[Advertisements⬇️]
[Continue Reading⬇️]
JENNIFA CHAPTER 17
Gaba dayansu rikicewa sukayi musamman Momy da ta dora hannu aka cikin wani mugun yanayi narashin tabbas Yar mutane ta mutu a dalilina rubayyace ta turesu daga jikin jennifer ta kamota sbd nauyi ta kasa sai da ta nemi temakon su sa’a suka kama mata ita suwaiba kuwa aikin rusa kuka take cike da jimamin faruwar abun da kyar suka iya dagata saboda mutuwar da jikinsu yayi suka sata a mota Rubayya taja motar suwaiba ta shiga sbd rudewar da sukayi bame me gyale asalima sun mance yanda suka fice Momy kasa xuwa tayi gani take babu wani sauki Jennifer ta riga mu gidan gsky hawaye ke bin fuskarta da tarin Dana Sani na rashin kula da yarinyar har wuta ta jata haduwa sukai ababban falo bamai cewa kowa uffan inbanda jimami da raddadi zahra ma arikice take hnklinta yai masifar tashi damuwa da fargaba suka taran mata tagumi tayi cike da danasani tana ta jera duk adduar da taxo bakinta akan Allah ya Sa Jennifer ba mutuwa tayiba Jidda ma tagumin tayi cike da mutuwar jiki tana mmkin ganinta yanxu yanxu amma har rai yayi hnlinsa tuni xuciyarta ta tsorata da hukuncin ubangiji cikin damuwa da jimami tacewa Momy yaakayi ta taba soket din har wuta ta jata kasa bata amsa Momy tayi dan ita kadai tasan me takeji aranta girgixa mata kai kawai tayi jin tmbyr da Jidda tayi yasa zahra kara rudewa dan itace ummul aba’isin wannan bala’in da ayanxu take matukar Dana sanin aikata hakan
Cikin asibitin suka shiga gadon daukar marasa lafiya nos sukaxo dashi suka dauki Jennifer cikin gaggawa suka shigar da ita dakin duba marasa lafiya agagguce likitocin suka rufu akanta suna iya bakin kokarinsu safa da marwa ruby take yi suwaiba na gefe adurkushe tana xubda hawaye a xuciyarta kuwa xabga addua takeyi na Allah ya tashi kafadar Jennifer lallai sai yanxu ta tabbatarwa da kanta tayi mugun sabo da ita sun dauki dogon lokaci suna cikin damuwa hade da fargabar halin da Jennifer take ciki bayan dogon lokaci Dr ya fito yace su kwantar da hnklinsu ta farfado xasuyi mata duk abinda ya dace ya wuce office dan ya rubuta musu abubuwan da suke so abata da magungunan daya dace da lalurarta hamdala dukansu sukayi cike da murna na sai alokacin suka gane yanayin da sukabar gida bayan Dr ya basu list din yace yanxu yanxu akeso ta karba ta fito akan suwaiba ta kula da ita xataje ta siyo sannan xata koma gida ta sanar da Momy sbd ta mance wayarta agida
A yadda ta barsu haka tashigo gidan ta samesu da sauri Momy ta kalleta tana son jin Karin bayani Momy ta farka numfashi taja mai karfi hade da ajiyar xuciya gumi ya karyo mata cike da murna tace alhamdulillah itama zahra hamdalar tayi aranta na jin dadin bata kashe rai ba bana tausayin halin da Jennifern take ciki ba ta mike xata hau sama ruby ta dakatar da ita zahra ! Ta tsaya tana kallonta kinsan ke kika jefa mu cikin wannan yanayin ?? Rai fa duk raine bata rai tayi kinga nifa bansan xata jata da yawa haka ba toma menene abinda yadace ta itane tunda jininta ya halatta ta karasa mgnr hade da yatsine fuska da murguda baki injiwa yace jininta halattacce ne ?? Ki ka kuskura kika dauki rai koda na kafurine in dai baya cikin sharuddan kisa a addini kin aikata babban kuskure kuma wutar Allah sai ta ciki tsaki zahra tayi to yanxu tunda bata mutunba sai asakar min Mara nai fitsari taja tsaki ta haye sama Momy da Jidda kasa mgn sukayi sbd mmkin da xahra ta basu hmmm Allah ya shirya min ke zahra ruby ta fada cike da damuwa da kuma mmkin kiyayyar zahra akan Jennifer
****************
Ta bude ido ta gansu akanta ta lumshe ido hawaye ya sauko mata ganin ta bude ido yasa suka fara mata sannu sannu kai ta daga musu ta riko hannun suwaiba muryar ta na rawa tace suwaiba naji dadi da Allah yasa ban mutu ba batare da na karbi addinin musulinci ba tabbas Allah na sona tunda har na rayu kuma ina Sa ran samun gafararsa da rahamarsa hawaye ya sauko mata in shaa Allah da lokaci yayi zan dawo kamarku nima xuciyta ta Dade da yadda da addinin musulunci tun ina yarinya karbane kawai banyi ba amma yanxu lokaci ya kusa gaba dayansu mmk ta basu da kuma tsananin tausayi Momy ta karaso kusa da ita inshaa Allah xaki rayu xaki karbi addinin Allah ki mutu acikinsa ki kwantar da hnklinki komai yana da time banko kofa akayi haisam tsaye bakin kofa cikin tashin hnklin yayo wajanta yasalam Jennifer sannu yanxu nakoma gida danjuma yake bani lbr ban baro gida ba sai da nakira office na nefa akan suxo su gyara wajan sannu my Jennifer kusa da ita yakara so fuskarshi cike da tausayinta da kuma tashin hnkl
******************
Cikin hukuncin Allah cikin kwanaki uku ta warware sbd yanda doctors din asibitin suke kula da ita lallai tasha gata awajan yan gidan tmkr yarsu haka suka maida ita komai na jin dadi sun ajjiye mata xahra ce kawai taxo hospital din sau 1 sukam kullum anan suke yini haka Momy ta kafa ta tsare akan bataso iyayenta suji zancen dan kada hnklinsu ya tashi su dauki matakin rabata da gidan ita kanta Jennifer batai karanbanin tunanin sanar dasu ba dan muddin suka Sani to dukkan plan dinta ya rushe kulawar da suka nuna mata yasa takara sakankacewa ta kuma dauki damarar duk rintsi tana tare dasu har burinta ya cike suka daine mutanen da tai mu’amala dasu ta kuma yi sabo dasu sabanin iyayenta dan mamanta bata barinta mu’amala da musulmai dan tsoron karta musulunta tunda sunfuskanci Sam addininsu bai damu Jennifern ba
[Advertisements⬇️]
[Continue Reading⬇️]
Yau aka salla mota suka dawo gida ta murmure sai rashin karbin jiki shima sai a hnkl xata koma nrml Momy canza mata daki tayi ta dawo da ita bangaren yanmatan gidan Jennifer taji dadin hakan sosai zahra kam taji haushi dan kiri kiri ta nuna bata so hakan ta faru ba da yamma suna babban falon gidan kamar yadda suka saba ya haisam ya shigo hira sukeyi banda Jennifer da tayi shiru tana tunanin wasu abubuwa da ita kadai tasansu ya xauna kusa da Momy ya dan kalli Jennifer yace ya jiki ? Kanta asunkuye cikin jin nauyi da kunya ta amsa da sauki Momy yaufa 12: jirginsu khaleel xai sauka Jidda cike da jin dadi ta mike tana rawa oyoyo my heart yau xai dawo dariya dukansu sukayi haisam yace ke kam kinfiya dauki ko irin Jan class din nan da kuma kunya tai far da ido wa zanjiwa kunya ?? Ya nuna Momy da ido tabbi momyn tawa ta taho da sauri ta rungume Momy momyn ta tallabota tana dariya wai fa kinji Momy ke xanji kunya
Murmushi kawai momyn tayi ruby tace ai Anty Jidda bata hada kowa da ya khaleel dinta ba inkaga tana rawar kafa to tana kusa dashi far Jidda tayi da ido sbd shi na musamman ne shiyasa nake rawar jiki akansa kada wata ta kwace min shi haisam yace ba mmk a tafiyar nan tashi yasamu wata girlfriend a can zaro ido tayi hade da bata rai ya haisam xamu bata fa ta shagwabe fuska Momy 😫😫kina jin yaya haisam ko Momy ta jijjiga ta sorry shareshi kin San halinsa dan tsokana haisam yace to shagwabatu da anyi mgn kice Momy 😫 kamar ke kadaice me ita
mikewa Jennifer tayi dan tagaji da jin hirarsu mai bata haushi dakinta sabo ta koma ta kwanta ta rufe kanta da bargo hawaye ya sauko mata
*****************
Tun 11: sukaje airport tarar shi Jennifer ma ta bisu dan yanxu sun maida ita tamkar tasu janta sukeyi sosai ajiki sbd sunji tana muradin addinin musulunci itakam taji dadin wannan mugunta ta xahra tunda gashi ta dalilin haka tana samun kulawa da kuma tausayawa tana ganin ta haka ne babban burinta xai ciki 12:10 jirginsu ya khaleel ya sauka suna tsaye wajan masu jira suka hangoshi hannunsa dauke da jakar shi dayan hannun kuma rike da iphat cikin kasaita da isa yake jefa kafarsa Jennifer na hangoshi gabanta ya fadi yayi Kyau yayi haske ya danyi kiba yana karaso wa Jidda tasa kukan shagwaba ta fada jikinshi yayi murmushi ya dan ture ta kadan hade da rike mata hannu yan uwan ma rungumeshi sukayi suna fadin oyoyo 1 week kawai amma kowa yayi missing dinka bai kula da itaba sai da ya kusa shiga mota ya ganta arakube ya kura mata ido bai San lokacin da yace kinyi rashin lfy ne ?? Turus sukayi gaba dayansu cike da mmkin tambayar da yai mata ganin jikinsu yayi sanyi yasa yace kin koma gefe kin rakube kamar Mara lfy oya Ku shigo mota mutafi nagaji ina son hutawa suka shiga mota dukansu suka bar wajan
*******************
Bayan kwna 2 da dawowarsa daga Singapore suna xaune basu Dade da gama yin breakfast va duk da yaga sauye sauye akan Jennifer bai nuna ya lura da hakan ba sbd miskilanci Jidda sai shishshige masa takeyi duk inda ya xauna tana kusa da shi Jennifer tun tana damuwa har tafa ra hkr ta xuba musu ido yauma tana kusa dashi tace sweeter ina tsaraba oh ! Ya fada na manta ke ! Yacewa Jennifer ta kalleshi ya miko mata key din dakinsa kije ki daukomin wata karamar jaka ta amsa tafice haushin shi duk ya kamata ta dauko ta kawo masa ya ciro wayoyi masu Kyau da tsada iPhone last ta wannan year din ya raba musu suka hau murna dukansu abin mmk ya dauko irinta sak ya mikawa Jennifer sororo sukayi dukansu ita kanta Jennifer mmk abin ya bata ciki kuwa har da Momy Jidda kasa boye kishinta tayi ya xakayi hk khaleel ka hada bamu kyauta da Yar aiki zahra ma mugun kallo tabi Jennifer ta shi ita kanta Momy da Rubayya wani rikitaccen kallo sukewa Jennifer ta sunkuyar da kanta kamar ta fashe da kuka tsawa Jidda tayi masa ganin bashi da niyyar amsa mata tmbyrta me kake nufi !? Ya dago kai hnkl kwance ni kikewa tsawa ? Sbd kin maidani danki ko ? Abinda kikeso xanyi ? Xaki iya hidimta min kamar yadda takemin gyaren daki girkina duk itace kifada min kintaba min daya daga ciki?? cikin jin haushi tace ai biyanta akeyi afusace yace ke kike biyanta abinda naga dama shinakeyi bakuma Wanda ya isa yace min danme idan kina so mushirya kibi tsarina idan kuwa ba haka ba ki kuka da kanki ya mike yabar falon tasa kuka ta mike tana sane ta takwa Jennifer hannu harda murxawa tai sama tana kuka
[Advertisements⬇️]
[Continue Reading⬇️]