[Advertisements⬇️]

TANA RAINA CHAPTER 2 - Bankinhausanovels
Thu. Oct 6th, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

TANA RAINA CHAPTER 2

 

 

 

Take ta kimtsa jikinta sannan ta mik’e tare da taimakon d’aya daga cikinsu, d’ingishi takeyi tare dayin kuka kamar da gaske, ruwa zansa tace dasu d’ayan ya ciro goran FARO ya mik’a mata ta karb’a ta shanye tas, yace a kara mikine a’a tace har suka fito kan titi.
Wata mota suka hango a tsaye a gefen titi, saurayine a tsaye ya juya bayansa yana ta kallon hagu da dama, d’aya daga cikin ‘yan iskan yace shikenan ku biyoni a baya, gun wannan saurayin suka karasa yasa masa bimdiga a k’eyarsa tare da juyo dashi suna fiskantar juna🙄, saurayin yace lfy bayin Allah mena muku da zaku samin bindiga akai? D’ayan yace me kakeyi anan, saurayin yace motatace ta tsaya sakamakon zafin da tayi ruwa nake nema kozan samu, d’ayan ya saki hannun kakkawar yarinyan take ta sake jiki ta zube a kasa, se alokacin saurayin ya lura da yarinyan, jikinta duk jini gashi a galabaice take tana d’an zubar da kwalla duk seyaji tausayinta ya kamashi barema yanayin daya ganta kuma tare da wad’anan mutanen da babu alamar tausayi a tattare dasu, yace wannan fa meya sameta haka, d’ayan ya bud’e motar danya hango wata kyakkyawar mata da kuma wata ‘yan mata a cikin motan suna zaune, bindiga ya daura musu akai yace dukku fito waje, ba musu suka fito jikinsu se rawa yakeyi, saurayin ya juyo yace me kuke sone, kome kuke so zan baku amma “please karku cutar min da mahaifiyata nd my sister” sannan ita kuma 👉🏻wancan meya sameta haka naga jikinta duk jini? 😆😆😆dariya sukayi dukkansu sukace baka gama tsiratar da family’n kaba har kana iya tuna wata, tunda kana son sani shikenan idan har kana son rayuwar mafily’nka to lallai sekayiwa wa wancan yarinyar fyad’e ko kuma muyiwa mahaifiyarka fyad’e a idanunka harma da k’anwar naka.
😳ido ya zaro yace haba bayin Allah meyasa zakuyi haka, anya kuwa ku musulmaine wani irin magana haka kukeyi, gaskya bazan aikata hakanba, ina rok’onku da kuyi hakuri bazan iyaba. D’ayan ya janye zanin dake jikin mahaifiyarsa tare da janyota kusa dashi, innalillahi wa inna ilaihirraji’un ta fara furtawa tare da cewa haba dan Allah kuyi hakuri nasan dai a haife na haifeku meyasa zakuyi haka, shin zakuso wani yayiwa mahaifiyarku haka, saurayin ya matso da sauri ya d’auki zanin mahaifiyarsa daya fad’i a k’asa Allah yasoma akwai dogon under wear a jikinta har k’asa, ya d’aura mata ya durk’usa har k’asa yana rokonsu, pls ku nemi wani abun daban amma banda wanna, d’ayan yace to shikenan, kokayiwa wancan fyade, ko kuma in fasa kan mahaifiyarka da bindigannan kuma karka dauka ko wasa nakeyi am serious se suka harba bindigansu sama dukkansu tauuuuu kakejin karan, dukkansu sun razana sosai dajin sautin bindingan tunba kyakkyawar yarinyannanba take jikinta ya fara rawa, ita kuwa k’anwan saurayin da gudu ta k’araso gunsa ta rik’o hannayensa tana kuka tana cewa YAH SUHAIL dan Allah karka bari su cutar damu kayi abinda sukeso pls, nan SUHAIL ya juya ya kalli mahaifiyarsa da take kwance a k’asa an d’aura mata bindiga akai sannan ya juya ya kalli yarinyar wanda idanunta kawai yake iya gani sakamakon nik’af dinda yake fiskarta, muryarta ya jiyo tana cewa karka bari a cutar da mahaifiyarka saboda ni dan bakada qacce ta fita na yadda kamin fyad’en😢 a tunaninta k’ila wannan MACEN zata sake zuwa don taimaka mata.
Suhail yace kiyi hakuri mum duk tarbiyan da kuka bani yau gashi zan rushar dashi domin cetonki😰 ina fata zaki yafemin, mahaifiyarsa tace Suhail karka aikata hakan pls yadda bazakaso ayiwa k’anwarka hakaba itama wancan yarinyar ka kalleta amatsayin hafsat k’anwarka nina gama zamanina dama danna mutu ba wani abu bane ka cecesu pls my son, No mum bazan iya rasakiba dan haka zan mata abunda sukeso😰 ahankali ya fara tafiya har inda yarinyar take kwance, se a lokacin suka cire bindigan akan Mum d’insa da kuma hafsat k’anwarsa, yace musu agaskya da kunya inyi mata hakan akan idon mahaifiyata da kuma k’anwata, d’ayan ya juya bayansa cikin ciyawi se yaga wani bukka yace gacan bukka muje ina biye daku, ba musu yarinyan ta mik’e da kyar tana d’ingisawa suna binsu da kallo mahaifiyar Suhail se kuka takeyi tana cewa Suhail dan Allah karka aikata abinda sukeso pls, yana tfy yana bata amsa kiyi hakuri mum na rasa dad bazanso ace na rasakiba kema ki gafarceni mahaifiyata👏🏻. Turata yayi ta fad’a cikin bukkan seya fito yacewa suhail ka shiga kuma inanan a bakin kofa ina ganinku idan kayi wasa da hankalina to wlh sedai ka tafi da gawa biyu da fatan ka fahimceni, shuru suhail yayi tare da juyawa ya kalli su hafsat sannan ya shiga bukka

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]