[Advertisements⬇️]

SALON SO CHAPTER 1 - Bankinhausanovels
Sun. Oct 2nd, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

SALON SO CHAPTER 1

 

 

 

Kyakkyawar yarinya ce ‘yar kimanin shekara goma sha bakwai, direbanta ya yi parking da mota ya zagayo ya bude mata ta fito ta shiga cikin wani hadadden gida kerarre, ke da kallon tsarin ginin kin san hoto ne daga kasar waje aka yi irin sa. A kofar falon ta yi sallama ta shiga. Matar da take hakimce akan kujera cikin tsantsararriyar kwalliya ta kece raini, tana ta girgiza kafa da wayar sadarwa a hannunta da take hira. Tana ganin shigowar yarinyar ta dire wayar cikin fara’a ta tare ta, tare da cewa, “A’a Jawahir ‘yar Dady yau a gari? Ko dai batan kai kika yi ne?” Jawahir ta yi murmushi yayin da ta durkusa gabanta ta ce, “Aunty ina yini?” “Lafiya lau Jawahir, amma dai a nan za ki kwanar min ko.? Tun da gobe ba ku da makaranta.” Jawahir ta yi dariya tare da cewa, Tafiya zan yi Aunty yau Dady zai dawo daga saudiya, da kuma ya dira a kasar nan ni zai fara tambaya, kuma ni ma ba zan so ya dawo ba mu hadu ba. Aunty ta yi murmushi ta ce Jawahir gidan Daddy ke dai kullum kina like a gida kamar daddawar daka ba kya son zuwa ko ina ko?” Amma zan je na samu mommy dinki na ji ko ita take hana ki zuwa.” Jawahir ta yi murmushi, “Wallahi Aunty babu rawan mommy Daddy na ne baya son na rinka fita. Sallamar da ta ji ce ta sa ta yin shiru, sai da aka amsa masa sannan ya shigo. Ya zauna a kan kafet tare da rissinawa ya gaisar da Aunty. Aunty ta amsa cikin kulawa ta musamman ta kalle shi ta ce, Ba dai har ka dawo daga office din ba?” “Wallahi Aunty vacci nake ji shi ya sa na taho gida don na kwanta na huta.” Aunty ta girgiza kai tare da cewar, “Ba ka kula da bakuwa ba ne?” Sai sannan ya kalle ta ya ce, “Wallahi ai kamar jawahir ko.?” Au ka mance ma? To ita ce, Jawahir ta dan rissina ta ce, “Yaya Haidar ina wuni?” Ya amsa cikin kulawa sannan ya ce, “Ya su Dady?” “Daddy ba ya kasar, yau dai muke sa ran dawowarsa.” “To Allah ya dawo da shi lafiya, Abin da Haidar ya ce kenan ya mike ya nufi sashensa. Jawahir ta mike Aunty zan tafi” “Haba jawahir har tafiya zaki yi.?” “Wallahi Aunty tafiya zan yi doki nake yi ne na je na fara shirin tafiya taryar Daddy. “To ‘yar Daddy ki gaishe min da shi, kafin na zo gobe yi masa sannu da zuwa. “Ta fito da sauri, direbanta ya karbi kayan da yake hannunta ya zuba a but ya bude motar ya shiga ya tayar suka miki hanyar gida +++++++++++++++++++++ Alhaji Ibrahim shine mahaifin Jawahir, mutumin kirki ne, akwai shi da son jama’a ga yawan kyautatawa na kasa da shi, sam ba shi da kyamar talaka. Yana da dadin zama idan ka kiyaye abubuwan da ba ya so, na farko ba ya son raini, kuma shi kaifi daya ne, in dai ya ce, “I, ko “A’a” to ba wanda ya isa ya tankwara shi sai uwarsa. Su uku ne a wajen iyayensu, shi ne babba sai Aisha wato Aunty babar Haidar sai Aminu, wanda shi ne autansu. Ubansu da suke kira da Baffa ya dade da rasuwa sai mahaifiyarsu Rahmatu da suke kiranta da Inna. Inna mace ce mai kirki da hakuri ga ta da son zumunci, duk inda aka ce ga dan uwa ko ta yaya suka hadu ta jawo shi a jiki ita bare ma jawo shi take yi don ya zo ya ci arzikinta. Tana zaune a unguwar sabon tatin mandawari. Tana matukar son jawahir don a cikin jikokinta babu wanda ya kama kafar son da Inna take yi wa jawahir. Alhaji ibrahim matarsa daya Hajiya Hafsatu, ita ce mahaifiyarsu Jawahir, suna ce mata Mommy. Mommy tana da ‘ya’ya shida biyar maza daya mace. Akwai Abba me sunan kakansu sai Abdullahi, sai Nasir, sai Jawahir da Auwal da Sani. Jawahir ita ka dai ce mace a gidan, kowa ji yake da ita ba ma kamar Alhaji ibrahim da yayyanta. Suna son ta suna shagwabata amma duk da haka ba ta sangarce ba don tana tsoronsu tana kuma jin maganarsu. Jawahir yarinya ce kyakkyawa tana da hankali da nutsuwa akwai ta da biyayya ba ta da rowa. Sai dai miskila ce ba kowa take iya sakewa da shi ba, ba ta fiya son magana sosao ba, in kinji hirarta ce ne da Daddynta ne ko yayyanta sai mommynta, to shi ne za ki ji har da dariya. Amma shagwababbiya ce ta kin karawa don ita har kannanta Auwal da Sani shagwaba take yi musu bare kuma su Yaya Abba da uwa uba Daddynta. Bayan Auwal ne ya dauke min babban turarena da ya fi kowanne tsada. Shi ne kike kuka? Rabu da shi zai gamu da ni ne je ki cikin dakina kan mudubi ki zabi wanda kike so share hawayenki ki yi dariya. Ta fada dakin Dady da gudu tana murmushi yaya Abba ya ce, Su jawahir sarkin rigima. Shi kuwa Haidar a zuciyarsa cewa ya yi, Kai wannan yarinyar tafi ya shagaba shi ya sa take ba ni haushi sai na ga kamar na doke ta in ana lallabata. Yarinya sai shagwabar tsiya sai ka ce ita ce Auta.” Tunaninsa ya katse ne a dai dai lokacin da jawahir ta fito daga dakin, hannunta rike da sunkumemen turare. Ta nunawa Dady ta ce, Dady ga shi na dauka. Yace, “To ‘yar Dady ya yi miki wannan din?” Ta daga kai, “To maza ki je ki boye abunki ki ta fesawa. Ta durkusa fuskarta cike da murmushi ta ce,Na gode Dad Allah ya kara girma, Ya shafa kanta yana murmushi ta yi waje a guje. Takaici ya cika Haidar a zuciyarsa ya ce, Ya za a yi ma wannan ‘yar yarinyar a ba ta wannan turaren? Ya za ta yi da shi? don kudinsa wajen dubu goma sha biyar ne,to ita ta san darajar kamshin ne ma. Yanzu haka wasanta za ta yi da shi kawai. Yaya Abba ya girgiza shi tare da fadin, Haidar me kake tunani ne? ko ka tuno America ne? da yake tare suka yi karatu a can shi da Haidar din. Dariya suka yi suka tafa. Kiran sallar da aka yi ne ya sa su tashi don zuwa su ba da farali. To irin wannan halayyar ta Haidar ita ce take bawa jawahir haushi don haka ko gidansu ya zo ba ta kula shi karkari ta ce masa ina wuni ta wuce shi ba tare da ta jira amsarsa ba. Dan mulki kenan. Ita jawahir duk da miskilancinta ba ta da daukan kai kuma akwai ta da yi wa mutum murmushi tana da halin kyauta duk inda ta ga talaka ko kaskantacce in dai ta san mai bukata ne, to za ta gayawa Daddy ya taimaka musu. wannan halayya tata ita take kara sa kaunarta a zuciyar Daddynta. Kamar yau da safe jawahir ta gama baccinta ta fada toilet a yi wanka ta fito ta tsaya gaban mudubi aka shiga kalailayar jiki, a shafe nan a goge can, ta tsara kwalliyarta cikin boyal shudi rigar fitet da zane ta sa hadadden fashion dinta yari da sarka da abin hannu me shudin dutse, Daddynta ne ya siyo mata daga london. Ta hadu iyakar haduwa fuskar tata sai sheki take yi ta feshe jikinta da turaruka ta fito ta nufi sashen Dady. Ta kwankwasa ya yi mata izini ta bude ta shiga. “A’a ‘yar Dady kwalliyar ta yi miki kyau, Ta yi murmushi ta durkusa ta gaishe shi, “Don Allah Dady ina so yau zan je gidan Inna. “Kin sani jawahir ba na so ki rinka yawan fita amma tun da gidan Innata za ki je ba komai sai ki je. To me za kaiwa Innan? Jawahir ta dube shi tana murmushi ta ce, Dady duk abin da ka ba ni. To shi ke nan ‘yar gidan Dady, daman ke ake jira tashi mu je a yi brek. Mominta ta fito daga cikin dakin Dadyn cikin rantsatsiyar kwalliya kamar me shirin zuwa fati. Jawahir ta yi saurin zubewa ta gaishe ta, mommy Daddy ya bar ni zan je gidan Inna Ta ce, “Yauwa koke fa, ai gwanda ki je kusan kullum Inna sai ta yo miki waya ta ce ba ta jin dadi idan ta dau lokaci ba ta ganki ba. Suka fito babban falo suka hau tabir inda ‘yan samarin suke jiransu. Jawahir ta gaida Yayyanta inda ita kuma kannenta suka gaishe ta, al’adar gidan ke nan kowa sai ya gaisar da wanda ya girme shi. Ta kalli Nasir ta ce, “Yaya Nasir za ka kai ni gidan Inna? Ya harare ta, Ni direbanki ne ina amfanin Idi direban da aka ajiye muku?” Yaya Abba ya ce, Wai kai me ya sa kake haka ne? duk yanda direba zai kula da ita ai ba kamar dan uwanta ba ko? Ki bari mu gama break sai na kai ki. Ta ce, “Yauwa Babban Yaya na gode Iyayen dai suna jinsu ba su tanka musu ba. Bayan gama break dinsu jawahir tanufi dakinta ta kara gyara fuskarta ta sako shudin takalmi da shudin mayafi ta fito, Dady za mu tafi,” To me za ki kaiwa Innarki? shiga sito ki jido mata abin da kika ga za ki kai mata Nasir ya ce, Wallahi Dady sito din Inna cike yake da kayan abinci da na masarufi. ka manta shekaranjiya ka ba ni kayan abinci da na amfani mota guda na kai mata? kuma da muke zuba mata a sito din ma akwai wasu a ciki. Abba ya ce, To sai a kai kudi kawai. Momy ta ce, Ki je wajen Rahane me aiki ini ta gama gasa kaji dana sa ta da akwai cake da samosa da na bayar akayi mata, sai soyayyiyar miyar zabi dana yi mata tun jiya. Alhaji ya ce, Wallahi dalilin da ya sa kenan kullum Hafsa nake kara son ki, kike dada shiga rai na don duk hanyar da za ki faranta min kin san ta, ga yanda kike kula da mahaifiyata, ni kuwa me za ki nema a wajena na kasa yi miki. Ta yi murmushi, Ba komai Alhaji Inna ai uwatace, ba abin da ba zan iya yi mata ba, don albarkarsu muke nema. Auwal da sani su ma suka ce, Dady mu ma za mu je gidan Inna. Jawahir ta turo baki, Gaskiya Dady ba za su bi ni ba, damuna za su yi ta yi da hayaniya sun fiya surutu. Dady ya ce, Ku yi hakuri Auwal ma je da ku da daddare, kun ga islamiyya za ku je in karfe biyu ta yi ku kyale ta ta tafi. Yaya Abba da jawahir suka fita suka nufi gidan Inna Yana tsayawa da motar ta fito a guje za ta shiga cikin gidan Abba ya kira ta, Zo ki debi wasu kayan mana. Ta ce, To suka kwashi kayan suka yi ciki. Salamu alaikum ‘yar tsohuwa, kina nan?” “A’a wa nake jin magana kamar bera?” Kai Inna ki ga zankadediyar budurwa ki ce mata bera.?” Inji yaya Abba. Inna ta ce, Ai lallai kuwa ‘Yar dady ta girma don ko yanzu ma a ka yi mata aure ai zama za ta yi. Jawahir ta rufe fuskarta da hannuwanta ta ce, Haba Inna yarinya ta da ni ni da ko saurayin ma ba ni da shi.” Inna ta ce, “A’a ba kya dai kula su ga Hafizu abokin Abba nan duk nacin da yake yi kin ki kula shi.” Jawahir ta ce, Ai ke kuma yanzu kin ga za mu bata. Abba ya duba agogo ya ce, Inna ni zan wuce office. To maigidana sai ka dawo. Yaya Abba ya tafi. Jawahir tana cinyar Inna tana yagar cinyar gasasshiyar kaza suna ta zuba hira. A hankali aka yi sallama a kofar falon aka shigo cikin takama da isa. Jawahir sanin me shigowar ne ya hana ta amsa sallamar bare ta dago kai ta kalle shi. Inna ta kama washe baki, “A’a yau saraki ne a gidan tsohuwa? Lallai kam batan kai aka yi. Yayi kasaitaccen murmushi ya durkusa gaban Inna ya gaisheta, ta ce, Bature ba a ganinka sai an cike form ko? Yayi kasaitaccen murmushi ya ce, Inna sai dai idan ba a so ganin namu ba. Ta ce, Wai yaushe za ka yi aure ne? ko so kake yi ka za ma tuzuru? Ya ce, Inna me kike ci na baka na zuba, kwanan nan zan kawo miki dakakkiyar yarinya ‘yar jami’a me cikakken ilimin boko wayayyiya. Inna ta ce, Ba dai cikakkiya ba sai ka kwaso min kwaila. Ya ce, Haba Inna me za ayi da kwailar mace, duk yarinyar da ba ta je jami’a ba ai ba ta waye ba namijin ya sha wuyar zama da ita, don hauka za ta yi ta yi masa.” Jawahir ta san duk da ita yake wannan habaicin maganar ita kuwa ko kallo be ishe ta ba. Inna ta ce, Jawahir kina kallon Yayanki ba za ki gaishe shi ba.? Jawahir ta yamutsa fuska tare da kau da kai gefe daya ta ce, Ai ban gane shi ba ne, Maganar ta yi masa ciwo amma da yake ba da shi ake maganar ba sai ya yi shiru yana jin su. Inna ta ce, Kin ci gidanku, in.. ban da iya shege yaya za ayi ke da dan uwanki ki ce baki gane shi ba?” Jawahir ta ce, To in ban da abinki Inna ai sai kana yawan ganin mutum za ka san shi ko.? Inna ta ce, Ba na son dogon surutu, ni dai ina horonku da ku rike zumunci, don zumunci ba abin wasa ba ne, don Allah Subhanahu wata’ala ya ce, Duk wanda ya yanke zumunci ba shi ba rahamar Ubabgiji. Jawahir ta ce, Inna ni fa ba yanke zumunci zan yi ba, gane shi ne kawai ban yi ba, to ba sai a yi min bayani ba. Ya mike, “Inna bari na karasa office.” To Haidar ba a abin da za kaci a gidan tsohuwa,. Ya girgiza kai tare da yamutsa fuska, Inna ba zan iya cin komai ba a nan don zuciyata tashi take yi. Ya bawa inna kudi ta yi masa godiya tare da sa masa albarka. Ya yi gaba jawahir ta mike ta ce wa Inna bari na raka shi bakin motarsa. Inna tace, Yauwa ko ke fa, ai gwanda ku rinka karfafa zumunci, don bi so nake kullum na ga kanku a hade. Jawahir ta same shi a harabar gidan yana kokarin bude motarsa ya shiga, Jawahir ta ce, A dai taka a hankali a daina jin kai da wulakanci, don duniyar ba matabbaciya ba ce, wata rana a karkashin kasa za a saka mutum. Ya kalle ta ya yatsuna fuska tare da zuba mata harara ya tofar da yawu gefe daya ya sa hannu ya toshe hanci wai doyi take yi. Ta yi shigewarta ciki ta bar shi a wajen yana kokarin shiga motarsa. A zuciyarsa ya ce, Lallai yarinyar nan ba ta da kunya amma zan yi maganinta ne,. Jawahir sun zana jarabawar fita daga Secondary har sun hada fatin gama secondry. Duk yawancin samarin da suke kawo kansu gare ta ba ta kula kowa sai wani Faruk da jininsu ha hadu daga mutunci suka zarce da soyayya. To suna son junansu don duk yanda jawahir take kin samari da an ce Faruk zai zo kaga rawar kai da girin girinkidishin yin tsararriyar kwalliya ta taron masoyi. Sannu sannu soyayya mai zurfi ta shiga zuciyarsu. ****************************** Aunty tana zaune a falo Abvan Haidar ya fito daga toilet ya zauna kusa da ita ya ce, Kin sani ne, Wallahi tun satin da muka je saukarsu Jawahir zuciyata ta matsu da sha’awar halayyar yarinyar nan. Tana da hankali da nutsuwa ga girmama nagaba da ita. Abin da ya fi bani sha’awa da ita yanda take karatun Alkur’ani a wajen saukar nan tasu, ta iya fitar da harafi ga zakin murya da bawa kowanne baki hakkinsa. Ni yanzu shawarar dana yanke zan je na samu Alhaji ibrahim da ya tallafa ya bawa Haidar auren jawahir. Aunty ta yi ajiyar xuciya ta ce, Wallahi da hakan za ta faru da na fi kowa farin ciki, amma abin da nake tunani Alhaji anya kuwa hakan za ta yiwu ka san halin miskilancin danka kada ya ki a zo zumincinmu yana baci a banza, gaskiya Alhaji ka duba ka gani.” Ya ce, Karki damu Aisha, Allah ya ga niyarmu ta kara donkon zumunci ce a tsakaninmu, insha Allahu ba za su bamu kunya ba. Ta ce, To shi kenan Allah ya taimaka, Ubangiji ya sa a yi a sa’a amin Da magariba Abban Haidar ya nufi gidan amininsa Alhaji ibrahim. Suka karbi junansu da murna da farin ciki. Suna sitting room dinsa. suna yin sallar insha’i a masallacin gidan suka dawo sitting room din suka ci abinci. Daga nan Abban Haidar ya zayyanawa Alhaji ibrahim shawarar da ya yanke na game da hada ‘ya’yansu aure jawahir da Haidar. Alhaji ibrahim ya yi dariya ya ce, Amma na ji dadi. Gaskiya wannan ai shawarace me kyau. Allah ya tabbatar mana da alherinsa, to amin. Allah ya sa ayi da mu.” Ko da Abvan Haidar ya tafi Dady ya shiga gida ya gayawa mommynsu jawahir komai. ita ma addu’ar ta yi tare da sawa abin albarka. Da safe bayan sun kammala break dinsu. Alhaji ibrahim ya kalli jawahir ya ce, To jawahir a yau nake son sheda miki lokacin aurenki fa ya yi, zan aurar dake don cika unarnin Allah subhanahu wata ala. Ta dafe kirji. Dady shekarata goma sha bakwai fa.” Ya ce, To menene, ai kin isa ko ba ki da saurayi ne?” Ta boye fuskarta a cikin hannuwanta ta ce, Daddy akwai Faruk, amma ce masa nayi ya dakata sai na fara zuwa jami’a tukunna na yi masa magana ya fito. Alhaji ta ce, Uhm jawahir ki kyale maganar Faruk ki ba shi hakuri kawai don ni na riga na yi miki miji. Ta dafe kirji cikin kwalalo ido ta ce, Na shiga uku sai kuma kuka don Allah Dady ka yi hakuri ka bar ni na auri Faruk shi zuciyata take so.” Alhaji ya girgiza kai, Kada muyi haka da ke, ki yi hakuri ki bi umarnina ki auri mijin dana zaba miki, insha Allahu ba za ki taba da na sani a rayuwarki ba, kin ji. Ta dafa kanta. Ta amsa da To Dady Allah ya zaba mana mafi alheri, Ta mike ta yi dakin mommy tana kuka. Momy ta ce, Lafiya ke kuma kike kuka? Ke da wa? Me aka yi miki? Mommy ki taimake ni Dady zai yi min auren dole, Ta kwashe komai ta gaya mata. To ke tun dsya ce yayi miki miji to ki hskura da Faruk din mana. Jawahir ta kuma fashewa da kuka, Don Allah momy ki taimaka min ya bar ni na auri Faruk. Momy ta ce, Kin ga kawai hakura ki bi zabin mahaifinki ni ba ruwana ina zaman lafiya ba za ki jawo min tashin hankali ba. Ki bari zan yi nafila da addu’0’i zan miki istihara don neman zabin Ubangiji, amma ba na so ki tayar da hsnkali, don komai mukaddari ne daga Allah, kin ji,ki share hawayenki kar ya gane har yanxu kuka kike yi. Ta ce,,To momy ta mike ta nufi dakinta. ****************************** A gidan Haidar kuwa Alhaji ya gama gayawa Aunty yanda suka yi da yayanta. Aunty ta ce Nina san yaya zai amince ni dai tsorona yaron nan ka san jin kansa kar a yi auren ya zo yana wulakanta min ‘ya.” Alhaji ya ce, Kirawo min shi mu ji ta bakinsa, ta daga waya ta danna lambobinsa ta yi ringin ya fi sau nawa kafin a daga sai can ya daga. Hello wallahi ban san ke ba ce sai da na kalli wayar sai na ga lambarki lafiya Aunty.?” Lafiya kalau ka zo falo Abbanka yana son magana da kai yanxu” To Aunty ga ni nan zuwa Suka ajiye kan wayar. ya yi sallama tare da tura kofar ya shiga bayan sun amsa masa, Ya zauna gaban Abbanshi a kan kafet, Abba ga ni. Ya ce, Yauwa Haidar na kirawo ka ne daman don na ji ko ka tsayar da matar da zaka aura? Haidar ya ce, Wallahi Abba ni ba ni da lokacin kallon matan ma bare na ga wacce ta yi min. Alhaji ya ce, Ni kuwa ka ga ina da lokacin kallon su, don har na samo maka matar da za ka aura, don nasan za ta yi maka yar uwarka ce Jawahir.” A firgice ya daga kai ya kalli Aunty ya ga karatunta ma take yi ya juya ya kalli Abbansa ya ce, Abba jawahir fa ka ce, Haba Abba me zan yi da wannan kwailar yarinyar, yarinyar karama zan aura? Haba ‘yar da ko kilewa ba ta yi ba, kwanan nan fa ta gama secondary. Alhaji ya daga masa tsawa, Kai ba ma son zancen banza, ni ita na zaba maka kuma ita nake so ka aura ta zamo uwar ‘ya ‘yanka. Haidar ya marairaice kamar zai yi kuka, Wallahi Abba jinina bai hadu da yarinyar ba ta da kunya shi ya sa na tsane ta. Aunty ta zaburo ta rufe shi da fada, Yar tawa kake cewa marar kunya ka tsane ta? To bari ka ji na gaya maka ko kana so ko baka so aure bsbu fashi, munyi niyyar hada ku kuma sai mun yi, in ya so ranar da aka kai ta dakinka ka yanka ta gunduwa gunduwa ka kawo mana namanta, wannan shi ne maganin kiyayya marar kunya wanda bai san mutunci ba. Abba ya dakatar da ita, To fadan ya isa haka, na san bai yi dai dai ba amma ki yi hakuri. Ya kalli Haidar, Ka tashi ka tafi amma ka sani jawahir ita ce zabinmu ba gudu ba ja da baya, sai ka je ka yi tuananin abin daka ya fi dacewa da rayuwarka. Haidar ya taso cikin bakin ciki, zuciyarsa tana kuna ya yo dakinsa yana magana a zuciyarsa yana zagaye falon nasa maganar har ta fito fili. Haka kawai a rasa yarinyar da za a ce na aura sai wannan figaggiyar yarinyar ‘yar karama, yarinyar da muka yi rainonta? me zan ji a jikin wannan kwailar, yarinyar da kyar ma in ta fara kirgar dangi? Haba ai an cuce ni, yanda nake ji da kaina nake so na auri katuwar mace wadda ta gama jami’a me hankali wadda za ta fuskanci halina ta bi ni yanda nake so mu zauna lafiya yaushe za a hada ni da wannan faratun? Yarinyar da ba ta fi ta tsaya min iya ciki ba, gaskiya a canja shawara, don in har yarinyar ta yarda ta aure ni sai ta gane kurenta.

 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]