[Advertisements⬇️]

RAYUWARMU A YAU CHAPTER 3 - Bankinhausanovels
Thu. Oct 6th, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

RAYUWARMU A YAU CHAPTER 3

 

Salmeert haka ta anshi kud’in tana godiya ta tafi gida, tana mai jin dad’in wannan kud’in da aka basu, da sallamah tashiga gidan…. Mama ta d’ago kanta tana ansa sallamar Ta ce ” ‘Y’ar albarka kin tadda Kawunki din agida.?..

Ta ce” eh Mama na tadda shi gashi sak’on .Ta ansa tana mai jin dad’in dayi masa Addu’a Salmeert ta ansa da ameen Mama..

 

Fannin su Ammar kuwa yana gama cin abinci ya tashi yana cema Momma ya tafi part d’in su Baffah….

Ta  ansa mashi da sai ka dawo Son en ka dawo ina ciki gurin daddyn ku.

Ya ce” toh Shikenan Momma

Yafita bai zarce koh enaba sai part d’in su Aysha….  Yana shiga yaci karo da Baffah zai fita.. Ya ce” takwaran Alhaji sai Yan zu ake ganin ka? “Ya d’an sadda  kai k’asa yana murmushi Ya ce”  Baffanah ina yini ya hanya an dawo lafiya ….. Baffah ya. Ansa da lafiya k’alau Alhamdulillah ya aikin?

Ya ce”  Alhamdulillah jibi mazantafi Lagos sun turani wani aiki…. Baffah Ya ce”  to toh masha allah Lagos zakaje kennan…. Ya ce”  Insha Allah. Baffah Ya ce” ka shiga kagaisa da Umman ku tana ciki ya ansa da toh Baffah…

 

 

Kinga Salmeert ansa kud’in nan ki kaima Malam Bala mai shago, kice masa nagode sosai kiyi sauri ki dawo kizo kitafi makaranta kinsan lokaci yakusa….. Ta ansa kud’in tafita ta tafi  cikin tafiyar tannan mai sanyi wadda haka Allah ya haliceta da sanyin hali Wanda zamu iya cewa agun Mama tagado…

 

 

Ammar Nashiga ya fara Addu’a da Aysha zataje part d’in Hajiya kakah (kakarsu kennan) …. Tana ganin shi tasaki murmushi Ta ce ” Yaya ina yini fuska a tamke ya ansa da lafiya ya huce ciki..  Ita  ko tabi bayanshi da kallo ta k’isima wani Abu cikin ranta Wanda ni (AUTAR MAMA)  bansan mai take k’isimawaba kawaida naga tana sakin murmushi…

 

Da sallamah ya shiga  pallon…. Wata mata tafito  cikin wani dan corridor tana ansa sallamar….. Wani murmushi ne naga tayi Wanda za’a Iya kiran sa da yak’e  tasaki,  tana cewa wana ke gani haka kamar dan Baffah Ya yi murmushi shima Wanda baikai cikiba Ya ce” aikoh dai nineh ina yini…… Ta ansa masa tana cewa ka zau na mana Ya ce” a’a Dama nazo gaishe da Baffah nane Ta ce” aikoh yah fita.. Ya ce” munhad’u dashi yan zuma gurin Hajiya kaka zanje nagaishe ta…. Tace toh shikenan ka gaisheta da Momman taku…… Ya ce” toh zasuji Insha Allah .. Ta ce” toh yafita tabi bayansa da harara tana cewa cikin ranta Insha Allah sai naga bayan zuri”arki Fatima(momma)

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

A raina nafita ina mamakin maiyakawo kuma batun ganin baya tsakanin Momma da Umma..

Hakanan nayi Kama dan bakina nayi shiru saboda bani da mai bani ansa•••••••••••••••••••••••••••••

 

B’an garen salmeert kuwa chan nahango ta tafi ya da alama dai harta kai sakon ta dawo haka muka jera muna fira kasa kasa har mukazo gida muka  shiga…… Mama Ta ce” har kin dawo? Ta  ce” eh Mama..

Mama Ta ce” toh maza ki shirya ki tafi makaranta.. Ta ansa da toh Tana gama shiryawa ta dauki Jakarta Ta ce” Mama na tafi……. Mama Ta ce” toh Nima zanje kasuwa kuma ina tunanin Killan inyi dare, dan haka idan kika dawo kikaga Gidan kulle kije Gidan su Rukayyat kijirani….  tace toh Mama na saikin dawo tafita tana tafiya  a tsanake kuma sanye da uniform d’in makarantar Islamaya maroon collor, kayan sunyi masifar yimata kyau, Dama wahalar da take ciki ya disashe mata farin da taje dashi…..

 

 

 

 

Tana cikin tafiyar sai taji ance keeeeeeeh! … Aida sauri ta juyo tana kallon wacce ta firgitata tana juyowa ta bata rai tana cewa banason haka fa Ruqayyat kinga yanzu kin firgitani….

 

Ruqayyat tana murmushi Ta ce” yi Hak’uri Besty  ban san Zaki firgitaba….

 

Hararar ta salmeert tayi Ta ce”naji aku Uwar Iya tsara zance

 

 

  • ••••••••••••••••••••••••••••••••bangaren Ammar kuwa baima san tana hararar shiba ya cigaba da tafiyar sa ,ganin haka Nima nabi bayansa muka shige pallarn Hajiya kakah… Can muka tadda daddalar Yaran Gidan Manya da k’anana, Wanda zasu kai su goma Manya shidda k’anana hud’u, a cikin Manyan akwai Ameera, Aysha, Khadija, Mus’ab, Abdallah, da kuma Muhammad…..

 

 

 

K’anana kuwa sune su Ilham, Ayman, Haneef da kuma Amsad

 

 

 

 

Sai aci gaba zakusa wayan nan Yaran waisu mai menene alakarsu da Ammar?

 

 

 

Wannan litafin na kudine amma zanyi free page daga 1 har zuwa page 30 duk free ne amma daga nan za”a fara biyan kudi

 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]