[Advertisements⬇️]

ZUCIYA DA GWANINTA CHAPTER 3 - Bankinhausanovels
Thu. Oct 6th, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

ZUCIYA DA GWANINTA CHAPTER 3

 

 

Kan dan dakalin da ke kofan apartment in su ya ke a zaune yana kallon yanayin garin da ya fara hada hadari. Tun jiya bayan tafiyan ta bai iya kara fita daga side in nasu ba. Daman ya san makarantar will never be the same sabida rashin ta a ciki. Duk yanda zuciya shi ke kwaidata mishi son kasancewa da Nabila, wani lokaci ya kanji cewa anya ba ta mishi karanta ba kuwa?
A haka abokin shi mansur ya zo ya iske shi a wurin. Kaman ba zai mishi magana ba da farkon sai can kuma yace “anya mutumina ba zamu shirya mu bi hanya Kaduna ba kuwa?” Murmushin dole yayi ba tare da ya shirya ma hakan ba. Mansur ya kara cewa “ina ga mafitan kawai kenan” tabe baki Abubakar yayi yace “to wai na ce maka ina son ganin ta ne?” Yanda yayi maganan cike da nuna basarwa ya sa mansur darawa “kai ma ka san ka gaya ma wani amma ba dai mansur ba da kuke kwana daki daya” Abubakar bai kara cewa komai ba sai ma mikewa da yayi ya shiga daki bai dade ba ya fito da gi! bag in da ta bashi jiyan kafin ta fice. Nan gefen mansur ya koma ya zauna, shi dai mansur kallon shi kawai ya ke. Hannu ya sa a cikin bag in ya fiddo wani album. Hard copy in hotuna guda uku ya ciro daga cikin folder, sai da ya gama karewa kyakyawan fuskan da ke cikin hoton kallo sosai sannan ya nuna ma mansur “I have this to talk to in ina son ganin ta” abin ma dariya ya bawa mansur, like who does that a wannan zamanin. Sai da yaga Abubakar ya bata rai sannan ya sausauta dariyan nashi “Ai dole in yi dariya Mutumina, wa ke wani amsan hotunan mace a wannan zamanin? If you want to see her call her video call or better ma kaje gidan su, in dai soyayyan gsky kake mata fa amma”
Dan Jim Abubakar in yayi kafin yace “ba ma sai na fada maka irin son da nake mata ba mansur, you know everything. Matsalan dai in ganin kaman tayi karama.”
Tsaki Mansur ya ja cike da takaici, kalaman abokin nashi kadai ya isa tabbatar mishi shi din bako ne a wannan fagen. “Kaga malam if you like her go get her, mace ba ta wani karanta kawai kai dai ka nemi soyayyan ta, ta yanda za ta amince da kai ko da a gidan su an hana ta sauraran maza ne sai ta shiga jami’a to fa in har tana son ka ka gama. Ai laggon mace kenan ka dana mata dafin soyayyan ka”
Sauraron mansur in ya ke har ya gama sannan ya ce mishi “kai kake ganin ban san halin mata ba, I know everything wannan in dai kawai ina ganin tayi karama ne da irin karatun da nake bukatan koya mata”
Da sauri mansur yace “then teach her everything, irin su ma sun fi saurin dauka” tafa hannu su kayi suna dariya, mansur ya sake cewa “just call her now”
“Ni fa ban ma da numbanta” sakin baki mansur yayi yana kallon shi “tab! Maganan babba ne, to kai ta ya akayi kayi gangancin nan? Amma we have many ways of getting her number” da sauri Abubakar yace “no need, I give her a letter daren grad insu, if she feel the need za ta kirana, na rubuta mata numbana”
A bangaren Nabila kam, bayan ta koma daga rakiyan Anty salma dakin da ta ke sharing ita da Amina ta nufa da tunanin coper Abubakar wanda ya ki barin ta sam ta sarara. Tun dazu ta ke tunanin abinda ya bata ana washegari graduation, wanda ta dau mishi alkawarin lallai lallai sai ta isa gida za ta bude.
Gi! bag ne na musamman, gabadaya ta zazzage jakan kan gado tana son ganin mai ya kunsa. Karamin kwalin da ya fara jan attention inta ta fara dauka, silver ring da bracelet ta gani masu dankaren kyau, ita kadai tayi dariya tana fadin “Allah sarki sir nagode” a fili. Unwrapping in sauran tayi. Books hard copy ne guda hudu, biyun novel na Collen hoover da Danielle steel, if she can remember ya bata lbrn books in tace za su yi dadi, wato shine yaje ya siyo mata. Biyun kuwa motivational book ne da poem collection. Dan note in da ta gani a gefe books in ta dauko tana dubawa. Handwritten in shi ne
“i hope you can read this books to avoid doing nothing at home before you start seeking for admission.
Abubakar Sadiq Mambila”
Ba ta san sanda ta rungumo littatafan tana kara kallon handwriting in shi ba, a zuciyan ta tana raya sir bai mata adalci ba da ya amshi hotunan ta shi kuma ya ki bata nashi duk da ta bukaci hakan.
Ajiyan zuciya ta saki kawai ta kwashi gi!s in tana kokarin mayar wa cikin bag in. A nan ta ga wani karamin envelope da tun tuni bata ankara dashi ba. Read me ne a rubuce a jikin shi. “Yanzu kuwa” ta fada a fili sannan ta yaga close envelope in ta gefe ta ciro papern ciki.
“Slm Nabila.
How can i even write this? Nothing seem like the right thing. All i know is, my heart is so heavy as am writing this. Not knowing the right way to express my ache. Is it the intense feeling i always have or my heart beating on to your name? You stop me from being so lonely, so how will i cope when you are not here? I never want to lose you, girl you are my everything.
I want to be with you for the rest of my life. This is a proposal, one which need to be considered. Just gave a thought about it beautiful. Call, 08xxxxxx. For a positive response. Hope i won’t be waiting forever.
Abubakar Sadeeq Gembu.
Har ta gama karanta gabadaya abinda lettern ya kunsa ba zata ce ga exact halin da take ciki ba. A hankali abubuwan da kawayen ta su ke fada mata kan Coper Abubakar in ya fara dawo mata. “Beela mutumin nan fa ya fada wlh”
“Beela kinga irin kallon da coper Abubakar ya ke miki kuwa?”
“Ke Beela ki fada mana gsky kawai, yanayin ki fa gabadaya canjawa ya ke in kika ga mutumin nan”
“Wannan irin murmushin da kuke wa junan Ku?”
Ba shakka kusan dukkan abinda su ka fada gsky ne in aka cire sharri irin na yan makaranta, wanda a jinin su yake. Kenan hakan yana nufin ba shi kadai ya ke son ta ba ita ma tana son shi? To in ba haka ba me ya hana ta katse shi jiya da yayi kissing inta bayan kuma tana da ikon yin haka? Abubuwan da ke ta mata yawo aka kenan.
Abinda ta fahimta a ciki shine, labarin da friends inta ke bata ya sha banban da irin nata. La’akari da su nasu a fatar baki ya tsaya amma nata fa? Har yanzu abun ya kasa shiga kwanyar ta, duk da a daren jiya har mafarkin shi tayi. Lettern ta kara bi da kallo dai dai inda numban shi ya ke rubuce. Ba ta tsaya wani dogo tunani ba ta dauko wayan ta kwashe numban. Ko bakomai ai akwai zumunci tsakanin su, ta riga da ta san ba zata taba iya mantawa dashi ba ko da ko ta so hakan.
Har za tayi dialling numban shi sai ga Amina ta shigo. Tana zama kan gadon idanun ta ya fada kan papern da ke hannun Nabeela. “Har kin dawo? Nabeelan ta tmby, ba ta tanka ta ba sai ma kokarin amsan takaddan da tayi a hannun ta. Da sauri Nabeelan ta dauke hannun ta ” ke miye haka? Daga ganin abu a hannuna sai kice zaki amsa?”
Dariya Amina tayi tace “Beela na san saurayin ki ne ya baki ai” da ke bata da gsky nan da nan fuskan ta ya nuna, duk da haka sai da tace “To ina ruwan ki? Yaushe kika fara sa ido” fada fada ta ke maganan. Ita dai Amina dariya take tace “Afuwan Sis kawai dai nasan jiya da Abbah ke ta Neman ki, wurin shi kika je” nan kam dole ta juya da mamaki tana kallon kanwar ta ta, tsakanin su duka duka shekara daya ne kawai da yan watanni. Yanayin ta kadai ya isa sa Aminan dariya, da dan karfin tace “Yeah i guess right” tsaki taja don ita duk a tunanin ta wani ne ya fada ma Aminan.
“Sis ni fa kawai yanayin ki nagani na gane”
“You are crazy sis ta ya ake gane yanayin mutum to?” Kai tsaye Amina tace “like if you experience it, kana ganin mutum za ka iya dagowa”
“Ke kina da experience in kenan?” Ba ta amsa taba sai dai irin murmushin da ke fuskan ta ya tabbatar mata da akwai kenan. “Who is the guy then?” Zaro idanu Amina tayi tace “kaji sis fada min naki mana ke, I promise zan fada miki nima”
“Ni fa ba saurayi na bane kawai service yazo school in mu, muka saba sosai dashi shine yanzu yace yana so na” tana maganan ne tana jin shi wani banbarakwai, ba wai ta saba irin maganan da Amina bane. Suna dai haka abun su su birne amma banda irin wannan issue in.
“You must have like him too” Ba tare da wani reaction ba tace “Haka kowa ke cewa, now tell me about yours” da sauri Aminan ta rufe idanuwan ta “Don’t laugh at me amma fa sis, Ya Amir ne yayan Sofie” Dariya ko sosai Nabeela tayi “Seriously? Shine fa kika ce min ba ki son zuwa gidan su Sofie saboda baki son ganin shi, you don’t like him” ita kanta Amina dariyan tayi “That was then sha, har fa ya fada wa Abbah, amma Abbah yace mishi ya bari ko za a fara maganan sai ma gama secondary amma wai ya amince dashi” zaro idanu Nabeela tayi jin zancen is serious har haka “ke sis SS2 fa kike, yau…”
Da sauri Amina ta katse ta “Ai ance miki fa sai na gama secondary zama ayi maganan. Jiya ma ya tafi masters a India, yace by the time ya dawo nima a dai dai kenan” rike haba Nabeela tayi tana kallon Aminan da ke ta fama kwararo mata bayani. A gefe ranta kuma tana jin wani relief, kenan ita ma inta gabatar da Coper Abubakar yanzu Abbah ba zai mata fada ba, tunda ita ta ma gama secondary in.
“Kuma Abbah na barin shi ya zo wurin ki?” Hararan ta Amina tayi “na fa ce miki ance sai na gama, ni ko a gidan su bama wani magana sai dai waya kuma shima ba ko yaushe bane ma, ya dai fi turo min text kawai sai in mishi reply. Amma ke tunda kin gama kawai kice mishi yazo”
“Ni fa ban son aure da wuri Allah” Kaman zata yi kuka ta ke magana, Amina tace “to in lokacin ne yayi ya za kiyi? Ki dai bashi chance kawai” still nervous rasa abin yi tayi sai Amina tace “to wai shi bai zai kira ki bane?”
“Bai da numbana ai, ya dai bani nashi wai in na amince na kira shi”
“Ki kira kawai Sis, ni bara naje na daura dinner kafin Mami ta shigo ta fiddo ni”
Kallon wayan ta ke tana contemplating akan kiran. Normal da su ke hiran su ba tare da taji ko da dar ba amma tun daga jiya ta san dole a samu canji a yanayin yanda suke, to balle kuma ga letter a rubuce da komai. Da kyar ta iya danna call in ta na kallo har ya Shiga. Duk karan wayan yana kara sautin bugun zuciyan ta ne. Duk da idanun ta na kan screen da ke fargaba ya dauke mata hankali sai bata lura da daga wayan da aka yi ba. Kwatsam dai amsa amon muryan shi taji yana furta hello hello, ita ta ma dauka tunani kawai ta ke. “Ya dai Hello” ta kara jin sautin muryan nashi a bayyane. Kaman Mara gsky tayi saurin kashe wayan ba tare da tayi maganan ba. Sai dai kuma ta dawo da kanta tana jin takaicin abinda ta aikatan. A dan sanin da ta mishi ta san ba zai yi calling back tunda ba tayi magana ba. Ita dai kadai abinta tana kwance kan gado tana ta juye juye, da sauri ta mike zaune ta jawo wayan saboda da dabaran da ya fado mata. Tun jiya Abbah ya sa mata credit, Subscription tayi ta kunna data. Messages ne su kayi ta shigowa dole ta bari su ka gama sannan ta gane daga group in mate insu ne wannan uban SMS in, sai da ta gama karanta wa tsaf sannan ta yi magana. Nan da nan ko hiran ya tafi da ita barin ma da aka dauka babin performance in da ta yi. Headboy insu ne ya turo Videon a kasa ya rubuta “Gsky you did very well Beela, kinga yanda kike trending a Instagram kuwa?” Sai lokacin ma ta tuno tana da Instagram Account. Bude videon tayi, ita kanta sai da abun ya kayatar da ita. She can’t even believe yanda ta yi kokarin tattaro karfin guiwan yin abun. Sai lokacin ta kara jin takaicin yanda ta kasa ma Coper Abubakar in magana a waya, tasan da bashi, ba ta yanda za ta fara kokarin yin performance in.
Fita tayi daga group in ta lalubo numban shi, wanda tayi saving da Sir kawai.
Unknown: ”Assalam Alaika”
tayi typing ta tura mishi. Ba ta ma duba ko yana online ba Sai dai kawai ta taga har ya karanta.
Sir: “Alaikisallam, Nabeelarh?”
Da farko mamakin yanda ya san numban tayi Sai kuma ta tuna pic inta dana Aiman da siyama ne a dp inta.
Gogan kuwa wani irin dadi yaji har cikin kan shi, tun dazu ya ke tsimayen ta.
Nabeelarh: “Nice sir, ina wuni?”
Sir: “Lafiya kalau, Ya kika je gidan? An samu kowa lfy, I hope kuma ba gajiya?“
Nabeelarh: “Alhamdulillah” kawai ta mishi sending
Sir “Ya kuma bayan rabuwa?” Ita kam har ranta ba ta son wannan jimlan da ake ta fada mata tun safiyan yau. Ba ta amsa shi ba saboda rasa abin ce mishi da tayi
Sir “Nabeelarh” Ya kira ta.
Nabeelarh “Naam sir, ya kano?” Dan darawa yayi yana kallon screen in
Sir “Kano ba dadi Nabeelarh, kun bar mu da kewan Ku ba”
Nabeelarh : ”To sir ai kuma kun kusa gamawa Ku tafi“
Sir : ”“still not the same. You must read my letter”
Daga nan kuma rasa abun ce mai tayi for some minutes tukkuna ya kara rubuto mata.
Sir: “Talk to me mana Nabeelarh” Nabeelarh: “Yes na karanta”
Sir: “Then what do you have to say about it”
dif tayi tana kallon screen in, duk wani amsa da ta hado za ta aika mai Sai taga kaman bai yi ba. A haka har aka kwashi kusan mintuna biyar.
Nabeelarh :“I have seen your gi!s, I like them all, nagode sosai”
Sir : “Let me call you”
Kafin ta samu daman amsa shi ma Sai ga call in shi na shigowa. Da kyar ta tattaro natsuwa ta daga wayan, ta kanga kan kunnen ta. Yana sauraron ta ya mata sallama ta amsa.
“Nabeelarh kika ce kin karanta letter na ko?” Cike da kunya ta furta “Ehmm”
“Okay, ya kike gani to?” Kasa magana tayi har sai da ya gaji da kan shi yace “To ko dai inzo Kadunan muyi magana ne?” Zaro idanu tayi kaman yana gaban ta tace “kaiii!”
“Me nayi ko Abbah zai yi fada ne?” Haka kurun taji idean zuwa gidan su bai kwanta mata ba, to mai ma zata cewa Abban? Za tayi bako komai? Ita kam ba taji zata iya. Duk da wani zuciyan yana fada mata come on kanwar bayan ki Amina tayi mai kike jira?
Katse mata tunanin yayi “Why the sudden silent Nabeelarh, ko kunya ta kike jine?”
“Aa kawai dai…” Ba ta karasa zancen ba tayi shiru. Yace “okay are you in?”
Rashin abince wa yasa tace “With what?”
“The R/ship mana. I just need the chance angel, Eventually you will come to get use of it”
Cikin narkakkiyan murya tace “Okay”
“Kin amince kenan?” Da sauri tace “Ehmm” ta katse wayan. Runtse idanu Abubakar yayi, da dan karfi yace “Yes! I get her”
Nabeelaru kam grinning tayi tayi bayan ta kashe wayan, she suddenly gone crazy, kanta ta wulla cikin pillow tana ta dariya kasa kasa. Taji dadin yanda bai tursasa ta akan sai yaji ra’ayin ta game dashi ba, he seems considerate. Ita kanta she can’t be sure ya ta ke feeling amma kuma since from the start Cooper Abubakar na matukar burge ta, tun daga ranar da ya shiga ajin su a matsayin wanda zai maye gurbin tsohon English teacher in su da yayi Resigning.
Vividly, tana iya tuna ranar. Immediately a!er break ne English period in. Da migraine ta tashi tun safe, ko lokacin break in ba abinda ta iya kaiwa baki. Kanta na kan table ya shigo Class in, Sama sama ta ke jin maganan shi yana introducing kan shi wa class. Daganan kuma ba ta san ya akayi ba sai ji tayi ana bubbuga desk in nata. Da narkarkun idanun ta da suka canja launi gabadaya zuwa ja ta dago ta zuba mishi su cikin idanun shi. From her look ma kadai ya isa ya gane ba ta jin dadi amma sai da yace “Why are you sleeping during class miss?” Kusan gabadaya ajin su ka hada baki wurin fadin ba ta da lafiya ne.
“Then go to the sickbay please” squeezing face inta tayi, Sickbay disgusts her sosai ta tsani warin asibiti barin ma da ta san ko sun bata maganin she had to sleep kuma ba za ta iya bacci a wurin ba, dormitory insu kuwa kulle shi ake sai a!er classes.
Ganin yanda tayi da fuskan ta yasa yace mata “Any problem?” Zainab ce tayi saurin ce mishi “Sir she don’t like hospital, the smell iritate her” Jinjina kai yayi in an understanding ya fara koyarwa. Sai da period in ya kusa karewa ya cewa Zainab “me ke damun ta”
“Migraine ne”
“Oh! Sannu, did she take any medicine?”
“I don’t think so” ta bashi amsa, dan buga mata desk in yayi ta dago, rinannun idanun nata ta kara zuba mishi, a ranta tana mita yana takura mata. “Wani irin magani kike sha in migraine in ya taso miki”
Fada mishi sunan maganin tayi, ya fita daga ajin. Ba dadewa sai gashi ya dawo da goron faro, maltina da kuma sachet in maganin a hannun shi. Zainaba kawai ya mikawa ma wa “Make sure ta sha fa and the maltina will help her saboda kar maganin ya dinga tada mata zuciya” godiya zainab ta mishi, yayi murmushi ya wuce. Nan fa yan makaranta su ka hau gulma. Har da masu rantse Nabeelarh ta birge shi ne shiyasa ya mata haka, ita kam tafi daukan hakan a matsayin tausayi kawai.
The next day ko yana shiga ajin, ita ya fara tmby jikin ta. Ta amsa da sauki sannan ta kara mishi godiya. Coincidentally, lokacin figure of speech ne topic in da ya fara covering, Nabeelarh kuma guruwan English ce, it her favourite subject duk malamin English in da ya dauke su sai ya gane hakan. Sai ya zamto duk tmbyn da zai yi hannun ta ya ke fara gani kuma ta bashi accurate answer sannan ita ma tana yawan tmby.
“I know you are all science student but is their anyone that can write poem among you” shiru ajin ya dauka. Ya kara cewa “Okay, anyone interested?” Nan ma ita ta fara daga hannu, murmushi yayi saboda yayi expecting hakan “What is that your name?”
“Nabeela Usman mainasara” gyada kai yayi yace “very nice Nabeelarh, I will tutor you” Tun daga ranar a!er prep su ke haduwa, sai ya dawo ma ba poetry kadai ba har wani abubuwan na English literature da basic English in yana koya mata. Daga haka suka fara sabawa kafin sabawa yayi taking turn daban.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]