JENNIFA CHAPTER 16

JENNIFA CHAPTER 16

 

 

Suna shiga gida daki ta wuce xuciyarta na kuna akan abinda zahra tai mata wai tana warin rashin tsarki girgiza kai tayi ita tasan Kristen ce ita amma tana kula da kanta asalima tasha taji ance bata kama da yare why zahra take mata haka ?? Tayi imanin babu abinda zahra ta fita na kyawun jiki asalima tasan tafita kyan fuska dana jiki harda na hali tunda ita bata kyamatar dan adam a kitchen ta yaradda Suwaiba tana aiki takusa gamawa Jennifer tasa hannu suka fara aikin suwaiba ce ta kalli Jennifer cikin kulawa Jennifer anya kuwa kina lfy ? Me kika gani ?? Naga ba haka kika fitaba kin fita cikin farin ciki kin dawo da bacin rai ko dai sun miki cin mutuncin da suka saba musamman zahra wllh ina gida ina addu’ar Allah yasa Ku rabu lfy dan wulakancin zahra ba Wanda ta bari hawaye ne ya saukowa Jennifer suwaiba ta fadi sunanta cikin muryar kuka shin Kristen awajan wasu ba mutun bane ??baxan iya cewa duka ba amma acikin kalilansu ina samun cusgunawa da wulakanci sosai durkushewa tayi awajan sakamakon kuka dayaci karfinta meyasa baxasu fahimta bane ? Baxasu fahimceni ba ina cikin matsala suwaiba matsalar dana ke ciki ta wuce tunani dan ta daukan rai ce ! Ta rushe da kuka suwaiba ta xaro ido cikin mmk tace bangane ba Jennifer ?? Ta daukan rai ? daga mata kai tayi tana goge hawaye karbar musulinci dai dai yake da daina numfashina ! Subhanallah suwaiba ta fada babu mai kashewa ko rayawa sai Allah kada wannan ya firgita ki kar ya baki tsoro girgixa kai takumayi tana cigaba da kukan suwaiba baxaki gane bane akwai abubuwan dana ke jira da lokaci yayi zan yankewa kaina hukuncin daya dace ta mike da ga durkutsan datayi zahra ta cimin mutunci sbd suna ganin kamar akwai wani abu tsakani na da ya khaleel xare ido suwaiba tayi cikin mutuwar jiki dan Jennifer ta bata tausayi kiyi hkr kin San kowanne mutun da kalar tunaninsa da kuma imaninsa wasu gani sukeyi kamar su na daban ne da Allah ya haliccesu da baiwa irin tasa ko dukiya Kyau ko wata baiwa su kam me xaisa suyi tunanin wani abu tsakanin ki da shi ? Hawaye na bin fuskarta ta ce sbd son xuciya me ya khaleel xaiyi dani ? Nifa Kristen ce abar kyamata sannan ba Yar kowaba mamana abinci take siyarwa ta kuma fashewa da kuka son xuciyane yasa sukai tunanin haka bayadda xa ai ya khaleel me ji da kansa me son addininsa ya iya jina aransa shi din sai manyan yara irinsu Anty Jidda tsarinsa da haduwar Sa Sam ba irin tawa bace takarasa mgnr da kuka kiyi shiru Jennifer ba Wanda yafi wani acikin halitta sai mai tsoron Allah kada kisa hk aranki yai miki tasiri komai yana iya faruwa hukuncin Allah yana sauya komai suwaiba jennifer ta kira sunanta kiyi shiru plx yarenmu ba daya ba haka ma addininmu amma ina jinki kamar yar’uwata nasan Ku musulmin kun San girman alkawari toh alkawarin ne xaisa na fada miki abinda ya khaleel yake min yana yawan tsareni da tmbyr ina da damuwa ? Ko ina da abinda zance musamman lokacin dayake waya da Anty Jidda me yake nufi ?? Tasa hannu da share hawayen da ya xubo mata ina son ya khaleel suwaiba ta xaro ido amma koda soyayyarsa xata kasheni baxan taba fada masa ba sbd ruwa ba Sa an kwando bane yafi karfina ina ganin hakan yagane a tattare dani shiyasa yakemin tmbyr nan dana dauketa ta rainin wayo duk da nasan babu aibu a addininmu mace tace tana son namiji amma shi tunda ya nuna haka yake son yaji na furta tokam baxai taba ji ba matsowa suwaiba tayi kusa da ita nikaina Jennifer na fuskanci akwai abinda ke son faruwa tsakanin ki da shi musamman yadda ba ya iya cin abincin kowa sai naki duk yawan ma’aikatan gidan nan ba yadda kowa ya shiga dakinsa sai ke ciki kuwa harda kannansa hakan yana daure min kai lallai kam yana ganin soyayyarshi a wajanki shiyasa yake miki wannan tmbyr ruwa ba sa’an kwando bane ya khaleel kam hakimtaccen namijine basarake me ji da gayu da miskilanci da Kyau da kuma aji da wayewa ko ba’afada ba ansan yafi karfinki mutumin da mgn ma cikin kasaita da isa yakeyinta babban kyawun halinsa shine baya wulakanta kowa to Harkan mutum ma bai shiga ba bare ya wulakanta ka hakane suwaiba zan cireshi araina duk Dana San da kyar in xai ciru addu’a xaki tayani zo mutafi daki tunda mun gama

 

 

 

Yau ta kama asabar da safe bayan sun gama aikace aikacensu sunfito daga kitchen zahra suka hango kuzo tafada da kyar kamar mai ciwon baki daki xaku gyaramin suka bi bayanta ta shiga gaba tana xuwa tabaje a kan gadonta tana musu kallon dai dai suwaiba fara karkade karkade Jennifer ta wuce toilet din ta ta wanke shi tas zahra ta shigo toilet din kinga kunna heater din nan inga ko tana da matsala Jennifer jikinta na rawa sbd tsoro hannunta da danshin ruwa takai hannunta ashe zahra tasan wajan yana da matsala da gangan tasa ta tana tabawa gam ya rike mata hannu shockin mai axaba ya jata ta kwalla kara da gudu suwaiba tayo wajan tana ganin me ke faruwa tasa ihu sbd yadda taga jikin jennifer na rawa gaba daya zahra na tsaye tana kallonta aguje suwaiba ta sauka tana kurma ihun kawo dauki hakan yaja hnklin yan gidan suka fito da kyar ta fadawa Momy tana zabga ihu hnklin Momy ya tashi da sauri ta fita data danjuma yakashe wutar gidan gaba dayanta suka hau saman dukansu cikin tashin hnkl akwance suka tadda zahra tana game a wayarta hnklinta kwance ga Jennifer kwance ba rai akasa wajan bakin kofar toilet dinta suwaiba tai kanta ta ba jikinta ba inda yake motsi araxane Momy ta ture suwaiba kusa da Jennifer hade da Sa hannunta akan cikinta numfashin Momy sai da yakusa daukewa sbd firgici innalillahi ta mutu Momy ta fada agigice Yar mutane ta mutu a hannuna araxane zahra ta mike tana zare ido cikin faduwar gaba wata kara suwaiba ta kurma mai gigita kunnuwa

 

 

 

About Ismail

Check Also

BAKAR INUWA CHAPTER 23

Ganin taƙi cin komai Anne ta kira sunanta. Ta ɗago domin amsawa taci karo da …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *