SALON SO CHAPTER 6

SALON SO CHAPTER 6

 

 

Bangaren Kausar kuwa kullum cikin yowa Haidar

waya take safe, rana, yamma da dare ma ba ta bar

shi ya huta ba kan maganar aurensu tun yana boye

mata yana cewa ta jira shi har dai ya fito ya gaya

mata gaskiyar batun matarsa. Amma ya ba ta

hakuri da ta jira iyayensu su dan samu nutsuwa sai ya tada maganar su zo.

Amma da ta kai ta kawo yau da Kausar ta tayar da

hankalinta sosai don gani take yi kamar Haidar din

sake subuce mata zai yi a karo na biyu, ganin

yanda ta samu kanta ne ya sa Haidar ya je yake

tuntubar mahaifinsa da zancen. Abbansa ya ce, Yanxu Haidar ba za ka hakura da

auren nan ba, kana kallon maganar nan ce ta tayar

muku da rigima ga shi ba a san inda ‘yar uwartaka

take ba ko?

Haidar ya ce, Abba ka tausaya min mana, yau

shekarar jawahir daya kenan da barin gidan nan. Abba kana kallon kullum ina hanyar gidan nan

don cin abinci ni ba na iya cin abincin waje bare na

rinka zuwa Otal ina ci. Abba ba ka tausaya min na

samu na yi auren nan ko ni ma na samu nutsuwa a

gidan?

Abba ya ce, “Yanxu kana ganin idan ka yi aure surutun mutane ‘yan uwa da abokanan arziki ba za

su dinga ganin ba ka damu da batan matarka ba?

Ka ga abin zai zama abin surutu ko?

Haidar ya ce “Wallahi Abba jawahir tana hannun

inna don ita ta boye ta.

Ya ce, “Ka tabbata? Daga bakin wa ka ji? Wallahi Abba migadin gidan Inna na ritsa na ce ko

ya gayan gaskiya ko na debo masa ‘yan sanda shi

ne yake gaya min tana gidan Inna to idan na je wa

da Inna maganar sai ta koro ni, ni dai ina ganin

gwara na yi auren in ta ga na yi auren za ta dawo

da ita. Abba ya ce, “To shi kenan Allah ya zaba abin da ya

fi alheri, zan je wajen Alhaji ibrahim din duk abin da

muka tattauna sai ka ji. Ya ce, “To Abba na gode.

Ya mike ya tafi.

Abban Haidar ya samu Dadyn jawahir yake gaya

masa yan da suka yi da Haidar din, Alhaji Ibrahim ya ce, ai ni tun da na ga hankalin Inna bai tashi ba

na san cewa jawahir tana hannunta. To na sha

tuntubar Aisha a kan maganar, to idan a ka bar

maganar ai anyi zalinci kuma an shiga hakkin

Haidar, shekara guda mace ta gudu ta bar ka kuma

a hana ka yin aure, ai da zalunci, ni dai kawai ina ganin in Allah ya kai mu jibi mu je gidansu yarinyar

a gama maganar komai Haidar ya samu mata kawai

Lokacin da suka je Abuja gidan kaninsa Alhaji

Aminu suka sauka tukunna sai da suka huta suka

samu nutsuwa sannan suka dinguma har Alhaji

Aminu zuwa gidansu Kausar. Sai bayan tafiyarsu sannan jawahir ta dawo daga

makaranta.

Antinta take bata labarin zuwansu Dadynta,

Jawahir gabanta ya fadi, “Lafiya kuwa Aunty.? “Eh

to, wallahi ban sani ba don sun tafi tare da Ankul

dinki kuma be gaya min inda za su je ba ko dalilin zuwansu ba.

Jawahir ta ce, “To Allah ya sa dai ba ganowa suka

yi ina nan ba. Amin da ‘yata, don ba na so a raba ni

da ke. Suka yi dariya.

Gidan su Kausar an yi wa su Alhaji kyakkyawar

karba inda iyayenta suka nuna karamci da dattako. A lokacin mahaifinta ya ce ya yanke ranar aure sati

biyu masu xuwa kawai nan fa a ka yi ta murna ana

sa musu albarka. To su Alhaji su daga nan suka

hawo jirgi suka juyo gida shi kuma Ankul din ya

koma gida.

Suna zaune da matarsa a falon suna tatraunawa jikin maryam duk ya yi sanyi da jin abin da ya

kawosu, Alhajin Abuja. Jawahir ta shigo falon tare

da yin sallama ta tafi kusa da Ankul dinta ta zauna

dab da kafarsa a kan kafet ta ce, “Ankul barka da

dawowa.

“Yauwa ‘yata sannu “Ankul me ya kawo su Dady? Ko sun san ina nan ne?

Ya girgiza kai, “Dady bai san kina nan ba kawai

abin da ya kawo su ne, shine na yi musu rakiya.

Ankul Dady bai tambayeni ba?

“Ai bai san kina nan ba ne shiyasa.

“Ankul ko dai maganar auren Haidar ce ta tashi suka zo suka gaya maka?”

“In ban da abinki idan auren Haidar ne ai sai su yo

min waya ba sai sun zo ba ko?

“Eh to, haka ne Amkul'” ya ce, “Kwaso littattafanki

mu gani, “Ta mike ta nufi dalinta.

. ***** ****** *****

Lokacin da suka isa gida suka shaidawa Haidar

halin da ake ciki, a satin suka hada hada kayan lefe

da komai da komai mata suka kai, duk wannan

halin da ake ciki hankalin Haidar yana kan jawahir

don haka ya je ya shirgo mata kayan fadar kishiya akwati uku hadaddun kaya na gani na fada, don

tsadaddu ne a ciki ya ai ka wa Inna ya ce a gaya

mata tun da ta rike masa mata matarsa ta hana shi

to ga kayan fadar kishiya ne don ba a gaya musu

da baki ba. Inna ta karbi kayan ta samu waje ta

adans su. Biki ya zo bangarensu Kausar sun sharyawa bikin

don kalolin fatin da za a yi da komai da komai

Kausar ce ta bude bakinta ta yi ta hidimarta ba ta

jiran ango don ta san halinsa auren ba dada shi ya

yi da kasa ba, ta yi hidima da bidirinta. Fati daya

kawai Haidar ya je shi ma, sai da ta dame shi da magiya sannan ya daure ya je.

Amarya ta tare a gidan angonta Haidar. Babban

falon gidansa na amfanin kowa da kowa ne, a

falon akwai kofa da take kallon gabas ita ce in an

bude an shiga sashen jawahir da katon falo da

dakuna uku a ciki, sai toilet, kicin da suke a ciki. To idan an dawo falon akwai wata kofar da take

kallon yamma wato tana kallon kofar bangaren

jawahir to ita ma in ka shiga katon falo ne da kicin

da tolet shi Amarya Kausar ta shiga, to a tsakiyar

babban falon bene ne wanda za ka hau ka je

turakar megidan, shi ma falon falo ne, da ya kushi dakuna biyu na bacci da tolet da kicin, sai wata

kofa da za ka bi a saman dai, shi kuma makeken fili

ne da aka kayatar da shi aka yi masa rumfa don

hutawa, to nan saman shi ne na megida Haidar.

Zama ya yi dadi tsakanin Ango da Amarya sai dai

sabanin halayya da ta zo bamban ta ango da amarya, don ita Kausar ta samo masu yi mata aiki

har mutum uku ta cika masa gida da mutane ke

nan, shi da yake dan hutu ba ya son hayaniya, to

amma duk dawowar da zai yi zai tarar da Kausar

uwar lalaci a mike a doguwar kujera ko kan kafet

masu aikinta suna yi mata tausa, wani karin abin haushi wai ba ta iya girki da kanta sai dai me aiki ta

yi musu wannan dalili shi yake hana shi cin abincin

gidan, an gudu ba a tsira ba kenan, don kullum sai

ya biya ta gidansu ya ci abinci

Karin abin da yake bawa Haidar Haushi da Kausar

wai gadon da suka kwanta sai dai ta kirawo me aiki ta gyara, wai ina abubuwan da jawahir take

sanya musu a gidan da dakunansa suke kamshi

ne, duk yanzu wannan kamshin mai dadi babu. Shi

wai shi yaya zai yi ne ya dawo da jawahir dinsa ne,

ko don lafiyayyen girkin da take yi masa mai dadi

ga ladabi da biyayya, duk yanda ya bata mata rai ba za ta fasa yi masa girki ba ko ta ki gaishe shi, ga

shi ya yi auren wayayyiya wadda ta yi karatu a

waje amma babu biyan bukata.

Don zamansa da tatsitsiyarsa ya fi sau dubu dari,

duk hanyar da ya bi don Inna ta dawo masa da

jawahir ya bi amma magana daya take gaya masa ita ma ba ta san inda take ba.

. Lokacin da jawahir ta ji labarin auren Haidar ta yi

kuka sosai ta tashi hankalinta har sai da Inna ta zo

Abuja don rarrashinta. Don lokacin Ankul dinta

yana legos. Jawahir kuka take kamar rainta zai fita

Inna kuwa sai sai rarrashinta ta ke yi tana bata

hakuri jawahir ta ce, ni ba wani abu ne ya sa ni kuka ba irin yanda ya wulakanta ni ya yi aure kin

ga ya sake nunawa duniya cewar bai damu da ni

ba kenan. ‘Inna ta tausayawa jawahir don ta

fuskance ta kishi ne yake damunta.

Inna ta ce, “Ki yi hakuri idan kina so ma yau sai na

mayar da ke gidanki. “Da sauri jawahir ta dago kai tare da saurin katse Inna, “Haba-“Haba Allah ya

sawake ai sai ya ga na damu da shi ne ya sami

hanyar da zai kuma wulakanta ni.

Inna ta ce, in dai wannan kike ji kwantar da

hankalinki domin kuwa yanzu Haidar ta damu

dake wanda ba kya zato, auren nan da ya yi ya yi shi ne don na yi fushi na dawo masa da ke ne, ta ba

ta labarin yanda hankalin Haidar ya tashi na

rashinta da yanda a kayi auren har kayan fadar

kishiyar da ya kai mata da irin korar karen da take

yi wa Haidar din, ko ba komai in kalaman Inna ya

sanyayawa jawahir zuciyarta har ta ji tana sha awar ta koma gidan Haidar ko dan ta ga wanne irin zama

suke yi da Amaryar ta sa.

Jawahir ta ce, “Shi kenan Inna ba komai Allah ya

kara rufa asiri.

Kwanan Inna biyu a Abuja ta juyo zuwa gida,

Maryam ta ce da jawahir kada ki damu diyata, ni na san shirin dana yi wa jikinki kowanne namiji in dai

ya dandana ki to ba ba zai iya kusanta ki da wata

mace ba, ni na fada miki haka kuma ki hakura ki

koma gidan Haidar ko don ki ba ni labari gaba,

idan ya dandani zumarki. Jawahir ta ji kunya ta

mike da gudu ta bar wajen. Bayan Inna ta koma gida washegari ta nufi gidan

danta Alhaji Ibrahim mahaifin jawahir, su momy da

Abba Nasir zuwa su Auwal da Sani sun yi murna da

ganin Inna gida ya rude a na ga Inna ga Inna. Inna

ta zauna cikin jikokinta ana wasa ana dariya Momy

kuwa tana ta hidimar kawo mata ababan ci da na sha. Momy ta zauna suka gaisa Inna ta ce,

“Maigidan kuwa yana nan.? Momy ta ce, “Eh yana

nan bari na yo miki magana da shi.”

Momy ta samu Dady rigingine a kan gado yana

kallon sili da alamu tunani yake yi, Ta yi sallama tare

da cewa, “Barka da hutawa. Ya amsa da yauwa: Inna ce ta zo take son magana da kai. “Ya mike

zumbur ya ce, “To gani nan fitowa.

Ya zo ya durkusa har kasa ya gaida Inna, ya ce

“Inna da kanki kika taho maimakon ki aiko na zo.?

Ta ce, “Kamawa ta yi daman na zo a kan maganar

yaran nan ne, ya ce, “Wanne yara?” “Ta ce, “Wanda ka hada auren dole yanzu kuma

kuka je kuka yi masa auren da yake so, ita kun

hana ta wanda take so ta mutu kenan ko.?

Ya ce, “Inna Allah ya ba ki hakuri wallahi ba haka

ba ne.”

Dady ya ce, “Don Allah don Annabi Inna ki yi hakuri kada ki yi haka ba mu san abin da auren

nan ya kunsa ba, kada mu yi wa Allah shisshigi a

lamarinsa.

Yanxu ki yi hakuri ki dawo da jawahir nan gidan

gobe sai na sa a mayar da ita gidanta.

Inna ta katse shi, “Kana nufin a mayar da yarinyar ya ci gaba da wulakanta ta ko?

“Wallahi Inna ni na san ba zai wulakantata ba, in

kika yi la’akari da yanda ya gigice da batan jawahir

din. Inna ai kun hora shi ya horu ba zai sake ba.

Inna ‘ya ‘yan nan duk namu ne wa za mu ki a

cikinsu.? Duk wanda za ta aura ai ba kamar Haidar din ba ko Innata?

Ta ce, “To shi kenan ai kokarinka ni ma na fi son a

karfafa zumunci. “Yauwa Innata yanxu ina jawahir

dina?

Tana can gidan kawunta. Dady ya rike baki “Wanne

kawun nata? “Tana da wani kawunne bayan Auta Aminu?” Alhaji ya ce, “Ikon Allah yanxu duk

binkicen nan da muka yi ta yi tana Abuja.?

Sallamar Haidar da Abbansa ne suka shigo nan fa

Abban ya nufi Innar ya durkusa gaban Inna yake

gaishe ta, “Haidar kuwa gaban Dady ya je ya gaishe

shi, shi ya ki kallon Inna. Dady ya ce, “To ni na amsa gaisuwarka ba ka gaida

uwata ba.?

Haidar dai ya yi shiru bai ce komai ba bai kuma kalli

Inna ba. Abba ya ce, “Ai yanzu ma shi ya je ya taso

ni dole har da kukansa shi fa sai an nemo masa

matarsa jawahir. Tun sallar la’asar ya tashi daga office ya je ya sani a gaba ga shi har bayan issha ya

ki tafiya gidansa shine na ce ya zo mu je wajenka

ko za a sami wani dan labari.”

Inna ta ce, “Daman abin da ni ma ya kawo ni kenan

na zo a karbo min takardar sakin jikata ita ma ta je

ta auri wanda take so.” Haidar ya yi saurin tasowa ya rike kafar Inna don

Allah don Annabi Inna ina jawahir take.?

Ta ce, “Ina

ruwanka da inda take ba kayi aurenka ba, to ka ba

ta takardarta ita ma ta auri wanda take so.”

Haidar ya ce, “Don Allah don Annabi Inna ki yi hakuri ki yi min rai ki dawo min da matata wallahi

zan kula da ita ba za a kuma samun kuskure ba.

“Inna ta ce, “A’a, ka je dai ka rike matarka ita ma sai

ta samu wani.

Haidar ya ce, “Ki rufamin asiri “Inna wallahi ko

cewa kika yi sai na saki Kausar za ki dawo min da jawahir sai na sake ta, don ni jawahir ta fiye min

kowace mace.

“Inna ta ce, “Ni da kake fushi da ni ba ka kula ni. Ya

yi saurin cewa, “To yi hakuri mu shirya don Allah

Inna jawahir tana ina.?

Inna ta ce, “Jawahir tana Abuja gidan kawunku tun washegarin ranar da ka koro ta daga gidanka na

tura ta can. “Tuni Haidar ya mike ya nufi bakin

kofar waje.

Abbansa ya ce, “Haidar ina za ka ne? Ya ce, “Abba

Abuja zan tafi yanzu.”

Dady ya ce, “Ba ka da hankali ne ka dubi lokaci fa yanxu karfe tara ka baro matarka a gida ba ka

gudun hakkinta, ka yi hakuri ka koma gidan na yi

wa kawun naku waya gobe za su taho a jirgi insha

Allahu a gobe za a dawo maka da matarka.”

Ya rissuna ya karayi musu godiya sannan ya tafi

gidansa cike da nishadi. Daga nan su ma suka gama tattaunawa a tsakaninsu Inna direbanta ya

maidata gida. Abba ma ya nufi nasa gidan.

Washegari sha biyu na rana a Kano ta yi wa Ankul

da Aunty da jawahir da ma tun goma na safe

kannan Momy suka tafi gidan Haidar don wankewa

jawahir kayanta tare da kade mata kura suka share mata sashinta suka gyara komai.

Dady da Momy sun yi mamakin ganin yanda

jawahir ta girma haka ta kara kyau da haske kamar

ba ita ba. Yaya Abba dai da Nasir sai da suka yaba

kyan nata.

Da yake Inna ma ta zo nan dai aka hadu da Inna da Ankul da Dady da Momi da Anti Maryam a ka yi ta yi

wa jawahir fada da nasiha yanda za ta zauna da

mijinta da kishiyarta lafiya, ki ci gaba da yi wa

mijinki ladabi da biyayya kada ki yarda wata rigima

ta kuma hada ku da mijinki sai mun saba miki.

Gaba daya kuma suka yi ta sama ta albarka. Anti Maryam ta ja ta daki ta dada yi mata bayanin yanda

za ta yi amfani da magangunnan da ta hada mata.

Da magariba suka raka ta gidan mijinta kamar

sabuwar Amarya. An dai sake yi mata fada da

nasiha daga nan kowa ya fashe ya barta.

Ta shige sashenta ta kuwa garkame kofa sai karfe goma na dare Haidar ya shigo gidan. Dakin Kausar

ya shiga ya same ta a mimmike a gado ya zauna a

gefenta ya tambaye ta jawahir kuwa ta dawo?

Ta ya mutse fuska tare da tabe baki kai da ka je ka

dawo da ita ba ka san ta dawo ko ba ta dawo ba

bare ni da ban san ta ba, ko na taba ganin ta ne? Be kuma ce mata komai ba ya yi tolet don inda

sabo ya saba da rashin ladabi na Kausar. Da ya

gama shirnsa ya nufi dakin jawahir sai ya ji shi a

kulle sai ya haye samansa ya yi dai-dai a gadon

bacci.

Har ya fara bacci ya ji shigowar Kausar ta bi shi gadon suka kwanta. Da safe jawahir ta riga su tashi

don haka ta hada birek dinta iya wanda za ta ci ta

gyara babban falon nan da dakunanta kamar

yadda ta saba ta turare su kamshi ya wadaci ko ina

ta shiga ta tsala wankanta da kwalliyarta ‘yar

ubansu. Shadda ganila ta saka wadda ta sha dinkin surfani

duk bulu da yalow da yake kwambineshin ce, ta

sha a don gwal fuskar nan tata sai sheki take tana

shainin. Ta zama cikakkiyar mace sosai kirjinta

kamar ya fashe don cika. Jikinta kuwa wani fitunan

nan kamshi ne yake tashi kamar an yi barin turare a jikinta. Ta fito falonta ta zauna, ba babban falo ba.

Ta dauki break dinta za ta fara ci kenan ta jiyo taku

an yo sashenta.

Haidar har ya tashi ya yi wanka ya gama shirnsa

cikin kayatacciyar shiga ta alfarma kamai yanda ya

saba, amma gimbiya Kausar ana gado a kwance ana ta sharar bacci.

About Ismail

Check Also

BAKAR INUWA CHAPTER 23

Ganin taƙi cin komai Anne ta kira sunanta. Ta ɗago domin amsawa taci karo da …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *