Advertisements
_____
KHAIREEYAH CHAPTER 3
Da asuba ta tashi tayi sallah, ta d’au Qur’ani ta biya karatun jiya, bayan ta gama ta tashi taje fridge ta d’auka totolin ta shanye tas ta d’auka Roci ta tsosa, akasa ta zube tafara bacci kamar ba gobe sai kusan karfe takwas Haule tazo ta tashe ta
“Hajiya ki tashi ki shirya zakiyi lattin makaranta”
Khairiya tace cikin bacci “yanxu karfe nawa neh”
Advertisements
_____
“Takwas hajiya, umm yi hakuri eight O’clock (8:00)
Khairiya batasan lokacin da ta tashi ba, cire kayan ta tafara agaban Haule, tace
“Haule cire mini uniform nawa, ki saka mini burger biyo da coke biyu a mota, socks nawa da takalmi na duk ki cire ki ajiye mini”
Tana fad’a ta shiga toilet tayi wanka cikin minti biyar tafito, mai ta shafa ta saka uniform nata, zama tayi tana shafa powder (huda) Haule kuma tana saka mata socks da takalmi a kafarta, bayan tagama tace Haule fito mini da jakata mota, takwas da rabi ta shiga mota ta zauna a ownest corner, d’aukan burger tayi tafara ci tana jiran driver yaja ta har tayi minti d’aya bataga driver ba
Fita tayi a motar tana ihun kiran Imran, amma shuru, dattijon nanne Garba yace
“Hajiya sai hakuri wlhy baiji sauki baneh shiyasa yau ma baizo ba”
Khairiya ta juya ta harare shi taja wani dogon tsoki tace
“Toh abakin aikin sa, kar na kara ganin sa a gida nah, nonsense” Garba na rokonta amma ku tsaya sauraran sa batayi ba
Shiga motar ta tayi ta fisga, kamar kullum tana gudu akan titi dan ita sam bata iya driving mota a hankali ba cikin minti takwas ta isa makaranta, karfe takwas maigadi yake rufe gate amma ita tana zuwa zai bud’e mata a kowani lokaci dan yasan halinta bata da mutunci kuma tana basa kud’i sosai
Shigan ta class malamin Biology neh a ciki, Corper neh (d’an bautan kasa)daga Imo state, sunan sa Christopher amma ana kiran sa da Corper Chris
Shiga tayi ba koh excuse,taku takeyi kamar batason taka kasa, kallo ya bita dashi sama da kasa yana had’e miyau, ya dakatar da ita yace
“Hea you, why do you come late”
Tana tafiya tace masa
“Issues”
Kallon mamaki yamata yace ” what’s your name” yana tambayar sunan ta
Sanda ta zauna akan kujeran ta tabaje kan tace
*” Kim”*
Yace “what type of name is this”
Batare da ta kalle shi ba tace “Meaning Khairiya Ibrahim Muhammad, my friends call me Kim that’s in shortcut”
Yana lashe le6a yace “Kim Met me after class”
Ko ansa masa batayi ba, yana koyarwa tana d’an joter wa, dan Jamb saura sati biyu, bayan an tashi a makaranta aka basu hutu sai bayan Jamb su dawo, zata shiga motar ta kenan sai ga Corper Chris yace
“What happen i’ve been waiting for you in my office”
_(ya baki zo office nawa ba ina ta jiranki)_
Khairiya kallon kama raina ni ta masa tace
“Nincompoop kawai”she mumbled, ta fad’a a hankali kan tasake cewa
“ni zanje na sameka a office, Allah sawwaka, just tell me your problem now banda time da zan samei ka a office”
Ba abun da yaji sai just tell me your problem, abun bai masa dad’i ba amma she’s too hot to ignore bazai iya barin taba, yana murmushi yace
“Amm I just wanna say you are Hot”
Tsoki taja ta kallesa sama da kasa tace
“I know m HOT, u don’t have to say it”
Corper Chris yana lashe baki yace
“Emm I want you to come to my house, so that we can catch some Fun”
Sarai tasan mei yake nufi, tufar da miyau tayi ta kalle sa, kallon tsana tace
“Kai amma Allah ya’isa tsakani na da kai, ni mazan larabawa da Indiya wa ma basa burgeni balle kai inyamuri, kama cuce ni ka raina ni wlhy, bari zan koya maka hankali” ta fad’a tana murmushi
Duk abun da take fad’a bai jiba, amma yasan bata amince ba, yace “I dnt get you Kim what do you mean”
_(Ban fahimce kiba Kim)_
Murmushi Khairiya tayi tace
“Dont worry Chris, just give me your address, tomorrow is Saturday right?, Expect me in d Morning around nine, I’m gonna spend the whole day with u, I love catching Fun, catching Fun is my favorite”
Wani shu’umin murmushi yayi, mika masa takarda da biro khairiya tayi tace “write it down, I mean your address”
Kar6a yayi ya rubuta mata har number wayan shi, yace
“What do u want me to keep for you”
Tayi murmushin mugunta tace
“You, I just want you en nothing else”
Wani dad’i yaji kamar ya kashe shi, sai godiya yake mata, ta hau motar ta ta fisge shi, tana barin haraban Makarantan Wayar ta ta kunna ta latsa numban Kamalu bad (shineh da yaransa suka ma Zil duka a shopping mall), Kamalu badd sunan da ake kiran shi kenan, shineh babban su a ‘yan ta’adda
Kamalu badd na d’aukan wayan Khairiya tace
“Akwai aiki tomorrow in the morning, kazo around nine kaji, kar kaje kana mini shirme kace baka ganeh time ba, what I mean is kazo kafin Tara na safe” koh jiran ansa batayi ba tayi hanging call d’in
9/10
Advertisements
_____