[Advertisements⬇️]

SANADIN SONKI CHAPTER 2 - Bankinhausanovels
Mon. Mar 27th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

A SANADIN SONKI CHAPTER 2

 

 

 

Umaru direba miji ne a wurin Fatima, auren so da kauna suka yi don sai da suka d’an jima suna soyayya kafin su yi aure.

Bayan sun yi aure ne suna zaman su lafia cike da so da kulawar junan su, don ma bai fiye zama a gida ba tun da direba ne shi suna tafiye tafiye zuwa garuruwa daban daban, amman hakan bai hana shi kula da ita ba sosai kwatsam ana haka sai Fatima ta samu ciki tun daga lokacin ta rasa gane kan Umaru don gaba d’aya ya canja mata, duk wata kulawa da yake bata ya bari.

Saboda sam shi baya son yara gaba d’aya wahala ne rainon su kawai, yayi rarrashin da ban bakin don kawai Fatima ta yarda a zubar, amman sam tak’i yarda saboda tana matuk’ar kaunar yara sosai, ganin tak’i yarda da buk’atar shi na zubar da cikin yasa shi fara gallaza mata tare da yi mata wulak’anci da rashin mutunci kala kala.

Amman duk Fatima ta shanye wannan wahalar da yake bata har zuwa lokacin da Allah ya sauke ta lafiya ta samu d’a namiji inda ya ci sunan shi Aliyu, saboda rashin babu ko suna ba’a yi ba balle yiwa yaro yanka kamar yanda ake yi a al’adance, saboda iyayen Fatima basu da k’arfi su ma kuma waje ba d’aya ba don suna da d’an nisa a tsakanin su, tun kafin ta haihu da Umaru ya sanya k’afa ya bar garin bai dawo ba har sai da tayi wajen wata biyu da haihuwa sannan ya dawo duk da kuwa yaji labarin haihuwar.

Nan ya bi ya tsani Aliyu ko kad’an baya kaunar yaron, ga zafin talauci da ya kunno mishi kai saboda motar da yake aiki da ita mai shi ya kwace abar shi, sai buga buga da yake faman yi.

Aliyu na da watanni 10 cif, Fatima ta sake samun wani cikin nan Umaru bak’in ciki ya isheshi, a lokacin babu irin cin mutuncin da bai yiwa Fatima daga k’arshe sai da yasan yanda yayi ya zuba mata maganin zubar da ciki a lemo, ya bata tasha babu dad’e wa ciki ya zube nan farinciki fal cikin zuciyar shi, yayin da Fatima bata zarge shi ba ta d’auka kawai 6ari ne tayi nan ta cigaba da rainon Aliyu wanda uban bai ta6a d’aukan shi ba, ko kallon mutunci baya yi mishi saboda tsabar tsanar da yayi mishi kamar ba shine uban shi ba.

Bayan zubewar ciki ne ya dawo da d’an bata kulawa kafin daga k’arshe kuma wani cikin ya sake bayyana a jikin Fatima, wannan karon ma zubar mata da cikin yayi wanda sai a lokacin Fatima ta ankara da hakan, nan tayi kukan bak’in ciki da takaici na abin da mijin nata yake yi mata na mugunta.

Sai da Umaru ya zubar wa mata da ciki sau uku bayan haihuwar Aliyu, ana hud’un ne kuma bai samu nasarar zubar wa ba har aka haifo Suhaima, sai da Suhaima tayi shekara 5 sannan ta sake samun wani cikin wanda har Fatima ta fitar da ran sake haihuwa ganin shekarun Suhaima sun d’an ja, kwatsam ta samu wannan cikin wanda ya sanya Umaru dana sanin auren Fatima a rayuwar shi ga talaucin da yake fama dashi mai tsanani.

Har zuwa yanzu babu abin da ya canja daga tsanar da yake yiwa Aliyu, Suhaima da kuma cikin da yake jikin Fatima, daman abinci ba basu yake ba komai na abin da ya rataya a wuyan shi na hakk’in matar shi da yaran shi baya yi, kanshi kad’ai ya sani idan ya samu kud’i zai ci mai dad’i a cikin shi, wani lokacin agaban su zai ci abin shi sai dai su yi ta had’iyar yawu, amman ko kad’an ne bazai ba su ba, sai dai da dare ya bi ya tak’ura wa Fatima da buk’atar shi, bayan kuma ko abincin kirki baya bata wani lokacin ma tun karyawar safe har zuwa daren ba zata samu cin wani abincin kirkin ba, haka zai bi ya gala6aitar da ita shi yasa kullum sake rame wa take ga jiki babu k’arfi.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Ban da uban dukan da su Aliyu da Suhaima suke sha a hannun shi, don kusan akan su yake huce haushin shi, har zuwa lokacin da Aliyu ya fara fita d’an aikin k’arfi yana d’an samun wani abin wani lokaci ya siyo musu abin da zasu d’an sa a cikin su, ko kuma idan makobcin su idan anyi girki da d’an yawa suna taimaka musu saboda sun san halin da suke ciki, bama iya su kad’ai ba kusan k’auyen gaba d’aya ma sun gane halin da suke ciki.

*** *** ***

*CIGABAN LABARI*

 

Haka su Fatima suka cigaba da rayuwar wahala a hannun mugun mijin ta uban yaran ta, da ita da yaran nata don gaba d’aya had’a wa yake ya ci musu mutunci son ran shi.

Kamar yau da sassafe suna zaune cikin d’aki, a gaban su garwashin wuta ne a cikin kasko suna jin d’umi, duk sun yi jigum jigum Fatima da Aliyu suna tunanin hanyar da zasu bi don su samu abin da za’a karya dashi, yayin da Suhaima kuma ta fara hawaye saboda yunwar da take nuk’urk’usar ta.

Bankad’o labulen d’akin aka yi aka shigo, kamar kullum ba wanda ya kalle shi, cikin sauri ya wuce uwar d’aki ko kallon inda suke bai yi ba, babu jimawa ya fito hannun shi rik’e da jakar kayan shi kaf.

Kallon matar ta shi yayi tare da cewa
“to ni Fatima tafiya zan yi, kuma bansan ranar dawowa ta ba, watak’il na dawo ko kuma na tafi kenan, tun da kin k’i yin abin da nake so, zan tafi zan yi nesa da rayuwar ku, zan bar ki ke da yaran ki.”

Tun da ya fara magana Fatima take kallon shi tana kuka, yana k’arasa maganar shi ya sanya kai zai fice zuwa waje babu alamar damuwa a fuskar shi, da sauri Fatima ta rik’o rigar shi cikin kuka ta fara cewa
“yanzu tafiya zaka yi ka barmu? ”
Babu wata damuwa yace
“tabbas tafiya zan yi, bazan zauna bak’in cikin ‘ya’yan ki ya kashe ni ba, tun kafin lokaci na yayi ”

Cikin tsananin kuka Fatima tace
“Don Allah kayi hak’uri ka dawo mu zauna, kada ka mance ina da auren ka akai na, sannan kuma ga yaran k………”

Kafin ta k’arasa fad’in maganar ta, Umaru ya sanya hannu ya ture ta da k’arfi, ta fad’i da6ar a k’asa, tuni marar ta tayi wani mugun d’aure wa, da sauri Aliyu ya nufi wajen Fatima shi da Suhaima suna mata sannu, cikin hassala da rashin mutunci yace
“kada ki k’ara danganta ne da wad’annan shegun yaran, kuma zan tafi babu uban da ya isa ya hana ni tafiya ”
Yana gama fad’in haka ya kad’a kanshi ya fita, cikin zuciyar shi wasai babu damuwa ko kad’an.

Dakyar Fatima ta iya gyara zaman ta, saboda mugun ciwon da marar ta yake, sakamakon ture ta da mijin nata yayi ta fad’i, wani irin zugi zuciyar ta take lokaci d’aya ta nemi hawaye ta rasa, ta kafe idon ta waje d’aya tamkar wata mara rai don ko motsin kirki bata yi.

Tun motsawar da tayi bayan ta fad’i, a hankali wani abu mai d’umi ya fara zubowa ta jikin ta, sai a lokacin ta motsa idon ta, zuwa kallon jikin nata, sai ta ga jini ne yake zuba sosai, alamar cikin nata yana cikin hatsari, koma yana daf da fita, sai a lokacin taji wani kuka ya zo mata mai k’arfi.

Cikin kid’ima Aliyu yace
“Umma jini a jikin ki, na kirawo miki Babaa lantana? ”
D’aga kai kawai ta iya yiwa Aliyu saboda yanda take jin jikin nata, yayin da Suhaima take kuka sosai, saboda ganin halin da mahaifiyar tasu take ciki, da gudu Aliyu ya fice daga gidan har yana cin tuntu6e da dutse, yana saurin k’arasa wa gidan Babaa lantana mak’ociyar su, domin neman taimakon ta…….

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]