[Advertisements⬇️]
[Continue Reading⬇️]
SANADIN SONKI CHAPTER 8
Tana k’arasowa inda suke Alhj Ahmad d’an fillo ya sanya hannun shi ya wanka mata mari a kumatu, kafin ta dawo hayyacin ta Hajjah Hauwaa ita ma ta wanka mata marin a d’ayan kumatun, ihun kuka kawai ‘yar aikin take yi saboda ba k’aramin shigar ta marukan suka yi ba, kallon ta suke sai huci sukeyi cikin harara Hajjah Hauwaa tace
“me kike kallo da zakiyi wa Sabeer haka, baki da hankali ne, ina so kafin cikar mintuna 5 Ki barmin gida ”
Duk da tsananin zafin marin da ‘yar aikin tasha hakan bai hanata durk’usawa a k’asa ba cikin kuka take cewa
“don Allah kuyi hak’uri tsautsayi ne amman kada ku kore ni bazan sake kwatanta hakan ba ”
Cikin 6acin rai Dr Ahmad d’an fillo yace
“baki ji abin da aka ce miki ba sai na kira police sunyi gaba da ke, wlh kika bari na kirawo police gidan nan sai kin yabawa aya zak’in ta ”
A kid’ime ‘yar aikin ta mik’e jikin ta na rawa ta fara kok’arin barin parlourn, Sabeer wanda yake jikin Dr Ahmad d’an fillo ya lafe yana sauke ajiyar numfashin ihun da ya gama ya bud’e baki dakyar yace
“keee ki zauna kada ki tafi but ki kiyaye gaba, kika sake min haka bazan Kyale ki ba ”
Cikin mamaki Dr Ahmad d’an fillo da Hajjah Hauwaa suke kallon shi sun ma kasa furta komai, da sauri ‘yar aikin ta tsugunna tana murmishin farinciki cikin rawar murya tace
“Ngde yalla6ai Allah ya kare ka yanda ka taimake ni kai ma Allah ya taimake ka a duk inda kake, kuma zan kiyaye gaba insha Allah ngde ngde sosai ”
D’aga mata hannun shi yayi d’aya tare da cewa
“is okay zaki iya tafiya ”
Jiki na 6ari ta bar wajen Sabeer ya bita da kallon tausayi don tabbas tausayin ta ne ya sanya shi barin ta don ta cigaba da aiki.
Kallon Hajjah Hauwaa yayi wadda take mishi kallon mamaki ya yamutsa fuska yana cewa
“a had’a min ruwa a toilet zan yi wanka ”
Sai lokacin bakin ta ya bud’e ta iya cewa
“yanzu shikenan Sabeer an barta baza’a d’auki mataki a kanta ba ”
“ni tayiwa laifi koh, kuma nace ta zauna kada ta tafi ko’ina don haka ku Kyale ta idan kuma naji anyi mata wani abun raina zai iya 6aci kum……”
Kafin ya k’arasa fad’i abin da zai fad’a Dr Ahmad d’an fillo yace
“kayi hak’uri kada ranka ya 6aci Sabeer baza’a yi mata komai ba komai ya wuce ” ya k’arasa fad’i yana shafa kanshi tamkar wani k’aramin yaro.
Kan shi ya gid’a idon shi na kan ciwon da ya d’an ji akan k’afar shi, Dr Ahmad d’an fillo ya kalli Hajjah Hauwaa yace
“ba’a haka yace a had’a mishi ruwa zai yi wanka ba? ”
Dafa kafad’ar Sabeer tayi tare da cewa
“zo muje da kaina zan had’a maka ”
Kamo hannun shi tayi ta jashi zuwa upstairs inda bedroom d’in shi yake (da yake yana da bedroom a side d’in kakannin nashi), da kallo Dr Ahmad d’an fillo ya bi Sabeer har ya daina hango shi tukunna ya juya ya fita.
Bayan Sabeer yayi wanka ya fito ya shirya cikin Kayan da Hajjah Hauwaa ta ajiye mishi saman bed, ya sanya su sannan ya kwanta kan sofa hannun shi d’auke da I pad d’in shi yana research a ciki.
“Assshhh ”
Ya furta a hankali sakamakon maganin da Hajjah Hauwaa ta sanya mishi a d’an ciwon da glass cup ya ji mishi, bakin ta ta sanya tana hura mishi k’afar tare da cewa
“sannu ”
Ta furta hakan tana rufe robar cream d’in da ta shafa mishi, d’an 6ata fuska yayi yana cewa
“shine baki fad’a min zaki sa min ba koh? ”
Da shagwa6a ya fad’i hakan, nan ta fara rarrashin shi sai da ta ga ya hak’ura tukunna ta fita daga bedroom d’in don ta barshi ya huta.
[Advertisements⬇️]
[Continue Reading⬇️]
8pm
Sabeer ne tsaye gaban dressing mirror yana sake gyara necktie d’in suit d’in shi, yayi kyau sosai cikin blue d’in suit ba kad’an ba shoes d’in shi black ne haka watch d’in hannun shi samfur d’in Gucci yayi kyau gashin kanshi yasha gyara sai shek’i yake.
Turo kofar bedroom d’in akayi Mummy ce ta shigo tasha gayun ta cikin wani tsadaddan black less mai adon flowers ash Sai ta nad’a laffaya ash colour mai kyallen duwatsun silver sai manya flowers black a jikin laffayar tayi kyau sosai baka d’auka ta haifi Sabeer ba gefen ta kuma wata matashiyar kyakkyawar yarinya ce tana sanye cikin wata gown na English wears sun kamata sosai daganin ta kasan idon ta a bud’e yake tasha wani uban hill shoes ga attachment da tasha sai farce daga ni sanya su tayi, fuskar nan tasha heavy make up sai wani iyayi take, kallo d’aya zaka yi mata kasan kusan sa’anni ce da Sabeer a shekaru.
Kallo d’aya Sabeer yayi mata ya d’auke kai don bai ga alamun tana da hankali ba irin wannan haukan kwalliyar da tayi, matsalar shi da Mummy kenan jajibo irin wad’annan yaran marasa kamun kai.
Cikin murmishi d’auke a fuskar Mummy ta k’arasa inda Sabeer yake tayi hugging d’in shi tare da cewa
“Wow son ka ganka kuwa U look so cute ”
“Thanks Mumy”
Ya furta tamkar baya son magana, cikin murmishi Mumy tace
“Son ga Fadilah ko baka gane ta ba ne? ”
D’auke kanshi yayi tare da cewa
“bansan ta ba”
Yana gama fad’in yayi gaba, kunya ce ta d’an kama Mumy don bata zaci Son zai mata haka ba ya kunyatar da ita a gaban d’iyar k’awar ta, wayance wa tayi da cewa
“Kyale shi Fadilah ranshi ne a 6ace don baya son wannan party da na had’a mishi ”
Sai lokacin matashiyar yarinyar da Mumy ta kirawo da Fadilah ta saki murmishi don ta shiga damuwa a time d’in da Sabeer ya nuna baisanta ba.
Kamo hannun ta Mumy tayi suka fito zuwa compound d’in gidan friends d’in Mumy da yaran su zuwa ‘yan uwan Sabeer ne sai shiga mota ake suna tafiya zuwa hall d’in da za’a yi party.
Wata black Range Rover na hango a tsakiyar compound na gidan sai shek’i da d’aukar ido take daganin ta kasan sabuwa ce, nan na hango Sabeer ya nufi wajen cikin takun tafiyar shi kamar bayason taka k’asa, kafin ya k’arasa wajen tuni driver ya bud’e mishi bayan motar yana k’araso wa shiga yayi ya zauna sannan driver ya rufe murfin motar, cikin sauri ya shiga mazaunin driver ya yiwa motar key ya fara tafiya a hankali don Sabeer bai fiye son ayi gudu dashi a mota ba idan bashi yake driving ba.
Suna k’arasa wa katafaren hall d’in da aka kama don yin partyn ko’ina yasha decorations na blue white, wajen yayi kyau sosai ta had’u ga wani cake mai hawa uku shima kalar shi blue and white ne yayi kyau sosai ya tsaru.
Ga manyan hamshak’an masu kud’i friends na Mumy da yaran su, ga ‘yan uwan Sabeer nan mazan su da matan su kowa yasha gayun shi na kece raini don kowa yana ji da kanshi ta fannin kud’i da gogewar ilimi da wayewa.
Driver yana yin parking motar da Mumy take ciki tayi parking kusa da motar da Sabeer yake ciki, nan Mumy ta fito ita da wannan Fadilah suka k’araso inda Sabeer yake, Mumy ta bud’e kofar motar tare da cewa
“Son fito mu tafi mutane na jiran mu ”
Cikin wani tak’ama da had’e fuska ya ziro k’afar shi d’aya waje sai da ya d’auki wasu seconds tukunna ya fito da d’ayar kafin kuma ya fito da dukka jikin shi zuwa waje.
Kallon shi Fadilah take tamkar ta lashe shi saboda tsabar maitar son shi da take, ita fah da zai aminta da ko bazai aure ta ya yarda suna biyawa kansu buk’ata don tasan Sabeer irin shine wanda zai yi mata yanda take so, amman zata fara gwada sa’ar ta ko zatayi nasara…
[Advertisements⬇️]
[Continue Reading⬇️]