[Advertisements⬇️]

JENNIFA CHAPTER 15 - Bankinhausanovels
Mon. Mar 27th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

JENNIFA CHAPTER 15

 

 

 

Tun xuwanshi saudiyya ya dage da addu’a sosai kullum yana masallaci yana adduar samun falala da kuma rahma awajan ubangiji xuciyar shi tafara haske damuwar dayake ji akan sanin wacece Jennifer ta taragu fiye da da dan da wani irin abu yakeji ya tsaya masa arai kansa ya kulle tunani ma rasa wanne iri xaiyi yanxu kam xuciyarshi tayi tass yasamu kwarin gwiwar da xaiyi binciken asalinta da kuma manufarta na munafuntarsu sai dai tunda yaje basu haduba daya idar da ibadarsa aikin nemanta yake tafiya haryanxu basu haduba

 

Kwanakin daya kesonyi sun kusa karewa xuciyarshi ta fara taradda din ko shareef al Hussain y samu nasarar kasheta ?? Dam gabanshi ya buga ya salam ! Dukkan mai rai mamacine amma baxaiji dadin mutuwar ta ba yaso ace ta musulunta ta tuba sannan yana son jin lbrinta dafa kanshi yayi shikam baita ba cin karo da wannan al’amarin ba koda kuwa a films tashi yai ya koma masallaci yai addu’a sosai sai dare ya dawo gida ya shirya kayansa a jaka dan gobe yake son wucewa ranso bai soba tunaninshi Jennifer bata raye ya kwanta ranshi abace

 

 

 

Washegari ya shirya ya fito ya hau motar daxata kaishi airport ya sauka daga motar ya shiga ciki

 

Bayan sungama masa komai ya xauna jiran time dan sai 1 jirginsu xai tashi wata mota ya hango mai Kyau sosai ta shigo tai parking ya kalli motar tai masa Kyau a ido ya kauda kansa ya cigaba da kallon shuke shuken da ke wajan dai dai lokacin daya ji sanarwar passengers wayanda suka da wo daga Egypt sun sauka ya sunkuyar da kansa kasa yana dagowa yaga wata mace mai kiba fara irin farin 9ja ya kuma kallonta yana son tunu inda ya santa wata ya hango sanye cikin riga da wando Pakistan ta yafa kyalen kayan akanta bayanta ya hango baiga fuskarba rungume juna sukayi suna dariya kana ganinsu kaga jin dadi da kwanciyar hnkl waiwayor daxatayi gabansa yai mummunan faduwa da sauri ya mike hade dayin Hamdala ya nufo su yana jin dadin sake ganinta kafin ya karaso har ta budewa babbar macen nan mota ta shiga itakuma ta xagayo tana kokarin budewa ta shiga Jennifer ! Ya kira sunanta ta waiwayo sbd yaxo gab da ita ta galla mishi harara tana mishi kallon raini fuskarta cike da tsiwa meyasa kike wasa da hankalina ? Dakata tace mishi baka da hnkl ya xaro ido yana mata kallon mmk ko kana da shi ?? Ta tambayeshi da rainin wayo shiru yayi yakasa bata amsa dan yasan da rainin wayo murmushi tayi ta bude mota kadan kaji ka kuma gani ta fada mota driver yaja ya wuce mmkinsa ya karo me yarinyar nan take nufi da kadan kaji kadan kuma ka gani ?? Tana nufin xata kuma cigaba da wahalar masa da tunani ?? Girgixa kai yayi zaiyi watsi da son sanin ko ita wacece koma metake son yi musu Allah ya fita hk time yayi ya hau jirgi ransa abace

 

 

 

 

 

Daki ta shiga ta xauna kusa da suwaiba tana kokarin kishingida suwaiba hnklinta nakan novel tana karantawa hannu Jennifer tasa ta warce buk din da sauri suwaiba ta kalleta tana murmushi dan Allah bani Jennifer in karasa haba a tsurawa buk ido ba’aji ba’a gani karatun novel kawai hmmm baxaki gane bane bakisan dadin da yake cikin karanta novel ba far Jennifer tayi da ido hade da tungura mata buk din gashi nan ki cigaba da aikin kurawa buk ido da sauri suwaiba ta dauka ta dago kai takalli Jennifer gobe Mr coffee xaiyi tafiya dariya Jennifer tayi hade da gyarama xama ya khaleel ba ina xaije xaibi dadi Singapore daxu ina babban falo zan kunna turaren wuta naji suna hirar Jidda tana ta zabga shagwaba Momy tana lallashinta kinsan abin ban haushi ? Jennifer ta girgixa kai kanshi na kan waya yana danne danne baice cikanki ba abin ban haushi tsaki Jennifer taja su suka Sani suwaiba ta cigaba da mgn nafuskanci khaleel din nan miskiline na karshe ace budurwarka na kukan missing dinka sbd xakayi tafiya ka kasa ce mata komai hmmm tabbijam ina son miskilin namiji amma na Mr coffee yayi yawa ajiyar xuciya Jennifer tayi tana jinjina xancen wayar hannunta ta duba kinga lokaci yayi tashi muje mu fara aiki mikewa suwaiba tayi ta cigaba da mgn duk cikinsu mahboob yafi sauki amma kinga Mr pepper karshe kenan haisam tunda ya dawo dai naga kamar yarage wulakanci Jennifer tai dariya watakil inda yaje ne suka Konya masa daraja dan adam sukayi dariya dukansu suka shiga kitchen dan fara aikin abincin dare

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

 

 

 

Washegari bayan yan gidan sungama cin abincin rana Jennifer ta fito tana kwashe kayan tana kaisu kitchen dukansu yan gidan suna babban falo kamar ko yaushe suna hirarsu ke ! Taji muryar ya khaleel yana kiranta ta tsaya cak zonan da sauri tai cikin falon ba wanda ya kalleta sai Momy key ya mika mata shiga dakina ki dauko min jakar akwatina ta amshi key din ta fara tafiya taji Momy nace mishi time fa ya kusayi katashi mana tafice dakinsa ta nufa a hargitse ta tadda dakin ta sunkuya ta sunkuci jakar tafito ta taddasu atsaye jikin motocinsu ta ajjiye jakar tana miko masa key din nop ki koma ki daukomin dayar guda biyu juyawa tayi ta koma ta dauko dayar har ya shiga mota shida Jidda suna baya driver na gaba dayar motar kuma Rubayya ce zahra na kusa da ita Momy ta kalli Jennifer ko xaki bisu shiru tayi tana murmushi jeki ki dauko gyalenki kiyi musu rakiya jiknta asanyaye ta je daki ta dauko gyale ta shiga bayan motar da Rubayya take ja suka bi bayan motar su ya khaleel

 

 

Bayan sun je airport din Jidda na zuba masa shagwaba ta rike masa hannu har time din da akai kiransu tasa kuka ya tsaya yana kallon fuskarta yasa hannu ya goge hawayen da ke xarya a fuskarta kiyi hkr plx 1 week kawai zanyi zan dawo tarike masa hannu biyun duka zanyi missing dinka sosai a wannan week din sannan tasaki hannun kallon Jennifer yayi ke ! Xo ki dauki jakar nan kibiyo ni da ita turuss gaba dayansu sukayi suna mmk da sauri Jidda tace bari na daukar maka a a ajjiyeta tamiki nauyi ganin ba wasa a fuskarshi yasa ta ajjiye jakar da tai saurin dauka sbd yace na dauka hannun Jennifer na rawa ta dauka tabi bayanshi yayin da suka rakata da muguwar harara sunyi tafiya sai da suka xo dai dai wajan da ba dama Jennifer ta shiga ya tsaya yana kallonta murmushin mugunta ya watsa mata da sauri ta sunkuyar da idonta tana son gane fassarar murmushin ke ! Yace mata kina da abinda xakice ?? Tayi shiru tana juya tmbyrshi dan tarasa gane kanta kina da damuwa ne ? Ya kara tmvyrta muryrta na rawa tace bani da abinda xance bani kuma da wata damuwa murmushin mugunta ya kumayi hade da cije lebenshi na kasa ya sunkuya ya dauki jakar da ta ajjiye yai gba tana waiwayo taga duk sun xuba musu ido gabanta ya fadi Takara so kusa dasu dukkansu suka bita da kallon tuhuma mota suka shiga Rubayya na xaune wajan driver zahra na kusa da ita Jidda ta bude baya ta shiga Jennifer ma bayan ta shiga Rubayya taja motar Jennifer Jidda takira sunanta naam ta amsa tana jiran tuhumar daxatai mata menene tsakaninki da khaleel? shiru tayi tana jinjina tmvyr Rubayya ce tai mgn muryarta asanyaye haba Anty Jidda menene kuwa a tsakaninsu ?? Kintaba ganin wani abune sabanin yau ? Mgn ake miki kibamu amsa! zahra ta kwasa mata tsawa Jidda ta kalli Rubayya datake tukin mota bantaba ganin wani abu kuma fatan ganin koma menene in dai akan ya khaleel ne me kuke cewa bayan kunbar kusa damu ? Shiru Jennifer tayi dan tarude tarasa amsar bata inbanda hawaye dake xubar mata a a va kuka nace kiyi ba amsa xakibani tsaki zahra tayi dama munafuki saurin kuka gareshi kin fiya shishshigi kitsaya matsayinki na Yar aiki kibar ganin kinxo gida da manyan matasa samari kyawawa dukkansu bavu sa’anki ke bari kiji gaba dayansu suna da yanmatan da xasu aura koya mahboob din da kike shishshige masa yana da wacca xai aura mufeeda Yar gidan ambassador na India in banda kwadayi ina ke ina xuri’armu ? Kibani amsata malama kar xuciyata ta fashe Jidda ta fada cikin tsawa da daga murya dabara ta fado mata cikin muryar kuka tace cemin yayi na dinka gyara masa daki ina karkadewa baya son ya dawo yaga yayi kura ko datti Hamdala Jidda tayi Rubayya tace shiyasa zargi bashi da amfani kunji ko ? Hankalinku sai ya kwanta dafa kafar Jennifer Jidda tayi kiyi hkr ina son ya khaleel fiye da tunaninki ban taba ganinshi da mace ba sbd yanda halinsa yake na rashin damuwa da mace ganinshi danayi dake naji takaicin da ban taba ji ba kiyi hkr tsaki zahra ta ja meye abin bada hkr ? Warning xaki yi mata ta fita sabgar mazan gidanmu dan masu ajine babu irinta bankiba ko mai gadi ko danjuma driver ya isa haka zahra Rubayya ta katseta mgn ta wuce tsaki zahra ta kumayi plx Anty Jidda mikomin air freshener na kusa dake warin rashin sarki ya dameni ta mika mata tafeshe motar dashi Rubayya ta kunna wakar India tana ji tana bin wakar hade da kyada kai alamun tana son wakar hawaye ya saukowa Jennifer ta runtse ido tana mmkin yan gidan wasunsu masu kirki wasu marasa kirki

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]