[Advertisements⬇️]

JENNIFA CHAPTER 10 - Bankinhausanovels
Fri. Mar 31st, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

JENNIFA CHAPTER 10

 

 

 

Da sauri yabiyo bayanta cikin rashin Sani ya ture wata tsohuwa ta fadi dolenshi ya dakata ya dago tsuhuwar yana bata hkr sbd yanda ta balbaleshi da fada haka ya samu da kyar ya lallashi tsohuwar yai hanyar da Jennifer tabi da gudu dugu cen nesa ya hango wani matashin balarabe sanye cikin uniform ya bude mata murfin mota tashiga hannunta rike da waya tanayi kafin ya karasa motar ta ja da gudu ta bace masa ya sauke numfashi yana.  kallon inda motar tabi hnklinshi atashe ranshi yakai kololuwar baci jikinsa asanyaye ya koma masaukinsu yarasa kalar tunanin daxaiyi dan al,amarin yfara bashi tsoro wacece Jennifer babu yadda xa ai ya yadda ba itabace dan tanayin mgn muryarta ta tabbatar masa da itace yasalam ! Meyasa take aiki a gidansu ?? Shi dai yasan Jennifer Kristen ce meya kawota saudiyya masallaci wajan ibada ?? Me ya kaita Dubai aikata mummunan aiki na fashi da makami ?? Anya kuwa xai iya bari yai mata kamun kaxar kuku ???? Ina baxan iya ba !! Yafada cikin huci da daga murya duk ranar da yakoma 9ja tofa sai tafada masa mummunan kudirinta akansu gabanshi ya fadi kodai Yar bincikece ??? To akan me xa a bincikesu alhali dadynsu ba mugun mutun bane mai aikata laifi ?? Wata ke bincika ??? Taya xa ai Yar bincike ta aikata fashi da makami ??? Ohhhh!!! Ya dunkule hannunsa ya naushi tafin hannunsa dashi baxaiyi yuba ! Jennifer wacece ke ?? Meyasa kika shiga rayuwar gidanmu ??? Shifa dama duk da ba kare mata kallo yayiba yasan Sam yarinyar batai kala da yare ba kokadan gaba daya xubinta na Hausa fulanine gumi ya rufeshi duk da sanyin a.c dake sanyaya dakin hk ya dinka sambatu hade Da gudire mummunan abinda xaiwa jennifer sai ta fada mishi wacece ita ?? Me yakota gidansu??

Satinsu biyu cif a saudiyyan suka dawo gida shikam haisam gaba daya hnklinshi nakan yadda xa’ai Jennifer ta cigaba da xama agidan su ranar da suka sauka ma’aikatan gidan mata basu da dawo ba mazan kawai suka tadda

Washe gari da safe ya fito daga daki sanye yake da 3 quarter da riga body Huck fara Sol ya hango inuwar mutun a kitchen da hanxari yayi wajan bayanta ya hango tana aiki sosai duhun mutun ta gani da sauri ta waiwaya atsorace taja baya yanayin da ta ganshi ya tsorata ta ya xuba mata ido yana mata wani irin kallo durkusawa tayi sannu da xuwa Yaya haisam cikin ladabi andawo lafiya ?? Allah ya karbi ibada shiru yai yana naxarinta yarinyar nan kuwa ba shedaniya bace ?? Yanayin yadda tai masa mgn ya matukar basa mmk kamar ba itace ta tsare shi da xagi a masallaci ba kee ! Ya fada akausashe wacece ke ?? Araxane ta kalleshi hade da mikewa tana kallonshi alamar bata fahimci tmbyr tashi ba tmbyr ki nake yi ! girgixa kai tayi ban fahimci tmbyr ta ka bane ta fada kanta akasa OK ! Ok ! Xaki fahimta yana fada ne tmkr zai kai mata duka munafuka ! Azzaluma barauniya ! Nafiki hatsabibanci kafura ! Koda yake shedancinki ya wuce duk me karancin tunani zan miki kyakykyawan rukon da xaki kasa kufcewa sai kinyi Dana sanin yaudarar mutane OK ! Nafahimce ki kinyi hkn dan ki xautani kisani cikin tunani ?? Atunaninki karamar kwakwalwa gareni irin taki ?? Kijira nawa hukuncin dan ubanki bakin kafuri ! Da sauri ta kalleshi ya wuce fuuuuu yana huci ko kadan batayi mmk ba asalima tana jiran fiye da hk xan gani haisam idan kai me babbar kwakwalwane kamar yadda ka fada ina gidanku babu abinda xai fiddani har sai burina ya cika koda kuwa xaka dinka yankan naman jikina

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Da wuri tagama aikinta ta koma daki tana shiga tai wanka ta canza kaya kwankwasa kofa akayi kafin tai mgn ya shigo fuskarshi dauke da murmushi yana kallanta oyoyo oyoyo oyoyo ya mahboob ya janyo stool ya xauna oyoyo sister nayi kewarki sosai nima HK ya mahboob ta fada tana satar kallonshi jiya naita xuba ido na nemiki na rasa ta rangwabar da kanta banyi xaton da wuri xaku dawo ba andawo lfy ? Lfy ya fada yana tabe baki sai rashinki kawai danayi tayi murmushi rashina kamar vana duniyar ? No nikaina nayi mmk sosai …..sarkin tsari xaka fara tafada aranta……yacigaba bansan nashaku dake haka over ba sai danayi 3 days ban ganki ba na damu sosai har abin yafara bani tsoro kullum cikin tunanin kyakykyawar fuskarki sai na kalli photonki nake jin dadi Jennifer ya kirata ta kalleshi cike da gundira da zancenshi dan ita sam batason namiji me tsara zance yawancin su makaryata ne …kin shiga raina sosai ban San yadda akai kawancen mu yai tsamari haka ba ya kura mata ido kina da babban fili acikin xuciyata na yadda dacewa kina daya daga cikin farin cikina ke kam kawace wacce zanyi alfahari da ita murmushi tayi shima murmushin yayi kina da Kyau Jennifer kyawunki shine kyawun dake fuxgar duk wani mahluki kyawunki shine asalin Kyau fatana yadda nayi missing aminiyata itama hk tayi kai ta daga masa tana tunanin inama da ya khaleel take wannan hirar look ! Yace cikin daure fuska banson wayo mgn xaki ba daga kai ba kibani lbrn missing dina da kikayi na isa nai maka wayo Yaya mahboob nayi missing dinka sosai ya mahboob dalilin dayasa ma naxo gidanku yau da asuba dan naga yayana ta rufe fuska da hannunta ya tabe bk ngd ya fada hade da mikewa anjima zan dawo OK Allah ya dawo da kai lfy sukayiwa juna murmushi ya fice ta murguda baki jagwab ta xauna kan stool din daya tashi mganganun ya mahboob suna sata gajiya

12:00 tashiga kitchen kamar yadda tasaba dora girkin rana karar telephone din kitchen taji tasa hannu ta daga muryarshi mai sanyi taji kamar baya sonyin mgn ki kawomin coffee ya ajjiye wayar tasaki ajiyar xuciya hade dayin murmushi da sauri ta gama tai bangaren su dan ta matsu ta ganshi sbd dadewar da sukayi basuga juna ba tana xuwa bakin kofarshi taji murya kasa kasa gabanta ya fadi tabbas wya yakeyi da wannan mayyar ! Sam batasan lokacin data kira ta da suna mayyaba ido ta runtse yaukam baxata saurari wayarsu ba da sauri tai sallama idonsu ya sauka kan juna gabanta ya fadi yana xaune akujera 3 quarter ne ajikin shi kalan fari ba riga kukam Allah ya shiryeku da bakwajin kunyar xama babu ishashshun kaya ajjiywa tayi da sauri sbd mgnr da taji yayi ….babyna I love u too…da sauri tajuya xata fita kinga “! Yace da ita tsam ta tsaya ki wankemin toilet ranta yai mummunan baci ta juya jikinta asanyaye tai hnyr toilet din ……ah no babyna ina mgn da maid house din mune kiyi hkr xnxo fa oh ya rabbi ! Allah ya kawomin ke lfy xanyi farin ciki da hakan ki daina mgn karan kanki dan nima nadamu darashin ki kusa dani ……..itakam Jennifer bakin cikine ya taru yai mata yawa hk ta wawwatsa ruwa a toilet din ta fito bai kalleta ba ta wuce yabi bayanta da kallo yana dariya kasa kasa hade da cije lebenshi na kasa tana fita tajanyo kofar da karfi ta wuce fuuuu tashiga kitchen suwaiba ta tadda xare ido sukayi dukansu sannan suka rungume juna suna fairin cikin haduwa

Yau takama alhamis dai dai dasatin su ya haisam 2 da dawowa gidan yau ba kowa sai su ma’aikata da suke abangaren su tana kitchen tna aiki suwaiba sun tafi kasuwa da Momy shara ta kwashe tai hanyar da ake xubar da ita taci karo da shi yana mata wani irin kallo ya haisam wacece ke ? Ta kalleshi takasa ce masa komai cikin tsawa ya kuma tmbyrta wacece ke ? Kafin ta ankara ya dankota ya shaketa shaka ba ta wasa ba

 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]