun da sukeyi, a bakin gate wasu sojoji neh sun saka bak’in glass fuskarsu a murtuke kamar wanda aka musu mutuwa, Khairiyya ce a gaba su Kamalu badd a bayan ta, Glass na motar ta ta sauke, wani bak’in soldier neh yace fito ki bud’e boot naki, ba musu tafita tana tafiyar ta mai d’aukan hankali ta bud’e boot nata, dubawa yayi yaga ba komai sai spare tyre, duk sojojin kallon ta suke dan Khairiyya ta d’auke musu hankali, sojan murmushi yayi yace

“Baby mei sunan ki”

Tana mai mayar mishi da murmushi tace “KIM”

Yace “Wow nice name, you are so beautiful”

“I know ” shineh kawai abun da ta furta tashiga motar ta, sojan nan haka ya bita yace

“Ki tsaya muyi magana mana”

Khairiyya tana mei kallon sa ba yabo ba fallasa tace

“Dont worry yanxu ina sauri yayata tace na kawo mata carpenters kaga suneh a bayana so please ba sai ka duba suba idan zamu fita zan tsaya muyi magana handsome”

Kiran shi handsome da tayi ba karamin dad’i ya mishi ba, sai washe hakura yake kamar mai tallan close up yace

“Ok ok no problem I will be here waiting”

Tace alright then sai mun fito, ta fisga motar ta ciki su Kamalu bad suka bi bayanta, Line A yana can ciki ciki haka dai suka shiga, suna duba koh wani numban gida, dan kowani gida an rubuta numban a waje, suka samu A36 suka zagaya sukaga A34

Wayan ta ta cire ta latsa numban shi, ringing d’aya ya d’auka wayan

Khairiyya tace

“Hello Corper Chris it’s me KIM”

Daga can Corper Chris yace “Ohh the damsel Kim, i’ve been waiting for you since, where you at”

Khairiyya tayi murmushin mugunta tace “At the door sir, can I come in”

“Sure Damsel Come In, fell free dear”

Tace “ohk”

Ta katse wayan, juyawa wajen su Kamalu tayi tace ku shiga bayan minti d’aya, suka ce an gama Kim

Tura kofan tayi ta shiga, ba laifi gidan tsab sai d’an warin toilet da yake tashiwa, washe hakora yake yana cewa

“Welcome Damsel, welcome”

Ya bud’e mata hannu alaman ta rungume sa

Kau da kai tayi tace “I am tasty”

“Ohhh sorry pls lemme offer you drinks but before then have a seat” nuna mata kujera yayi ta zauna ya bud’e fridge ya ciro faro water da Coke na roba, kan ya ajiye a gaban ta su Kamalu suka shigo gidan

Corper chris sai ganin maza karti yayi akan sa da kayan aikin su, muryan sa na rawa yace

“Who are you, What do u want? ”

Kamalu neh ya amsa yace

“Uwaka da Ubanka neh”

Khairiyya ta fashe da dariya Coper chris ya juya yana kallon ta with suprise on his face yace

“Why Kim, Why? ”

 

Dariyan ta tacigaba tace

“Ohhh Corper Chris you love catching Fun right, we gonna catch some fun now”

Muryan sa yana rawa yace “what do u mean by that, Please Kim I beg of you don’t do anything stupid”

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Su Kamalu bad da yaransa suma sai dariya suke masa dan kusan duka basuji mai suke cewa ba

Zaiyi ihu Kamalu ya kai masa bugu bakin sa, Khairiyya tace

“Ahswear Chris don’t you dare try that, bamu fara catching fun ba but you are already looking like a fish who has mental issues, ohhh you are such a frickle doodle”

D’aura shi sukayi da igiya mai karfi hannun shi da kafan shi, gum mai karfi suka manna bakin shi dashi

Khairiyya tace “Wow I’m gonna enjoy this”

Shiko duk an d’aure shi ga baki an toshe ba abun da yakeyi sai hawaye

Dukkan su dariyan sa suke Khairiyya tace

“We ain’t even started, save your tears for letter durling”

Zuwa wajen fridge nasa tayi ta d’auko ruwa masu sanyi ta watsa masa a jikin sa, sai shure shure yakeyi, gashin kansa daman yatara gashi irin na gayu Razor Kamalu bad yacire sabowa yasaka sabulu da ruwa akansa yafara masa aski, gabad’aya yabi ya 6ata masa kansa kaca kaca

Wani k’aton bulala Khairiyya ta d’auka ta fara zane shi da bulala tana cewa

“Ohhh I love this, this is fun, no more than that,  ohhhh” sanda hanun ta yagaji ta barsa, tace Kamalu mu barsa haka atleast yayi catching Fun yanxu, kuma nasan bai ta6a catching Fun irin na yau ba en it will stuck in his brain forever

Corper dai sai hawaye dan kuka ma bazai iyayi ba dan an rufe bakinsa,Khairiyya tace

“Tell nobody, Idan kafad’a hmmm i’m gonna rip off your head en then feed it to your bitches” taja tsoki

Khairiyya da mutanen ta suka barshi a wajen suka shiga motar su, fitan su a gidan wani yagansu ya shigo da gudu yaga Chris a d’aure, neman wuk’a yayi ya kunce sa ya bud’e masa baki, yace

“Brother Chris what happen”

Kasa magana yayi Chris sai neman wayan sa da yake, yana samuwa ya danna wani numba an rubuta my brother, latsa number yayi yakira

Ana d’aukawa Chris ya fashe da sabon kuka yace

“Broh m finished, some people came en beat me up, don’t allow them out of the gate pls broh, don’t let them go” ya kara fashewa da kuka dan yaji zafin dukan da Khairiyya ta masa, ga naushin da Kamalu yamasa sanda bakin sa ya fashe

Yayan yace “what type of car Chris”

Chris yace “i don’t know lemme ask Gabriel”

Ya juya wajen Yaron da ya taimaka masa yana hawaye yace

“Abeg Gabriel what type of car do you see them with”

Wanda aka kira da Gabriel yana d’an tunani kan yace

“Yes the guys with Odesys en the babe with S-Cross”

A take ya fad’awa yayan nashi, yayanshi d’aga kai da zaiyi ya kalla motan sun kusan zuwa gate d’in, a take ya tashi yana ihu yana cewa

“Don’t let them out” da karfin sa, duk sojojin suka tashi suka tsaya bakin gate d’in sukayi cracking gun  (gyara bindigansu) hankalin su atashe duk a zaton su an kawo musu attack neh

Su Khairiyya sai gani sukayi sojoji sun seta bindiga akansu, gaba d’aya sun tsorata

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]