[Advertisements⬇️]

JENNIFA CHAPTER 11 - Bankinhausanovels
Mon. Mar 27th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

JENNIFA CHAPTER 11

 

Shakar ta yayi sosai tun tana iya ganinshi dushi dushi har sai da ta daina ganin komai I said who are you ?!!! Nishi kawai take xabgawa cikin mayuwacin halin Sam batasan Inda kanta yake ba da gudu mahboob ya karaso ya bankadeshi da karfi yaraf ta fadi ta xube kasa kanta ya bugu da wani katon dutse goshinta ya fashe yana xubda jini  baka da hankali haisam meyasa kk kokarin  kasheta ?? Wannan wane irin zaluncine ina ruwanka da ratuwarta meyasa xaka takura mata wllh!  wllh ! Muddin Jennifer ta mutu sai ankasheka kana son shiga rayuwar da babu ruwanka aciki dan kai ita Kristen cen itaka daice a duniya itaka daice bata  da addini ?? Tmbyr ka nake azzalumi to wllh kasani Jennifer tana da gata babban gata nikaina gatanta ne baxan bari ka cuci yarinyar mutane ba dan kawai takasance Mara addini kai meye bakayi wanne irin aikin ash sha ne baka aikaita wa baki kawai haisam ya saki yana kallon yayansa yana xabga masa fada tamkar Wanda baya cikin hanklinsa ranshi ya baci shima cikin daga murya da karaji meye naka innaka sheta ?? Kaine ubanta ?? Shaka mahboob ya kawo masa haisam ya goce hade da ja baya xaka kashe nine ?? Ko fansa xaka daukar mata khaleel ne ya karaso wajan da gudu ya sureta cikin tashin hnkl mahboob yabi bayansa yasata a mota mahboob ya shiga yaja motar da gudu mai gadi ya bude get ya fice daga gidan cikin tashin hnkl

Oh ya rabbi ! Meye yake faruwa haka ??me Yasa mahboob yai masa wannan shouting din kamar yana fada da babban makiyinsa ? Sun San kuwa irin gatan dayake son musu tabbas yaga bacin rai irin Wanda bai taba gani a fuskar dan uwansa ba musamman khaleel irin gudun daya ga yana zabgawa akan ceton yarinyar ya akayi yai sake haka ta faru ?? Anya kuwa hukuncin daya kamata ya dauka kenan kansa ya Sara da sauri yasa hannu ya rike kan cikin tashin hnkl jiyake tamkar jijiyoyin kansa xasu sinke kan ya fadi ya runtse idonsa yana jijjiga kan subhanallah subhanallahi muryar Momy yaji tana salati haisam ya dago kai da kyar ya kallesu Sam baiga shigowar su ba ita da suwaiba meyasa meka ?? Take tmbyr shi cikin tashin hnkl bakomai Momy kaina ke ciwo tasa hannu ta taba kan tashi muje asibiti a axanje da kaina da sauri ya tashi yana tafe yana yamutsa fuska ya fada mota sororo tayi cikin mutuwar jiki tana kallonsa har ya fice daga gidan

Afusace yake jan motar bai San ina take kaishi ba don’t kill him ! Kuuu yata ka burki muryar Jennifer ya tuno a Dubai data hana dan uwanta dan fashi yakasheshi mmkin kansa yake meyasa ya dauki mummunan mataki irin wannan akanta ?? Wannan ba matakin da ya dace ya dauka ba koka dan baiyi kokarin kasheta ba tayaya xaiyi kisa ?? Baya tunanin koda arashin Sani yataba kashe kuda amma meyasa yashaketa ?? Bai kyauta ba yanxu ya xaiyi in yarinyar ta mutu ?? Shikenan yaxama makashi gabanshi ya fadi fargaba ta darsu aranshi hnklinshi kasa kwanciya yayi zai dauki mataki amma ba irin wannan ba anya kuwa xai iya daurewa batare da yaji a wanne hali take cikiba ?? Motar yaja jikinshi a sanyaye yai hanyar komawa premiere hospital yasan nan ne asibitin gidansu kai tsaye ya shiga cikin asibitin jikinshi asanyaye khaleel ya hango ya jingina  ajikin mota hannunsa rike da kansa girgixa kai yayi ko bai fada ba yasan jinjina halin dayasa Yar mutane yakeyi karaso wa yayi inda yake muryarshi araunane yai masa sallama dagowa khaleel din yai ya amsa ya kuma kauda kai ranshi ya dan baci da abinda khaleel din yai mishi ya dake cikin kwarin gwiwa ya jikin yarinyar kuwa ?? Kafin ya bashi amsa ya hangosu mahboob ya riketa kanta annade shi da bandage hannunshi rike da magungun harara mahboob ya xabgawa haisam kanta akasa bata kula da haisam din ba sai da sukaxo gab da motar yace mata sannu da sauri ta dago kai bata San lokacin data kara kankame mahboob ba tasa kuka sosai dan Allah ya hisam kayi hkr wllh ban fahimci me kake son saniba kunya ta kamashi khaleel ya kalli hannun da ta kankame mahboob haushi ya kamashi da kuma tausayi cikin karfin hali mahboob yace kiyi hkr babu abinda xai miki komai ya wuce asanyaye haisam yace kiyi hkr Jennifer ban kyauta miki ba amma ya wuce hakan baxai kuma faruwa ba tsaki khaleel yaja wanda babu Wanda yasan dalilin tsakin kofar motar ya haisam ya bude Jennifer tashiga har alokacin a tsorace yake dan gani take xai iya kara rufeta da duka khaleel ya shiga yaja motar sukabar haisam anan yana kallonsu har suka fice daga asibitin shima ya shiga motarshi yana mmkin amsar da Jennifer ta bashi kayi hkr ya haisam ban San me kk son Sani ba tsaki yaja natsaneki Jennifer sbd natsani munafunci yaja motarshi yabar asibitin

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Gida suka shiga aharabar gidan suka tadda Momy tana sintiri sbd jinin da taga ni sannan taga haism cikin wani yanayi hnklinta yaki kwanciya ganin Jennifer cikin wannan yanayin ya daga mata hnkl ya’a kayi haka Jennifer meyasa meki ?? Shiru sukayi suna nazarin bata amsar da ta dace da sauri jennifer ta nunawa Momy dutsen idonta ya ciko da kwalla faduwa nayi akanshi innalillahi mahboob kira min danjuma yaxo yafitar da dutsan nan sannu Jennifer ya salam ! Hannu tasa ta janyota jikinta sorry kiyi hkr bansan meyasa sukabar dutsan cen anan ba tashi kije daki ki kwanta wucewa khaleel yayi baice uffan ba sai mahboob daya bi bayanta da magungunan ta

Washe gari ta tashi wuyanta yai tsami ko yaya ta juya sai taji ciwo kanta tasa a filo tana tuna shakar da haisam yai mata taji matukar ciwo ta yadda kam haisam yai mata muguwar tsana wacce xai iya ganin bayanta ta shi tayi dan tagaji da kwanciya bandage din kanta ma ya isheta gashi Momy ta hanata aiki fitowa tayi harabar gidan ta shiga babban falo ta tadda Momy da Rubayya suna kallo suna hira rubayyan takalleta araxane Momy me yasa mi Jennifer ?? Oh Jennifer  ba bigewa tayi da dutse yasalam rubayyan ta fada sannu Jennifer yauwa Anty ruby shigo ki xauna Momy tace mata adarare ta shigo falon ta xauna tana xama sukaji sallama da sauri suka kalli kofar parlour din wata budurwa ce kyakykyawa fara doguwa tana yanayi da su zahra ta shigo sanye cikin less dinkin riga da siket matsatstsu dan sun kamata sosai tayi rolling din kanta da karamin gyale kanta babu dankwali sai gashinta da yasha gyara tayi fakin gashinta gyalen sharara ne kana hango jelar gashinta da sauka awuyanta da sauri Rubayya ta mike cikin murna da daga murya oyoyo oyoyo Anty Jidda ta rungumeta itama jiddan ta rungumeta suna dariya Momy ma dariyar take zahra ta sauko da ga up stairs tana gudu hade da dariya tana fadin oyoyo oyoyo Anty Jidda ta fada jikin jiddan itama ta rungume ta sannan suka saki juna ta karaso ta rungume Momy ta xauna zahra tace Anty Jidda ko ki fadamin xakixo ?? Murmushi jiddan tayi wllh nayi hakane dan nabawa ya khaleel mmk dariya sukayi plx karku fada mishi akwai abinda na shirya mishi Momy tace wayasan tsakaninku babu me fada mishi kunfi kusa wannan miskilin ina ga ke kadaice mai iya fahimtarshi hnklin Jennifer tashi yayi wannan itace jiddan ya khaleel din ranta ya baci cikin mutuwar jiki ta mike xata fice karaf Jidda tace Momy kunyi bakuwa ne bansanta ba oh new house maid ce zahra ta bata amsa ayya taji ciwone naga kanta da bandage ? Eh faduwa tayine sai alokacin zahra ta kalleta dan bata saniba itama amma sbd miskilanci ta kauda kai sannu kinji Jidda tafada cikin tausayawa Allah ya kiyaye gaba amin Jennifer ta amsa ta fice daga falon kwalla ta taru a idonta ta goge ta koma daki ta kwanta bacci ya kwasheta

5:00 ta tashi da sauri ta shiga toilet tai wanka ta fito kitchen ta tadda suwaiba na aiki tana shiga kitchen din telephone tai kara suwaiba ta daga….a a ba itaba ce amma gatanan ta miko wa Jennifer kan wayar ta amsa ta kara a kunnanta muryarshi tji kamar yadda tasaba jinta ki ka womin tee ta ajjiye wayar sannan ta dora masa ta sauke taxuba aflask tai hnyr dakinsa sallama tayi ta shiga gabanta yai mummunan faduwa sbd abinda idonta ya gane mata ya khaleel ne daga shi sai 3 quarter jikinshi ba riga hannunshi rike da iphat Jidda sanye cikin riga me yankakken hannu kalan blue light da wando pencil gashinta a daure kanta akafadar ya khaleel yana kyalkyalar dariya suna danna iphat din gaba daya gefen jikinta ajikinshi yake Jennifer ta runtse ido ta ajjiye flask din lokacin da xata juya suka hada ido dashi yna mata wani irin kallo tmkr mai tausayawa majinyaci ta fito daga dakin hawaye ya sauko mata haisam ta gani agabanta yana mata kallon da dan sanda kewa barawo inya kamashi yana sata 19/20

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]