[Advertisements⬇️]

ABINCIN ZUCIYATA COMPLETE - Bankinhausanovels
Thu. Oct 6th, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

ABINCIN ZUCIYATA COMPLETE

 

Tsaye take abakin titin shatale talen wunti, sanye cikin uniform ɗin makarantan Iƙamatus sunnah Gwallaga, wanda yake unguwar gollah a cikin garin Bauchi, ligth Brown ɗin wando da farin riganta iya gwiwa, da hijabinta fari da aka kewaye kafaɗan da light brown ɗin bayes,  tsayin hijabin bai wuce tsayin Hanunta ba, sniker ne a ƙafanta kalan yadin wandonta, kai kace da yadin wandonma aka ƙera takalmin, da fari sol ɗin safa a ƙafan, jakantama ligth brown ne kalan takalmin anmasa kwalliya da farin rubutu a jiki, tsaf da ita abun dai sai wanda ya gani,  kalle kallen ababen hawan da suke karaina akan titin take,  wasu iyayensune suka ɗauko su amota, wasu Drivern gidansu ne ke kaisu, wasu kuma a mashin Ake kaisu na acaɓa, wasu kuma mashin ɗin iyayen sunne, wasu kuma a kwaso su a Napep, Ga kuma ƴaƴan Talskawa da suke tafe aƙafa, wasu Makarantan Gomnati suka nufa, wasu na kuɗin da bai taka kara ya karya ba

Ta maida kallonta kan hanya cikin tausayin kanta, ta tsallaka titin da gudu tana share guntun hawayen da ya gangaromata, tana tuna Dogon tafiyan dake gabanta, bayan wanda tayi mai yawa, Babban abunda take tsoro shine Dukan da zata sha agun su Amiran gidansu wacce ta kasance ɗaya daga cikin prefect, “Shikenan idan akace mahaifinka ya faɗi ya mutu, baka da sauran gata a Duniya? Ba wanda zai tausayamaka? Ba wanda zai ɗaukeka ya daidaita ka da ɗan cikinsa? Ba mai taimakonka, Kowa ya tsaneta agidan inbanda Umminta da Sadiya, sai Dady da Hajjah, sune kawai basa nunama ƙiyayya,

Taja Dogon sheshsheƙa a fili tace “Amira nima ba asona na dawo gidanku ba, Mutuwa Abbana yayi ya barni, Kukan kunji daɗinku Dadynku yana nan, ta ƙarashe tana matsa Hanunta da Amiran ta Jimata ciwo dalilin janta da tayi acikin Motan Tafiyansu makaranta ta wurgota waje, ta yarfe hanun, sannan ta kalli doguwar hanyan da zata ƙureshi kafin ta isa school ɗin, sai kawai tasa gudu,

============-=============-========

Zaune yake a bakin gado yana ƙara laluman Numbern wayan Amaryansa Jamila,  wanda tun shigowansa yake sa ran shigowanta, anma har ya shiga wanka ya fito ba alamanta,  Dan haka ya ke ta lalumanta a waya, akashe yaji wayan yanzu, saɓanin ɗazu da ake ce ba Network, cikin takaici yayi jifa da wayan akan gado, gami da jan dogon tsaki, sakamakon tuno rabuwan da sukayi da ita da rana da da ya dawo cin Abinci, yasake jan tsaki, a fili yace “wai fushi Jamila tayi dani? Anma tsawon zamana da ita shekaru kusan huɗu kenan bata taɓa fushi dani ba,

Yaɗan jinjina kai gami da cewa, “yau da gobe dole ta fara fushi da kai, duk haƙurinta sai ka ƙurota, irin yawan faɗan da kake mata kuma agaban ki shiyoyita,

Sai kuma ya kuma cewa, “to ai itama sam bata kyatamin, fisabilillah ace duk ranan girkin Jamila, Ban isa cin Abinci a cikin gidana ba, daga ta rambaɗa gishiri mai tsanani sai yaji mai tsanani,  nayi nayi da ita tabar girkin, ta dingayi kaman yanda sauran ƴan’uwanta suka sakarma mai aiki, anma taƙi, wai ita da kanta zata nayi, ya ƙarashe maganan cikin zafi kaman yanzu abun ke faruwa,

Ya miƙe cike da takaici ya fito palour, ya zauna akan sofa, gami da canza tasha daga aljazira zuwa Bollywood, wai duk dan ya manta da kashinta, sai dai abun yaci tura, dan kyakykyawan Fuskanta ne kawai yake gani akan akwatin Tvn, daradaran idontanna datake jujjuyamasa su, a duk lokacin da suka haɗa ido,  da ƙayataccen murmushintannan mai kawar masa da duk damuwan dake tare dashi,  ya mirgina kansa a saman kujeran gami da lumshe idonsa, yana sauƙe ajiyan zuciya,

Daddaɗan ƙamshin turarenta ne hancinsa ya shaƙomasa, firgit ya miƙe ya nufi ƙofan palourn gami da kama handle ɗin ya buɗe ba tare da ya shirya ma hakanba,

Ɗan kalle kalle yayi abakin ƙofan, yaleƙa, sannan ya fice, sashinta ya nufa kai tsaye, daddaɗan ƙamshin turaren wutanta na tsinke mai suna ramadanne, ya doki hancinsa, ya mai da ƙofan ya rufe gami da jingina bayansa a jikin ƙofan yana ƙara lumshe idonsa, yana bin falon da kallo, wani nitsuwa da annashuwane ya ziyarci zuciyansa,

Komi a bisa tsari yake a palourn, fes fes gwanin sha’awa, nan idonsa ya sauƙa akan twince sadiq da Usman da suke dunƙule da juna, a kan doguwar kujera suna Baccinsu, a hankali ya ƙarasa garesu, ya duƙa ya kwahsesu dukansu biyu, ya rungumesu a ƙirjinsa ya zuba musu ido, yana murmushi, tunowa da yayi da ido biyu suke da yanzu sun ƙanƙameshi kman zasu yardashi, suyi ta ture 2, kowa yanason a fara ɗagashi,  yakuma murmusawa gami da ƙara rungumesu, ya nufi Bed room, ya tura ƙofan ya shiga da guntun sallamansa,

Tayi saurin sa hanunta ta goge hawayen da tunda ya fara zirya a fuskanta bata gogeshi ba, sai yanzu da taji motsi, ko baagayamata ba tasan maigidannatane,

Ta ɗauki soson powder tana gyara rantsatstsen kwalliyanda da ta caɓa,

Badundai tasaba da yinba, har inbatayiba sai ta jita kaman bata da lafiya ba, da ma bazatayinba, tsaban ƙuncin da takeji,

Cigaba tayi da gyara kwalliyan tana kallonsa ya shimfiɗa yaran, ya musu Addu’a gami da sauƙe musu net,

Ya juyo da kallonsa gareta, suna haɗa ido ta kashemasa ido gami da sakarmasa   murmushi,  tace “welcome nawan, yaɗan harareta yace “bana so,

Ta langaɓar da kanta, “im sory!

“naƙin ince fushi kikayi dani?

Ta zaro ido waje, “Fushi kuma Dear?

“Eh mana tun yaushe na dawo, kina jina, kikaƙi zuwa dan kawai na miki faɗa a kan gaskiya?

Wani takaicine ya ziyarceta,  aƙasan zuciyanta ta mai maita, “Dan namiki faɗa a kan gaskiya?  

“Gaskiya? Nandanan  taji ranta ya kuma ɓaci, ji take kaman a yanzu abun yake faruwa, yanda ya tsaya a tsakar gida yacimata mutunci son ransa, a gaban kishiyoyinta, da y’ay’ansu, duk da bata da laifi, a iya saninta batasa borkono ko kaɗanba, gudun kar asamu akasi tunda tasan mai gidan bayaso, tasani sarai makircin da akasaba matane,

“ok yanzuma fushin zakiyi min?

Tasaki ƙayataccen murmushi cikin salon son kawar da komi aranta, ta shagwaɓe fuska a sanyaye, tace “Haba Hubbi ta yaya zan iya fushi da kai?

Ashe nima zan iya fushi da kaina kenan,

“ga alama, sai da na biyoki,

“yi haƙuri ba fushi nayi ba Hubbi, kaina ne yake min ciwo nasha magani, na ɗan kwata, dafatan zaka gafarceni, ta ƙarashe tana masa fari da idanu, salon da yake jefa zuciyansa cikin shauƙinta kenan a koda yaushe,  

Ya matsota gami da shafa goshinta,

“kash! Sory bugun zuciya na, wlh nazaci fushi kikamin,

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

So ya kan?

Ina fatan ya daina ciwo,

Tagyaɗa kanta kaman irin yanda yara sukeyi tace, “tunda yaganka ya daina,

“yauwa anma ya kyauta, da yabarmin kaina,

Mutafi, tace “to Abincin fa mu tafi dashi pert ɗinka ne? Ko zakaci anan?

Yayi diri-diri, yana kallonta, cikin kame-kame, kamar mara gasiya, yace “no karkidamu, nasha tea a ƙoshe nake, ke kawai nakeson gani kusa dani Jamila na,

Jamila tayi saurin kawar da takaicin da ya tosamata, tace d’azunnanfa na dafamaka wani Abincin,

Yad’an Had’e rai, ” anma Jamila na hanaki yin girki nawa ni kad’ai a kitchin d’inki, saboda fitinan y’an’uwaki, yanzu sai sufara Bala’in nasu, suce basu yarda ba, wani abun kikasa a Abincin, inkasana Halin mutum kasha maganin Zama dashi, ya sauk’e maganan a hankali, kaman mai Rad’a, yana kallonta, kanta a sunkuye tunda yafara maganan, cikin sanyin muryanta tace “kayi hak’uri insha Allah, zan kiyaye.

Yad’an murmusa gami da d’agota yace, ” ok zo mutafi, ya wuce,

Da ƙyar take ɗaga ƙafa, tsaban takaici, itakam yanzu ta fara gajiya da wannan abun haushin, haƙurinta ya ƙare, sam bata saba irin wannan Rayuwa ba,

Jamila irin matannane da suka ɗauki rayuwar aure da matiƙar muhimmanci, suka ɗauki na miji ɗan goyo da zani har a ɗamareshi da majanyi, sosai suka ɗauki na miji kaka bama uba ba, takan iya sadauƙar da farin cikinta ta ɗauki baƙin cikin muddin shi zaiyi farincikin, takan sanyashi dariya koda daga baya zatayi kuka, sosai ta riƙi aure babban ibadan da yake kai mace ga tudun na tsira, Aljannanta kawai  take nima ba kama hanun yaro,

Shiyasa ta daure ta ɗauki tozarcin gidan Alhaji Ahmad, takanyi iya bakin ƙoƙarinta taga bataji ɓacin raiba, na irin abunda kishiyoyinta, da ƴaƴansu, kai da shi kansa ma, sukeyi mata,  duk da Rayuwan gidan da takeyi rayuwane da bata taɓa mafarkin yin irinsaba,  sam ba irin haka tasaba a gidan mijinta na farko ba,  tayi Rayuwa cikin jin daɗi da farin ciki agidan marigayi Auwal, sungina Rayuwansu cikin tsananin so da tattalin ƴan’uwa,  kafin mai yanke jindaɗi, da akasin haka a rayuwan Duniya yazo ta yanke musu wato (mutuwa)  da wannan tunani ta shiga sashinsa, Bed room d’insa ta shige kai tsaye, tacire Hijabinta, ta ninke ta ajiye a cikin Sif, ta kuma gyara kwalliyanta, sannan ta d’auki Rigan Baccin a Drowern da take Adana kayanta, tasakaka, ta gama feshe feshen turarukan da tasaba, sannan ta mayar ta rufe, ta gyare d’akin tsaf kamar yadda ta saba, sannan ta fito, idonsa  cak akanta, takunta takeyi kamar Hawainiya, har ta matsoshi, ya bud’emata Hanu ta fad’o k’irjinsa, dai dai lokacin aka turo k’ofan palourn a zafafe aka shigo,  Karima ce ta shigo rik’e da kunkumi, tana binsu da kallo, Jamjla tayi k’ok’arin zamewa daga jikin Alhaji Ahmad, ya maida ita yana kallon Kariman Rai a b’ace yace “Lafiya kuwa Karima? Ban gargad’e kan shigomin d’aki a irin wannan lokacin ba Sallama ba niman izini ba?

A fausace Karima tace, ” Eh ai dole zakace Haka, Mara Adalci,

“Ni kike k’ira Mara Adalci?

” Eh, ko bakai bane kace bazaka dinga bin d’akunaba? Saidai a biyoka?

Yanzu daga ina kake? Da idona naga ka fito daga d’akin wannan kilakin, baka ko jin kunya, tsofai tsofai da kai, kuka fito kana sak’ale da Hanunnta, Wlh ni nagaji da zaluntana da kakeyi a gidannan, kabani takardana kawai, bazan iyaba, ta k’arashe tana kuka,

Rai b’ace Alhajin yazame Jamila da take kwance luf ajikinsa kaman batasan wainar da ake toyawa ba, Ya mik’e tsaye ya nunamata Hanyan fita da yatsansa, “Malama yinan tun Ban b’atamiki raiba, Gobe in Allah ya kaimu kizo ki karb’i takardankin, yanzu kam ina da abunyi, zata kuma yin magana ya tako gabanta cikin b’acin Rai ya nunata da yatsa, ” Nagayamiki ki ficemin a nan, inkin k’i wallahi komi na iya faruwa,

Tsaban b’acin Ran da ta gani a kan fuskansane, yasa ta fita ba shiri Dan ba hakan tasoba, taso taci ma Jamila mutunci ne sosai, yabi bayanta, Yayi ma k’ofan key, sannan ya dawo ga Jamilan ya rik’o Hanunta gami da kashe TV, suka shige ciki,

Rarrashinta yake tayi kaman yanda yasaba a duk lokcin da Matan sukamata wani cin Zarafin, ahaka ya cigaba da Bidirinsa, yayinda ita kuma ta lula Duniyan tunanin Rayuwanta na baya, ahaka Barci Yayi gaba dasu, da safe kuwa da wannan fitina aka karya a gidan Alhaji Ahmad, Dan da Asubah Da Mama Karima taje Gaida Momy Amina kaman yanda sukasaba a gidan Ko wani asuba da sun idar da Sallah zasuje Su Gaida Hajjah Maman mai gidan, sai suje Su gaida Momyn,  kasancewarta Uwar gida,  tunda Karima wacce yaran Gidan suke kira da mama taje gaida Momyn kaman yanda yaran suke kiranta dashi itama, nan ta kitsamata k’arya da gaskiya, tace mata Tunda Alhajin ya shiga dakin Amaryansun Wato Jamila, sai da akayi assalatu ya fito, Nan da Nan Momyn Ta cika bam, kasancewan dama tafi kowa kishi da Jamilan saboda wasu dalilai nata, nan ta sha Alwashin shukamusu rashin mitunci, Dan Haka batama jira Alhajin ya shigo gaishetaba kaman yanda yasaba inyadawo daga Sallah ya shiga d’akinsa Yayi azkar d’insa sai yabi Kansu yagaidasu kafin ya dawo Yayi karya Yayi shirin fita Kasuwa, tunda Yaji an turo k’ofan yabi k’ofan da kallo a tunaninsa ‘yay’ansane suka fara shigowa gaidashi, sai dai tun da Yayi kwalli da Aminatu, hakanan yaji k’irjinsa ya buga, Dan yasan ita Ungulu ce bata Diran Baza, ya gyara zamansa gami da jingina bayansa ajikin sofa, yana cigaba da Azkhar d’insa, a saman sofan ta zauana daf dashi, tana jijjiga, tana cika tana batsewa,  ta k’asan idonsa yake k’aremata kallo, yana mamakin yanda Halayenta suka sauya gaba d’aya tun bayan aurenshi da Jamila, yasani tana da kishi mai zafi, anma dai abun nata bai kai hakanba, sosai take d’aga Hankalinta, ta d’aga ma duk mutanen Gidan Hankali akan Jamilan, ya shafa Addu’an gami da mik’ewa yana Duba agogon dake Manne a b’angon d’akin,

“Gurinka fa nazo ka kuma San da hakan, naga kana shirin tafiya abunka, yana d’an had’e Rai gami da cewa, ” inajinki, ya kuma kallon agogo, dai dai lokacin Jamila ta shigo da kayan Karin kummalonsa, Kai tsaye wajen ajiye abincin ta nufa, Ajiye ta juyo, fuskanta a d’an sake ta kalle Momyn, cikin girmamawa tace “Ashe kina nan nashiga gaidaki baki nan, Ina kwana? Rai ab’ace Momyn ta watsamata Harara, ” Me kike nufi da ashe ina nan? Kina tunanin makirci da Asirce asircenkin yayi tasirine kenan, Da bazan shigo d’akin mijina ba? Bak’ar munafuka, Bak’ar makira, to wlh kinyi kad’an, Jamila tayi murmushi tace, “Ba haka nake nufi ba Hajiya, Allah ya baki Hak’uri,

” Haka kike Nufi mana, tsohuwar Kilaki, mai halin karuwan zamani, Alhajin ya zauna akan Sofa, yana kallon Momyn, yace “ke Aminatu ya isa haka,

” Jamila tafi abunki, Jamila ta juya ta fita idonta Baya ko ganin hanya da kyau,

DOWNLOAD HERE

ABINCIN XUCIYATA complt

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]