[Advertisements⬇️]

KHAIREEYAH CHAPTER 4 - Bankinhausanovels
Mon. Mar 27th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

KHAIREEYAH CHAPTER 4

 

 

Tana shiga gida tayi parking na motar ta a parking space, tafita a motan ta taji murya ta bayan ta ana cewa

“Queen Khairiyya daughter’n Abba ya makaranta” wani dattijo neh dogo bak’i kyakkyawa yana murmushi

Tura baki Khairiyya tafara tace

“Ni ba ruwana da kai ai Uncle Hisham, tun da katafi Lagos sau d’aya ka kirani, ka manta dani gaba d’aya”

Wanda takira da Uncle Hisham yace

“Haba khair kinsan aikin mu ba Hutu, kuma ke kullum kin cika canje canjen number”

Tayi murmushi tasan yana da gaskia dan a wata sai ta canza Sim card sau biyu wani sa’in sau uku ma, tace

“Toh naji Uncle, yanxu ina tsaraba ta”

“Haba khair baza mu shiga ciki mu zauna ba kina maganar tsaraba”

Tana kumbure kumbure tace “toh mushiga”

Suna shiga parlour Uncle Hisham ya zauna ita kuma tashiga kawo masa kayan motsa baki, gaban shi dam ta ciki dasu snacks da drinks, ba abun da yasha sai Malt, ya d’an sha kad’an yace

“Khair Sarauniya, nazo na d’auke ki muje gida nah kiyi koh wata d’aya”

Khairiyya tana washe baki tace

“Laa Uncle Yaa Ammar yadawo neh”

“A’a bai dawo ba Khairiyya sai nan da wata shida”

Ta tura baki tace “gaskia Uncle Hisham Abba ma yace na zauna a gida baya so ana barin gidan ba kowa empty” a zuciyarta sai cewa take Tab naje gidan ka Matar ka ta hanani sakat ana zaune kalau, da Yaa Ammar yana nan neh ma toh zan iya zama amma shima bayanan ga gobe akwai catching Fun na bika Kut ai bazai yuba

Uncle Hisham yace “Haba Khairiyya yanxu kina jin dad’in zama Ke d’aya daga ke sai masu aiki, kina yarinya karama wannan wace irin rayuwa ce ehh”

Hawaye tafara tace “Uncle Hisham tun ina karama nake living like this miserably, ina garin da kake aiki can mahaifiya ta take, wannan maganar kuma ba ni yakamata ka mini ba Ammi ce yakamata ka mata, ita tabar loneliness helpless child”

Shiga d’akin ta tayi da gudu ta kulle kofa tana kuka sosai, wani irin iyaye Allah ya had’a ta dasu, gwara Abban ta tasan dalilin neman da yakeyi,and she cant stop him amma Ammi fa, taje tana jin dad’in rayuwar ta ta manta dani”

Tun Uncle Hisham na buga kofa har yagaji ya bar gidan, tana jin motar shi yabar gidan tayi sallah Zuhur tayi Asr, abinci ma ta kasa ci, tun da nazo duniya da ‘yan aiki nake rayuwa, wannan wace irin rayuwa ce wai take fad’a da ihu

Kofan d’akin ta ake bugawa, Khairiyya tace

“Who the hell is knocking my door”

Dije ce a kofan tace

“Hajiya abincin ki na kawo miki”

Khairiyya ranta ya kara 6aciwa dan idan ta shiga cikin damuwa batason kowa ya mata magana, tace

“Dan kaniyar ki yar shishshigi ni nace ki kawo mini abinci, toh kije bazan ciba”

“Haba Hajiya dan Allah”

Wlhy idan na fito ranki zai 6aci kibar mini kofa nace, ta fad’a a tsawace, hakan yasa Dije ta bar wajen

Khairiyya bud’e fridge nata tayi tasha codein da benelyn kwal6a biyu kan taji daidai, zubewa tayi a kan babban gadon ta wanda zai iya d’aukan mutaneh biyar tafara bacci, itace bata farka ba sai karfe bakwai daidai ana kiran sallar Magrib, da kyar ta iya yin sallah tsaban yunwan da takeji, rabuwar ta da saka abu a baki tun burger na safe

Dining taje taga empty, Haule ce kawai take kwana

a gidan, kiran Haule tayi da muryan da Allah ya bata da karfi, Haule tazo ta durkusa tace

“Na’am hajiya ganinan”

“Wai uban mei kikeyi a ciki inata kiranki sai yanxu kikaga daman fitowa” cewar Khairiyya

“Hajia Wlhy kina soma kirana koh second ban karaba na fito”

“Ahh toh sharri na miki koh, Haule ki amsa mini na d’aura miki sharri kike nufi koh”

Haule ta sunkuyar da kai tace “Hajiya kiyi hakuri ba hakan nake nufi ba dan Allah”

Tsoki Khairiyya taja tace “Mei Dije ta girka”

“Hajiya Shinkafa da wake da miyan ja”

Wani kallo Khairiyya ta watsa mata wanda yasa har cikin Haule yayi kuka kuuu, Haule muryan ta na rawa tace

“Yi hakuri Hajiya Rice/Beans with stew”

Khairiyya tayi jimm, ta fusgar da iska tace

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

“Amma lalle Dije ta raina ni, sau nawa zan gaya mata bana son kayan tusa, musamman da daddare, cikin mutum ya 6aci inje inata tusa ina shigan toilet ba gaira ba dalili, mtseww kuma Wlhy yunwa nakeji”

Haule tace “Hajiya koh zan dafa miki wani abincin neh”

“Ai toh Haule da kin iya dafa abinci bazan tsaya ina 6ata lokaci nah ina miki dogon zance ba, your food makes me puke, kawai had’a mini G&G ki kawo mini banson stew”

Haule a zuciyarta cewa take ai gwara ni ina kokarin abincin kefa, tsawan da Khairiyya ta mata shi yadawo da ita da maganan zucin da takeyi

“Tunanin Uban mei kikeyi neh Haule, idan tunanin saurayi neh toh Allah sawwaka nidai kije ki had’o mini abinci” Khairiya ta fad’a a tsawace

“Umm Hajia yi hakuri naji kamar kince G&G ni kuma bansan abincin ba balle na girka” cewar Haule

Kai kai Yaa Salaam, wai ni Abba da wani irin villagers masu aiki ya had’a ni dasu neh, toh abincin kauyen ku wanda kukeci kullum, abun da nake nufi Shinkafa da wake yi mini had’in garau garau dashi yi sauri inajin yunwa”

Haule ta tashi tayi hanyan kicin sai cewa take Allah shirya Khairiya garau garau ma baza ta iya fad’a ba sai G&G taja tsoki

Bayan Haule ta had’a mata garau garau nata taci tayi nak, tayi alwala tayi sallan Isha’i, wayan ta ta d’auka ta kira Abba,

“Abba yau throughout baka kirani ba fa” ta fad’a tana tura karamin bakin ta

Abban yace “wollah Mamata i’ve been trying your line d’azu but baya shiga, yakike ya shirye shiryen Exams”

Tace “Abba gaskia karatu da wahala kuma jamb wani sa’in ba karatun ka baneh a had’e da sa’a kayi wani abu dan ni inason next section nashiga jami’a”

Abba yace “Khairiyya kiyi karatu kinji, In Shaa Allah zaki ci, now kiyi bacci you need to rest”

“Ohk Abba sai da safe gudnyt” ta katse wayan

Mallam Ali baizo yau ba,dan haka  shiga su Snapchat da Instagram tayi, bayan tayi dube duben ta, tayi addu’a ta kwanta bacci

Washegari da safe bayan tayi sallan Asuba ta kwanta bacci ita bata farka ba sanda wayan ta ya damei ta da ringing, d’aukan wayan tayi batare da duba wanda ya kira ba, taji ana cewa

“KIM muna kofan gate na gidan kifa tun d’azu ina kiranki bakya picking”

Cikin muryan bacci “tace Kamalu badd yanxu karfe nawa”

Yace “Kim yanxu Tara da rabi fa”

A take ta tashi tace “Toh ka bani 30mins zan fito kaji”

Yace ba damuwa KIM koh nan da awa d’aya neh mu masu jiranki neh

A gaggauce ta fad’a toilet tayi wanka, dining taje taci abinci dan sauri ma bata tsaya cin mutuncin Dije ba yau ba, bayan ta gama ci ta shiga d’akinta ta saka wani dogon rigar yar kanti armless (ba hannu)mei kala red da black, ta saka jacket baki akai tayi rolling da gyale red, simple makeup tayi yau daga powder sai lipgloose da mascara,da wani Red takalmi mei uban tsayi, d’aukan paper da Corper Chris ya bata tayi ta fita parking space ta shiga motarta taja wajen gidan, a waje bakin gate nata ta gansu Kamalu badd suna zaune acikin motar su Odesys, Kamalu badd yana ganin ta ya fita a motar, yazo dab kusa da motar ta ita kuma ta sauke Glass, yace

“KIM wani aiki neh haka”

Khairiyya tace “wani neh nakeso mu d’an koya masa hankali”

Kamalu badd yace “Hajiya KIM an gama, wani anguwa neh”

Ba tare da tace komai ba ta cire paper da Corper Chris ya bata ta mika masa, Kamalu badd yace

“Haba KIM kinsan ni ban iya abun ku na boko ba kawai karanta mini”

Batare da tace komai ba ta bud’e paper ta karanta _shagari low cost house A no34_ ga number wayan shi akasa

Kamalu badd ya bud’e baki yace “Kutt KIM, kinsan Shagari lowcost anguwan soldiers (sojoji)neh koh, kuma gaskia bazan 6oye miki ba tsoron sodoji muke,ga ‘yan anguwan sunsan bariki basa tsoro,  kafin a shiga anguwan ma suna checking kar su kama mu tun a gate

Dariya Khairiyya tafara tace

“Kai ban ta6a sanin kana da tsoro ba sai yau, amma ka bani kunya Wlhy, kar kaji komai zamu sake musu kud’i idan kud’i batayi aiki ba ma gubza dasu, balle ma nasan cash zaiyi aiki, shiga motar ku kawai mu tafi”

“Angama Hajiya KIM”

 

Ya Khairiyya zasu kare a anguwan sojoji da  Coper Chris,

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]