JENNIFA CHAPTER 13

JENNIFA CHAPTER 13

 

 

Mmk ya kamashi da ganin message din bincike ya cigaba dayi yaci karo wani test din daya kara firgitashi na Elmustafha Wanda yaga comment dinshi …. Hi mahbobb plx ina kasan sulthana ??

 

Shiru yayi yana tunanin amsar ba shi da sauri ya tura masa

Class mate dina ce …

 

Bai dade da turawa ba reply ya shigo

Hmm …

Yayi mmkin amsarshi

 

Wat meaning hmmm…

 

Reply ya dawo masa da

Bakomai……

 

Yayi shiru yana naxarin amsoshin almustafha dabara ta fdo kasa da sauri ya tura masa da

Amma yanxu bama tare kwata kwata …

 

 

Shiru bai dawo masa da amsa ba ya koma wajan ammar ibn Muhammad ya tura masa ….

 

ngd sosai bros amma ita din wacece haka ??

 

Yai sa’a shima yana online ya turo masa reply da ….

 

babbar shedaniya ce hatsabibiya Yar safarar kayan maye da fashi da makami kuma babbar yar damfara nayi mmkin ganinka da ita sbd nasan kai mutumin kirkine ganinka da hindu xai iya jefaka cikin masifa dan mutumin arxiki baxai hada sabgarshi da itaba yanxu hk a Dubai wanted ce …..

 

Shiru haisam yayi yarasa amsar bashi

Wani test din Muhammad ya kuma

 

turo mishi…..

Kaima ka shiga tarkonta?? Hindu tana da Kyau kyawunta ke fuskar maza kuma da kyawun nata take amfani wajan yaudaran mutane kayi gaggawar cireta aranka

 

…….

Haisam ya tura masa reply da

 

ngd sosai bros naji dadin shawararka kuma zanyi aiki da ita amma ba Sonta nake ba munyi karatu ne kawai da ita

bai ce komai ba Muhammad banda xare ido da yayi

 

…yana kokarin sauka test din Elmustafha ya shigo da sauri haisam ya duba

 

….. Dole Ku rabu dan yarinyar ba ta da hali fitsararriya ce

 

……

Da sauri haisam ya tura mishi da

…..

Hakane wannan kam shine halinta na rashin kunya….

 

Ya dawo masa amsa …. Neman yarinyar nan nake ruwa a jallo duk lokacin dana ganta sai na lalata mata fuska kowa ya huta tana amfani da kyawun nan nata tana ciwa kowa xarafi

 

…… Shi dai haisam mmk ne sosai ya cikashi ….

Dame xaka lalata mata fuska?….

 

Da acid ….

 

Wanne laifi tai maka ??…

 

Ta ciwa ubangidana zarafi har ta mareshi sanadiyyar hk na rasa aikina shi kuma tundaga wannan lokacin yake bakin ciki zanyi hakanne dan nasashi cikin farin ciki ….

bata kyauta ba …

 

Nayi alkawarin kudi mai yawa ga duk Wanda ya kawomin ita in dai xaka iya kofa abude take ga numb dina nan +9……

Ya karewa number kallo yayi ajiyar xuciya

 

 

Sulthana asaudiyya

Hindu a Dubai

Jennifer a 9jaa

Wacece ita ??

 

Hannu yasa ya dafe kansa wannan al’amari da daure kai yakai Sam yakasa fahimtar komai xame masa dole ya gano wacece ita ?? Me ya kawota gidansu ??? Lallai ya yadda shedaniya ce tunda tana nuna msa shedancinta tanayin abu kamar bai taba haduwa da ita a katsashen nan biyu ba dan karamin tsaki yaja cike da jin haushi xakiyi Dana Sani dan sai na tona mki asiri awajan mutanen da suka yadda dake suka amince miki

 

 

 

 

Tana kwance adaki suwaiba na karatun kur’ani duk tabi ta rude tana saurarenta hnklinta amatukar tashe jikinta har rawa yakeyi wayarta tai kara tana dubawa taga sunan Momy aladabce ta daga ….Jennifer xo ina son ganinki ….

Ta amsa da toh ganinan Momy da sauri ta mike tai bangren momyn ababban falo ta sameta a xaune Jidda tayi matashi ta cinyar ta tana kallon tv tashigo falon suka gaisa yauwa Jennifer xakuje kasuwa tundaxu na aiki danjuma shiru bai dawo ba ga yamma xatayi kuma ba kowa sai haisam da khaleel nasan bakwa shiri da haisam khaleel xai kaiki da sauri Jidda ta daga kanta daga cinyar Momy Momy nima xani murmushi momy tayi svd kinji nace khaleel ne xai kaita sarkin kishi tayi dariya aa Momy bana son ya dinka kallon wasu yanmatan ne a kasuwa ko su su gane minshi kwara na bi abina rike haba Momy tayi oh ! To sai kibishi kiyi ganinsa ta mike bari naje na shirya ta ayangance take tafiya kamar batason taka kasa bakin ciki ya dami Jennifer bata maraba da wannan tafiyar Sam ! Koka dan batayi farin ciki da itaba Momy ta kalli Jennifer kije ki shirya nai masa mgn toh tace ta mike tai bangarensu ranta abace ta koma daki ta canza kaya gown tasa ta atamfa blue da adon yellow ajikinta daura dankwali na bata wuya dan bata saba sakashi ba karamin gyale yellow tasa tai rollin din kanta dashi powder kawai tashafa a fuskarta ta fito ranta abace xata hada tafiya da Jidda da kuma ya khaleel ta runtse ido tasan yau kam sai sun sata takaici babban falo ta koma ta taddashi xaune shida Momy yana sanye da 3 quarter blue black da Riga maroon wacce ta kamashi me kajeran hannu ta fuskanci yana matukar San 3 quarter dan in dai ba wajan da xashi me matukar muhimmanci bane tofa shigar shikenan kwas kwas sukaji da takalmi ta sakko itama sanye cikin wando pencil da riga brown ta Dora kimono gown asamansu sai dan karamin gyale da ta yafa tayi Kyau sosai runtse ido Jennifer tayi cikin tashin hnkl musamman kallon dataga ya khaleel yana mata ga mmkinta sai taji yace Jidda kije kisa hijab ta turo baki tana diren diren kafafu tana shagwaba wanne irin hijab ya khaleel nida ba sallah zanyi ba OK toh babu inda xaki cikin kukan shagwaba ta kwabe baki Momy ??kinga ya khaleel ko ?? Wai baxai je dani ba ni wllh sai naje Momy tace haba khaleel ka kyaleta mana tunda ta riga ta shirya mikewa yayi baice komai ba yafita Jidda tabi bayanshi tana cigaba da kukan shagwaba da dire diren kafafu murmushi Momy tayi ta mikawa Jennifer jakar kudin da xatai siyayya da list din abinda take bukata ta amsa ta fito fuskarta a damke haushin Jidda ya kamata tana kallon lokacin da ta budewa ya khaleel mota sannan ta xagayo ta shiga gaba jikin Jennifer asanyaye ta bude baya tashiga ta rufo mator tana dai daita zamanta cikin motar list din abinda xata siya ya fadi ta sunkuyar da kanta xata dauko dai dai lokacin da Jidda ta Dora kafarta aka taya khaleel da sauri Jennifer ta dago ta jingina da kujerar motar dama tasan kawai yau cinikin bacin ranta xaayi yaja motar suka fice daga gidan Jidda tana xuba masa hira kala kala shi dai yana binta da uhhim ko um ko yace himm a haka sukaje kasuwar a mota Jennifer ta barsu ta shiga ciki bata bata lokaci ba ta gama ta hangosu tsaye ajikin mota taxo gab dasu ya bude mata but taxuba kayan kwala mata kira taji anyi kafin ta waiwayo taji an rungumeta tana waiwayowa taga Janata kawarta a skul cikin murna ta kankameta Jennifer kina nan ?? Ta tmbayeta cike da murna tunda muka gama skul ba’ajin lbrinku wani ne ya karaso kusa dasu sanye cikin coat ash colour ya dafa kafadar Janata yana murmushi Jennifer wannan shine Emanuel yayana da yace karatu a England ya mikowa Jennifer hannu su gaisa da sauri ya khaleel ya mika nashi suka gaisa hade da jifan Jennifer da harara mmk ya kamat ita jidda mmk tayi suka gama gaisawa hade da musayar numbers sukayi sallama suka shiga mota

 

 

 

 

Bayan sun dawo gida ta koma wajan Momy tana falo ita dasu zahra suka shigo tabar Jidda acen wajan ya khaleel tana zama ta shigo ta xauna akan kujera hade da fadin wash ! Momy mun dawo Jennifer ta mike tana shirin tafiya Jidda tqce ta hau sama ta wanke mata toilet Momy tace a a bari sa’a taxo ta wanke miki zahra tace no mom kibari ta wanke tunda itace a nan ta nufi upstairs xata hau Jidda tace kinga kada kiyi wahalar wanke pants din ki hada har pad din ki xubar kai kawai Jennifer ta daga mata ta wuce cike da takaici tana bude toilet din ta ganshi faca faca ga karnin jini haka ta gyara toilet din pants me hade da pad Wanda tai amfani dasu gasu nan xube ta hade su ta xubar xuciyarta na tashi dan tatsani karjin jini tagama xata fito Jidda tashigo dakin cikin fara’a kin gama ko ? Ngd ta miko mata turare Jennifer ta amsa hade da godiya ta fita tana komawa dakinsu ta wuce toilet ta kwara amai tana jinjina wannan kaxantar ta fuskanci Jidda na da kirki kamar Rubayya

 

Da daddare suka shigo itada suwaiba dan debe kayan da masu gidan suka ci abinci a dining suna jin hirarsu kamar ko yaushe cikin nishadi da jin dadi dady yace haisam gobe fa xamu tafi Dubai tare dakai da tare da khaleel xamu tafi kasan yanxu yayi bakuwa ba shi ba barinta dariya dukansu sukayi tana jin muryar zahra harda kyalkyalawa da sauri Jennifer ta kwashe sauran kayan ta fice ranta bace

 

Washe gari da yamma suna babban falo dady da haisam sun shirya xasu tafi Jennifer ta shigo falon tana hawaye lafiya Jennifer ?? Momy ta tambayeta cikin muryar kuka tace rashin lafiyar David ce ta tashi suna asibitin nassarawa zanje nagansu dady yace ayya ! Sorry Allah ya bashi lfy dukansu suka amsa da amin banda haisam da mmkinta yasashi cikin bahagon tunani dady ya xaro kudi masu yawa yabawa Jennifer ta amsa tai gdy ta fito daga falon suma suka fito suka shiga mota driver yaja me gadi ya bude gate dai dai lokacin da xasu fita haisam ya ganta tashiga adaidaita sahu ya runtse ido cikin fargaba dan yasan inda xata shin idan sun hadu da ita acen me xatai musu ? Kasheku xatai xuciyarshi ta bashi amsa kan wane dalili ? Abinda yakasa Sani kenan

 

About Ismail

Check Also

BAKAR INUWA CHAPTER 23

Ganin taƙi cin komai Anne ta kira sunanta. Ta ɗago domin amsawa taci karo da …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *