[Advertisements⬇️]

SANADIN SON KI CHAPTER 10 - Bankinhausanovels
Mon. Mar 27th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

SANADIN SON KI CHAPTER 10

 

Cikin nutsuwa Suhaima ta fito daga d’akin ta cikin shirin uniform na tahfiz da yake ranar asabar ce, cikin kitchen ta k’arasa inda Aunty Aliyah take had’a abin karin kumallo ganin sinasir take yi ne ya sanya Suhaima sakin murmishi da yake tana son sinasir sosai, cikin jin dad’i tace

“Wow Aunty sinasir kike mana yau amman naji dad’i sosai bari nayi sauri na tafi kada nayi latti ”
Murmishi itama Aunty Aliyah tayi tare da cewa
“Ai shikenan sai kin dawo, zaki sha ‘yar tafiya kuwa yau don Yayan ki ya fita tun asuba zuwa kai kaji da kwayaye kasuwar birni ”

D’an murmishin ta mai kyau Suhaima tayi tare da cewa
“Yeeeeee ai ni yau naji dad’in haka zan tafi a k’afa saboda kullum shi Yaya shi yake kaini kuma yaje ya d’auko ni ko’ina mutum zai je sai dai a kai shi ni fah yanzu na girma ” ta k’arasa fad’i tana rawa har da juyi duk dad’i ya ishe ta.

Rik’e baki Aunty Aliyah tayi tana cewa
“Tabbb kenan dad’i kike ji ai kyasha tafiya kuwa yau ”

“Eh naji Allah ya dawo da Yaya lafiya ni na tafi kada ki ja min latti ”

Suhaima ta k’arasa fad’a tana dariya ta fice daga gidan da sauri, tabar Aunty Aliyah itama tana dariya kafin ta mayar da hankalin ta kan abin da take yi.

 

Cikin d’an sauri Suhaima take tafiya saboda ganin ta kusa latti aikuwa tana shiga cikin makarantar aka rufe kofa lokacin kaman ‘yan latti yayi, wata ajiyar zuciya Suhaima ta saki ganin Allah ya taimake ta bata sha dukan latti ba da sauri ta wuce cikin ajin su, da yake k’auyen nasu babu laifi akwai masana ilimin addini dana zamani dai dai gwargwado, musamman ma ilimin addini sun fi bashi muhimmanci fiye dana boko, shi yasa suke da makarantar islamiyya da tahfiz.

 

K’arfe 11 na safe aka tashi su Suhaima nan tayi sallama da k’awayen ta ta wuce zuwa gida, don ba ‘yan kusa da su a makarantar, saboda sune kusan gidan su na k’arshe k’arshen k’auyen, a nutse take tafiyar ta kanta a sunkuye yake tana tilawar karatun alqur’an a hankali koda kana kusa da ita ba lallai kaji abin da take fad’a ba sai dai kaga le6en ta na motsawa a hankali alamar dai akwai abin da take karantawa.

Tayi nisa da tafiyar ta don tayi wajen rabin tafiyar da zata kaita gida, horn taji ana yi mata amman sam batasan da ita ake ba tafiyar ta take kawai abin ta hankalin ta kwance.

Bata ankara ba taji mota ta goge ta kad’an a jikin ta har sai da madubin motar na waje ya bige ta a gefen hannun ta, wani irin zafi Suhaima taji a hannun ta da sauri ta d’ago kanta tana kallon motar da ta bige ta zata wuce saboda hanyar bata da kyau sosai akwai ‘yan kwazazzabai shi yasa bata sauri, ganin mai motar bashi da alamin tsayawa ya bata hak’uri ko yayi mata sannu ne yasa Suhaima cikin fusata tace

“Kan ubancan! lallai mutumin nan baka da mutunci a bige ka ko sannu babu ka wani wuci kamar ka bige dabba ba mutum ba ”

Ta fad’a da k’arfin ta ranta a 6ace, ganin ba alamar tsayawa yasa ta d’auki wani dutsen wuta a k’asa ta saita glass d’in motar ta jefa da iya k’arfin ta sai dai bai samu glass d’in ba sai fitilar motar ta baya ta samu, aikuwa babu 6ata lokaci ya ba da sautin k’arar fashewa, babu shiri mai driving d’in motar yaja motar ya tsaya.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Suhaima kuwa dad’i ne ya kamata da taga hakan taso ma glass d’in ta samu ta fasa tun da bashi da mutunci har da sakin wani murmishin mugunta.

Cigaba tayi da tafiyar ta abin ta har ta k’araso inda motar tayi parking amman babu wanda ya fito daga motar gashi glass d’in motar mai duhu ne ba’a ganin na ciki, sai dai na cikin ya gan ka, ita Suhaima ko alamar tsoro babu a tattare da ita ta wuce motar, baifi taku hud’u tayi ba tsakanin ta da motar taji alamar an bud’e kofar motar amman bata jiyo ba saboda bata da ra’ayin ganin wanda ke cikin motar.

Cikin fusata na cikin motar ya nufi inda Suhaima take tafiyar ta cikin zafin nama ya sanya hannun shi ya janyo hijab d’in ta na baya, tare da jiyo da Suhaima saitin inda yake ya d’aga hannu zai mare ta cak ya tsayar da hannun shi ya kasa karasar dashi kan fuskar Suhaima kamar yanda yayi niyya, sakamakon had’a ido da yayi da ita duk wani 6acin rai da ya kwaso shi yaji ya tafi a lokaci d’aya.

Kallon kyakkyawar face nata yake da eye’s nata masu matuk’ar d’aukan hankali, runtse idon ta Suhaima tayi cikin tsoro jikin ta har ya fara 6ari na tsoro don ta zaci mari zata sha, eyelashes d’in ta yabi da kallo yanda suka bi idon suka kwanta kan beautiful face nata.

Jin bataji saukar mari ba ya sanya ta bud’e idanun ta a hankali ta sauke su kan fuskar kyakkyawan saurayin da yake gaban ta, ganin yanda ya zuba mata ido yana kallon ta ya sanya ta fincike hijab d’in ta da ya rik’e mata tare da gyara taayuwar ta aka wani rik’e kugu cike da tsiwa tace

“Malam lafiya da zaka wani rik’e min hijab? ”

Sai da ya guy din ya lumshe idanun shi don jin saukar dadad’ar voice d’in Suhaima kafin ya sake bud’e idon nashi yana cigaba da kallon ta tamkar wadda ya samu wata tv yana kallo ko motsin kirki baya yi, sosai abin ya bawa Suhaima mamaki cikin zuciyar ta take cewa shi wannan baya jin tana magana ne ko kurma ne shi? da alamar ma daga birni yake.

Cikin tsiwa ta sake cewa “wai malam baka ji ina maka magana ko kai kurma ne? ”

Ganin again ya kuma share ta sai kallon ta kawai da yake yi ne har da wani hard’e hannaye saman kirjin shi yasa Suhaima juya bayan ta cikin sa’a ta hango wani yaro na kusa da su hannun shi rik’e da robar ruwa a kanshi ya d’auko zai tafi gida.

Dad’i ne ya ishi Suhaima har da d’an murmusawa na mugunta don tasan abin da zata yiwa wannan mayen d’an birnin, yaron yana k’arasowa inda suke zai wuce da sauri Suhaima ta sanya hannunta saman kanshi ta d’auke robar ruwan.

Kafin yaron ya juyo tuni ta watsawa wannan guy d’in ruwan a jikin shi dukka tare da jefar da robar gefe d’aya, lokaci d’aya drivern da yake tsaye jikin motar da wannan yaron da Suhaima ta d’auki ruwan shi suka d’ora hannu a kansu cikin tashin hankalin da abin da Suhaima ta aikata, wata k’atuwar ajiyar zuciya ya sauke lokaci d’aya jin wannan ruwan mai shegen sanyi a jikin shi tsikar jikin shine ya tashi kafin ya sanya hannun shi a fuskar shi yana goge ruwan da yake di’gowa daga saman gashin kanshi yana kok’arin bud’e idon shi.

Ganin haka ya sanya Suhaima kwasa da gudu ita da yaron har ma yafi Suhaima gudu tamkar shi yayi laifin daman tuni ya mance da wata robar shi don anashi tunanin aka tashi kama da Suhaima har dashi za’a had’a, sai abin ma ya bawa guy d’in dariya sosai ganin yanda suke gudu kallon su yake fuskar shi d’auke da murmishi har sai da ya daina ganin su….

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]