[Advertisements⬇️]

KHAIREEYAH CHAPTER 2 - Bankinhausanovels
Mon. Mar 27th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

KAHIREEYAH CHAPTER 2

 

Har kofan gida suka kaita, bud’e zip na jakar ta tayi ta cire bundle na d’ari biyar ta mika musu, sai godiya suke mata suka hau motar su suka tafi, horn tayi da karfe aka bud’e mata gate tashiga, da kyar ta iya takawa zuwa falo tana d’ingishi dan tasha duka
Tana shiga parlour ta baje akan kujera, masu aiki neh har uku suka zo kanta suna gaishe ta hajia Ina yini
Koh amsawa batayi ba tace
“Haule kije ki kawo ruwan zafi da towel” toh hajiya wanda aka kira da haule tabar wajen
Khairiya ta kara juyawa tace “Indo kunna mini TV ki mika mini remote” hakan kuwa Indo tayi
Sai ta kara juyawa wajen d’ayan mai aikin tace “Dije wani abinci kika dafa”
Dije tace abinda kikace na dafa da safe hajiya
Wani kallo khairiya ta watsa mata tace “da ban manta ba zan 6ata lokaci nah na tambaye ki neh very stupid mata kawai”
Dije ta durkusa har kasa tana cewa hajiya kiyi hakuri sauce na kwai da coconut rice na dafa
Wani dogon tsoki Khairiya taja sannan tace “toh yanxu banso na cishi, soya mini plantain sai ki had’a mini da pizza nah ki kawo mini”
Dije ta durkusa har kasa tace toh hajiya, Haule tazo da abun da Khairiya tace ta kawo ruwan zafi da towel
Khairiya ta tashi ta shiga d’akinta tacire uniform na makarantan ta tad’aura towel ta fito zuwa parlour, tacewa Haule
“Zoki matsa mini jiki”
Haule ta tsuguna tafara matsa mata da ruwan zafin, tagama ta shafa mata aboniki (man zafi), hajiya mei yasamei ki haka
Kallo Khairiya ta watsa mata tace “Ina ruwan ki dani, nifa bana son gulma, iyayen da suka haife ni ba mance wa dani sukayi ba, ke ina ruwan ki”
Haule sai hakuri take bata tana cewa hajiya kiyi hakuri dan Allah, tsoki khairiya taje tace “oya tashi ki bani wuri” Haule ta tashi tabar mata parlour
Kallon TV take a channel na Dubai sport suna nuna games da akeyi na Olympic Rio wanda akeyi a Brazil, wayan ta neh yafara ringing, screen d’in ta kura wa ido, number neh yake kiran ta amma ba code na nigeria baneh, tasan Abba baya Nigeria yana Qatar amma wannan ba code na Qatar baneh, d’aukan wayan tayi tasaka a loudspeeker ta ajiye a table na gaban ta tace
“Hello”
Dagacan 6angaren muryan wata mata neh mei zak’in gaske tace
“Baby nah yakike, ina ta trying number ki for the past sati biyu amma baya shiga”
Khairiya ta numfasa, tayi shuru na wasu second (dakikai) batace komai ba, matar takara cewa
“Daughter na bakya ji neh koh network naku bakyau”
Khairiya katse wayan tayi taja wani dogon tsoki, haka wayan yana ringing bata d’auka ba sai can daga baya ta d’aga wayan,ta saka a loudspeaker ta ajiye a cinyan ta, matar tace
“Hlo haba baby nah kiyi hakuri zanzo na duba ki very soon, your mum really miss you karki damu zanzo kinji baby”
Tun Khairiya na hawaye har ta fashe da kuka, matar nan tana jin kukan Khairiya tace
“No pls don’t cry baby nah, kiyi hakuri kinsan halin Alhaji bature baya bari nah sosai amma will have time nazo na duba ki I promise you, na miki alkawari kinji pls kidai na kuka, yanxu Ina Brazil kinsan ana Olympic games a wajen, Ina Abban ki”
Khairiya tana kuka tace “Ammi yanxu har mijin ki yafi miki akan ‘yarki na cikin ki, sai kiyi sati biyu, uku wata d’aya ba tare da kin kirani ba, kiyi shekara bakizo dubani ba, dan Allah kar ki sake kirana ma na hakura” ta katse wayar
Wani kuka ta fashe dashi, sanda tayi mai isarta tayi shuru, kwalawa Haule kira tayi, Haule tazo ta durkusa a gabanta tace hajiya gani
Khairiya tace “Haule yau wace rana”
Haule tace “Hajiya yau Alhamis”
Khairiya tace “ke ni bansan miki wani Alhamis ba idan zaki mini da yaren da zan ganeh toh ”
Haule ta durkusa tace “Hajia kiyi hakuri yau Thursday”
Mtsew shineh sai kin 6ata wa mutum lokaci, shiga ciki ki d’aukan mini hijabi nah da Qur’ani nah yau malamin nan zaizo nayi sallah na koya hadda, kuma kicewa Dije idan bata kawo abincin nan a minti d’aya ba toh abakin aikin ta, very lazy people kawai

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Can da daddare bayan Sallah isha’i malam Ali yazo, shineh malamin da yake kara mata Qur’an, tun da tazo duniya bata ta6a ganin mutumin da take shakkan sa kamar Mallam Ali ba, ita kanta abun mamaki yake bata, idan yakara mata karatu zama take tsakanin ta da Allah dan ganin ta haddace, bayan yazo ta basa hadda yamata karen karatu ya tafi, tana shiga d’akin ta taga wayan ta yana ringing, Swt Abba a rubuce akan screen d’in, da sauri ta d’auka tana murmushi tace
“My swt Abba, yaushe zaka dawo ina missing naka” tana fad’a tana tura bakin ta
Yace kar ki damu Mamata very soon zanzo, gobe zanbar Qatar zanje Cuba akwai wani meeting da nake dashi a wajen
Khairiya tace “gaskia Abba nagaji da zama ni kad’ai kayi aure kuma kaki”
“Kar ki damu Mamata ina zuwa sai ki nemo mini matan aure kinji” Toh daddy tana dariya
Abban yakara cewa “Mamata yaushe zaku fara Exams”
“Abba zamuyi jamb Next 2weeks (sati biyu), Waec da Neco ma zamu fara wata mei zuwa
Abba yace “Yawwa Mamata kiyi karatu kinji, hope dai Mallam Ali yana zuwa”
“Eh yana zuwa Abba”
“Yawwa Mamata kiyi karatu kinji, zuwa sati uku zan dawo, take care”

Khairiya tace ” ok dad” ta katse wayan, d’aukan Qur’ani tayi dan koya haddan da Mallam Ali yamata d’azu, ita a rayuwar ta bata ta6a zuwa islamiya ba, bata san komai ba sai Qur’an da Tajwid, bata san komai akan su Fiqh da Hadisai ba da sauran littatafai (yan uwa kar muce Qur’ani ya ishemu yana da kyau musan sauran littattafai is very important)
Bayan nan tahau gadonta ta karanta fatiha, iklas, falaq, nas, da ayatul kursiyu tashafa ajikinta takwanta bacci, wayan ta neh yafara ringing, yatayar da ita daga baccin tana dubawa taga number da d’azu Ammi takira ta dashi ne kin d’agawa tayi tacigaba da baccinta.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]