[Advertisements⬇️]

TANA RAINA CHAPTER 12 - Bankinhausanovels
Mon. Mar 27th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

TANA RAINA CHAPTER 12

 

Kamal ne dasu sabreen akan daining suna breakfast, babu wanda yake cewa komai gabad’aya jikinsu a mace yake tunba kamal ba. Bayan sun gamane sabreen ta koma d’akinta tana kwance akan gadonta suna waya da munira tana dariya, bayan sun gamane ta kira aunty rukayyama sukasha hira sosai dayake kamal yasa mata credit aciki.
Wani number ta gani yana kiranta, ta d’auka tare da cewa hello, muryan yah kamal taji yace sabreen kamal ne na kirakine in sanar dake wannan number nane kiyi saving kinji, ok toh nagode ya kamal ka fita ne? A’a yanzu dai zan fita akwai wani abune, emmm dama inaso inje shago ne akwai abinda nakeso in saya, toh menene gayamin se in sayo miki koh, shuru tayi batace komaiba, yace “sabreen” tace emmm nafiso inje da kainane yah kamal😉, murmushi yayi yace toh shikenan fito muje kisaya, toh nagode sannan ta katse wayan ta dauki himar d’inta tasa tayiwa kaka sallama sannan ta sami ya kamal agun motansa, gaba ta bud’e ta shiga sannan yaja suka isa wani d’an babban shago, sabreen tayi saurin cewa yah kamal ka zauna kawai ni zanje yanzu zan fito, toh yace mata sannan ta fita ta wuce shagon, bayan shigantane kamal ya fito yana biye da ita a baya batare data saniba ya shiga. Part kawai sabreen ta dauka guda 2 sannan tazo gun biyan kud’in, mai karaban kud’in yace ki barshi kawai, tace yah za’ayi kace in barshi ungo karb’i kud’inka, mai shagon yace wani ya riga daya biya miki, tace wani kuma waye shi? Mai shagon ya nuna mata motan kamal, kunya sosai taji tace yanzu yasan abinda na saya kenan😁, k’in fita tayi tana tsaye a cikin shagon segashi ya shigo fiskansa a d’an d’aure yace baki gama bane sabreen, shuru tayi ta wuceshi ta nufin gun motan kunya kamar ta shiga k’atsa.
Tunda suka fara tfy batace komaiba kanta na gefe, kamal yace sabreen ya kikayi shuru, tace bakomai, murmushi yayi yace aida kin gayamin in sayo miki me aciki muna sayowa hafsat ai nida suhail, kunya taji sosai tasa himar d’inta ta rufe fiskanta tana dariya batare dayajiba, shima dariyan yayi yace kidena kunyata sabreen domin ni bana kunyanki kinji koh? Batace dashi komai shima bai sake cewa komaiba har suka iso gida, bayan ya tsayane ta bud’e kofan tare da cewa nagode batare data kalleshiba, dariya yayimata wanda ya kara masa kyau yace bakomai na tafi gun mum se dare zan dawo, toh zallah ya tsare, ya ameeen sannan ta rufe motan ya tafi. 9:00pm kamal ya dawo gida, bayan yayi wanka yaci abincine seya kira sabreen a waya yace inason magana dake ina palo, doguwar rigan atamfane a jikinta da d’ankwalinsa da tayi lullub’i dashi yana hango gashin kanta harta k’araso gunsa sannan ta zauna akan kujera tace gani yah kamal, kamal ya gyara zama yace sabreen kin tab’a yin soyayya? Wani iri taji dan bata tsanmaci wannan tambayar daga garesaba, daurewa tayi tace a’a yah kamal, ya sake cewa amma dai nasan kina da masoya ko, tace eh akwai amma gaskya ban tab’a kula ko wani d’a na mijiba, kamal yace shin ko akwai wanda kikeso aranki? Ananne sabreen tayi shuru dan bata san me zata ce mishiba, sake maimaita tambayan yayi tareda cewa ina sauraronki sabreen, kanta a sunkuye tace a’a babu. Kamal ya sauke ajiyan zuciya yace ko zan iya sanin dalilin k’inyi soyayyar? Sabree tace babu wani dalili yah kamal, yace toh shikenan tashi kije😊, kallonsa takeyi har cikin ido shima haka sannan ta wuce d’aki. Murmushn jin dad’i kamal yayi tare da tashi ya shige d’akinsa da farinciki sosai aransa. Ita kuwa sabreen mamakin tambayoyin da yah kamal yayita mata takeyi har bacci ya d’auketa25/26

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]