[Advertisements⬇️]

JENNIFA CHAPTER 14 - Bankinhausanovels
Mon. Mar 27th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

JENNIFA CHAPTER 14

 

 

 

 

Al’amarinta ya daina bashi mmk sai ta’ajjubi kansa ya daure sosai ya rasa kalan tunanin da xaiyi ya samu mafita ya kwantar da kanshi jikin kujerar mota ranshi na suya shin me xatai musu in sunje cen ?? Meyesa anan take boye muguwar akidarta a can take bayyanawa ?? Oh rabbi ! Kanshi ya daure tamau ahaka suka isa airport xuciyar na suya basu dade ba jirginsu ya tashi fargabarshi ta karu sbd rashin sanin matakin da xata dauka akanshi musamman shi dayake kuntata mata

 

 

 

Cikin dare suka isa direct gidansu na cen suka wuce dakinshi ya zarce yai wanka ya sauya kaya ya bude jakar shi ya dauko laptop din mahboob dan bai mayar mishi ba sbd baya son ya San komai akan Jennifer yafison sai ya ganota Kafin ya tona mata asiri yagama danne dannenshi ya ajjiye laptop din ya kwanta yana kallon rufin dakin girgixa kai yayi hade da futar da iska daga bakinshi ya gyara kwamciyar da yayi ahaka barawo bacci ya kwashe shi

 

 

 

 

Washe gari suka shirya dady ya wuce wajan meeting shi kuma ya tafi wani company dan cen dady ya turashi yaje sugana da masu companyn kan wani aiki da xasuyi musu a darare yaje atunaninshi kowanne lokaci xata iya kawo masa farmaki yagama duk abinda xaiyi sai yamma ya dawo ya tadda dady agida shima ya dawo

 

 

Kwnansu 3 a Dubai har yanxu fargabar Sa bata yankeba dan ko alama basu hadu da ita ba tunaninshi yarinyar ta Sa musu ido tana kallon duk abinda sukeyi tunda duk inda sukaje sai sun ganta tun yana fargabar haduwarsu har ya dake so yake su hadu yasan wacece ita ?? Da daddare suna falo shida dady suna kallon news dady yana yanka lemon bawo yana sha cikin kulawa ya kalli haisam da hnklinshi ke kan tv tunaninshi kuma na cen yadda xasu kare da Jennifer haisam ya waiwayo ya kalli dady naam dady kana lafiya kuwa ? Naga kwana biyu kana yawan tunani kamar kana cikin damuwa gyara xama haisam yayi akan kujera ya kishingida dady bakomai ina lfy katabbata ?? Dady ya tmbyeshi na tabbata dady ya fada yana Sosa gashin kansa OK to haka akeso gobe nake son wucewa Singapore sbd aikin da nafara ina son naje agama shi akan idona kaikuma sai ka tsaya idan companyn cen sungama kaduba kayan ka gani sai ka tura su 9ja xuwa jibi sai ka koma gida to dady Allah ya kaika lafiya amma dady yayi shiru yana kallon wta talla da akeyi a chanal din da suke kallo ina jinka dady ya fda yana kallonshi kallo na kulawa ina son zanje umara zan wuce cen daganan OK to Allah ya kaimu ngd dady murmushi yayi ya cigaba da shan lemon shi yana jin soyayyar yayanshi tamkar hancin cikinsa Wanda inbashi ba rayuwa

 

 

 

 

Washe gari yaraka dady airport bai bar nan ba sai da jirginsu ya tashi ya dawo kan hanya takaici fal ranshi jibi yake son barin Dubai gashi basu hadu da Jennifer ba yaja tsaki natakaici sosai ya koma gida ya shiga daki yai wanka yasauya kaya ya fito falo turus yayi sai da yaji gabansa ya fadi duk da yana namiji wasu manyan garada ya gani marasa kyan kamanni fuskokinsu atamke hannayensu dauke da manyan bindigo lafiya ?? Ya fada da mmk yana kallonsu suwa ye Ku daxaku shigomin gida haka ? Kafin ya gama magana suka rufu akanshi suka daure masa hannu da idanu suka ingixa keyarshi suka fice daga gidan cikin mota suka turashi sannan suka ja motar suka bar gidan

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

 

 

 

Yana cikin mota yayi jigum hnklinshi amatukar tashe yarasa inda xasu kaishi tafiya sukai mai nisa sannan yaji alamun xasu tsaya suna tsaya suka fito dashi suka ingixa keyarshi cikin wani waje Wanda baisan ko inane ba suka tsayar dashi hade da bude masa ido ya bude idon shi da sauri ya rufe sbd hasken wajan da yaiwa idonshi yawa ahankali ahankali ya bude idonshi ya sauka a tamfatsetsen falo me dauke da kujeru jajaye da labulaye ja komai na falon jaa ne babu sirki da sauri ya mike yana kallon garadan dasuka kawoshi nan wajan cikin daga murya yai magana me yasa kuka daukoni kuka kawo ni nan ?? Me nai muku suwaye Ku ?? Ko kallonshi basuyi ba bare su bashi amsa haushi ya kamashi yai musu ashar ko xai tunxirasu su kulashi daga karshe ma GAM suka Sa suka rufe mishi baki suka kuma daure masa ido suka ingixa keyarshi cikin wani waje suka rufe

 

 

Yana cikin wannan halin xuwa wasu awanni sannan yaji alamar bude kofa suka shigo suka bude masa idanu da bakinshi hade da tura masa plate dankaren da abinci wani mugun kallo yake binsu da shi hade da yiwa abincin kallon ko inkula dam Sam bayajin yunwa asalima halin daya ke ciki baxai barshi ya iya cin wani abinciba xugum yayi yana son tuna wanne irin laifi yai aka kawoshi nan ?? Shigowa suka kuma yi hade da ingixa keyarshi xuwa inda suka fara kaishi da farko maza ne manyan garada xagaye da ita dukkansu suna dauke da muggan bindigu tana sanye cikin wando jeans blue black da riga baka gashinta asake ta Dora kafa daya kan daya kana kallonta xaka hango bindigun dake sarkafe jikin aljihunan wandonta fuskarta amurtuke tana masa kallon tuhuma ya wurga mata harara hade da fadin ke wcece ?? Me kike nufi da rayuwarmu ?? Wanne laifi mu ka aikata miki kike kokarin ganin bayanmu ?? Magana nake miki jennifer meyasa kike wasa da hankalina ki fadamin wacece ke ?? Meyasa kika yaudari yangidan mu kika je musu a matsayin Yar aiki ?? Jennifer meyasa kike bibiyarmu duk inda mukaje ?? Ya fada cikin tsawa da daga murya bata ce komai ba in banda mugun kallo da take binshi da shi nakasa gane miki Hindu a Dubai Jennifer a 9ja Sul……….. Yayi shiru hade da rufe kunnanshi sakomakon karar harbi me karfin gaske da sukaji a guje wani katon mutn ya shigo madan da matsala fa shareef al Hussain ya kawo mana hari mikewa tayi adake kowa ya shirya ta nuna daya daga cikin garadan duk rintsi ka maida guy din nan gida ta nuna haisam muje taxaro bindigunta tai waje suka bita haisam ya mike katon nan ya tura shi suka fita ta baruniyar hanya yana jin karar fitar harsashi hnklinshi ya tashi sosai katon yasashi a mota sai da sukai nisa da wajan sannan ya cillo haisam daga mota yatafi ya barshi cikin mutuwar jiki da fargaba ya tari taxi ya maidashi gida da kyar ya shiga gida ya xarce toilet yai wanka ya dauro alwala yai sallolin da baiyiba ya baje a gado yana maida numfashi lallai babu komai afashi face rayuwar wahala da fargabar harin makiya sai yanxu yakejin tausayinta xaiso dalilin dayasa take wannan rayuwar xaiso kuma dalilin dayasa bata cutarda shi ba tabbas da tana son cutar dasu da tuni tayi to meyasa ? Kansa ya daure meyasa bata bashi amsar tmbyoyinsa ba xuwan da su shareef all hussani sukayi ne ya dunkule hannunshi hade da kaiwa iska naushi daren nan da kyar yai barci

 

 

Shiru shiru yana jiran ko xata dawo yaji babu alamunsu har ya gama avinda xaiyi baiji dadi ba Sam yaso ace sun kuma haduwa karo na biyu ko dai su shareef al Hussain sun sami nasarar kasheta ?? Gabansa yai mummunan faduwa nan da nan ya tsinci kansa cikin mugun yanayi no ! No ! No ! Baxaki mutuba Jennifer ina bukatar jin ke wacece ?? Yana xaune a airport hnklinshi atashe jikinsa asanyaye dolene yaje yai addu’a sosai a dakin Allah kafin wannan tunanin yafara yi masa illah ahaka ya shiga jirgi yana addu’ar Allah yasa Jennifer tana cikin kwanciyar hnkl muddin tana lfy dole ta sake nemanshi lumshe ido yayi ranshi na suya idan har tana cikin mugun yanayi bai xama lallai ya taradda da ita a saudiyya ba shi dai babban fatansa Jennifer tana nan araye dan yana jin sautin fitar karar bindigar su shareef al Hussain mai ban tsoro da firgici

 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]